Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Tsutsar Nama Book 2 page 28

 𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_

       _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕_



......Washe gari Mom ta tashi da shirin komawa sashen da akaima gyara. Sai dai tsabar wuce wuri batayi hakan kai tsaye ba ta shiga gayyato ƙawayenta da maƙwafta ta waya wai zata shirya walimar komawar tare da bikin baikon Baby. Aiko zuwa sha biyu sai ga gida cike da ƙawayenta da maƙwafta da take ɗan gaisawa da su. Gida fa yaci decorretion harda su dj. Ana gab da fara shagali Gwaggo Gudidi da yaranta da wasu a dangi suka fara isowa da kulolin abinci. Duk da al'amarin ya bama Mom matuƙar mamaki sai tayi ƙoƙarin ajiye komai gefe tai tunanin ko Abba ne ya sasu suzo dan su tayata murnar baikon Baby ɗin. A take kuwa ta hau musu gwalangwaso har da habaici ƙawayenta ke jefa musu. Isowar su Gwaggo Gudidi baifi da mintuna talatin ba sai ga mata har mota guda daga Gwarzo. Sai ga Musaddiq da ruwa da drinks masu yawa. Anan ne fa al'amarin ya fara girmar kan Mom, ta tare Musaddiq da tambaya. Rasa amsar da zai bata ya sashi faɗin, “Mom kuyi magana da Gwaggo kamar zaifi”. Daga haka ya juya yay ficewarsa ya barta da kallon kallo tsakaninta da ƙawayenta. Zabura tayi hankalinta a tashe zata fice a ɗakin dan dama kwalliya ake mata ƙawayen nata suka dakatar da ita. Sune suka tausheta kan ta dakata dai Abban ya shigo taji mike faruwa a bakinsa kamar zaifi. Badan taso hakan ba ta dakata sai dai ta shiga dokama Abba kira ta waya dan rabonsa da gidan tun da safe. Shiru bai ɗauka ba har kusan kira biyar, sai da wata ƙawar tata dai ta fargar da ita lokacin salla ne maybe yana massalaci sannan ta dakata. Bayan kamar mintuna biyar dan ita ko sallar ma bata nema yi ba, dama can ba damunta tai ɗin ba balle yanzu da aka zuba kwalliya. Bugu ɗaya kuwa Abba ya ɗauka, sai dai tana fara magana ya dakatar da ita da cewar gashi nan tafe gidan. Wayar ta cillar tana kaiwa zaune wutar bala'i na cin zuciyarta. Ko mintina ashirin kuwa ba'a cika ba su Abba suka iso. Tsaiwar motoci da jin buɗe-buɗe ya saka zuciyar Mom harbawa da masifar ƙarfi. Hakama ƙawayenta gaba ɗaya sukai tsitt da surutun da sukeyi dan tabbatar da inda ghuɗa ke fitowa....


       💞✨💞✨💞


        Muna fitowa mukaci karo da mama Balki. Ita ta bama umarnin rakani sashen ita kuma tayi gaba. Gani nayi Mama Balki ta sauke ajiyar zuciya. Kamar ba itace duk na ga cikin damuwa ba yanzu. Har ƙofar da zata sadani da sashen nasa dake ta cikin main perlor ta nuna min. Nai mata godiya na shige kaina tsaye dan naji farin cikin sakani wannan aiki da akayi. Hanyace mai ɗan tsayi daga main perlor ɗin kafin akai ainahin sashensa. Tun daga cikin dogon corridor ɗin zaka iya shaida mayataccen ƙamshin turarensa da baya ɓoyuwa a duk inda yake. Baki na taɓe tare da yamutse fuskar takaici. Dan ni kaɗai nasan kalar rashin mutuncin da yau zan zazzage masa tunda na samu damar ganinsa matsoraci kawai, ba ruwana da rashin lafiyarsa ba raga masa zan ba. A rufe ƙofar da zata sadaka da sashen nasa take. Dan haka na danna bell da ɗan ƙarfi ina hararar ƙofar. Shiru babu alamar za'a buɗe min har cikar minti ɗaya. Sake dannawa nayi nan ma shiru, na bada wasu sakanni babu dai alamar za'a buɗe ɗin. Cikin fusata na danna bell ɗin da ƙarfin tsiya batare da na ɗaga yatsana a kai ba harda su cije baki. Sai gashi kuwa an buɗe ƙofar kamar a fusace. Baki na taɓe da ɗaga ido dan ganin wanene ya buɗe ɗin, sai a cikin mayun cat eyes ɗinsa kuwa. Yanda yay wani masifar yin kicin-kicin da fuska gashi ya tsatstsareni da idanu ya sani sake tamke tawa nima ina laɓe baki. Ɗauke nasa yayi tare da juyawa ya bar wajen. Da kallo kawai na bisa cikin yanayin harara. Sosai ya zube a tsaye cikin ƙanƙanin lokaci, sai dai a zahirance bazaka taɓa ma yarda baida lafiya ba dan yana nan a dakensa. Kamar bazanbi bayansa ba sai kuma dai nabi shawarar da zuciyata ta bani, dan haka na sunkuya na ɗauki basket ɗin nabi bayan nasa ina kwaikwayon yanda yake tafiya. Ina saka ƙafata a katafaren falon da ya haɗu ya gama haɗuwa shegen karen nan nasa dana taɓa gani a Kano ya taso a zabure. Ai bamma san na fasa ƙara da ƙoƙarin sakin tray ɗin ba. Sai dai jin ban faɗi ba ni da tray ɗin ya sani buɗe idanun nawa a hankali ina mai sauke ajiyar zuciya. Kallon cikin ido mukaima juna. Ban san lokacin da numfashina ya fisga ba alamar neman barin ƙirjina da gangar jikina, da ƙyar na fisgoshi na maidoshi cikin ƙirjina ina sake waro idanun nawa waje gaba ɗaya. Shima sake tsatstsareni yay da nasa tamkar zai cinyeni da su duk yanda naso haɗiye razanata ta ganin karen nasa tsaye a kusa damu na kasa hakan. Illahirin jikina da duk wata gaɓa da jini ke gudana ta cikinta sun bar aiki. 

           “K! Baki gajiya da pretending ɗin faɗuwa dan a tare ki”. Ya faɗa a daƙile cike da rainin wayo.

      Har cikin tsakkiyar kaina naji haushin furucin nasa. Da sauri na sakesa gaba ɗaya tare da ƙoƙarin turashi nima nai baya. Sai da me ko gezau, yana nan a tsayensa ƙyam saman ƙafafunsa tamkar dasashiyar bishiyar data kafu a muhallin daya dace da ita. Kallo ɗaya yay min da shegun idanun nan nasa kalar na maguna ya janye tamkar bai fahimci abinda na jima haushin ba. Ga fuskar tsamm babu alamun rahama ko sassauci balle ma kai tunanin yayi maganar ne dan raha. Duk yanda naso janye nawa idanun daga kansa na gagara hakan saboda tsabagen shiga mamakin mutumin nan da rashin mutuncinsa ga shegen sonma mutane sheri. Kamar ko yasan mi nake tunani akan nasa ya raɓani ya wuce yana mai kiran sunan shegen karen nasa acan ƙasan maƙoshi. Da gudu kuwa ya bisa yana wani kaɗa bindi. Da harara ba rakasu su duka tare da ajiye basket ɗin hannun nawa ina bin falon da kallo. Dan babu ƙarya ya haɗu iya haɗuwa. Karaf kuwa sai idanuna suka sauka akan wayoyinsa dake a saman Centre table ɗin har uku, sai laptop a gefensu. A take wani tunani yazo min. Cike da rawar jiki da zumuɗi na ɗauka ina addu'ar ALLAH yasa babu password. Sosai na sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, tare da shiga loda number ɗin Mansoor. Cikin sa'a kuwa ta shiga. Sai dai harta yanke ba'a ɗaga ba. Kamar zan sake kira sai kuma na fasa na saka ta Yaya Musaddiq. 

      “Mr M” ya fito ɓaro-ɓaro. Da mamaki nake kallon sunan da sake duba numbers ɗin. Number ɗin Yaya Musaddiq ɗin ce dai. To miya kawota cikin wayar wannan mutumin? Bani da mai bani amsa, dan haka nai dialing kawai dan tabbatar wa. Bugu biyu kuwa aka ɗaga, na ɗan yi shiru. Sai ko ga muryar Yaya Musaddiq tar-tar yana sallama. Sai dai muryar tasa a ɗashe alamar barci ya tashi ko yake son yi. Maimakon amsa sai hawaye suka cika min ido. Muryata na rawa na furta, “Yaya!”.

     Ina jin alamar yanda ya zabura. Sai kuma cikin rawar harshe ya furta, “Samraah ke ce?”.

      Kuka na sakar masa kawai maimakon amsawa. Sai naji duk ya sake rikicewa. Kukan na sake fashe masa da shi da faɗin, “Yaya anya kana sona har yanzu kuwa?. Tsahon wata guda mutumin nan ya sace ni ya sace min Mansoor ɗina amma babu ku babu labarin ku. Yaya ina Mansoor ɗina kada ya halakar min da shi.....”

         Cikin wata irin sautin sauke ajiyar zuciya Yaya Musaddiq ya tari numfashina. “Samraah relax. Ki kwantar da hankalinki, babu wanda ya ɗauki Mansoor yana gidansu. Shi kuma wannan ɗin shine mijinki yanzu ba Mansoor ba. Yayanki kuma na sonki har gobe da jibi da gatan gata ma”.

      “Yaya!!!”.

    Na faɗa a matuƙar razane jikina na rawa, dan duk da shi ɗin ya sanar min shi mijina ne jin tabbaci a bakin Yaya Musaddiq ɗin sai ya sake sakani a matsanancin ruɗani. Sake tareni yay da faɗin, “Nace ki kwantar da hankalinki dan ALLAH Samraah. Yanzu yaya jikin naki kuma?”.

     “Yaya taya kake son na kwantar da hankalina? Ta yaya kake son kaji naji sauƙi? Bayan an ɗaura min aure da Mansoor na ganni kuma tare da wani ace na kwantar da hankakina”.

         “Samraah dama ba'a ɗaura miki aure da Mansoor ba. Da shi ɗin dai wannan mai suna Muhammad aka ɗaura miki aure. A yanzu kuma shine mijinki. Ki manta da Mansoor da duk abinda ya shafesa dan ALLAH ki fuskanci sabuwar rayuwarki da in sha ALLAHU muna fatan bazamuyi nadamar kaiki cikinta ba. Haba Samraah kefa mai ilimice. Har kin manta da wannan rayuwar izayar ta gidan Abba da kika sha ne?”.

    Baki na buɗe zanyi magana hawaye na rige-rigen sakko min kawai naji an zare wayar. Gaba ɗayana na juyo, dai-dai yana yanke kiran da jefa wayar cikin aljihun wandonsa. Afusace nake kallonsa, shima ɗin kallona yake tsakiyar ido. Tsahon minti ɗaya muna a haka batare da ɗayanmu yayi yunƙurin janye nasa ba wayar daya ƙwace a hannun nawa kira ya shigo cikinta. Nasa idanun ya janye tare da zaro wayar daga aljihun daya sakata, ya ɗan tsira mata idanu na sakani kafin naga ya kaita kunnensa tare da barin wajen ya nema kujera ya zauna. Da farko ban fahimci dawa yake wayar ba, sai da ya ɗago ya kalleni cikin yanayin ɗage gira da amsar da naji ya bada sannan. Da sauri na nufesa, babu zato yaji na zare wayar nima kamar yanda yay min. Kafin yay wani yunƙuri na nufi ƙofar dana shigo da gudu. Sai da naje jikinta sannan na juyo na masa gwalo nai ficewata.........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



Post a Comment for "Tsutsar Nama Book 2 page 28"