Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Tsutsar Nama 9


 *_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑵𝒊𝒏𝒆_



........Sai da Yaya yayma Ruƙayya dake shirin barin wajen godiya sannan ya juyo gareni. Kallo ya ƙare min daga sama har ƙasa sannan cikin yanayin fusata ya ce, “Miyasa kike da taurin kai ne wai Samraah?. Yanzu ga abinda kikayi jiyan wace riba kikaci tunda kinfi kowa sanin halin matar nan?. Amma ke da yake ba'a taɓa faɗa miki kiji shine yau ma kika kuma. To ai gashi nan ta sake ƙulla miki sharri kala-kala ita da yaranta. Tun ɗazu ina gidan basu barni na fito ba sunata min masifa akan wai ni nake sakaki. Har Abban na saka sharaɗin ko dai ki ajiye aiki ki dawo ki cigaba da aikin gidan ko kuma ya aurar da ke ga wa wanda ita Mum ɗin ta kawo. Idan yaga shi zai barki yin aiki ki cigaba, amma albashinki dolene kema ki dinga rabawa biyu daga yanzu kina basu rabi ana haɗawa ayi cefane. Nama kawo masa batun Mansoor yaƙi ya saurareni sam. Wai shi bai san da wani Mansoor ba kuma bazai aura masa ke ba, wanda Mum ta kawo kawai ya sani kuma shi zai bawa dan yaron nada tarbiyya sosai, kuma shi ya gamsu da hakayensa....”

      Kuka na sakar masa mai taɓa zuciya. Hakan ya sakashi yin shiru ya gagara cigaba da magana ya zubamin ido kawai. Kusan mintuna uku ina kukan sosai kafin ya kai zaune kusa dani. A jikinsa ta gefe ya sakani kawai shima hawayen na cika masa ido. “Amma kin san bana son kuka ko Samraah”. Ya faɗa muryarsa na rawa. Ɗagowa nai a karo na farko ina kallonsa. Sai kuma na sake fashewa da wani sabon kukan ganin yanda idanunsa suka kaɗa sukai jazur gasu cike da hawaye. “Yaya ya kake so nayi, shike nan haka zamu lalace a yima waɗanda basu taɓa jin tausayinmu ba biyayya. Kullum burin matar nan wulaƙanta mu, Yaya tun fa ban isa iya aiki ba nake bautar gidan nan, amma ko sau ɗaya ba'a taɓa min adalci ba idan nai kuskure a yafe min. Kullum kuma a banayi nake. Su Baby na kwance. Yaya na gaji wlhy, ji nake kamar na gudu na bar gidan nan kawai....”

        “Shiii!!! Karna sake jin irin wannan maganar a bakin ki. Samraah ai wuya bata kisa. Da ace tana yi wlhy da bamu kai haka a rayuwa ba. Duk can baya baki ƙosa ba sai yanzu da aski yazo gaban goshi. Kwana nawa ma ya rage miki a gidan. Bama ke ba da kike mace zaki tafi gidan aure hatta ni da Hafizzullah in sha ALLAHU mun kusa bar musu gidansu. Gara kawai na tada gini na kamar yanda kike bada shawara mu koma can kawai. Amma dan ALLAH ina roƙonki kada ki sake maimaita abinda kika faɗa yanzu. idan kin gudu ina zaki? Ki daure ki cigaba da musu abinda suke so. Watarana sai labari ai. Maganarki kuma da Mansoor na yanke shawarar zuwa wajen dangin mahaifinmu, duk da sun watsar damu basu taɓa waiwayen mu ba tunda ɗan uwansu yabar duniya zanje na roƙesu su shiga wannan maganar a baki wanda kike so tunda dama sune ai da wannan alhakin ba Abba ɗin ba. Ki tashi kuma muje asibiti dan jikinki akwai zazzaɓi sosai.”

       Ɗagowa nai zanyi magana ya girgiza min kai alamar kar nace komai. Dole na haɗiye kuwa. Ruƙayya ya kira da wayata, yace ta tattare masa kayana dan ALLAH. Cikin mintuna kaɗan ko sai gata. Da taimakonta muka fita inda mashin ɗinsa yake. Ta taimaka min na hau muka wuce dan Mansoor yau baizo office ba sunje wani aiki Jigawa. Sai da muka fara tsayawa a camix aka dubani kafin mu ƙarasa gida dan nata roƙonsa kan bazanje asibiti ba, sanin da yay min na ƙin jinin asibitin shima yasa ya barnin mukaje camix ɗin kawai aka bani magani.


      Kamar yanda Mum ta shirya cin ubana shima Abba ya shirya hakan yau, sai dai a yanayin da Yaya ya shiga dani gidan ya saka jikinsa yin sanyi shi. Dan Mum ta fara min tujara da ƙoƙarin kai mari ya dakatar da ita. 

   “Uhm Jalilah inaga ya kamata ayi hakuri ai, baki kula da halin da take a ciki bane? Kiyi haƙuri harta warke ni da kaina zan sauke mata taurin kan nan nata nayi miki alƙawari”.

     Wani shegen kallo ta watsa masa a fusace. Kamar zatayi magana sai kuma mita tuna oho tai shiru. Fuuu ta wuce bedroom ɗinta ta barmu tana faman huci. Wannan zazzaɓi dai shine ya ceceni a wannan rana. Washe gari kuwa duk da weekend ne asubar fari Mum tazo ta tadani. Bata damu da yanayina na har lokacin ban gama dawowa dai-dai ba. Nima sai bance mata komai ba na tashi na hau aikin da take buƙata, dan kwana biyun nan fa da banyi komai ba haka gidan yake zaune kaca-kaca. Kafin takwas na safe har brackfast na kammala haɗawa, na ɗauki na Yaya Musaddiq na kai masa. Na samu ya kammala shirin wucewa Gwarzo kamar yanda ya faɗa zaije. Ba haka naso ba, dan naso ace munje munga Hafizzullah kamar yanda muka tsara. Zama nai muka karya tare yana ƙara lallashina da mun nasiha, jinsa kawai nakeyi, dan gaskiya bazan iya haƙurin wani abun ba in har nayi wani. Amma dai zan rage taurin kan kodan shi. Ban bar ɗakin ba sai da ya ƙarasa shiryawa muka fito tare, yau zai dawo, amma ya musu tsaraba. Ciki na koma na samu mutanen gidan gaba ɗaya a falo zagaye da Abba. Sai dining dake kaca-kaca sun gama karyawa amma babu wanda ya iya kawar da ko cokali. Abban na gaisar, ya amsa min babu yabo babu fallasa, itako Mum bama ta amsani ba. Ban damu ba dan ba yau na fara ganin hakan ba ai daga garesu, na nufi ɗaki da nufin yin shirin islamiyya da nake zuwa duk weekend Mum ta dakamin tsawa.

       “K dan ubanki waye zai kwashe miki waɗan can kayan”.

    Ɗan jimm nayi a tsaye zuciyar na yunƙurowa, sai dai nasihar Yaya Musaddiq dana tuna ta sakani komawa cool. Batare da nace mata komai ba na nufi dining ɗin na shiga tattare kayan. Sauri-sauri na wankesu na fito, har yanzu suna a falon, ɗaki nai wucewata na shirya, na sake fitowa dai na samesu. Da harar Mum na fara cin karo, ɗauke kaina nayi kamar ban ganta ba, a ladabce naje gaban Abba na duƙa. “Abba zanje islamiyya saina dawo”.

        Kansa kawai ya jin jina min ya cigaba da kallonsa. Nima sai na miƙe. Mum dake watsamin hararace tai saurin faɗin, “Ya kake bata damar tafiya Abban Abbas, idan ta tafi ubanwa zai mana girkin rana? Islamiyya take zuwa ne ba yawon iskancinta ba”.

     Ƙoƙarin ficewa nake da sauri dan nasan zai iya dakatar dani. Amma a mamakina sai naji yana faɗin, “Baga su Baby nan a gidan ba suyi girkin su mana tunda sun ɓarar da tasu islamiyyar su....” daga haka ban ƙarasa jin abinda yake faɗaba nai wucewata ina murmushi. Wani lokacin idan Abban yay abu sai kaga kamar mai mutunci. Koda yake dama ba laifinsa bane ba, zama kawai ake ana shirya mana sharri a wajensa maybe ma harda asiri. Dan nikan ban taɓa ganin mijin dake tsoron ɓacin ran matarsa irin Abba ba. Oho koma dai minene su suka sani ina ruwana.. Tunda na isa islamiyya na samu ƙawayena biyu na manta da wata hidimar gidanmu. Sai ƙarfe huɗu muka tashi, anan nai sallar la'asar sannan na dawo gida. Abin dariya abin takaici, a galabaice na samesu wai babu wanda ya tashi yay girkin ana jirana, Abba dai ya fice sai su kawai. Sai Abbas dana samu a gidan shima ya shigo. Ko kallon inda yake banyi ba dan ni da shi bama magana. Haka na tuɓe uniform ɗina na shiga kitchen ɗaura musu girkin da suke jira ɗin. Abu mai sauƙi na musu nayi komawata ɗaki..

       Yaya Musaddiq bai dawo a ranar ba kamar yanda yace. Koda na kirashi a waya sai yace nai haƙuri bai samu kawu Musa bane a gida, su kawu Sa'adu kuma sunce dole ya jirashi. Mun ɗan yi hira mukai sallama saboda kiran da Mansoor keta faman yimin. Hira sosai mukasha da Mansoor, dan sai kusan ɗaya mukai sallama. A hakan ma ba kwanciyar nayi ba. Tambayoyin da zanma wancan mutumin nai zaman tsarawa, har biyu sannan na miƙe na gyarama su Bibaa rufa na ɗauro alwala. Nice ban kwanta ba dai sai kusan biyu da rabi, amma hakan bai hanani tashi da asuba ba yin ayyukana.  

  

         Washe gari da yamma Yaya Musaddiq ya dawo gidan. Na dawo daga aikan da Mum tamun rijiyar lemo wajen ƙawarta na samu ya dawo. Naji daɗi sosai, dan bamma shiga gidan kai aikar ba na zauna muka hau hira. Duk yanda sukai da su Kawu Musa ya sanar min. Sunyi faɗa sosai, da farko ma ca sukai su babu ruwansu. Shi Abban daya nuna musu shine dolenmu yaje ya aurar damu. Amma Yayan ya dinga basu haƙuru, da ƙyar dai suka haƙura, sun kuma tsaida shi kawu Sa'adu zai zo ya sami Abban. 

        Hakan kuwa akai, dan washe gari Litinin sai ga kawu Sa'adu. Lokacin mu duk mun fice wajen sabgoginmu. Shima Abban a office kawun ya samesa suka tattauna. Duk da dai a farko taso tayi tsami a tsakaninsu. Kasancewar kowanne yana son nuna ƙarfin ikonsa a kammu da kuskuren da ɗan uwansa yay masa. Bayan dai sunyi sama sun faɗo suka dai-daita kansu. In da da ƙyar Abba ya amince da batun Mansoor........✍️




_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Post a Comment for "Tsutsar Nama 9"