Cheaters Club 29
_*CHEATERS CLUB...*_
_(Babban goro sai Magogin ƙarfe...)_
#ROMANCE
#FICTION
#ADULTHOOD
#SEXADDICTS
#WOMENPOWER
BY
_SURAYYAHMS_
_08060712446_
*Only chat oo, i no dey Available for calls on this number.*
⏯️2️⃣9️⃣
Tun ƙarfe goma na dare shema'u ta shiga wanka amma bata fito daga bayinba sai can wajajen 11:30pm na dare dan tunda ta lume acikin hadadden rose berry jacuzzi warm bath dinta ta lumshe idanunta Babu abunda takeyi face mafarkin kanta acikin irin rayuwar datakeso wanda shine kawarta hadizan ta samu anata rayuwar.
Memakon dadewar datayi a ruwan wankan ya saukar mata niima ajikinta sai kuma ta fito tanamai jin wani irin sabuwar kasala da haushin kanta gabaki daya.
Hadiza maitama is living her dream right in front of her eyes and all she feels is miserable right now..
Gabaki daya ta rasa menene guda daya takeji aranta da kuma kwakwalwarta dan ya mugun cunkushewa har bata san ta ina xata billo ma tunanin lamarin rayuwarta ba.
Bacci ma kasa zuwa mata yay sai juyi kawai take daga dungu zuwa dungu na gadonta aranta tanata kasafi da lissafin yadda itama zata kai kanta izuwa wann babban matsayi da hadiza take ciki..
Wani irin maqudan bakin ciki ne ta tsaya mata a makworo tanata hadiye yawu da kyar idanun ta duk sunyi sanyi acikin radadin damuwa da yake cinta aranta bana wasa
Tay juyi nan tay juyi can sai can ta tsaya cak awaje guda tare da sauke ajyar zuciya ta lunshe idonta gam snn tace ma kanta.."..Enough is enough! All hurts.. witout a solution, solves nothing. Dan haka dole ne ta fixge kanta acikin wann raunataccen yanayin domin ta samu sauki da kuma mafita
Tana kammala ayyana hakan aranta ahankli ta bude idanun nata tare da dada jan lallausar bargonta izuwa jikinta.
tunani dayawa sunzo kanta sede raba hadiza da nata mijin baizo mata acikin lissafin neman mafitarta ba, sabida gani take kamar aurenta da mahmud ne makasudin baqin cikinta shine ma ya jawo mata komi datakeji aynxu.
Lisssafin duniyan nan tay aciki harda shawarar data yanke na neman wani hamshakin mijin mai narkakken kudi dede da mijin hadiza ko wanda ma yafishi, wanda inhar ta sameshi toh tabbas bagudu ba ja da baya zata kashe aurenta da mahmud tabishi babu wani bata lkci.
Wann mafitar shiyafi ƙarfi aranta duba da ta yarda sosai da ƙirar da Allah ya xuba mata na kyakywan mace wayayyya ta ajin farko dan haka ta tsayar da zuciyanta akan wann shawarar har bacci yazo ya dauketa tunanin ta inda zata fara zura kafa domin cika sabuwar burinta takeyi.
Ata dayan bangaren kuwa Tun karfe takwas da minti talatin engr suka bar gidan Alhaj Aliyu suka isa dutse intl airpot domin catching flight dinsu. Tara da rabi dede jirginsun ya tashi izuwa garin lagos. daga seat din hajya badiatu aai na hafsat wanda Tunda suka kamo hanyan lagos ajirgi bacci kawai takeyi Sabida maganin zazzabi da aka bata tasha dazu hadi da yunwa daya gama kashe mata jiki.
Mahmud kuwa babu abunda yake ayyanawa aransa face matarsa shema'u daya bari agida.
Daga zarar ya kalle hafsat sai yaji tausayin matarsan dik ya dabaibaye masa zuciya har kwayar idanuwansa na nunawa a fili.
Dan Har yanxu Gani yake kamar bai kyautawa matrsa shema'u dayay auren nan bada sanninta ba,a ta daya bangaren kuwa shikansa yasan tausayin hafsat din bazai kyalesa ya yanke mata wani tsatsauran hukunci ba. Har ynzu bai san a wani matsayi zai riƙeta aransa matsayin auren amana suke koko na qaddara????..?
Dan Babu tantama ko shakku yasan matsayin hafsa dana matarsa shemau bazai taɓa zamowa abu daya aransa ba dan baijin kamar zaiso wata ƴa mace a duniya kamr yadda yake kaunar matarsa shemau.
Yanayin daya kasance aciki kenan har suka shafi iya awannin da xai kawo su garin lagos sun iso dede ana neman wajajen 12 na dare saura. Lkcin jikin hajiyar sa duk yay tsami dakyar take tafiya sabida gajiyar hayaniya da dawainiya da mutanen kauyen hafsa da suka wuni yi tun safe, ga nan hafsat dinma bakanta dan a daddafe ta farka da jiri jiri tabi ta tsaya cak abayansu bata ko motsi.
hajy na karasowa kasa ta kalle engr ganin baima kalle inda hafsat din take ba bare ya san me take ciki.
Ahankli ta dubesa kamr tasan meyake ciki na rudani aransa da muryan lallami mai taushi tace "haba mahmud, da wuri ya juyo ya kalleta, suna hade ido tay masa nuni da baya inda hafsa din ke atsaye. Sihirtaccen ajiyan zuciyace ta kufce masa, jinta yay tana cewa ka koma baya ka riko mini yarinyar nan karta fadi inaga jikin nata ne har yanzu bai saketa ba..cikin kyabe baki tace "Allah sarki mutuwar uwa ba wasa ba,kaidai Kay hakri ka kawomin ita mota jikina yy tsami wallh bana iyawa ai namaka kkri ma..
tana fadin hakan ta wuce gaba tana tafiya ahankli ta barsa atsaye awajen ya bita da kallo ganin ko juyawa ta kallesa bata karayi ba.
Daga can baya ya hange hafsa ta dafa jikin wani movable truck ta tsaya a tsomare kamar mejin sanyi.
Gani yay ta tsayawa cak bata motsi alaman juyawa da kanta yakeyi sosai tanajin kamar inta daga kafafunta jiri zai wainata ta fado kasa.
Babu yabo ba fallasa ya daga kafafunsa calmy ya karaso harta gefe da ita snn ya dakata tareda zuba mata narkakkun idanunsa dasukenan acike da kwarjini, dada tantame kanta tay ayanayin rudewa tare da rikicewar tunani, kirjinta taji na bugu guff gufff kamar zai ballo waje tsabar bugawa atake hawaye suka cika uwan idanunta.
kallo daya yay mata ganin kamar ba ita ba sabida abayar sosai ya sauya mata kamanninta daga na hafsa me aiki ta dawo tamkar wata daban dabai sani ba.
Ajiyar zuciya ya sauke aransa yana mai satar kallon baquwar yanayin nata,.snn yace muje gaban mota driver yazo zakuje gida tare da hajiya.
Dago kai tay da niyyar amsashi sai kuma taji ta kasa yin hakan sabuda wani irin mummunn tsoronshi dataji ya kankameta É“ari jikinta ya farayi ahankli shikuwa bai lura da yanayin data shiga ciki ba Ahankli Ya kuma cewa ki daure muje gaban mota sabida akai ku gida nasan kin gaji ko
Jin muryansa nasa ya saka hawaye masu mugun dimi suka yanko mata izuwa kan fuskarta yuuuuu tanajin kamar ta rusa ihu awajen cos she still cant believe that an aura mata mijin shema'u
Gani take kamar shemaun zata yankata dan batajin akwai wani nau'in mugunta da shemau bazata dandana mata a duniyan nan ba.
Take ta soma tunawa da ire iren duka da baqaqen zagin datasha akan zargin datake mata na cewa tana kallon mata mijnta agidan yo me kuma zai faru intaji wann batu na aure?
Kamar ruwa haka Hawayenta suke sauka engr ya tsaya kallonta duk a tunaninsa mutuwar mahaifiyarta ne ke jefata acikin wann yanayi.
He decided to respect that duk dama ya gaji da jiranta. Da kyar ta iya budar muryanta dake nan a toshe da makurarraen kuka aciki, cike da kkr wajen hadiyeshi Tace ina zuwa, oga kaje kawai ina zuwa abayanka kaina kemin ciwo. Ya gyada kansa alaman yaji baice mata komi ba yanata kallonta.
Satar kallonsa tay Ganin har yanzu bai tafi ba. Da gefen idanunwanta dake fidda ruwan hawaye masu sanyi ta karemai kallon tsaf tun daga sama har kasa jin zuciyarta da gabobin jikinta na ragwabuwa
Wani kakkarfan ajiyan zuciyane ya kufce nata ata ciki dan ani take kamar an cuceshi da aka hadasu aure kwata kwat wann mutumin yafi karfin ace shine mijinta, gnin shi mai ilimi, kyakkwa wayayya, mai kudi da kuma gata. Ita kuma bata da komi face dakon maraici da baqin ciki na rayuwa datake fama dashi. Data tuna zancen kawunanta akauye duk tsoro sai ya mamaye mata zuciya, atake taji ta kasa samun nitsuwa.
Jira take kawai take ya tafi a tunaninta inya tafin ne kawai zata iya yanke hukuncin guduwa daga nan ta barsu ta wuce wani waje inda zata tsira.
wani irin makudan hawaye ke saukowa daga idanunta tay wani tsam da jikinta gwanin ban tausayi tanata shirya hakan aranta, Shikuma sam baison ganin hawayen dan hawayen mace yana kashemai jiki sosaii Kallo daya ya mata snn Yace in na tafi zaki iya tahowa?
..Ahankli ta gyada masa kai. Ba yabo ba faolasa Yace mata okay baijira amsarta ba ya kama hanya zai bar wajen itama da sauri ta juya zata ɓaçe dan har ta hango wani hanyar da zata bi inda bazasu sameta ba.
Tana kuwa juyawa jiri me shegen karfi ya rike kafafunta gam da kasa saitaji ta kasa motsi.
atake kafafun nata suka hau É“ari kar kar kar suna neman ragwabewa kasa kamar ancemai ya juyo baya dan ko karasa juyowan baiyi ba yaganta luiiiiiiii zata fado kasa da wani irin sauri ya dawo ya tareta ta fado gabaki daya ajikinsa sumammiya.
Sunanta ya kira da dan karfi snn ya jijjigata ajikinsan sosai wai koda ma zata farka ta bude idanunta dan lkcin baima lura da idanun dedekun jama'a dake kansu ba.
Gabaki daya hanklnsa ya zubashi akan fuskarta ayayinda yake lura da yadda nakasashen numfashinta yake tafiya ahankli yana gushewa,
wani karamin gurnani take na baqar yunwa da azaban gajiya dake ciccin hanjin cikinta.
Ahankli yace "Hafsat? Hafsa...ya dada jijjigata akan faffadar kirjinsa..
jin nauyinta na dada karuwa yasaka ya ciccibeta sama ya rikota gam a hannayensa duka biyu in a brdal style suka fara tahowa ahnkli.
Harsaida ya doso jama'a tare da ita snn yaji wani iri ganin yadda mutanen dake wajen suketa kallonsu, atake kuma sai ya daure fuskansa tamau ya maida idanuwansa kan hafsat din data kwanto masa a kirji ta kankame masa rigarsa sosai. Narkakkun idanunsa ya zuba kur akan fuskarta, sai kuma yaji yakasa dauke idanun nasa akan doguwar eye lashes dinta daya jike da ruwan hawaye dake nan lumshe, tun daga kan karan hancinta yake kalla har izuwa bisa karamin bakinta dake nan kamar an masa kwalliya mai daukar hankli.
Ahankli ya soma tafiya tare da ita ahannunsa kirjinsa na bugawa yana kallonta yanamai duban hanyar da suke takawa at same time yana dan tahowa da ita da sauri sauri, gani dayay idanun mutane sun karu akansu yasaka ya lura da
Veil din abayanta daya dan zame kasa a hannunsa. Koda ta kalle kantan sai dayaji wani abu ya tsargamasa dan tsabar yawan suman dake kanta da mutane suke kalla, akan dedekun matayen dake wajen suna jiran jirgin dare idonsa ya sauka ganin sunata rade raden masha Allah wasu cewa suke ji natural hair akan wann yarinya tubarkallah.
tsayawa yay da ita ahannunsa na dan wani lokci sai ga wata security mace ta zo wucewa, ahankli yace excuse me? Tana juyo ta kallesa ganinsa ahaka yasaka ta karaso,"can i help u sir"
yace yes, sai kuma ya rasa me zaice. Can dai ya daure yace Can u Cover her up for me??
Security tana murmushi tace yes sure. Nan ta kama veil din ta ciresa gabaki daya daga hannunsa,lumshe ido yay batare da ya san yay hakan ba jin suman hafsat din ya wani silalo kan hannunsa laushinsa na sending masa chills har cikin gabobin jikinshi,
Da kyar ya iya kwace kansa ya bude idon, masha Allah suma ne taf akan hafsa irin mai cika da yawa din nan ya cika cunkus alaman ba ataba sakamai wani chemical ko relaxer ba,..sai satar kallon gashin yake dan shiknsa bai bata ganin suma mai duhu da yawa irin wann ba idanunsa kurrr akai har secruty ta kammala gyara mata veil din ya rufe ta gaba daya.
Tana gamawa tay murmushi tace sir am done,ammm is she ur wife. Tafada in a frendly manner.
Ya kalli hafsa din ya kalle matar he wonders what gave her d impression of wife saida ya ga yadda hannun hafsat din ya tantame masa rigarsa sosai.
Kunya yaji ya lullumeshi jikinshi taciki a muce Yace "no, she is a sister..security tace ohh nooo wonder she is so pretty like you sir. Baice komi ba yy murmushi ya kara da gaba.
Direct gaban motarsu yay da ita Suka samo hajy na cikin motar ta zauna tanata jiransu.
Can Ya tsaya ya rasa yadda xaiyi ya aje hafsa agaban mahaifyarsa har saida hjyar ta sauko musu abazata suna hade ido yay saurin dauke nasa Kansa ya saukar kasa da sauri.
Yi tay kamar bata san meyake ciki ba ta karaso daf dashi tanacewa subhanallah Mahmuda meyasa surkuwan nawa
Tsabar nauyinta dayake ji Bakinsa na bari har yana batar kalma Yace "Maama inaganin suma tay. Ko zaku wuce gidan saini na kira muku likita naga dare yay.
Hannunta ta dora akan hafsat din tanamai Girgiza masa kai alaman a"a' tace ni nasan meyake damunta kawota nan cikin motar muje gida kawai
Duk kkrinsa na son ya zille ya barsu awajen yaci tura, haka ta temaka masa ya saka hafsa a seat din baya tay sauri ta koma gaba ta zauna ta barshi tare da ita abaya.
Tana zama tacewa driver ta marmaza yay sauri ya kaisu can gidanta surkuwanta ne ba lafiya.
Mahmud dake baya sankame da hafsa ajikinshi bai iya cewa komi ba sabida kunyar mahaifyarsa daya lullumesa yabi ya rufemai baki.
Can Sai ta juyo kadan ta sace kallonsu tay dariya aranta ganin hafsa din manne da kirjinshi gam gam da yadda shikuma ya sunkuyar dakai kamar an dauresa.
Baima san tana satar kallonsu ba Kamar wacce take magana dakanta sai tace.."Allah sarki halamaa tana jin sanyi ne karka saketa ka riketa sosai dan Allah mahmuda rashin uwa fa ba wasa ba.
Allahu akbar Nida uwata habiba ta rasu ji nayi kamar an mini tsirara kaima in naka ta rasu zakaji metakeji.
Baice komi ba tanata kawo masa labarai na da da can masu ban mamaki tana gaya masa labarin fulanin daji da suke garin jigawa har ya farajn kamar tasan mutanen datake labarinsun ne.
Ahankli cikin labarin shirmen nata ya soma fahimtar dan karamin binciken asali datayi..
Duk zamansu a kauyen suna zaman makoki gani kawai yay tana shige da fice tana shigewa jikin mutanen garin tanakuma jan matayen kauyen ajiki
Dik ya dauka duk dan halinta ne na saurin sabo ashe ita har ta kusane domin jin asali da samo labarai kala kala game da iyayen hafsa fannin uwa da uba dan ta san wacce irin zuria zata hada da nata jinin.
Acikin hirar shirmen datake musun take kan bashi labarin iya abunda taji musmmn wayanda suka burgeta aciki, ance mata mahaifyar hafsa din tana da hali na gari dakuma ilimi addini dan itacema ta soma kawo musu karatun allo a kauyen, labarai kala kala babu wanda bata ji ba, sosai mahmud ya jinjina ma kaifin basira tare da ƙwazon mahaifyar tasa aransa, tareda godema Allah datake kkri wajen kareshi wanda har saida suka iso gidanta snn tay shiru.
Nan ma haka tay wucewarta ciki ta barsa ya dauko hafsa din a hannu daga mota ya kawota cikin gida.
Already dare yay sosai lkcin anata neman sha biyu da minti arbain amma hakan bai hanata kiran likitanta emergency ba.
Acikin Wani hadadden daki na saukar manyan baki ta musu jagora ya kwantar da hafsat din ahankli akan wani tanfatsetsen gado tare da gyara mata kanta akn pillow hankli ya soma kkrin kwace rigarsa data tantame da hannunta sede rikon datay masan ne yay ƙarfi sosai tattare yake da alaman tsoratar datake ciki.
Shikuwa sauri yake ko dan ya koma gidansa ga matarsa shemau. Cikin sauri ya saka hannunsa zai cire rigarsa ahannun ta da karfi caraf yaji muryan mahaifyarsan akansa Tanacewa me kakeyi haka mahmd kamar wanda baida imani yaya kake fiffige mata hannu kamar yar kaza?...
Daga kai yay xai magana cikin tsaresa ta hade rai tana bambami tace nifa bangane ba wai saurin me kakeyi haka?.kana nufin haka zaka barni anan inata maka jinya??
Baki bude yace amma mama, cikin tsaresa tace habawa mahmud nifa rokonka nakeyi Dan Allah kazauna tare da yarinyar nan Likitan nan yana zuwa munyi waya dashi ynxun nan..cikeda lallami ta dafa kafadunsa har saida tasaka ya lumshe ido batare da ya shirya ba"...tace ainasan sauri kake zakaje gidanka toh amma ynzu inka tafi wani abu ya sameta fa ni ya zanyi da ita???
yadda tay maganan a dame yasaka muryansa yay sanyi, agajiye yace toh naji hajya karki damu zan jira likitan yazo ai shikenan ko....tace eh yawwa ai hakan yafi...
Toh bari de ina zuwa...kafin nan ya hankara gani yay harta kama hanyar ficewa a dakin tanamai cewa toh ka zauna dai anan ina zuwa...bata wani jima da fita ba sai ganan mai aikinta ta kawo musu ruwan shayi dayaji kayan qamshi acikin wani hadadden white colour royal tea set da design din gold ajikinshi da karamin snack agefe.
A ladabce ta gaishesa snn tace sir Hajya ce ta hada maka shayin snn tace nakawo maka kasha. Tace inkana bukatar cin wani abu kafadi min sai nagaya mata tace ita dakanta ma zata dafa maka yanxun nan..
Fuskarsa ba asake ba yace no this is enough. Kije Kice mata taje ta huta ni bana bukatar komi..and if u allow her cook dis nite am going to fire u...
Kanta akasa Tace sorry sir..snn ta fice da sauri ta nufi wajen hajya danta kai mata sakon cikin gaggawa...
Da hannu daya ya kama rigarsa ya kwaceshi snn ya sauko kasa ya hada ruwan tea din yasha kadan duk hanklinsa ba ajikinsa yake ba yanata tunanin what if hanklin shemau ya tashi ata dalilin rashin dawowarsa gidansa a yau dan inba tafiya yay ba baya iya jimawa awaje.
Wayarsa ya dauka ya dada dubawa baiga kiranta ba bare saqonta nan hanklinsa ya dada tashi yaji kawai yanason yaji muryanta to make sure she is fine dan duk wani sakon daya tura mata tun suna gidan Abokinsa a jigawa batay reply ba, Wanda ya tura mata ta watsap din ma ya duba yaga har ta budeshi wajen karfe goma saura ta karanta amma bata amsashi ba ta barshi a seen din kawai.
Baisan cewa ita batashi ma takeyi yau ba amma shikuwa anan ya damu akanta bana wasa ba..
fitsari ne ya tada shi ya shiga bathrum din yay fitsarin snn ya kunne sink yanamai wanke fuskrsa da ruwan sanyi kodama anxietyn dake damunsa xai ragu.
Motsin daya soma jin adakin ya sakashi ya doso kofa cikin sauri,
yana bude kofar yaga likita a tsaye tare da hajyarsa yanata faman gwaje gwaje akan hafsa bayan nan ya soma kkrin jona mata ruwa.
Karasowa cikin dakin yay suka gaisa sama sama likitan ya gama komi yace musu jininta ya da. haura snn duk yadda akayi su tabbata taci abinci yau din nan.
Bayan nan allura biyu ya mata a jijiya Wanda shine ya farkar da ita
Still idanunta a lumshe amma da rikitaccen kuka ta farka tana mai kiran ummanta har aban tausayi.
Ganin hanklinsu ya soma tashi yasa Doc yace musu she will be fine she is in a state of mental stress amma zai wuce
nn ya musu sallama zai fita mahmd ya mike zai rakashi..da mamaki yaga hajiya ta sha gabansa tana cewa 'a a kaine mijinta ka zauna ka tabbata taci abincin akwai maganan da nake so nayi da likita na a waje.
Mahmud yaji kamar yay ihu gashi a mugun matse yake duk bai shirya kwana anan ba amma bisa ga dukkan alamu ya harsasho yuwar hakan daga moves din da mahaifyrsa take nuna masa.
Haka yay hakuri ya koma
Bakin gadon ya tsayawa hafsat ayayin da hajya ta fice tare da likita.
Suna fita tace toh likita sai da safe in akwai wani abu zakaga kirana
Da mamaki Likita yace hajy amma naji kmr kina cewa zaki gayamin wani abu.
Karamin dariya tay tace ayya subutar baki ne likita babu abunda yake damuna face bacci..
Likita yace toh shikn saida safen hajya.
Yana ficewa ta haura sama cikin dakinta ta haura akn gado taja bargo ta rufe jikinta dashi tana cewa kajimin yaro yawani kame kame yo nima haka aka kawoni gidan ubansa gatsau kamar diran yesu lkcin banma san shi ba,daga nan bata wani jima ahaka ba bacci mai nauyi ya dauketa.
Ata dayan bangaren kuwa prince femi ne akwance akan makaken gadonsa as usual yay wanka ya tattala jikinshi yay masifar kyau a cikin wata dark blue pyjamas data amshi kalar fatarsa datake sheqi hutu yabi ya gama ratsata.
A ruf da jiki ya kwanta wani katoton ipad rike a hannunsa, wani abu yaketa kallo aciki, fararen idanunsa stiiff akan video din victoria da kaninta da camerar daya jona musu acan gidan yake hasko masasu yanamai kallon duk wata motsinsu acan.
Dake shine ya bashi gidan tuni yasaka aka sakamai secret cameras acikin gidan da wajen gidan duk dan yadinga monitoring din rayuwar yaron sosai sabida yana da baqar kishine bana wasa ba.
tsiraran yatsun hannunsa da sukaji manicure yake daddanawa akai yana mai sake memeta inda nile yake kaima victoria korafi yanamai jan tsaki.
Yanxu haka jira kawai yake ta dawo gidan yaji me zatace masa akan hakan.
vicky tana barin gidan nile din bata tsaya ko ina ba sai nata gidan, tana danna horn abakin gate mai gadi ya taho da gudu yazo ya bude mata gate din ta shigo ciki, tun tana kammala parking femi yaji karar shigowarta nan da nan ya kashe ipad din snn ya bude personal drwarsa ya saka aciki tare da kullewa da keys.
Jikin Window yana nufa ya daga labule ya leka kadan ya hangota daga can wani irin devilish smirks ne ya kufce masa batare daya shirya ba
Ita kuwa tanaganin motar mijintan a ajiye batare da tasaka komi arantaba ta dauko clutch din ta sauko ta nufi cikin gidan agajiye..
Dake ta gaji Batako nemesa ba ta nufi nata bangaren tana kaiwa room dinta jakarta kawai ta aje akan table ta dawo bakin gadonta ta zauna agajiye da niyyar zata soma kwance igiyan heels dinta kafin ta shige wanka. Har ta cire dayan takalmin ta ajeshi zata soma jan igiyar dayan kenan dadaddar qamshin turaren femi shine ya dakatar da ita. Ahnkli ta dago kai ta dube kofa sai gashinan ya faso cikin dakin fuskrsa a dore babu wani excuse ya tsaya cak agabanta a gadarance yanamai jefa mata wasu irin kallon rainin hankli da bata gane kansu ba kuma baice mata uffan ba.
Ya gama shiryawa aransa cewa zai mata wani abunda zai saka taji tsoron komawa gidan kaninta nile bare haryana samu daman kai kararsa wajenta.
He want to have total control akan nile amma ya lura kamar sabida vickyn ne kawai nile zai iya masa biyayya acikin sauki, ji yay gara ya fara dealing da ita tunda yana da iko da ita sosai inyaso ko ta wajenta yasan zai soma cin nasara akan nile.
Dauke kanta tay akansa aranta tanamai kyabe baki ahnkli dan ayadda class da girma ya dan shigeta nan wani bin gani kawai take kamar da akwai wani damshi damshin yaranta da yake damun kwakwalwar mijinta femi .
Kallon rainin dayake mata yasa tafara tuna abunda nile ya gaggaya mata wanda aganinta ma ba ajinsa bane shiga hurumin yara beside nile ba yaro bane da zaina masa irin wann abubuwan saka idon
with his behvr na yadda ya shigo mata dakin gatsau she just conclude in her mind dat femi is being immature kwana biyun nan and its seriously disgusting her.
Batare da ta kulashi ba tana kan jan igiyar takalminta Muryanta ciki ciki tace "whatsup Femi you just barge in to my room like a beer palor meyafaru...
Kansa sama sama cikin ji dakai yace "yes i barged in.. it is my own house and so what???
Wuyanta a karye ta dago ta kallesa da mmki suna hade ido yawani ja mata tsaki , with comand a voice nashi yace "Daga ina kika fito????Sharesa tay bata amsashi ahaka ba, tasan tana hakuri dashi sosai amm bata fiye son daukar raininsa ba, Duk abunda yake mata ynxun gani kawai take kamar gigin yarantan ne dayake damunsa.
batare da ta kulashi ba sai can tace" i'm with my friends and u you knw dat..Wani irin kallo ya mata da daurarren fuska sigar neman magana yace "Hmmm Ure with ur friends fa kikace?? tace yes why are you..tun bata karasa kalman dake shirin fitowa abakinta ba cikin dakamata tsawa yace will you shut up dat ur lieying trunk?kina haukane da zaki min karya....karya kike yi i swear to god badaga nan kike ba...Victoria U think i am a fool right?..
Cikin katsesa shi tace Bangane ba femi akan meye haka kake dakamin tsawa tou ai Saika gayamin daga inda fito..Wani irin bacin rai ne taji ya rufeta Tun igiyar takalmin bai gama ficewa akafarta ba ta fixge shi ahatsale ta jefarshi agefe jikinta harna É“ari ta mike tsaye cikin tsawa ta kuma maida masa maganar azafafe "
What do you mean by that femi...yau bana cike da masifa.. cos am already not in the mood to talk to you...nagaji nagaji nagaji da zargina da kakeyi i will not take it anymore. And i wll not let u imprisoned me na wuce wann ajin.
Tafi ya fara mata me karfi yanamai cewa Yace wow wow wow woow woww the independant vicky williams..mrs lecturer..oya educate me naaa...educate me oo.. ki gayamin abunda ya dace nace da wanda bai dace ba sabida ke isasshiya ce .. "big woman gang awon busy body...oya naaa..
Duk da bacin ran daya gumeta amma bai saka ta kasa calming kanta ba
Cak ta tsaya agabansa tanamai kallon kwayar idanunsa snn tace what is the meaning of this rubbish ure doing femi?
Kaje kasha wani abu ne?
Yace excuse me woman dont you dare change the topic i knw ure not with ur friends..u went sumwher else..nan ma a sigar zargi da rashin yarda ya fada mata hakan wanda bakaramin raunata yakeyi ba.
Cikin idanunsan take kalla da kar take kkri wajen nitsar da kanta
ranta yay mummunan baci batare da ta daga murya ba Tace mishi yes I went to see nile...is dat all u want to hear?..
Yace no..dats all u shud have told me..toh meyasa bazaki gayamin cewa zakije wajensa ba??? Snn me kikaje yi awajensan and meyasa baki gayamin kinje ba
Dauke kanta akansa tay tanamai can tsaki har kamar bazata amsa shi ba sai can tace toh akan me dan zanje wajen dan uwana saina gaya maka?yaushe muka fara wann yarantar?
Yace Ohh yaranta ne ma,toh ni mijinki ne and u must respect me in dis house.
A fixge ta juyo tacemai i do respect u alot femi amma kasani u must respect my family too.
Nile yakira ni ne domin gayamin abunda kace ma abokinsa. He is insisting on leaving ur house tomorw inde wai sei abokinsa ya fita..
Beside ni banga dalilin da zai saka kana shiga hurumin yaran nan ba.
Nasan waye nile fiye dakai, kuma na damu da rayuwarsa sosai,..nile baya aje abokan banza wann yaron da kake gani childhood freind dinsa ne tun na primary schl har iyayenmu ma sunsan lucio...so please femi am requesting u to stay out of this silly issures kabar yaran nan suyi rayuwarsu
Please have some respect for my family femi.
Bata hankara ba taji ya fixgota da karfi ya matseta sosai tsabar zafi da tsoratar datay atake hawaye suka ciko acikin idanunta
A hatsale tace meye haka, meya haka..? "Leave me alone femi, ure hurting me. Hawaye ne suka soma sauka a idanunta jin ranta na dada hargitsewa da mummunan bacin rai
Kkrin kwace kanta takeyi a hannunsa ya dada matseta da uban karfi wasu mugayen smirks suna masa kufcewa akan fuskarsa da alaman dadi ma yakeji aransa daya ga tafara masa hawaye dan yanajin dadin kallon babban mace acikin raunataccen yanayi..it gives him some sense of power and ego sai yanaji aransa kamar ya cika cikakkem namiji ne.
Tana kicin kicin ya dada fixgota da karfi muryansa a karsashe Yace.."Ke yanxu baki ji kunyar abunda kike gayamin ba? "Are u dis stupid.. "Mani kike gayawa haka? Respect ur family, respect ur family
Respect ur family na nawa?
Ihu ta masa cikin bori tace"...Let me go femi!
Yaki sam ya saketa yana cewa...i did my part vicky..ina da kudi and i did evrything for you, ..evrything,..for you. For your family, and ur brother now why cant u just sit at home and respect me too?
Cikin katseshi da hatsala tace "..You have done nothing for me femi kar ka sake rikeni haka ka haukace ne"! Da ƙarfin tsiya ta kwace kanta hawaye na zuba a idanunta ganin inda ya matse matan yay jaaa yana mata zafi sosai hakan yasa ta dada fashewa da kuka mai karfi.
Is like She dint even knw what is happening she bacome so confused it feels like haka kawai femi ya rikice mata dan bataga waani abun tashin hankli a maganan data masa ba.
Ta inda yake fita bata nan yake shiga ba Yace Sabida kin rainani ko? Ko ban gaya maki cewa nine zan kula dashi ba, toh meye naki aciki and why did u go der witout my permission?..akan me xakije kina zugashi akaina..ni inason na bashi kariya amma ke dakike yar uwansa kece zakina Bashi dama yana jefa kansa acikin hatsari na abokan banza?
Are u even aware that young men living in the same house is toxic? Idan nile yabi abokinsa ya fara shaye shaye fa,ko yafara jansa suna kwana da karuwai?? That lucio or wateva, can be a gay, or a thief or drug dealer i just dont like him around nile.
Tsabar ranta ya baci da ihun dayake mata akai cikin tsaresa da tsawa tace "Ur likes does not matter sabida rayuwar kanina ne bana ka ba so you cant control his life like dis femi..Tsabar abun yaci mata rai hawaye kawai ta zage tanayi agabansa muryanta har na rawa rawa tace yanxu akan wann maganan da baifi muyi shi acikin fahimtar juna ba kake min irin wann tsawar?
Da gadara a muryansa yace "Na isa ne..zan kuma miki magana a duk yadda na ga dama bcos i am the man here. Iya abunda nace miki kiyi shine kawai zakiyi..
A zuciye Tace in banyi ba mai zaka iyayi me zaifuru femi? Ina de fitar dani zakayi agidan nan..do it do it mana...ka fitar dani ko ynxu dan alkcin ne zaka gane cewa Ur everything is worthless to me.. dan da arxikina ka ganni ka aure ni iyayena kuma ba matsiyata bane bare kace kaine ka musu komi rayuwar kanina ne kawai bazan kyaleka kayi controlling dinsa batare da wani kwakwaran dalili ba..so u can go to hell..do ur worst, ka fitar da uwarka agidan nan ma bare ni? Bata hankara ba taji saukar maruka har biyu tasss tasss akan fuskarta saida ta kusa kifewa kasa agigice.
Jikinsa har na bari jamar zai tattakata ya matso kusa da ita yana diri yace how dare u talk about my mother..ke ki shiga hanklinki fa.. this is a warning to u vicky tunda kince rainani zakiyi then fine...aje ahaka..nile da abokinsa zasu zauna tare amma karda ki yadda na sake naganin ki agidan sa koda a mafarki ne.
I forbid you frm going der tunda ke bakida da hankli ni ai ina dashi. I think i will just talk to ur mother directly regarding his safety.
Yana fadin hakan ya kama hanyarsa fuuu ya fita ya barta cikin wani irin yanayi na hajijiya dan tunda ta zube kasa kuka kawai takeyi har aka kira asubahi bata iya runtse idanunta ba.
Gaba daya ta rasa ma'anan borin dayay mata yanxu she dint even realise cewa its just an emotional manipulation.
ya zafafa maganan ne dan ya dorata a matsayin me laifi dan ace yana iya bakin kkrinsa akanta da yan uwanta itace kawai bata gani.
Tunda ya barta anan bai sake waiwayota inda take ba da kyar bacci ya kwasheta da asuba ta farka da wani irin zazzabi tare da jiri wanda hakan ya jawo bata iya fita wajen aikinta yau ba.
Ko awa biyu batay da kwanciyar ba Karar wayarta ya tadata a firgiceta farka ta jawo wayar da kyar batare da ta duba waye bane ta saka a kunnenta ahankli tace "Hello?
firgita ta mikie zaune dan da wani irin muryan bacin rai mahaifyartan ta tare dashi tanamai cewa zata tona musu asiri.
Duk bayanin da vicky take kkrin mata bajinta takeyi ba dan jiya acikin daren femi ya kirata har yana kuka.
Yace mata vicky tana masa gori snn tana nuna masa cewa shi ba jagora bane ga rayuwar kaninta nile, ya juya maganan yace ai beisan lucion bane shiyasa ta tanbaya amma vicky tazo taci masa mutunci harda zagin maman shi, yace musu sei abunda taga dama take masa agidan
..ya gugguduma karya wanda yasaka iyayen vickyn suka amince dashi sosai...
Washe gari da sassafe yabi ya turo musu da makudan kamar wanda baiyason kudin yanamai kuma basu hakuri akan karsu yi ma yaransu fada akansa.
Bakaramin tausayinsa sukaji ba aganinsu femi is doing too much for vicky amma bata gani.
Kalar masifa da bakaken magana da mahaifyarta ta gaya mata akan wann maganan har saida taji zazzabi ya rufeta.
Kuka kawai ta wuni tanayi akan gadonta harta soma tunanin cewa bazata ma kara zuwa gidan nile din ba tunda yanzu iyayenta sun nuna mata cewa sun fi amincewa da zantukan mijinta akan nata.
Mahaifin nasu shine ya kira nile ya masa fadan akan daya duba lamari femi da zuciya daya sedei dayake yana mugun son danshi a matsayinsa na dan auta shikan lallami ne yafi yawa atanashi fannin basumasa fada sosai kamr yadda sukama vicky ba.
Ata fannin Femin kuwa dake yasan be kulla gaskiya ba tun dayay ma vicky hakan da sassafe ya zille yajeshi hutun wucen gadi a abuja wajen dadironsa chief okoro.
Ata fannin engr kuwa tunda yaji shiru hajy bata dawo ba adan dolensa ya koma ga hafsat datake kuka ajikin radadin ciwon rashin mahaifyarta ga rudewar sabuwar aure da aka mata ma bazata
Ga makudan yunwa dayagama nakasa ta.
Da kyar ya lallameta da dukkan haqurinsa har tadan sha shayin da snack din aka kawo musu dakin, sede tana shan shayin batakai rabi ba cikinta ya dinga murdawa haka ta dinga kwaxa masa amai seda duk yabi ya rude ya rasa yadda zaiyi da ita gashi dare ya nitsa gidan yay shiiru sukadaine suka rage wanda basu kwanta bacci ba.
haka ya lallame zuciyarsa ya kuma cire kunya aransa gabaki daya yafara kulawa da ita sosai, nan yay moping floor din snn ya dawo ya temaka mata ta cire kayan jikinta duka ya mata wanka da ruwan dumi snn ta sauya izuwa towel ya wanke mata fuskarta da bakinta ya dawo da ita kan gadon ya kwantar da ita.
Itade a sama sama take jin abunda yake mata kanta na juyawa bisa gajimare, Lokcin alluran ne kawai yana famar wainata bata cikin hayyacinta ma bata san meyake faruwa da ita ba.
Zaman diris yy agefenta yana bata baki har bacci ya dan saceta ta kwanto ajikinshi nan da nan duminta ya mamayeshi kafin kace wani abu ya samu ya runtsa kadan.
Bacci suka kwasha Har wajajen karfe shida da rabi saura na safiya basu farka ba. Dan juye juyen datakeyi ajikinshi da sunan ummanta yasaka ya firgita ya tashi yanata kallonta ashagale ganin towel din gabaki daya ya zame daga kan kirjinta .
Cikin lymshe ido da budewa yay sauri wajen zare jikinshi anata kafin nan ya gyara mata zaman towel dinta ya dada gyara mata kwanciyarta ya mike tsaye ya shiga bathrom da sauri sauri yay alwala ya fito.
Ahankli ya fice a dakin batare da sannin kowa ba dan duk abubuwan daya faru ajiyan cikin daren sune suketa dawowa masa a idanunsa har bai tabbatar makansa ko zai iya sake hade ido da yarinyar ba... daga masallaci bai dawo tanan ba ya wuce gidansa direct yana isa dakin shemau ya nufa ya samu tanakan sharban baccinta hanklinta akwance.
Karasowa yay ya tasheta dan tay sallah suna hade ido ta wani gallara mai harara acikin gigin baccin tacemasa taji..yana ficewa tay banza da shi ta cigaba da sheka baccinta. Shima bai wani jima da kwanciya anasa dakin ba wani nannauyar baccin gajiya tay awon gaba dashi...
SHARE .
Post a Comment for "Cheaters Club 29"