Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Zarrah 47-48


47-48*_

 

Shigewa tayi daki ta mayar da qofarta ta kulle yayi murmushi yaci abincinsa yayi hani’an ya tashi ya shiga bathroom yayi wanka ya fito ya zauna a parlourn qasa ya kunna kallo yana kallon qwallo Mimee ta fito taci uwar kwalliya ta nemi guri kusa dashi ta zauna tana satar kallonsa mgn takeson yimasa amma yanda ya hade rai yayi kicin kicin waya ya dauka ya kira layin Asmah ta fito daga wanka tanasa rigar bacci ta gama shafe jikinta da turare dagawa tayi ta kara a kunnenta yace “ki shiga dakina ki dau komai fice system dita ki kawo min” hararar wayar tayi ta aje ta hade gashinta ta daure ta sakeshi a baya hijjab tasa ta shiga ta dauko masa system din ta nufi parlourn tana baza uban qamshi janyo qofar tayi ba qaramin faduwa gabanta yayi ba ganinsu zaune da Mimee a parlor jan qafarta tayi daqyar ta nufi parlourn tana ganin yanda Mimee ta wani tabe baki.
Rusunawa tayi ta miqansa a ladabce yakai hannu tunanin ta karba zaiyi kawai ya janyota jikinsa ya hadata a jikinsa ya tura hancinsa a wuyanta yace “bakijin zafine Baby ki cire hijjab dinnan” kallon idonsa tayi da tsananin mamaki kashenta ido yayi ya zame mata hijjab din yana kallonta gabadaya jikinta ya mutu shima jin nasa jikin yakeyi a mace yakai hannunsa saman wuyanta yace “kinyi min kyau kamar Sarauniya…..” Miqewa Mimee tayi taja uban tsaki tayi ciki tare da banko qofa ajiyar zuciya Aseem yayi ta janye jikinta ta miqe yayi saurin sake janyota ya miqe shima ya dagata cak ya nufi part dinta da ita ta janye tana qoqarin direwa ya sauketa yace.

 

“Saboda kinga inajanki a jiki zakike yimin hauka ko kauce ki bani guri shashasha kawai” jan jiki tayi ta fice daga dakin ta nufi nata ya fada gadon ya kwanta yana miqa ya rasa baqar jarabar dake damunsa akan yarinyar yakasa jurewa yau dinma so yake yajita a jikinsa

 

Juyi yayi ya janyo pillow ya rungume a ransa yanason tashi yakai mata ziyara yana kuma tsoron ta rutsashi hakanan dai ya kwana a daddafe da safe ta shirya domin zuwa practical ta shiga kitchen ta hada break tana karyawa ya shigo kitchen din bai kulata ba ya dauki cup ya hada tea ya zuba soyayyen dankali ya fita parlour ya zauna yaci ya qoshi ya miqe zai fita itama ta fito ya dubeta kawai ya watsar itanma bata saurareshi ba ta nufi daki ta dauko hijjab dinta tasa ta fito ga mamakinta taganshi tsaye tabi ta gefensa zata wucce ya riqo hannunta ya juyota ta qarfi yace “ba a koya miki gaisuwa bane a gdanku?”
Kawar dakai gefe tayi tace “inajin” baiyi tunanin amsar da zata bashi ba kenan ta janye hannunta ta fice daga parlourn nata ta shiga babban parlour gimbiyar tana zaune a dinning tanata danna bread da farfesun naman kaza Asmah ce tace mata “barka da sfy” bata amsa ba dama batasa a ranta zata amsa ba ta fice da Sauri shima ya fito ya wucceta, takaici ya cika Mimee ta miqe tace “kan ubancan wato gadi ma zanyi musu a gdan duk sun fice sun barni wlh nima ficewa zanyi” dakin ta nufa ta zaro mayafi ya fito tana kada mukulli lkcn motarsu ta fice, kowa sai huci yakeyi zuciya fal qunci sunayin parking ta bude motar ta fice.

 

Ta nufi Lab Jiddarh ta gani zaune ta miqe da Sauri tace “inata kiran wayarki bata shiga meye ya hanaki zuwa jiya” zama sukayi tace “ki bari kawai abubuwa sun faru da yawa jiya yini nayi banida lfy yau kam da sauqi” jinjina kai Jiddarh tayi tace “ai jiya naje nayiwa Inna magana tace zatasa a karbo miki magani, hamdala tayi sukaci gaba da hirarsu da aikinsu wajen hudu ya shigo yana kiranta ta miqe tanacin magani Jiddarh tabita da ido shidinma ya fahimci hakan yace “menene?” Tsuke fuska tayi tace “babu komai” murmushi yayi yace “idan kin gama ki fito mu tafi” komawa tayi ta dauko Jakarta Jiddarh tace “kinga ki saki ranki yanzu bada bane kina tare da kishiyarki komai kikayi idonta akai”
Kawar dakai tayi ta fice yana Mota yana jiranta ta shiga suka tafi suna isa ya bude ya fito ya bude mata ta fito yaya.

 

Rufe ya nufi cikin gdan ya nufi dakin Mimee yaganshi a kulle yayi qwafa wato itama ficewa tayi bude dakinsa na bangaren yayi ya shiga yayi wanka ya fito neman abinci bai samu komai ba hakan yasa shi nufar gurin Asmah ya taddata a kwance tana danne² a waya ya sanya hannu ya karbi wayar yace “ina buqatar coffee” lumshe idonta tayi ta motsa dan qaramin bakinta tace “bazan iyaba kaina yana ciwo ne” zama yayi yakai hannunsa yaji kan nata yadau zafi ya samu yanda yakeso ya miqe yace “bari nayi miki allura zakiji sauqi” saurin girgiza masa kai tayi tace “Aa gsky nikam banson Allurar nan” Wata uwar harara ya watsa mata ya fice ya dauko tarkacen magungunansa yazo yasata a gaba da kuka da komi yasanta qarfi yayi mata Allurar zazzabi ya sauko mata ya maqaleta a jikinsa yana Shafa bayanta a haka bacci ya dauketa.
Fita yayi ya samawa Kansa abinda zaici har ya gama ya tashi Mimee bata shigo ba yayi qwafa ya kulle musu bangarensu ya sake wanka ya isheta tanata bacci ya rinqa sarrafata yana lallabata har ya samu nutsuwa ya koma yana mayar da numfashi yau kam batayi masa shure² kamar baya ba daqyar yayi wanka ya kwanta bayan ya gyarata sukayi baccinsu me dadi tana maqale a jikinsa da asuba ta farka tajita maqale a jikin mutum tsoro ya kamata ta miqe da sauri ta wawuro wayarta tana qoqarin kunnnawa yakai hannu ya kunna sweech din dakin haske ya gauraye dakin idanunta ya sauka kan faffadan qirjinsa tayi saurin dauke kanta tace “meye hakan? Me kazo yimin dakina?”

 

Tashi yayi zaune yace “haka naga dama” daga haka bai kuma cewa komai ba ya miqe ya shiga bathroom yayi wanka ya dauro alwala ya fito ya dubeta yace “kiyi alwala ina jiranki” miqewa tayi tanajin yanayin ta daban ta nufi toilet din tayi wankan tsarki gabanta na faduwa ta fito sukayi sallar bayan sun idar tana azkhar tana hawaye ya zubanta ido yace “ke wai kuka baya miki wahala ne?” Yana mgnr yana matsawa jikinta ta kwantar da kanta a jikinsa ta fashe da kuka gabadaya sai tausayinta ya kamashi ya rinqa Shafa bayanta har ya samu tayi shiru yace “meyene?”
Cikin kuka tace “jiyama yazo ni na rasa yaushe yake zuwa” dubanta yayi yace “waye?” Kukanta ta qarawa qarfi tanason fada masa amma tsoro ya hanata ya rinqa tambayatta taja tayi shiru haushi ya cikashi kawai ya tashi ya fice a dakin dole ta miqe tayi shirin fita suka fice babu me cewa wani sai cika yake yana batsewa, haka lkc ya rinqa tafiya duk da Asmah bata jin dadin zaman gabar da sukeyi da Mimee haka ta biye mata shikam Aseem bai wani sauraronsu harkarsa yakeyi lkcn daya fahimci Allurar da yakewa Asmah ta fara sabawa da jikinta sai ya koma zuba mata Maganin a lemo ko a wani abinci ya takura mata sai taci ya lallaba ya lalubeta yasha ganinta idan sunje Asibiti tana kuka tana fadawa Jiddarh damuwarta dole tasa Jiddarh cire kunya tazo ta sameshi ta zayyane masa komai yayi Jim kamar me nazarin wani abu sannan ya dago yace “ok jeki kawai zansa azo ayi mata ruqiyya” taje ta fadawa Asmah sosai taji Sanyi a ranta suna komawa gida kuwa ya hauta da bala’in wai taje tana fadawa qawa sirrinta shi ta kasa fada masa itadai banda kuka babu abinda takeyi gabadayanta ta rame saboda damuwa da zullimi a qarshe dai daina cin duk abinda yabata tayi duk da baibada qofar da zata iya gane komai ba amma ta kasa aminta da hakan tana tuhumar kanta meye yasa sai ranar girkinta yake bata,

 

Shima daya fahimci ta fara saqa wani Abu a ranta saiya canza salo ya koma yimata aiki da hodar kashe jiki aikuwa ya samu yanda yakeso duk da baya kusantarta ko yaushe kuma yamai da abin na kullum duk ranar girkinta zai cita kamar babu gobe ranar girkin Mimee kuwa sai wasanni tanaji zaita jagwalgwalata amma bazata iya gane komai ba idanunta bata iya budewa har yayi bidirinsa ya fice itadai wannan Abu na taba zuciyarta sau daya tak ya taba mgn taji muryarsa sosai ta tsorata ranar amma sai zuciyarta take raya mata aljanin ne ya canza salo yake zuwar mata da muryarsa,
Ana haka Mimee ta tsiro da wani wulaqanci dokar da yasa a gidan duk wacce tayi girki ta jera a dinning kuma dole a hadu aci, da farko abin kamar abin arziqi Mimee tabi dokar itama Asmah tabi idan aka zauna cin abincinnan ta Mimee ta rinqa shafeshi da narke masa kenan itadai Asmah yar kallo take zama kuma babu ruwanta da girkinta shima haka yake biye mata sosai abin yake sosa ran Asmah wani lkcn har kuka takeyi saboda takaici cikin shekara daya da Rabi sau daya ta taba kwana a qirjin mijinta ita aikinta kawai ta girka suci idan girkinta ne ya shigo ya shige daki ya kulle tabbas itakam ta fara gajiya da wannan rayuwar gara asan nayi.

 

 

Ana haka ta farajin sauyin yanayi a jikinta ita kenan zazzabi da ciwon kai amai da tashin zuciya itakenan bata son wannan qamshin bata son wancan ga muguwar kasala batada aiki sai bacci kamar kasa da yake sun gama practical din sun koma makaranta hakanan dai take lallabawa tana shiga.
Yau tun safe ta tashi kasancewar zasuje wani research aminu Kano kuma Dole sai sun biya ta asibitinsa hakanan ta shirya ta fita da yake shi fitar wuri yayi tana zuwa suka tafi abinda ya kawosu duk wani Abu da sukeyi Jiddarh keyi mata saboda kanta dake ciwo suna gab da gamawa ya shigo turarensa ne yayi mata sallama aikuwa zuciyarta ta wani hautsino ta miqe da gudu ta nufi toilet ta rinqa kwara amai Jiddarh ta rufanta baya tana mata sannu shikam ya kasa komai sai kallonta da yakeyi har suka gyara gurin suka fito tana toshe hanci ya dubeta yace mata “sannu” ko kallonsa batayi ba wani haushinsa takeji ta fadansa bata son turaren nan nasa yakai sau uku yaqi ya daina sawa Jiddarh ce ta dubesa tace “anya yallabai Asmah ba ciki gareta ba?” Kallon juna sukayi da Sauri gabansu ya buga a tare yace “ciki kuma?” Jinjina kai Jiddarh tayi tace “eh alamomi sun nuna haka kaima ka nutsu zaka fahimta bata iyacin komai duk ta rame ta qara haske dubi yanda da taji qamshin da baiyi mata ba take kwara amai haba ai abin abin da dubane fah” gumine ya karyo masa ya zuba mata ido hawayen idonta wani nabin wani tace “aa Jiddarh wlh indai cikin mutum ne bani dashi saidai na aljani kinfasan komai Jidda meye zaki rinqa janyomin masifa har gda” sake ji yayi gumi yana karyo masa ya juya da Sauri yace “ok ina zuwa”……..

 

#Comments
#Share
#Vote

 

_*Oum Hairan*_
[24/06 7:38 pm] Oum Hairan: _*Zarrah*_

 

_*Fauziyya Tasiu Umar*_

 

_*Elegant Online Writter*_

 

_*Wattpad-Realfauzahtasiu*_

Post a Comment for "Zarrah 47-48"