Tsutsar Nama Book 2 page 5
*_Typing📲_*
*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_
_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_
_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒊𝒗𝒆_
____________
Toh Nazo maku
Da kayan arziki
Kudai kunsan mata sai da gyara
Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta
A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE
Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne
Muna da
Shedaniyar gumba
Gumba mai saying
Garin mai kabbara
Mai dalalan miyau
Wayyo dadi
Mai bunsuru
Dan jarida
Soyayya dole
Bakin kyalle
Tadire ta girke
Gumba mai likkafani
Maza taye
Zumar kwakwa
Zumar ridi
Zumar dabino
Zuma mai ma'ul ijaba
Farin jini
Mallakoki
Gumba kalla kalla da dai sauran su
A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba
Ga kuma maganin slimming
Gyaran nono
Maganin hips
Maganin Kara kiba
Da dai sauran su
Kayan mu tested and trusted ne
Muna maraba da masu siyan Daya ko sari
Muna Nan cikin garin kaduna
Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah
Ni ce taku har kullum
AMINA GACHI
07034404975
CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE
KADUNA
Phone no 07034404975
_____________
.......“Alhamdulillah, I am very happy today we will send you off. I am very happy with the way you calmed down and gave us your cooperation. May God give you good health and protect the future”.
Murmushi na saki kaɗan ina jinjina kaina. Kafin a hankali na furta. “Thanks you doctor”.
“Ni ya kamata nayi godiya”.
Dariya yanda ya haɗa hausar da yanayin fitar kalaman ya bani, amma sai banyi ba nai murmushi kawai. A ƙasan raina ina jinjina karamcinsa gareni duk da kasancewarsa ba ƙabilata ba, sai dai ya nuna min kusancin musulunci dake tsakaninmu yafi na ƙabilancin. A kusan tare muka miƙe ni da shi, a dai-dai nan akai knocking ƙofar ɗakin jiyyar tawa. Kai tsaye ya bada izinin shigowa. Cikin gurɓatacciyar hausa hamshaƙiyar mace fara tas ƴar duma-duma tayi sallama ta shigo. Kallon cikin ido mukaima juna. Sai kuma matar ta janye nata tana maidawa kan doctor tare da rissinawa tana gaisheshi irin dai girmamawar ƙabilu. Ya amsa mata da kulawa. Sai kuma ya nuna mata ni. Hankalinta ta sake maidowa gareni tana murmushi. Sai kuma cike da kulawa ta gaidani da jiki. Amsa mata nayi a ɗarare, dan haka kawai naji matar batai min ba. Sai dai me bayani naji doctor na mata akan ya gama komai daya dace sai ta wuce dani. Kallonsa nayi a firgice zanyi magana sai kuma zuciyata ta ƙwaɓeni dan na tuna aljananci da hatsabibancin mai asibitin. A take na canja yanayi kawai na fara masa godiya.
Nurse ɗin da suka kula da ni ne sukai min rakkiya har inda motar matar take. Babu abinda zuciyata take face luguden daka da saƙawa da kwancewa. Dole fa a wannan karon na kuɓutar da kaina dan wannan ce kawai dama ta ta ƙarshe ta ƙuɓuta a hannun mutumin nan. Saboda zuciyata ta gama tabbatar min shine ya turo matar nan, idan kuma bashi bane to tabbas zai iya min wani tarkon da ita kamar yanda akai min a Kano sanda na baro gidansa.
“Ya rabba aiko nayi mantuwa”. Na faɗa dai-dai ina ƙoƙarin shiga motar da Semi ta buɗe min. Su duka kallona sukai, amma sai na sake zabura cikin hanasu damar min tambaya ina faɗin su jirani zan ɗakko na dawo yanzun nan. Yanda naga babu wacce tai yunƙurin bina nasan sun fahimceni, daga haka nai gaba cikin ɗan sauri-sauri da sassarfa irin ta mai gaggawa. Ina tabbatar da na ɓacema ganinsu na canja hanya. Duk da a rikice nake hakan bai hanani nemawa kaina dakiya ba na fara tafiyar nutsuwa. Da ƙyar nake iya gane inda nake jefa ƙafa har ALLAH ya fito da ni wajen wasu fanfuna da igiyoyin shanya. Akwai mutane tsiraru a wajen suna wanki, da alama wajen an tanadesa ne domin haka. Caraf idona akan hijjab dake shaye a igiya, tuni na tuɓe na jikina na ja wancan na saka, ɗan kwalin abayar jikina na naɗa a fuska tamkar niƙab. Daga haka na fito a wajen. Tambaya na dingayi har ALLAH yasa na fito a cikin asibitin gaba ɗaya dan babu laifi babbane sosai. Ajiyar zuciya mai haɗe da hawaye ne ya kufce min ganina akan titi, sai dai babban tashin hankalin banda ko sisi a jikina banda kuma abin siyarwa sisi. Ba kuma zan yarda kowa yaban lift ba dan an koyan hankali a baya. Haka na shari titi ina addu'a, ganin nayi nisa sosai da Asibitin zuciyata ta tabbatar min da zafa su iya biyo bayana su ganni duk da na canja hijjab. Ai tuni na kauce a titi na shiga wani street da naga an rubuta a ƙaramin symbol dake farkon shiga. Ganin an rubuta street nasan komai nisa zan fita, dan haka na zage damtse sosai naita tafiya duk da rashin ƙarfin jiki ga kuma rana mai zafi dake dukana ban damuba.....
★★★....
Tun su Semi na irga mintuna har suka kusan haɗa ashirin. Mamaki ne ya kamasu, dan haka ɗayar nurse ɗin tace Bara ta duba Samraah ko ta ɓata hanya ne. Mintuna uku da wasu sakanni ta dawo a hargitse tana sanar musu itafa bata ganta ba. Sannan mutanen dake ata wajen sun tabbatar da bata dawo ba. Su dukansu har matar da doctor da aka je aka sanar mawa rikicewa sukayi. A take kuma doctor yay kiran Hayatu a waya...
Tako ina an bincike asibiti babu Samraah. Har cctv footage aka bincika, sai dai ta iya gaba kawai aka ga shigarta wajen inda ake wanki, kasancewar ta wajen babu camaras ɗin sai ba'a fahimci komai ba. Saboda ta canja hijjab sannan ta fita, ta inda ta fitan ma camara na wajen yana da matsala. Matuƙa Hayatu ya tada musu da hankali, gashi yayi kiran Maash ya sanar masa amma sai yaƙi ce masa komai. Ya kuma san minene ma'anar shirun ogan nasa, dan haka ya sake birkicewa ya birkita likita da Nurses har ma da matar nan da tazo ɗaukar Samraah ɗin. Kai dama kowa na asibitin dan har securitys basu tsira ba da sauran ma'aikatan...
💦💞💦💞💦
Ƙuuuuu!! Razanannen taka birkin ya karaɗe illahirin titin tare da sautin ihu mai firgitarwa. Ba hamshaƙiyar matar dake cikin danƙarereiyar motar kawai ba, hatta da mutane dake kai kawo a street ɗin tuni sunyo caa. Sosai Samraah da aka kusa kaɗewar ta matuƙar razana, dan durƙushe tai ta cusa kanta a cikin ƙafafunta nuna alamar sadaƙarwa kawai. Haushi da takaici ya saka mutane yimata caa da faɗa, dan duk wanda al'amarin ya faru akan idanunsu sun tabbatar da laifin ta ne ba mai motar ba. Ganin yanda wasu ke ƙoƙarin kai mata duka ma adalilin yanda har yanzu taƙi motsi daga durkuson razanar da tai yasa matar dakatar da su da sauri ta hanyar riƙota ta miƙar. Rawa jikin Samraah ya cigaba da yi har hakan na rinjayarta tamkar zata faɗi. Duk wanda ya kalleta yasan a gigice take har yanzu, dan haka matar ta shiga bama mutanen daketa faman hargowar zagin Samraahn haƙuri tare da jan hannunta ta buɗe motar a gefen mai zaman banza ta sakata. Sai da ta rufe sannan ta sake fuskantar mutanen da har yanzu sun kasa barin wajen..
“Kowa yayi haƙuri dan ALLAH kuma mu mata uziri. A yanayin halin rayuwar da ake ciki yanzu muma zamu iya tsintar kammu a fiye da yanda yarinyar nan take ciki yanzu. Tun dai ma komai bai sameta ba ai Alhamdullahi ko, sai muyi fatan ALLAH ya kiyaye gaba”.
Da kalmar (Amin) suka shiga amsa mata cikin nuna gamsuwa da yabama ƙyaƙyƙyawar zuciyarta, dan ba kowa bane zai iya yin abinda tai ɗin. Daga haka kowa ya fara watsewa itama ta shiga motar dan ta tsarema mutane hanya har wajen ya fara tara mutane musamman masu gadi na cikin gidaje nata fitowa. Bayan rufe motar ta ɗan kalli Samraah ta sauke numfashi mai kauri, batare da tace komai ba taima motar key cike da ƙwarewa ta harbawa saman titi da ƙyau. Tafiyar da bata gaza mintuna uku ba ta samu waje ta gangare gefen titin, dan bata son tai nisa da anguwar ta zamto kuma anan yarinyar take duk da ta ganta da niƙaff a fuska. A yanzu ma dai yarinyar kanta ƙudundune yake a cikin ƙafafunta, yayinda sautin shashshekar kukanta ke fita kaɗan-kaɗan.
“Ɗiyata a ganina godema ALLAH ya kamata muyi, dan da abinda yaso faruwa ya faru da ga ni har ke da ba wannan matsayin muke ba ai. Kiyi haƙuri ga ruwan nan kisha ki samu nutsuwa ko”. Shiru kamar bazata motsa ba, kusan cikar minti ɗaya kuma sai ta ɗago, Samraah ƙyaƙyƙyawace sosai ta yanda hawayen da suka ma fuskarta kaca-kaca bai hana bayyanar hakan ba.
Idanu na tsira mata mai haɗe da sauke ajiyar zuciyar dawowa hayyaci, sai kuma na kauda kai na, a hankali na furta, “Ba kukan tsorata nake ba Hajiya, kukan baƙin cikin rashin tabbatuwar abinda nai fata ne ya sakani kukan nan. Inama ace kin kaɗeni na huta da wannan rayuwar da babu komai a cikinta face kayan ƙunci da baƙin ciki da ruɗani. Inama ace kin kaɗeni na mutu banko shuraba na tafi tafiya ta har abada da babu dawowa na iske su Abbana. Hajiya dan ALLAH ki fitar dani a motar nan na sake tarar gabanki ki bi takain.....”
Cikin sauri ta katseni da faɗin, “Haba haba ɗiyata wace magana kenan! Miyay zafi haka da irin waɗannan furuci masu tsauri. Ai duk da mun san zamu mutu bama fatan mutuwar a kayinmu sai dai dan babu makawa sai ta zo ne. Amma muna addu'ar a koda yaushe ALLAH ya jinkirta mana kodan tara ayyukan alkairi da neman gafarar UBANGIJI da ga na sharri da muka aikata. Minene matsalarki? Miyasa kike ma kanki fatan mutuwa a wannan ƙarancin shekarun naki da zamu iya kallo a matsayin yanzu ma kika fara rayuwar, ko kika fara buƙatar ta? Idan ban shiga abinda ba hurumina ba ki daure ki sanar min ko zan iya fahimtarki da taimakonki da wani abu....”
“Ba taimako nake buƙata ba Hajiya, sannan babu wani abin sha'awa ko birgewa da ƙawatarwa a labarina ko bayana. Ganni ki barni a yanda kika ganni yanzu kawai.” na ƙare maganar da yunƙurin ɓalle murfin motar zan fice. Da sauri Hajiyar ta riƙoni tana girgiza kai. “A'a ɗiyata yi haƙuri ki saurareni”. Juyowa nai na ɗan kalleta, sai dai bance komai ba........✍️
_Kuyi haƙuri da wannan Please. Zuwa anjima idan na samu damar yin wani zan ƙaro muku. Wlhy abubuwane suka min yawa amma ina fatan kammalawa na dawo muku da ƙarfina😘😘_
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
Post a Comment for "Tsutsar Nama Book 2 page 5"