Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Cheaters Club 28

 _*CHEATERS CLUB...*_ 

 _(Babban goro sai Magogin Æ™arfe...)_ 




#ROMANCE

#FICTION

#ADULTHOOD

#SEXADDICTS

#WOMENPOWER


BY

 _SURAYYAHMS_

 _08060712446_

*Only chat oo, i no dey Available for calls on this number.*


⏯️2️⃣8️⃣

Wani irin jan ajiyan zuciya mahaifyar hafsat din tay tanamai cewa la ila illallah cikin kakkarfan gurnani ayayinda su hjy badiatu suke kkrin tayata karasa kalman shahadar suna masu tausayawa mata sosai. Rudewa hafsat tay ganin jikin mahaifyartan na rawa kar kar agabanin fitar rai.


wani irin bakuwar sanyi taji na mamayar sassan jikinta hawayenta na diga kasa Ahnkli ayayinda da takejin yadda gabobin jikin mahaifyartata yay sanyi daga bisani  ta kwanto ajikinta a ragwabe daga nan sai bata Æ™ara wani motsi ba..


Ƙureta da idanu hafsa din tay wani abu na gaya mata aranta cewa ta rasa mahaifyarta, kuka mai karfi ne ya shakureta amagworonta sai kuma taji kukan nata ya kasa fitowa fili,sassan jikinta a ragwabe ta rungume mahaifyantan gam gam tana hawaye masu tsuma da rauni dan jitake kamr nauyin duniyar ne gabaki daya ya sauka akan kafadunta ita kadai.


Tantame idanunwanta tay hawayen nata suna sauƙa kamar ruwa amon sautin muryan mahaifyr ta da nasiharta na karshe shiyake mata yawo acikin kwakwalwantan ayanxu.


Kukan bai tashi kufce mata ba harsaida hajya badiatu tyi yunkurin kwacota daga jikin gawar mahaifyartata,a nan ne ragwababben kuka mai mugun saka tausayi ya kufce mata muryanta a dishe tana cewa umma na, ummana, ummana ummana..hjy badiatu na sauke hawaye ta rikito tanamai lallashinta sai kuka takeyi ajikinta bbu kakkautawa kusan kowa awajen hakuri kawai yake bata ayayinda mudi ya bude kofar ya fice cikin sauri batare da sun lura ba,can waje yaje snn ya ciro karamar wayarsa daga aljihu datasha ÆŠauri da rubbering ya danna lambar magajiya yanayi yana waige waige.


Da kyar magajiya ta dauki kirar, Ya budi baki zai magana kenan cikin tsaresa da masife tace "toh mudi sarkin son kudi aika jira inga kira daga hajya kafin kafara takuramin da kira akan maganan kudinka haba sai kace akanka akafara talauci???


Muryansa kasa  kasa Yace ke magajiya ni ba wann ne yasaka na kiraki ba. A hantare tanajan tsaki Tace toh meye?

Yace magajiya da akwai matsala"..Tace matsala ? Wace irin matsala kuma


Dada komawa gefe yay sann yace wann lamari fa ya zafafa, yuwrsa da kamar wuya halama sai kun shigo ciki.


Tace "assha!!! Tirrr dakai mudi.. ai dama nasan kai fanko ne iya zallan cika baki kawai ka iya bazaka iya tabuka mana komi ba. haba da Allah bafa kisan kai akace kaje kayi ba...magana kawai aka ce ka mata amma ka kasa sabida tsabar tsoro da ragwanci, lallai mudi kai kam kaji kunya wallah kanabada maza haba da Allah....


Yace ke magajiya karki gayan magana ba,da can kinsan da cewa mijin matar nan shine ya kawosu asubutin shine kikace nazo?.. yo gashi yazo da jatumarsa da wani babban mutum sai bubbudemin idanu suke suna min tambayoyi akan hansatu. yanzu haka ma sunce saida na basu hansatun zasu kaita kungiyar marayu 


Yana share zufa dake tsatsafowa akansa yakuma cewa "yanxu haka da nake miki magana uwar hansatun ma ta rasu na rasa yadda zanyi na zille gashi nace musu zan kaisu gaban alkali..ni ko zaki gayawa hajyar takine ta temaka ta saka mana baki danni bani da ko kandala da zan ja dasu agaban alkali.


Baki bude Magajiya tace tab di jam yau ana ga wata... yo kai mudi kaji tsoron Allah ka dena zunduma mini karya haba abun naka yay yawa ga wauta ga ragwanci ka karya dame zaa soma maka hisabi a ranar karshe? Mudi Kasan me kake fada kuwa? Yo kaf kauyenku in aka hada bazasu ji kamshin hajiya ba bare kuma mijinta....kai subhanalla amma mudi zanci maka mutunci  inka sakemain irin wann karyan rainin hanklin shaye shaye kake yi kome?....


Yace au tsawa kike dakamin to shikenan  zakiga shaye shaye kuwa inde bazakuyi wani abu ba nizaan koma ciki muyi cinikin hansatu dasu inyaso suban dubu goman sai na kama gabana dashi.


Har Zai katse wayar cikin sauri da É“arin baki magajiya tace kai mudi kai mudi tsaya kaji mana?mmmm Kace wai alhaj yana wajen kuma harda kyatumarsa?


Yace to da girmana sai na miki karya?


Da tsananin mamaki ayanayinta ta jinjina kai snn Tace tab ji jam..to wallhi ka nitsu ka gayamin duk yadda akayi saimusan yadda zamu billawa maganan dan mutanen nan nada kudi yanxu sai sukamamu duka su kullemu agidan yari mu bamu samu kudi ba kuma munji wuya..

hajy kuwa cewa zatay bata sanmu ba


Sauke ajiyan zuciya Mudi 

Yay sann ya hau gaya mata abunda ya farun tiryan tiryan bai boye mata kome ba.


Mamakine ya hana magajiya magana sai salati da hmm hmm takeyi dan a tunaninta kaf masu kudi irin haka basu kaunar talaka, snn basada lokcin kallon masu aikinsu bare ma harsu bar abubuwanda ke gabansu suzo har wani garin domin taimakawa.


Mudi yana kammala mata bayani ta sauke nannauyar ajiyar zuciya snn tacemasa Duk wann case din me sauki ne amma sai in zaka bani cikakken hadin kai Dan muddin bamu hade kanmu waje guda ba Alhaj zai iya kama mu, idan kuma muka tona magana hajya zata iya kamamu itama kuma kasanta bata da imani wallahi.


Yace toh me zamuyi yanxu.


Shiru tay cikin nazari kafin ta gaggayawa masa iya abunda zai yi da kuma riban da zasu samu aciki. 


Shikam bai damu ba dan inde zancen kudi zai fito aciki to komi ma zai yu.


Yana komawa cikin asibiti ya samu har an rufe mahaifyr hafsat din da mayafi. Hajy badiatu na rungume da hafsa da already zazzabi mai zafi ya rufeta ayayinda su engr suke tattaunawa da likitoci akan yadda za'ayi akaita kauyensu a emergncy truck na asibiti inda za'a mata wanka snn a binneta.



Sauya fuska kalar tausayi mudi yay yana sussukunyar dakansa kasa cikin jimami kamar yadda magajiya ta zayyana masa yayi snn yazo ya tardasu a wajen yanajin me suke cewa.


Alhaj aliyu ne ya dubesa snn ya karkda kai yace yawwa malam mudi tunda ka dawo sai ayi hkri amance komi ka mana jagora izuwa kauyenku domin ayi mata duk abunda yakamata.


Da mamakin su mudi Bai musu musu ba aka hau shirya komi dashi aka dauko gawarta aka saka acikin motar asibiti daga drivern sai mudi, engr mahmud kuma ya dauko Hajya badiatu tare da hafsat din sai Alhaj aliyu dake bibiyarsu abaya.


Tun ahanya mudi ya kikkira sauran yan uwansa ya zayyana musu komi da harshen yarensu sabida karma driver yaji me suke kullawa.


Daga can kuwa Sunajin zancen kudi atake jikinsu ya fara rawa babu sanya suka soma kulle kullen yadda zasu yi su yage rabonsu ajikin wayannan mutanen dan koda anbarsu a kauyen da hansatun sunsan ba riketa zasuyi ba gara taje duk inda zataje kawai dan suhuta maransu da jarabar gulman jama'a 



Tafiyar Awa daya yakaisu har cikin kauyen Direct akayi da  gawar gidan mijinta, Sann aka arranging masu wanketa da shiryata kamar yadda addini ya tanadar babu wani jinkiri aka mata sallah aka kaita makwancinta..


Hajiya badiatu taso ace hansatu ta zauna tay makokin mahaifyarta koda na kwana uku ne amma lura da tsananin jahilci da tsana dake kewaye da zuciyar yan uwan mahaifinta yasaka ta yanke hukuncin kawai ta tafi da ita asalin gidan mijinta dake Abuja dan hutune da businesses dinta kawai yake kawota lagos, manyan foundations dinta kuma yafi karfine a kano da kaduna da zamfara state. 


Kawunan hafsan kudi kawai suka nuna suna so abasu kota halin kaka dan harta gadonta ma saida suka ce ba nata bane, inji babban wan mahaifinta yace ai gida da filin kofar gidansun ma duk ya cinye acikin basukan da suke bin iyayenta harma suna neman kari akai bayan hansatu da dedeku acikin mutanen gari sunsan duk karya sukeyi basa bin dan uwansu ko asi.


Case aka dingayi hajy badiatu nata kkrin kwatowa hafsa hakkinta amma Rantsuwar da suka dingayi akai yasaka engr yace abar musu shi, 

Hatta yar dubu uku da dari biyar da suka kara akaima duk ya dauka ya basu snn aka dawo da tattaunawa kan batun makomar rayuwar hafsa.


Ko ajikinsu suka tsunduma ciniki dasu kamar wata yar akuya zasu siyar..


Dan Adam bazai taɓa sanin amfani da darajar da iyayensa suke dashi ba musmmn in suna raye sai a ranar da akace masa babu su a duniyar, ranar ne zai asalin fahimtar cewa baida wani gata ko mutunci bare kuma security face na kulawar iyayen nan nasa.



Yadda yayun mahaifin hafsatu suke tsaurara zancen hana tafiyar Shikansa mudi saida ya matukar sha mamakin yadda suka shirya makirci adan kankanin lkci. 


Babban yayan su mai suna dogara yace inhar kungiyar marayu ne zata dauki hansatu saidai a biyasu kudade ko ahada harda sauran yayansu marayu da uwayensu mata suka mutu akaisu binnin suma 


Dake hajya badiatu tasan halayyar dan kauye tuni ta ja gefe ta kira awaya dominta shawarce mijinta,..sun jima suna magana sai can suka kammala snn ta nemi tayi ganawar sirri da hafsat din. 


Koda ta shige cikin dakin a dukunkune ta sameta kwance akan tabarman mahaifyar tata tana wani irin rawar É—ari zazzabi mai zafi ya rufeta.



Daga waje kuwa Engrn mahmud ne a zaune tare da abokinsa alhj aliyu agindin wani bishiya inda ake karban gaisuwar mamaciya, caraf sai ga kirar mahaifinsa ya shigo.


Ciro wayar yay daga aljihunsa dan Bai sha mamakin ganin kirar ba sabida yasan hala mahaifyarsa ce ta gaya masa komi shiyasa ya kira domin yaji ba'asi.


Ajiyar zuciya engr ya sauke sann ya kara wayar a kunnensa cike da girmamawa ya rusuna kai kamar wanda mahaifin nasa yake gabansa, muryan mahaifin nasa ya tsunkayo yana cewa asalmu alaikum..yace wa Alaiksalam Abu an wuni lfya?.. Daga ta dayan bangaren mahaifin nasa yace masa lafya kalau alhamdullh mahmud ya kuma akaji da hakurin wann matar data rasu??


Yace hakuri Alhamdullh.


babu yabo ba fallasa yace toh Allah ya jikinta ya mata rahma, Allah ya saka namu in taxo tazo mana da sauki.


yace Ameen ya rabbi."


"kuma da kuka tsayawa wann marainiyar yarinya Allah ya baku lada ya dora muku shi a mizani.

Engr yana amsashi acikin jimantawa yace hmmmm mutuwa nasiha ce mahmuda.Toh wann sai ya zame maka ishara, ka kuma sani bawai Allah bayason wann yar yarinya bane ya dauke mata gatan ta a duniya, dukkan mu yan adam a bisa kan hanyar jarabawa muke rayuwa, Allah yay mata hakane dan ya jarabeta ta, kaima da ka taimaka mata ba ikonka bane Allah ne ya nufa zaka samu wann ladar.


Engr yace hakane abu


Daga nan Nasiha masu shiga jiki ya dinga jero masa akan qaddara yana kawo ayoyi da hadisai da kisosi har kaman zai sakashi fidda hawaye.


Bayan ya gama kashe mai jiki sai ya danyi shiru 

snn yace mahaifiyarka ta fayyace min duk abunda ake ciki da yan uwan uban yarinyar, kai kuma me kace akan haka!


Ahankli engr Yace Abu dama duk wani abunda ya shafi karatunta nace zan dau nauyi tunda hjy tace zata dauketa a karkashin kungiyarta na marayu


Yace toh madallah amma dai kaji batun kawu nan nata kasan fa shi mutumin kauye kamar taÉ“ababe yake yanzu akan wann abun saiga sun mata hassada sun hanata samun wnn alherin daga tattare daku, 

toh nidai atunani tunda ba haramun bane ai ko kai zaka iya temakawa ta dawo karkashinka gabaki daya inyaso kawai sai arabata dasu tunda zaman nata dasu ba alheri bane. mahmuda kayi tunani wann jihadi ne babba, kuma shi aure ai nufin Allah ne inda Allah be nufa ba bazamu ma kawo tunaninsa aranmu ba..toh zai iya yuwa wata babban kyauta ce da Allah ya karkato maka dashi kai din baka lura ba. 


Cike da rashin fahimtar furuncin nasa engr yace Toh abu aure kuma bangane abunda ake nufi ba?..


Kai tsaye mahaifin nasa yace masa ina nufin tunda ba haramun bane kai me zai hana ka auri yarinyar...

ka fahimceni ni ba tursasa maka hakan nakeson nayi ba kuma bance sai kamin hakan dole ba amma a matsayina na mahaifinka inaga hakan ne dede. Koba dan komi ba kayi dan Allah dan ka ceto rayuwar marainyar nan daga halaka dan muddin kuka barta a hannun wayann bakusan wani irin mummunan rayuwa zata fada aciki nan gaba ba.


ATake Engr ya cire hularsa yahau fifita jin wata zazzafar zufa na karyo masa, gabaki daya yaji zuciyarsa da kwaklsa ta cirke sai yaji yakasa furta wata kalma sai kame kame dayakeyi shikadansa aransa batare da yasan me zaice ba.


Dada kwantar da murya Mahaifinsan yay yanamai cewa karka damu  mahmuda nasan kai É—a ne mai hankli da biyayya dankace min bazaka yi ba ai ba wani abu bane dama shawara kawai nake baka akan abunda zai ficce ka har Agaban ubangiji..babu wani soyayyar da zan nuna maka a duniya face in bida kai ta hanyar da zai kaika ga samun kyakkwan karshe.


Zuciyar engr na bugawa cikin neman dedetu makansa yace "Hakane Abu..hakan ma yay, In sha Allah koda umarni kabani zanbi bare kuma shawara me kyau kabani namaka alkwari in sha Allah hakan za'ayi nagode Allah ya kara girma yasa agama ibada lafiya.


Murmushi mahaifin nasa yay snn yace Allah yay maka albarka mahmuda

...Allah ya tsare bayanka da gabanka snn yasaka wann aure da zakayi ya zamu alheri gareka duniya da lahira.


Muryansa ararrabe Yace Ameen Abu... amma inason amin alfarma nayi dan nazari akai kadan sabida...bai barsa ya kammala zancen ba yana dan murmushi yace dakata mana malam ai duk munyi lissafin wann Mungama magana da ni da mahaifyarka,munsan baka shirya ba dan haka ne ma tacemin koda an daura auren bazata tare agidanka ynxu ba harsai ta gama mata yan shirye shiryenta by then ma an dan samu fahintar juna kaga inka shirya kaita gidanka willingly sai ka zo ka dauketa ku tare acan. Tare da sauke ajiyar zcya yace toh masha Allah hakan yay dama abunda nake so ince kenan.


Mahaifin nasa yace Toh inda akwai wani Abu dai zaka iya gaya mata ai alfarma muke nema awajenka mahmuda duk wani abunda kake so in sha Allah zamu duba.


Yace a'a Abu karka damu in sha Allah zanyi duk abunda kukace din.


Albarka ya dinga sakamai kafin nan ya katse kirar.


Daga nn Komawa yay ya jingina kansa ajikin motarsa ahankli yake furta lahawla wala kuwwata illa billah... hasbiyallah wa neemal wakeel...dan kwata kwata baisan meyakeji aransa ba sabida baiyi tsammnin hukuncin da iyayensa zasu yanke akansa ba kenan.


Wani bangaren  zuciyarsa yana ma abun kallon saukakka wani bngaren kuma tunamasa da rikicin shemau yakeyi dan yasan abune me wuyar dauka awajenta barinma ace mata yar aikin suce, dan yasan  bakaramin wutar balai bane zai huru agidansa wanda hala zai iya jawowa ya rasa matarsa dayake matukar kauna.


And He does not want to hurt shemau in anyway sabida yana sonta aransa bana wasa ba sedei ata wani fannin kuma bazai taba iya butulcewa ko ya saɓawa umarnin iyayensa ba har abada dan haka ya samo masa kamar dolene ma ya amshi batun auren nan.


atake yaji kansa ya cirke  abun na neman tay masa nauyi, zuciyarsa na neman toshewa da tunanin wata mafita...


sake sake yakei aransa har saida abokinsa aliyu ya dan taɓa kafadunsa kafin nan yadan dawo hayyacinshi wanda kallo daya yay masa ya gane cewa ba lafiya.


Yace abokina Meyafaru ko baba ne kuma ba lafiya?


Cikin lumshe ido da budewa engr yace lfyarsa kalau yana saudi arabiya ma.. yace ma zai kiraka anjima....ynxu de wata magana mukayi dashi da take son dagamin hankli.


Alhj Aliyu Yace sirri ne ko zan iya ji?


Yace no bawani abun sirri bane aliyu...kawai cewa yay wai na amince a auramin yarinyar dan mubata daman rayuwa. Nikuma Na amsa mishi na amince amma kai abun na min nauyi a zuciyata gaskiya..i just dnt feel like its a right decision for me now

..wallh akwai matsala a

Aliyu...yadda baba ya kawo zancen rike yarinyar nan tamkar yabani Amanarta ne, amma kuma matata ta gida fa bazata taɓa fahimtar haka ba karshe ma tafara zargina tunda kaga aiki yarinyar take mana.


Alhj aliyu yy murmushi mai sanyi yace haba mahmud wallh ure overthinking it, i knw yin aure gatsau nada wuyar dauka, amma wann ai ba wani abun tashin hankli bane, inde akan fitinar mace ne duk zaizo ya wuce amma farinciki da albakan iyayenka akanka is priceless mahmud, ni ynzu da ace mahaifina na raye i wont mind doing anything for him wallh ko a bola aka tsinceta yacemin na aura zan aura badon komi ba saidan sabida nasan duk duniya sune zasu cigaba da tsayamin alkcin da bani da komi sann sukadai ne kawai zan saÉ“a musu inyi babban asara tunda aljannata akarkashin kafafunsu yake bana matata ba. 


Think about it aynxu ahaka inda ace wani abu zai same arzikinka macen dakake ikirarin kanaso itace zata fara azabtar dakai wata ma rabuwa dakai zatay atake

Dan haka a shawarce ni banga wani abu aciki ba

Just calm down and think about yadda abun zai kasance.


Engr Yace haka ne amma Aliyu still dis is  not easy as u said. I mean taya zan fara gayama shemau cewa nayi aure just like that ....i think is not fair kuma inajin nauyin ince ma baba a daga auren

Zuwa wani lkci..aiko Addini baice in zakama mace kishiya ka mata a sigar da zai daga mata hankli ba.


Aliyu yace hmm zaku tare da yarinyar ne ynxu? 


Yace a'a....bana tunanin hakan just yet sabida za a sakata a makaranta a can Abuja..im talking about the future, kasan dei dolene shema'u tasan nayi aure wata rana sabida dolene inzo na hadasu susan juna.


Aliyu yace toh dont tell her just yet mana tunda bayanzu zaku tare ba

..ka dai tsaya kayita tunanin hanyoyi mafi sauki da zaka fito mata maybe hala kasamu wata yar maslaha da zata billo maka acikin wayann lokutan. 


Engr Yace toh nasan hakan zaiyu, tunda mama ne tace zata riketa for the main time amma ina tsoron wani abu yaje south wallh dan shemau bata da sauki ko kadan


Murmushi Aliyu yy yace tunda ba da niyyar cutar da ita kayi ba nothing will go south.. kawai kayi Adalci snn ka kula da yarinyar koba dan komi ba bakasan albarkan dake tattare da ita ba.


Suna cikin wann hirar aka zo aka kirawosu lokcin hajy badiatu tay iya bakin kkrinta wajen lallama hafsa dan ta aure danta

Sede da kyar da wahala hafsat din ta amince badan komi ba saidan mummunan tsoron shemau datakeji aranta sedei jin hajy tace mata agidanta na Abuja zata zauna yasaka taji dan dama dama amma ko kadan aranta bason auren takeyi ba kawai dan bata da yadda ta iyane.


Koda aka baje magana Kawunanan nata sun sha baqar mamaki jin cewa baqin nasu sunce zasu amshi auren hansatu atake.


Sede aransu gani suke kamar auren bogine ake nema dan wani dan birni ne zai aure yar kauyen tukuf irin nasu wanda batay ilimi ba kuma ma marainiya??


Hakan yasaka basu wani dau abun da muhinnnci sosai ba.


Daga lkcin da aka binne mahaifiyar hansatun izuwa karfe biyar na yamman ranan aka kammala komi dan uwan mahaifin engr dake zama a kano shi yazo har kauyen ya wakilce auren dake tsakanin jigawa da kanon baki da hanci ne.


Duk wata al'ada ta aure anyi, Nan aka kawo dubu Dari biyar sadakin hafsa aka basu, Nan ma sukay kutunkutun suka hana hafsa ganin sadakinta sukace ai sadakin nasu ne tunda sune ubanninta.


Da yamma lis aka daura auren akofar me garin kauyen, ana kammalawa  basu wani É“ata lkcinsu ba suka bar garin inda har suka fita a kauyen suka nufi gidan alhj aliyu asalin cikin garin jigawa hafsatu bata dena kukan rudani da baqin cikin yadda rayuwarta ya juya mata a lkci guda ba.


Anan sukayi magrib da ishai matar alhj Aliyun ta musu tarban mutunci da mutuntawa sosai, matar tasa mai suna murjanatu cikakkiyar bahaushiyar kano ce yar babban gida datasan darajar dan adam dan ko kadan bata raina yanayin dataga hafsa ba. Koda ta bawa hjy badiatu masauki bata zauna ba,nan da nan ta jawo hafsa suka wuce ciki tamata jagora tay wanka da sabulai masu qamshi ta fidda dauda kyanta ya dada fitowa sarari, hafsa ba fara bace snn bazaka kasaata a layin bakake ba amma wani irin narkakken natural beauty take dashi wanda fuskrta sam baya bukatr wani kwalliya.


Idanuwanta yan dedei ne farare sol gata da shatin saje baki dake nuna alaman yawan suma da Allah ya albarkaceta dashi, girarta ma acike yake tam snn tana da doguwar hanci mai kmr pencil da dan karamin bakinta pink colour me shatin baki kamar an zana mata da gazal, bazaka kuma ce da ita mai kiba ko tsiriya ba dake tana da diri na lafiyayyar budurwa mai fitinannen kyau mai kuma ban sha'awa  kana kallonta kaga zubin bafulatanar jeji futuk.


sabuwar abaya mai kyau matar aliyu ta bata da inner wears new pant da bra ta saka ajikinta duk dama sam taki sakewa da su bare taci abinci.


Aliyu da matarsa Sunyi sunyi akan su kwana musu agidan amma haka engr yace sam, shidai yayi musu alkwari cewa zai kawo musu ita ziyara inkomi ya lafa musu in the future.


Suna zaune suna dan hira hafsa na tare da hjy badiatu ata ciki dan haryanxu jimamin mahafyarta takeyi.


Nan da nan Engr yay booking musu jirgin karfe 8:30pm na dare amma basu samu ba sai aka maida musu shi 9.30pm wanda ya saka suka dada samun hutu kadan.



Dagata fannin victoria kuwa tun kafin dare yay nisa ta isa sabuwar estate din mijinta ya kama ma dan uwanta nile.


Tun tana parking motarta  a haraba ta dinga kallon wajen tana mamaki ganin yadda aka sankamawa gidan security camera ta ko ta ina.


Bata kawo komi aranta ba harta sauka ta karaso gaban apartmnt din nile tay knckng abakin door din after few min wani saurayi yazo ya bude mata kofar ta shigo ciki


Cike da girmamawa gayen yace mata "Gud evening sister vicky..Ta kallesa da fuskar rashin sani atakaice snn tace 'evening young man am here to see nile and who are you?...


Tun bai bude baki ba saiga nile din yana saukowa daga matakala 

As usual looking breathtaking sassnyar murmushinsa mai ratsa zuciya bisa kan fuskarsa yana kallonta direct da sanyayyun ruwan idanunsa. Atake ta daga kai itama tana kallonsa sabida yanada wani irin fitinannen kyaune na fitar hankli.


sanye yake da armless shirt baki da 3qtr shot na kamfanin puma wani irin fresh kafarsa yay acikin lallausar roam about sleepers din da ya zura akafafunsa na kamfanin fenty.


Har ya karaso kasa gabanta bata dauke idanunta akansa ba har saida taji saukar lallausar labbansa agefen kuncinta yanamai cewa hey sis,.. hannunsa ta kama izuwa nata tanacewa Hi Darling "Whats up..ahnkli tace and who is this? Yace ohhh..Gefen abokin nasa ya dawo yana murmushi snn yace this is my friend lucio..kin tunashi tare muka fara scndry schl back in the days,

sumtimes muna canada tare.. He is my gee, even mum and dad knws him very well.


Yana maganan vicky ta kure gayen da idanu sai can kafin nan ta tunasa tafara dago fuskarsa na yaranta  tace ohh okay lucio wilson.. The model guy right?


 Lucio yana murmushi yace yes sister vicky its me.


Tace lu willy???


Dariya suka fashe dashi jin ta ambacesa da  sunansa na yaranta.


Lallai an girma da ahanya naganka ma ai bazan gane ka ba, well is

Nice seeing again lucio


Yace thanks sister vicky. well, am on my out zanje na karbo mana abinci me kikeso kici sai na taho miki dashi.


Tace nothing dear ba jimawa zanyi ba, yanzu zan koma gida.


yace okay bye then daga nan ya fice yabasu waje


Nan Ta juyo kan nile tanata kallonsa kafin nan ta nemi waje ta xauna akan lallausar sofar dake falon, nan shima yazo ya zauna kusa da ita yay shiru.


Tace Ehen kacemun nazo wajenka cikin gaggawa sann nazo kuma kamin shiru..i even tot it was emergency hanklina duk ya fara tashi kawai sainazo naganka looking all fresh and good bama abunda ke damunka a duniyan nan face ka dagamin hankli. 


Yace nooo sister vicky ba haka Bane. Dagaske akwai abunda yasaka nake nemekin kuma yana da muhimmnci.


Tace okay am all ears.

Gayamin da sauri tun kafin abokinka ya dawo dan inada aiki sosai a schl gobe.


Dan shiru yay kafin nan Yace sister vicky dama maganan akansa ne....


Tace okay.


Ahnkli Yy gyaran murya Yace Bance mijinki baiyi kkri ba amma This house and evrything is too boring for me so i tot inna kawo lucio yana taya ni zama it will be fun...


Cikin katsesa tace nile wait..is dat why u call me?


Yace yes amma ki tsaya kiji mana...


Tace kafadamin gaskiya ka kawosane ya tayaka zama as bodygurd ko ya zame maka houseboy dan nafa san halinka sarai nile bazaka iya yin komi makanka ba tsabar lalaci and maybe dats why u needed him...right?


Karamin Dariya yay snn yace nooo sister haba im not that cliche..yes just for security reasons sabida duk neibors dina yan matane yan runs kuma banason cringy situations kinsan yadda karuwan garin nan suke behaving kamar mayu Shiyasa bana son ina zama anan nikadaine


Snn...kiyi imagining  ace wann katotonn gidan nikadai ne aciki sumting can happen to me kuma am surely gonna be depressed.


Tace so what do u want me to do??? Kasan bazan hanaka zama da abokinka ba musmmn ma dayanzu naganeshi sosai ko


Yace yeah nasan bazaki hanani ba. Kai tsaye yace  Amma ai mijinki Yazo dazu da abokinsa wani ana ce mishi henry, sis i dont like the way he talked me about my friend asking me to kick him out sabida bai yarda dashi ba. Kinga tun farko abunda yasaka nace miki banason na zauna a karkashin kowa kenan.

Ke kanki kinsan bana zama a inda za'a yi controlling rayuwana bcos i am not a child i can take care of my self


Dan haka nakeso pls ki gaya ma mijinki inhar lucio zai bar gidan nan gobe to i will be leaving along with him Cos I can't stay under his control am really sorry sister vicky!!!


Yanayin tune din ya mata maganan cikin nitsuwa da kamala da kuma saukakkiyar harshe kamar abun bai wani darashi ba shiya kashe mata jikinta sosai.


Atake ta fahimce sa ta kuma gane inda ya dosa dan tasan nile baison nuna bacin ransa a fili amma muddin ya kawo karar mutum to ba mamaki ya kuresa ne


Cikin sauke ajiyar zuciya tace oooh god nile, am soo sorry about that amma ka tambayesa dalilin daya saka yace baison lucio ya zauna dakai kode yana da wani hali ne da bakasani ba.


Nile yace i dont think he knws him datbm much agabana fa ya masa wasu tambayoyi harda wanda bai kamata ba.

And Der was noting on lucio.. Lucio yana da business dinsa na boutique baya harka da mutanen banza.


Nikuma Kawai ce min yay bazai amince na dinga kawo abokan banza gidan nan ba,.. like the what the fuck..i m not his child..kuma ke kanki kinsan bana tara abokan banza akan me zaice bazan zauna da namiji dan uwana ba?


Tace calm down nile..

Its okay..naji naka side d amma kayi hakuri naje gida naji ta bakin femi maybe ders sumting dabaison ya gaya maka

Idan naji both side of the story zan yanke hukunci.


Cikin kyabe baki yace what ever.. kema kunsan sabida ke nake zama anan..if not da tun lkcin daya cima lucio mutunci dana mika masa keys din gidansa na bar nan wajen... lucio ne dai dabaida zuciya yace nayi hakuri nide bazan zauna a cimin mutunci haka ba


AYanayin damuwa Vicky tace its okay nile ya isa haka ..ai nace mka zan duba kan maganan. Pls

Kaje ka kawomun wani abu me sanyi nasha.


 bai mata musu ba ya tashi ya wuce gaban wine celler ya hado mata negroni drink ya kawo mata gabanta snn ya zuba mata ice cubes aciki ta amsa ta sha.


Shirune ya ratsa wajen dan Maganganun daya gaya matan ne yaketa yawo acikin kwakwalrta gabaki daya sai taji ranta ya lalace da abunda femin yay, sai sake sake take aranta tana sakawa tana kuma warwarewa yanayinta atake ya sauya gaba daya har bata lura da irin Kallon da nile yake mata ba.


Cikin katse mata tunanin ya dube kayan dake jikinta daya kenan fari kall snn yace "mmmm sis u look like a fairy today.


Scoofing tay bazata snn tace "uff young man,..

stop admiring my beauty kaje kanemi budurwa

...mai tsoron mata kawai!


Dariya yay mai sanyi snn yace da gaske nake kayan ya miki kyau, mmm all white is for angels right..amma ahaka kike zuwa lecturing din looking like a hot cake?


Rolling idanunta tay tace mai "of course no..daga gidan kawata hadiza nake we had a mini girls date..


Cikin kyabe baki yace wow aiku manyan matane kunajin dadin rayuwa, but you knw what acikin kawayenkin nan akwai wacce take balain burgeni.


Da mamaki a fuskarta 

Tace and who is dat.


wayarsa ya ciro a aljihu yay strolling IG snn ya mika mata ta ga hoton halisa ne agaban screen din.. yace this woman, ranar naji dadi da kika zo min da ita.


Tace mmmm so are you now crushing on my halsy?


Da sauri Yace no...kawai de i love how strong she is ne..i mean...she is a matured and emotionally strong person, i think she will be my role model. Dan bakowace mace ba ce zata zamo so calm and bold kamarta,msmn ayadda ake baza magananta a social media kowani lungu ana kirkiran karya akanta dan aurenta ya wargaje .im sure da wata ne haka ya faru da ita da hala ma ta kashe kanta aynzu..


Tay dariya tace yes oo amma ai haka halsy take, she is bold and strong kam da wuya kaga wani abu na baqin ciki ya kaita kan gwiwarta..dan koda abun ya faru da ita ma she didnt really react awfully mune muketa kuka.., kawai de kasan abune mai wuya ka cire abun aranka but she is fine now.


Yace okay send my regard to her when ever u see her and tell her am her biggest fan. 


Tana dariya tace okay ooo Inkanaso wata rana zan jawota muzo mu sake wuni maka anan tunda tana burgeka sosai.


Yace no kibari sainayi budurwa tukuna bana son kizo ki zanca maganan ya dawo wani 

abu nikam baturiya nake so na aura ba yar nigeria ba. 


Tace iyyeee wama zai baka  yar nigeria See you...


Awasa suka kare hirar batare da ya kyaleta tagane cewa ya jawo zancen halisan bane kawai dan suyi raha ya kuma cireta a tunanin dayaga ta tsoma kanta acki, dan yasan dolene zata daga hanklinta akan maganan daya gaya mata ynxu akan mijinta


Suna cikin raharsu sai ga nan lucio ya dawo da kwalayen pizza da kuma hadadden suya a kumshe a leda yana wani irin qamshin yajin tafarnuwa me dadi da tarkacen drinks da cokolote daya kawo ma vicky ta karbi chokolate din tana masa godiya.


Tun basu fara cin abincin ba tace musu ta gaji zata wuce gida.


Ahaka suka bar abincin suka rakata har bakin motar ta snn suka dawo ciki suka cigaba dacin abincinsu acikin kwanciyar hankali.



Daga bangaren shemau kuwa tunda aka barsu su biyun take famar bugan cikin hadiza domin ta gaya mata abunda ake ciki. Sabida yarda da kuma amana yasaka Hadiza bata boye mata komi ba tace mata yanxu hankalin alhaj ya dawo kanta infact hutun dayace zataje ma tare dashi zasuje su shakata a new zealand sai bayn sati biyu zasu dawo.


Sosai shema'u tay mata murna abaki amma har cikin zuciyarta baqirin yake da  tunanin inama ace itace acikin wann yanayin.


Da wann boyayyar baqin cikin aranta ta dawo gidanta tazo ta samu mijinta bai dawo ba, tsaki taja bata ko nemesa ba dan haushinsa tafara ji tana ganin kamar shine ya jawo mata rashin sa'ar datayi aida can be aureta ba hala itama da irin mijn hadizar itama zata aura.

SHARE TO UR GROUPS DAN ALLAH...MY HAND NO GO REACH EVERY WHERE.


SURAYYAHMS 08060712446

CHAT ONLY NO CALLS...

Post a Comment for "Cheaters Club 28"