Cheaters Club 30
_*CHEATERS CLUB*_
_BY SURAYYAHMS_
30.
Duk yawan Daƙikanin lokutan da halisa ta dauka acikin shiru bashi yahana jasmine tsura mata idanuwanta ba.
Ajiyar zuciyane ya kufce mata tace "Hey Halsy i am asking u a question kin min shiru, nace kin gayawa hadiza maitama kuwa?...Juyowa halisan tay ta kalleta Ahnkli snn ta sauke ajiyan xuciya fuskarta kamar na wacce bata cikin hanklinta tace.."No...bangayawa kowa ba. jasmine batace komi ba ta kura mata ido tanata kallon mood dinta daya sauya gabaki daya yadawo na damuwa.
nauyin idanun jasmine dake yawo akanta shiyasata lumshe idonta ahnkli snn ta juyo ta fuskanceta tace...
"Jasmine look,..nifa bana son nagayama kowa maganan nan ne, atleast kedin ma kawai ya isa..ni de kawai banason tashin hankaline. Atake jasmine tace but why not?Akan meye sauran bazasu san me kike ciki ba cos dis is pretty serious ba abun wasa bane..zach yana miki kwantan bauna ne halisa, kafin kizo ki hankara zai kamaki a inda bakiyi tsammani ba so, we all have to think fast..
Idanunta ta lumshe muryanta na rawa rawa nervously tace ..."Im thinking jasmine...i am seriously thinking..kawai de...kasa cigaba da maganan tay dan dede nan taji wani baqon rauni ya rufeta atake kalma ya dauke akan harshenta cak tanajin kamr ta fashe ma jasmine din da kuka.
wani irin yanayi mai gajiyarwa taji yana kkrin shigarta, idanunta a lumshe sosai cikin yanayi mai kashe jiki ta cusa hannayenta can cikin suman kanta tana calming kanta ahnkli kasar makoshinta tace "ohh jesus christ, i am sooo done..wayyo Allahna na shiga uku na!
Da sauri Jasmine ta riko hannunta sigar lallami tace baki shiga uku ba halisa,i am with u..kawai ki kira hadiza yanxu kuyi magana dan ita kadaice take da cikakken hanyar da zata binciko mana moves din boys din zach acikin kankanin lokci. Kekanki kinsan mijinta yana da iko da security system na garin nan, it wont take them a minute to figure those guys out.
Agajiye halisa ta bude lumsashun idanun nata da suka jike da ruwa aciki ta kalle jasmine da sacewar jiki tace
" ..Jasmine i knw..
Amma wann fa ba mafita bane ki yarda dani.. Dan dukan kawayena bazasu tsaya su fahimce komi ba dan suna balain jin haushin zach, sun asalin tsanarsa wallh idan na gayawa hadiza ka ita daima she will make sure tamasa wani abu mummuna, snn koda hadizar batay ba shemau da meenal fa? They dont have chill..sunajin cewa zach ya dawo kaina wallh komi zai lalace karshe kuma nice a tsakiyansu dan asirina ne zai dinga tonuwa duk duniya sai ansan past dina wanda shine dama abunda mutane dayawa suke jira akaina ayanxu.
Kafadunta jasmine ta dafa da sanyin jiki snn tace toh yanxu ido zamu zuba masa kome?
Shiru tadanyi kafin nan tace "mafitar dayane shine ta hanyar amfani da wann doctor da kika gayamin amma ai kinsan bazan iya deceiving din feelings din kowa ba, kar nazo na dan sakemai fuskane ya fara tunanin ko inasonshi ne bcos i will neva...i don't even find him atrractive..yana da banzan hali he is too boastful yana son yaba kansa da son bata sunan wasu.
Jasmine tace cmon halisa aike ba ajinsa bane ma amma ai bada son ranki bane zaki kulashi and is just for a while...abokantaka fa bazai taba zama cutarwa ba.
Da sauri muryanta kasa kasa ahanki tace jasmine nifa bana bukatan wani abokantaka...araina bana tunanin zan sake iya kula ko son wani É—a namiji aynxu,and with zach being around me i dont even knw whats gonna happen to me, raina zaina baci inna gansa a inda nake,ni bana son mu dedeta i dont even want him to apologise to me"...Adede nan hawaye masu zafi suka soma zubowa a idanunta tabi ta sunkuyar dakanta can kasa tanata kallon kasa hawayen nata na diga ahnkli.
Shiru ne ya ratsa awajen jikin jasmine yay sanyi tanami shako sheshkarta dake kkrin danneshi da karfi.
Da kyar kafin ta iya fidda kalma abkinta, muryanta na rawa ahnkli tace."i just want to move on with my life jasmine..bani da wani gata, sai wanda nake nema nabawa kaina a duniyan nan. Idan har ƙimata da mutunci ya zube kasa zai xamo kamar rayuwata ne ya kare. nide banason kwata kwata na koma cikin rayuwar zach har abada wallh banason shi yariga yafice min araina.."why is he back for me for god sake ??????? Jas baki san ya nakeji bane..
nikadai na san wahalar da nasha da zach ya rabu dani saboda nasoshi na kaunaceshi da imani na, na bashi zuciyata da dukkan yaddata, Da kyar na iya cireshi araina ynxu haka ko gama warkewa banyi ba.
Jin numfashinta na neman sauyawa yasaka tay shiru hawayenta nata saukowa ahnkli tafi minti biyar tana hawaye mai sanyi batare da tasake cewa uffan ba.
Jiki a muce jasmine ta jawota jikinta tabita rungumeta sosai acikin sigar lallashi,kukan taji ya ballo mata ta kwanta jikin hasmine tanayinshi harsaida tay kukan yawuce mata aranta kafin nan tasaketa ahankli tanamai kallon idanuwanra da sanyin murya mai cikeda tausayawa.
hannunta jasmine ta riko snn tace calm ur self Halsy i know how u feel. Kidena tunanin ko ban fahince abunda kikeji ba..,Zach is going to distract u and u dont need to allow that..I totally get it..amma kiyi hkri kinji. Karki bari hakan ya taɓa maka ranki In Allah ya yarda zaki kufcewa duk wani mummn shirinsa akanki.
gyada kai Halisan tay ahnkli Batare da tace mata komi ba tay shiruuu cikin nazari sai can bayanta dedeta nitsuwarta snn tace" iya mafitar kenan frndshp dina da doctor dinnan amma zanje nayi tunani akai sabida gaskiya bana son na cutar da zucyarsa da yaudara, Banason na zama kamar zach i just cant destroy anyones life with love or friendships.
Dafa kafadunta Jasmine tay ahnkli snn tace Kiyi tunani akai din dai...ur life matters alot too. And Selfish ppl live longer just try dis once.
Batace komi ba ta share hawayenta duka snn ta dauki ruwan sanyi a bootle tasha tace bani cigarattes din chan..mika mata jasmine tay ta dauka ta kunna tafara sha ahankli tana buso da hayakin waje cikin jan ajiyan zuciya har saida yafara distracting mind dinta daga tsoron datake ji aranta na fuskantar abunda zatay anan gaba.
Anan ta karace zamanta bata wani jima ba bacci ya dauketa, har uztaz ya kammala bincikensa ya kira wayarta, lkcin tana bacci, jasmine ne ta dauki wayan sukayi magana ta gaya masa abunda suke ciki daga nan ya wuce office ita kuma ta cigaba da abunda yake gabanta.
Ata dayan bangaren kuwa Koda engr mahmud ya tashi daga baccin huce gajiyar jiya it was late aroud 7:45am in the morning..gani yayi kamar shema'un batama shigo dubasa ba, nan ya mike daga kan gadon ya shiga bathrum don ya kimtsa ya samu ya fito dubata. yana shiga ya kunna ruwan shower akansa,blkcin babu abunda yakeji aransa face quilty consience na auren mai aikinsu hafsa da yaje yay abayan idanun matarsa dan gani kawai yake kamar bai kyauta ma shemau ba daya dauko hanyan yaudararta da karya..
Kafin ya kammala ya fito ya shirya It was already past 8am. Daga gaban mirroe yay tsaye Yana kammala taje suman kanshi da hadadden gemunsa Agurguje ya shafa ma jikinshi mai snn ya dauko jallabiyar sa ta muharramain mai kyau daya siyo a makka kalarsa brown kalar kasa
Ya zura ajikinshi ya fetsa turaren mousuf wardi yabi ya shafa oil perf na baccarat rouge 550 snn ya nufo hanyar dakin shema'u.
Tafiya yake yanata tunanin yadda zai je ya sameta abunka da wanda baisaba karya ba gabaki daya sai yakejin kansa daban. Dede bakin main room nata ya tsaya kafin nan ya danna lock press yanajin shi a kulle ya kirata awaya nan ma ba a daga ba.
Yakai 15 min yana tsaye yana knocking tanajinshi taciki bata amsa shi ba bandama tulin hararar datake bin kofar dashi.
Agogonsa ya kara dubawa ganin takwas ta wuce yasan tabbas ta farka abarci, sede Ganin kamar bazata amshi ba yasaka ya hakura ya wuce babban palonsu ya zauna tare da daukar remote ya kunne tv just for a while ya saka channel din labarai.
Ana neman 9:20 lkcin shema'un ta riga ta gama shirin ta yau kam Riga da skirt tasa mai tsada irin na silk material din nan matured rusty olive and black colour na kamfanin christian Dior. skirt din straight ne baki wuluk rigar kuma olive mai shegen tsantsi tare da Doguwar hannunsa mai adon black swvroski stonea ajiki..
nan ma ta sauke straight malaysian wig din data saka bisa kanta side by side suka zubo mata harkan kafadunta wanda ya dada bada kim kardashian white colour na fatar jikinta wata fitinanniyar classy look.
wani kalar kyau na ban mamaki yau tay dan babu wani abu waishi sanya acikin lamarinta dan haka ta rigada ta soma bida kanta inda zata samu cikar burinta na samun wani mijin mai narkakken kudi irinna kawarta hadiza ba ire iren normal millonaires kamar mijinta engr mahmud ba.
Karamin Jakarta da Takalminta na miu miu kalar rigar ta sakalasu a jikinta designs dinsu badai daukar ido ba, tsabar tsinin takalmin da igiyoyinsa aka daureshi wanda yasaka take bida takunta ahnkli kamr wata sarauniya..
Yau Ko mayafi ta kasa yafawa ajikinta da kyau don dama chan ganin darajar auren mahmud akanta yakesa in zata yi irin wannan shiga wani bin saita rike veil a hannu wani lokaci kuma tayi rolling kawai amma yanxu batama son kwata kwata dressing din da zata komoyi yay kama da na wancce take da auren wani akanta dan kar hakan yaje ya kashe mata kasuwa.
A hankali ta ke saukowa cikin catwalk mai daukar hankali sai dai cikin ranta a cunksuhe yake da haushin ganin mahmud a zaune a falo da safen nan ya kunna tv kenan yana dan kallon chanel news.
Wani irin tamke fuskarta tay snn ta cigaba da takun ta tana saukowa ahnkli qamshin turarenta na mousuf sexy shine ya soma sauyawa iskar wajen launi da dadinsa.
she knew mijinta bai da hayaniya sosai so zata dan daure ta gaishesa badan kallon haushi dayake ata aranta ba.
If not for the Adalcin da mahmud yake mata na bata duk wani abu datake so a duniya da tuni ta gayamasa cewa she is suffocating in his wife..infact ji take kamr tana cikin halin dan danasanin aurensa datayi a rayuwa.
Tun da qamshin turarensa ta bugesa ya ya dade da maida kallon sa kanta karasowa take kamr bazata taka kasa ba, Da kyar batare da ta kalleshi ba cikin shan qamshi mai tattare da azaban rigima, muryanta ciki ciki tace "ohh kaine anan? Toh sannu!
Gaisuwar datay masa kamr ansakata dole shikuwa Dressing din nata yaketa kalla a mamakance, humbly and calmy yace good mrning my wife and where did u think ure going dressing like this?..
Sama da kasa ta kalleshi cikin shan qamshi ta jefa kanta cannnnn batama kallonshi, kasar wuya tace" ina kuwa zance inba Aiki ba !!..
Shiru yy bai amsa ta ba Da idanunsa masu cike da kwarjini kawai ya kureta har saida ta soma duban kanta da kanta a dan sace, karamin tsakine ya kufce mata tace "wai meyene, ehen? me ya same dressing dina kuma mahmud kakemin irin wann kallon kauyanci? Ohh please kabarni fa na sha iska!!
Ajiyar xuciyane ya kufce masa jin hanklinsa na neman ya tashi yace shemau badai ahakaan zaki fice ba ko?..Fuskarta a dore tace ahaka kamar yaya? tsirara na fito ne ko ya... Ban gane maka ba what is wrong with u ?
Yace Hmmm babu komai"nothing is wrong with me...
kishinta yasaka ya dan kau da kansa ya cigaba da maganansa a nitse yana cewa mrs slay stylish of the 21st century kuna sanin cewa dai da aure akanku kuma Allah zai tambaye ku irin shigar da kukeyi awaje.
"Tsaki ne ya kufce ma ta cikin jin haushin maganan ahankli tace its enough dan Allah kar mifara da safen nan,.ni wannan preachy preach tales din ya isa haka
mahmud kaga i dont want my mood to get ruin by ur local mindset
And religous sentiments.
Kayi rayuwarka inyi nawa
Yace Just saying the truth...bata ma barsa ya karasa ba tace "truth,? Oh my gudness, taayi rolling masa eyes... Toh naji but im not here to listen to ur truths saboda haka ya isah zanje aiki ta juya witout wasting time zata wuceshi..ba yabo ba fallasa yace shema nima xan fita anjima wat about my breakfast?looking and Sounding annoyed ta Yarfa suman nata baya snn tace "Dama na saba maka breakfst ne?
Yace No. but amma ai babu mai yimun yau kuma kema kin sani, and since baki da lkcin saurarata agidan nan atleast u can make a simple break fast for me. Please shema'u wallh yunwa nakeji..
Tsaki ya dada kufce mata abazata Tace toh ni ina ruwa na da yunwarka mahmud, .
Ganin rainin nata yafara yawa yasa ya mike tsaye yanamai cewa Yace what? Cikin katseshi da mugun kallo Tace eh mana aitun da ka auro ni nace maka bazan na maka abinci ba kuma ka amince toh akanme zaka aiki me aikinmu garinsu snn kazo kace min ni na maka girki ayadda na gama shiryawa hakanne kakeso na shiga kitchen na maka breafst tab di jammmm.
Ransa adan harde yace but u dont have to talk to me dis way have some respect?..bata amsashi ba amma irin kallon data masa yasaka atake yaji ransa ya mugun sosuwa.
Tace stop blaming me for ur choices..Aida breakfast kakeso da baka aiketa garinsu ba sarkin diddigi da tausayi in yunwar ta isheka inna fice sai ka kirata kace ta dawo yanxu tazo ta maka breafast aikinta ne banawa ba.
Tsawa ya daka mata saida ta razana taja baya ransa a bace Yace "What is wrong with ur manners
Nine kikecewa inyunwa ta isheni in nemo wata tamin girki? Shema kina da hankli kuwa???
A tsorace da tempern sa taja baya tana huci, cikin bacin rai tace "Eh eh ehhhh na fada ka nemo wata ta maka nide baxan yi ba..Inade akan hafsa kamin tsawa...
Ransa abace Yace ya isheki haka.. tunda kin ban amsa i will try my best in dawo da ita cikin gidan nan.
Tace To saime, if u like go and marry her let her come and be cooking for u forever amma karka sake kamin tsawa akan mai aiki...bazan dauki wann rainin ba kanaji na.
Jikinta harna rawa taja tsaki ta fice agidan cikin fusho tabarshi anan atsaye da mamakinta.
Iya abunda tace na karshen ya tuna ahnkli yanamai girgiza kansa snn yayi wata kasalallen murmushi, kwafa yy aransa snn yace "Allah ya kyauta.. inade fatan zaki iya tuna wann kalaman da kika gayamin ynxu aranar da zan kawo miki abunda kike so din.
Kasa zama yay ya haura sama da tunanin lamarin shemau, gani yake kamr dan duk akan karya hanata fita da wann shigar ta haura masa ba gaira ba dalili, amma harga Allah har kunya yaji ace da mutuncisa matarsa shi ce take ficewa babu mayafi ko rufi kamar ba matar aure ba. shidai yasan ya hanata saka anything revealing and Artificial agidansa amma is like shema'u bata masan yanayi ba, he will talk amma duk a banza batta sauya abu musamman in ba ra'ayi tayi ba. ajiyan zuciya yay.."Shikam ya rasa meyasa Allah ya bashi macen da bata damu dashi ba sam sam.
..sumtimes sai yana ganin kamar laifinsa ne dayake nuna mataso sosai,wani lkcin yakan kawo ko wani abun yake mata unknowngly wanda shiyasa take purnishing dinsa ta wannan hanyar.
its almost 2yrs da suka yi aure but he just hate to admit that auren su yanzu sam ba soyyaya, in ma akwai to ba' a kulawa shi.shidai haryau baiji kamar baison matarsa ba. Kullum acikin ransa Allah yake roka ya shirya masa ita ko kuma ya sauya masa soyayyarta da mafi alheri aransa.
Cikin hakan ya tuna cewa Yau Yana da Important meeting a Abuja, nan ya jawo wata Dark colour mustard yellow shadda sabuwace kal bai taɓa sawa ba gashi taji ruwan aiki mai tsada tana zuba sheqi, nan ya suturta jikinsa dashi hade da hular data dace da kayan sosai kayan yay masa kyau bana wasa ba dan kuwa koda ya fice waje bakaramin ido ke juyowa kansa ba Shiknsa Baisan yay kama da ango ba saida ya fito fili.
Abujan kawai yay niyyar wucewa direct dacan har ya kama hanyar airpot yana driving yanata tunanin kiran shemau aransa, he wish zata kalli hotonsa daya tura mata ta gayamai wani magana me dadi koda hanklinsa zai dan kwanta yaji sanyi
Sede tuna irin yanayin da suka rabu yasaka ya cire ransa akan hakan nan hafsa din ta fado mai aransa koma ya jikin nata yake oho, bai tsaya ba ya rage gudun motar snn ya dauki wayarsa ya kira hajiyarsa kusan 6 missed calls bata daga ba, a slow ya komo driving yana dan bada lokaci yana jira ko zata kirashi amma still, sai can ya sake kira har sau uku amma shiru bata daga ba, tinani yake aransa ko hala jikin hafsat din ne yay tsanani, yana daf kusa da shiga airport saiya tuna cewa tunda ya bar gidan hajiyarsa bata nemesa a waya ba which sounds unusual, nan da nan ya juya kan motar ya dawo ciki Koba dan auren ba amananta da iyayensa suka bashi baison yay wasa dashi. Ahnkli yake tafiya hanklinsa gaba daya yabar kan shemau ya koma kansu yanata adduar Allah yasaka lafya.
Yana karasowa cikin gari agaban wata hadaddiyar five star restaurant ya tsaya da sabuwar jeep dinsa sharp sharp ya shiga yay odering chicken wings da Chops, salads da fruits staters garnished with apricots and kale. Da one park of straw berries da apples Sei ya hada da manya manyan gorunan unsweetend youghut guda biyu ana bashi ya kama hanyar gidan mahaifyarsan batare da wani bata lokci ba.
Dagata fannin vicky kuwa bata wani samu cikakken nitsuwa aranta ba face saida kaninfa nile ya kirata awaya ya rarrasheta sosai snn ya qamsar da ita cewa babu komi, duk wani abunda ya farun jiya yace mata tabarsa kawai amatsayin saɓanin fahimta tunda iyayensu ma sun ce hakan.
Nan Yay mata alkwarin zai girmama mijinta snn inyana bukatar ganinta zaizo wajen aikinta ya sameta basai ta sabawa mijinta akansa ba...
Bata ji sauki aranta ba inbanda wayar da sukayi da nile daya kwantar mata da hanklinta sosai.Yana mutuwar son
Yar uwansa to the extent that bai barta ta gane nashi bacin ran ba kawai ya maida maganan ya dawo kamar bakomi ba dan yasan dolene itace zatafi kowa cutuwa acikin lamarin nan.
Shibaisan wani mummunam hali femi ba amma Tunda mahaifinsa yay masa fada jiya akansa ya soma fahimtar cewa kamr femi yana amfani da kudinsa ne wajen kare kansa agaban iyayensu shiyasa aransa yay alkwarin cewa shima sai zama garkuwa wa yar uwansa ayayinda kowa yake ganin kamr itace mai laefi. Besides ji yake aransa kamr all this thing is happening bcos of him, kenan ya zama masa kamr dolene yay supporting dinta cos he just cant let her get sad koma yayane.
Kusan awa biyu suna waya yanata lallashinta har ya dawo yana sakata dariya da jokes dinsa masu sanyi masu shiga rai, har saida ya tabbata tacire abun aranta kafin nan ya kyaleta ya shirya yaje wajen project dinsa.
Suna kammala waya da nile saiga kirar shema'u tana daukawa shemau ta sanar da ita cewa zasu raka hadiza airpot tafiyar gaggawace ankira ance mata mijinta ya fadi uncounsious awajen meeting gashi meenal da halisa are not reachable duk wayoyinsu baya shiga.
Jin hakan yasaka ta diro dagakan gadonta ta shige toilet agaggauce tay wanka ta zo tafara shirya kanta agaban madubi duk yadda taso tay sauri ta kasa sabida yadda fuskanta ya haura sosai adan dole ta nitsu ta shafa concealers akai domin ta boyesu.
Kafin ta gama shirin saiga mai aikinta ta shigo wajen, tace madam u have a visitor
Downstairs tace tanata kiran layinka baya shiga.
Bata ko amsa ba saiga kiran shema'un ya shigo.
Daukawa tay at same time tana kkrn saka botton din gaban rigarta agaggauce.."Hey babe kina ina ?? Gani nan Nagama shiryawa.
Shema'u tace finally..toh ki sauko ina waje ina jiranki abeg hurry up vicky, Agaggauce tace okay snn ta katse wayar ta jawo hadadden white sandal booth dinta ta zura akafarta kafin nan harmai aiki ta gama hada mata kominta acikin jakarta.
Karba tay tana mai cewa
"Take care of the house suzana, Banajin zan dawo da wuri ina da aiki.
Mai aiki tace yes maa
Bata amsata ba sabida tsarguwa datayi da irin kallon da mai aikin take mata duk atunaninta hala fuskartan haryanzu yana nuna alaman marin da kuma kukan data kwana tanayi jiyane.
Duk dama tay balain kyau anma aranta she is really really insecured of her self dan bata taɓajin kanta a tsarge kamar nayau ba.
bude wani scrolls tayi ta dauki wata sharbaben farar gilashi ta kamfanin rayban ta kimashi akan fuskrta snn tafice da sauri sauri.
Tunda ta fito bata kalle kowa ba bare ta amsa wani gaisuwa, Daga cikin mota shema'u take kallon fitowartan harta karaso wajenta bata iya daukevidanunta akanta ba, Slim fit pper red suit ta saka mai faffadar wando Da wani irin white shoes mai dan karan kyau dede da kalar yar cikin suit dinta daya kenan fari kal shima kuma shara shara....
dan haurawan da fuskartan yay a sakamakon marin da femi yay mata yasaka tay kwalliya mai dan yawa danta rufe wajen dake bata saba ba sao kwalliyar yay mata kyau sai ta fito daban bakamar kullum.
A tsarge ta shiga motar shema'un gani take kamr duk zasu gane halin datake ciki, sede Tana zama acikin motar shemau ta kare mata kallo ganin irin kyan datay yasa tay murmushi snn tace Damnnnn gaskiya yau ina taya prince femi kishi cos what is this vicky?
Rau da ido vicky tay kirjinta na dan bugawa tace 'what?..menayi.
Dariya shemau tay tare da kunne motar tana cewa "girl i aint gonna lie u look super doper wani yaganki ahaka ai zaice ure just 20. U look so gorgeous..hummmmm
Murmushi vicky tay cikin sauke boyayyaen Ajiyar zuciya na relive, snn tace thanks my lady.. kema ai seki yi ahnkli da wann irin wankar dan bazan iyama gayu bayanin cewa ke matar wani bace dan bazasu yadda ba..
Atare sukayi dariya ayayinda shemau ta kama hanya dasu izuwa inda hadizan take tana driving tana jan vicky da hira dan sosai taji dadin cemata da akayi batay kama da matar aure ba dan dama babban burinta kenan yanxu.
Murza stiring motartan take cikin shakar santin hirar tana dariya tana cewa Ai baku ga komi ba vicky, am just getting started.
Vicky tace is a lie ooo, E get why..kode kode engr yafara hango wasu babes dinne
Dariya shemau tay mai karfi snn tace Allah ya sawwake,..yama isa ne ya kalle wata bayan ni? Shin akwai wata warce ta isa ta goga kafada danine ma, hahaha phew..I just want to be a queen that i am..ina son sauran mata akaina su gane cewa aure bashine karshen rayuwar su ba kin gane. I gat to Dress to kill meye amfanin duniyar inbakaji dadinsa ba, Dan haka get ready to see me slayyyy.
Vicky tay dariya tace team slay mamas
Shemau tana shawo kwanan anguwan tun bata amsa vicky ba sai kiiiiiiiiiiiiiiiii sukaji antaka break da karfi saida dukansu suka razana suka firfito da idanunsu waje.
Wani hadadden bakar sport car ne sabuwa ta tsare musu gabansu a acikin yanayin ganganci babu ma ta inda zasu wuce batare da sun koma da baya ba.
Tun daga cikin motar Vicky ta kare ma motar kallo sama da kasa ahankli ta kyabe baki ganin ferrari ce sabuwar fitowa kimanin milliyoyin dala na amurka .
Ran shemau daya riga da ya hatsale a fusace ta buga kan stiring benz dinta yay kara pim pim pim pimmmmm, and who the heck is this bitch.
Vicky tace bana tsamamnin mace ce aciki hala namiji .
Shema'u tace sam namiji bazaiyi tuki haka ba, inba mace bane waye zaina tukin ganganci haka acikin anguwa.
Sunfi minti biyar suna danna ma mei motar horn amma ba'a fito ba sann bai basu hanya ba
Gashi bawajen tsagawa sedei in zasu koma baya su bada hanya which aganinsu hakan bazai taba yuwa ba.
Da alama kowa na ji dakansa.
Shemau already tay zagin duniyan nan ta dauka irin karuwan slay queens din nan ne masu dauko manyan motocin samarikansu yan siyasa suna baqu da shi agari.
Karuwae banza jaka Halama bata iya tuka motar bane ya tsaya mata anan..mtsw
Aikuwa inde bazata mata ba saidai mu kwana anan dan wallh bazan matsa mata ba.
Tana kan masifarta vicky ta saukar da nata girman kan ta sauko kasa ranta a mugun harde tana jan tsaki tanufi gaban motar direct cikin wata mayyar cat walk daya jefa yaron acikin wani irin yanayin da shikansa bai isa yace zai iya fassarashi ba dan tundaga cikin kwaryan kwakwalrsa yakejin sonta na fisgarsa with sparks kamar anjonasa da wutar lantarki.
Jikinshi take ya dau rawa har izuwa tafin kafarsa yakasa yin komi ya tsurawa vickyn ido harta karaso gaban motar snn ta kwankwasa masa glass, kansa ya zamar a kan seat din tareda komawa da baya ahnkli ya jingina amarairace yana sauke ajiyan zuciya batare da yasan yay hakan ba, jin dadaddar muryanta na tsagawa harta zuciyarsa yasashi lumshe ido ahkli jin tana cewa"..Hello..Excuse me
Ure on the way...u got to fuck off.. saida ta fada kamar sau biyar dede inda muryan nata ya qamsheshi kafin nan ya danna wani abu ajikin kofar ahnkli glass din ke sauka dakansa kasa
Lokcin har shemau ta sauko itama ranta abace sosai sun kafe motar da ido suna jiran glass din ya gama sauka suga wata tantiriyace aciki.
Ko rabi da sauka Glass din baikai ba kayden yay tozali da abar kaunarsa kuma muradin ransa wato vicky williams.
Akallon da sukama juna na farko saida wani quick shocking sukaji me mugun karfi, kyawanwan idanunsa ya zuba anata tabi ta lumshe nata idon ta bude atake jinwani abu yana tsarga mata azuciyarta. wani irin maitan kallo yay ma kwayar idanunta dake sarkafe anashi sending her chills all over her body... wani irin zutttt zutt taji na tsarga mata har cikin brain nata atake ta kwace idanunta da karfi anashi cikin sauke ajiyan zuciya mai zafi tare da dauke kanta akansa da sauri.
Itakanta bata san me taji datagansa ba kirjinta kawai ta dafe ta juya tana kallon shemau
Tace "Oh my gudness shema'u its not even a bitch its one mother fucker who can't drive.
Itako shemau mamakine ya rufe mata baki dan dik tunaninta mace ce aciki
Ganin kayden din tay na farko sai kuma tayi sanyi ganinsa saurayi danye sharaf wanda alaman hutu da nera ya gama ratsamai fatar jiki.
Daga gefenta vicky take satar kallonsa cos he is fucking handsome like filthy gorge and cute, skin colour shine iya abunda ya rabashi da kaninta nile wajen tsayi da dirin jikin mai matukar daukar hankli.
Dadaddar sanyi da qamshin turaren da ke fitowa acikin motarsa suke shaka ta waje kamar zai sakasu bacci.
..Gashi nan chokolate skin ne amma irin kyau mai sanyi din nan ne ke tafe da yanayinsa mai sace gabobin jiki da kuma narkarwa, ga wata cool smiles dake zaune daram akan dan karamin bakinsa dats so soft and socculent yashafa gloss akai dake nuna alaman tsaftarsa da nitsuwarsa, daga ganinsa kaga wanda hanklinsa yakenan akwance baida wata damuwa a duniyar nan.
Acikin sanyin jiki da saibi yabude kofar ferrari sport car dinsa ya sauko kasa dukansu suka bishi da kallon tsaf daga sama har kasa dan bai ishe su kallo ba.
Jan riga ya saka da bakin wando wanda basai an gayama maka ba kasan original ne daga can kamfanin parco rabbane koda ya sauka kasa jingina da jikin motarsa kawai yay baice musu komi ba ya tsura musu gajiyayyun idanunsa wanda yay kamar baiya kallonsu sede rabi hanklinsa da brain dinsa nagakan vicky ne data tsareshi da wata iriyar muguwar harara.
Smirks ne ya kufce a fuskar shema'u dan haka kawai taji jinintaya hadu dashi, . a nitse take kallonsa, kafin nan tace excuse me young man, yana murnushi ya kalleta tace i hope u knw ure on our way..?
Tun bata karasa ba vicky dake hararsa tace "Now get in ur car and move back... okay?
Ahankli yace okay.
But i can't move..
Shema'u Tace why?
yace i just cant reverse back.
Vicky tace"Are u insane??
Ure driving a car and u can't reverse?...Where are ur parents kid.
Yace hey am not a kid .
Ranta aharde in a very bossy tone tace
"Then drive.
YiYay kamar baijita ba Saida ya lumshe idonsa ya bude a mugun kasale snn yace i told you.
tsawa ta daka mai
"you told me what kid?
Tun Kafin ya amsata tarufesa da fada.."Baka da Hankine ana maka magana kana kallon mutane cikin ido did i look like ur mate?
Cikin tsareta shema'u tace vicky pls calm down yaro ne fa karkina dakamai tsawa.
Ahatsale vicky tace a'a shema'u zamu tsaya ne yaro yana rena mana hankali waibaisan ya ake reversing mota ba toh Uban wa ya bashi motar ahaka? I can't tolerate this shit. ...jiranmu fa hadiza takeyi and these kids of now adays yan iska ne ba a lallabasu kawai yaja akwalar motarsa anan yabamu hanya jare.
Masifa take amma batasan dadin muryan nata yake ji har cikin kokon ransa ba...
shidai baicewa komi musammn ma daya gane cewa sakalcin dayake baza musu acikin nitsuwa shiyake dada hatsalata, shemau kuwa burgeta yaron yay har cikin kokon ranta dan ita fa duk inda ake harkan kyau, aji da nuna nera a fili tanason hakan aranta.
Abu kamar wasa Hakanan sukayi sukayi dashi yabar kan hanya amma yaki sam yace bai iya reversing ba, sai rigima da shagwaba dayake ma vicky mai ban dariya har da ce mata "mama" "mummy".. har kiris ya rage vickyn ta wankamai mari ta dinga mai masifa kamar wani danta shiko dadin hakan yakeji aransa bana wasa ba.
"I dont blame u i blame ur parents"..go and kill ur self zaka gane, da uwar katon kanka awajen kamar zuma rock.
Intay masifar sai ya sunkuyar dakansa kasa yay karamin dariya inya dago kuma saiya fuske ya marairace mata fuska sai kuma yaita kallonta kamar zai hadiyeta.
Karshe dai shema'u ce ta amshi key din motarsa zata jaaaa tamaida shi baya domin su samu hanyar wucewa tana shiga key din ya ki aiki cos bata iya operating irin wnn cars din ba dake bata san manual din latest edition na ferrari sports cars ba, hakanan ta dinga rokon vicky dake tasan mijinta femi yana iya siyar duk wata sabuwar sport car agidan nasu sede in bai fito ba, hakanan itama taki firrrrrr tace bazata shiga motarsa ba, ahaka saida suka É“ata wani 20 mins awajen dakyar ta amince tana shiga motar shima yabita ya shiga shima ya zauna abunshi ko kallonsa batay ba tajashi baya da mugun gudu acikin yanayin tukin ganganci saida ya raxana ya kureta da ido.
Tana jefashi gefe ta bude motar tafice yanata kallon bracelat dinta daya zame kasa acikin motar nasa baice mata uffan ba. Dadi yakeji aransa kamar shaukin zai kasheshi jin qamshin turarenta da ya cika masa cikin motarsa bana wasa ba, Suna barin wajen ya tsuguna ya dau bracelet din ya saka a aljihunsa yana murmushi ahnkli yaja motarsa ya dau hanyar gidansu hanklin sa akwance
Bakaramin dariyar vicky shemau tay ba ayayinda tke memeta mata irin masifar data zubawa yaron ba.
Tana dariyar sosai har tana shakewa Tace habawa vicky u no get chilll ashe?Ni wallhy bansan kina da wann halin african mummys din ba duk kinbi kin balbale yaro da masifa kamar ke kika haifesa u no even see as the boy fineeee kamar in sace shi
Hade rai vickyn tay tare da jan tsaki tace Abeg abeg forget dat part shema wann ba abun dariya bane the boy is freaking annoying kiga wani rigamar dayakeyi kuma yasan bai iya tuka mota ba zai dauko motar gidansu yahau kan hanya dashi. Inyaje ya kashe mutane fa...ko ya kashe kansa. Shirmen banza kawai i do blame deir parents da suke barinsu suna mana yawo agari da motocin gidansu da sunan nuna musu gata wawan yaro kawai.
Banda dariya babu abunda shemau takeyi
Cikin dariyar tace Dis Adorable angel cannot die ooo he is too cute abeg. Kiga jikinshi so fresh..so young.
Vicky ta ciza yatsarta gwanin ban dariya snn tace naso da wanka masa mari nayi wallah kiji fa harda cemin _"i am sorry mumy"_ ..jesus ..kai kai saiyanzu ma abun yamin zafi..shema shebi u told me i look young and beautiful today amma meyasa dan iskan yaron nan zai karemin kallon snn yace min mumy? Nayi kama da uwarsa ce????
Tuntsirewa da dariya Shema'u tayi tana cewa sugar mummy mana ke kuwa ki gane mana duk ya rude agabanki wallh
har suka isa inda hadiza take bata dena tsokanar vicky akan mummy din da kayden ya kirata dashi ba.
Suna isa wajen hadizan suka sameta harta kammala shiri tana jiransu basu wani bata lkci ba suka rakata airport suna masu mara mata baya harsaida ta bar kasan kafin nan suka rabu kowacce ta wuce inda zataje
**************
Baccin awa biyu masu kyau halisa ta samu agidan jasmine kafin nan ta kira uztaz yazo ya dauketa yakaita gida.
Tun ahanyar har isowarta babu Abunda take tunani face yadda zata soma playing fake friendship da Dr khalid dan harga Allah bata jin shaawar keeping company na wani namiji arayuwarta musammn ma da sunan soyayya ko abokantaka.
Bata wani yanke hukunci ba harsaida tay wanka ta sauya suturarta izuwa kaya marasa nauyi snn ta samu abinci tanaci ahankli har ta amince da maganan aranta.
Tabarta ta kunna tana zuka a brain dinta cewa take She have to do this badan son ranta ba sedan ta rabu dajin fargaban dawowar zach rayuwarta na har abada.
Wani dn karamin mac book dinta ta dauka tana daddanawa can ta bude sabo kuma boyayyen instgram acct dats anynomous ta zuba wasu mayun hotunanta na modeling akai wnda duk wnd ya kalla saiya sake kalla.
Bayan ta kammala nn taje tay searching din acct din Dr khalid din ta dudduba contents dinsa snn tay liking hotonansa dayake posting kamar guda biyar snn ta sauka.
Tana barin wajen ta koma daki sama sama tay kwalliya snn ta nemi wani simple material gown baki ta saka ajikinta tay rolling kanta da veil kalar gown din da wani hadadden flat shoe na kamfanin zara ta dauki side bag dinshi dan karami ta rataya ta fetsa turare masu qamshi.
Kai tsaye ta wuce gaban wata highlander jeep dinta ta kunna bata tsaya ko ina ba sai offishin aminiyarta meenal talba
Ahnkli take takawa tana zukar tabarta batare da ta kalle kowa ba harta shige ciki, agaban new sectarynta ta dakata bayabo ba fallasa tace mata tagayawa meenal din ta iso, mikewa sctaryn tay ta shiga after like 3 min ta fito tace meenal ta bada umarni nan aka kawota ciki.
Juyawa halisa tay tanata kallon sectaryn ganin irin kallon datake mata kamr tasanta.. tana ficewa ta karaso ciki, Suna hade ido Wani irin rungumar halisar meenal tayi kamar na wanda sukayi watanni basuga juna ba.
Tace wayoo Allah halsy bakisan dadin danaji dana ganki yanxu ba dan tsabar damuwa kaina ciwo yakemin, i badly need sumone to talk to.
Please Have a seat.
Halisa batace uffan ba taja kujera ta zauna suka gaisa sama sama.
Meenal na Allah Allah tafara kawo mata korafi akan mijinta cikin katseta halisa tace mata nikam haryanxu baku samu fadila bane?...
Atake meenal ta yatsine fuska Kamar wanda aka ambato mata kashi murya ciki ciki tace waye kuma fadila????
Rau kawai halisa tay da ido bata amsata ba.
Tace ohhh u mean that prostitute of a girl??
Halisa ta hade rai tace ohh please meenal kidena fadin wann kalman mana....Inkin zageta da wann kalman tamkar kin zageni ne..
Ta bata rai tace Halisa kidena hada kanki da wancan kazamar yarinyar fisabilallh wai meye damuwarki da ita.
A nitse Halisa tace Babu..i just want to knw what happen to her..haba meenal. Shekara nawa Yarinyar nan tana miki aiki since when she is 15yrs fa. Bai kamata ace ta bace kuma kun mance da zancenta ba she is qualify to be call a family
Tsaye meenal ta miƙe cikin bacin rai tace
"NOT MY FAMILY halisa
"Not my family, i reject it with every thing within me... gosh...Allah ya kiyaye.. mtchewwwwww.
Mikewa halisan tay cikin sauke muryanta kasa kasa ta dafa kafadunta cikin sanyin jiki.
Snn tace Meenal nifa ba fada nazo muyi dake ba
Nazo ne naji damuwarki yar uwata. And is only fair idan nagaya miki abunda yake raina kinsan bana iya boye miki komi
Turo baki gaba meenal tay ta juyo tana kallon halisar.."Fadilar damuwata ce da zaku tambayeni daga zuwanki haba halisa..i have tons of matsala da aure na baki damu akai ba sai akan wata yar iska jaka da bakisanta bama.
Cikin lumshe ido da budewa halisa tace toh naji,just tell me what happen to her atleast saina dena damunki.
Ajiyan xuciya meenal ta sauke badan taso ba saidan tasan halisa bazata taɓa saurarar damuwanta inbata gaya mata komi akan bacewar fadila ba.
Tace toh shikenan ai sai mu zauna ko.
Suna zama saiga sabuwar sectarinta rukayya ta shigo da wasu files a hannunta tana sum sum alaman itama tsoron meenal din takeji...
tun shigowarta office din meenal din take bin tada wasu irin mugayen kallo harta kammala abunda zatay ta fita a office bata dena binta da tsaki ba
halisa tay kwafa tana mamakin meenal ahankli tace wann din kuma me tamiki haka.
Tace kedai nifa basa burgeni ne..they are all bunch of idiots basa son aiki sai rigima kwakwala ba komi aciki.
Halisa tace hmm
Okay..inajinki ina fadilar take.
Tace halisa nifa bansan inda take ba. Toh uwarta ma ta nemeta ta rasata sainine zan sameta?
Halisa tace you mean she is lost for real...no it can't be...bakida wani clue akan inda zataje ne atleast ai ko mummynki zata iya gane inda zata iya zuwa since itace ta kawo ta lagos din nan in the first place
Cike da shirya karya Meenal tace Halisa yarinyar nan fa first class yar iska ce kece kawai kike kallonta mutuniyar kirki..wallh mun nemeta ask around kitambayi mumyna zakiji..karkiga ma wahalar da mummyna tasha itace kiran gidansu akauye kullum to uwartan ma aicewa tay mudena damuwa zai iya yuwa tawuce gidan wani saurayinta ko tamabar kasan nan da wani yo meyasa zan sama kaina ciwon zuciya akanta. Please and please kibar ni da zancenta hakanan ni iya abunda na sani kenan.
Halisa tace toh shikenan tunda kince haka Amma banso hakan ya kasance da fadila ba. I mean she shud have come to me da na taimaka mata koda da kudi ne amma wann rayuwar ai bazai bille mata ba.
Cikin kyabe baki meenal tace kece ma dakika Damu da ita..
Halisa tace Dolena na damu da ita mana meenal she is a woman like us...nide incase kika sameta kimin magana i want to talk with her ban yarda da cewa babu abunda yake damunta ba.
Meenal tace hmmm kina cikin damuwa kinason ki dauki na wata ki dora makanki ko toh wallh bazan yarda ba..
Murmushi kawai halisan tay tace cmn meenal ciwon ya mace ai na ya mace ce nide duk inda kika sameta just tell ko wajen therapist nakaita ai na taimaka.
Sounding unintrested tace ke kikaji wajen
Abeg lets talk about another thing
Halisa tace okay toh gayamin menene matsalar taki?
Nannauyar ajiyar zuciya meenal din ta sauke tay shiru acikin tunani, within a spec of some secnds nan danan harta kirkiro labarai na karya masu zafi a mind dinta game da mijinta khaleel, kafin halisa ta hankara gani kawai tay meenal na sauke mata hawaye....
ASSALAMU ALAIKUM READERS WE HAVE ONLY 2-3 PAGES BOOK 1 YA KARE. SO IF U NEED TO READ THE BOOK 2 ZAKI IYA CHAT DINA A 08060712446 TUN YANZU DOMIN YIN SUBCRIBING DIN GROUP FOR BOOK 2#.
SHARE.
Post a Comment for "Cheaters Club 30"