Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Tsutsar Nama 11



 *_Typing📲_*









   *_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*

             _(Itama nama ce)_





_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_




_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝑬𝒍𝒆𝒗𝒆𝒏_




........Tun kafin mu fice duk sun cika motar da hira, ni dai ban saka musu baki ba face ma bitar questions ɗin dake rubuce dan karna kwafsa. Dan a nawa shirin ina son masa tambayoyin ne batare da takarda ba. Duk da ma dai har cikin waya na kwashesu gudun samun matsala. Lokaci ɗaya naji motar ta ɗauki shiru, kamar zan basar sai kuma na gagara hakan, dole na ɗago domin ganin abinda ya sakasu nutsuwa haka. To nidai banga komai ba face uban cinkoso na ababen hawa da titin ya samu tamkar ba safiya ba kuma weekend. Da ƙyar drivern mu ya kutsa ya samu wajen parking ma. Haka muka firfito kowannemu na bin katafaran ginin da kallo. Dan sai yanzu na fahimci abinda ya saka su yin shiru ɗazun. Gini ne da akayisa da wani kalar zallar gilashi mai garai-garai ta gabansa. Ga wasu manya-manyan symbols da hoton motoci masu shegen ƙyau da mashina irin na masu kuɗin nan. Da manyan haruffan baƙi an rubuta *_MAASH_*. 

       Tako ina jami'an tsaro ne, hakan yasa komai ke tafiya a nutse duk da alamu ma sun nuna duk wanda ka gani a inda motarmu ta samu damar shigowa to ba ƙaramin mutum bane, ko kuma dai yana da izinin zuwa wajen. Dan zuƙa-zuƙan motocine na nunama tsara. Yaku bayi kuwa na daga can tunkushe a titi an hanasu shigowa (🤥😞😏). Dan ƙa'idar sai ka nuna invition ɗin nan zasu bar motar ka ta wuce. A ƙafa muka cigaba da takawa saman lafiyayyen titin da aka ɗauka tun daga babban titi har zuwa cikin companyn. A dai-dai katafaren gate ɗin ma dai sai da muka nuna invition ɗin. Sannan akai searching namu aka tabbatar da bama tare da komai sannan muka shige bisa rakkiyar wani jam'i. Da alama wajen zaman ma a tsare yake kenan. Bazaka tabbatar da Companyn mugun ƙato na gaske bane sai ka shigo ciki. Ashe ta gaban duk wasan yara ne da ado kawai. Duk girman harabar an gyarata da uban decorations mai matuƙar ƙyau da ɗaukar hankali. Hakama an tsara kujerun zama cike da birgewa. Da ga can gefe abincine aka jera irin dai na taron ƴan gayun nan, dan ga masu zungura-zunguran hulinan nan irin nasu o,e a kitchen sun jeru kamar ƴan cocin yarabawa (😂lol). Mune ƴan jarida na farko da suka fara isowa, hakan ya mun daɗi, dan koba komai mun samu sits ɗin gaba a inda aka tsara domin ƴan jarida. Tuni su devido sun dasa camaras namu kuwa a inda komai bazai wucemu ba. Zuwan namu kamar ya buɗe ƙofa ne, dan sai ga mutane da ƴan uwanmu ƴan media nata shigowa a nutse babu wata hayaniya ko kace nace. Tun shigowarmu kuma tuni mun fara nuna komai live kamar yanda contract ɗin yake. Dan haka kusan komai daya fara da tushe kai tsaye ana fara ganinsa ne daga gidan tvn mu. Ni dai har lokacin ina a zaune dan ba'azo kan aikina ba. Kafin cikar awa guda waje ya gama cika taf da manyan mutane. Muryar mc kawai ake ji yana sanar da isowar manyan baƙi, sai mu kuma ƴan jarida dake namu bayanin domin gidajen tvn mu kai tsaye. Goma dai-dai dake tabbatar da duk wanda ake buƙata a wajen ya iso hatta da gwamna da sarki ma aka sanar da isowar mai gayya mai aiki. Wato *_Awwab El-Mu'azz Maashi_*. Tsitt wajen ya sake ɗaukar shiru kasancewar dai-dai nan zuƙeƙiyar baƙar mota da irinsu shugaban ƙasa kawai nake gani a ciki ta shigo. Ta gefe da gefenta da gabanta da bayanta kuwa wasu irin murɗa-murɗan basumadayen garada ne da gani kasan ba bugun Kano bane sai dai Lagos ɗin dan bamu da masu irin wannan suffar gaskiya😞. Su duka riƙe suke da bindigu kai kace zasu iya hana mutuwa ɗaukar wanda ke'a cikin motar ne😏. Har tsakkiyar filin motar ta shigo, inda mutanen dake a cikin motar bayansu suka fito a lokaci guda su huɗu. Mace ɗaya maza biyu. Wanda ke mazaunin driver ne ya buɗe booth da hanzarinsa ya ɗakko carpet maroon mai shegen ƙyau an rubuta *_Maash_* a jikinsa da golden mai ɗaukar ido. Yayinda macen baturiyar ta iso da sauri sauran mazan biyu a gefe da gefenta. Daka ganta kaga cikakkiyar baturiya. Duk tsaye sukai a ƙofar motar kowa cikin nutsuwarsa da kamewar girmamawa abin zam mamaki. (Humm jama'a MANDA fa duniya ce😜). Kusan minti ɗaya cif muna zuba idon ganin abinda ke faruwa kafin wanda ke gefen damar matar nan ya kai hannu jikin handle ɗin ƙofar ya buɗe tamkar mai gudun tashin yaro a barci. Wasu sakanni goma aka sake kwashewa kafin wani almurin baƙin takalmin haIf cover shoe mai adon golden ya sauka saman maroon carpet ɗin a hankali. Sai da aka sake jan wasu sakannin kamar uku sannan ɗayar ƙafar ma ta sauka baƙin wandon suit ya bayyana. Sannu a hankali sauran gangar jikin ma ta fito. Kaf wajen har masu ji da mulkin da kuɗin babu wanda bai bi wanna halitta da kallo da ga ƙasa zuwa saman ƙyaƙyƙyawar fuskar mamallakin jikin ba. Tsaye yake gam akan tsahonsa na tsayayyen namiji da babu ko ranƙwafawa. Suit ɗin jikinsa da basai an zauna ɓata lokacin lissafin kuɗin da suka lashe ba sun masifar zauna masa da tabbatar da shi a matsayin jaruminsa mai gara kan naira ta yanda duk yaso bisa damar da ALLAH ya bashi. Komai na jikin nasa baƙine, sai ɗan adon takalminsa da ta kasance golden da neck tie.. ɗinsa shima golden mai azabar ƙyau. Kamilalliyar fuskasa ma'abociyar kamewa da tsare gida ko nace baƙin hali a tsuke, sai kwantaccen gashin kumatunsa siriri daya zagaye bakinsa zuwa haɓarsa tamkar an zana ba biro. Yau ɗin ma dai akwai ɗan kunne ɗaya manne a kunensa, hakama zanen tattoo ɗinsa mai fuskar lion na nan zaune daram. Saɓanin hoto yau gashinsa ne a ɗaure kamar yanda mata ke parking sai dai shi nashi acan ta ƙasa ya ɗauresa har yana ɗan sauka jikin rigarsa dan babu kitso yau. Wanda bai sani ba tuni yake sakashi a jerin larabawa. Babu mai ganin idanunsa kasancewar sakaye suke a cikin eyeglasses mai masifar ƙyau daya ƙara fidda taswurar halittar ƙyawun hancinsa daya zauna ɗaram kan fuskarsa. Kafin kace mi tuni ƙamshinsa ya baje wajen kai kace mu namu turaren baida tasiri ne ko Companyn da suka wallafo namu basu iya zaɓar ƙamshi ba. Kai jama'a akwaifa ƙyawawa a duniya. Idan kaga wani sai kaga kamar ka yanka kanka ka ɓoye wuƙar ƙawai. Bily karfa ki zata wannan bayanin da nake zayyano miki a kansa ya wani birgeni ne. Mtsowww ko kaɗan..

       Gaba ɗaya yaran nasa sake kame kansu sukai cikin nuna tsantsar girmamawa a garesa. Karan farko na ɗan taɓe baki takaici kamar zai halakani. Shike nan a wannan rayuwar in har kana da dukiya ka zama saraki ko mai mulki?. Kai wani abun ma da ake maka ko kai mulkin ba lallai ya samu ba. Dibi dai wannan mutumin yanda yake wani busar isaka da shan ƙamshi fuska tamm kamar wanda aka aikama saƙon mutuwar tsoffinsa.

       Cikin isa da bajinta, a slowly tamkar wanda ake ɗauka a faifan video yay wani kalar haɗe hannayensa duk biyu a waje guda ya ɗagasu sama alamar gaisuwa wa duk jama'ar wajen. Kusan kowa dake wajen sai da sukai yanda yay ɗin idan ka cire gwamna da sarki. Sai ko ni ƴar balaja'un ku da saida Khulsoom ta zunguran amma na fuske naƙiyi, sai ma laɓe mata baki da nai na sake maida idanuna dake cikin glasses kansa ƙurr kai kace nice camara ɗin ma. Har inda aka tanada domin zamansa a tsakkiyar sarki da gwamna yaran nasa sukai masa rakkiya. Sai da ya zauna sannan suka koma ta bayansa suma duk suka zauna. 

        Isowar tasa ta saka taron fara motsawa yanda ya kamata. An fara da gabatar da addu'oi kafin gwamna yay bayani mai birgewa a matsayin uban taro, dan ya nuna jin daɗinsa da farin cikinsa matuƙa game da wannan cigaba da aka kawo jiharsa, yana kuma fata da kira ga wannan shugaban kamfani akan idan har yaranmu sun cancanta yana roƙon ace sun zama mafi rinjaye da zasu samu aikinyi a ciki, yana kuma fatan ALLAH yasa kamfanin ya zamewa Kano dama arewacin ƙasar alkairi baki ɗaya.

     Kowa yaji daɗin bayanin gwamna. Dan zaka tabbatar da hakanne a fuskokin jama'ar dake a wajen ma. Sai sarki shima dai a matsayin uban taron. Sosai jawabansu suka ƙayatar suka kuma birge shima ɗin dai. Dan yayi kiranye sosai ga masu arziƙinmu da su shigo su kafa cibiyoyin kasuwancin a arewa domin matasanmu su samu aikinyi, hakan da zasu dingayi zai rage mana raɗaɗin rayuwa da ake ciki a wannan ƙarni. Zai kuma ƙarama matasan himma da nisantasu da ga shaye-shaye ko ɗaukar makamin da bai dace dasu ba a matsayin neman abincinsu ko zaman banza a bakin tituna mara amfani. Idan kuma har masu arziƙi suka cigaba da janye jikinsu da dukiyoyinsu da ga arewa to lallai watarana sai an wayi gari kowa ya zama abinda ba'a so. Idan kuma hakan da ba'a fata ta kasance ba arewan kaɗai ba, hatta su ma kudancin da wasu maƙwaftan ƙasashe zata shafesu, suma kuma ta nakasasu kamar yanda muma muke a nakashe yanzu. Bayan waɗan nan bayanan wasu masu muhimmanci ma sun sake biyo bayansu kafin shi ma ya miƙe........✍️


          _(🤭Ni dai nace faɗi gaskiya dai Samraah bama son kwana-kwana😜 idan Yaya Maash ya miki ne sai ai miki hanya🥱, dan kunsan bana ni gaskiya ƴar team Yaya Maash ce. Mu dama muna gidan kuɗi babu kwana-kwana🤣👌. Saura naji wani yace kwaɗayi🙄dan ɗan uwanmu ne Ya Maash ɗin na jini🤯, ai gwajin jini kuma a gani🤥😌)._

      

          



_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*09033181070*


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_





*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Post a Comment for "Tsutsar Nama 11"