Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Tsutsar Nama Book 2 page 17

 𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_

       _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒆𝒆𝒏_


......Akan takalman ƙafarsa na fara sauke idanuna, yanda suke sheƙi da ɗaukar idon mai kallo ya isa tabbatar maka almubazzaracin da akai da kuɗi wajen sayensu. Coffee brown suit ne a jikinsa, sai rigar ciki milk color. Kamar kullum botiran farko a buɗe har ana iya hango jikinsa kaɗan. Luf-luff gashin kumatunsa ke kwance a saman fuskarsa tamkar masu barci, sai wani irin sheƙi suke suma. Hannunsa ɗaya a cikin aljihun wandonsa ɗayan riƙe da wayar dake manne a kunnensa yana wani motsa ƙananun pinkish lips ɗinsa a hankali kamar wanda akaima tilas. Kamar kullum kunnensa ɗaya manne da ɗan kunne, daga tacan saman kansa zane da kitso ƙwara biyu zane ata gefe da gefe, tsakkiya wiving kusan biyar, cikkune dan haka ɗaure yake a tsakkiya ƙarshen kitson kuma gashin a warware ba'a kitseba dan haka ya sakesa kawai a baya yana lilo. Wani irin takaici da haushi ya sakani kallon fuskarsa duk da nasan tabbas yayi ƙyau. Karaf kuwa idanuna a cikin nasa. Bamma san lokacin dana balla masa harara da murguɗa nawa bakin ba. A mamakina sai kawai naga ya lumshe nasa idanun tare da buɗesu a lokaci guda yana cije gefen lips ɗinsa ya ɗauke kansa. nima ɗauke nawan nayi kamar zan fasa kuka, ji nake tamkar naje gareshi yanzu na zazzage masa abinda ke a raina. Amma dai na dake, sai harara dana sake jefama jelar PA ɗinsa dana fahimci tunda idonsa ya sauka a kaina yay suman tsaye. Niko na ɗauke kaina tamkar ban san da zamansa a wajen ba. Tunda nasan dai duk abinda mugun ogansa ya ƙulla tare da shine makirin shima.


       Addu'ar da aka fara gabatarwa ya saka kowa a wajen sake nutsuwa. Mu dai marasa gata duk muna a tsaye kan ƙafafunmu, yayinda suko ke zaune a kujerun da aka ƙawata wajen. Sosai yanda akai addu'ar wa kowa harda iyayenmu ya sake saka min nutsuwa har idanuna na tara ƙwalla. (ALLAH sarki rayuwa, da ace muma namu iyayen na raye babu yanda za'ai mu tsinta kammu a cikin wannan gararin rayuwar. Amma ko yanzu ma alhmdllh, koba komai mun rayu cikin aminci tunda gallazawar rayuwa batasa mun lalace ba). Kewar su Yaya Musaddiq ce ta sake taso min sabuwa har na zurfafa a tunani batare dana farga ba. Taɓanin da Bahijja tayi ne ya maidoni a hayyacina. A hankali na sauke ajiyar zuciya da nannauyan numfashi. Cikin raɗa-raɗa a saitin kunnena ta ce, “Aunty Kandala muje zamu fara bada drinks”. Kaina kawai na iya jinjina mata, dan gaba ɗaya babu wani ƙarfi a tattare da ni. Ta wajen babban table ɗin da aka shirya nau'ikan abinci dana lemuka da ruwa muka nufa. Bahijja ta zari handglob guda biyu ta miƙamin tare da mun nunin na saka. Itama ta zara ta saka a nata hannun sannan ta buɗe ƙatuwar kular da kayan ruwan ke ciki ta ɗiba lemunan da ruwa duk ta loda a babban tray data jawo guda biyu. Sai da ta gama zuba nata da nawa sannan ta ce, “Yauwa to muje. Kowa a gabansa zaki fara ajiye ruwa sannan ni kuma na ajiye lemon da suka buƙata”.

       “Kamar ya?”.

   Na tambaya cikin rashin fahimta. Ƴar dariya tayi. Kafin ta ce, “Na zuba miki ruwa ne dan kar su baki wahala. Shi ruwa zaka ajiye ne kawai. Amma lemo dole sai mutum ya zaɓa sannan”.

       Kaina na jinjina mata alamar gamsuwa, sannan na kama tray ɗin na ɗaga ina ɗan taɓe baki. Ai da sauri na maida na ajiye ina waro idanu. Ai wlhy bazan iya ɗauka ba yamun nauyi. Ragewa na fara yi, hakan ya sata zaro idanu waje alamar nuna mamaki. “Lafiya kike ragewa?”.

      “Yamun nauyi wlhy Bahijja bazan iya ɗauka ba”.

    Sake waro idanu tayi, niko ban sake kulata ba na rage fin rabi sannan na ɗauka. Kallo take mun na tama rasa abin faɗa. Ni ko na sake ɗauke kaina gefe kamar ban ganta ba. Dole itama ta barni muka bar wajen tana gaba ina biye da ita. Suma sauran kowa ya fara aikinsa dan komai a tsare yake. Mun fara da table ɗin farko. Mai ɗauke da mutane huɗu kamar ko ina. Maza biyu masu tsananin kammani, a fisge kuma suna kama da mutumin can Maash. Sai dai kawai su baƙaƙe ne. Tabbas nasan mai irin fuskar nan amma na manta a ina. Sai mata guda biyu ƙyawawa suma, ɗaya fara tas ɗaya black beauty. Su duka sunci ado sosai mai tsananin ƙawa. Ganin kallon da suke min na rashin sani yasa naji kamar duk na daburce. Amma sai na dake kaina a ƙasa na shiga haishesu ƙirjina na bugawa da sauri-sauri. Mazan ne kawai suka amsa min, yayinda baƙar matar ta dubi Bahijja a gadarance ta furta, “Wannan fa?”.

          Jikin Bahijja har ɓari yake. Cikin in-ina ta amsa da, “Au...aun..Aunty Mama ce tazo da ita randa ta iso”.

    Su dukansu ɗan kafeni sukai da kallo, sai kuma duk suka janye cike da basarwa. Jiki a sanyaye na bar wajen, batare da ina kallon gabana ba saboda zancen zuci na iso table na gaba. Ganin nayi tsaye kawai Bahijja ta ɗan zungureni, firgigit na kawo numfashi, ɗagowar da zanyi na sauke idanuna a kansa. Zaunensa yake a harɗe fuskar nan kicin-kicin tamkar ba wanda ya tara jama'a ba. Gaba ɗaya hankalinsa na akan tab dake a hannunsa ne. Yanda yay serious a kanta zai baka tabbacin abinda yake yi mai muhimmanci ne. Ga uban ƙamshin turarensa da ya mamaye wajen gaba ɗaya. Fuska na yamutse tare da ɗauke kaina. Harara na ballama ɗan koren PA ɗinsa dake table ɗin bayansu. Ƙasa naga yayi da kansa yana murmushi. Jinai zuciyata ta ƙulu da murmushin nasa, amma sai na danne tare da cije lips ɗina kawai....

        “Woow! fine girl ko ana mana rowan ruwan ne?”.

     Ɗaya daga cikin waɗan da ke zaune a table ɗin tare da shi ya dawo dani a hayyacina. Ni sai ma yanzu na lura da sauran dake zaunen a tare da shi. Su duka su nasan fuskokinsu a wajen taron buɗe Companyn sa na Kano. Dan ALLAH ya bani baiwar da dawahala nai maka gani ko ɗaya ne na manta fuskarka koda ace ban riƙe suna ba ko a inda na sanka ba. A hankali na ɗan yamutse fuska ta. Batare da nace komai ba na fara ajiye musu ruwan. Uku na ajiye abina batare da nashi ba, dan kowa a gabansa na ajiye amma shi banda shi. Na ɗaga tray ɗin zan bar wajen wannan dai da yay maganar ya ɗan waro idanunsa yana nuna min shi. “Beauty baki ajiyema boss ba fa”. Yi nai tamkar ban jisa ba sai da Bahijja tasa hannu ta ɗauka ruwan ta ajiye masa jikinta har yana ɗan rawa. Harararta nayi batare dana san dalili ba. Itako ta waro idanunta na nuna mamakina. Tray ɗin na sake ɗagawa da nufin barin wajen ina dallamasa harara ta gefen ido dan tunda mukazo wajen ko sau ɗaya bai motsa ba balle kai tunanin yama san da zuwan namu, batare da nasan yanda akai ba, ta yaya kawai tray ɗin ya suɓuce min na tafi gaba ɗaya na. Idanu kawai na runtse tare da sallamawa, amma sai na jini zaune jikin mutum, yayinda shi kuma tray ɗin ya suɓuce a ƙasa sauran ruwan suka tarwatse. Wani irin zuƙa da nayima mayataccen ƙamshin turarensa ya saka gabana faɗuwa. Da sauri na buɗe idanuna dake a rufe. Sai kawai na waro su tare da yunƙurawa da sauri zan miƙe amma hakan ya gagara. Dan sake zamewa nayi na koma jikin nasa gaba ɗayana har ma fiye da farko.  

      “Sai kice son hawa kike ba sai kinyi pretending ba”.

    Naji saukar muryarsa a cikin kunnena. A wani irin zafafe na sake yunƙurawa gaba ɗaya na na miƙe jikina har tsuma yake, sai da Bahijja data gama firgita ta riƙoni. Jinai bazan iya daurewa ba, idanuna na tara ƙwalla na watsa masa harara, sai dai ina motsa lips ɗin na nufin juye masa abinda ke raina naji na gagara hakan. Sakamakon wani shegen kallo daya tsatstsareni da shi tare motsa lips ɗinsa a hankali, “Kina cewa tak sai kowa yasan ke MATAR MAASH ce”.

    Da masifar ƙarfi na cije lips ɗina hawaye na sake ciko min idanu. Badan na samu horo akan aikina game da salon da yay maganar ba da bazan fahimta ba. Amma gamu ƴan jarida yaren magana da ido ma an karantar da mu balle na motsa lips. Da wani irin salon rainin hankali ya kai yatsarsa manunuya saman goshinsa tamkar zai gyara silin gashi yay salute tare da sakin wani matsiyacin murmushi gefen baki ya kanne ido ɗaya.

     “Sai na tarwatsa rayuwarka”.

  Na faɗa nima a saman lips ɗin ina haɗiye hawayen da suka ciko min idanu. Sanin zasu iya zubowa na kai durƙushe nima ina taya Bahijja tsinci ruwan daya tarwatse. Sai faman haɗiyar zuciya kawai nakeyi dan ni kaɗai nasan abinda nake ji a cikinta, nu mutumin nan zai cema ina son hawa masa jiki ne dama. Ƙasa-ƙasa Bahijja ta furta, “Aunty Kandala kice masa yayi haƙur....” ruff ta rufe bakinta tare da haɗiye sauran abinda ke bakin nata saboda hararar dana balla mata. A fusace na miƙe tare da sunkutar tray ɗin nabar wajen. Mama Balki ce tai min nuni da nazo inda take. Dole na nufi inda muka ɗebo ruwan. Amsar tray ɗin tayi tana faɗin, “Badai kiji ciwo ba ko ɗiyata? Alhamdullah ma Alhaji ƙarami na kusa ya taimaka miki da kinyi muguwar faɗuwa ai. Sai naci ƙaniyar Bahijja kuwa, tunda bance harda ke za'ayi aikin nan ba amma ta jaki”.

          Sosai naji raina ya ƙara zafafa. Wato su abinda suka fahimta kenan nazo zan faɗi ya taimakeni, alhalin ina zargin taɗeni akayi da ƙafa, tunda karo naci da abu a bazata, kuma babu wani dutsi ko ƙarfe balle ace shine. Ko rantsu nayi ba'a bina bashin kaffara mutumin nan shine silar faruwar komai, dan shine ya taɗeni da ƙafarsa........✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*



*_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_


Post a Comment for "Tsutsar Nama Book 2 page 17"