Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Cheaters Club 32

 32

#SURAYYAHMS

CHEATERS CLUB...



Hannunta ya riko ahnkli jin haka yasata ta dada fashe masa da wata ragwababbiyar kuka mai nunnuke da azaban tsoronsa datakeji aranta sosai.


baice komiba Muryansa a tausashe yace hakurin me kike bani hafsa????Wani abu aka maki ne


Da sauri ta girgiza kai 

Ayanyin nuna damuwa 

Yace toh menene..?


Yanayinta na kuruciyar ce ya fito masa fili, kanta na kasa tana hawaye cikin sanyin murya tace nide Kauyen mu nakeso na koma..nide bazan iya ba.


Yace bazaki iya me ba??


Tay shiru tana digar hawayen sosai, cike da lallami yace haba hafsat gayamin mana ko kinajin kunya nane kuma...ajiyar zucya mai nauyine ya kwace mata cikin dauriya tana kukan ahnkli sam taki ta dago ta kalleshi bare su hade ido cikin shehekar kukan tace nide kayahakuri kayafemin...

Ai..ai..ai hjyace tacemin na amince amin auren Tace wai zata aura maka ni..nikuma ina tsoro dan Allah ka kaini kauyenmu saikace mata nice na gudu Aidama ana gudu agidan aure ko? 


Sunkuyar da kansa yay dan Magann nata sosai yaso yabashi dariya amma yay kamar baiji hakan aransa ba, nan ya fske yace hmmm aiDama kauyenku kikace nakaiki saina kaiki amma guduwa kuma?meyasa zaki gudu agidan aurenki


A tsorace sosai cikin sassnyr kuka Tace sabida ban dace dakai ba

Dama Kawunai na sunce mun kai ba sa'ar aurena bane Kuma ai gaskiya sukafadi tunda kana da matarka ta asali.


Muryanta harna shakurewa cikin kukan tace Kawai an cuceka ne aka bakani yar kauye, Dan Allah karka gayawa kowa Ka auri yar kauye ai duk lefinane dana amince, kayahakuri dan Allah karkaji haushina na amsane sabida kar hajiyarka taji haushina in bakason auren nima bana so..


 cikin katseta yace "toh aitunda kin amsa zaki zauna damu kece ynxu zakiyi hakuri ki zauna tare da hajiyata dan inkin tafi kauyenku ynxu zataji babu dadi ko kina son haka? Tace aa, yace toh ki tuna ummanki ta rigada ta bawa hjy amanarki kinason inkika tafi taji aranta cewa taci amanan ummanki ne?..shiru tyi cikin sheshkar kuka batace mai komi ba. Saiga mai aiki ta shigo da cutleries 

Ta gaishesa cikin girmanawa ya amsa tabi ta gaishe da hafsa din wanda tsabar tsoro yasa bata iya amsawa ba.


Dada tamke hannun tan yay bayan me aikin tafita snn yace "toh sauko kici abinci saiki sha magani.


Tacen toh ynxu shikenan saina ce ka aureni?? Dan Allah Dan Allah oga .


Bai tsaya jin shirmen nata ba Cikin datsar numfashinta Yace inkin ci abincin zan gaya maki kona aureki ko ban aureki ba share hawayenki ki sauko.


Da hakan ya lallama zuciyarta ta sauko kasa jikinta a sanyaye ta zauna bisa lallausar turkish carpet dake tskiyar dakin ta zauna a mugun takure, doguwar pink hijab ne ke jikinta tun wanda hjy ta bata tay sallah dashi Dazu bata cireshi ba, shidakansa ya sauko ya dan bubbude mata abincin ya turasu agabanta yana daga zaune agabanta ya dauko stater din ya nika mata da kyar ta amsa ta rike sabida kunya, snn yace mata wann kayan marmarine shine zaki faraci, inkin gama dashi sai kici abincin ina zuwa zanje inyi tunani..idan har naga bana son auren

Saina kaiki kauyenku yanxu amma muddin nazo naga baki cinye abincin ba toh bazan gaya maki komi ba kuma bazaki koma gida ba haka zaki cigaba da zama anan.


Ahankli ta gyada masa kai, ya dauki wayarsa ya fice a dakin tabishi da wani irin sassanyar kallo.


Tana dauke kanta a hanyar dayabi Hawayene suka zubo mata na tausayin kanta.


Gani take Har yaushe takai matsayin da zata kira kanta matarsa jiki duk qarnin talauci tana nan a matsayin jahila bakauyiya wacce bata waye ba, ji take koda ta waye bazata taɓa kamu kafar matarsa shemau a kyau da ilimi ba. She will be making a fool of her self inta zauna musu gara taje kauyen ko surfe da bara ne zatayi.


Tuna yace sai ta cinye abincin kafin yakaita kauyen yasata dauki spoon din tafara cin staters din berries ne da apples da su apricots da sauran fruits aciki ahnkli take kaiwa bakinta tana ci jin suna karama bakin nata taste yasata ta sake jikinta taci sosai. Tsabar son ta koma gida yasaka ta daure ta tattaba dukan wani abunda yake wajen

Kafin kace wani abu har jikin nata ya dan samu karfi yunwar dayake cinta ta ciki tuni ya kawar.


Jira take taga ya shigo amma sai shiru..tagumi ta rafka agaban Abinci sai can taji kamr an bude kofa daga bayanta.


Mai aikice tashigo da yanayin sakin fuska tace

Hajya tace ki saka wayann kayan kixo ki sameta akasa tanajiranki


Mikewa tay snn ta Karba kayan tace toh nagode ace mata ina zuwa.


Mai aiki tana fita ta warware kayan tagani hijabi ne milk colour da wata doguwar riga aciki 

Girmama hjyn datakyi aranta yasaka bata wani bata lkci ba ta sauya izuwa kayan ta fito fes

Snn ta kwashe duk sauran abubuwan datacin ta fito dasu waje.


Ahnya sukaci karo da mai aikin ta amsheta tana cewa hajy ai ba saikin tattara ba aikin mu ne bari naje na gyara miki dakin ..itade batace komi ba. Har mai aiki ta juya zata tafi tace anty ko zaki kaini wajen hjya?

Da sauri ta juyo tace toh bari na aje wann ina zuwa..tana kuwa aje takarcen tataho ta mata jagora izuwa babban falonsu dake kasa...


Ahnkli take karasowa har suka iso dauke da sallama abkinsu suka samesu anan azaune hajiya ta shirya itama sanye da wata lafaya lace red colour dayay mata azaban kyau tay lullumi tass dashi.


Tafiya take kanta na kallon kasa kafafunta na harhardewa agabansu har ta samu waje akasa ta zauna hajiya tace hafsatu harkin fito??

A kunyace sosai tace eh

Tace toh madallah ya kamata mutafi kinga wai yana da meeting acan Abujan shima. Batace komi ba, harsuka mike shiya fara ficewa snn ta biyo bayan hajya suka taho har waje. Kasa iya karewa gudan kallo tay tsabar nauyinsu da kuma kunyarsu dataakeji abubuwa masu dumbin yawa suna mata yawo acikin kwakwalta da zuciyarta.


tana kallo aka zuba kayayyakin hjya abayan mota, Allah Allah take kar abarta tare dashi, caraf saiga driver ya taho da babban jeep landcruiser mai tinted glass dukansu a mota daya aka wuce dasu airport mahmud na zaune agaba ita da hjya na gidan baya.


Ko wani cikakken mintina 10 basu anan ba jirginsu ya tashi dake ana yawan samun masu jigilar tafiya Abuja daga lagos..


Wajajen 12 na rana suka isa Abuja, Direct gidan mahaifyrsa dake cikin garki suka wuce, tun shigowarsu gidan hafsa take takallon gidan dan haryafi na legos dinma kyau da yelwatan fili...

Ga wasu irin fulawowi masu daukar idanu akowani kusurwa...


Suna sauka masu aiki sukazo suka tattara kayan hajya sukayi dashi ciki. Acikin wani fankacecen falo suka dan zauna aka kawo musu abun sha hajiya na mata bayanin cewa ta saki jikinta sunzo gida amma ina hanklin hafsa harynxu baya tare da ita.


Mahmud kam tuni ya barsu ya haura sama izuwa personal room dinsa na gidan dan nan din ne asalin gidan mahaifinsa na Abuja yana shiga dakinsa ya sauya dressing dinsa izuwa wata gogaggiyar cambridge grey suit data amshe dirin jikinsa ta masa kyau sabida bayan azahar ne zai wuce wajen meeting din nasa. 


yana saukowa kasa ya samu basu nan, bai tsaya nemansu bakawai ya wuce abunsa daga nan bai dawo ba harsai can da yamma bayan ya kammala meeting din nasa. 


Ya dawo kenan ya samu hjyarsa harta kammala nunawa hafsa ko ina acikin gidan har izuwa dakin baccinta Dakenan kamar a mafarki dan bakaramin tsarin yan gayu yake dashi ba, babu wani abu da babu aciki na jindadi Har tsoron sakewa adakin takeji gabaki daya tarasa meke mata dadi gani take kawai kamar rudarta akeyi bazai taɓa kasncewa ta iya zamowa mata ga oganta ba.


Duk sakewar da hjy tay ita haryanxu adar dar take iya magana da ita wani bin batama iya hade ido da ita kwata kwata. Sabida nauyi da kuma tsananin tsoron lamarin daya shigeta daga zarar ta tuno da shemau sai kaga ta firgita tana hawaye daga nan kuma saita fara tunanin komawa kauyensu dan tasan duk wuyar da zata sha acan bazai kai wanda shemau zatazo ta bata intaji cewa an aura mata mijinta ba.


Shigowarsa gidan keda wuya yasame hjyarsa a dakinta sanye da wata doguwar riga na atamfar holland dark purpl tanata kkrin kunna turaren wuta tay alwala kenan tana jiran sallahn magrib adakin nata. 


Da ssanyar sallama abakinsa ya shigo dakin ta amsa masa tana murmushi Har kasa ya tsuguna ya gaisheta snn take gaya masa yanayin da suke ciki da hafsat din..Duk dama bata fiye nunawa ba amma sosai ta fahince cewa tsananin tsoro na damun yarinyar wanda aganinta ba iyakar auren ne kawai yake firgitata ba sede in akwai wani dalili na daban wanda harsashen ta gani take kamar ko kawunanta ne suka tsoratata.


Itade tausayin hafsat din takeji har cikin kokon ranta. Tafara tambayarsa ko da akwai wani abunda yake ganin za'ayi mata dan ta samu nitsuwa ta dena firgita ta fuskance rayuwarta na gaba.


Cewa yay adan bata lokci zafin rabuwa da mahaifyar tata ya dan saketa Kafin nan su fara mata zancen makarnta, Snn yay mata alkwarin cewa a sati na gaba zaizo abujan bayan ya kammala shiryawa dukkan wani abu datake bukata.  Hajy bata masa musu ba. Dan ta lura kamar akan kafarsa yake zai koma lagos gashi bata son tana takura masa musmn ma gani datay yana kkri wajen mata biyayya sosai.


Bayan sunyi sallama da ita ya fito kai tsaye ya wuce dakin hafsa din dake dayan sashen kusa da inda nasa dakin yake


Ahnkli ya turo kofar bakinsa dauke da yar karamar sallama,a zaune ya hangota akan gado jikinta sanye da hijabinta ta takure kanta sosai agefe tabi ta lumshe idanunta cikin doguwar tunanin inda zata billawa rayuwa..


Har ya karaso daf da ita ya tsaya Batasan ma ya shigo ba harsaida yay yar gyaran murya kafin nan ta firgita ta bude idanunta ta kalleshi idanunsu cikin na juna da sauri ta kwace nata idon tay dashi kasa a cikin girmamawa sosai ta zame kasa cikin nitsuwa ta soma gaishesa da sanyin muryanta dake fitowa da kyar.


Babu yabo ba fallasa ya amsata,tare da zaunawa akan drawar gefen gadon yanata kallonta, sai can yace akwai wani abu dayake miki ciwo ne? Kanta na kasa tace "a'a..yace toh good ni zan wuce gida duk wani abunda kike bukata saiki gayama hajya zata gayamin kinji ko. 


Wani irin rauni taji ya mamayeta har ya mike zai wuce batace dashi uffan ba sanda ya kusa kaiwa kofa cikin tsareshi da sarkafaffen muryanta tace oga injiniya kace idan naci abincin zaka kaini kauyenmu kuma har naci. Muryanta na rawa rawa ta karashe maganan a tsorace 


juyowa yay daga wajen ya kalleta ganinta a durkushe kanta na kallon can kasa ajiyar zuciyane yadan kufce masa saiya dawo inda take ya zauna daga bakin gado.


Sunanta ya kira dakyar ta dago ta kalleshi yace mata ba matsala inkinje kauyen naku me zakiyi acan??? Dan shiru tay snn tace nima ban sani ba hala inyi aikin surfe 

Muna kaiwa kasuwa.

Yace toh kinfison surfen akan makaranta ko? Shiru tay bata amsa shi ba, but frm her watery eyes he has seen alot of excuses and reasons she wanted to give so badly amma nauyinshi takeji yanzu gani take kamar bazata iya memeta masa maganan kamar yadda tafadamai lkcin datake cikin halin jin yunwa ba 


Nasiha mai shiga jiki ya soma mata yace Allah yana karban Adduar bayinsane ta hanya iri iri zai iya yuwa ya amshe adduar iyayenki akanki ne daya hadaki zama akarkashin hajiyata.


wanda shi Qaddarar ne ya rabaki da abunda kikafi kauna badon kinaso ba saidan ya baki wani sabuwar rayuwa a karkashinta a matsayin surkuwanta.


..Karki manta Babban Burin iyayenki ne kiyi karatu ki zama yarinya me ilimi ki wayar ma sauran yan uwanki kai ki zama ta daban acikin mata. Shiyasa tun farko mahaifinki bai zabe kiyi surfe ba, duk dama Allah bai saka ya rayu ya sakaki a makarantar ba. Hakama ummanki...ranar kinaji tace bada son rantane bane kika fara aikatau dolene ya kamata.  Ki tuna irin tashin hanklin data shiga ciki da baki tare da ita, Yanzu babban dama ce tazo miki da zaki cika musu wann babban burin nasu kisakasu farinciki..

Ki aje maganan auren agefe tun da baki son shi, nima ban miki alkwarin komi ba sabida umarnin iyayena nake girmamawa. Duk wani abunda kikeso zan miki shi badan wani abu daya dangance alakar aure dake tsakaninmu ba sede dan na karfafa miki gwiwa wajen cika burikan iyayenki, ina shawartanki daki kwantar da hanklinki kiyi

Tunanin yadda zaki kai rayuwanki anan gaba wanda zai kasance abun alfahari awajen iyayenki a dik inda suke ynxu, karki manta kina musu adduoi..Aure nufin Allah ne bake kika tsarawa kanki ba..muma anan bamu da ikon tsara miki qaddararki na aure zai iyayuwama nan gaba ki samu wanda kike so wanda ya fini..kiyi hakuri da yanayin da kika tsinci kanki aciki kinji?.


Kuka kawai take harma batasan meyasa take kukan agabansa sosai ba..tana mutuwar son tay karatun amma kuma rashin iyayenta da kuma auren bakaramin wargaza mata tunaninta yay ba sai yanxu ta ji dama dama daya gaya mata cewa shima bai dauke auren abakin komi ba. The value of respect she have for him sosai ya karu acikin ranta,the way he talk gently with her, shawarar daya bata da yadda yake nuna mata saukin kanshi batare da kyamata ko nuna fifiko ba. Da kyar ta dedeta nitsuwarta snn tace mishi taji ta amince zata zauna domin ta cika burin iyayenta snn ta gode masa sosai.


Tausayinta yaji ya lullumesa yace mata tay tunani duk wani abunda takeso idan ya dawo Abujan next week zai tambayeta dakansa. Daga nan sukayi sallama ya wuce Airpot domin ya dawo gida har ya iso gidan nasa babu abunda yake tunawa face ita.

08060712446

*PART 2 DIN SHINE GUNDURIN ROMANSIYYA DA NISHADI TARE DA DRAMAR DAKE CIKIN LABARIN.. ME SON YA SHIGA CIKIN WANN TAFIYA YA MUN MAGANA  DOMIN YIN REGISTER PAID GRP*

08060712446

Post a Comment for "Cheaters Club 32"