Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Tsutsar Nama Book 2 page 21

 𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_

       _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚 𝒐𝒏𝒆_



.......Ina idarwa na ɓingire a wajen sai barci. Ban tashi farkawa ba sai da A'i ta tasheni wai Hajiya Mammah na kira na. Yanda take maganar cikin nuna tsoro da damuwa ya sakani tsira mata ido. Sai dai bata bani damar mata tambaya ba ta juya sukuku ta fice tana faɗin, “Kiyi sauri ki shirya muje kar mu sake wani laifin kuma. Dan ga Mama Balki can tasha maruka akan guduwar da kukayi jiya da dare duk da ƙaryar kareki da tayi kan baki da lafiya ne shiyyasa”.

     Sosai naji wani irin masifaffen ɓacin rai. A take ta bududdugin ta motsa (zuciya) na shiga taunar lips da ƙarfi-ƙarfi tamkar zan hudashi. Gaba ɗaya wata irin tsanar matar mai tsananin gaske ta shiga zuciyata. Yanzu dan ALLAH babbar mace kamar Mama Balki ce za'a mara wai. Kai wannan wane irin gidane haka na marasa tarbiyya da girmama mutane. Dan kawai mutum nada dukiya sai akace zai iya taka kowa a yanda yake. Kaicon wannan rayuwa mara fasali da rashin sanin daraja da kimar ɗan Adam.

      A gurguje nayi wanka na shirya cikin Uniform ɗin da A'i ta ajiye min. Koda na fito a falo na sameta tsaye tana jirana. Kallon juna mukayi. Ta ɗan kafeni da kallo sai dai batace komai ba tayi gaba na bita a baya...


       💞👉💞👉💞


    “Alhamdullah su Abba sun isa ƴan tumaki lafiya. Tafiyar da Mom bata da masaniya a kanta, dan har yanzu Abba baya shiga harkarta. Ita kuma ta tada hankalinta sunata bibiyar teachers domin sabunta ayyuka akan Abban dan ta lura komai fa na neman canjawa. Kullum cikin ƙaryar fita take duk da kuwa yana gida yana jinya. Bai taɓa hanata ba, kamar yanda Gwaggo Gudidi bata taɓa tanka musu ba. Da tambaya da kwatance suka gano gidan su Halime da ƙyar kasancewar sun sami cikakken address wajen mai kawosu aikatau daga ƙauyen. Wadda da ƙyar suka samu ƙawar Mom ta sanar musu bayan sun danƙa mata kuɗaɗe. Tako kai su amma ta roƙi Abban da kar ya sanarma Mom ita ta faɗa, duk da kuwa ita bata san manufar Abban ba. Ya sanar mata ne kawai zasu bincika idan Halime taje gida kar a samu kuskure tayi wani wajen daban. Ta gamsu ɗari bisa ɗari dan tanama Abban kallon girmamawa duk da tasan aminiyarta ta daɗe da gamawa da shi. Koda yake itama ɗin ta gama da nata mijin ai duk da basu taɓa tarayya da Mom wajen zuwa gidan teachers ba. Kowa nayin al'amarinsa ne a bayan fage..


        Sun ɗauki kusan mintuna talatin a gidan mai anguwa da sukai dabarar fara zuwa kafin Baba da aka aika kira ya ƙaraso. Tun shigowarsa Abba keta sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya, dan ko makaho ya laluba yasan shine mahaifin Halime saboda kama da sukeyi matuƙa tamkar yayi kaki ya ajiyeta. Sake gyara nutsuwa Abba yayi, hakan har ya saka Alhaji Sadisu sakin murmushi. Bayan Baba ya gaisa da mai anguwa ya juyi gasu ba. Kafin ma ya gaishesu su sun shiga gaida shi. Dan ko babu batun abinda ya kawosu zai girmesu gaskiya. Bayan an kammala gaggaisawar mai anguwa ya nunama baba su Abba. 

       “Malam Yusufa baƙine dama suke neman gidanka. Naso saka yaro ya rakasu sai suka buƙaci haɗuwa da kai anan shiyyasa na aika akayi kiranka”.

    Da ɗan nuna alamun mamaki Baba ke kallon su Abba. Ganin yanda Abba ya duƙar da kansa Alhaji Jafaru ya fara magana a nutsensa. “Ni sunana Jafaru, wannan sai ƴan uwana Alhaji Sadisu da Alhaji Imam. Baba baka Sammu ba gaskiya. Wannan ɗan uwan nawa Alhaji Imam shine mai gidan da ƴarka Halimatu take zaune acan birni.....”

      Sosai Baba ya waro idanu, tare da sakin salati ya ce, “Kai kai Masha ALLAH. Bawan ALLAH ashe baka rasuba Sa'adiyya duk ta kasa zaune ta kasa tsaye. Tunda ta iso garin nan kwana biyar kenan kullum bata da aikin daya wuce kuka. ALLAH mun gode maka”.

           Murmushi Abba yayi cike da jin sanyi a ransa Halimensa ta damu da shi. Murya a sanyaye ya ce, “ALLAH kam shine abin godiya Baba. Nima kuma ina ƙara gode masa da ya zamto gida tayo ba wani wajen ba. Dan muna can hankalinmu duk a tashe da ƙyar aka samo wadda ta ɗauketa daga nan ta bamu address.”

     Sosai Baba ya nuna jin daɗinsa da wannan kulawa. Fuskarsa washe da murmushi shima ya ce, “Ai dama duk tsanani Sa'adiyya bazata nufi ko ina ba sai gida. Nima Nagode sosai da wannan kulawa taku, lallai na yarda da gaske yarinyata tana a hannun mutanen kirki. ALLAH ya kiyaye gaba ya ƙara lafiya”.

    A tare duk suka amsa da Amin. Kafin Alhaji Sadisu ya ɗora da bayani bayan sun ɗan yi jimm na wani lokaci. “Baba dan ALLAH idan bazaka damu ba muna neman wata alfarma ne”.

      “Ku faɗi komi kuke buƙata a gareni kai tsaye in dai baifi ƙarfina ba zan muku shi in sha ALLAHU”.

   Cike da jin daɗin furucin nasa Alhaji Sadisu ya cigaba da faɗin, “Muna neman alfarmar ka bamu auren Halimatu”.

       Ba baba kawai ba hatta da mai anguwa sai da ya waro idanu sosai cikin nuna ƴar tsorata......


       🌛🌟🌜


    Kallo ɗaya nayima Mama Balki dake gurfane gaban Hajiya na ɗauke idanuna zuciyata na suya. Da ƙyar na iya control ɗin kaina nima na kai durƙushe. Latse-latsenta take a laptop tamkar batama san da zuwan namu ba. Gefenta Azizat ce kwance itama tana latsa wayar fuskarta mamaye da fara'a. Sai da ta mula dan kanta sannan ta ɗago bayan ta rufe laptop ɗin. Fuska a yatsine kamar taga kashi ta daka min tsawa. Dakewa nayi batare da nuna razana ba. Sai cemata da nayi “Ina kwana”.

        “Daban kwana ba ƙya ganni firiritacciya. Ke mai ido a tsakar kai kinzo cin arziƙi gidan mutane har da marin ƴar masu gida ko?”.

     “Ko kuma ƴar cin arziƙin itama ba”. Na faɗa ƙasa-ƙasa.

     “What! Mi kikace?”.

   Ta faɗa a matuƙar tsawace. Idanuna na ɗago na kalleta fuska a shagwaɓe. “Nifa bance komai ba Mamma. Please ki daina faɗan firgitani kike sake yi”.

      Ba ita ba hatta Azizat ɗin Tata sai da ta juyo tana kallona da mamaki ƙarara a fuskarta. Balle su Bahijja da suka waro idanu da wangale bakuna. Niko yi nai tamkar ban gansu ba na sake shagwaɓe fuskata da taɓeta. Sai kuma na ɗauka ruwan dake a cikin kofi a gabanta na miƙa mata. “Kisha ruwan sanyi Mamma zuciyarki zatayi sanyi. Ba'a son masu shekaru irin naku da yawan faɗa za'a iya samun matsalar hawan jini daga nan ta zama ta zuniya”.

      Galala ta sake yi tana kallona. Niko na tsatstsareta da idanu ina sake tura baki da marairaice face. Da wani irin masifar ƙarfi ta cije lips ɗinta tamkar zata hudasu. Sai kuma tasa hannu ta kaɓar da kofin hannun nawa. A take ruwan ya tarwatse mana a jiki har ita. Cikin masifar ƙaraji da wutar bala'i ta ce, “Balki!!!”. A razane Mama Balki ta amsa tana miƙewa daga durƙuson da tayi zaram. “Na.. na... Na'am Hajiya”.

     “Ɗauki yarinyar nan ku ɓace min anan kafin na haukata jikunan ku da duka ku duka. Na kuma fasa aikin nata a sashena ki kaita sashen Hajiya Babba ta gyaro shi kafin nan kafin azhar”.

          Wani irin waro idanu na masifa Mama Balki tayi, cike da tashin hankali da suɓutar baki ta furta, “Sashen Hajiya Babba kuma Hajiya?”.

      “Ko bazaki kaitan ba ne?!!”.

   Cikin rawar jiki mama Balki ta shiga girgiza kanta da faɗin, “To to to Hajiya ALLAH ya huci zuciyarki, za..zan kaita mana.” mama Balki ta faɗa tana kama hannuna jikinta na rawa sosai. Da ƙyar na iya danne dariyar dake cina har muka baro wajen, dan tana ambaton Hajiya babban naji tamkar na dirga tsalle dan daɗi. Muna kammala hawa upstairs ɗin a stairs ɗin ƙarshe na ɗan kallo ƙasan, sai da na haɗiye dariyar dake cina sannan na kwaɓe fuska kamar zan fasa kuka. “Mammah dan ALLAH ni dai ina neman alfarma. In dai akwai matsala da zarar kunji na banka ihu a kawo min ɗauki koda sassaƙa-sassaƙan garadan nan na bakin ƙofar gida ne a turamin idan ma ku bazaku iya ba”.

       A matuƙar fusace ta watso min muguwar harara da gwala-gwalan idanunta “Sai dai a turo miki Ubanki. Ƴar iskar yarinya sheɗaniya. Da alama kema dai mahaukaciyar ce get out of my side kafin na canja miki kamanni”.

     Baki na tura mata cikin sake narke fuska da yamutseta na ce, “Ai dai ubana yana aljanna in sha ALLAHU badai shi b....”

         Kafin ma na kai ƙarshe Mama Balki ta fisga hannuna jikinta na rawa. Duk yanda naso ta sakan taƙi yin hakan har sai da muka ɓacema ganinsu. Kamar zata saki kuka ta ce, “Kandala baki da hankali ko? Yanzu wannan hukuncin da suka zartar a kanki bai isheki ishara ba ki koya kimtsa bakinki? Dan ALLAH ƴar nan kada ki sakamu a masifa mutanen gidan nan sun wuce fiye da yanda kike tsammani a fitina wlhy. Kiyi fatan Alhaji ƙarami bai bar gidan nan ba yazo ya fiddaki a wajen nan da wuri, zanje na samesa yanzun nan”.

      Da sauri na ce, “A'a mama dan ALLAH kada ki kirashi. Miye dan tace nazo nayi aikin anan?”.

     “Yarinyar nan baki da hankali, wautarki tayi yawa wlhy. Kandala wannan sashen da kike gani baida maraba da rami mai kwazazzabo da in ka faɗa a cikinsa sai abinda ALLAH yayi. Gara kiyi aiki a sashen Hajiya Mammah ɗin dan ita masifa ce kawai da takura, amma nan ranki ma zaki iya rasawa. Ni dai ki jirani anan zan je na duba Alhaji ƙaramin ALLAH yasa bai fita ba”.

      Ƙasa kawai nayi da kaina batare da nace mata komai ba.. Ita ma sai bata sake magana ba tai gaba.......✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_


Post a Comment for "Tsutsar Nama Book 2 page 21"