Rainon Soja 86-87
86-87
*Littafin na ku?i ne please don Allah kar ki karanta indai baki biya ba . Regular payment?500 Vip payment?1000 SPC payment?1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne sai ki tura ta wannan number 09061466409….?????
#Mamanteddy#mrsusm.*
Book 3
Gidan Alhaji Adamu
Tun daga Wajen gidan ya zamana babu masaka tsinke sai ?an Adam da talakawar layi da ya saba taimaka masu . Da yawa nayi ma ALLAH godiya don sunyi farin cikin Dawowan sa a hayyacin sa , matan sa kaman ashirin su ya tonu ne don da yawa an sam amanar sa suke ciki ?warai ”. Gawan Hajiya Falmata da aka shiga daga shi ne yasa Alhaji Adamu furta “ Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un…. Lahaula wala ?uwata, Saurin kama shi Malam Barau yayi yana nufar ?arayi daban da shi da sauran su Daddy da suma basu da Labarin Mutuwar nata sai a yanzu . A takaice Cikin sasan Hajiya Turai suka nufa inda itam a take zaune tsumi kama r wacce ruwa yaci yacinye ta. Don gaba ?aya suna Wani hali , ga Hajiya Atika can an sata a ?aki an rufe tana hauka tuburan tare da fa?in duk wani abu da ta aikata a rayuwar ta da Alhaji Adamu .
Sai bayan an kai Hajiya Falmata gidan ta na gaskiya ne ,sannan Su Daddy da Abokan Alhaji Adamu dashi kan sa suka nufi ?angaren Hajjiya Turai daga nan suka wuce na Hajiya Atika anan ne Alhaji Adamu sai da yayi ma kan sa Hawaye. Iraki Mom Hajara ji take kamar ta dam?o wuyar mahaukaciyar a cewan ta tayi mata dukan Tsiya, Amma haka ta Daure tana kuka ta fice don sosai mijin ta ya bata tausayi ?warai .
Mami taso su zauna amma firrr ta?i zama don dole suka tarkata da cewan zasu yi ta zuwa har a gaba zaman makoki ayi uku . A kwana ukun nan asiri ne kawai ke tonuwa ta faru ta ?are , don dangin Alhaji Adamu suma da kan su sai da suka ce ai rabuwa da duka matan zaiyi , daga ?arshe Allah ya bashi mata ta Gari . A haka suka tashi babu tsuntsu bare tarko . Nasreen kuwa ko dangin mahaifin ta sun?i amsar ta bare mahaifiyar ta. Yanzu Tasan menene rayuwar Duniyar?.
**
Tsaye take a bakin ?akin Chawai inda yake ciki yana she?e ayar sa da ?ammatan sa . Hannu tasa tana bugun ?ofan wanda kaman mintuna biyar sai gashi ya fito fuska a murti?e babu harka da walwala yana fa?in “ Meye kuma , haba Don Allah mutum yana jin da?in sa da mata masu da?i kinzo kina Wani damun mutane ?ara gaba Malama!
Kallon sa Nasreen tayi jiki a sanyaye kana tace “ Haba Chawai nafi minti arba’in anan Wurin , yanzu kuma ka fito kana mun fa?a aka , Chawai ko ka manta wacece Nasreen? . Don kece Nasreen sai aka yi yaya? Malama ?an Allah karagaba, kar na sake ganin ki a rayuwata! Duka munji abun da mahaifiyar ki tayi mawa mijin ta Alhaji Adamu, kai har uban ki ma ance itace ta kashe shi . Don haka bana son ?ara ganin ki Idan kuma kin?i ji ba zaki ?i gani ba”. Ya furta yana rufo ?ofarsa baaaaammmm tare da barin Nasreen anan Wurin tsaye …….Juyawa nayi ina kare mata kallo , gaba ?aya ta sauya kamanni fuska tayi ba?i tayi kanta na talauci da shiga Masifar rayuwa . Ni kuwa nace dama komai yayi farko zai ?arshe ,ka ?ulla Alheri sai bayan yayi ?yau .wannan kenan!
**
Wow Uncle kayi ?yau sosai ina zamu je da sanyin Safiyar nan? . Ma’eesha ta furta tana kallon Aliyu inda ya yayi shigar Sa ta cikakken bahaushe shadda milk an masa ?inkin zamani ?inkin yabi jikin sa yayi ?yauuuu ?warai.
Har wani ?an ?iba yayi ?wana biyu ya aje ?an ta?a ka?an na Hutu da ?wanciyar hankali . Murmushi yayi yana kashe mata ido ?aya tare da cewa “ Yau gidan Mami zamu je ”. Wani irin farin ciki ne ya kama ma’eesha da Sauri ta kai hannun ta tana Rungume shi tare da tsallen murna , har yanzu yarintar bai sake ta ba . Murmushin shima yake yi kana yace “ Ai ba da?ewa zamuyi ba . Kawai saboda ina so mu ha?u da mijin Mom Hajara ne , to zamuyi masu kwana biyu , don naji Ance An maida Auren ma nasu yanzu haka tana gidan mijin ta. Kuma nan da Sati ?aya za’a daura Auren Khalil da Maryam ”.
“….Hummmm”. Sauke Ajiyar zuciya Ma’eesha tayi kana ta ce “ Yayi ?yau Uncle , Allah ya kaimu lokacin ???? ”. Amin ya furta yana ri?e mata hannu tare da nufar Farfajiyar gidan ……! Gidan Mom Hajara zamu fara zuwa …..ya furta yana ra?a mata a kunne . Ita dai kawai taji gaban ta na ta fa?i, musamman yawan sunan Mom Hajara da yake kira , kuma gashi tasan yanda ta tsane ta a rayuwa . Wannan yasa ta yin shiru tana ta tunanin zuciya ita ka?ai don tsoro ne yake kamata.
Bayan sun shiga garin Abuja”.
?aga Wayar sa yayi yana kiran Mom Hajara inda yasa Wayar a amsa kuwa. Hello Mom gamu a hanya zamu zo Ni da Amarya????matata ”. A lokacin Mom Hajara tana zaune ne a daya daga companin Alhaji Adamu na shinkafa tana gudanar da Wasu Ayyuka tare da bin ?wa??wafin inda yake da magu?i don ta yi gyara sosai . Gyara zaman Gilashin ta tayi tana kallon Alhajin nata tare da murmushi, Sai tace “ Alright Kar kazo kuma kayi mun wannan rawar ?afar akan yarinyar nan , Wacce kake jin ta tamkar ran ka , da tana da iyaye to da tabbas nace An shanye ka ne ba a hayyacin ka ka be .
?aassa ma’eesha tayi da ido ?wallah na turuwa a cikin su. ?an cije la??an sa yayi kana yace ” Mom stop please…ai gaskiya ne….kayya! Wai Da wane kike magana haka Hajara ? Muryar Alhaji Adamu ya katse ta , inda ta furta “ Da yaro na ne Aliyu , ina masa fa?a ne akan matar sa da ya Aura ko nace Yarinyar da ya Raina ….Ammmm kana jina Haidar?. Sauke numfashi Aliyu yayi a ?an ?asa ?asa yace “ Ina jin ki Mom ”. Hunmm na ta?a ?ar zinare ba , dole ka amsa Ni ?asa ?asa . To yau akwai event da za’a fara na Maryam , mu ha?u a guest house ?in Mamin ka duka har dashi yanzu zamu nufa can . Duk da taron sai 4:00pm ne , Amma mu tun yanzu zamu je don a fara komai a idanun mu . Ohk ya furta yana datse wayan tare da danne damuwar sa kar hankalin Ma’eesha ya tashi………..!
[2/1, 3:35 PM] Real~Mamanteddy: *???RAINON SOJA???*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*
Post a Comment for "Rainon Soja 86-87"