Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Cheaters Club 27

 _*CHEATERS CLUB...*_ 

 _(Babban goro sai Magogin Æ™arfe...)_ 




#ROMANCE

#FICTION

#ADULTHOOD

#SEXADDICTS

#WOMENPOWER


BY

 _SURAYYAHMS_

 _08060712446_



⏯️2️⃣7️⃣

3:pm na yamma hadiza maitama ta kammala shiryawanta ta taho waje a inda kawayentan suke nan a zazzaune. wani irin nishadi yau takeji acikin ranta, musmmn inta tuna yanayin yadda rayuwa ya ke neman sauya mata acikin dan kankanin lkci.


Dan Ko a mafarki batay tsammanin cewa hidimar su da hjya ramatu zai iya juya al'amari harya sauya mata wani bangarena mugayen halayyar mijin nata ba,yaudin tasha kyakkwan mamaki da alhaj kyari ya zage tare da nuna mata cewa ya girgiza sosai da lamarin da ramatu tazomasa dashi na tsafi da yaudara wanda hakanne yasaka yafaraji aransa cewa lallai hadizarce mace na asali datake kaunarsa tsakani da Allah badon abun hannunsa ba.


All the love and care she was looking for azaman aure wanda bata samu ba adacan saida yau ta sameshi awajensa tasha tarairaya da rarrashi snn ya tsaya ya saurareta yaji dukkan wata matsalarta snn yay mata alkwarin gyarawa.


Yaune karo nafarko da ya barta agida ya wuce business trip dinsa acikin dadin rai sann yana isa S.A din ya kirata ya sanar da ita cewa ya isa.


Duk wani abun duniya da ya damka mata jiyan a sanadin rarrashi bashine damuwarta ba bare har ya sakata acikin wnn farinciki datakeji yanxu,.. iya wann sauyawar nasa izuwa namiji me kulawa da matarsa yafiye mata komi wanda shine ya saka ta kira gaggan kawayenta na amana dansu zo sutayata farincikin da ita kadai ta barwa kanta sirrinsa acikin zuciyarta dan hatta shemau datake iya gayawa komi tay bata fetsa mata zancen cewa alhaj yana neman sauya musu rayuwar aurensu ba. 


kwalliya aka tsantsarawa kyakkwar fuskarta na kece raini,tay masifar kyau gameda wata sassanyar nishadi dake kwance akan fuskarta yanamai karama kyaun fuskarnata annuri mai ratsawa hartacikin  zuciya da gangan jiki..


Tahowa take ahnkli tana murmushi designer dress data saka ajikinta irin Draped gown din nan ne marar nauyi na kamfanin jeager le coulture red in colour da swavroski stones work ajiki ,rigar me fallen neck ne amma jelarsa har kasa yake binta yana bazuwa tana tahowa dei dei kamar wata hamshakiyar sarauniya hannunta da wuyanta sai wal wal sukeyi da tsadaddun gwalagwalai.


Lkcin da ta isko kawayen nata ata inda suka shirya  hidimar tasu gani tayi babu abunda yake tashi atsakninsu face musu da surutayya na mata nayau da kullum. 


faffadar murmushin datake sakewa acikin ranta shine ya fito fili dan ganin su datayi ahakan cikin nishadi yasata karajin wani sabuwar farinciki marar misaltuwa acikin ranta.


tun xuwarsu meenal da shema'u gidan halisa take tare dasu..,vicky na karaso kuwa suka cika dedei and since then it has been Banters here and der ana ta tsokanar juna ana kankaro hira na nishadi wanda zaka iya rantsewa sun jimane basuga junansu ba.


Tsayawa cak hadiza tay daga dan nesa tanata kallon  irin soyayya da aminantaka tare da nishadin dake wanxuwa atsakaninsu ayayinda suke hira mai ban dariya.


Yadda suke bawa bukatun junansu na rayuwa muhimmanci yasaka duk suka aje abubuwan dake gabansu sukaci kwalliyar kure adaka kowa tay kyau tazo gidan domin amsar kirar hadiza duk dama basusan dalilin wann karamar shanawa da ta haÉ—a musu ba.


They All look soo beautiful meenal talba acikin peach colour jumpsuit dinta tun zuwanta ta makale kusa da babban aminiyarta halisa mansa data saka wata hadaddiyar black color cascade mini gown na versace dabai kai kan gwiwarta bama tun da suka zauna tambayar halisan kawai takeyi gameda batun lafyarta duk tabi ta damu, wani bin har tausayinta halisan takeji dan yadda take nuna ta damu da ita sosai zaka iya rantsewa cewa babu wata wanda take sonta da amana kamar meenal arayuwa.


shema'u marafa data saka hadadden golden colour valentino garavani dress dinta up and down riga da wando wanda ya fidda hour glass shape din manyan duwaiwakan ta,tun da tazo bata zauna ba dan ayadda takeji da hadadden dirin jikinta wanda tamkar itace kim kardashian wajen shape.


Tsaye tay agabansu tanakan basu labarin dalilin dayasaka bazata taɓa yadda ta haihu da mijinta engr mahmud ayanxu ba.


Acewarta haihuwa da shayarwa suna lalata siffar mace dan haka batason dirin da Allah ya bata take murzawa ya lalace da wuri bare mijnta yazo ya fara reinata dan tun da aka haifeta tazo duniya kallon matar manya kawai take ma kanta.


 vicky dake tsaye agefenta sam bata amince da wann ra'ayi nata ba, dan haka suka ta rusa musu atsakanin su.. dake ita haihuwar ne ma yake shiga tsakanin ta da uwar mijinta cewa take itakam koda siffarta zai lalace ta dawo mei shape din Amoeba ne inhar Allah ya kawo mata haihuwa zata amsheshi da hannu bibbiyu sabida Æ´aya albarka ne na musammn daga wajen ubangiji.


Kamar yadda Meenal ke bin bayan ra'ayin shema'u akan haihuwa kai da kafa haka halisa ma take bin bayan ra'ayin vicky sosai sabida halisa sosai take son yara duba da taso ne itakadai bata da wani dan uwan jini.


wanda musun nasu ne ya jawo surutayya mai yawa wanda har baka iya jin muryan kowa awajen. saidai hirar tasu ce gwanin ban Dariya,dan a sigar hira ayi nishadi kawai sukeyinshi kowacce Acikinsu na fadin ra'ayinta ne kawai batare da wani manufa ba.


As usual meenal na shiga cikin maganan ne amma sam bata iya fitowa fili ta fadi dalilin bin bayan ra'ayin shemau marafa datake yi saboda aranta ta riga tasan cewa ita da mahaifyarta sunyi agreement akan bazata haihu da mijinta Dr khaleel ba sabida batason taxo ta mutu khaleel din ya gaje arxikinta adalilin abunda zata haifa snn ya auro wata macen su more arzikinta tare.


Ji take da ace ta mutu  khaleel ya mallake dukiyarta gara shi din ya fara mutuwa yabarta a duniya inyaso ita ta mallake harda nashi arzikin..


Shema'u kuwa har da yaran ma ta tsana, gani take kamar a child is a burden, haihuwa ai takura kaine kawai,..ko gaisuwa taje daga an mika mata jinjira sai kaji tana cewa "no please babies are messy"hardly kaga shema'u ta dauki dan wani ta rike a hannunta wanda shiyasa sam batasan darajar yaran da ake kawowa dan suke mata aiki ba.



Ana cikin surutun nan halisa ta hango hadiza acan ta makale a hanya da hawayen farinciki taf a idanunta at same time tanata murmushi...


shirya mini girls to girls date iya yasu yasu kusan dadaddiyar Al'adace data zame musu jiki a tafiyar click din nasu sau tarin yawa sukan shirya ire iren karamin meeting haka domin su baja kolin damuwarsu ko su tattauna wani labari na farinciki kona cigaba ko kawai dan hutawa ko a tattauna wani abu mai muhimmanci daya shafe kawancensun musmn ayanzu da suke kallon kansu kamr yan uwan juna.



MiÆ™ewa halisa tay tana murmushi taje ta jawo hannunta ahankli suka karaso cikin filin dayagaji da hadadden gyara, nan da nan hanklin sauran kawayen ya dawo kanta  suka mimmike tsaye suna murmushi har saida halisa ta karaso tsakiyarsu tare da ita snn ta saketa 


Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke a tsakiyarsu  sann tace you look amazing girls..duka suka amsa da murmushi vicky tanamai cewa we cant wait to hear the good news dan harsashe takey a mind dinta ko ciki hadizan take dashi!!.. 

Shemau tay kamar bata san komi ba.  Murmushi hadizar takeyi snn ta umarce maids suka kawo kala kalan drinks a dump waiter dan kowacce ta dauki kalar abunda take sha. Shemaun ce ta saka hannu ta dauki glass din Mojito mai sanyi ta fara sha,hadizar ta dauki na  margrita, piña colada halisa ta rike snnn ta zuba blocks din kankara aciki, snn meenal talba ta dauki chilled manhattan and lastly vicky ta dauki glass of martini duka suka zubawa hadiza idanu suna masu sauraran abunda zai fito daga bakinta ganin she looks really happy  nevours and emotional at same time.


Cikin lumshe ido da budewa tace okay guys Abu biyu nake son na sanar da ku..na farko marar dadinji ne, na biyun kuma sabanin haka..


Kallon juna sukayi duka Kirjinsu na dan bugawa banda shemau data dan ja baya tanata shan drink dinta ahankli.


Halisa ce tay gyaran murya kadan snn tace toh da me dadinjin zamu fara ko?...


Vicky tace noo halsy. Negative befor positive dai..whats up hadiza whats bad?..


Meenal da shemau basu ce komi ba. Ahnkli meenal din takai drink dinta baki a kwakwarta tanata nazarin shin wani abun baqin ciki kenan da har hadiza zata kirasu duka ta gaya musu while she is still smiling ita da tasan hadiza da rauni da kuma saurin karaya???


Saidai Ko kammala lissafin nata a mind dinta batayi ba cikin sauke ajiyar zuciya Hadiza ta dubesu su ukun snn tace

Vicky,meenal, halsy mijina ne yay aure jiya kuma.....Tunma bata karasa idda kalaman ba Abazata meenal tay Wani tufffff da qarfi ta fetso da drink din data kurba waje tare da dago kanta sama in shock tanamai kallon bakin hadizar looking confused kamar bataji abinda tace da kyau ba..


Hannun vicky harna rawa ta matso kusa da hadizar a sigar i dont quiet get you well,suna hade ido da halisa kusan atare dukansu uku suka ce ..


"Hadiza kkce mijinki ya miki kishiya?


Shemau dake tsaye bata motsa ba Kamar zatay  dariyar tune din da suka furta hakan dashi amma ta fuske  jin Hadiza Tace 'yes..wani irin nunfashi meenal taja snn tace tabdi jam...Juyowa hdzar tay ta kalli shemau snn tace shemau is aware of it cos i called her..

..banason na daga muku hankli ne shiyasa..


Cikin katseta da masifa vicky tace"..No hadiza. Wann ba magana bace i mean Matsalarki ai matsalar mu ce akan me zakice haka??? Kishiya gatsau haka sai kace wani almara?


Halisa ta tsaya in silence batace komi ba danji tay kamr kanta na juyawa.


haka kawai ta tsani taji duk wani mummunan labari da zaina daga mata hankli ko ya saka mata damuwa dan muddin tafarajin hakan to atake ciwon depressiin dinta yake dawowa mata kamar sabo a brain dinta sai taji hanklinta yana tashi sai kuma tafarajin kmr batajin dadin komi.


Kacokam meenal ta aje drink dinta akan table jin tarasa taste din bakinta gabaki daya dan arayuwarta gani take kamar cikin kawayenta duka babu wacce bata fi karfin ayi mata kishiya ba bare kuma ita. Yo me namiji zai nema awaje inhar ya aure daya daga cikinsu? Gani tay Suna da kyau, ga diri, kudi, suna da kuma muhibba acikin sauran mata.


cikin sassarfa ta karaso ta dafa kafadun hadiza datakeji kamar ta mata kuka snn tace babe wai wacce shegiyarce ta shigo gidanki kuma yaushe aka shirya wann abun da bamu sani ba, this is an insult to all of us ..to wabillahillazi sai munyi waje road da ita dan gidanki ba gidan zamanta bane .


Hadiza zatay magana cikin katseta shemau tace guys calm down mana aii ni zan muku bayani, but first mu zazzauna tukuna.


A mugun sanyaye su ukun suka zauna dan lkci lkci guda annurin dake yawo akan fuskokinsu ya dauke cak kamar an walkiya an dauke.


Cike da salon lauyanta magana shemau ta kirkiro part din datake son sujin tahau gaya musu shi acikin sauki 


Dede wajen da ramatu ta tonawa kanta asiri tare da saki uku da alhaj ya dankara mata a daren farkonta iyashi kawai ta gaggaya musu shi.


Sauran zancen kuma duk bata gaya musu ba dan batason suduka su san cewa itace takai hadiza gidan malami sukayi wani abu Na tsafi sai kawai ta nuna musu cewa asirin ramatun ne kawai ya tonu sabida hadiza bata da haqqinsu wanda Kasancewarta kwararriyar lawyer shiya dada sakawa lkci guda kowa acikinsu ta amince da zancen nata batare da wani tantama ba...



Tunda maganan ya fito fili wani sabuwar surutu ya kaure awajen kowa na fadar ra'ayinta as usual shema'u da meenal sune masu nuna cewa sun mugun tsanar kushiya dan haka su sukafi kowa zage zage da dariyar mugunta.


Hadiza na basu sauran labarin yadda abun ya wakana da aka cicciro kayayykin tsafi ajakar ramatu Abun al ajabi amma dariyar mugunta su biyun sukadingayi suna shewa suna tafawa.


Vicky was busy wajen tausar zciyar hadizan tare da dada bata haquri da kalamai masu sanyi ayayinda zancen ya rikikita ma halisa hankli duk tunaninta shine yadda ramatu ta shirya wnn mugunta kamr bazata mutu ba sai taji ta kara tsorata da lamarin duniyar gabaki daya


"Hmmmm Hadiza tay kkri fa.. Ai randa mahmud ya kuskura yace zaimin kishiya wallh rabuwa dashi zanyi inje cahn in nemi mijina tun ma kafin ta shigo gidan dan banason rainin wayo wann ai raini ne...


Shemau ta fadi hakan cikin nuna isa tana jujjuya kai cikin bunkasa da kadadi .


Cikin kyabe baki Meenal tace Tab di jam..ke shema wani wargin ma waje yake samu. Duk fitinan uwar mijina akan cewa batasona ai kinga bata isa ta kawo masa mace tace ya aura ba bayan ina nan ba bare shi kuma..ai

Inkinga khaleel yay aure to ni Amina ali talba na nabar masa duniyar ne amma muddin ina raye wallh bai isa ya auro wata macen ba.


Vicky dake rike da hadiza tace u guys pls banda cika baki dai kar azo ana amai ana lashewa.


Halisa batace komi ba ta dauki taɓarta ta kunna ta zuka ahankli dan gani take kamar har ta mutu hala bazata san dadin soyayya bama bare tasan me akeji in mijinka zai kara aure.


Cikin share zancen vickyn, Meenal tace guys This actually calls for a celebration...wallh naso ace ina nan akayi draman nan badan komi sai dan inga shegiyar tana hauka..


Shemau tace abeg her chapter is closed...

 "good riddance...Vicky ce ta karasa mata da cewa "to bad rubbish!!!


hahahah suka fashe da dariya mai karfi.


Sautin wakar hadiza yar gidan malamai shemau ta saka music player dake wajen suka jawo hadixar tsakiyarsu suka zagayeta suna rawa da jikinsu suna mai mata wakar suna tafi suna balain zugata aciki..


Kai mata!

A rike darajar aure da kyau, A bar hushi da ikon Allah, Dan ikon Allah ya wuce hushi.


Lale Hadiza lale lale

Hadiza yan malamai


Kun ga Hadiza ta burge ni, Ina cikin yawo na, na ga Hadiza ta burge ni

Kun ga Hadiza ta burge ni, Yara suna kiranta amare mata suna kiranta amare, Ni ina cikin yawo Na ga Hadiza ta burge ni


Na aure diya ta amare

Lale Hadiza lale lale,Hadiza yar malamai

Kun ga Hadiza ta burge ni,Ko wa taba Rakumi shi ga hauka, Jaki bai kula da bugu ba, Ko wa taba Rakumi shi ga hauka Jaki bai kula da bugu ba

Lale Hadiza lale lale


Gyara gida Hadiza

Duk naki ne

Gyara wuri Hadiza

Duk naki ne

Gyara mujinki Hadiza

Duk naki ne

Toh ladabi biyayya

Duk naki ne

Ba ni ruwa Hadiza


Sai ta durkusa

Ba ni hura Hadiza

Sai ta durkusa

Ba ni tuwo Hadiza

Sai ta durkusa

Ruwan wanka Hadiza

Sai ta durkusa

Gyara gida Hadiza

Duk naki ne.....


Lokcin da suke rera mata wakar suna zagayeta Zuciyan ta tarr... Wani nishadi ne ya mamaye ta

Ganin yadda kawayen nata sukayi spicing din wakar dan har kasa meenal da vicky suke kaiwa wajen rausayawa


Shemau tana rausaya kanta na kaduwa kamar tsohowar kadangariya


Chan halisa ta dada kunna hayakin tsadadden tabar marlboronta ta hadashi da shisha pot ta bula masa wuta tana busa shi yana fadada hayaki dan ita bata wani fiye son hayaniya sosai ba.


Wajen gabaki daya ya dau zafi da nishadi sautin wakar tana wani irin buguwa a speaker da sunan hadiza evrywher is giving all the vibes na big babes celebrations.


Bayan nan Aka bude shafukan ciye ciye, an sarrafa namar kaza dana tolo tolo ga shawarma da sinasir, sushi, salad da small chops, ana ci ana babbaka dariya akan lamarin hajy ramatu da kusan ince aynxu ta zama tarihi a hannunsu.


Meenal was extremly proud of yadda hadiza ta zama sanadiyar kawo karshen gagarumar matsafiyar can badan komi ba saidan hakan zai karawa wa clique dinsu daraja a idanun manyan mata bana wasa ba.


Duk wata hamshiyar yar iska irinta idan taji labarin cewa clique din sune suka kawo karshen  ramatu dolene a basu darajawa ta musammn acikin taro.


To make the date very meaningful yasaka hadiza ta kawo wani karamin words games inda kowa zata bada random advice and motivational quotes.


Bayan sun kammala cin abinci sun koshi Akan wani shirgegen turkish capert awajen haka suka zazzauna vicky ce zata ta rubuta sunan kowa ajikin paper sai ta watsashi akasa wanda ya riga bude nashi zai kira sunan wanda yake ciki sai yazo tskiya ya bashi word of advice ko motivation.


Karon farko ana wurgawa akan uwar gayyar ya fado,hadiza tana bude nata papern taga sunan shema'u ne aciki.


Vicky ta kalli shemau tace ki zo tsakiya ki gayama hadiza one Word of advice or motivation


Babu tantama shemau ta  taso ta iso tsakiya tana fuskarta hadiza datake zaune..


Alokacin babu abunda yake yawo a akwarwlta face kishi da kuma kaico.

Dan bansan yadda zan fassara muku radadin yadda takeji aranta kamar qaddararta ne hadiza ta sace mata a duniyan nan ba.


Lumshe ido tay sann ta bude tace "Dear hadiza, i will give a word of advice:  


"Hadiza tana murnushi  tace am all ears.


Sihirtaccen ajiyar zuciya shemau ta sauke snn tace "Cin amana baya taÉ“a zuwa daga wajen makiyi sai masoyi. Cos Friendship's demise, is  a tale of shifting tides."but alwys rembr dat Betrayal is an inherent part of love!!!.


Tafi wajen ya kaure da shi jin kalaman shemaun ya burgesu.... banda hadizar data tsaya shiru cikin sakin murmushi a mind dinta tanamai kkrin fahimtar sakon da shemaun ta jefa mata acikin maganan nata dan magana ce a dunkule wanda yake nuna alamar cewa da akwai sauran rina akaba. 


Murmushin dole kawai takeyi tana cewa thank u amma badan ta fahimce komi ba dan Har shemau ta koma wajen zaman ta zauna hadiza bata dena nazarin kalamanta ba..,tsoro takeji Kode shema'un tasan wani abu akan mijinta ne and she is hiding it from her ko kuma hala kawai shawara take son bata akan ta kula da zuciyarta sosai musmmn wajen trusting mutane.


Ana sake juyawa game din sai takardan ya fado akan vicky wann karon itace zata bawa shema'un option..


Vicky tace oya shema come forwad and choose a Word of advice or Motivation 


Shema'u tace anyone.


Snn vickyn ta taso tsakiya ta dubeta tace..


Dear Shemau.. ure a lawyer the hope of the hopeless. Ina son kina tuna cewa" A duk lkcin da kika tsinci kanki cikin yaqi da gaskiya kisani cewa tamkar kina yaqi da rayuwar wani ne. And dat one person you hurt, might put a whole generation in pain...


Gabaki daya kawayen suka dauka da tafi raf raf raf batare da sun lura da wani irin Shiru da shemau tay jin maganan vickyn ya cakke zuciyarta ba.. sede tun kanfin su juyo kanta a cikin sauri ta bi ta hadiye maganan ta bige da murmushi mai fadi snn tace Thank you vicky i wll do my best and deliver justice..


Who is next?


Ana sake rolling sai ya fado kan halisa da meenal..


Atake meenal tafara sauya fuskarta dan taso ace itace zata bawa halisa motivation ko wani shawara domin ta isar da sakonta a 

dunkule dan haryau gani take kamar halisa bata warke bane sabida aganinta haryau din halisa tana son zach aboye snn zai iya yuwa inya dawo mata wata rana zata amsheshi su shirya Sede ba haka abun ya fado musu ba.


A nitse Halisa ta je tsakiya da karar taɓarta a hannu hadiza da vicky suna dan dariya a sigar neman tsokana shemau tace sssss halsy kafin ki fara, bari mu baki word of ardvice. Kallon junan su sukayi suna dariya kusan atare suka juyo sukace mata"..smokers are liable to die young...

Meenal tace yes so Quit smoking!!!. Dariya halisa ta fashe da shi ganin yadda suka hade mata baki snn ta offing wanda yake hannunta cikin gyaran murya tace "Dear meenalin mummy,..ure rare, ure a gem..but rembr the things u do in life,can only be forgiven but not forgotten!.


Cikin lumshe ido da budewa meenal tace thank you soo much my love snn tay shiru batace komi ba.


Haka aka sake murzawa ya dawo kan meenal da vicky inda ta gayawa vickyn maganan da itama yay tasiri sosai aranta tafara jin kamar is better tafara nemawa kanta mafita dan tabbas tasan bazata iya cigaba da rayuwar datakeyi aynxu agidan aurenta na har abada batare da samun cikakken gamsuwa awajen mijinta ba.


duk dama bata taba fadawa kowa matsalar dake cimata kwarya a aurenta ba amma jitake kamar tafi kowa shiga matsala da damuwa.


is true, the silent battle might be an endless war dat solves no future problem. Amma ta rasa waye zata gayawa wnn maganan batare da ya bata shawarar rabuwa da mijinta ba.


Gani take kamar inta rabu da femi akan wann maganan tay masa butulci snn taci amanarsa duba da yadda yake nuna mata zallan madaran soyayya sama da uban kowa nashi a duniya snn babu wani abu data nema ta rasa awajensa na more rayuwa.


Sede Taji dadi sosai da meenal ta tuna mata cewa life is too short to be unhappy aynxu mafita kawai yakamata ta fara nema ma rayuwarta mai dorewa.


Halisa kuwa bata wani bata lkcin ta wajen nazari akan shawarar da su shemau suka bata ba dan ji take kamar bazata kara amincewa tay wata soyayya anan kusa ba.


Tasani sarai aranta cewa xata iya dawowa normal tay rayuwatta kamar yadda take adacan amma batun soyayya kam yanxu haka ta cireshi gabaki daya a dictionaryn rayuwarta kenan..



Bayan angama wann games din masu salla sukayi salla snn aka dan sha hira vicky ce tafara tafia tabarsu anan sabida kaninta nile daya bukaci ganawa da ita cikin gaggawa.


Meenal kuwa nason ace sun kebe da halisa dominta kawo mata zancen khaleel saidai hakan baisamu ba dan 7:30 pm na dare nayi Halisa ta kira uztaz awaya akan yaxo ya kaita gida ta huta kadan duba da gobe zata sake komawa asibiti domin ganawa da dr khalid.


after few minute ya iso suka rakata har gaban motarta inda tacewa meenal din zata sameta a office dinta gobe.


Tafyrta ke da wuya meenal din ma ta musu sallama ta wuce gidan ta aka bar shemau ita kadai agidan hadiza dan so take abarsu danta kalalleme adiza taji komi da komi dan karda abarta abaya.



Ata dayan fannin kuwa kimanin mintina arbain da biyar aka dauka ana yi ma mahaifyar hafsa aiki


Koda aka kammala saida aka barta tay hutun awa guda sabida ta dawo hayyacinta dan sosai wahala da talauci ya nakasa mata garkuwan jiki, tsabar yunwa ya shigeta da kyar da wahala ragwamar jikinta yake amsar treatment din.


Ahaka dai aka tattaro ta aka dawo da ita ward banda safa da marwa babu abunda mudi yakeyi yanata zzzare ido kamar wanda yaci kudin aika 


duk lissafin shi shine yadda zai isar da sakon shemau dan ya caske dubu gomansa yacikawa rigarsa iska.


Lkcin mahaifyar hafsa  tanakan bacci likita ya aiko yanamai bukatar ganin makusantantarta amma hakanan mudi yay kamar baya wajen ya bi ya share ta tabi ta rasa yadda zatayi, shidai Allah Allah yake ya samu shiga dakin domin ya isar da sakonsa ya bar asibitin  dan badamuwarsa bane halinda suke ciki bare ciwon dake damunta


karshe  Dai alhj aliyu ne yaji tausayinta ya shiga wajen lokutan tare da ita


Suna shiga wajen likita mudi ya garzayo yahau lellekawa ganin bakowa atanan din yasaka yay sanda ya bude kofar dakin ya shiga ahankli


Yana turo kofar ya tsaya cak daga can yanata Kallonta ganin yadda aka sankaya mata igiyar ruwa ga kuma injin taya nunfashi tay wata fayau kamar  busasshiyar itace dan ko motsi batay bare kace arayetake.


Ganinta ahaka yasaka yaji wani iri aransa amma bashi ya hanasa karasowa gabanta da daurarren fuska dan ya tasheta suyi magana ba..


A gefen gadon datake kwancen ya tsaya muryansa kasa kasa yace ke uwar hansatu Da Allah ki tashi muyi wata magana ni fa sauri nakeyi ba zamana zo yi wajenki ba mutum yazo tun sahe babu abunda yasaka abakinsa sai ruwa haba da Allah. 


Jin bata motsa ba yasaka ya dan taɓata a hannu amma sai shiru.


Nan ma ya kara daga muryans yana me umurtanta akan data farka amma sai shiru.


Abunka da jahili bagidaje

Sai yahau masifa yana cewa dagangan tayi shiru taki ta amsa shi dan ta tsanesa tana gaba dashi.


Nan ya fara zazzago mata bakaken magangnu kamar yadda suka saba yanamai ce mata mayya itace ta cinye musu dan uwansu...


Tun daga cikin kwakwalrta ta fara tsinkayo surutayyar nasa tun tana jinsa sama sama Harta fara jinsa garau amma bata iya motsi bare ta iya bude idanuwanta ta kallesa.


Wamu zaki gwadawa iko da hansatu dan kinga yayan mu baya raye? To wallh baki isa ba...


Yadda kikeji ke tantiriyace to mu munsha gabanki.


karshe ma ya hau tonawa kansu asiri cikin bambami, yanamai ce mata sun tsaneta ne sabida itace ta sauya musu dan uwansu daga jahili ya dawo mutumin kirki har mutane suke sonsa fiye dasu, snn yace mata ai asiri suka rufa mata da suka tashi kasheshi suka barta ita araye akan yarta, da sun so tagayyara rayuwarta da sun hada harda ita sun kashe, snn su bar yar tasu dasukeson sukaita makarntar marainiya mai biye biyen maza ko mabaraciya titina na duniyan nan.


Bakaken maganganun dayake fetsa mata yasaka ta fixge kanta da karfi ta farka da tsananin baqinciki da hawaye masu zafi acikin idanunta...


bata ma iya magana amma bai fasa ba, ta inda yake shiga batanan yake fita ba har ya kammala isar da sakonsa da shemau ta basa.. kuka kawai takeyi tana nunashi da yatsa da karsashin Allah ya isa a cikin kwayar idanunta datake zubda ruwan hawaye masu rauni aciki...


Nide Kinji na gaya miki

Karda ki sake ki amince ki tura yarinyar nan binni idan bahaka na rantse miki ba bazaki sake ganinta da idonki na har abada ba dan daga mun karbeta ahannunki aure zan mata da almajiri na taje kauyen jikas acan tay aikin niƙa da surfe.


Da karfi yake mata maganan cikin gadara da iko...É“ari jikinta yakeyi kar kar tanata Kkrin fidda magana abakinta kenan sai aka bude kofar dakin nasu abazata.


cikin sauri mudi ya dawo gefenta cikin sauya fuska ganin mutanen da suka shigo ciki. A daburce ya soma sose sosen kunne yanacewa sannu sannu matar yaya karki motsa jikinki, inadai hansatu ne.. ai nace miki zan je na kirawota. 


Ciki da kame kame ya daga kai yana satar kallonsu engr mahmhud da mahfyrsa daga can bakin kofa, saican yace ina wuninku hajiya da alhaji? Hihihihii Wani kuke nema ne? banan bane dakin agabane..


Mahaifyar engr mahmud hajy badiatu  ta kuresa da idanu batace uffan ba dan kaf zancensa na karshen dayake cewa zai raba hafsa da mahifyta sunji shi akunnensu ita da danta ayayinda suke shigowa ciki.


Bakaramin tausayi matar take dashi ba dan ta saba handling ire iren wann aiyukan na jin kai shiyasa da danta ya kawo mata zancensu hafsa tacemai basuci ta zama ba kawai suzo jigawar tare ta gansu da idanunta musmmn ma dataji yadda suke rayuwa babu me temaka musu ga yunwa ga talauci ga ciwo ga kuma maraici


Engr yace ma mudi sannu malam...kai wayene?


Cikeda kame kame Mudi ya amsa da yawwa sannu ni sunan mudi... yana fadin hakan yanamai kkrin zame jikinshi agaggauce daga dakin dan sosai jikinsa ya bashi cewa sunji irin bakaken magana da tsawar dayake dakamata daga waje.


Dedei zai fice hajiya badiatu tace ikon Allah kai malam kai kuma waye nasu?


Mudi ya juyo yace nine kawun hansatu...yana fadin hakan ya fita da sauri kamar ana hankadashi waje, baki bude hajy badiatu tace ma engr maza kabishi ka kirawo min shi kacemai inada magana dashi tunda shi kawunta ne.


Aladbce engr yace toh mama snn ya fice yabi bayan mudi da sauri ganin bazai cinmasa ba yasaka security suka bishi domun a dawo musu dashi.


Karasowa gefen umman hafsat din hajya badiatu tay da sigar tausayi a fuskarta tana mai cewa sannu baiwar Allah, sannu Allah ya baki lfiya.


Umman hafsa Batace komi ba sai kuka mai sanyi da takeyi tana tuna munanan kalaman mudi wanda ya fi mata ciwo dayace mata sune suka kashe mata mijinta abar kaunarta kuma gatan ta a duk duniya waidan sabida tsanar da suka mata dan ta gyara masa rayuwa da kuma dan yace zai saka yarsa a makarnta tay ilimi.


Inta tuna wani abun da suka mata na tozarci a bayan rasuwarsa sai taji numfashinta ya sarkafe gaba daya bata iya fitar dashi waje, ko ayanzu ji take kamar bazata iya daurewa ta cigaba da rayuwar nan datakey me cike da ababen bqin ciki acikiba. Sedei daga zarar ta tuna da cewa itace gatar hafsa sai taji bata sha'awar mutuwa dan haka take iya bakin kkrinta wajen danne gulluton bakin cikin daya mamaye mata zuciyarta

Ayanxu yake hanata fitar da nunfashi.


Daf kusa da ita hajy badiatu ta zauna harta ta kammala share yan hawayenta kafin nan ta budi baki cikin sanyin murya sosai tace "Ina kwana hajiya?..hjy badiatu tace lafya baiwar Allah ya jikinki..da kyar take kwace maganan daga bakinta daya fayau ya faffashe asanyaye tace lafiya Hajy Allah ya saka da alheri, nagode nagode da kuka taimaka mani naga hansatu,

Nnn...nagode sai kuka ya kufce mata mai karfi mai ban tausayi.


Idanun hajy badiatu atake ya ciko da hawaye mai mugun zafi Ta rikota ajikinta kenan zata soma lallashinta sai ga nan hafsat din ta shigo ciki cikin sauri ta fada ajikinta acikin wani irin raunataccen yanayi.



Lkcin Engr mahmud  da abokinsa Alhaj aliyu suna daga waje lokcin harya saka security sun kirawo masa mudi ya dawo yanata kumbura fuska yana kukkuni.



Duk a tunaninsa hansatun ne take so ta kai kararsa wajen yan boko tunda shide baisan mutanen dayake ganinta dasu din ba kuma bai tsaya dan ya tambayeta koda sau daya ba


Alhaj aliyun ne ke mai da ma engrn abubuwan da likitar ya gaya musu cewa chance din survival din matar baida wani yawa amma cikin ikon Allah zata iya samun sauki.


Daga ciki kuwa tunda hafsa ta iske mahaifyarta suke rungume da junansu gwanin ban tausayi suna kuka wanda yay kama dana rabuwa ta har abada.


..tunda taga hafsa babu abinda take saka mata sai albarka, tare da nasiha akan duk rintsi duk wuya ta rike mutunci

Sann tay hakuri da rayuwa koda itadin bata raye.


Hajya badiatu da take gefensu tanajin wasiyyar da uwa take yi ma yarta atake itama tahau tunawa da nata mahaifyar da ta rasu da jimawa da cutar cancern jini, hawaye kawai take saukewa sosai dan bakaramin tausayi suka bata ba.


...kuma gamida birkicewar da hafsan tay yasaka kusan dukansu dake wajen suka gaggauta shishigowa dakin harda mudi..


Samu sukayi hajy badiatu na kkokwar raba hafsa da mahaifyarta sai rokonta take akan karta mutu ta barta...


Da kyar saida umman nata ta lallameta kafin nan tay shiru..


Nan Hajy badiatu ta gabatar dakanta ita da danta engr mahmd tare da alhaj aliyu tanayi tana mata nasiha akan komi zai wuce talauci maraici da ciwo duk jarabawace ta ubangiji bawai nakaso bane.


Acewarta tazo ne domin su teimaka musu sann suna tare dasu har sai ta sami sauki.


Fadin irin Godiyar da tayi musu har babu iyaka dan tunda take arayuwa babu wanda ya taɓa kawo musu dauki bare kuma taimako.


Tunda suka fara maganar take sakwa alhj mahmud da abokinsa albarka da irin halin imani da rike amanar da sukayi. Akabar mudi da kikkifta mata ido acan gefe yanata Allah Allah ta kallesa dan baison yay asarar dubu gomansa.


Koda hajya badiatu ta dawo kansa da tuhuma nunawa yakeyi cewa sune basu nemi taimakonsu ba.


Duk ta gane cewa baida dandanin gaskiya amma Har hakuri ta bashi snn ta nemi alfarman cewa tanason ta amshi hafsa ta tafi da ita birni a karkashin kungiyarta na marayu.


Tunda yaga hajya na neman alfarmansa a mutunce Mudi ya tubure Yayita fadin maganganu masu zafi yana nuna cewa ai zuwansa nan asibitin ma basune suka sanar dashi ba agari yaji dan haka basa darajashi


Borin kunya ya dinga yana cewa an rainasa  shiyasa aka kawo bare suna tuhumarsa kamar baishida daraja agaban idanunta har ake neman yanke hukunci cikin iko da gadara da bazasu lamunta ba.


Baqin cikin karerayin dayakey yasaka mahifyr hafsat din taja mai Allah ya isa suka rabu baram baram yacemata zai maka ta a kotu domin ai hafsa din yar yayansu ce banata ita kadai ba dan haka basu amince ta yanke wani hkuci a rayuwar hafsa batare da izininsu ba.


Rashin kunyar da fitsarar dunuyan nan saida ya tamfatsa musu baima ga girman hajiyar ba ya zauna ya gaggasa musu maganganu irinta cikakken jahili dan kauyen kayau duk baqin cikinsa dubu gomansa ne da sukeson sumasa asaranshi a wajen shemau yake damunsa alokcin.


Bayan ficewarsa ta dube hajya badiatu hawaye na zuba a idonta tace mata tunda tana iya taimakawa marayu ta taimaka ma yarta ta kubutar da ita daga hannun yan uwan ubanta.  Inde dan itace tabar musu amana hafsa har abada dan bata da kowa da zata mika masa rayuwar hafsa ayanxu inbasu ba.


Hannun matar na rawa ta riko yarta tana cewa hansatu Ko duk duniya zasu tsaneki ki zama me gaskiya, Ko duk duniya zasu gujeki karda ki koma zama a karkashin yan uwan ubanki musmmn ma mudi, wayann mutanen basa kaunar ki basa kaunar rayuwarki. Kisani Allahn daya halicceki bazai barki ahaka ba. In sha Allahu albarka ta na tare dake a duk inda zaki taka a duniyan nan...wani irin jan ajiyan zuciya tay tanamai cewa la ilah illah

SHARE......

Post a Comment for "Cheaters Club 27"