Tsutsar Nama Book 2 page 24
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒇𝒐𝒖𝒓_
.......Zuwa yanzu labari ya gama shiga kunnen mutane da dama game da wannan aure na baƙo daga Kano da Halime. Ciki kuwa harda innarta da sauran matan gidansu kasancewar family house ne part-part. Dan har ƙannen mahaifinta da matansu duk a gidan suke suma. Koda su Abba suke isowa sun samu gida a matuƙar hargitse innarta nata tsiya da bori ana rirriƙeta. Abin nata zabban takaici. Dan suna shigowa ta dire tsalle ta shaƙe wuyan rigar Baba tana surutai da girgiza, ga zagi manya-manya. Da ƙyar ƙannensa da matansu suka ɓanbareta. ALLAH sarki Baba duk sai ya daburce. Fahimtar yanayin nasa yasa su Abba dakewa su. Tare da nuna masa cewar hakan ba komai bane daga halin banza irin na wasu mata kamar su Inna. Abba kuma ya sake ƙarfafawa Baba gwiwa akan in sha ALLAHU zai riƙe Halime da daraja ta yanda sai Inna ta yi kuka da idanunta. Baba yaji sanyi a ransa, hakan yasa yayma Abba alƙawarin nan da sati guda Halime zata tare kawai. Yanzu ɗin ma dan yana son sanarma dangin su Innar (dangin mahaifiyarta kenan) shiyyasa bazai basu ita ba. Sun gamsu da hakan, saboda suma suna buƙatar komawa su ɗan kimtsa. Gidan mai-anguwa suka koma aka kira musu Halime. Sai dai da ƙyar ta fito fiskarta a ƙunshe cikin Hijjab. Duk yanda Abba yaso ya ganta taƙi yarda ta buɗe fuskar. Aiko Alhaji Jafaru da Alhaji Sadisu nata ƙumshe dariya. Abba ko nata balla musu harara. Da ga ƙarshe ya korasu waje. Suna fita yay kan Halime yana lallashi, kamar almara yana kai hannu kan hijjab ɗin nata da nufin ɗagewa ta zungura da gudu cikin gida ta barsa da hannu a sage. Duk da yanda yaso dannewa ya gagara, tuni ya shiga ƙyalƙyala dariya yana mai jinjina wautar ta. Lallai akwai aiki gabansa tuƙuru kenan....
★•★•★•★
Duk yanda mama Balki taso samun nutsuwa ta gagara hakan. Sai faman kaiwa da komawa take yi hankalinta gaba ɗaya na akan Samraah. Tun tana irga sakanni har ta koma mintuna, amamakinta sai ga awa ta shuɗe. Awa ɗaya, biyu, uku itama ta shuɗe. Tsaye take akan kula da girkin rana dasu Kubrah keyi amma kaɗan-kaɗan sai ta fito daga kitchen ɗin, tun ma basu fahimtaba suma har suka fara tsarguwa. Cikin gulma suka dinga nunama junansu ita da ido da baki. Sam Mama Balki bata san ma sunayi ba, saboda hankalinta a rabe yake. Ƴar hayaniyar su Arwa dake falo da zagin da taji sunayi ya sata fitowa zumut daga kitchen ɗin. Hannu taga duk sun saka suna famar toshe hancina. Yayinda tuni Muhsin ya fara kakarin amai. Dai-dai nan itama mahaukacin warin ya daki hancinta, da sauri takai hannu ta toshe hanci, sai kuma ga jama'ar gidan suma sun fara fitowa daga sassansu kowa na tambayar warin minene haka?.
Rasa mai bama wani amsa akai sai nuni da sama saitin sashen Hajiya Babba kawai akeyi. A dai-dai nan katifar da Samraah ta jingina jikin ƙarfen da aka ƙawata adon wajen da shi da bata zauna dai-dai ba ta sulmiyo downstairs ɗin gaba ɗaya. Ihu yaran suka buga a tare suna tarwatsewa. Sai kuma yunƙurin amai dan gaba ɗaya falon ya ƙarasa gumamewa. Cike da fusata Hajiya Mammah ta koma upstairs ɗin tana ƙwala kiran Samraah da “K!! K!! K!!” dan ko sunanta bata sani na. Ihun nata yaja hankalin sauran iyayen dama su Azizat ɗin suma suka bita. Hakama su Falilah ba'a barsu a baya ba. Mama Balki ce ƙarshen bin bayansu.
Isowarsu ƙofar dai-dai da ƙwalla ƙarar azaba da Samraah tayi, a take kowa ya tsaya cak. Ƙarar da Samraah ta sake fasawa kuma duk sai suka ja da baya. Dan basa buƙatar ƙarin bayani ta ƙwaɓe ne tsakaninta da mai sashen. A matuƙar tashin hankali Mama Balki ta juya da gudu ta sauka downstairs ɗin jikinta na ɓari. Bama tasan sanda takai kanta sashen Maash ba. Kawai tsintar kanta tayi a gabansa durƙushe cikin kuka da roƙo ta kama ƙafafunsa....
“Alhaji ƙarami dan ALLAH ka taimake mu. Kandala. Kandala ce gata can a sashen Hajiya Babba...” numfashinta ya nema ɗaukewa gaba ɗaya saboda yanda take a kiɗime. Shiko Maash da tun shigowar tata a guje da tsawar da Hayatu yay mata na son ta dakata ya tsaya cak daga duba abinda Hayatun ke nuna masa a tab sai dai bai ɗago ba sai da ta ambaci Hajiya Babba dan shi bai ma san waye wani Kandala ba. Idan ka cire ita a gidan da mijinta sai wasu tsiraru a masu aikin da suka daɗe a tare da su kawai zai iya cewa ya sani har ma ya shaidasu koda a wajen gidan ya gansu. Amma daga basu ɗin ba babu wanda zai iya shaidawa a cikinsu.
Cak Hayatu shima ya dakata da ga yunƙurin maganar da yake, dan sai a lokacin yama fahimci wacece ɗin. Shine yay ƙarfin halin faɗin, “Mama waye Kandala? Mi kuma ya faru da Hajiya Babba?”.
So take tai magana amma ta kasa, sai nuna ƙofa kawai take ga hawaye na kwaranya mata. Ƙarasowa Hayatun yay da sauri inda take. Ya kama hannunta ya miƙar daga gaban Maash da take durƙushe. “Kinga relax. Calm down kiyi magana yanda za'a fahimta. Rufe idonki ki shaƙi iska ki fesar Mama”.
Kai mama Balki ta shiga jinjinawa tana haɗiyar kukan da sauri-sauri. Yanda duk Hayatun yace tayi tayi, ya miƙa mata ruwan gabansa ta sha maƙwarwa biyu sannan ta sauke nannauyan numfashi. Shi dai Maash kallonsu kawai yake amma ya gagara cewa komai. Cikin ƴar nutsuwar data samu ta sake faɗin, “Kan...kandala ce sabuwar mai aikin da Aunty Mama ta kawo. Ta..ta tafi sashen Hajiya Babba gata can tana ihu da alama....” sai kuma ta kasa ƙarasawa. Sosai Hayatu ya waro idanu a firgice. Yayinda Maash yayi wani masifar runtse nashi da ƙarfi, sai kuma ya ajiye tab ɗin hannun nasa ya miƙe. Baima tsaya ƙarasa jin zancen ba ya nufi ƙofar da kan sadashi da sashen mahaifiyar tasa kai tsaye daga sashensa. Sai dai kuma a kulle take. Jikinsa ya shiga shafawa neman key, amma da alama baya tare da shi, har ya kalla Hayatu zai yi magana sai kuma ya fasa. Komawa yay da baya ya fito, da sauri Hayatu da Mama Balki suka take masa baya. Ta babban falon gidan da ya gama gumamewa da warin katifar nan ya ratsa, da bibbiyu ya dinga haɗa stairs ɗin tsabar tashin hankalin da yake a ciki. Dan duk duniya bai haɗa al'amarin mahaifiyar tasa da komai ba. Cikin rufewar ido da ɗimuwa yake sa hannu ya ture duk wanda ya tare masa gaba. A haka har ya shige ciki gaba ɗaya dan su mutanen gidan suna a falon farko ne cirko-cirko sun gagara shiga ciki dan tsoro. Sai hayaniya da suka cika wajen da shi. Yana shiga securitys ɗin da sukai kira na cikin gidan na isowa. Suma takema Maash ɗin da Hayatu baya sukayi...
Sosai nake kakarin mutuwa. Idanuna kam sun gama firfitowa. A wannan gaɓar na sallama da rayuwa. Ta ALLAH kawai nake jira ta kasance. Wata irin bugawa da tama kaina a bango ya sani fasa wahalalliyar ƙara da ko sautin kirki babu yanzu saboda galabaita dana gama yi. Daga haka ban sake sanin mi kuma duniya ke'a ciki ba...
Shigowar Maash dai-dai da wancakalo Samraah da Hajiya Babba tayi kai kace irin an yadda magen nan. Baya yay taga-taga zai faɗi, sai da Hayatu ya riƙesa. Da sauri ya kai dubansa kan abinda ta wurgo ɗin, a kuma dai-dai nan itama ta sake wawuro abin morpping irin na wutar nan da Samraah ta ajiye tare da sauran kayan shara. Ji kake bummm!! Akan goshinsa. Kamar ƙyaftawar ido ta sake rarumo wani abun, jifan kan mai uwa da wabi ta shiga musu kamar yanda take yi a duk sanda take a irin wannan yanayin. Dole su Hayatu suka shiga fita a guje. Yayinda Maash ya kasa yin hakan shi. Dan shi damuwarsa ba ciwon data jimasan bane. Kar ita ta jima kanta ciwon. Ƙoƙarin nufarta yayi da son kwashe sauran kayan sharan. Amma ina jifa kawai take kai masa dasu tako ina...
Cikin wani irin karyewar murya ya shiga ƙoƙarin kai hannu gareta yana faɗin, “Please Ummie na kar kiji ciwo, dan ALLAH ki ajiye zai ji miki ciwo. Hannunki Ummie hannunki.”
Ina ita bama tasan yanayi ba. Jifan kawai take kai masa har sai da taga kayan sun ƙare, sai kuma ta koma kai masa duka da hannu. Cikin sa'a shima ta shaƙuro wuyarsa. Dai-dai nan masu kula da lafiyarta da akai kira a waya suka iso. Da ƙyar aka ɓanɓare Maash a hannunta bayan sun mata allura mai ƙarfin gaske. Zama yay ƙasa batare da jin ƙyanƙyamin komai ba ya riƙeta a jikinsa ya zubama fiskarta idanunsa da suka rikiɗe gaba ɗaya. Yanda Adams apple ɗin sa ke kai da kawo zai tabbatar maka da kukan zuci yake yi. Yafi mintuna goma zaune a haka shiru, duk maganar da su Hajiya Mammah suke masa bai ko motsa ba. Sai da Paah ya shigo ya kai duƙe kusa da shi, hannu ya fara kaiwa ya riƙo na Ummie dake kwance ka shirɓan allamar barcin nata yay nisa matuƙa, idanu ya zubama hannun cike da tausayawa shima nasa na cika da hawaye, dan har yanzu har gobe yana matuƙar ƙaunar matar tasa rufin asirinsa kuma. Hawayensa ya share kafin ya sauke ajiyar zuciya tare da kiran sunan Maash da bai ko motsa ba.
“Muhammad”.
A hankali ya ɗago idanunsa ya zubama Paah ɗin nasa batare da ya iya cewa komai ba, sai kuma ya ɗauke ya maida kan (Ummi) Hajiya ƙarama da ke tare da sauran masu kula da lafiyarta dan itama likita ce. Sake ɗaukewa yay ya maida kan Samraah dake kwance gefe a sume babu wanda yabi takanta. Yanda ya tsurama wajen ido na tsahon mintina kusan biyu ya saka kowa maida kanhalinsa ga kallon abinda yake kallon. Shima kansa Paah sai a lokacin ya lura da Samraah ɗin.......✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
Post a Comment for "Tsutsar Nama Book 2 page 24"