Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Tsutsar Nama Book 2 page 20

 𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_

       _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒘𝒆𝒏𝒕𝒚_


........Wani irin huci Mahahaifiyar tata take tana kallon Alajah. Idanu Alajah ta rumtse tana ɗan dafe kanta. Sai kuma ta ɗago idanunta akanta. “Please Aunty Nafee relax. Bafa yanda kike tunanin al'amarin b....”

     “Kamar ya ba yanda nake tunani bane Mashi'a! Ƴar aiki ta mari mun yarinya a gabanki amma ki gagara ɗaukar mataki sai ma ki hanata sanar min. Wai ke bazaki taɓa canjawa bane ba. Shike nan nagode, ai kin tabbatar min bake kika haifi Azizat ba. Da Imran ko Sahla ta mara ai da kin ɗauki mataki ko. K!! Kuma zaki ci ubanki. Zan sauke miki rawar kan da kika shigo da shi. Ai dama tun randa tazo dake na fahimci idanunki a buɗe suke irin na marasa mutunci.”

     Idanu na na runtse sosai dan har cikin ƙwaƙwalwar kaina nake jin hargagin nata. Na tabbatar da ace ta kusa da inda take nake tsaye babu abinda zai hanata kai min duka. Abinda ya matuƙar sake bani mamaki shine babu wanda ya iya tanka mata a wajen hatta shi Alhaji El-Mu'azz ɗin. Balle kuma ƙanin nasa ma. Matansu kuwa kawunansu duk a ƙasa kai kace mala'ika ke kansu. Karo na farko na kai idamuna a kansa. Fruit salad ɗinsa yake sha hankali kwance. Sai ka rantse ma baya wajen dan ko sau ɗaya bai kalli kowa ba duk wannan hargagin da akeyi. Hasali ma a dai-dai sanda Hajiya Mammar ko nace Aunty Nafee kamar yanda Alajah ta ambaci sunanta ke faɗin, “Na soke maganar aikinta na farko. Daga gobe zata fara aiki a sashena. Ke kuma Azizat tashi ki rama marinki”. A kusan tare duk wanda ke a wajen ya ɗago yana kallon ta. Yayinda Azizat ta miƙe zaram cike da farin ciki ta nufo inda nake alamar dai zata zo rama marin kenan. 

       Idanu duk suka zuba min musamman Aalaja da ranta yake a ɓace. Amma shi sai ya ma miƙe abinsa tamkar baiji mima ake faɗar ba. Cike da takun nan nasa mai cike da ƙasaita ya ratsa ta bayansu yazo ta gabana ya gitta kamar ɗazun zai wuce. Wani kalar kallo dana kasa fassarawa ya jefa min....

        “Muhammad!”.

    Alhaji El-Mu'azz ya faɗa dai-dai zai raɓani ya wuce gaba ɗaya.. Amamakina sai naga ya tsaya cak. Tamkar bazai juyo ba sai kuma ya koma da baya tamkar wanda akama dole a hankali ya amsa da, “Yess Paah”.

     Idanu mahaifin nasa ya ɗan tsira masa. Sai kuma yay ɗan murmushi cike da kulawa ya ce, “Ba zaka ci abincin ba kuma? Naga fruit salad ɗin ma kaɗan kasha fa”.

     A daƙile, sai dai cikin sanyin Muryar nan tasa ya ce, “I'm okay Paah. Kaina namun ciwo ina son na ɗan kwanta”. 

     Sosai fuskarsa ta nuna damuwa. Hakama sauran duk sai kowa ya maida hankalinsa a kansa musamman Azizat da budurwar nan data gyara masa wajen zama sanda yazo. Dan har wata ƴar zabura sukayi a kusan tare. Cikin jimantawa da kulawa sosai suka shiga masa addu'a. Kansa kawai ya jinjina musu yay wucewarsa ya fice. Sosai zuciyata ke ƙara jinjina rashin mutuncin mutumin nan. Ashe bamu ƴan waje kawai ba hatta family ɗinsa basu tsira da wannan baƙin halin nashi ba. Lallai sai a jinjina masa. Ganin yanda duk suka maida hankalinsu a kansa nasa ƙafa na taɗe Azizat dake ta leƙensa kamar mai son binsa. Razananniyar ƙarar data fasa ya saka kowa zabura sukayo kanta.

     Da wannan damar Mama Balki taja hannuna da sauri hankalinta tashe muka sulale muka fice. Ashe ita taga abinda nayi, suko sai suke tambayar miya faru? Yaya akai ta faɗi. Oho mudai tuni mun ware bamu san yanda suka ƙare ba kuma....


     🤣🤣ALLAH ya shiryeki Sam-G.


       ❤️★❤️★❤️


     “Gwaggo maganar auren nan dama nake son mu tattauna kafin ki wuce. Dan ina son ayi komai a gaggauce cikin watan nan”.

     Cike da ɗunbin farin ciki Gwaggo Gudidi ke kallon Abba dake maganar, ta saki dariya tare da yin guɗa. “Kai kai da ace na iya ghuɗa babu abinda zai hanani tsallarata sama har sai duk ƴan anguwa sunji Imamu. Ka daɗe baka sakani a farin ciki irin yau ba. ALLAH yay maka albarka. Amma ince dai ƴar mutunci ka sama mana ba irin wannan matar taka ba dan bana son a sake yin jifar gaffiyar ɓaidu”.

      Kai Abba ya girgiza yana ɗan murmushi, “A'a Gwaggo in sha ALLAHU sam ba halinsu ɗaya ba. Yarinyar da suka doka ɗin ce dama.”

     “Kai kai to Masha ALLAH. Aiko kayi ƙyan kai, dan hakan da zakayi shine babban murtani da zaka maidawa matarka tasan ka haifu cikin uwa da uba. Amma kuma ai naji yaran na faɗin ta gudu tun a ranar da abin ya faru? Ko kasan inda take ne?”.

           “A'a Gwaggo ban sani ba. Amma dai ta sanar min da garinsu. Nasan kuma insha ALLAHU can ɗin zata nufa tunda Alhaji Sadisu ya bincika daga inda Jalilahn ta ɗakkota ance bata koma can ba. Dan haka nake son muyi azamar bin bayanta tun kafin abin yayi nisa”.

      “Eh to hakan ma dabara ce ai. ALLAH ya bada sa'a da nasara. Yaushe zaku je ɗin?”.

     “Da dai gobe idan ALLAH ya kaimu ne. Sai shi Musaddiq ya jamu dan ni bazan iya tuƙi ba. Alhaji Sadisu ko baida jimirin yin tuƙi a doguwar tafiya sam”.

     Ɗan jimm Gwaggo tayi alamar tunani, dan in bata manta ba Musaddiq ya sanar mata gobe ne zai je gwaji da akace za'a musu a inda aka ɗaukesa aiki. Da ɗan sauri ta girgiza kanta. “A'a inaga shi Jafaru sai ya jaku kawai dan yasan ƴan tumaki sosai tunda shima matarsa ƴar wajen garin ce. Kaga ko ai faɗuwa tazo dai-dai da zama ba sai anta faɗi tashin tambaya ba”.

       Cikin nuna farin ciki da gamsuwa Abba ya shiga tabbatar mata da hakan yayi, ya ɗora da godiya. A take kuma babu ɓata lokaci yay kiran Jafaru ɗin. (Jafaru shine ɗa na biyu a wajen Gwaggo Gudidi. Kusan sa'anni suke ma da Abba dan komai na rayuwarsu tare sukayi. A dalilin Mom tarayyar tasu ta samu rauni. Dan yanda take nuna bata ƙaunar ƴan uwansa su raɓesa duk wanda yazo sai ya tafi da tabon rashin mutuncinta yasa Jafaru janyewa daga jikin Abba. Saboda akwai wani zuwa da yayi Mom ta cimasa mutunci harda ƙwallarsa. Daga lokacin ya tattara Abba ya ajiye gefe sai dai su gaisa sama-sama ta waya ko idan wata sabgar ta haɗasu ta dangi ko in sun haɗu a gidan Gwaggon. Abin na damun Gwaggo amma ta gagara sasantasu, sau yanzu ga dama ta samu kuma)....


         ✨💫✨💫✨💫


     Ko kaɗan Mama Balki batai min faɗa game da abinda naima Azizat ba. Sai ma Sosai yanda ta nuna tashin hankalinta ita da su Bahijja game da batun komawata aiki sashen Hajiya Mammah ya bani mamaki. Dan na sake fahimtar al'amarin babba ne. Duk da kuwa Bahijja ta ɗan bani labarinta a ƙaice ni banga wani abun tsoro tattare da ita ba, idan masifa ce na saba data Mom da ƴaƴanta ai. Sambatu suke sosai da nuna jimantawa har Mama Balki na faɗin na gudu kawai tun ma kafin komai ya faru. Zata saka mijinta ya taimaka min na fita a daren yau. 

        Murmushi na saki a hankali duk da kuwa nima ina jin shakkun al'amarin a zuciyata. Sai dai wani sashe na ƙarfafani dan koba komai zan samo labarai. Haka kawai kuma ina son sanin gaskiyar labarin tushen komai. Atake naga fuskokin masu dariya da nuna farin ciki a kaikaice a cikinsu na sauyawa a dalilin murmushin nawa. Nima sai kawai na basar da canja yanayina. Ƙwallar ƙarya nayi ƙoƙarin tarama idanuna. Tare da nuna tashin hankali ina mai roƙon Mama Balki data taimaka min na gudu ɗin... A bazata mukaji an saki tsaƙi, kusan mu dukanmu muka kalli mai tsakin. Ba kowa bace face aunty Kubra. Yanayin shock na gani a fuskar Mama Balki, da alama dai ta fahimci tayi ɓaranɓaramar sakin zancen gaban kowa. Sai dai bata iya cewa komai ba

      Cike da taɓe baki Aunty Kubra ta cigaba da faɗin, “Mama ina baki shawarar ki rufama kanki asiri. Ke dai kinfi kowa sanin halin Hajiya Mammah a gidan nan. Sannan ita ɗin ba ita ta jama kanta ba. Banda kauɗi da rawar kai uwarwa ya kaita marin ƴar masu gida. Jarumta tafi wani a cikinmu da muke haƙurin shekara da shekaru da su ko mi? Kinga yanzu ai ya rage nata ta ajiye kauɗinta da iyayi gefe ta nemawa tsoffinta kuɗin cin tuwo cikin sallama. Idan ba hakaba wataran ba sashen Hajiya Mammah ba Sashen Hajiya Babba zasu kaifafa ko kuma da karnukan gidan nan wlhy zasu haɗata”. Daga haka ta miƙe tai ficewarta tana wani rausaya da girgiza jiki.

      Shiru kowa ya gagara cewa komai, sai shashshekar kukana kawai kake ji. Kusan mintuna biyar Mama Balki tayi ƙarfin halin bama Bahijja umarnin tafiya dani ɗaki na kwanta. Babu musu Bahijja ta miƙe ta kama hannuna. Sai naga itama A'i ta miƙe fuskarta cike da tsantsar damuwa itama ya kama ɗayan hannuna....


       Duk yanda naso rintsawa barci a wannan daren kasawa nayi. Dan komai ya tsaya min arai ne. Duk yanda nake jin rashin damuwa game da yin aiki a sashen Hajiya Mammah ɗin wani sashi na zuciyata na tsoratar dani da nuna min illar hakan, dan na fahimci matar bata da mutunci sosai. Dan duk mai hankali ya auna yanda kowa ke nuna damuwarsa akan batun zai sake tabbatar da bada wasan yara bane al'amarin. Ganin yanda zancen yaƙi barin raina sai kawai na tashi na ɗauro alwala na fara nafilfili. Har asuba ban runtsa ba sai da nayi salla..........✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_



Post a Comment for "Tsutsar Nama Book 2 page 20"