Diddigar Kaya 21
DƘ
21
Kimanin sati biyu kenan da faruwar abunda ya faru amma ta lura har yanzu ba wani shiri suke yi da Fatima ba, ya bata key ɗin kitchen na ƙasan gabaɗaya sbd rashin zamanshi don sun koma aiki ka'in da na'in, bata shiga harkar Fatima da take ji kaman ta hadiye zuciya ta mutu sbd yadda Faizan ya ɗauki fushi da ita akan abunda take ganin be taka kara ya karya ba, ita da ya kamata yanzu ya tarairayeta ya bata kulawa.
Ita dae Fauza tunda tana da husna bata da matsala don yarinyar na debe mata duk wani kewa, tare suke koman su cikin hira da dariya lokuta dayawa gani take kaman husnan sa'ar ta ce in gujel gujel ne ma duk haka suke zagewa su yi kayansu.
Kaman yau a parlorn ƙasa suka yi la'asar sbd cookies da suke yi kar ya ƙone, bayan sun idar suka zuba shi a tray me kyau, da Homemade pineapple juice tayi musu har zasu haura dashi se husna tace
"Aunty mu je garden pls you promised fa cewa weekend nan zamu je ni kam I want to play with swing"
Fauza ta kalleta tace
"ke kam kina da aiki mutum baya mantuwa? To mu je"
Juyawa suka yi suka fito, daga hannun hagunsu akwai wani ƙofa suka shige sun ɗan yi tafiya kaɗan se ga garden ɗin masha Allah kore sharrr, akwai lilo sbd hutawa, gefen shi akwai table da chairs, nan ta ajiye snacks ɗin, suka je suka hau Lilon suna lilawa Fauza na tsoron juwa bata so da karfi amma da gangan husna ke wullawa da karfi wadda ke saka Fauza ihun kiran sunanta ita kuma ta watse da dariya.
Zaune yake a balcony ɗinshi bayan ya dawo daga sallar la'asar sanye da farar jallabiya wacce bata kai kasa ba don kana iya hangen black trouser da ya sa daga ciki, fuskanshi yayi wasai yayi wani irin kyau, dariyar su da kuma ƙarar Fauza shi ya saka shi miƙewa tsaye, chan ya hange su suna ta lilo, lumshe idanunshi yayi ya buɗe kan tray ɗin dake gefensu, ba karya his tongue have been craving for the tatse of her food again barin ma tea ɗin nan da sati biyu kenan da yake so yace ta mishi yana fuskewa.
Jaridar ya ɗauka ya koma ɗakinshi ya buɗe kofa ya sauƙa ƙasa, a natse yake tafiya cikin ƙasaitacciyar tafiyar shi da already ya zamar mishi jiki ya isa garden ɗin.
"Husna bari! Bar lilawa hakanan jiri ze yarda ni"
Ta faÉ—a tana runtse da idanu, husna kam ina ruwanta ta maida kafafunta baya ta cilla da karfi daidai ta buÉ—e idanunta ita kuma ta hantsila tana shirin faÉ—uwa yayi azamar tare ta duk idanu suka zubawa juna..
Da sauri kuma ta miƙe tsaye tana gyara ɗan kwalinta da ya zame ya bayyana baƙi sidik ɗin gashinta da ta tsefe kitson bukin ta ta tufke saboda ihun da husna tayi na
"Uncle zo ka hau lilo tunda Aunty na tsoro.."
Ta faÉ—a tana wangale mishi wawulonta, murmushi yayi yace
"zan zo babyn uncle amma yanzu cigaba da abun ki ke kam"
Ya karashe yana zama akan chairs ɗin wurin tare da crossing kafanshi, duburcewan da tayi yake kallo ƙasa ƙasa duk in yana wuri sakewarta ba sossai ba don tun sati biyu da in har yana gari ya kan shiga sau biyu ya duba su ya lura da hakan musamman idan husna ta rike shi da surutu ya ɗan jima se ta rasa natsuwa.
Juyawa kawai tayi tana cewa husna
"in kin gama se ki dawo É—aki"
Har ta juya ta ji sassanyar muryarshi me cike da natsuwa ya ce
"Ji mana..!"
Baki ta tura tace a ranta se kace wata budurwa da ake shirin tarewa a titi.
Juyowa tayi bayan ta gyara bakin da ta turon tace
"Na'am"
Yace yana kallonta kai tsaye wadda har tsikar jikinta take jin kallon
"Ni dodo ne da in na zo wuri kike guduwa?"
Bakin ta sake turowa tana cewa a ranta
"ai ka fi dodon ma razanarwa, in ka so kayi kirki in ka so ka tabka tsiya ko a gyalenka"
A fili kuma tace
"A'a kawai ina da abunda zan yi ne a cikin"
Yace
"ok, before then zan samu shayi?"
Kai ta gyaÉ—a mishi kan ta juya ta fice, cookies É—in ya É—au É—aya ya sa a baki yana mamakin yadda ta iya abubuwa haka masu daaÉ—i.
Cikin mintuna da basu fi ashirin ba ta dawo da tray me É—auke da karamin glass tea flask da cups É—inshi a jere a gefe, a gabanshi ta ajiye tana kallon yadda yayi nisa a cin cookies É—in nata.
A ranta tace
"ko tayi ba'a yiwa mutum ba ya zage ya cinye mana abunmu"
Kaman kuwa ya san me take cewa yace
"daina min kallon ba'a gayyaceni ba na ci, ladan kati na da kika ƙarar ranan ne"
Wara idanu tayi a kanshi yana tsiyaya tea É—in a cup bayan ya gama ya É—ago yace
"yes"
Ta langwabe kai tace
"to Ayya in sake maka cookies É—in ka bani in sake waya dasu? Bana jin daaÉ—i yadda na kwana biyu ban ji su ba"
Yace
"no bana son wannan, wani abu daban nake so"
Ta Yi saurin cewa
"menene?"
"Zaki dinga dafa min wannan tea É—in kullum"
Da saurinta tace
"eh na yarda"
Murmushi ya saki wadda ya sakata kusan shagala da Kallonshi yace
"wayan na sama in mun haura zan baki"
Tsallen murna tayi tana cewa ta gode, kallon da yake mata yasa ta natsu ta juya ta wuce cikin don bazata iya zama a inuwa É—aya dashi ba Sam bata iya sakewa.
Kaman yadda yayi alkawari bayan sun hauro da Husna ya bata ta kai mata, taji daaÉ—i sossai amma ta ji haushi da ta duba taga ya goge hotunan da tayi a wayan kuma da gayya ne tunda ga na matarshi da nashi na ciki nata ne ya goge, a daren suka sha hira da jadda har da su fa'iza da faaazila sun gaisa sbd tayi kewarsu.
Mammi ma sun jima suna waya kan ta ba husna ma ta ishe ta da surutu, bayan sun gama ta bata wayan ta maida mishi.
Tun daga wannan rana kullum da safe da dare kaman ka'ida se tayi mishi tea ɗin nan, yawanci tana samun shi ko a dining ko a parlor ta ajiye mai, sadda Fatima tayi noticing kusan hauka ta saka mishi ai ba bata iya bane be ce yana so bane, shi kuwa namijin duniya kai tsaye ya ce mata na hannun Fauza yake so ba nata ba shiyasa be tambayeta ba, tayi kukan maganan nan, kudirinta da haushinta kan Fauziyya kuma ya ƙaru, dukda Auntyn ta tayi fushi me girma da ita sbd abunda tayi kwanaki tace ya so lalata musu aiki don in ta bari Faizan ya fara tausayawa Fauza so ze iya shiga idan kuma so ya shiga tabbas ze saka alamar tambaya akan son da yake yi mata ita.
Ta dawo daga lectures tana haurowa suka kusa cin karo da fauza dake shirin sauƙa da kayan tea ɗinshi da yanzu kenan ya gama sha take shirin sauka dashi, tare ta Fatima tayi.
Matsawa tayi zata bi ta gefe ta sake tare gefen, tana kallonta tace
"Fauza me kike nufi da mijina?"
Har kaman bazata amsa ba se kuma tace
"me kuwa nake nufi? Last time da na bincika duniya sun sheda Cewar matan Faizan biyu ne, ko kunnuwanki sun toshe ne a sadda amsa kuwwa ke bayyana cewa an shafa Fatiha fauza ta zama ta Faizan?"
Wani irin takaici ne ya zowa Fatima wuya
"ke har kin kai macen da zaki yi ikirari namiji kamille irin Faizan ze so ki? Sauran wasu ce fa da sauran shaye sha...."
"Shhhhhhhhh"
Fauza ta faÉ—i tana sa mata hannu a lips É—inta tace
"wannan kuma tsakaninmu ne kin gane ko? So kiyi ta kanki gwara ni ban bi hanyoyi masu yawa da haramci wurin mallakarshi ba, ban kuma zauna na É“ata hawayena wurin kukan in ban same shi ba zan mut....."
Ɗaga hannu Fatima tayi zata mareta tayi saurin tarewa wadda ya saka tray ɗin hannunta faɗuwa ya fashe tartsatsa, hannun Fatima ta cillar wadda ya sakata loosing balance ta tafi suuuu tana kwala ƙara.
Razanar da tayi yasa Dukda bata faɗi kan cikinta ba cikin ya ƙulle har jini ya balle mata, Da sauri ya karaso yana ambaton innalillahi wainna ilahi rajiun, Fauza ta buɗe baki zata mishi magana ya ɗauke ta da wani irin mari wadda ya sakata yin baya kafanta na dama ya sauƙa a kan glass da ya fashe a wurin, runtse idanuta tayi da karfi tana jin zafafan maganganun da yake jefanta dasu.
Bata buɗe ba har ya sauka ya kama Fatima dake kuka haikan sbd baƙin ciki don ta san wannan ciki kam se wani ikon Allah suka fice daga gidan da hanzari.
Ilai kuwa Fatima ta rasa cikin tayi kuka har kaman ba gobe, likitan ya tabbatar musu da cewa mahaifanta is weak already shiyasa abu kaÉ—an ya iya É“arar da cikin, haka ta saka shi a gaba tayi ta kuka wadda ya saka tausayinta kama zuciyarshi, Baba prof ya kira ya sanar mai da É“arin.
Ko da ya tambaya ta yaya hakan ya faru cewa yayi haka Allah ya tsara wadda kai tsaye Fatima ta dakatar da kukan tana kallon shi tace
"Haka Allah ya tsara fa kace yaya? Ko kuma Fauza ce ta zubar min da shi?"
Be so baba prof ya ji ba sede a yadda tayi maganan dole ya ji, tambayar shi yayi ya hakan ya faru? Taya Fauza zata zubar mata da ciki? A gaban jadda da Baba Alhj yake amsa wayan wadda duk hankalinsu ya koma kanshi jin wani sabon zance.
Yace
"Baba ban san me ya hada su ba na fito daidai lokacin da Fauziyyar ta hankaÉ—a hannunta wadda ya saka kafafunta gaucewa kasancewar tsaye take a kan stairs hakan ya saka ta faÉ—i amma bata faÉ—i kan cikin ba tsoratar da tayi ne ya saka cikin É“arewa"
Kuka me karfi ta saka tana cewa yana shirin baiwa Fauza kariya bayan ya gani kiri kiri ita ta turo ta ta faÉ—i, yadda take ta maganganu har take nema ta wuce layi yasa baba prof yace ya bata wayan amma shima bata wani saurare shi ba sbd kuka da take tayi.
Allura kawai Faizan ya sa aka mata a take bacci ya É—auke ta, Baba prof ya tambayi ina Fauza?
Se a lokacin Marin da yayi mata ya dawo mai, lumshe idanunshi yayi yana É—an sauke numfashi yace
"tana gida baba"
Baba yace
"To ka tabbatar baka yanke hukunci cikin fushi ba, ka zauna kaji both side da yadda komai ya faru, abunda ya faru ya riga ya faru fushi ko hatsaniya ba ze dawo dashi ba, in har ka gama sulhunta gidan ka se ka HaÉ—ani da Fauziyya É—in"
Ya amsa a ladabce.
Baba Alhj yace
"tayi wani abu kuma ko?"
Baba prof yace
"tayi, amma wannan tsakaninsu ne, ba zamu saka baki ba sbd idan muka zama masu saka idanu da yawan magana akan rayuwar gidanshi to lallai zuciyarshi zata mace, mu zuba idanu kawai ya gyara gidanshi da kanshi idan ba ya nemi mu shigan bane babu anfanin shigan"
Duk sun gamsu da hakan prof mutum ne me hange sossai, sun fahimci dalilin shi na yin hakan don duk sauran yaran nashi ba idanu yake saka musu a Gidajensu ba Idan har ba sun zo gabanshi bane da matsala so na me ze saka akan su Faizan?
A ta É“angaren shi kuma ya jima zaune zuciyarshi babu daaÉ—i, dukda be kwallafa rai a kan cikin ba amma akwai zafi ace ka rasa gudan jininka da kake fatan gani a duniya, abunda kuma ya fi bashi haushi yadda sautin Marin da yayi mata ya kasa barin kwalwanshi a kuma ranshi yake jin zafin hakan.
Mikewa yayi ya nemi izinin tafiya zuwa anjima ze dawo su kula da ita sossai pls, Dr yace ba damuwa ba ma lallai ta tashi yanzu ba don allurar ze jima yana aiki sbd bata samun cikakken hutawar ruhi dama chan.
A hankali yake murza sitiyarin motar yana amsa wayan Jafar a kasalance, yana faÉ—a mishi matarshi na asibitinsu tayi miscarriage, tausayinshi yasa Jafar yayi ta bashi baki murmushi kawai yake É—an yi yana furta ba komai haka Allah ya tsara.
Bayan ya kashe be fi mintuna biyar ba se ga kiran Faisal wadda shi kuma lecturer ne a makarantar su Fatima, shima cikin tausayawa don a cikin abokanansu Faizan ne kaÉ—ai be da yaro ko yarinya wacce zata kai shekaru bakwai sbd be yi aure da wuri ba, bayan yayi auren ma ga wani matsala nan na É“arewar ciki.
Shima dai nuna mishi yayi haka Allah ya tsara.
A harabar gidan yayi parking ya sauka yana karewa gidan kallo kaman sabo ne a idanunshi, kofan motan kawai ya tura ya nufi ciki, a stairs na karshe ya tsaya yana kallon broken glasses dake zube a wurin, gabanshi ne ya faÉ—i ganin jini me yawa da har ya soma bushewa a wurin.
Da idanu yabi É—igon É—igon da jinin ya bi se ya kare kan kofar ta, yana haurawa husna dake zaune jugum ta tashi ta zo wurinshi da gudu kaman zata yi kuka tace
"uncle na tashi bacci na samu Aunty tana ta kuka daga karshe ma ta koreni tace in zo in kalli MBC waye ya daketa?"
Shafa kan yarinyar yayi yace
"Babu, na san ma ta daina husna je ki kalli cartoon É—in bari na duba ta"
A hankali ya buɗe kofan ɗakin nata ya sanya kai ciki, jinin ya diga har gaban gadonta, tana kwance rub da ciki kafan na daga ƙasa ɗauke da kwalba me girma jini se diga yake har lokacin amma ita kam kuka kawai take yi, ita kanta ta rasa wannan kuka da take yi don tana da taurin zuciya ta rasa yadda aka yi abunda Faizan ya mata yayi mata zafi sossai da sossai.
"Subhanallah! Fauziyya?"
Ya ambaci sunanta yana riƙe kafan, zare kafan tayi daga hannunshi ta maida gefe tana me cigaba da kukanta, sake riƙe kafan yayi ta sake zamewa, guwiwanshi ɗaya ya saka kan gadon ya mirginota tare da ɗaga ta zaune se ta kara sautin kukanta cewa yake
"baki da hankali ne zaki zauna jininki na ta diga haka a ƙasa in ya kare fa?"
Ba tare da ta kalleshi ba tace
"se in mutu kowa ya huta tunda dama an tsane ni....."
Cakkk magananta ya tsaya jin ya sungumeta gabaÉ—ayanta tayi hanzarin saka hannayenta ta zagaye wuyanshi gudun kar ta faÉ—i....
DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira É—ari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰
Karku sake a baku labari.
🖤Gureenjoh🖤
Post a Comment for "Diddigar Kaya 21"