Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Tsutsar Nama Book 2 page 27

 𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_

       _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏_



.......“Sai idan Alhaji Ƙarami baya nan suke mata hakan. Da sunga zai dawo suke kwanceta su dawo da ita falon nan na farko shiyyasa bai sani ba. Yau ɗin ma ALLAH ne yayi da rabon zai gani kuma akai sa'a sarƙar taci mata jiki dan kwana biyu kenan da ɗauretan randa yay tafiya. Da alama kuma basu san yau zai dawo gidan ba ne shammatarsu yayi. Ban kuma san yaya akai yaransu basu sanar musu da shigowarsa ba dan mafi yawan masu aikin gidan nan su sukema aiki”.

      Kasa daurewa nayi a zafafe na ce, “Mama dan ALLAH su waye wai?, Nasan dai harda Hajiya Mammah ɗin nan ko?”.

     Kai ta girgiza min tana miƙewa. “Duk yanda kike tunanin al'amarin ya wuce haka kandala. Ke dai kawai kar ki saka kanki a masifa”. Daga haka ta nufi hanyar fita abinta.

       Badan naso ba na yarda na haƙura. Sai dai maganganunta sun sake ruɗar dani matuƙa. Har takai damuwar dana sakama raina ta sake assasa zazzaɓina. Dan yinin ranar gaba ɗaya a kwance na yisa rijif cikin ciwo har washe gari ma. Sai a cikar kwanaki uku da faruwar al'amarin zuwa yamma ya ɗan sakeni naji dama-dama. Amma a haka Hajiya Mammah ta aiko a kirani a wannan ranar. Cikin dauriya da ƙarfin hali na isa sashen nasu. A falon ƙasa na samu su Azizat zaune kowa na harkar gabansa. Ko kallon inda suke banyi ba nai nufin wucewata. Amma sai kawai gani nayi ansha gabana. Ban yi niyar ko kallon ma wanene ba, na raɓa zan wuce aka sake shan gabana. A hakan ma ɗauke kaina nayi na koma damana nan ma aka sha gabana. Runtse idanuna nayi da ƙarfi tare da cije lips ɗina ina ƙoƙarin controlling kaina. Kafin na ɗago gaba ɗayana babu alamar wasa a tattare dani. 

       “Oh da kika ɗago a fusace kamar wata zakanya zaki dakeni ne?”. Maleeka ta faɗa a wulaƙance cikin huci. Maimakon amsa murmushi na sakar mata mai sanyi. Sai kuma na lumshe idanun na buɗe cikin yanayin isa da ƙasaita. A hankali na motsa lips ɗina na furta, “Karki fara abinda bazaki iya ba. Dan wannan kogin ko manyan jirage da takatsantsan suke gittashi balle ke da baki wuce matsayin jirgi mai saukar angulu ba”. Daga haka na raɓata na wuce abina. Da alama hausar tawa take ƙullawa da kwancewar fassarawa. A falon sama na sami Hajiya Mammah ɗin da Alaja. Cikin girmamawa na gaishesu, Hajiya ƙarama ta tambayi yaya jikina. Na amsa mata cikin nuna jin daɗi da kulawarta. Baki Hajiya Mammah ta taɓe, kafin ta kalleni a wulaƙance ta jefo min tambaya. “K kin iya girki?”. Ɗan jimm nayi kamar mai tunani, sannan na amsa mata da, “Eh na iya Mammah.”

       Sai da ta ɗan ƙara taɓe bakin ta cigaba da faɗin, “Kije ki mun abu mara nauyi yanzun nan. Ba kuma nason ɓata lokaci”. Kaina na jinjina mata ina miƙewa. Dai-dai zan bar wajen muka haɗa ido. Sosai zuciyata ta harba da ganin wani irin shegen kallo da take bina da shi na ƙwaf-ƙwaf. Sai dai ban kawo komai ba nai tafiyata ina mai karanto addu'ar neman tsarin ALLAH daga sharrinta gareni. Inda nabar ƴammatan gidan anan na sake samunsu. Sai dai a yanzu hankalinsu baya kaina, amma da alama cecekuce da zagin da suke duk a kaina ne, dan haka har na wuce basu sani ba. Karo na farko na fara shiga kitchen ɗin gidan. Da mamaki su Aunty Kubrah duk suka watso min idanu, cikin dakiya na gaishesu tare da sanar musu abinda ya kawoni kitchen ɗin. Sai gani nai Aunty Falilah da Aunty Kubrah ɗin sun kalla juna suna yamutse fuska. Kafin Falilah taja tsaki ta cigaba da aikinta. Hakan da sukai min yay min ciwo, dan haka nima na watsar da su na ƙarasa shiga kitchen ɗin ina kallon tsarinsa da haɗuwarsa tamkar ba'a Nigeria ba. Dai-dai nan sai ga Mama Balki tamkar an jehota...

       “Kandala miya kawoki nan keda baki da lafiya?”.

    A shagwaɓe nace mata “Mama an sani aiki ne?”.

   Cikin nuna mamaki tace, “Aiki kuma? Waye ya sakaki ke da baki da isashen lafiya? Kuma banan bane sashen aikin ki”.

       “Nice ko ban isa ba?”.

   Aka amsa mata daga bayanmu. A tare duk muka juya, jikin Mama Balki na rawa ta ce, “A'a Hajiya ALLAH ya huci zuciyarki ai ban san kece ba.”

   Tsaki taja tana ɗauke kanta ta dawo da shi gareni. Cikin isa da bada umarni ta lissafo min duk abinda take buƙata. Kafin ta kalla Aunty Kubrah tace ta sameta da black tea bedroom ɗinta tai ficewarta. Ina kallon Aunty Kubrahn ta bita da uwar harara, ni dai sai na fara ƙoƙarin neman tukunya hannuna dafe da kaina dan bana jin daɗin jikina da har yanzu. ALLAH sarki da taimakon Mama Balki nayi girkin, yanda take ta nuna damuwarta akan sakani aikin da Hajiya Mammah ɗin tayi sai ya dinga bani mamaki. Amma sai ban ce da ita komai ba ni dai dan bama fahimtar inda ta dosa ɗin nayi ba, na dai dinga ƙarfafa kaina dan na rage mata damuwa. Mun kammala da ƙyar ina faman dafe kai sai ga Hajiya Mammah ɗin ta dawo. Tsaf take cikin sabuwar kwalliya da alama wanka ta sake. Abubuwan dana zuba abincin ta shiga buɗewa a yamutse. Sai da ta gama tsaff sannan ta kalleni.

       “Kije kiyi wanka ki sameni da kayan abincin bedroom ɗina”.

   Karan farko na ɗan kalleta. Kamar zanyi magana sai kuma na fasa ganin harta juya abinta ta fice. Side ɗin da Mama Balki take na duba. Ganin yanda fuskarta duk ta nuna damuwa ya sani sakar mata murmushin ƙarfin hali. Itama murmushin ta ɗan sakar min. Fuska na ɗan ɓata cikin marairaicewa na ce, “Amma Mama matar nan ta cika mulkin mallaka da iyayin tsiya. Yanzu kai abincin ne sai nayi wanka? ALLAH kaina ke ciwo ina son naje na kwanta”.

        Cikin yanayin damuwa ta amsa min da, “To yaya zamuyi Kandala. A ƙarƙashinsu muke ai. Sannu kinji ALLAH ya sawwaƙe. Kije kiyi wankan sai ki sameni na tayaki ɗauka kinji. Ni dai bana fatan a dinga yawan kuka da ke a gidan nan balle har a fara kaima Alhaji ƙarami ƙararki.”

     Zuwa yanzu na fahimci wa take cema Alhaji ƙarami a gidan, dan haka bance komai ba na fita hannuna dafe da kaina. Kai tsaye sashenmu na wuce, na samesu duk sun koma dan yanzun lokacin hutunsu ne. Bedroom na wuce na shiga wanka. Bayan na fito na gyara jikina da ƙyau kamar yanda na saba sannan na fito. A'i ce ke tambayata ina zanje. Kai tsaye na bata amsa aikin da zanyi na dawo. Babu wanda yace komai face a dawo lafiya da Bahijja tai min. Nayi mamakin samun Hajiya Mammah a kitchen ɗin yanzu ma, sai dai ban nuna ba face gaisheta da nayi na fara ƙoƙarin haɗa kayan abincin. Ita kaɗaice a ciki babu Mama Balki. Ina gab da kammalawa akai kiran wayarta, sam ban maida hankali a kanta ba balle nasan da wanda take wayar, sai da ta ajiye kan wayar ta kirani da “K!” sannan na juyo. 

      Cikin yanayin kafeni da idanu tamkar zata cinyeni da su ta ce, “Ki haɗa abincin nan a wani tray ki kaima Awwab sashensa ki dawo yanzu ina jiranki.” ɗan jimm nayi kamar mai tunani, sai da ta daka min tsawa sannan na amsa mata da to. Yanda ta bada umarni haka nayi, na haɗa komai a wani tray ɗin daban sannan nace mata, “Mammah ban san sashensa ba ai”. Shiru babu amsa, na ɗago na kalleta sai naga ta zuba min idanu ne kawai kamar ɗazun. Jinai raina ya fara ɓaci da kallon ƙurillar nan nata. Amma sai na dake na sake maimaita mata tambayar tawa. Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi tana mai ɗauke kanta daga gareni, sai kuma ta fice tana faɗin na biyo ta....


      💢🌟💢🌟💢

   💢✨💢✨💢


         Cike da kulawa da tattali bayan Abba ya kammala cin abinci Mom ta kwanto jikinsa. Sai da ta saka hannunta cikin nasa murya a narke ta fara magana da kissa. “Nagode sosai Abban Abbas. Dan ALLAH ina sake roƙonka ka yafemin kuskuren da nayi, wlhy sharrin shaiɗanne amma bazan sake ba. Ni nasan kai mutumin kirki ne, dan gashi ka tabbatar min da hakan ta hanyar gyaran gidan nan da kayi. Kaga zamuyi bikin nan cikin mutunci batare da muma anga raggarmu an rainamu ba”.

      Shiru Abba baice mata komai ba. Sai wani murmushin da ya saki mai faɗi da akwanakin nan baya barin fuskarsa. Ganin haka itama sai ta sake lafe masa a jiki da kai hannunta saman fuskarsa tana shafawa. Komai baice mata ba, bai kuma hanata ba dan shima yana buƙatar hakan duk da gobe in sha ALLAHU amaryarsa zata iso gidansa. Amma yasan cakwakiyar da gobe zatazo da shi ba lallai ne ya kai ga hutawar ba. Dan haka ya biyema Mom ɗin. Sosai kuwa ya sami nutsuwa dan an bi da shi ta hanyoyin da shi a karan kansa sai da ya manta kan nasa.........✍️



      _Hummmmm Abba adai bi a sannu ehe🥱_



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama


     


Post a Comment for "Tsutsar Nama Book 2 page 27"