Tsutsar Nama Book 2 page 6
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒊𝒙_
........A hankali ta ɗan sakar min murmushi da faɗin, “Ko zaki iya mun alfarma”.
Cikin ƙosawa nace, “Tami?”.
“Ta sanin inda zakije yanzu?”.
“Ban san inda na nufa ba, sai dai ina fata da addu'ar koma ina ne ya kasance hanyar cimma ajalina”.
Ɗan jimm Hajiyar tai kamar mai nazari, sai kuma ta saki murmushi mai ban mamaki tana wani juya idanu cike da salo, “Bazan hanaki tafiya ba, amma zan so ki bani dama ta ƙarshe muje gidana, maybe zan iya nuna miki hanyar cimma nasararki ta barin duniyar kamar yanda kike fata”.
Idanu sosai na tsira mata tamkar mai son tankaɗe gaskiya da rairayeta akan fuskarta, kusan minti ɗaya na ɗan kauce zuciyata na ayyana min na bita na samu mafaka koda na wasu kwanaki ne, dan na tabbatar a yanzu na koma Kano makirin nan zai iya bina. Kuma Abba da su Kawu bashi ni zasuyi, amma yanzu idan na laɓe a bayanta zan iya kiran Yaya Musaddiq muyi shawara dan shiga Kano kai tsaye yanzu haɗari ne. Sai dai kuma ita kanta bawai ina jin na yarda da ita bane ba ma ai. Amma bari na gwada sa'ata mugani. fuskata na ɗago na ɗan kalleta da faɗin, “Kina so kiyi wasa da hankalina ne kawai Hajiya”.
Da sauri ta dakatar da in da faɗin, “Ko ɗaya ba haka bane ba. Mizaisa nai wasa da hankalinki ni kuwa, dama kawai nake buƙata daga gareki zaki tabbatar da abinda na faɗa ɗin in sha ALLAHU”.
Nan ma dai shiru nayi ina kallonta kawai, tai saurin faɗin, “Ki yarda dani koda na sati guda ne, idan kinga ba hakaba zaki iya ɗaukar mataki kowane iri”.
Shiru na sake yi na wasu ƴan sakanni kamar mai nazari, sai kuma batare da nace komai ba na dawo da jikinna cikin motar sosai tare da jawo ƙofar na rufe kamar yanda take. Sosai Hajiya ta sauke ajiyar numfashi da har ya bani mamaki, sannan ta ɗan kalleni, sai dai batace komai ba. Nima ban sake cewa komai ba ina dai addu'a a zuciyata ALLAH ya hanata nasarar cutamin, ALLAH kuma yasa ba daga ƙarƙashin makircin makirin nan Maash tazo gareni ba.
★(✷✷✷‿✷✷✷)★
Tunda Hayatu yake bai taɓa shiga tashin hankali irin na yau ba musanman a yanzu da yake waya da Maash yana mai sanar masa guduwar Samraah daga asibiti. Dan Maash ɗin yayi wata ƴar tafiya ne ta gaggawa, tunda ya fara harkar business duk inda zai je yana tare da Hayatu, amma a wannan gaɓar ya barsa saboda al'amarin Samraah da ya kasance da ga shi sai shi suka sani.
Har tsawon mintuna biyu babu alamar Maash zai amsa. Kuma yana online. Hankalin Hayatu ne ya sake tashi, muryarsa har harɗewa takeyi wajen sake faɗin. “Wlhy nayi duk yanda kace Sir, zaman jiran isowarsu gidan kawai nake ma amma tai kirana wai basuganta ba. Ba laifina bane, ba daga ɓangarena bane aka samu kurkure ka yarda dani. Ka kuma bani izinin sanarma ƴan sanda na tabbatar tana cikin garin Abuja bata isa fita ba”. Shiru nan ma Maash yaƙi ya tanka. Wayar Hayatu ya cire daga kunnensa ya duba, har yanzu yana online ɗin dai tankawar ce bazai yi ba. Yafi kowa sanin halin Maash yanzu, dan ko iyayensa bazasu faɗa masa hakan ba. Ko motsi da idanu ogan nasa yayi yakan fahimci yaren balle. Ya tabbatar shirunsa a yanzu na ɓacin rai ne, kuma bazai tanka masa ɗin ba har sai idan shine yaso hakan. Hakan kuwa akayi, bai tanka masan ba shi kuma ya kasa yanke kiran saboda shakka, haka ya haƙura akaita ɗibar masa kuɗi har tsahon fin awa sai da shi uban gayyar ya gaji dan kansa ya yanke kiran sannan hayatu ya kai zaune cikin kujera jagwab dan tun ɗazun ko zaman ya kasa yi. Kansa kawai ya dafe yay shiru zuciyarsa na gudu. Dole ma duk yanda zai yi yayi dan gano yarinyar nan kafin cikar awanni ashirin da huɗu. Idan ba hakaba yasan akwai matsala.....
💞💞💞💞
Wata shegiyar dariya Alhaji Sadisu mai agogo babban aminin Abba ya saki harda ƙyaƙyƙyewa. Cikin ƙuluwa da nuna jin haushi kuwa Abban ya zuba masa idanu. Sai kuma ya yunƙura zai tashi amma Alhaji Sadisun ya riƙosa yana faɗin. “Afuwan afuwan Imamu. Wlhy abin naka ne zabban dariya. In kana abu sai naga kamar wani ɗan yaro bai mai garjejen saurayin ɗa kamar Abbas ba. Yo banda abinka Gwaggo ai gata tamaka wlhy. Ka buɗe bakin aljihu kawai malam musha biki ai ba wuce auren kai ba. Dama dai kaine kaso maida kanka pastor zama da mace ɗaya shekara fin ashirin bayan ALLAH ya baka dukan rufin asiri. Yo ALLAH na tuba da ana yin fin huɗu da ba tuni nayi ba”.
“Amma dai ai na sanar maka matsalata ko Alhaji Sadisu. Kuma kaina shaida ne akan halin Jalilah tunda na gwada son ƙara auren a shekarun baya har sau biyu amma aka nema nakasa yaran mutane.”
“Yo dan ta samu nasara a baya sai akace yanzu ma ka karaya zata samu. Alhaji Imam zama namiji kaji, tun farko kai ne kake ɓata shirin dama da kake sanar mata da wuri. Kayi shirunka yanzu har sai ɗinyar makaho ta nuna a hannunsa sannan ka bada filin fara wasan jifa tunda tsoronta kake ji”.
“Humm bazaka gane ba kawai, amma zan iya yarda da shawararka akan ɓoye matan. In kuma hakan zata faru fa sai dai na nema auren a wajen kano.”
“Wannan duk mai sauƙine, kabar komai a hannuna kawai. Kai dai jeka ka fara shirin gyara inda amarya zata zauna nan da sati ɗaya zan maka jagora kai da kaina sai ka gode min saboda inda zan kaika wlhy”.
Murmushi Abba yay a karo na farko, dan haka kawai yake jin kuma batun ƙara auren na sake masa tasiri a zuciya....
🥱Hummm Abba cin amana ko.
_________★
Gida ne mai ƙyawun gaske madaidaici muka isa a anguwar mai tama kamar yanda na gani a symbol, dan komai najin daɗin rayuwar gani da ido a kwaishi. Ƙamshi da tsarin gidan yafi komai ɗaukar hankalina, dan haka nake ta ɗan kalle-kalle a kaikaice. A karo na babu adadi Hajiya da tuni takai zaune cikin ɗaya daga kujerun falon ta dubeni ganin yanda nai tsaye a farkon shigowa. Cike da kulawa ta ce, “Ƙaraso ciki mana ɗiyata. Kar kiji wani shakku ko tsoro, wannan shine gidana anan Abuja, sai dai bana zaman daya wuce sati biyu a cikinsa a duk ƙarshen shekara. Sai kuwa idan wani uziri ne ya kawoni nakanzo nai kwana ɗaya biyu har ma zuwa uku wasu lokutan na koma. A yanzu haka ma kwana biyu ya rage na wuce”. A hankali na haɗiye yawu alamar son cewa wani abu, sai dai kafin nace ɗin Hajiya ta katseni ta hanyar ƙwala kiran sunan “Janny!”.
“Yes Ma'am”.
Wata murya ta amsa daga can gefen wata ƙofa da hanyarta aka shirya kujeru da tebiri. Kafin na gama nazarin tsarin da kujerun dining ɗin sukayi da zamansu a wajen wadda Hajiya ta kira da Janny ta fito. Budurwa ce itama sai dai zata girmeni sosai, da gani shigarta da uban gashin attachment dake saman kanta ya isa baka amsar ba musulma bace. Cike da girmamawa Janny ta sake gaida Hajiya tana ɗan satar kallonna. Nuna ni Hajiya tai da faɗin, “Kije da ita ciki, tai wanka a bata abinci”.
Murmushi Janny tayi a karo na farko, cike da girmamawa ta amsawa Hajiya tana nufoni. “Sannunka”. Abinda Janny ta faɗa kenan tana mai riƙo hannuna. Ban amsa mata ba, sai ma ƙoƙarin turjewa da nayi alamar bazanje ba. Hajiya dake kallonmu ta sake sakin murmushi. “Kinga ɗiyata nasan mike a ranki, karki damu shi komai na rayuwa mataki-mataki ne tamkar ajin makaranta. Ki kwantar da hankalinki zamuje gaɓar da kike buƙata. Bani nai miki alƙawari ba”.
“Amma Hajiya.....”
“Shiiii!! Kar kice komai bita kawai”. Hajiya ta faɗa cikin katseni tana tsuke fuska a karo na farko. Canjawar fuskar Hajiyar ya ɗan firgitani, dan haka nabi Janny kamar yanda aka bata umarni tun farko....
Cikin dauriya da danne duk abinda ke mun kai-kawo a cikin rai nayi wanka na fito fes dani cikin doguwar riga mara nauyi ƴar kanti da Hajiya ta bani na saka. Ga wani ƙamshi mai daɗi na tashi a jikina. Hatta da dunƙulallen gashina da zaman asibiti yasa baya samun gyara sai da na wanke na busar da hair dryer dana gani a toilet ɗin. Yanda na fito da shi ne a buɗe yasa Janny sakin baki tana kallona. Fuska na ɗan tsuke amma sai hakan bai sata yin shiru ba sai da tayi magana. Da ga ƙarshe ta laƙemin wai zata tayani gyarawa. Mai sosai Janny ta saka min masu daɗin ƙamshi da ma wasu abubuwan da suka sake miƙar da tsahon gashin nawa daya fara dankwafewa tsaff, sannan ta fake min shi a ribbons. Ni a karan kaina sai da naji daɗin kan nawa dama a kwanakin nan ya isheni da ƙaiƙayi. Shiru nayi kawai zaune ina ƙarema kaina kallo, a take naji tausayin kaina ya kamani. Wasu hawaye masu zafi da ɗaci suka shiga sakko min. Hannu nakai na sharesu da sauri, saboda tuna nayi alƙawarin bazan sake kuka ba akan halin da nake ciki. Plate ɗin da aka kawo min na abinci na ɗan tsurama ido, sai kuma na tureshi gefe dan bana buƙatarsa a yanzu duk da uban ƙamshin dake tashi mai tabbatar da abincin zaiyi daɗi koda banga minene ba. Zamewa nai kwance a saman lallausan carpet ɗin da shima ke ta tashin wani irin ƙamshi mai daɗi, gashi tsaf babu datti. Gajiya da wahalar dana sha ya sa barci yin awon gaba da ni cikin ƙanƙanin lokaci..........✍️
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
Post a Comment for "Tsutsar Nama Book 2 page 6"