Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Ameenatou 32

 *_Arewabooks@Mamuhgee_*

32


Abinci siddeeq yayi order tareda abubuwan dayasan Haroon zai buqata kafin ya fice ya koma dakinsa Dan sanarda JEEY ciwon Haroon gaba yakeyi sosai.


Bai samu wayar JEEY a lokacin ba Dan haka Shima abincin yaci kafin ya kira manyan ma'aikatansu da zasuyi Aiki dasu Dan Yana buqatan fara zuwa site din yaga komai ya gana da tarin ma'aikatansu masu yawan gaske kusan shine zai karbi Ragamar Aikin sbd Haroon Babu abinda zai iya.



Su Hafiz da suka shirya tsaf washe gari tinda safe suka halarci site cikin farin cikin dawowansu bakin aikinsu Dan suna samu sosai a aikin.


Kusan ma'aikata sama da hamsin Dana garin da wainda da yawansu daga wasu garin suke zuwa, manyan kuwa daga Lagos wasu suka taho wasu Kuma daga Abuja Dan haka tini site ya rayu ya cika da leburorinsu da masu kulawa dasu da masu tsari da Zanen.


Lafiyayyar tanti aka kafawa oga kwata kwata Haroon seelah da kujeran zamansa da table da duk abubuwan da zai Dan buqata a zaman da zai ringa yi idan yazo site din.


Siddeeq dayake sosai yakeda nasa ilimin da qwazon aiki tareda dubaru irin wainda duk ya koya a karkashin maigidansa na Amana JEEY Dan haka tinda suka taho shine yake fitowa site din ya gana da ma'aikata da abokan aikinsu na project din suka sake Bude sabon bayani tareda gabatar da kansu da ayyukansu tini aka fara aiki Babu wasa sbd kowa da gaskensa yake.


Saida aka kwana biyu Haroon ya koma daidai kafin ya fara fitowa site aiki zuciyarsa cikeda fatan samun nasarar abinda sukeso

Ta bangare Daya Kuma ya tsananta bincikensa akan Abinda su Dad suka Hana kansu zama da tsayi gurin nema sbd ya samo information me amfani dazai Hana Dad yafesa idan aka samu matsala a wannan aikin.



***Yar Budurwan Babbah kuwa kusan tafi su Hafiz shiga farin cikin komawansu aiki Dan kuwa tasan baturenta zata sake Gani Wanda kamanninsa suke Zane daram a idanuwa da zuciyarta Dan haka ta daga hankalin babbah da Dadah Saida suka Saka Abdul ya Dinka mata sabon uniform duk da a shekarar zata kammala Amma sbd rigima Saida aka Dinka mata sabbin uniform din.


Shi kansa Babbah da Dadah akan dole suka ringa farin cikin komawansu Hafiz aikin site sbd Ameenatoun data sakasu nuna murnan dolen.


Da daddare bayan Yaya Abdul ya shigo mata da sabbin uniform din a leda me kyau ya miqa mata Yana cewa


"Wlh safar banza ma bazan Kara Siya Miki ba sbd bansan uban me zakiyi dasu ba keda duka duka baifi wata uku ba zuwa hudu ki kammala karatun Amma shine tsaban an renamun da wayo zaa sakani dinko sabon uniform."


Hafiz Daya fito wanka Ya gama shafa Mai Yana gyara kansa da brush na brushing Kai yace


"Kafin ma aje can ka fada mata yanda ka dinko sabon uniform dinnan tana faduwa jarabawa da su zataci bikin sallah Dan Babu uban dazai mata Dinkin sallah da f9 duk cikeda takarda...."



Babbah Dake shigowa ne ya katsesa da cewa


"Ubanta ne zai Dinka mata basai kaja da Nisa ba,

Kuma faduwa jarabawan ma ai rabo ne tinda yafi Babu...


Cikin narke fuska tana kokarin ciko idanuwanta da Hawaye tace


"Babbah to ai na Maka alkawarin bazan Fadi bafa ka gaya masa,

Kuma ni Allah wanna sallan shi kadai ma nakeso yamun komai tinda ya koma aikin site...


Wurgi yayi da Brush din hannunsa Yana yowa kanta yace


"Bazaki Dena renani ba ko?

Na rantse a gidan Nan kika kawo faduwan jarabawa silipas bazan Siyaba na sallanki sedai duk me Shure.....


Katsesa dadah tayi da cewa


"Babu me shurewa Dan bakayiba."


"Ai da kin bari ya qarasa da bakinsa Muji waye ze Shure din" inji Babbah Yana karban ledan hannun Ameenatou datake nuna masa kayan babu guga.


Miqawa Hafiz kayan yayi Yana cewa Maza gama shiryawa ka goge mata ko a shagon abokincan naka me dinki ne.


Kallan ledan kayan yayi Yana sake Jin takaici na siqesa ya juya ya kalli inda Yaya Abdul yake zaune Yafara cin abincinsa hankali kwance yace


"Dena kallona Dan kasan Babu inda zani guga yanzu Kaine me abokai masu shagunan dinki"


Kanta ya dawo da kallansa zeyi magana Dadah ta bisa da rarrashinda yasan anriga an cucesa ne ake toshe masa Baki.


Jinjina Kai yayi Dan zata shiga hannunsa ne gobe tinda shine zai daukota makaranta.


Wucewa yayi daki ya qarasa shiryawa ya fito baicewa kowa komaiba ya fice Yana jinta tana masa a dawo lafiya itada Dadah yayi musu shiru ya fice Dan wankan dayayi fita zashi aka sakashi zuwa guga duk yaje ya sake hado gumi duk da Daman shine mai yi mata guga Amma dai yau din ba lokacin yinsa bane.


Bayan fitarsa Abdul ne ya fara yiwa Ameenatou din fada Babbah ya dakatar dashi da cewa yabar zancen Nan tinda dai ba fandarewa yarinyar Nan tayi na.


Da daddaren kafin ta kwanta Saida ta Jira Hafiz din ya dawo sukai karatu dayake sake nuna mata abubuwan da Bata ganeba

Anan dai ya shiririce firar da Bai tafi ba kenan.


Washe gari Abdul ne yakaita makaranta ya wuce aikinsa daga can.


Karfe biyu saura Hafiz ya iso makarantar cikin sauri sbd aikinsa Daya baro ya taho yakaita gida ya koma.


Tana ganin sun kama hanyar gida ta riqe hannunsa tana narkewa tana rokonsa suje site tinda zeyi latti kafin ya dawo kuma ai uku suke tashi Dan haka bama wani Jira zataiba zai gama su wuce gida.


Yana Jin Hakan yasan wa takeson Gani Kuma cikin sa'arta maigidan nasu Yana Nan kaman yanda ta Saka masa suna bature Suma gurin tinda dadewa suka Saka masa suna baturen.


Kaman bazaije da itaba sbd ba gurin zuwan mata bane idan ba irin masu tallan nan ba duk da an dauki nauyin abincinsu acan ake basu abinci tin farkon aikinsu Amma dai yanzu tinda aka dawo dinnan baa fara Basu ba hakanan suke siyan na masu Siya shi Kam dai iyakacinsa ruwa Basa cin abincin siyarwa waje.



Kallanta Yayi Yanajin kaman bazai tafi da ita ba Amma mum matsalarsu shine Bata iya rokon Abu su kasa Bata shi Dan haka yace


"Muje Amma tattara aikina zanyi na ajiye mu dawo gida sai gobe na Dora."


Wani kyakkyawar murmushin daya lotsa simple dinta sosai ta sake tana Jin dadi tace "Eh na yadda Yaya Hafiz dina Rabin Raina"


Harararta yayi Yana yin gaba tana biyosa tareda miqa masa Jakarta ya karba Yana kallan fuskanta kafin ya kalli ranar da ake qwalawa yasan zeyi wuya batai zazzabi ba idan ta Dade a cikin Rana Dan haka kudin aljihunsa ya taba ya ciro yaga nawa ne.

Wani shago ya tsaya ya shirya umbrella ya Bude mata yana miqa mata.


Karba tayi murmushin tsananin kaunar yayan nata datakejin sonsu fiyeda yanda suke jinta kawai dai Bata iya zama basuyi rigima ne ba Amma tasan kaunarta a zuciyoyin iyayenta da yannanta bame misaltuwa bace.


Bata tafiyan sauri Dan haka a natse suka iso site din ya Kaita inda ya Saba cewa ta zauna ta jirasa yace ta zauna ta jirasa din.


Tinda suka iso gurin taji zuciyarta tayi wani irin sanyi da farin ciki Mai nutsuwa lokaci Daya ta rasa wane irin yanayi ne ma takeji akan wannan kyakkyawan baturen Daya fita idanuwa da zuciyarta.


Zaunawa take kokarin yi a inda Hafiz ya goge mata ya wuce idanuwanta sukai kyakkyawar sauka akan Haroon Daya tinkaro inda take Kai tsaye siddeeq na gefensa Yana duba wasu takardu hakama wasu ma'aikatan na biye dashi.


Sanye yake Dan kananun kaya Ash Shima da fcap a kansa sedai Babu sunglasses a fuskansa.


Kasa zama tayi ta tsaya cak tareda zuba masa fararen idanuwansa tana Jin farin ciki na dabaibaiyeta sedai Kuma idanuwanta sai suke ganin sauye sauye a tattareda shi duk da ta Dade sosai Bata gansaba.



Kyakkyawar fuskarsa da batai hasken ta Jamaal ba ta zubawa dukkanin fararen idanuwanta tana kallan mamakinta na qaruwa zuciyarta na sake hasko kamanninsa na Baya da suka tsaya tsaf a cikin idanuwanta.


Wayar dake hannunsa ce tayi ringing Yana gap da isowa inda take ya dakata tareda dago wayar Yana ganin sunan Wanda yake Kai ya daga Kai tsaye Yana ambatar sunansa cikin sautin nutsuwa da turancinsa me dadi Shima.


Lumshe fararen idanuwanta tayi ahankali lokacinda take Jin sauyin a sautin muryansa ma,


Bude idanuwanta tayi tana sake Dorasu akansa muryansa na sake ratsa jinta,


Idanuwanta da kunnuwanta sun tabbatar mata da sauyin abubuwa akansa sedai a zuciyarta shi din daine takeson Gani da Kuma ji Dan haka sai alokacin ta saki wani kyakkyawar murmushin daya sakata Jin kunyar kanta tana rufe fuskanta da tafukan hannuwanta tana Jin tin ganin datai masa farko shine Gani mafi farin ciki dataiwa Abu.


Haroon Daya gama wayarsa ya qaraso Yana kallan abinda sukazo dubawa gurin baima lura da mutum ba saida ya qaraso daf da ita yaganta ciki mamaki ya tsaya zai kalleta daidai Nan ta janye hannuwanta daga fuskanta kyakkyawar fuskanta daukeda murmushi sedai batasan da isowansa a gurin ba Dan haka ganinsa ya Sakata yin Baya da sauri sbd firgita da mamakin data shiga me qarfin gaske.


Shi kansa bayan yayi ahankali sbd kusancin da suka samu gashi murmushin dayake fuskanta wani faduwan gaba ya sakar masa Dan baitaba samun kusanci da mace ba haka a rayuwarsaba bayan Ayesha da yayan Dad Lameenu wainda su kannensa ne ba maganar Jin komai akansu.

##MAMUH#



*_ZAFAFA BIYAR_*


1 *_Ameenatou!!_*

_Mamuhgee_


2 *_Tsutsar Nama!!_*

_Billyn Abdull_


3 *_Gudun Kaddara!!_*

_Safiya huguma_


4 *_Kwankwason Jimina!!_*

_Miss xoxo_


Guda Daya 400

Guda biyu 700

Guda uku 1k

Guda hudun 1200


*_6019473875 MUSAA ABDULLAH SAFIYAH keystone bank_*


*_ATURA SHEDA ZUWA 09166221261_*


*_MTN/VTU 09134848107_*


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din 09033181070*_


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

Post a Comment for "Ameenatou 32"