Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Diddigar Kaya 16


 DƘ


16


A natse suke saukowa jirgin, Ya fadila na riƙe da hannunta da kallo ɗaya ka mata zaka san cewa wannan ɗin amarya ce, don kwalliyarta na ban mamaki, ba fa na fuska ba lafayarta kaɗai ka kalla ze tabbatar mata da ita ɗin Amaryar babban gida ce.


Hannunta dake riÆ™e da jakanta ya bayyana lallenta me kyaun gani, chan jikin mota Faizan da Fatima ke tsaye suna jiran su har yanzu mita take mishi 


"habeeby ka san halin Fauza, wlh tsoro nake ta tarwatsa mana gida muna zaman lafiyanmu, ba wai ina ja da shawaran Baba bane amma raba mana gida shi ya fi alkhairi"


Ya ɗan kalleta sbd tausayin da take bashi don ya san fitinar Fauza babu wadda ze shaƙa dayawa irin Fatima duk yadda kuwa yayi, yace mata cikin natsuwar shi

"Na sani Fatima, amma ba mun gama maganan gida ba? Baba be lamunce min raba gida ba tunda tun tasowarku a tare kuka taso da Fauza kowaccenku kuma ba baƙuwar ɗaya ba ce, na san baki da fitina kiyi hakuri ku zauna tare har ku samu fahimta"


Ajiyar zuciya ta sauke tare da É—auke idanunta daga kanshi, se suka sauka kan su Fauza dake tahowa yadda take tafiya kaman Æ´ar sarki dole ya fusgi hankalin jama'a ga kyau tayi, abunda ta san zata nunawa Fauxa hasken fata ne kaÉ—ai ko tsawo Fauza ta É—ara ta Dukda ta fi ta shekaru, dama kuma Hausawa sun ce tsawo rabin kyau, da sauri ta maida kallonta kan Faizan se taga su yake kallo shima.


A take ranta yayi baƙi kirin, ta tabbatar ba don Fauza bata son Faizan ba da se ta saka mata hawan jini in ta gane tana mutuwar kishin shi, hannunshi ta kama ta rike wadda ya saka shi ɗauke lumsassun idanunshi daga kan su Fauzan ya maida shi kanta.


"Tunda sun taho mu shiga motar habeeby kafafuna sun fara ciwo"


Ya juya cikin kulawa da hakkin shi yace 

"so sorry, na barki a tsaye"


Motar ya buÉ—e mata ta shiga ya rufe, motar bayan wadda na abokin shi ne Faisal shi ya nunawa ya fadila suka shiga, shi kuma ya zagaye suka zauna da Fatima wadda hakan yayi mugun yi mata daaÉ—i har suka isa gida tana gayamishi abubuwan da likita yace ta dinga yi a kan É“arin da take yawan yi.


Bayan sun sauƙa a tamfatsetsen gidan nashi dake maitama da kanshi ya musu jagora zuwa ciki Dukda ya fadila da ita aka zo jeren na Fauza, a bakin kofa Fauxa ta ja ta tsaya a hankali tayi ta karanto adu'o'in da Baba prof ya umurceta ta karanta kan ta shiga gidan, bayan ta gama tayi sallama tare da sa kafar dama se ta lumshe idanu, shikenan fa ita kuma wani sabon baabin qaddara ya buɗe mata, Allah kaɗai ya san abubuwan da zasu faru a cikin wannan gida kuma Allah shi kaɗai ya san ko gidan zaman ta ne ko ba gidan zamanta bane, ko a mafarki bata kawo auren mijin Fatima ba, ba ma wannan ba kuma wai Ya Faizan har yanzu kwakwalwanta be gama ɗauka ba bare zuciya da gangar jiki.


Tamfatsetsen parlor ne wadda ya ɗauke set ɗin kujeru har biyu, ya ƙawatu sossai masha Allah, kofofi uku ne a parlorn daga tsakiya wani hadadden staircase ne golden color wadda ya tafi a karkace har zuwa sama, dukkansu shi suka bi zuwa madaidaicin parlorn dake saman wadda na kasa ya fishi girma sede ya fi na kasa haɗuwa, dining section ɗin ma kaɗai abun kallon ne haka TV stand ɗin daga ka ganshi zaka san ba karamin kuɗi ya ci ba, console har biyu ne a parlorn ɗaya a dining section ɗaya daga tsakiyar stairs in kana haurowa, kofofi huɗu ne a saman, na farko daga dama ya fadila ta buɗe suka shige da Fauza da ya kaka.


Yayinda shi kuma ya shiga na biyun yana cewa Fatima ta duba ko me aikinta ta gama abunda su ya fadilan zasu ci, ta amsa da to tana shiga nata É—akin wadda yake next to nashi, jakanta kawai ta ajiye ta fito, ta san shi. shi mutum ne me matukar son yaga nashi a gidan shi, yana son en uwanshi har bata san yadda aka yi ya rabu dasu yake ketare kasashe da sunan aiki ba, idan yaga nashi a gidan se abunda babu ne baya saya, ya dinga tambaya kuma ko akwai abunda kake bukata ayi maka, hakan ya sa itama dole take yi don bata son É“ata mishi Sam.


Kitchen na ƙasa ta je don ita kaɗai ke shiga na saman, ta samu me aikin nata ta gama duk wasu abunda ta faɗamata tayi a waya don haka a tare suka kwaso suka hauro sama dashi kwankwasa kofar tayi tare da buɗewa da sallama.


Su ba baƙin juna bane don haka tun tuni ma Fauza ta yaye lafayarta tana kwance a kan tamfatsetsen gadonta tana karewa tsaruwar ɗakin nata kallo, Baba prof da jadda sun yi kokari don su suka mata komai, dukda be so jadda ta sa hannu ba amma tace auren Fauxanta guda in bata fasa asusu ba na wa zata fasa kenan.


Mammi kuwa ita ta zubewa ya fadeela kuÉ—i akan wadda Faizan ya tura mata da umarnin Baba prof ta HaÉ—a mata lefe na gani na faÉ—a, kamshi da kyaun É—akin kaÉ—ai ze tabbatar maka da lallai nan É—in na Amarya ne, akwai set É—in kujeru akwai TV akwai kuma fridge a É—akin, daga dan lungu window kuma akwai coffee table É—aya da kujerun shi guda biyu masu kyau se karamin kofa da ze sadaka da madaidaicin balcony É—inta wadda be wuce na tsayuwar mutum É—aya ba an tare shi da wani black and gold glass. 


Kofan bayi kuma na daga kudu, duk yadda Fatima take Tunanin tsaruwar É—akinta se taga na Fauza ya fi nata don ko ba'a faÉ—a mata kudin kayan nan ba ta san ba laga laga bane Dukda natan ma masu kyau ne amma na Fauza sun fi nata, ash ne da gold É—akin haka labulayen gold da light ash, dressing mirror É—in yayi mata sossai kaman ta É—auke, idanunta kafe kan show glass na zamani wadda aka cika shi makil da wasu hadaddun turaruka wuta take rayawa a zuciyarta; lallai an nuna mata wariyar launi a nan wurin, an nuna mata kuma Fauxa ce yar gida kuma er gata.


Da kyar tayiwa su yaya fadilan sannu ta ajiye abubuwan hannunta, daidai lokacin me aiki na shigo da saura tace 

"ya fadeela ku ci abinci, bari na É—an sha magani don har yanzu cikina ciwo yake"


Cikin tausayawa suka mata sannu ko kallonta Fauza bata yi ba har ta fice.


"Fauziyya ya kamata fa a ce zuwa yanzu duk wani baƙin halinki kin baro shi chan yola kin nemi natsuwa da salama kin ɗaurawa ranki, daga Fatima har Faizan yayyunki ne suna da ikon hukunta ki da duk iskancin da zaki yi, kina ƴar fitsitsiyarki har kin san kishiya na ciwo ko sannu bazaki ce mata ba?"


FaÉ—a sossai take mata wadda wacce ake wan ta lumshe idanunta kawai tana tunanin yadda zamanta ze kasance a gidan, ko sauraron ya kakar dake faÉ—an ba yi take ba.


Bayan ta gama suka ci abinci wadda Fauziyya bata ci ba, bayi yaya kaka ta shiga don yin alwala yayinda ya fadeela ta É—ago Fauzan ta zaunar da ita.


"Fauza kar mu fara haka dake mana? Kin manta kin ce zaki zauna lafiya dasu bazaki neme su rigima ba in har ba su suka neme ki ba?"


Tace 

"ban manta ba, amma dae kin san tun da ba magana nake mata ba me don ta ce cikinta na ciwo zan buÉ—e baki in ce mata sannu bayan bata kasa dani ba? Yaya fadila don Allah ku Rabu dani in ji da abunda ya dameni, matar nan kuma ta ci darajar Jaddah wallahi"


Tana kai nan ta koma ta kwanta abunta, girgiza kai ya fadila tayi tace 

"kina da aiki wallahi, amma ba komai duk sadda kika so zaman lafiya da samun kwanciyar hankali se ki neme ni"


Daidai lokacin ya kaka ta fito, Ya fadeela ma ta shiga suka zo suka gabatar da sallah, suka ɗan kara kakkabe mata ɗakin don akwai injin shara a ciki, kuma ya fadila daman su dashi suke anfani a lokacin ne ma ta mike zaune tana kallon yadda ya fadeelan ke operating, bayan sun gama suka kara gyara mata wardrobe ɗinta da rabin shi glass ne ita kanta bata taɓa ganin ɗakin da ya burge ta irin natan ba, ta kuma sanyawa baba da jadda albarka don sun zuba kudi ba kaɗan ba a kayan nan, abunda kuwa yafi burge ta shine lefe don yadda take son gayu haka ya fadeela ta zaɓa mata isashun kayan gayu da ado.


Sun gama kenan sun kara sa turaren wuta a burner ya shigo da sallama, kwanciya tayi tare da juya baya, be ma san tana yi ba don ko inda take be kalla ba, akan kujeran É—akin ya zauna ya gaishe da ya kaka tare da mata ban gajiya, ya kuma tambayi ko akwai wani abunda suke so, suka ce babu yanzu ma shirin tafiya suke.


Se lokacin Fauza tayi saurin É—agowa 

"Ya fadeela yau Zaku tafi wai?"


Se a lokacin ya kalleta babu ɗan kwali kanta gashinta ya sha kananun kitso irin na kanuri yiri yiri ya zuba a bayan wuyan ta wasu ta baya wasu sun sauƙa a kirjinta, doguwar riganta na Holland babba ya tattare daga sharabarta sbd irin kwanciyar da tayi.


Tsaki ya kaka ta ja tace 

"yo to dama zama zamu yi? Yau zamu koma tunda mun kawo ki fatan dae Allah ya baku zaman lafiya"


Rau Rau tayi da idanu tana jiran jin amsar yaya fadeela, shi kuwa tun kallon farko da ya mata ya É—auke kanshi, ya fadeela tace 

"zamu tafi Fauxa, haka kowacce mace take hakuri a duk randa aka kawo ta É—akinta amma ba gaki ga fadyaa ba zaku ke haduwa nima kan in koma Australia zan zo kin ji?"


Kanta ta mayar kasa tana jin kewan gidansu na shiganta, duk yadda ta so tayi dauriya a sadda suka fito tayi musu rakiya kasawa tayi ta fashe da kuka tare da rungume ya fadeela, barin ta yanzu zasu yi da wannan munafukar da kuma azzalumi? Yanzu kenan kowa baya son ta? A haka zata zauna dasu su biyun su kasheta a banza? 


Ya fadeela ne ta kalleshi tace

"Ya Faizan se fa ka tayamu riƙeta"


HaÉ—e fuska yayi yace 

"ke! Ban fa son hauka me haka? Se kace wacce za'a bari a gidan yankan kai?"


A zuciyar ta tace 

"kaman ka sani wallahi babu maraba"


Ganin bazata sake fadeelan ba yasa ya taka ya sanya hannu ya zarota daga jikinta suka shiga mota driver ya ja suka fice daga gidan, suna fita ya saketa  ba tare da ya ce mata ci kanki ba ya juya ya koma, don Fatima bata fito ba wai ta sha magani kuma bacci me nauyi yake sakata shine suka ce kar a tasheta ai tayi kokari ma.


Ta jima tsaye a wurin tana share fuska kan ta juya ta nufi steps na parlorn tana dan kallon black rumfa da aka yiwa mashigar yayi kyau sossai ba kaman normal da ta saba gani ba, koda ta turo parlorn ta shigo babu kowa.


Stairs ta nufa ta fara hawa se a lokacin ta lura da dining area na parlorn kasan da daga saman stairs kana hango shi daga sama, akwai washing hand base da console a wurin shima, se kofa wadda babu tantama na kitchen ne, ba laifi gidan ya mata kyau ya burge ta.


Parlorn saman ma ba kowa se kawai ta shige ɗakinta ta maida kofa, bata kwanta kaman ɗazu ba ta hau kalle kalle da taɓe taɓe kaman ba itace ke kuka yanzu ba, babu abunda bata duba ta taɓa ba, duk da yadda take zabga kamshin humra da turaruka haka tayi ta sake fesa na kan mirror ɗinta wai tana jin kamshin su, bayan ta gama tsab ta wuce bayi nan ma tayi ta dube dubenta, ba laifi bayin ya tsaru ta kan yi mamakin toilets na hotels da suke zuwa musamman irin su transcorp sede wannan ya ci uban waenchan haɗuwa.. Ita bata san ma akwai kayan bayi ruwan gold ba se anan ɗin kusan komai ruwan gold ne Fararen kaɗan ne.


Bayan ta gama tayo fitsari dama bata sallah, ta ma yi mamakin wannan period nata be zo mata da ciwon da ya saba ba ko don sbd tashin hankalin da ta shiga ne oho.


Fitowa tayi ta cire Rigan jikinta don ya ishe ta ta duba leggings da vest ta saka abunta ta zauna ta ci tayi Nak kan ta hau gado tayi É—aiÉ—ai ta fara bacci.

(Su Fauza an samu duniya)


Chan cikin baccin ta me daaÉ—i taji ana buga kafafunta, bata da nauyin bacci hakan yasa ta mike zaune tana É“ata fuska hasken bulb da É—akin ya dauka ya tabbatar mata da dare har ya shiga bata sani ba tana baccin da ta kwana biyu bata yi ba.


Kallon Fatima da ta tashetan take yi tana jira taji me zata ce sede shiru tayi tana sake kallon Fauxan zuciyarta na hautsinewa da wani zazzafar kishin yarinyar ta ko ina.


"Lafiya zaki wani tasheni ina baccina kuma ki tsaya kina kare min kallo kaman yau kika saba ganina?"


HaÉ—e rai Fatima tayi tace 

"kul ki soma min rashin kunya daga shigowanki gidana, idan baki sani ba ya kamata ki sani da ba yanzu bane, a da ina kallonki ne kawai a matsayin shashasha wacce bata san me ke mata ciwo ba shiyasa nake kyaleki kike abunda kike so, amma a yanzu da kika amsa sunan kishiyata yanzu ne zaki sake yanke rago ki tabbatarwa da duniya cewa Fatima munafuka ce duk na baya wasa ne"


Murmushi Fauza ta saki tace 

"kishiya? Mtseww ke kika san wannan, in baki sani ba ya kamata a ce na saka wannan a bayan tosheshen kwakwalwarki, ban shigo gidan nan da niyyar komai ba don daga ke har mijin naki ba kwa gabana, amma daga sadda kika bari na harzuƙa zan nuna miki cewa kin riga kin bar kari tun ran tubani, zan zame miki kadangariyar bakin tulu se kin yi nadamar fara auren mijin kaddarana. Don haka ki kiyayeni"


Yunkurawa Fauza tayi zata miÆ™e daidai lokacin da aka turo kofa hakan ya sa Fatima yin baya baya zata faÉ—i cikin zafin nama yayi hanzarin isowa ya tarota yana aikawa  Fauza dake tsaye tsakiyar gadon bata kai ga SauÆ™ar da tayi niyya ba wani irin dead look.


*Yanzu wasan ya soma*


DIDDIGAR ƘAYA...(Mai wuyar tsincewa) wannan littafi littafin kuÉ—i ne.. 

Ze zo muku a Naira É—ari uku kachal #N300.

Acc no. 0545475847 

Acc name. Fatima Muhammad Gurin 

Bank name. Gt bank

Se ki tura shedar biya ta wannan layin

09039206763.

Yi maza ki biya naki ki sha karatu cikin kwanciyar hankali, ina me tabbatar miki bazaki taɓa nadama ba🥰


Karku sake a baku labari.



               ðŸ–¤Gureenjoh🖤

Post a Comment for "Diddigar Kaya 16"