Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Diddigar Kaya 20

 DƘ



20


Ihun da husna ta sa na yeeey an kama uncle shine ya dawo dasu daga wata duniyar da suka tafi, da sauri ta matsa baya tana saukar da kanta Æ™asa, shi kam basarwa yayi ya riÆ™e husna dake cewa shima a É—aura mishi yayi tunda an kama shi yace 

"A'a husny zan yi amma Ba yau ba, baki ga yanzu na dawo ba?"


Tace cikin yarantarta 

"eh uncle, ina tsarabata?"


Ya kalli Fauxa yace 

"Auntynki ta zo ta karɓa miki"

Yana kai nan ya juya ya fice.


Husna taje da gudu wurin Fauza tace 

"Aunty fauza uncle wai ki je ki karɓa min tsarabata"


Fauza tace 

"Toh husna"


Husna tace 

"Aunty in kallo MBC kan ki dawo?"


Kai kawai Fauza ta É—aga, kan ta É—auki hijab É—in sallarta ta zura tare da fitowa, baya parlorn don haka É—akinshi ta wuce tayi knocking aka bata izinin shiga.


Ta tura a hankali ta shiga, this is the first Time da ta shigo É—akin, tsaruwa da haduwar É—akin ya tafi da ita kasancewar shi me son fari hakan yasa komai na É—akin fari ne, sossai tsarin rashin hayaniyar É—akin yayi mata kyau, a kan kujera yake zaune ya tankwashe kafa, hannunshi wani daily trust ne yana dubawa.


Ta É—an rusuna tace 

"ga ni yaya"


Da hannu ya mata nuni da ledojin da suke kan table wadda Fatima ce ta ajiye ta je kuma É—auko plates da sauran abubuwan da zasu yi anfani dashi ne, yace 

"Ki dauka muku É—aya"


Tace

"An gode Allah ya saka da alkhairi"


Se a lokacin ya ɗago yana kallon face ɗinta da ya fito fess a onion hijab ɗin nata, daidai lokacin kuma Fatima ta shigo ɗakina gabanta ne yayi wani irin faɗuwa wadda seda cikinta ya nemi kullewa, a makogoronta taji wani abu ya tiƙe ta me take yi a ɗakin nan? Ta tambayi kanta kan ta karasa daidai lokacin ita kuma Fauza ta ɗauka ta juyo.


Da wani irin banzan kallo Fatima ke bin ta, ta san duk sbd wannan Husnan nan ne har Fauzan ta samu shigowa É—akin mijinta, daga yarinyar har Fauza ji take kaman taje ta sa musu wuta a É—akin su mutu, sbd yanzu bayan shigan asuban shi duk in ya dawo se ya shiga, gashi Faizan mutum ne da babu fuskan kawo mai wargi ko tace zata hana shi abunda yayi niyya, gaskiya bazata iya hakuri ba kaman yadda take aika mata da harara haka itama ta rama tare da jan tsiririn tsaki wadda ya sake hasala Fatima har bata san ta furta


"kan uba!"

ÆŠagowa Faizan yayi yace 


"lafiya?"


"Baby yarinyar nan wai ta buge ni kuma ko sannu babu tayi wucewarta?"


Yace

"Fauza?"


Haushin kiran sunan tan ma ya sake mamaye ta tace 

"ita fa"


Shi har ya manta da ainihin halinta don yanzu yana ganin babu shiru shiru irin ta, sannan ga saurin bada hakuri wadda wannan na daga cikin abunda yasa tunda ta zo gidan faɗa me tsayi be taɓa hada su ba don duk ɓacin ranshi da zaran ka ce mishi yi hakuri shikenan, fauza bata san shi ba bare ta san lagon shi.


"Tunda har ta fita bata sani bane na san da ta baki haƙuri, yunwa nake ji zo yi serving ɗina"


Wani haushi ne ya sake turnike Fatima, yau Faizan ke kare Fauza? A kufule tayi serving É—inshi ta mike yana tambayarta bazaki ci bane? Ko bata juya ba tayi ficewarta, girgiza kai yayi yana mamakin halayyar da take nuna mishi tun daga shigowanta gidan, tabbas ba don shi jajirceccen namiji bane da se abunda Fatima tace a gidan za'a yi, ita in har ba'a yi ra'ayinta ba tayi ta fushi kenan tana kumbure kumbure?


Abincin shi ya ci ya koshi ya wuce toilet yayi brush da wanka ya zo ya sauya zuwa kayan bacci, kwanukan ya fitar da sauran abubuwan makulashen da ya sayon ya kai fridge É—in kitchen, daga nan ya wuce É—akinta ya samu wai har ta kwanta be tanka mata ba ya fito ya nufi É—akin Fauza.


Suma ya sa mu sun kwanta kuma har ma sun yi bacci, fitowa yayi kawai ya koma dakinshi ya kwanta shima don yana da flight 8 zashi Lagos amma around 9 na dare ze dawo..


Washegari yana idar da sallah yayi sauri ya watsa ruwa ya shirya kan ya fice bayan ya leƙa Fatima da bata tashi Bama, don ita wai don ze yi tafiyar sassafe ta samar mai abinci bata san wannan ba sede in yaje airport ya karya a chan kan ya wuce, be damu ba sbd dama chan haka yake yi.


Tana jin fitan motan shi ta mike zaune, tare da sauka daga gadon dama tayi wanka kawai ta saka kaya ta yafa gyalen ta ta fito, tun wata biyun farkon aurensu ya koya mata mota kuma ya saya mata wata karamar Hyundai, direct kitchen na sama taje ta rufe da key, ta sauƙa kasa ma ta rufe ta haɗe keyn ta watsa jaka kan tayi ficewarta daga gidan.


Bayan su Fauza sun tashi tayiwa husna wanka itama tayi suka gyara gidan tare duk bata lura kitchen a rufe ba se bayan ta gama taje ta murɗa kofan ta ji shi a rufe, kitchen na sama ta dawo taji a rufe, da mamaki take kallon kofan kan ta wuce kofan Fatima ta murɗa shima a rufe, ajiyar zuciya ta sauke kan ta kama hannun Husna suka koma ɗakinta da Tunanin Fatima ba nisa tayi ba Dukda dae ita bata taɓa gani an rufe kitchen ɗin ba duk zamanta a gidan.


Sauran kazan jiya ta turawa husna da Admiral 'A Dukda yayi sanyi sossai haka dae ta lallaɓa husnan ta ci, bata san lokacin da zasu dawo ba hakan yasa bata ci ba ita gudun kar kuma basu shigo da wuri ba husna ta sake jin yunwa.


Wasa wasa har azahar babu wadda ya dawo a cikinsu gashi lokacin yunwa ya fara kama Fauza da babu abunda ta saka a cikinta, sauran kazan ta sake baiwa husna ta cinye.


Tun suna kallo har taji bazata iya cigaba da kallon ba sbd yunwa da yake shirin yi mata illa, bayan sun yi la'asar ta duba jakanta ta fiddo kuÉ—in da Jaddah ta sanya mata ciki tun randa za'a kawo ta tare da sanya hijab ta kama hannun husna suka fito, saide me gadin wadda yoruba ne yace mata oganshi ya mishi umurni kar ya barta ta fita daga gidan ba tare da izininshi ba.


Rokon shi ta fara saide tsoron rasa aikinshi yasa be kula ta ba, don Sam be san ita É—in matar Faizan bace ba ma, haka suka hakura ganin tsayuwar baze yi musu ba suka koma ciki amma fa ganin magrib yayi ga dukkansu biyu yanzu sun jikkata don husna har ta fara kuka yasa ta sake fitowa ta roke shi ko ze kira mata ogan nashi da Wayanshi don ta san dae duk muguntar Fauzan in har ita ze iya mata to baze iya yiwa É—iyar kaninshi ba, unfortunately layinshi baya wucewa.


Haka suka sake dawowa parlorn kasan tana jin yadda ƙasan cikinta ya riƙe kam kam kaman zata mutu, daurewa take tana rarrashin husna da yanzu ta fara kiran iyayenta se tausayin yarinyar ya kama ta, fita tayi ta fara duba gidan, ba irin gidansu bane bare ta iya zamewa ta fita, ba kuma zata iya faɗawa me gadi abinci babu zata je su saya ba sbd ta san hakan kaman wani tonon asiri ne ga Faizan wadda be kamata gida kaman nashi ace babu abinci ba me gadin ma ba yarda ze yi ba.


Hawaye ne ya gangaro mata ta sa hannu ta share, bata da waya bare tayi order a kawo mata har gida.


Komawa sama tayi zuwa dakinshi banda sassanyar kamshi shi babu abunda yake tashi, duk irin dubawar da zata yi bata samu wayan da ya ara mata jiyan ba. Kuma Sam bata kula da lockers É—in gefen fridge ba waenda snacks ne a ciki da su dangin cereals tunda ta san ita nata babu komai ciki.


A Æ™asa ta saka gwiwowinta ta É—aura kanta a kan gadon hannunta dafe da mararta dake wani irin kugi, husna ce ta biyo ta tana kuka sossai ita tana jin yunwa, miÆ™ewa tayi ta kama ta tace 

"mu je mu yi isha se mu koma ko mai gadin ze yarda mu fita"


Komawa É—akinta suka yi ta bar É—ankwalinta anan a É—akinta suka yi sallah shima ba natsuwa, ko da suka sake fitowa neman yiwa mai gadin bayani take saide be kula ta ba, masifa zata fara mishi saide bata da karfin hakan kasancewar bata bar ko ruwa ne ya shiga cikinta ba.


Rarrashin husna kawai take suna tsaye kaman marayu se suka ji horn, da sauri me gadin ya karasa ya duba ganin oganshi ne yasa yayi hanzarin wangale gate É—in.


Wutar motar shi ne ya haske mishi su yadda suke tsayen yasa gabanshi faÉ—uwa.

"Peter, me ya kawosu bakin gate?"


Peter yace 

"Sir tun da afternoon suke ta so su fita kuma ka ce kar in yarda in bar kowa fita bayan madame, ta sakani nayi ta kiran phone naka saide baya shiga sir"


Ganin hawaye a fuskokinsu duk su biyu ya sa ya san ba lafiya ba, da hanzari ya karasa da motan tare da buÉ—ewa ya fito yana kallon su yace 

"Fauziyya lafiya? Me kuke yi a nan? Ina Zaku je?"


Kasa magana tayi se hawaye, da gudu husna taje ta rungume shi tana cewa 


"uncle yunwa muke ji, tun safe Aunty bata ci komai ba nima sauran kazan da ka sayo mana jiya tayi ta bani kuma ya kare nima na fara jin yunwa, gateman kuma ya hana mu fita mu sayi abinci... Ina ta kuka amma Aunty tana ta rarrashina dukda itama tana kukan bata so na gani"


Wani irin yanayi marar misaltuwa ya shiga, yana rike da yarinyar yace 


"yunwa? Fauziyya?? Me ya samu kayan abincin gidan?"


Kanta Æ™asa tace a hankali 

"tun da muka tashi suke rufe"


Kokarin controlling bacin ran da ya shiga yake yace 

"Fatima fa?"


"Itama mun tashi bamu sameta ba"


Ze yi magana se ga knocking na Fatima, me gadi yaje ya buÉ—e ta shigo tana ganin Fauzan tace 

."Oh baby ashe ka dawo? Ina ta kiranka tun six bana samunka, ka ga ban dawo da wuri ba ko? Wlh na fito lectures 6 mota na ya lalace masu gyara suka ta É“ata min lokaci yanzu haka ma na bar musu ne na biyo bo....."



"Fatimaaaa!"

Ya daka mata tsawa muryarshi with so much anger yace 

"me ya rufe kitchens É—in gidana tun safe?"


Zata yi magana ya sake daka mata tsawa

"don't you dare lie to me, me yasa kika rufe kitchen kika tafi da keys alhali kin san akwai mutane a gidan? Kisa kike son yi? Fatima a gidana har a yini da yunwa??"


Kuka ta fashe dashi tana rasa abun faÉ—a don kwakwalwanta rasa irin karyar da zata yi tayi, in ina ta fara daga yadda fuskanshi yayi turning red ka san ranshi ya kai makurar É“aci.


Kallon Fauza da bata sake Kallonsu ba yayi yace 

"Fauziyya shiga mota muje"


Wucewa Fauza tayi ta buÉ—e back seat É—in motan shi ta zauna yayinda yake rike da hannun husna yana nuna Fatima da hannu wacce ta fara cewa 


"A'a ina zakuje? Ga fa keys É—in na dawo dasu..."


"Ki tabbatar kin tanadi furucin kare kanki a gareni kan in dawo don wallahi wallahi ranki se yayi mummunan É“aci akan wannan abunda kika aikata, ko babu aure Fauziyya da husna sun fi karfin yunwa a gidana Fatima..."


Yana kai nan ya zagaye da husna ya buÉ—e mata gaba ta shiga, ya dawo side É—in driver ya ja motar ya fice da gudu.


Hannu Fatima ta É—aura a kai tace 

"na shiga uku!"

Da gudu tayi cikin gidan don kiran Auntyn ta ta nemi mafita kan ya dawo, garin neman gira tana shirin rasa idanu, ita da ya kamata ta nisanta su gashi tana shirin kawo kusanci tsakaninsu, ina zasu je? Me zasu je suyi? Shine kawai tambayar dake ta mata kai kawo.


Driving yake yana sauraron sheshekar kukan da fauza ke yi, husna ganin Fauza bazata yi shiru ba yasa itama ta fara kuka tana waigawa ta kalli Fauza da ta É—aura fuskanta a tafin hannunta ta kuma kwantar bisa cinyar ta tace 

"Aunty yunwa kike ji ko? Kiyi haƙuri yanzu zamu je mu ci abinci ko uncle?"


Shima Fauzan yake kallo a kai a kai ya gyaÉ—a kai yace 

"in shaa Allah Husna"


Restaurant mafi kusa ya kaisu, husna na fita ya zagaye ya buÉ—e mata kofan.


A hankali ta sanya kafa ta fito yace 

"kukan nan shi ze kosar dake ne?"


Bata tanka shi ba suka nufi ciki tana tafiya a hankali sbd cikinta da ya kama, tea me zafi ya fara ordering Allah ya sa VIP É—insu room ne so in ka shiga babu me ganinka, suna shiga ta nufi zubewa yayi saurin tarota suka karasa kan lallausan shimfidun dake wurin ya ajiyeta ta zame ta kwanta, sake kiransu yayi a landline dake wurin cikin mintuna se gasu da shayi kan ya basu ordern abincin da zasu kawo musu.


Da kanshi ya ɗagota ya miƙa mata shayin, kurbi biyu zuwa uku tayi se amai.. Da gudu ta karasa washing hand base dake wurin ta fara kwala amai, yana riƙe da kafadanta hannunshi ɗaya na shafa bayanta cikin tsantsar tausayi yake furta

"sorry! Sannu am so sorry"


Daga ka ga aman ka san na wahala da yunwa ne, bayan ta gama suka sake dawowa ya bata tea É—in ta sha, bayan ta shanye ya matsar mata da abincin da aka kawo É—in tuwo ne da miyar vegetable, yatsina fuska tayi tana kallon tuwon, husna har tayi nisa a cin nata.


"Bakya so?"

Kai ta gyaÉ—a don ita bata son tuwo, janyewa yayi ya sake kiransu tana ta Kallonshi da idanunta da suka kara girma, yadda duk tausayinsu ya kasa boyuwa a fuskanshi kaman ze yi kuka, tambayarta yayi tace rice and stew with plantain. Nan take ya faÉ—a musu suka kawo.


Zama yayi yana kallon yadda take cin abincin Dukda yunwa da take ji amma cin ba wani sauri ko hargagi a natse take kaiwa bakinta, ganin zata É—ago yasa ya É—auke kai ya fara cin tuwon da taki ci É—in.


Ba su suka dawo gidan ba don ya biya dasu sahad sun sayi abubuwa snacks masu yawa dangin su biscuit da su drinks da kayan tea su custard da oat, golden morn, coco pops ba abunda be saya ba.


Don anan ma yaga laifinshi da be ajiye musu abubuwa haka a É—aki ba, tunda daga dakinshi har na Fatima akwai snacks da drinks kuma a fridge.


Pizza da shawarma spot suka je ya sake saya musu kan suka nufi dawowa gida, duk abubuwan da yake yi É—in sede suyi hira da husna amma ita kam tak bata ce ba, tana jingine da jikin motar daga karshe ma bacci ne ya kwashe ta.


Ko da suka dawo gidan a gate ya tsaya ya cewa gate man É—in ya janye maganan da ya faÉ—a duk sadda Fauza ta nemi fita ya barta ta fita.


Daga haka suka karasa ciki, zata É—auki kayan yace ta bari.


Haka ta wuce ta Barsu da husna, bata ko kalli Fatima dake zaune a parlorn kasan ba ta haura abunta, kayanta kawai ta sauya ta kwanta akan gado sbd wani irin bacci da take ji.


Shi kam dashi da Husna suka kwashi kayan zuwa sama saida ma yayi sawu biyu, da kanshi ya shirya abubuwan inda suka kamata, kan ya kama hannun husna suka yi É—akinshi tana cin shawarma.


"Yaya..!"

Fatima ta kirashi ko kallonta be yi ba, tayi saurin binshi É—aki ya juya ya daka mata wani hargitsatsen tsawa

"get out of my sight tun baki sanya ni yin abunda zamu zo duka muna dana sani ba.."


Zata sake magana yace 

"outt!"

Ya sake daka mata tsawa, da sauri ta fice tana kuka. 


Duk abubuwan da ya kamata yayi yayi har wanka yayi ya sauya kaya kan lokacin husna tayi bacci, É—aukanta yayi ya fito zuwa dakin Fauza.


Saida ya sauya mata kaya kan ya nufi gadon da ita ya kwantar idanunshi kan Fauza dake bacci peacefully, Adu'a yayi musu kan ya fito.


A hankali ta buÉ—e idanunta ta bi bayanshi da kallo har ya maida kofa ya rufe, ajiyar zuciya ta sauke kan ta gyara kwanciyarta cikin nazarin yadda zata ci uban Fatima na abunda tayi mata...


DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuÉ—i ne.. 

Ze zo muku a Naira É—ari uku kachal #N300.

Acc no. 0545475847 

Acc name. Fatima Muhammad Gurin 

Bank name. Gt bank

Se ki tura shedar biya ta wannan layin

09039206763.

Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰


Karku sake a baku labari.



               ðŸ–¤Gureenjoh🖤

Post a Comment for "Diddigar Kaya 20"