Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Tsutsar Nama Book 2 page 26

 𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_

       _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒔𝒊𝒙_



.......Wani ɗan iskan Murmushi Abban ya sake mata da cewa to kawai. Hakan ya sakata sake shiga cikin farin ciki da tabbatar da lallai aikinsu ya ci Abban. Washe gari kuwa sai ga kaya ana kawowa danƙara-danƙara. Sosai farin cikin Mom ya kasa ɓoyuwa a wannan yini, dan har sai da ta kira Ummanta ta sanar mata. Da yamma kuwa masu aikin na gab da kammalawa sai gata ta isa gidan. Har sashen suka shiga ita da Mom ɗin, sunata faman santin kayan da yaba aikin malamin. Tun a ranar Mom ta fara haɗa ƴan kayanta, dan a bata haukar itace zata koma can abarwa yaran inda take. Da Abba ya dawo gida da yamma ya sami tarba ta mutunci daga Mom ɗin, hatta da abincinsa ranar da kanta ma tayisa bata saka sabuwar mai aikin ta ba. Shi dai komai baice mata ba, duk abinda tace shi yake yi, a can ƙasan ransa kuwa dariya take bashi...


        ★★★....


      Bayan wucewar su Samraah ya jima zaune a wajen batare daya tankama duk surutun su Hajiya Mammah dake a falon ba. Sai da Paah ya kira sunansa sannan ya ɗago ya ɗan kallesa sai kuma ya sake maida kan nasa ya duƙar ba tare data amsa masa ba shima. Shiru falon yayi dan kowa zuwa yanzu ya fahimci ransa a ɓace yake har shi Paah ɗin. Ilai kuwa basu gama zancen zucin nasu ba ya sake ɗagowa yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya tamkar mai lissafa yawansu. Da sauri yaran suka shiga rige-rigen barin wajen, hakama Hayatu saurin fita yayi hankalinsa a tashe, dan dama duk a ɗari-ɗari yake da yanayin ogan nasa. Suna gama fita Maash daya tsare iyayen nasa da kallo cikin daƙilallen yanayin nan nasa dake sake fiddo tsantsar ɓacin ransa ya furta, “Paah sayin mi na gani a hannu da ƙafar Ummie? Ina masu kula da ita da har yarinyar nan ta shiga inda take?”.

          Kai Paah ya shiga girgizawa, kafin cikin nuna damuwa shima ya furta, “Muhammad tare da kai muka bar gidan nan a shekaran jiya. Na dawo jiya da dare ka dawo yau da safe. Ban san komai ba kamar yanda kaima baka sani ba”.

     “Har yanzu baka shiga duba Ummie kenan?”. Ya faɗa a zafafe.

    Dabircewa Paah ɗin yayi, zai fara kare kansa Maash ya katsesa ta hanyar maida kallonsa ga Hajiya Mammah. Sosai ta fara mazurai. Sai dai shi ko'a kwalar rigarsa dan itama tasan baya tsoron duk wani hargaginta. Kame-kame ta fara tunma kafin yace da ita komai. 

        “Ko yau da safen nan na shiga duba ta ni dai, kuma banga wani ciwo a jikinta ba Awwab. Sai dai idan munafukar yarinyar nan ce ta aikata mata wani abun. Shiyyasa sam yarinyar bata min ba tun randa Mashi'a ta kawota. Ni inama zargin wani ne ya aikota dan ta cutar damu, yarinyar fa sam bata shakkar gasawa mutane magana, kai ma shaida ne ai tunda a gabanka ance ta mari Azizat....”

       Idanunsa ya runtse da ƙarfi yana mai masifar cije lips ɗinsa. A take jijiyoyin kansa duk suka firfito ruɗu-ruɗu. Idanunsa suka kaɗa gwaiduwar tsakkiya ta koma siririya. A matuƙar zafafe da akan daɗe ba'a gansa a yanayin ba ya miƙe. Gashin jikinsa har mimmiƙewa suke saboda masifar dake cin zuciyar ƴan maza. Cikin daka tsawa ya ce, “Mammah!! Idan itace ta jimata ciwo shi kuma dattin dake a sashen itace ta zuba shi kenan?! Dama wannan dalilin ne yasa a duk lokacin da nake gari ake maido Ummie falon sashenta na farko!!!”.

        “Muhammad!!”.

   Paah ya kira sunansa a tsawace shima. “Kana cikin hankalinka kuwa? Addata kake ma tsawa haka kamar kana magana da wata sa'arka?!!”.

          “Ni kuma ina magana ne akan mahaifiyata idan ita ɗin Addarka ce Paah! Idan kuma kana son tuna min kana nan baka canja ba to nima fa akan Ummie ban canja ba. Ba kuma zan taɓa canjawar ba. Kaf ɗinsu har kai ɗin ban ma kowa tilas a zaman gidan nan ba, tunda dama ban gayyaci kowa yazo ya zauna da mu ba a cikinku kune kuka kawo kanku. Ku gaya min na taɓa tsallake dai-dai da rana guda wajen biyan masu kula da Ummie ne? Ko na taɓa tauye wani likita a cikin masu duba lafiyarta. Kai da Baba kuka tirsasani wannan kai da kawon kasuwancin badan ina so ba. Kuka kuma min alƙawarin kulawa da mahaifiyata bakin rai bakin fama har takai da an tattaro wannan gayyar an zube a gidan nan. Idan kun manta bari na tuna muku wannan gidan mallakin wadda kuke wulaƙantawar ne. Amma ku kuna zaune cikin salama da tsafta ita tana cikin ƙazanta. Saboda son zuciya kuma kuna lulluɓe duk wata hanya dazan fahimci haka. Shin dama kun tirsasani barin kulawa da itane dan ku tozarta min it...” ya kasa ƙarasawa saboda hawayen dake neman kufce masa. Ga wani irin masifar sarawa da kansa yayi cikin ƙanƙanin lokaci falon ya shiga juya masa. Hannu ya kai da ƙyar yana ƙoƙarin dafe kan amma hakan ya gagara, sai ma layi daya fara. Gaba ɗayansu sukai kansa hankali a tashe. Dai-dai ƙarasowar Paah inda yake ya tafi gaba ɗayansa zai zube ƙasa babu alamar numfashi tattare da shi. Da ƙyar Paah da Hajiya Mammah da Mummy suka iya tallabesa. Dan Maash tsayayyen mutum ne ƙaƙƙarfa a tsayensa. Ihun Azizat dake laɓe daga upstairs tana sauraren komai ya jawo hankalin su Hayatu dake main perlor. Da gudu ya shigo hankalinsa a tashe. Dama abinda yake gudu kenan tun farko. Tunda ya fahimci ran ogansa a ɓace yake yasan akwai matsala. Ba shi ba ko shi kansa ransa ya ɓaci da ganin yanda sashen Ummie ɗin yake. Yana ji a ransa kuma an jima ana wannan ha'incin sai yau ne ALLAH yayi asiri zai tonu. Dan a watan nan zai iya cewa ko sau ɗaya basu shiga ainahin sashen Ummie ba. A falon farko suke isketa a duk sanda suka dawo suka shiga dubata, kuma Hajiya Mammah ce kan tsatstsare ta babbake komai ta hanasu shiga can cikin. Ashe akwai abinda ake ɓoyewa.


           ★★★★...

   

    Da taimakon Mama Balki na gasa jikina da ruwa mai zafi, dan duka dai kowa yasan na sha shi. Ina fitowa daga bayin zazzaɓi mai zafi ya rufeni, sai rawar sanyi. Al'amarin kamar wasa sai ga ƙaramar magana ta zama babba. Dan ciwo sosai har washe gari ina kwance, ban san abinda ke faruwa ba a gidan sai da safe bayan su Bahijja sunje sunyi aikinsu sun dawo kowa ya dawo sai naga ya dawo jiki a sanyaye. Hankali tashe na shiga tambayar Bahijja mike faruwa? Kuka ta fashe min da shi, kafin ta sanar min ai gidan ne babu lafiya ciwon Uncle Boss ya tashi. Da mamaki nake kallonta, kafin na ce, “Ciwonsa? Dama yana da wani ciwo ne?”.

     Kai ta shiga jinjina min tare da sake fashewa da kuka. Cikin sarƙewar harshe da jan ajiyar zuciya irin ta mai kuka ta ce, “Eh, sai dai nima tunda nazo gidan nan sau ɗaya ya taɓa tashi masa. Amma yau naga hankalin kowa a tashe yake sosai alamar abin babbane. Dan naga har Baba prof ma yazo shi da akan daɗe ba'a gansa a gidan nan ba sai idan yazo duba Hajiya Babba ne ko wani babban dalili.”

       Idanu kawai na zuba mata cike da nazari, kafin na ce, “Wane irin ciwo ne ke damunsa?”.

     “Nima ban sani ba aunty Kandala. Yakan dai yanke jiki ya faɗi ne, daga nan yakanta ciwon kai mai tsanani har sai wani bawan ALLAH babban masani yazo ya bashi magani daga ƙasar Togo. Dan ance ya taɓa bama Hajiya Babba ma magani harta samu sauƙi sai kuma abin ya sake dawowa sab......” ta kasa ƙarasawa sakamakon shigowar Mama Balki. Sai ma miƙewa da tai cikin wayancewa ta fice wai tana zuwa. Da kallo kawai na bita kamar yanda itama Mama Balkin ta bita da kallo. Sai da ta fice na sauke ajiyar zuciya mai nauyi ina maida kallona ga Mama. Itama ni take kallo yanzu. Sannu tai min da tambayata yaya jikina. A hankali na amsa mata, sai kuma na tashi zaune sosai dai-dai itama tana ƙarasowa inda nake ta ajiye kwanon hannunta. Hannun nata na kamo dan haka ta juyo tana kallona. Hawayen da nake ta riƙewa ne suka ziraro min.

        “Ya salam Kandala miya faru kuma? Jikin ne?”

     Kaina na shiga girgiza mata ina ƙoƙarin share hawayena. Itama sai kawai ta riƙoni jikinta tana lallashi. Tsawon lokaci muna a haka har sai da na daina kukan sannan ta ɗagoni, cike da kulawa ta ajiye abinci a gabana. Kaina na girgiza mata. Cikin damuwa na ce, “Mama na ƙoshi, sai dai ina son kimin wata alfarma”.

        “Alfatma kuma Kandala? Ta mi?”.

    “Ta bani tarihin wannan gida. Dan ALLAH mama ina son sani. Idan har kema kin sani badan ni ba dan rahamar da UBANGIJI yay mana.”

    Jimmm tai alamar tunani, kusan mintuna biyu sannan ta nisa a hankali. “Kanda kin roƙeni tare da haɗani da wanda bazan iya bijirewa ba. Sai dai abinda kike buƙatar sani jinsa a bakina zai iya zama haɗari idan har wani ya jimu. Amma ina mai baki haƙuri da in sha ALLAHU watarana zan gaya miki duk abinda na sani. Dan ina aiki a ƙarƙashin wannan ahali tun ina da ƙarancin shekaru koma nace miki iyayena ma sun hidimta musu suma. Wannan baiwar ALLAHr da kika gani a halin jarabawar rayuwa yau itace ta suturtani da ilimin addini dana zamani dan kusan tare muka tashi da ita amma ta girme min. Ta kuma yimini aure da mutumin kirkin da ƙaddara ta rabamu badan mun shirya ba. Bayan rasuwarsa ne na sake auren Malam Umaru dake koyar daku karatun addini a yanzu. Abinda kawai nake so dake ki kula, gidan nan ya wuce duk yanda kike zatonsa. Ki bi komai a hankali kinji. Muma badan bazamu iya bane muka zuba ido sai dan anfi ƙarfinmu ne kawai.”

      Ajiyar zuciya na sauke ina jinjina mata kaina. “Shike nan na gode Mama. Amma dan ALLAH ki amsa min tambaya ɗaya”.

    “Ina jinki”.

  “Dama haka ake ɗaureta?”.

Sai da ta ɗan waiga ta kalla ƙofa kafin ta juyi tana ƙara sauke murya ƙasa cikin raɗa.........✍️



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_


Post a Comment for "Tsutsar Nama Book 2 page 26"