Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Tsutsar nama 49

 *_Typing📲_*











   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓𝒕𝒚 𝒏𝒊𝒏𝒆_


____________


_Assalamu alaikum... HGL CHARITY FOUNDATION. Na neman temako me hamsin me dari ko sama da haka ko da kayan abinci ne zaa dafa a tallafa abawa mabukata da sukayi azumi a wannan wata mai albarka..._


_idan kudi zaa bayar ga asusun banki na opay 9044191709. Haka zalika idan kayan abinci zaa kawo zaa zo unguwar tarauni dake garin Kano sai akira number opay dincan dake sama_


_zaayi abincin azumi, kosai da Kuma kunu. Wani lokacin harda kankara ta ruwan sanyi ma da za rabawa mabukata masu buda baki.._


_kofa a bude take ga duk Wanda zai taimaka. Allah yabada saa ya hadamu a ladan duka amin_


______________



......Daga can tsakar gida kam taro yay taro gida ya kacame da hayaniya irin ta biki, anan ɗakin ƙawayena na zagaye dani. Wasu na hotuna wasu na kwalliya, wasu na hirarsu akan batun dinner da za'ayi bayan an kai amarya. Dan can gidan su Mansoor ɗinne suka shirya. Kiran da Yaya Musaddiq yazo yamin ne ya sakani saka gyale na rufe har fuskata. Shine ya kama hannuna har falon baƙi. Tunda muka fito kuwa gidan ya sake ruɗewa da buɗe-buɗe. Ni dai kaina na ƙasa a cikin gyale dan haka kawai sai naji ina jin kunya kowa. 

      Ban ida daburcewa ba sai da muka isa falon baƙi. Dan ganin kaf kawunaina na ɓangaren uwa da uba harda Abba. Sai gwagganni da innoni suma dai duk suna nan na kusa sosai. A tsakkiyarsu Yaya Musaddiq ya kaini ya zaunar ƙasan carpet. Shima sai ya nema waje ya zauna.

       Kawu Musa ne ya fara min da nasiha mai ratsa jiki. Kafin sauran ma su dinga karɓa ɗaya bayan ɗaya. Daga baya suka koma faɗa da gargaɗi, yayinda ni kuma nike sharɓan kuka ta cikin gyale. Dan babu abinda ya tadamin hankali sai jin muryar Yaya Musaddiq na rawa alamar karaya sanda yake min addu'ar zaman lafiya a gidan aurena. Abba ma dai yamun tasa a taƙaice, daga baya kiran wayarsa da akai ya nema excuse ya fita, da alama kuma kiran da akai masan nada matuƙar muhimmanci ne. Dan naga sai da ya fara magana da Kawu Musa suka miƙe tare suka fita. Fitar tasu bai hana iyayena cigaba da mun nasiha ba, sai da suka gamsu sun min yanda suke buƙata kafin suka sallaman Inna Hauwa ta kamani ta maidani ciki, dan mazan zasu wuce massalaci ne daga can kuma za'a ɗauro aure. Dole sai da aka sake min kwalliya bayan nayi sallar azhar saboda na ɓata fuskar dan kukan da nasha. Kaya na canja zuwa wata shadda da taci uban aiki da stones sai walwali take yi. Ga ƙamshi irin na amare ƴan ƙwalisa ina zubawa. Acan ƙasan zuciyata kuwa jina nake duk wata iri kamar yanda aka san duk amarya da shiga irin wannan yanayin a irin ranar nan. Lokacin da ƙarfe biyu ke cika maza suka fara dawowa alamar an ɗauro auren gabana sai ya shiga wani irin luguden daka da sauri-sauri. Wani irin tsoro da fargaba na ratsa min cikin ɓargo da jijiya har ina jin wani kalar sanyi-sanyi duk da kuwa uban zafi ake zugawa a gari kasancewar watan azumin Ramadan na kawo jiki. Ƙawayena sun shiga min shaƙiyanci da buɗa a saman kai, sai na samu kaina da sakin hawaye masu zafin gaske da ban san dalilin yinsu ba. Shin murna da farin cikin mallakar matashin saurayi ƙyaƙyƙyawa ɗan ƙwalisa mai cikar kamala da dattako irin Mansoor ne, ko kuwa fargabar rabuwa da ƴan uwana biyu ne da ke a cikin tarkon wancan terror ɗin. Bily a lokacin sam na kasa ganewa. Na gagara banbance komai a yanda ya dace na fahimcesa. Sai ma wani sabon bugun zuciyar da na sake ji sakamakon shigowar aunty Zakiyya kamar a firgice tana kiran Gwaggo Gudidi data shigo tana miƙamin fura a kofi da aka dama wai na sha. Koda Gwaggo ta tambayeta lafiya, sai tace mata su Kawune ke kiranta kuma sunce tai sauri dan kamar dai akwai wata matsala. Da saurin kuwa ta fita alamar itama tana a cikin ruɗanin ne..

       Na cigaba da zama kamar butun butumi a tsakkiyar ƙawayena daketa hotuna abinsu batare da su sun fahimci kamar akwai abinda ke faruwa ba. Muna nan dai shiru hayaniyar gidan na sake ƙaruwa alamar mutane na sake cika gidan ƙananun magana suka ɗan fara fitowa. Sai dai anƙi a fito da komai a fili ana ta son basar da mutane dai. Abinda ya ɗan fara tsayamun a rai shine rashin zuwan Mansoor gidan. Dan a burikanmu akwai zuwa hotuna bayan ɗaura aure da yace zasuyi shi da abokansa da kuma ni da ƙawayena da ƴan uwana. Amma dai zuciyata nata tausata akan masa uziri, dan maybe mutane sun masan yawan da hakan bazai yiwu ba ya cika wannan alƙawarin. Wannan tunanin yasa na danne zuciyata na ajiye wannan batun a gefe.

      Isowar masu kiɗan ƙwarya bayan sallar la'asar yasa Inna Hussaina zuwa ta fita dani a ɗakin ni da ƙawayena. Sosai gidan ya cika da mutane har sai da naji ƙwalla ta cika min ido. Dan ban san munada taron dangi har kamar haka ba da zasu iya nuna wannan soyayyar garemu a irin wannan ranar. Ko a wajen kiɗan ƙwaryar ma duk da ba rawa nake ba tsaye kawai nake tsakiya ƙawaye na da ƴan uwana masu rawar zagaye da ni sai da dinga shigowa ana min liƙi, wasu kuma sukanyi hoto dani a waya harda masu video. Kusan ƙarfe biyar sai ga Gwaggo Magajiya riƙe da hannun Yaya Musaddiq da Hafizzullah wai sai sun min liƙi. Kallo ɗaya na musu su duka biyun na fahimci sunyi kuka. Dan idanun Yaya Musaddiq jajur suke. Na Hafizzullah kuwa har sun kumburo saboda shima fari ne kamar ni, dan mu biyun munfi Yaya Musaddiq haske. Hankalina ne ya tashi a take nima idanuna suka ciko da ƙwalla ina binsu da kallo. Amma sai suka ƙi yarda mu haɗa ido sai liƙi da sukemin kawai ana ihu kawunansu a ƙasa suna murmushin da ni kaɗai na fahimci na yaƙe ne. Duk yanda naso riƙe kukan nawa hakan ya gagara, bamma san sanda na riƙo hannayensu su duka ba cikin nawa. Dole suka kalleni a tare. Kukan na sakar musu kawai na faɗa jikin Yaya Musaddiq. Shima sai Hafizzullah ya ya rungumemu mu duka biyun ya saki nasa kukan. A take wajen yay tsitt, wasu na ganin mun birgesu da fassara abin namu da tsananin shaƙuwa ne da soyayyar juna. Wasu ko da suka san wani abu dake ɓoye sai suke jin tsananin tausayinmu da jin karaya suma. Nan take aka ringa tuno alkairan iyayenmu da musu addu'a. Dole dai Yaya Musaddiq ya jamu muka fita daga filin. Nan Gwaggo Gudidi ta jamu zuwa ɗakinsa ta dinga lallashinmu da mana nasiha. Haka kawai maganganun nata sai suke ta min kai da kawo dan na gagara fahimta da fassara wasu nikam. Kiran Yaya Musaddiq da akai a waya ne ya sashi miƙewa ya fita. Babu jimawa ya dawo yay kiran Hafizzullah. Anan ne Gwaggo ke tambayarsa lafiya? Sai yake sanar mata zasu maida kayan can gidan ne dan an gama kwashesu. Cikin nuna gamsuwa tace, “Oh to hakan yayi, bari na tattara su Zakiyya su sameku acan yanda aikin zaiyi sauri. In sha ALLAHU ai yanzu zakaga an kammala”. 

      Da to ya amsa mata yana ficewa. Hafizzullah ya canja riga suka fice. Babu abinda na gane a zancen nasu, amma na gagara haƙuri sai da nace, “Gwaggo kodai akwai abinda ke faruwa ne? Naga sai magana kuketa yi kamar a ƙudundune?”.

         Kai tsaye tace min, “A'a babu komai ƴar nan. Kinga tashi mu koma ciki dan da anyi magriba zaki yi wanka a wanke wannan fentin da aka cika miki a fuska. Koda masu ɗaukar amarya dai sun zo ɗin sai dai mu yazam mune muka jirasu basu zasu jiramu ba”.

    Banda tacewa face bin umarninta. Tunda dama nasan dai ya kamata a kainin da wuri kodan dinner da su Mansoor suka shirya. Amma kwalliya kona wanketa dole a sake wata basai munje can gidan ba kuma aita dibi-dibi nasan Mansoor da ƙosawa akan abu, sam baya son jira. Acan ƙasan zuciyata kam ina jin babu daɗi saboda rashin ganin duk jama'ar gidan a cikin sha'anin bikin nawa. Dan yaran duka babu wanda na gani har Auta da su Yaya Abbas da Nabel da shi banama zaton yazo gidan yana makaranta. Gara ma ita Mum ɗin bayan ɗaura aure sanda Yaya Musaddiq yazo ya fita dani ɗin nan zuwa falon baƙi na ganta ita da wasu ƙawayenta a tsaye sunata faman dariya da alama akwai abinda suke tattaunawa a tsakaninsu.


       ★★Bayan nayi sallar magrib kamar yanda Gwaggo ta faɗa aka haɗamin ruwa mai zafi da kayan turaren ƙamshi a ciki nayi, koda na fito da taimakon Gwaggo na kimtsa jikina. Ta kuma tsareni sai da naci abinci da wani nama na musamman mai romo a cikin kula. Naman yayi daɗi dan haka na saki jiki naci sosai, koda tace sai na cinyesa ma ban musaba na dage na cinye nasha romon. Hakan yasa cin abincin bai armashi ba garan sosai. Tun ina kallon agogo harna daina. Sai dai a raina inata mamaki, dan tara dai-dai ya kamata ace muna a wajen dinner. Amma gashi anan har taran yama wuce ba'a kaini gidan su Mansoor ba balle ai batun zuwa dinner. Bily kar kiga kamar na cika zumuɗi ne fa. Kawai dai bana son naga an saɓama Mansoor alƙawari ne, to amma yaya zanyi, sai sanda aka kaini. Matsalata kawai da babu waya a hannuna.

     Muna nan zaune Gwaggo na ƙaramin nasiha kusan goma saura akace su Yaya Musaddiq sun dawo sai a fito da amarya ga motoci sun zo. Sai a lokacin kuma naji duk na rikice. Nanfa na saki musu kuka. Duk yanda akaso na miƙe naƙi nai hakan har sai da Kawu Musa da kansa ya shigo yana faɗa sannan. Kuka nake sosai har numfashina na shiɗewa. Amma babu wanda ya saurareni, sai ma gaban Mum da aka kaini na roƙi yafiyarta. Cikin taɓe baki tana wani fisge-fisge ta ce, “ALLAH ya yafe mana baki ɗaya sai aje aita haƙuri, dama ita rayuwa ai haka take babu tabbas...” ganin tana neman sakin layi Gwaggo ta kamani muka fito. Abba ma an sake kaini na masa sallama. Yaya Musaddiq kam ya rufe kansa a ɗaki yaƙi yarda. Nasan kuka yake, dan haka nima na ƙara ƙarfin nawa kukan ina tutturjewa, amma babu wanda ya saurareni sai dai wasu nata bani haƙuri wasu na tayani matsalar ƙwallar aka fita dani. A rikicen da nake yasa bamma san kala ko adadin motocin da suka zo ɗaukata ba. Ni dai kawai an sakani a motar da ƙamshin da take yaso sakamin razani a zuciya, sai dai kuma rashin ƙarfinsa sosai da ruɗanin da nake a ciki na rabuwa da ƴan uwana ya hanani bama abin muhimmanci. Gwaggo Gudidi da Inna Magajiya ne tare da ni, sai gaba Ruƙayya ce ta office ɗin mu data zame min kamar babbar ƙawa ita da ƙanwar mijin Aunty Zakiyya........✍️



_🤭Uhummm inji mai ciwon haƙori._




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Post a Comment for "Tsutsar nama 49"