Tsutsar Nama Book 2 page 7
*_Typing_*
*_TSUTSAR NAMA....!!_*
_(Itama nama ce)_
......“Madam bafa taci abincin nan ba, ko buÉ—e plate É—in ma batai ba kuma tayi barci.” Janny ta faÉ—a cikin nuna damuwa.
Ƙaramar dariya Hajiya ta sauke tana wani lumshe idanu, sai kuma ta buÉ—esu akan Janny cike da salon irin na wayayyun mata da suka gogu da sanin duniya. “Barta yunwar ai ba Æ´ar gidansu bace, dan kanta ma zata É—auka taci”.
Dariya tayi itama Jannyn da jinjina kanta. “Hakane Madam. Amma yarinyar yana da Æ™yau fa sosai, ina ka samo shi haka? Ko dashi zamuje Lagos ne?”.
“Tsintacciyar mage ce, dan haka ma na dawo da tafiyarmu gobe kafin ta canja shawara. Saboda na kula babbar kaddarace wannan, kwalliya da sutura kawai take buÆ™ata”.
Sosai Janny ta washe haƙwara, dan duk hausar da Hajiya tai tsaff ta gane kasancewar taji hausa sosai. Hajiya ma murmushin taketa faman yi, dan ita kanta tasan zata ƙaru da yarinyar sosai...
★Washe gari kamar yanda Hajiya ta faÉ—a suka tashi da shirin wucewa Lagos, harda Samraah nan dako sunanta basu sani ba har yanzu. Tunda suka tambayeta sau É—aya tayi shiru basu sake tambayar ba. Tun jiyan kuma tana É—aki kwance sai dai akai mata abinci a É—akko kwano.. Janny ce mai Æ™oÆ™arin kai-kawon, Hajiya dai nata bada umarni kawai, bakuma ta sake neman ganin Samraah ba tun shigowarsu gidan sai a yanzu da suka kwana suka yini dan tafiyar yamma zasuyi.
Ita dai Samraah bata san ina zasu je ba. Koda ta tambayi Hajiya kuma sai cewa tai ta jira zata gani. Badai tace ita ƴar Kano bace, zata bata mamaki ne. Al'amarin kamar asiri Samraah ta gagara cewa da Hajiya komai. Hasalima jinta take jikinta duk ya gama mutuwa ga bakinta ya mata nauyi. Sannan bata jin zata iya tsallake umarnin Hajiya sam koda cewa tai ta shiga wuta ta ƙone ko ruwan teku.
Post a Comment for "Tsutsar Nama Book 2 page 7"