Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Tsutsar Nama Book 2 page 23

 _𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_

       _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_



_________


_Koda kuɗinka sai da rabonka. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge mai kallonka. Albishirin ku ƴan kasuwa da masoya. Kuna ina? Ina kuka shiga? Maza ku garzayo kantin sauƙi da rahusar ingantattun kaya na kasarku dama ketarenta. Bari na kaiku, *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* ke muku sallama irin ta addinin musulunci da babban albishirin shiryawa tsaff domin kawo muku kayayyakin buƙatunku na yau da kullum. Tun daga kan irinsu, atamfa, lasses, shaddoji, materials, abayas, takalma, handbags na zamani, vails ƴan yayi. Hijjabai. Sarkoki da dangoginsu. Kayan shafe-shafen dana kwalliye fuska. Agoguna harma dasu eyeglasses na manyan mata. Kai kai Karfa na cikaku da zance, dan zaku iya ganin komai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING* domin farin cikinku. Kayan yara harma dana maza ba mata kawai ba. Ba'a sayen ɗai-ɗai zamu tsaya ba harda sari ga mai buƙata zamu bada in sha ALLAHU kuma akan RAHUSA mai sauƙi da kaima zaka samu naka rabon. Zakuma mukai maka kaya a duk inda kake a *NIGERIA* in sha ALLAHU. Ƴan kasuwa masu sari da masu sayen ɗai-ɗai ku garzayo nan domin gani da ido in sha ALLAHU. Ka gani su birgeka, ka saya ka birge masu kallonka sai a *BILYN ABDULL ONLINE SHOPPING*👇_



https://chat.whatsapp.com/LkRMFFQZakP55c7xK0QaMG




https://chat.whatsapp.com/D1Ki9jt2lNkKVetOWNuFN5

___________


.......Komawa nayi baya ta hanayar dining ɗin nan ina mai addu'ar samun kayan shara. Ƙofar kitchen ɗin akwai key a jiki, dan haka na murɗa a hankali, sai da na leƙa cikinsa sannan na shiga gaba ɗayana ina sauke numfashi. Babu komai a cikinsa shima. Sai dai shi ɗin fes yake babu wani datti sai ƙura ta rashin gyarawa. Sosai kitchen cabinet ɗin da aka ƙawatashi da shi yay matuƙar ƙyau kamar ka zauna kayita kallo. Ganin ina neman shagala a kallon cabinet na zabura neman kayan shara. Cikin Sa'a kuwa sai gasu na samo a store dake cikin kitchen ɗin duk masu aiki da wuta. Cike da ɗoki da zumuɗi na kwaso duk abinda zan buƙata. Tun daga store ɗin da shima babu tarkace sosai na fara gyarawa har zuwa kitchen, sannan na fito dining ɗin. A nan kam na jigatu kafin na dawo falon mai gayya da aiki. Tun ina yin aikin da marmari har na fara jigata. Amma haka na dinga dauriya. Sau biyu ina jima hannuna ciwo. Na maida abinda zai iya maiduwa. Wanda suka tashi a aiki na tattarasu na fitar can barandar da aka ƙawata ta waje bayan na zuge labule na ganta. Ashe wajen glass ne amma an rufesa da wani irin abu mai taushi nasan duk dan kar taji ciwo ne. Kaf labulolin data jeho na tattaresu dan duk abincine da fitsari a jikinsu. Hakama carpet ɗin na cireshi shima. Hatta wanda sukai min nauyi da yawa haka na dinga turasu, sai santsin Mable's ɗin ya dinga taimaka min har na kaisu balcony ɗin duka.

     Ni kaina yanda falon ya dawo a hayyacinsa sai da nayi murmushi. Na baɗe ko ina da freshiners masu ƙamshin daɗi dana gani a wata drawer. Ac na kunna kaɗan dan falon ya sake samun nutsuwa. Ganin lokacin salla na neman ƙuremin na dawo falon farko nayi salla ganin akwai toilet a cikinsa shima. Duk da matuƙar gajiyar da nayi da buƙatar hutu da nake da shi haka na sake miƙewa na koma. Yanzu kam ina ƙara ƙarfin addu'a a bakina na tunkari ƙofofin ɗakunan nan biyu. Ta farko na murɗa amma sai na jita a kulle. Na koma kan ta biyu sai naji ta buɗe ita. Da sauri nayi baya saboda wani irin wari dake fitowa a cikinsa mai ban tashin hankali. Take zuciyata da cikina suka shiga yamutsawa, dole na fito a guje zuwa bayin dake a falon farko. Amai sosai na shiga yi kamar zan amayar da kayan cikina. Tun ina amaryar da ruwa dana sha kawai har na koma yunƙuri kawai babu komai, da ƙyar na samu nutsuwa na wanke bakina na fito ina hakki. Har na yanke shawarar fita na haƙura zuciyata ta zabureni akan muhimmancin aikin lada. Hawaye naji sun cika min ido dan zuciyata na ayyana min idan Umminmu ce a wannan halin kenan zanji ƙyanƙyamin kasa tsaftace mata wajen kwananta? Da sauri na shiga girgiza kaina tamkar mai magana da mutum. Bamma san lokacin dana zabura na koma ba. Sai dai ina zuwa ƙofar na zame vail ɗin kaina na nannaɗe fuskata gaba ɗaya har zuwa hancina sosai. Amma duk da haka ina ɗan jin warin kaɗan-kaɗan. Haka dai na dake ina karanto addu'a a bakina ga hawaye na ɓulɓulo min cikin idanu saboda tausayi da tashin hankali. Yanzu nan ɗan adam mai rai, mai gata ne a irin wannan ɗakin? Bily ban san yaya zan musalta miki ba. Amma duk yanda kike hasashe abin ya wuce nan, ƙazantace sosai a ɗakin mara daɗin misali. Amma haka na duƙa na fara tattarewa ina kuka. Dole naje na kwaso labulolin dana cire a falo da burin wankesu na dinga naɗe ƙazantar a ciki. Sai da na tattare komai tare da fito da katifar ɗakin da ƙyar dan itace kawai anan sai labuloli da wadrobe ta jikin bango. Ina jin mutanen gidan sun fara hayaniyar wari-wari, dan da gayya na kaita falon can na farko da zaka iya hanga ta dawn stairs. Juyawa nayi na koma ciki ina ayyana kowa yau dan ubansa sai ya shaƙa shima. Shine punishment ɗin ku. Sam ban kawo cewa tana a cikin ɗakin ba, dan ganin ban ganta ba a farko kuma har nayi kusan kashi ɗaya bisa ukun gyarashi yasa nai zaton tana ɗayan ɗakin ne ko can sama hawan ƙarshe. Toilet na nufa, cike da tsantseni na buɗesa. Bamma san na daka uban tsalle ba nayo baya cikin matuƙar razani jikina na karkarwa. Gurnani da nishin dake fitowa a toilet ɗin yasa hankalina ya sake tashi, a take hoton abinda na gani ya shiga dawo min da kansa. Mutum zaune sarƙa a ƙafa da hannayenta an saƙalo jikin fanfo. Gaba ɗaya hannunta da ƙafafun sunyi jina-jina alamar son ƙwace kanta ya kaita ga jin ciwon. Kanta a duƙe yake shiyyasa banga fuskarta ba, sai gashinta dake a wani irin cirkuɗe danƙare a kanta mahaukaciya dai cikakkiya. Tausayi da tashin hankali ya sakani durƙushewa a wajen ina kuka. Nafi minti uku sannan na miƙe na sake komawa toilet ɗin. Sosai idanuna sun gama rufewa, nama bar tunanin zata iya cutar dani kamar yanda Bahijja ta faɗa tana duka. A gabanta na zube zuciyata a dake na shiga kwance sarƙar ƙafafunta da suka kumbura suntum sukayi jina-jina. Har na kammala kwancewa bata ɗago ba, sai nishin nan dai mai ban tausayi da tashin hankali kamar wadda numfashi ke shirin barin gangar jikinta. Da ƙyar na iya kammala kwance sarƙar ƙafafun, na shiga shafa ƙafar hawaye na cigaba da zararo min. Wata irin ajiyar zuciya mai ƙarfin gaske ta sauke. Sai kuma ta ɗago a hankali. Wani irin bugawa da sauri-sauri zuciyata ta shiga yi saboda ganin yanda fuskarta tayi kaca-kaca da tabbunan raunuka, sai sabbin da har sun fara bushewa suma kusan uku. Gaba ɗaya baka iya shaida kamaninta saboda dauɗa data gama mamayeta. Dan kayan jikinta ma duk a yayyage suke fata-fata. Rawa jikina ya cigaba dayi, hawaye masu zafi na sake gudu a cikin idanuna. Bamma san lokacin da na kai hannuna saman fuskar tata ba ina shafawa. “Kiyi haƙuri Ummi, dan ALLAH kiyi haƙuri, ALLAH ya gaggauta saka miki, ALLAH ya baki lafiy.....” kuka ya sarƙeni na gagara ƙarasawa. Ƙara ta saki a hankali sai kuma ta shiga fisgar hannunta a galabaice. Zaram na miƙe cikin karkarwar jiki. “I'm sorry Ummu, I'm so sorry bari na cire miki. In sha ALLAHU koda fansar raina ne zan bada wajen taimakonki. Sai na ƙwato miki hakkinki, sai na san gaskiyar mafarin lalurarki. In har da saka hannun wani sai na tarwatsa masa tanadi”. Sambatu nake da kuka ina kwance mata hannayen suma. Suma dai sun kumbura sosai duk taji ciwo. Ga tabbuna nan da sayin sarƙar alamar ba yau ne aka fara ɗaureta hakan ba. Ina gama kwancewa ta saki ƙara mai ban tausayi da alama hannun ya mata nauyi, durƙushewa nayi a gabanta nai ƙoƙarin kamo hannuwan nata ra riƙe. Sosai kuka mai ƙarfi ya sake kuɓuce min harda shashsheka. Ɗago idanuna nayi ina kallonta, sai naga itama ni ta tsurama ido tana kallo kamar mai lafiya. Murmushi na saki mai haɗe da kuka. Sai kuma na buɗe baki da nufin bata haƙuri a bazata naji an damƙi wuyana. Sosai na waro ido waje dan azaba. Sai kuma na saki wahalalliyar ƙara jikina na rawa dan shaƙa ce bata wasa ba. Tamkar wulgawar walƙiya aka jehoni cikin ɗakin. Razanannen ihu na ƙwala na azabar buguwa da kaina yayi da bayana. Kafin na yunƙura na tashi domin ceton kaina har ta iso gareni, sake kai hannu tayi a wuyana ta shaƙoni......


         💦💫💦💫💦


     Sosai Musaddiq ke a cikin farin cikin da baki bazai iya musaltashi ba duk da bai samu tabbacin samuwar aikin ba. Sai dai yanda interview ta kasance ya matuƙar bashi ƙwarin gwiwa. Ga karramashi da akayi sosai a wajen har abin yaso bashi mamaki. Sai dai ganin harda wani da ya samu da nasa takardun shima ya cirema kansa shakku. An sallamesu akan kowa zaiga massage daga nan zuwa safiya. 

     Cike da ɗoki kuwa ya dawo gida, ga wani irin farin ciki daya gama mamaye masa rai, sai dai wani fanni na zuciyarsa na matuƙar jin kewar Kandalarsa, da yanzu ita zai fara sanarma albishir ɗin komai da bata labari. Amma ba komai ko yanzu ma bata ɓaci ba. Waya ya jawo ya shiga laluben layin mijin nata. Sai dai har ta tsinke ba'a ɗaga ba. Sake kira yay har sau uku nan ma shiru. Hankalinsa ya nema fara tashi sai ga shi an kirasa back da number ɗin. Cike da zumuɗi ya ɗaga. Suka gaida da mutunta juna. Mijin ya ɗora da bashi haƙuri akan ba'a kusa yake ba sanda yay kiran. Cikin mutuntawa Musaddiq yace babu komai. Sun ɗan yi shiru kowa da tunanin da yake yi, sai kuma suka yunƙuro kusan atare zasuyi magana. Dariya abin ya basu, dan haka Musaddiq ya dara, da ga can kuma mijin na Samraah ya murmusa har Musaddiq ɗin najin sautin murmushin nasa.

       “Afuwan ina jinka”.

     Da sauri Musaddiq ya ce, “Ni zan nema afuwa ai ina jinka”.

“Okay, dama zance ma bana gida ne, amma in sha ALLAHU dana koma zan haɗa ku. Sannan in babu damuwa tsoffin numbers nata ka ɗan turamin dan a mata welcome back ɗin su”.

      Cikin jin daɗi Musaddiq yay masa godiya. Daga haka sukayi sallama. Dole ya haƙura yay kiran Hafizzullah dake makaranta yay masa albishir ɗin shi, murna suka dingayi, daga ƙarshe suka koma hirar Samraah ɗin dan da gaske kowa a cikinsu yayi kewarta sosai........✍️




       _Humm, ni dai inada tambaya anan😂. Yayanmu Maash ne ko kuwa🥱🥱Bara dai bayi hiru to._



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

Post a Comment for "Tsutsar Nama Book 2 page 23"