Tsutsar Nama Book 2 page 18
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒆𝒊𝒈𝒉𝒕𝒆𝒆𝒏
_*_Assalamu alaikum. Gaisuwa a gareku da fatan alkairi bayin ALLAH. Dan ALLAH kuyi haƙuri! kuyi haƙuri! kuyi haƙuri!!. Ba haka naso al'amarin ya kasance ba. Sai dai kana naka ne ALLAH na nashi. Nashi kuma shine gaskiya. Saboda ku na tsara kwanaki biyar, amma suka koma kwana tara. Amma in sha ALLAHU gamu mun dawo filin daga. Zakumin haƙuri na dinga baku ko 2pages ne dan na samu na rage nawa aikin nima daga nan ko zuwa kwana uku ne. Ngd Ngd sosai da haƙurinku gareni da uzirin da kukayi min. Wanda suka kirani kuma, kuma nagode, wanda sukai ma amarya da mai rasuwa addu'a a group duk na gode ALLAH ya bada ladan zuminci😘😘🙏._
........“Kinga maza jeki ki zauna dan baƙya cikin wannan aikin”. Mama Balki ta katse min tunani. Kaina kawoi na iya ɗaga mata da faɗin, “Nagode” a taƙaice na wuce ina haɗiyar zuciya. Inda muke tsaye da da Bahijja na koma na tsaya, sai dai duk bayan sakan sai na harari inda yake. Haka dai taron ya cigaba da gudana. An ƙara gabatar da addu'a musamman akan wadda aka tara taron da fatan ALLAH ya bata lafiya, na fahimci ba kowa yasan ainahin ciwon da take tare da shi ba, dan ina jin wasu mata biyu na gulma ƙasa-ƙasa game da hakan. Wai shekara da shekaru anata ciwo-ciwo amma anƙi sanarma duniya wane kalar ciwo ne. Sosai suka bani mamaki, a raina nace duniya kenan, mutum na jikinka amma baya maka so dan ALLAH.
Natsuwar fara addu'ar na samu damar fara bin kowa dake a wajen da kallo daki-daki. A hankali Bahijja da duk hankalinta ke a kaina dan tuni sun kammala raba lemon da ruwa sun dawo inda muke ta furta, “Aunty Kandala kinga waɗanda ke a table ɗin kusa da nasu Uncle Boss ta hannun dama da muka fara bama ruwa da drinks mai milk shadda shine mahaifinsa. *_El-mu'azz Mashi_ kenan. Sosai na tsurama wanda ta faɗa ɗin ido ta gefe dan ɗazun ban iya musu wani kallon kirki ba. Eh tabbas da gani babu tambaya, dan ya ɗebo wasu a cikin kamanninsa. Kamar tsaho, dogon hanci da makamantansu. Sai dai shi baƙine sannan alamun girma ya bayyana kaɗan a tare da shi. Musamman akan gashinsa akwai furfuta tsilli-tsilli. Haka kawai nake sake jin tabbas nasan fuskar, sai dai a ina? Na manta sam dan na kasa tunawa. Cikin katse min tunani Bahijja ta cigaba da faɗin, “Sai matar dake kusa da shi. Hajiya ƙarama kenan. Itace matarsa ta biyu kuma amaryarsa. Itace mahaifiyar Arwa. Ance ta taɓa haihuwa da shi sau ɗaya tagwaye duk maza a shekarar farkon aurensu amma duk sun rasu, ba kuma ta sake ba. Arwa dai da ita tazo. Matar bata da damuwa sosai, sai dai akwai miskilanci da mulki tamkar itace ma uwar Maash ɗin. Sai dai abubuwa nata da yawa na matuƙar birgeni, duk da dai wasu na bani haushi musamman yanda Hajiya Mammah ke takata yanda take so amma bata iya cewa komai ko nuna ikon ta na matsayin matar gida, wani lokacin ma sai ka ɗauka itace matar gidan ba Hajiya ƙarama ɗin ba”.
Sosai na tsurama matar idanu itama. Ƙyaƙyƙyawar mace kam ga suffar kamala black beauty da ita. Amma da gani kasan miskilar ce dan sam babu fara'a a fuskarta kamar dai ɗazun da tai tambayar ni wacece a daƙile.
Bahijja ta cigaba da faɗin, “Na kusa da shi kuma Alhaji Abdullahi Mashi, ƙani wajen Alhaji El-Mu'azz kenan. Uwa ɗaya uba ɗaya. Ta kusa da shi Hajiya Mubeena matarsa uwar ƴaƴansa uku. Itama dai tana da ƙarancin damuwa, sai dai ta hannun damar Hajiya Mammah ce dan ƙiri-ƙiri take nuna banbanci tsakaninta da Ummi ɗin (Hajiya ƙarama) na taɓa jin su Aunty Falila suna gulma wai ai dama ƙawarta ce acan ƙasar Niger da tayi aure, kin san mahaifin su Azizat buzu ne, shiyyasa kike ganinsu da shegen gadarar nan da masifa duk da dai shima wannan family ɗin masifa kamar a jininsu take, fitinannun mutane ne na bugawa a jarida, Uncle Boss ne kawai nake gani ma shiru-shiru a cikinsa ko magana da wahala kaji yana yinta, in ma yayi ɗin ba lallai kaji sautin muryarsa ba, sai ko Aunty Mama itama tana da sauƙi sosai, idan kinga tana faɗa an ɓata bata rai ne matuƙa. Daga table ɗin gefensu akwai Azizat ita kam kin haddaceta” tai maganar da shaƙiyanci, sai kuma ta cigaba da faɗin, “Sai Mabrukah autar Hajiya Mubeena, sai....”
Da sauri tayi shiru saboda yafito ta da Azizat ɗin tayi, jikinta har rawa yake ta nufeta. Wani takaici ne naji ya ƙwaƙume min zuciya. Bamma san na saki sirrin tsaki ba da taɓe bakina na ɗauke kaina daga sashensu ma gaba ɗaya. A bazata suka sauka akan Hajiya data ɗakkoni daga Abuja. A mamakina sai naga ta sakar min murmushi harda kashe ido ɗaya. Ɗan tsira mata idanu nayi cikin nazartar yanayin nata dan haka kawai komai daya faru a tsakaninmu tun daga Abuja ya shiga dawo min. Yanda take wani bina da kallon ƙurilla ya sani balla mata harara na bar wajen gaba ɗaya dan muna facing juna. Dai-dai nan mc yay kiran sunan uban taro cike da girmamawa. A tunani na Alhaji El-Mu'azz ɗin ne zai tashi, amma sai naga makirin nan ne ya miƙe cike da ƙasaita bayan ya gama shan ƙamshi da busar iska da fesarwa. Taku yake tamkar mai tafiya a kan gilashi, dan sai ka ɗauka ma bazai ƙarasa inda mc ɗin yake ba dan jiji da kai. Mic ɗin ya amsa, sai kuma yay ɗan shiru kamar wanda ya rasa abin faɗa. Baki na taɓe tare da watsa masa harara sai idona a cikin nashi. Da sauri na ɗauke ina mai murguɗa bakina kawai....
“Hummm!!” ya faɗa cikin mic ɗin ta yanda kowa dake a wajen sai da ya ji sa. Amma a mamakin kowa ya sake ɗinke fuska kamar bashi ne yace hummm ɗin ba. Sai ma cigaba da maganarsa da yay cikin harshen turanci mai haɗe da faransanci, yau dai ALLAH ya taimake mu ba'ai Hausa ba balle a ɓaga mana yare. Godiya ce kawai yayi a taƙaice tare da roƙon cigaba da tayashi addu'a ALLAH ya bama Ummiensa lafiya. Sai kuma yay shiru kansa a ƙasa fuskarsa na nuna tsantsar damuwa. Kusan minti ɗaya kafin ya ɗago yana mai kai handkerchief saman fuskar sa ya goge. Sai kuma ya saki wani lalataccen murmushi yana ɗan lumshe idanunsa da buɗewa a lokaci guda ya saukesu akan mahaifinsa. Murmushi ya sakar masa, sai kuma ya miƙe tare da nufosa shima. Yana isowa ya rungumesa yana ɗan bubbuga bayansa alamar lallashi. Daga haka ya amshi mic ɗin hannunsa shima ya fara magana. Kusan abinda dai ɗan nasa ya faɗa shima ya maimaita, sai abubuwa kaɗan daya ƙara a kai sannan suka yanka cake a tare. Baban ne ya fara ɗibowa ya kai bakinsa. Cikin wani yanayin narke fuska ya motsa ƙananun lips ɗinsa kaɗan, sai dai baban na zuwa gab da bakin nasa sai ya juya hannunsa zuwa nasa bakin ya cinye cake ɗin tare da lakata masa sauran na hannunsa a saman hanci. A take wajen ya ɗauki tafi da dariya. Shima murmushi yayi yana kauda kansa. Sai baban ya rungumosa yana dariya.
Haka kawai na tsinta kaina da yin murmushi akan wasan nasu, sai kuma na haɗiye da sauri dan tuna akan wa akeyi. Bayan sun je sun zauna Hajiya Mammah, Aunty Mama, Hajiya ƙarama, Hajiya Mubeena, Alhaji Abdullahi duk sun fito sunyi bayani tare da addu'a ga Hajiya Ummu-Hidaya kamar yanda naji suna ambata dama rubutawa da akai jikin ƙaton cake da wani irin golden color mai sheƙi tamkar ba cake ba. Gaba ɗaya zaman wajen bai wuce na awa biyu da mintuna arba'in ba. Aka raba ƙyauta har da mu daga haka taro ya tashi. Bayan tsirarun baƙin da aka gayyato irin su Hajiya sun wuce Aunty Mama ta bama Mama Bilki umarnin zuwa dani garesu bayan sallar isha'i. Ta amsa mata da girmamawa yayinda ni kuma nai kamar ban jisu ba dan hankalina gaba ɗaya ya tafi wani waje daban.....
🌜🌟🌛
Matuƙar tashin hankali Musaddiq da Halime tai gudu ta kira ya shiga ganin Abba cikin jini. Rasama abinda zai yi yay har sai da maƙota suka shigo. Sune suka ambaci asibiti sannan hankalinsa ya dawo jikinsa. Ga Bibaa da Auta na famar darzar kuka. Baby kuwa sai surutai takeyi. Duk wanda ya shigo kuma sai ta nuna Mom data maƙure gefe jikinta na maƙyarƙyata.
“Kun ganta nan itace ta kashe mana Abba. Kawai itama a kasheta dan nice alƙali na yanke hukunci”. Abinda Babyn ke faɗa kenan cikin Muryar ƴan maye da surkulle. Duk da kowa kanji shock da abinda ta faɗa ɗin da kuma yanayin da take ciki babu mai bi takanta. Burin kowa dai a kai Abba asibiti kada ya rasa ransa....
Koda suka isa asibitin da ƙyar aka amshi Abba, dan sai da Yaya Musaddiq yay ƙaryar faɗuwa yay a banɗaki sannan. Da gaggawa suka shiga bashi kulawa, yayinda aka bar su Musaddiq kai-kawo a waje kowa na addu'a a zuciyarsa. Sun kwashe tsahon lokaci kafin doctor ya fito. Bayanin da yay musu na cewa yaji ciwo sosai a kan nasa kuma bai farfaɗo ba har lokacin ya sake tada hankalin Musaddiq. Duk yanda yaso daurewa ya kasa. Dan harga ALLAH duk abinda Abban ke musu shi da ƴan uwansa bai taɓa jin ya tsani ƙanin mahaifiyar tasu ba. Saboda yana kallon fuskarta ne akan ta kawun nasu. Tun a daren yay kiran ƴan Gwarzo da Gwaggo Gudidi. Sai dai suma bai faɗa musu gaskiyar al'amarin ba dai. Hankalinsu ya tashi, washe gari kuwa tunda sassafe sai ga Gwaggo Gudidi. Wajen tara sai ga ƴan Gwarzo suma har da su Kawu Musa saboda kara. Dan su ta ɓangaren mahaifinsu suke bata ɓangaren Abban ba. Har Azhar Abba bai farfaɗo ba, asibiti ya ciga da dangi amma babu Mom. Sai su Bibaa da Baby. Abbas ma sai kusan azhar ya iso hankali tashe. Dan bai san mike faruwa ba sai da yaje gida yake ji a anguwa. Koda ya shiga cikin gidansu ya samu Mom nata darzar kuka gefenta mahaifiyarta Inna zaune jigum ta zuba tagumi da hannu biyu. Bai iya cewa da su komai ba dan yanayinsu da sambatun da Mom keyi ya tabbatar masa da abinda mutanen suka faɗa. Kiran Musaddiq yay a waya ya sanar masa asibitin da suke. Sai ko gashi ya iso. Hankalinsa ya sake tashi da jin Abba fa yaƙi farfaɗowa, harma likitocin na maganar ya tafi doguwar suma........✍️
_Wayyo Abbanmu kada ka tafi ka bar Halime😌😌_
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
Post a Comment for "Tsutsar Nama Book 2 page 18"