Diddigar Kaya 19
DƘ
19
"Ayya don Allah yaaaya su bar mana ita anan pls!"
Yadda tayi maganar yasa dole ya kafeta da idanu yana kallonta, ta wani narke fuska se yaji wani abu ya mitsini zuciyarsa, ya lumshe idanunsa ya buÉ—e.
"Da nan É—in da wurinsu duk É—aya ne tunda mu ma iyayenta ne"
Ya faÉ—a yana zama, da kallo ta bishi babu laifi ta fahimci guy É—in ta ko ina ya haÉ—u, komai nasa me kyau ne, kuma ko wani irin sutura ya sa ta kan zauna daidai da tsarin hallitarsa, É—auke kai tayi ganin ze kalleta ta dubi husna tace
"zamu zauna ko husna?"
Kai yarinyar da bata wuce six years ba ta gyaÉ—a tana dariya.
Su fadyaa ma fuskansu cike da murmushi Alhamdulillah ko gobe ne yanzu kam zasu iya tafiyar su, Gaisawa suka yi da Yayan nasu, kiran sallahn azahar ya sa mazan suka fice sallah yayinda su kuma suka shige É—akinta bayan sun yi sallah fadyaa ta dube ta tace
"Fauza ba wani matsala ko?"
Fauxa ta É—an yi kasa da kai kan ta É—ago tace
"ya fadyaa dama can kin san ni da Fatima Bama shiri to dae har yanzu bata sauya zani ba, ta É“angaren shi kam ba wani matsala, matsala ta É—aya ne"
"Uhm"
Fadyaa ta faÉ—a jin ta É—an yi shiru
"me yasa nake jin Ammi ta sauya min daga wacce na sani? Meyasa bata so na zauna lafiya a gidan nan kaman yadda kowa ke buri? Duk yadda zan duba na kasa fahimtarta Ya fadyaa"
Shiru fadyaa tayi na mintuna har saida Fauza ta sake kiran sunanta ganin fuskanta ya bayyana damuwa tace
"Fauza babu abunda zan iya ce miki saide kiyi haƙuri da ita, uwa ta wuce gaban wasa amma ina me tabbatar miki ni kaina tun daga randa na amsa auren ya Faahim Ammi bata sake sakarmin fuska kaman yadda take yiwa su Fadeela ba, ban sake jin daaɗinta a matsayin uwa ba, ban sani ba ko tsanar da take yiwa Mammi da ahalinta ne ya shafemu ko yaya"
Ajiyar zuciya Fauza ta sauke gaskiya halayyar Amminta na ɗazu ya dameta, jin motsin mazan yasa suka miƙe suka fito.
Yana kallonta yace
"Fatima fa?"
Tace
"bari na duba ta"
Karasawa kofan ta tayi tayi sallama shiru tayi knocking sau biyu shiru, juyowa tayi ta kalleshi shima ita yake kallo kan ta murÉ—a kofan da nufin shiga sede a rufe yake ruff da makulli.
"Baki faÉ—a mata sakona bane?"
Tace
"ban ji motsinta bane shiyasa"
Wayanshi ya fiddo yana shirin kiran Fatiman yayinda ita kuma tayi dining ta fara kwaso abincin tana kawo su tsakiyar parlor, gabanshi ne ya faÉ—i kardae ita ce ta kwaba musu abunda zasu ci? Ai da bari ma tayi ya saya a waje tunda bata samu Fatima ba da jagwalgwalontan nan. Amma kuma ina Fatima ta tafi ba tare da ta sanar dashi ba?.
Jin wayan na shiga ya sa ya tashi ya wuce É—akin shi don kar su ji tambayar da ze yiwa Fatiman sanin ba girman shi bane taya za'a yi mace ta fita babu izinin miji?
Ita kuwa bayan ta gama ta kwaso plates da spoons da forks haÉ—e da tissue ta kawo, babban warmer me É—auke da pineapple rice É—in ta buÉ—e a take kamshi ya cika su nan ta É—auki plate zata fara serving kawai taji hannunsa mai azabar sanyi da taushi cikin nata.
A razane ta É—ago se suka HaÉ—a idanu ya kauda kai yana zare serving spoon É—in yace
"kama wani let me help with this"
Janyewa tayi tana jinta wani iri, basarwa yayi ya fara serving yana kawowa Faahim Hirar aikinshi da kusan akan zancen jirgi ne tunda shi Sojan sama ne.
Miƙewa tayi ta sauka kasa ta samo silver tray me Adon gold ta fidda zobon da ta yi ta ɗaura a kai ta jera cups ɗin jug ɗin a gefen tray ɗin kan ta dawo ta ajiye musu fadyaa na mata sannu.
Kifin ta yaye wa foil paper da ta NaÉ—esu dashi, shi kuma yana sanyawa kowa pepper chicken É—in, fadyaa na kallon su da burgewa don ba karamin kyau suka mata a taren ba.
Bismillah yayi duk suka sauko, zuciyarshi dae a tsinke kar su sha kunya ya É—ibo abincin a spoon ya kai bakinshi.
Lumshe idanu yayi se ya buÉ—e a kanta maganganun su da su Faisal É—azu a office É—in Jafar ne ya dawo mishi.
Bayan ya sauke wayanshi a sadda ya faÉ—a mata su fadyaa na zuwa Faisal yayi dariya yana cewa
"kaga mijin mata biyu cikin wata biyar ba... Kai fa kana morewa ba'a fita a angonci ba an sake dulmiyawa sabuwa dalll me sirrin ne?"
Tsaki yayi yana furta
"kanku ake ji"
Jafar yace
"kaima za'a ji naka ne a sadda ka shiga hannun Fauza"
Wani dariya yayi na baka da hankali yana dawo da kwakwalwar shi baya wurin Tunanin suffar ta da har za'a ji kanshi, a ganin da ya mata na ɗakinshi, da ganin da yayi mata randa aka kawo ta ya san kwarai tana da cikakkiyar siffa da sura, abunda kuma ke kashe shi ba ƙarya sune idanunta waenda baya jurar kallon cikinsu ba tare da yaji wani yanayi da be san menene ba, ba karya yarinya ce me cikakkiyar suffa da daradaran idanu, hotonta rungume da Zubair a elevator ne ya dawo mishi wadda ya saka shi saurin kau da Tunaninta yana sakin tsiririn tsaki.
"Ya dae angon mata biyu? Yaushe ne za'a gayyacemu cin abinci ne kaga dae tun kawo Fatima kake mana haka haka, matar Faisal har ta haihu muna gari É—aya baka bar matarka ta zo ba"
Cewar Jafar
"sannan ka manta Fatima tana rashin lafiya ne? Bari na zo na tafi kar baƙin mu su zo bana nan, amma karku damu kanku in shaa Allah nan kusa zan gayyaceku cin abincin ku maida kwalamarku Mayu kawai..."
Yana kai nan ya nufi kofa
Dariya suke yi Faisal yace
"eh mun ji, wlh ko me zaka faÉ—a se mun zo mun kwashi gara ah to"
Yana murmushin zancen ya karasa mota ya shiga ya dawo gidan.
Boyeyyen ajiyar zuciya ya sauke yana kallon yadda take ta ba husna abinci a baki suna hira da dariya da yarinyar, ta bashi tsananin mamaki guda biyu a yau
Na farko be taɓa kawo zata girka abincin da ya kai wannan daaɗi ba don ze iya rantsuwa bayan abincin mammi be taɓa cin abinci me daaɗin wannan ba, se kuma abu na biyu yadda ta tarbi su Faahim be taɓa zaton tana son mutane har ta ja su a jiki haka ba duba da yadda duk inda ta zauna se an samu hatsaniya da ita, kannenta karan kansu ba son zama kusa da ita suke ba don masifa da saurin hannu amma ji ta yadda take yi da su fadyaa ko don ta kwana biyu bata ga mutane bane?
Har suka gama cin abincin suka cika cikinsu da zobo be Daena mamaki ba, tattare kayan suke ita da fadyaa da ta mike tana taya ta suka yi kasa suka Barsu su biyu, don yaran sun biyo bayansu, wanke wanke Fauza ke yi fadyaa na daurayewa suna Æ´ar hira tsakaninsu.
Sun gama suna shirin haurawa saman kenan se ga Fatima, sake fuska tayi tace
"ya fadyaa kune a gidan ashe?"
Fadyaa tace
"eh wlh Fatima mun zo kin fita"
"eh na É—an je na ga doctor na ne, Alhamdulillah kuma da sakamako me kyau na dawo"
Fadyaa na murmushi tace
"masha Allah, Allah ya jishe mu alkhairi"
Dukda ta so Fadyan ta tambayeta menene don ciki ne da ita na sati biyu kachal amma har ta bazawa mutane tana faÉ—in a taya ta da Adu'a, wai ko Adu'a ne ba'a yiwa cikin yasa baya zama ga saurin conceiving da take dashi.
Duk haurowa suka yi kanzil be HaÉ—a su da fauza ba, ta gaida Faahim ta shiga cikin su ganin Faizan be nuna komai a fuska kaman yadda ya Rufeta da faÉ—a a waya ba.
Har suka yi la'asar a gidan still Fauza taje ta dafo musu shayi sak irin wadda mammi kan yi mishi itama kuma wurin jadda ta koya don Baba prof na matukar so kaman yadda shima yake so, be taɓa sanin ta iya something like this ba, ya sha shayin sossai don kusan abunda yake matukar kewa kenan a duk sadda aka ce yayi nisa da yola.
Se dab magrib suka rako su zasu wuce Dukda Fauza ta so su zauna se dare amma akwai inda Faahim ze je kuma ze iya kai dare sossai shiyasa ba zae Barsu yaje ya dawo ba, husna kam kin bin su tayi Fauza na murmushi tace
"yauwa Æ´ar gidana, ya fadyaa ku hado driver kawai da kayanta pls"
Duk dariya suka yi ganin yadda take ta murna daga ita har husnan, sallama suka yi musu suk fice da nufin za'a aiko mata da kayanta.
Tun a parlorn kasan Faizan ya dubi Fatima yace
"Ashe kina fita daga gidan nan ba tare da izini na ba? A iya sanina baki da lectures yau kuma na barki kina bacci"
"Yaya kayi hakuri wlh bayan fitan ka ne amai da juya ya matsa min nayi ta kiran ka kuma ban sameka ba shine na tafi ganin likita"
Ta faÉ—a a marairaice.
"Amma ya kamata ko Fauziyya ki sanarwa da zaki fita ba wai kawai ki fita kiyi tafiyar ki ba"
Ta Yi saurin cewa
"da ka dawo bata gaya maka ba? Na fa ce mata in ka dawo ta taimaka ta faÉ—a maka wallahi"
Fauza da tayi nisa a kan stairs ta dakata tare da juyowa da mamakin rantsuwar da Fatiman ke yi a kan karya, ganin kallon tuhumar da yake aika mata yasa tace
"kayi hakuri mancewa nayi"
Daga haka bata tsaya ba tayi wucewarta, a É—akinta suka yi sallah da husna nan suka shiririce a kallo tana kuma sauraran surutun husna don husna akwai aikin surutu.
A ranar dae ba'a samu an kawo mata kayanta ba se wani shirt nata dogo ta sanya mata ya kuwa zauna mata suka je kitchen suka dafa pasta ɗan kaɗan a ƙasan suka ci kan suka hauro sama zuwa ɗakin Fauza..
Har sun yi shirin kwanciya don tana sanye da pjamas fari me layi layin baƙi me yauƙi wando da riga ya zauna mata sossai kanta ba dankwali tana kara kakkabe musu shimfiɗa ya shigo da sallama.
"Oyoyo uncle"
Husna ta karasa ta rungume shi
"oyoyo babyn uncle"
Hannunta ya kama suka zauna ya É—an kalli Fauza da ta gama gyara gadon ta zauna daga baki tana wasa da nails É—inta yace
"kin ci abinci?"
Kai ta gyaÉ—a tace
"Aunty Fauza ta yi mana pasta me daaÉ—i mun ci, it was so yummy uncle kaima ka ci ka ji ko?"
Girgiza kai yayi yace
"ban ci ba baby husny amma zan ci"
"babu wata matsala ko?"
Ya jefa tambayar ga Fauza.
Kai ta girgiza tace
"babu"
Sakin hannun husna yayi yace
"OK, baby go nd sleep karki manta da Adu'a"
Tace
"ok uncle"
Da gudu taje ta hau gadon ta zauna tare da HaÉ—a hannayenta wai tana Adu'a, murmushi duk suka yi na wayon yarinyar.
Miƙewa yayi ya sanya hannunshi duka biyu cikin aljihu yace
"madam ina wayata?"
Tace
"oh, yi hakuri ina ta zuci zucin baka na mance"
Tahowa tayi wurin kujerun ta É—auka a inda ya tashi ta san ya gani ko me ya hana shi É—auka se ya sakata zuwa É—auka ta mika mai hanu da hanu oho mishi.
Karɓa kawai yayi ya juya, kaman tace mishi saida safe amma tana tsoron dizginshi har ya fice ta rage wutan ta dawo ta hau gadon ta kwanta tare da lumshe idanu tana tuna yinin ta na yau, se kuma ta tuna bata goge hotunan da ta ɗauka ba, ajiyar zuciya ta sauke tare da taɓe baki ta gyara kwanciyarta.
Shi kuwa yana komawa ɗakinshi Fatima na shiga da shirin bacci, farin takarda ta mika mai tana murmushi, karɓa yayi ya buɗe a take shima fuskanshi ta cika da murmushi Dukda be kwallafa rai ba sanin cikinta baya zama amma shima yana son ganin gudan jininshi kaman yadda kannenshi kusan duk suke da nasu.
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Allah ya sa wannan me zama ne fatee"
Tace
"in shaa Allahu Ameen"
Nan ta zauna tana gayamishi yadda Dr yace ta kula da cikin don kar a samu matsala, bayan ya gama sauraron ta ta kwanta shi kuma ya zauna tare da jingina bayanshi da gadon airpod ne a kunnenshi take ya shiga wani wuri a wayan yayi connecting ya sake komawa wani wuri ya fara duba voice recording guda biyar da ya gani.
Ba wai yana ghosting É—inta bane, kawai natsuwarshi har yanzu be kama a kanta ba yana tsoron halinta na baya sossai shiyasa ya zame mishi dole saka idanu a duk al'amuranta.
Wayansu da jadda ya fara saurara, sossai yayi murmushi jin yadda suka drama a kanshi, yadda Fauzan ta zage take ta bada jawabi akan duk abunda jadda ta faÉ—a mata an yi a gidan yayi ta bashi dariya, bayan ya gama ya saurari nata da mammi, kaÉ—an yaji darajarta a zuciyarshi jin duk ta yadda mammi ta so taji laifinshi daga gareta ta tare.
"Ashe tana da hankali"
Fatima da ta fara bacci tace
"Na'am?"
Yace
"no yi baccinki maman baby"
Murmushi tayi kan ta sake runtse idanu cikin jin daaÉ—in sunan da ya kirata dashi.
Shi kuwa cigaba da sauraron Hirar ta yayi da Baba prof,, ya san tunda baba prof yace hakan dole ze fara mata shirye shiryen makarantar babu yadda ya iya.
Hiran ta da Ammi ne na karshe da yaji shi ya saka shi yin shiru ya tafi nazari, duk yadda yake Tunanin Ammin na ƙin shi ya wuce nan, kuma shi tun tashin shi ba ze ce ga abunda ya taɓa yi mata har ta tsane shi ba, akwai shakuwa me yawa tsakanin shi da fadeela sbd da kaɗan ya girmeta, yana sonta sossai matsayin kanwarshi ya kan je sashen Ammin a lokacin don wasa da fadeela saide yana iya tunawa vividly yadda baya barin sashen se da kuka, har ya girma yayi wayau Ammi bata taɓa kaunar shi ba, gashi yanzu ya auri ƴarta.
Fita yayi yana shirin kashe wayan hannunshi ya danna gallery, Jan kalar riganta ne ya saka shi sake kallon hotunan da suke jeren, hannu ya sa ya danna É—aya, dariya ne ya kama shi ganin yadda ta tura baki wai ita nan tana style amma tayi kyau ba laifi, kallon hotunan yake yana dariya marar sauti daga karshe bayan ya gama ya girgiza kai yace
"this girl is crazy"
Ajiye wayan yayi ya kwanta tare da lumshe idanu bacci ya sureshi.
Washegari da safe aka kawowa husna kayanta, duk inda zata Fauza zata ajiye kafa husna na biye da ita, ga surutu tun tana amsawa har ta gaji, yamma likis husna tace se sun yi game.
"Toh faÉ—i wadda kike so se ayi"
Fauza ta faÉ—a don ta addabe ta da maganan game É—in nan
Husna tace
"muyi wasan É“uya Aunty"
Dankwalinta ta cire ta daurewa husnar suka hau wasan É“uya duk sun cika É—akin da hargowa Dukda su biyu ne kachal, bayan husna ta kamata da rigima da satar kallo itama aka É—aura mata ta fara laluben husna..
Sam bata ji sallamarshi ba se jin mutum tayi da hanzari ta cabki hannunshi tana cewa
"yeeeeeyyyy wa na kama...?"
Dib dariyar ta ya É—auke jin taushi da sanyin hannun ba na husna bane, da sauri ta zare kyallen dankwalin tana Kallonshi kaman yadda shima yake kallonta...
DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuɗi ne..
Ze zo muku a Naira É—ari uku kachal #N300.
Acc no. 0545475847
Acc name. Fatima Muhammad Gurin
Bank name. Gt bank
Se ki tura shedar biya ta wannan layin
09039206763.
Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰
Karku sake a baku labari.
🖤Gureenjoh🖤
Post a Comment for "Diddigar Kaya 19"