Rainon Soja 88-89
88-89
*Littafin na ku?i ne please don Allah kar ki karanta indai baki biya ba . Regular payment?500 Vip payment?1000 SPC payment?1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne sai ki tura ta wannan number 09061466409….?????#Mamanteddy#mrsusm.*
Book 3
Kallon ta yayi yana sakin mata murmushi kana yace “ Guest house zamu wuce yanzu ”. Tom ta basa amsa fuskar ta ba tare da ta nuna masa Wani damuwa ba.
**
Wani ?ayataccen gida ne mai ?yaun gaske , Amma girman sa yayi yawa , Don kamar ba guest house ba . Wannan yasa Idan zasu yi ?an taro yasu yasu suke zuwa nan. Tun daga Wajen falon take jin Muryar ta cike da izzan nan nata da mulki wanda sai da gaban Ma’eesha ya yanke ya fa?i dammmm” . Saurin kai hannun ta tayi tana ri?o Hannun Aliyu wanda Cike da kulawa yake kallon ta ….idanun ta ne yayi rau-rau , cikin narkakkiyar murya ta furta “ Uncle Bana son shiga ”. Ma’eesha su Mami ne fa a ciki , kar ki damu ko Mom Hajara ba zata yi Miki komai ba , ai yanzu ta rage wasu abubuwan da yawa , taho muje! Ya furta yana kamata tare da ri?e hannun ta suna shiga cikin tsakiyar falon bakin su ?auke da Sallama .
Ha?a ido Ma’eesha tayi da Mami wacce daganin ta fara’anta ya ?aru, Ma’eesha na! Ta kira sunan ta tana kare mata kallo . Da sauri Ma’eesha ta nufi mami tana Rungume ta tare da furta “ I miss You mami ”. Rungume ta mami tayi tana shafa bayan ta tamkar jaririya a hannu …..Kana tace “ Lallai Ali ya kula mun dake sosai , kin ga yanda kika yi ?yau dake Baby na….ko da yake yanzu babyn Haidar ne kar yayi mun iyaka?? dariya Aliyu yayi yana zama a ?aya daga kujerun dake zagaye kana ya gaishe dasu Daddy da Alhaji Adamu wanda shima ganin su yake ta sakin Fara’a .
Muryar Jidder ne ya katse su tana cewa “ A’a Momy meke faruwa ne ?”…..duka juyawa suka yi suna kallon inda Mom Hajara take gaba ?aya bin Ma’eesha take da Wani irin kallo tamkar zata cafke ta ….Hajara wannan kallon da kike mawa Aishatu na menene? Muryar Alhaji Adamu ya katse su. Hummmmm Wani irin Ajiyar zuciya Mom Hajara ta sauke tana mi?ewa tare da ?ara ?are mawa ma’eesha kallo , kawai sai ta juya ga Alhaji Adamu tana furta “ Ka kalle ta da ?yau ko dai idanuna ne? . Ali wannan itace wannan dai Ma’eeshan ko wata ce daban? .
Aaaahhha’aa! Mami ta furta itama tana mi?ewa, yayin da Ma’eesha duk sai taji tasha jinin jikin ta. Yanzu kuma mene zata ce akan ta ? Abun da take Tambayar Zuciyar ta kenan ?. Kaman Wanda Alhaji Adamu ya san Ma’eesha cikin ?arfin murya yace “ Ita ce dai gata nan menene kuma?”.
Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un….ta furta tana kallon su duka , Wasu irin marayun ?as?antattun hawaye na zubo ma kuncinta sharrr³. Cikin sauri Jidder ta ri?o Mom Hajara itama tana fara kukan tare da cewa “ Mom don Allah wai menene? Meke faruwa ne Mommy? . Kallon su tayi kana ta kalli Ma’eesha wacce ta ma?ale jikin Mami….Jan numfashi Mom hajara tayi tare da cewa “ Wannan ba Ma’eesha Bace! Zahara ce!! Zahara tace!!!
Wani irin kallo su duka suke bin ta dashi , kana Aliyu yace “ Anya Mommy babu matsala kuwa a tare dake ?.
Gaskiya kam! Mami ta furta tana bin ta da wani irin kallo , kana ta cigaba da cewa “ Ya kamata a bincike ?wa?walwar Hajara gaskiya da matsala.
Cikin matsanancin damuwa da rashin sanin hujjar ta , ta kalli mijin nata Alhaji Adamu kana tace “ Ka fa?a musu Wannnan itace Zahra na , ko kai ma ka manta da ?ar da muka haifa ne? Idan su basu san ta ba kai ai ka san ta! Ta furta cikin ?aga murya wasu hawayen na da?a ?waranya mata ”.
Shiru Alhaji Adamu yayi kaman mai nazari …Gaban Ma’eesha kuwa wani irin fa?uwa yake yi yana bugawa da ?arfi da ?arfi . Kallon al’amarin take yi kamar a mafarki , Wani irin magana Mom Hajara ke yi wai itace ?ar ta ? Kai gaskiyar Mami ne da tace a bin cike lafiyar ?wa?walwarta ”.
Mtswww!!! Dogon tsaki Mami taja kana tace Shashancin banxa da wofi. Kawai saboda kin dawo hayyacin ki da tunanin ki , shikenan sai ki kalli yarinyar da take nan tsawon shekaru Kice wai ?ar ki? .
Kuka Mom Hajara ta fashe dashi tana furta “ Wallahi ?a ta ce! Nifa na haife ta tayaya ko tsufa tayi zan gane ta , Ma’eesha Ni ce mahaifiyar ki.
Mom Hajara ke maganan kamar mahaukaciya. Khalil ne ya kalli Alhaji Adamu wanda shima ya fa?a tunanin Abubuwa gami da Ma’eeshan ,tabbas a jikin sa yake jin gaskiyar maganar Mom Hajara . Amma kuma baya da wata ?wa??waran shaida.
Ni na san bata mutu ba Wallahi ?a na ta raye.
To ai sai ki nemo ta , Wannan dai Ba yar ki bace . Mami ta katse ta cike da fushi .
Cikin Muryar dattako Alhaji Adamu ya kalli Mom Hajara kana yace “ Ya isa Hajara mu wuce mu tafi gida yanzu ,zan Miki bayani……Kallon sa tayi tana gani yana tasata tare da yi masu Daddy sallama wanda Duka jikin su yayi sanyi.
Bin ta da kallo Ma’eesha ke yi jikin ta yayi sanyi Qlau. Kawai ji tayi bata jin dadin ganin Mom Hajara a wannan halin , Zuciyar ta na mata babu Da?i ”.
Har sun kai ?ofa ne Muryar Aliyu ya katse su inda yake cewa “ Abba momy ku dakata! Juyowa suka yi suna kallon shi , inda ya juya yana kallon Ma’eesha dake tare da Mami .
Da gaske ne Ma’eesha diyar Mom Hajara ce babu shakka a ciki , ita ?ar Mommy ce!?? . Bu?e baki jidder tayi tana fa?in bamu gane ba? . Ita kuwa Mom Hajara saurin fizge hannun ta tayi a hannun Alhaji Adamu tana furta ‘ Kaji ko wallahi na fa?a maka Zahran muce!
Wani irin magana kake yi haka Ali? Mami ta katse shi tana yi masa wani irin duba .
Uncle?
Muryar Ma’eesha ma ya katse shi tana kiran sunan sa , idanun ta na ciko da ?wallah kana tace “ Wasa kake yi ne ko? Don Allah Uncle ka bari , bance maka ina son ganin Iyaye na ba , bare har ka bani uwar da batawa , ina jin da?in zama da Mami da kuma Daddy don….. Na ta?a Miki ?arya? Ina da hujjoji na babu shakka Ma’eesha ?iyar Mom Hajara ce ta cikin ta . Idan kuna tantama ku muje Asibiti ayi maku gwajin jini . Sannan kar ku manta da Nine fa na tsince Ma’eesha a cikin moton da ke ci da wuta . Kar ku manta su ma hatsari suka yi ……Ya Salam! Furucin da su Daddy suka furta kenan!
Yayin da Alhaji Adamu yayi wani murmushi yana furta “ Alhamdulillah….” Ni tun a ganin farko naga ?a ta , amma kuma nayi shiru ne ko da tace ?ar muce na nuna mata ba haka ba ,saboda taji zafin tsanar data dingi nuna ma ?ar ta na cikin ta bata sani ba. Yau gashi Wa gari ya waya? Da wani zaki kalli yarinyar ki? Kina ma da bakin yi mata magana?”.
Wani irin kuka mai tsuma zuciya Mom Hajara ke yi ….Itako Ma’eesha ta kasa motsi jin abun take yana juya mata .
Ma’eesha da gaske Ga Abba , ga kuma Momy! Aliyu ya furta yana sakin mata murmushi wanda ta tsaya tana bin sa da kallo cikin Muryar kuka ta furta “ A’a Uncle ka barni da Mami, wannan sam ba mahaifiya ta Bace!
[2/1, 4:10 PM] Real~
Post a Comment for "Rainon Soja 88-89"