Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Tsutsar Nama Book 2 page 4

 *_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_

       _𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒖𝒓_



.......Wani irin sake sarawa kaina yayi, dole na kai hannu na sake dafesa tare da saurin dafe ƙarfen gadon dan ji nake zan zube ƙasa, hasalima sam bana fahimtar maganganunsa a yanzu. Sai kalamansa ne na farko ke faman maimaita kansu a cikin kaina cikin matuƙar amsa kuwwar data zarce ƙarfin muryar daya sanar min su. (Idan nan ne GARIN AUREN ni ne MIJIN fa?) Kalamansa suka shiga min amsa kuwwa a cikin kunne tamkar wadda akema shelarsu. Gaba ɗaya ma brain ɗina ta toshe, sai nake jin kamar na kasa fahimta ko fassara su a bigiren daya dace. (Kai ina wannan gangan ne) wani gefe na zuciyata ya ambata. (Samraah dawo cikin hankalinki mana) sashen zuciyar tawa dai ya sake maimaitawa. Hannuna dake a saman kaina na sauke tare da kaisa saman kumatuna na ɗan bubbuga, dan nafi tunanin mafarkine kawai. (Kai amma wannn mummunan mafarki da muni yake) na sake faɗa ina bubbuga fuskar sosai da ƙarfin gaske kozan farka. Zafin daya ratsata ya sakani rumtse idanun da ƙarfi. A masifar jigace da ƙoƙarin haɗiye hawayena na ce, “Wai kai minene alaƙarka da ni ne? Mi kaje ka ƙulla? Miye matsalarka dani?”.

       Idanunsa ya ɗauke da ga kaina gaba ɗaya. Sai kuma ya ɗan taɓe baki alamar yanzun ma bazai tanka min ba. Rainin wayonsa ya gama zuwa min ko ina. Dan haka na fisgi ɗan ƙarfen dake cikin tasar asibiti a gefena na ɗago ina kaisa saman cikina cikin soyewar ido data zuciya. “Dana zauna da kai a matsayin miji gara na kashe kaina na san ban mori komai a rayuwata ba.”

       Idanunsa dake min wani kallon ƙasa-ƙasa ya sake ja luuu kamar zai rufesu gaba ɗaya. Sai kuma ya buɗesu warr cikin yanayin i don't care manners ya furta, “So! Ai ba hanaki zan ba. Abinda kawai nake buƙata kafin ki mutum ki bani video”.

      Wani irin sakartaccen kallon tsana da takaici nake masa. Na cije lips ɗina da masifar ƙarfi. “Har abada kuwa buƙatar taka bazata biya ba. Dan wannan videon bazai taɓa zuwa hannunka ba har gaban abada.”

     “Ashe kuwa ko kin mutu gawarki zata cigaba da zama a gareni. Ahalinki kuma zasu cigaba da amsar hukuncin laifinki”.

          “Idan kuma kai na kashe fa?”. Na faɗa ina jefar da ƙarfen cike da tsantsar fusata da tafi ta ɗazun. Idanunsa ya ɗan zuba min, sai kuma cikin nuna rashin damuwa ya janyesu yana wani shegen annamimin murmushi daya ƙona min rai. 

      “Oh are you threatening me? Ai game dani ba wasan yara bane ba. Har yanzu bamu fara wasan ba, balle ki tunanin samun game over. Zan iya baki damar kwanaki domin shiryawa. Ba kince kinfi ƙarfin laɓewa bayan wani domin faɗan sunƙuru ba. To gana gaba-da-gaba nan kin samun bissmillah. Matsoraciya kawai. Kwana uku kacal har kin fara banbance tsakanin aya da tsakkuwa”.

      Bamma san lokacin da wani irin ƙarfin zuciya yazo min ba. Cikin tsantsagwaron ɗaukar alwashi da tsawa na ce, “Har abada nafi ƙarfin yin laushi a hannun matsoraci irin ka. Dan ni har yanzu banga MAZANTAKA ba anan tunda sai da ka laɓe a bayan aure yanzun ma. Kasaka a ranka daga yau ni Samraah bint Abdul-wahab Gwarzo, sai na sakaka lissafin lissafa kwanakin rugujewarka daga yau har zuwa ranar dana ɗeba maka da zan kuma koma ga masoyina. Ni nan sai na sakaka gudu, gudu irin wanda babu wajen zuwa a tsakkiyar sahara mai tsananin zafi rana da ƙarancin ruwa. Wlhy sai kasan ka ɗakko KARA DA KIYASHI. zakuma kasan TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE”. Daga haka na ture wayar ƙasa batare da na jira jin abinda zaice ba. Sai ma wani irin izza da ƙarfin iko da naji yana ratsa gaɓɓaina, duk da sara min da kaina yake tamkar zai rabe biyu. Sai kuma hawaye sharr suka shiga kwaranyomin masu zafin gaske....



       (🥱🥱tofa irin wannan alwashi haka Sam-G).



         💦💞💦💞💦💞


   “Magana ta gaskiya Alhaji yaronka Mansoor na cikin haɗari. Sai dai akwai mafitar da in na baku shawara kuka gamsu da ita ina fatan za'a dace......”

      Cikin tarar numfashi da taune harshe Dad ya furta, “Ka faɗi ko minene mu masu baka goyon bayane Doctor. Bama son rasa Mansoor dan ALLAH ka taimaka mana”.

    “Wannan duk na ALLAH ne Alhaji. Idan kuma muka cigaba da roƙonsa shi mai amsawa ne. Shawarar dama itace ai gaggawar barin ƙasar nan da shi zuwa India. Akwai ƙwararren likita dana sani game da ciwonsa. Kuma inada yaƙinin in sha ALLAHU zai basa dukan kulawar da muke buƙata koma fiye da ita. Sannan ku shirya yaƙi na gaskiya game da nisanta komansa da abinda ya sake jawo wannan matsalar tasa da mukai tunanin ta barsa tun a shekarun ƙuruciya. In ba hakaba akoda yaushe komai zai iya faruwa magana ta gaskiya”.

       Sosai zukatansu suka ƙara raunana da zancen Doctor. Dan duk dakiyar Attahir sai gashi yana share hawaye. Basu wani yi ja'inja ba dan basa fatan rasashi, tun ma yana yaro sanda matsalar ke da zafinta basu nutsu ba balle yanzu. A take aka fara shirye-shiryen fita da Mansoor zuwa India. Abinka da masu hannu da maiƙo, cikin kwana ɗaya da yini komai ya gama kammala. A cikar kwana na biyar da ɗaura auren Samraah da Maash aka wuce da Mansoor. Da ga shi sai doctor da Attahir ne suka wuce. Su Dad kuwa sai nan da kwanaki biyar saboda tsaiko da aka ɗan samu game da visa ɗin Amal. Duk wani masoyinsu ya bisu da fatan alkairi. Yayinda tausayin Mansoor ya sake cika zukatan wasu. Wasu ko nama iyayen nasa ALLAH ya ƙara kasancewar koma a wane hali yake sune suka jaza masa. Dolene kuma sakayyar Samraah ya bisa. Dan gashi itama ance babu lafiya har an wuce da ita asibiti. Dan tun a randa aka wuce da ita Abuja labari ya shiga kunnuwan mutane sakamakon shegen surutun Mom da ita take faɗa cike da nuna jin daɗi. Dan itafa jinta take fes uwa ya zuciyar sabon jariri haihuwar yanzu. Har faɗama mutane take ai mijin Samraah ɗin dama irin kwatakwalin yaren nan ne shiyyasa ma ya wuce da ita Abuja ɗin dan ya kaita ga danginsa a bata jiƙe-jiƙensu amma babu wani asibiti duk joni ne dan kar ai mata dariya. Wasu dai sun hau sun zauna, yayinda wasu ke fassara al'amarin nata da hassada kawai. Duk da dai mutane ba ganin mijin Samraah ɗin sukayi ba. Kowa dai batun an ɗaura aure da sunan wanda aka ɗaura ɗin mai suna Muhammad Mu'azz kawai sukaji. Sai kuma waliyayyansa da kowa ya gani ƙuru-ƙuru da ido dan wasu ma harda video sun ɗauka domin yaɗawa a media kasancewar Sam-G ɗin cele ce, yanda auren nata ya canja akala cikin ƙanƙanin lokaci sun san zai jawo magana. Ya kuwa jawo ɗin, dan har a yau da yake cika kwana biyar cif da ɗaurawa ba'a daina yawo da hotunanta da ƙananun magana ba harma dana Mansoor. Sai dai duk bin ƙwaƙwƙwafin mutane na son ganin sabon ango da iyayenta sukai mata auren huce haushi da shi har yanzu babu wanda ya gani. Duk da anata editing hotonta da maza daban-daban matsayin ita da angon nata. Masu ƙarancin hange sun yarda, masana da hangen nesa sun ƙaryata. Daga baya ma dai abokan aikinta da yawa sun fito sun ƙaryata ba ita bace editing ne..


  ★★★★


      Gwaggo dan ALLAH ki daina kukan nan hakanan. Ni wlhy ba wai ba zanji shawararki bane ko maganar ki. Ba kuma ina tsoron Jalilah bane da har zan gagara ƙara aure. Kawai dai ni ra'ayina kenan zama da mace ɗaya.”

      “Ra'ayinka ɗin banza da wofi Imamu. Har ni zaka gayama wani ra'ayinka can na yahudanci. Mika rasa ko wane sharaɗine baka cika ba na ajiye mace fiye da ɗaya? Kaje bazan sake magana ba. Amma ka sani wlhy in dai na haifu cikin Balkisu da Usama bazan sake shiga sabgar zuri'arka ba. Sannan ina so daga yau ka saɓe hannunka daga ƴaƴan ƴar uwarka. Dan ba sai gobe ba a yau ɗin nan Musaddiq zai dawo wajena da zama. Shima Hafizun yana gama makarantar nan zai dawo. Kaje ka cigaba da rayuwarka da naka ƴaƴan da matarka tunda dama haka take so kai ma kake so ku rayu daga ku sai ku batare da wani ya raɓeku ba saboda kada mu rage muku jin daɗin duniyarku..”

        “Amma Gwaggo dan ALLAH k.....”

   “Na gama magana ta Imamu, tashi kaban waje. Ka dai tabbatar min bani na haifeka ba kuma na amince da hakan. Sai dai Alhamdullah bakai kaɗai bane ɗa balle hakan ya dameni, gasu nan bila'adadin harda jikoki duk mun godema UBANGIJI”. Daga haka ta miƙe ta bar masa falon. Da kallo kawai Abba ya bita zuciyarsa na kai-kawo tamkar zata fito. Babu abinda ke dawo masa a rai sai furucin mahaifiyarsu a lokacin da take gargarar barin duniya dan jinya tayi mai tsanani, kuma Gwaggo Gudidi itace ta kula da ita har ta koma ga ALLAH. (Imamu kona bar duniya nayi imanin baku rasa uwa ba kai da ƴar uwarka. Dan haka in har kuka bijirema umarnin ƴar uwata ban yafe muku ba. Kuma in har ina da hakki a kanku a matsayina na mahaifiya nasan bazaku taɓa ganin dadai ba. Ku ƙyautata mata, ku bita tamkar yanda zaku bini in sha ALLAHU zaku ribantu da hakan ba kuma zakuyi kukan rashina ba). Sosai tsigar jikinsa yaji ta tashi da tuno wannan magana. Dan tamkar a yanzu ne mahaifiyarsu ke faɗa masa shi da ƴar uwarsa mahaifiyar su Musaddiq. Bayan rasuwar ta kuma Gwaggo Gudidi itace ta cigaba da riƙe su. Itace tai musu aure da ga shi har ƴar uwarsa. Bata taɓa kuma gazawa ba a ɗawainiyarsu data ƴaƴansu har zuwa yanzu da tsufa ya risketa. Anya kuwa idan ya butulcewa wannan baiwar zai ga dai-dai? Bakin mahaifiyarsu kuwa bazai kamashi ba? Dan yana ƙyautata zaton shine ma ya taɓashi a yanzu abubuwa ke masa gangal-tangal uwa ya motar tirela mai ɗauke da siminti akan gadar icce dake tsakkiyar teku, dan yasan wasu kaso na rashin mutuncin da Jalilah ta dinga ma Gwaggo nasa a baya. Sai dai baisan miyasa baya iya tsawatar mata ba duk da abin na masa matuƙar ciwo a zuciya. Sannan yana matuƙar ƙaunar Gwaggo Gudidi, yana kallon fuskar mahaifiyarsu ne akan tata fuskar saboda tsananin kamannin da sukeyi. ya rabba yana a cikin tsaka mai wuya, dan baya jin zai iya ma Jalilah kishiya, yana kuma tsananin tsoron bijirema Gwaggo Gudidi bakin mahaifiyarsu ya kamashi.........✍️



      _🥱To Abba adai sake tunani._

      



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Post a Comment for "Tsutsar Nama Book 2 page 4"