Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Zarrah 63-64


*63-64*_

 

Jinjina kai tayi zuciyarta a karye ta fara duba abinda zata buqata ta hadansu duk abinda suka buqata ta jeransu a dinning din falon ta shige dakinta ta kwanta zuciyarta na hautsinawa ba kowanne qamshi take iya dauka ba bata tashi ba sai wajen goma na dare shima amai ne taji yana taso mata ta nufi bathroom da sauri ta fara sheqashi a wahalce saboda bataci wani abincin kirki ba, tana tsaka da aman ya shigo ya qarasa bathroom din da sauri yana zuba mata sannu ta dago ta dubeshi ta kawar dakai ta miqe ta share gurin ta zagayeshi ta fice tanajin yanayin yana mata babu dadi,
Matsowa yayi gareta ya zauna gefen gadon ya kamo hannunta yace “kin kuwa ci abinci?” Numfashi ta sauke ta kada masa kai alamun eh yaja fasali yace “amma meye yasaki amai?” Qasa tayi da kanta ya dagota cikin yanayi na tausayi yace “kiyi hqr bansan meye yasa na takura miki kiyi girkin ba amma bazan qara ba tashi ki samu wani abun kisa a cikinki taso yimasa gardama ya narke mata dole ta karbi cake da yourghut din da yazo dasu ta faraci tana yatsina fuska a haka taci da dama ya taimaka mata tayi brush sannan ya miqe yace “mu kwana lfy ki kulamin da babyna”

 

Yana fita ta fada gado taja ajiyar zuciya to ko menene yasashi canza mata dazu? Girgiza kai tayi tare da cewa “Allah shine mafi sani” da wannan tunanin bacci ya qara dauketa bata farka ba sai gaf da asuba tayi raka’atainil fajri ta zauna tana lazumi lkcn asubs na qarasawa tayi ta dauki qur’ani ta fara karatunta ta jima tana karatun kafin ta ida tayi addu’o’inta ta miqe ta gyara dakinta ta bude dakin ta fito ta tarar da falon kaca² bata jurewa ganin guri da qazanta hakanan ta zage ta gyara ta nufi kitchen ta dafa Indomie ta fito.
Clear sukayi da Mimee ta fahimci hankalin mimee akan cikinta yake kuma batada niyyar kauce mata hakan yasa ita ta kauce tare da cemata “barka da safiya” bata amsa ba saima tsaki datayi murmushi Asmee tayi tace “dadina dake baki gajiya da tsaki kamar tsaka” mgnr ta daki Mimee ta juyo zatayi bala’i kafin ma ta iso ita ta shige dakinta ta kullo ta zauna tanacin Indomien ta da qwai tanajin dadinta sosai, koda ta gama bata fito ba ci gaba tayi da chat dinta har azahar ta miqe zatayi sallah wayarta ta fara ruri takai hannu ta dauka sunan Aseem tagani akai ta daga ta gaisheshi cikin ladabi yaja numfashi yace “shine kinga na fice da wuri amma ko ki tambayeni ya na tashi ko Soul?” Murmushi tayi tace “Allah bansan da wuri ka fita ba da nayi sallah bacci na koma ban tashi ba saida babynka ya tasheni”

 

Langwabar dakai yayi kamar yana gabanta ya karyar da murya yace “me kike shirya min yau?” Tace “name ba?” Murmushi yayi yace na tarbar mijinki 2 days baya tare dake yayi kewarki sosai” ajiyar zuciya tayi cikin salonta me narkar dashi tace “au dan wannan ma me kakeso na shirya maka?” Cikin jin dadi yace “komai indai daga gareki ne” dariya tayi tace “har dani?” Shima dariyar yayi yace “kedin nafi buqata dama” haka suka yita shirmensu suna sanya junansu nishadi sannan sukayi sallama ta kashe wayar yinin sur da ita ya yini a ransa gashi abubuwa sun riqeshi bai dawo gidan ba sai tara na dare Asmee tayi niyyar qunsawa Mimee yau dinnan don ta lura itama da shirinta tazo.
Tunda tayi wanka ta dau kwalliyarta ta dawo falo ta harde tana latsa wayarta abin yabawa Mimee mamaki wato yarinyar ta gama raina ta dariya tayi a ranta tace “a banza kiwon makahon kare yarinya boka yace karna damu na bari ya kusanceki qaryarki ta qare daga yau”  bude qofar yayi ya shigo idanunsa nakan Asmah ta miqe da sauri ya bude mata hannunsa ta fada qirjinsa ya rungumeta yana sunsunar wuyarta yaja wani numfashi me qarfi yace “wow miss you my favorite nayi kewar qamshin nan naki” wani farr tayi da idanunta ta harari Mimee tace “nikuma nayi Missing sweet lips dinka….”

 

Bai barta ta gama mgnr ba ya hade bakinsa da nata ya fara tsotsarta da salonsa me mantar da ita komai
Sun jima a haka suna maqale da juna ba shi da banmasan da Mimee a gurin ma hatta Asmah da tayi don gayyah ta manta da ita saida sukaji ta saki glass cup a qasa ta fara bala’i fadi takeyi “au tanan kuma kuka bullo qananun yan iska lallai ma Aseem ka qaro wulaqanci to bari kaji na fada maka indai iskanci ne wannan bai isheni gani ba saika tubeta a gabana ka zura mata burarka sannan zan yarda kun tabbata yan iska……”
Daganta hannu Asmah tayi tace “Assha Aunty Mimee kiyi qasa da muryarki kada ki qware nifa laifin ma da akayi miki banganshi ba mijinki ne mijina ne babu inda akayiwa wani shamaki da inda zai haska zuciyar mijinsa ni a son raina ma a falon nakeson ayi komi……” Hannu takai zata dauketa da mari yace “karki soma wlh” idanunta ne ya ciko da qwalla tayi kamar zatayi magana ta fasa ta shige dakinta sake kwantar dakai asmah tayi a jikinsa ya dagata cak suka shige daki daqyar ta samu ta bambareshi yayi wanka ta dauko masa abinci yaci sannan suka kwanta ranar sun gurji juna iyaka sannan sukayi bacci manne da juna.

 

Tunda suka shiga daki Mimee ke kasa kunnan taji Aseem ya wartako Asmah kamar yanda Boka yayi mata alqawari amma shiru har asuba har gari ya waye bataji komai ba hankalinta bai qara tashi ba saida taga sun fito sunata dariyarsu ta rakashi qasa ya fice, data dawo a falo ta tarar da Mimee ta riqe qugu tanata hucci koda ta shigo bata kalleta ba ta nufi dakinta ta fincikota da qarfi abin tsautsayi kawai ta kifa a akan cikinta ta saki wata qara daidai lkcn da Aseem din ya turo qofar yaganta tsaye akan Asmah daketa juyi cikin fitar hayyaci ya matsa kanta a guje ya bangaje Mimee ya dagota yana kiran sunanta ta bude idonta cikin tsananin azabar ciwo tace “way….wayyoh cikina Soul zan mut….” Dagawar da zaiyi yaga jini ke binta ya saki wata qara tare da cewa “Maryam ciki…. Ina kika daketa kashemin su kikazo kiyi dam…..” Bai iya qarasa mgnr ba yayi waje a mugun guje ya nufi asibitin cikin gurin take suka shiga bawa Asmah taimakon gaggawa sun gama fidda rai da cikin na jikinta saboda daqyar suka samu Ubangiji ya taimakesu cikin ya tsaya bayan sunyi mata daurin mahaifa saboda budewar da bakin mahaifarta yayi suka kafa masa sharruda kuwa masu tsauri akanta haka ya rinqa amsawa da to.

 

Bayan komai ya lafa ne ya fito ya nufi inda dakinsu yake yariga ya gama yanke mawa Mimee hukunci dole a wannan karon taje hutu saboda abin nata yayi yawa yasani ita tasa Hajja ta dakar masa mata sannan ita ta hada mata gobara a part dinta duk ya kawar dakai yanzu kuma ta fara bibiyar rayuwarta,
Dakin Asmah ya shiga yayi wanka ya sanya kayansa ya fito ya nufi fita ta fito da sauri da waya a hannunta tana rusa ihu tace “don girman Allah kada kayimin haka wlh na daina….” Tureta yayi yace “wlh saikin koma inda kika fito Maryam na gaji da iskancinki duk da cewa nine na baki qofa tun farko amma kin zaqe da yawa Banga uwar da yarinyar nan ta tsare miki ba kike neman rayuwarta bakisan duk wani motsinki kallonki nakeyi ba na dade da gane inda kika dosa, Maryam kada na dawo na tarar dake a gdannan igiya daya na yanke ki fadawa duk wanda zaki fadawa saboda dan dake cikin matata da kikayi qoqarin salwantarwa na datse igiyar aurena daya a kanki idan kuma na dawo naisheki a gdannan labari zai canza zakiba da labarin nace ki tafi da saki daya kinqi shiyasa na qarasa yanke biyun saboda na fahimci tafiyar zatafi miki dadi”

 

Yana gama fada ya juya yayi ficewarsa daga gdan ya koma asibitin zubewa tayi a gurin ta rinqa rusa kuka tana regretting na abun data aikata yanzun gashi tajawa kanta auren da take taqama dashi ya guntule, tana hada kayanta tana hawaye Naja’at da Hajiyan Aseem sun cuceta sune sukayita zugata ta biyosa ashe rabon shan duka ne yasata dauko qafa ta taho Boka yace Asmah zata dawo a hargitse ashe itace zata koma a hargitsen Naja’at takaita ta baro itace ta rakata gurin bokan ashe reshe ne zai juye da mujiya,
Daqyar taja akwatinta dama dashi kadai ta taho ta fita ta tsari texi ta dauketa zuwa gidan yayanta dake zaune a qasar koda matarsa ta ganta tasan da damuwa amma dake ba jituwa sukeba bata tambayeta ba.
Wasa² saida Asmah ta kwana uku a asibiti sannan taji sauqi ya gama shirya musu barin qasar Dad ya kirashi yace daganan ya wucce Sweeden akwai wata kwangila da zai kula masa da ita har tsayin 4 months yaji dadin hakan sosai duk da cewa hankalinsa yanakan Asibitinsa amma ko ba komai zai qara samun shaquwa da matarsa kuma zaiyiwa Hajja nisa yanda bazata takura masa da mgnr wata Mimee ba.

 

Hakan kuwa akayi ya dauke matarsa suka lula Sweeden acan ne Asmah taga sabuwat rayuwa Ashe da Aseem ba komai yakeyi mata ba na kulawa yanzun ne zai fara bata kulawa, babu abinda yake barinta tayi da kanta komai shine yakeyi mata gashi kullum cikinta qara girma yakeyi ya dauki so da qaunar duniya ya dorawa cikin nan a cikin lokutan ne kuma Hajjah ta kirashi take fada masa lallai ya dawo da Asmah gida ta haihu tunda yasan watan haihuwarta ya kama, yaso yayi mata musu amma yanda ta dage yasa dole badon ransa ya so ba ya dauki hutun sati uku ya shirya musu tafiya.
Tun suna jirgi takejin mararta na damqawa tana daurewa ai suna isa airport ciwo ya sako kai ta kasa taka qafarta bayanta ya riqe ta cije lebe tana girgiza kai gumi na keto mata, dagata yayi ya nufi motar Jabir da ita yana zubanta sannu ciwon ya lafa suka dauki hanyar gida kai tsaye gdan Hajja suka nufa itadai ga azabar ciwo ga faduwar gaba batasan da wacce siga hajja zata karbeta ba suna isa bata fito a mota ba ciwo ya dawo sabo maimakon a shiga agaida hajja sai sune suka fito ita da Nasmah da Aseemah ya dubeta sosai yana sharce gumi yace “Hajjah tun kwana uku EDD dinta ya qare inajin fah haihuwa zatayi….” Da gudu Hajja ta matso ta cakumeta tayi mota da ita driver yaja suka nufi asibitinsa suna dubawa kuwa sukaga a matakin qarshe take allura sukayi mata saboda ta gama jigata shine ya tsaya a kanta tana nishi yana mata sannu yana duba mintunan da suka rage mata yanajin kamar ya rage tsayinsu aikuwa lkcn na cika tayi wani nishi ta qanqameshi babyn ta danno kai kuwa qatuwa da ita tana gama fitowa suka sauke ajiyar zuciya a tare tare dayin hamdala don nuna gdyrsu ga ubangiji.

 

Tun kafin nurse din ta yankewa Babyn cibiya Hajjah ta danno dakin ana yankewa a cikin jinin ta karbeta tana hamdala wasu hawaye na zubo mata tabbas taso tayi kuskure data biyewa zuciya ta salwantar da gudan jinin danta da suka dade suna jiran zuwansa shekara da shekaru, ashe dai da gaske ne rabo meshi yakebi rabon ba a jikin matar son nata yake ba a jikin wacce ta dauka a matsayin abokiyar gaba yake yanzu da da take qoqarin rabasu ina zatakai rabon wannan sankaceciyar budurwar? Tambayace da bata da amsa a sanyaye ta miqawa Asmah dake kallonta yarinyar cikin tsananin kunyar kai tace “kiyi mata addu’a Asma’u duk abinda kika roqa mata shine zai bibiyi rayuwarta a daidai wannan lkcn qofar karbar addu’a tsakaninki da ita dama duk wanda kikasa a addu’arki a bude take”
A kunyace ta karbeta ta zubanta ido ta dago ta kalli Aseem da yaketa sharar qwallar farin ciki yanaji a ransa Asmah ta gama masa komai tayi masa murmushi ta soma yima yarinyar addu’a bayan ta gama ta miqa masa ita jikinsa na rawa ya karba ya zauna ya zubanta ido tsananin kamar yarinyar dashi abin abin masha Allah gabadaya yama manta dame zaiyiwa yarinyar kawai kallonta yake yana murmushi yana sharar Hawaye saida Asmah tace “Soul takace fah halak malak kowa tafiya zaiyi yabarka da ita please kayi mata addu’a kaji”……

 

#Comments
#Shares
#Votes

 

 

_*Oum Hairan*_
[08/07 2:21 pm] Oum Hairan: _*Zarrah*_

 

_*Fauziyya Tasiu Umar*_

 

_*Elegant Online Writers*_

 

_*Wattpad-Realfauzahtasiu*_

Post a Comment for "Zarrah 63-64"