Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Wutsiyar Rakumi Complete Hausa Novel

 *_Typing📲_*




  *_💡HASKE WRITER'S ASSOCIATION_*

      _(Home of expert and perfect writer's)_




   *_💞WUTSIYAR RAK'UMI....!!💞_*

               _(Tai nesa da k'asa)_



                 *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*




*بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ* 


_In the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful._



*_Alhamdulillahi, barkanmu da dake saduwa a wanan littafi WUTSIYAR RAƘUMI...., ALLAH ka bani ikon rubuta abinda zai amfani al'ummar MANZON ALLAH, ka tsare harshena da hannayena rubuta abinda zai cutar daku dani baki ɗaya😭🙏🏻_*


*_Ya rabbi ka gafartama masoyina, mahaifina, da dukkan sauran al'ummar musulmi tundaga zamanin Annabi adam har kawowa yau😭🙏🏻_*


_Ban yarda wani wani yaymin amfani da buk ɗinnanba ta kowacce hanya sai da izinina😊🙏🏻._




*_No. 1_*


                 

                 *_ƘAUYEN ƊILAU_*



          Tun daga farkon dosowa kwanar gidan zaka farajin luguden daga da taɓare, yayinda mata ke arerewa da shewa irinna nishaɗin madaka, hardama masu buɗe hanci su callara guɗa a kwashe da dariya ana ƙara ƙaimi wajen dakan surfen masarar tuwo ko dawa da akeyi.

      Na kutsa kai cikin gidan domin ganema idona wainar da ake toyawa, mata ne da adadinsu zai iya kai goma sha, sun kasu group-group suna daka a turame da aƙalla zasukai huɗu. A gefe kuma ƙarƙashin inuwar dalbejiya wasu matanne dasuka ɗan manyanta zazzaune suna tasu hira da taɓin daddawar sayarwa ta ɗaya a cikinsu, sai wata can gefe tana faman hura wuta a gabanta da bokitan fenti biyu, maida kallona nayi ga wadda ke gefenta tana ta motsa wani abu a tunya tamkar taliya, sai zabga zufa take saboda hucin wutar da itama take aiki kusa da ita, sai kuma da'irar yara daketa sheƙi da ƙasa suna wasa.

       Wanda bai san BABBAN GIDA ba a garin Ɗilau idan yazo zai iya rantsuwa taron biki sukeyi kona suna, sai dai sam ba haka baneba, dukkan waɗannan jama'ar da kuka gani mazauna gidanne, a hakama babu wasu yaran masu wayo da kuma mazan gidan,  wasu sun tafi binni neman kuɗi, yayinda ƙalilan a cikinsu suna waje a majalisun da mazan ƙauyen kan kafa, yara kam wasu an aikesu wasuko hidimar gabansuce ta fiddasu.

             Duk bayanin dazan muku gameda alaƙar jama'ar wannan gida bazaku fahimtaba, dan kuwa ƴaƴan wane dana ƙanne da ƴaƴan ƴaƴa da matansu, kai harma da jikoki sun auro suma kuma sun hayayyafa.

      Malam Buhari shima mazaunine a wannan gida, kuma yana ɗaya daga cikin wannan ahali, matansa uku da ƴaƴa goma cif, matarsa ta farko itace Yalwa, amma suna kiranta da suna baba yalwa, yaranta biyar, uku maza biyu mata, kasancewar mazan sune manya duk sunyi aure, suma matansu na nan acikin gidan, sai ta biyu, Ɗahara, itakam ƴarta ɗaya Ummukulsoom, haihuwarta kusan huɗu amma suna wabi (suna mutuwa bayan ta haihu), sai akan Ummukulsoom ne ALLAH ya barmata, bayan haihuwar Ummu takuma samun ciki, a wajen haihuwar cikinne ta rasu, lokacin Ummu tanada shekara Uku a duniya. Sai amarya Asabe, yaran Asabe huɗu, mata uku sai Namiji ɗaya shine auta.

     Sana'ar Malam Buhari itace Saƙar mafitai da tabarma, fai-fai irinna fulani dadai sauransu, shiyyasa ake cemasa MAI KABA. Bama shiba duka jama'ar gidan wannan sana'ar suce, sai dai kuma wasu sun bari tuni, sai ƙalilan a matan gidan keyi, shidai ya riƙe gam kuma yanacin amfaninta, dan yakan ɗauka yashiga birnin Kaduna da Zaria ya sayar ya dawo gida, wani lokacin kuma ƙanwarsa Laraba dake aure acan take aiko ɗanta ya karɓa kokuma ita tazo da kanta.

      Da wannan sana'ar malam Buhari ke riƙe da iyalansa, sai noma da yake a kowacce damuna.


       Matasan ƴan mata kusan bakwai da shekarunsu bazasu gaza sha biyarba suka shigo a tare, kowacce kanta ɗauke da bokitin fenti alamar ruwa suka ɗebo. Sannu matan dake surfe a tsakar gida suka shiga yimusu, suko suna amsawa kowacce na nufar sashensu.

      Baba Yalwa dake faman zufa a gindin murhu ta riƙe ƙugu bayan taja murfin tukunyar taliyarta ƴar murji ta siyarwa ta rufe.

     ”K Hadiza ina kuka baro Umma?”.

     Wadda aka kira hadiza ta sauke ruwan kanta tana ɓata fuska, “Yo Baba yalwa tana can baya wannan mayen saurayin nata Basiru ya tsaidata wai zai koma makaranta suna sallama”.

     Ashariya baba yalwa ta lailayo ta dire, “Kai amma ƴarnan anyi tsinanniya, to ni kodai lallatseta yakeyima shiyyasa sukabi suka nanuƙe ma juna?”.

     Kwashe da dariya matan gidan sukayi, dukda kuwa akwai surukanta matan ƴaƴanta a ciki. Kafin wata ta samu damar tofa tata Ummu tayi sallama. Tamkar zasuga abinda Baba yalwa ta ambata a jikin Ummu, duk sai suka zuba mata idanu. 

     Gaba ɗaya sai Ummu taji ta ƙara muzanta, sum-sum ta nufi inda baba yalwa take a gindin murhu...

     “Sai yanzu kuka gama iskancin?”.

    Furucin baba yalwa ya daki kunnen Ummu, cikin rikicewa ta ɗaga idanunta da har sun fara tara ƙwalla ta dubeta, “Baba iskanci kuma?”.

     “Oh tambayata ma kike na sake maimaita miki?”.

     A hankali Ummu ta girgiza kanta alamun a'a.

   Baba yalwa taja tsaki, “ki kikaima Hanne ruwan wajenta, dan ita ta rantamin  na ɗora taliyar, tun da ke kinacan wajen saurayi, da kinsan ma bazaki ɗebomin da wuriba ai da bakice zakijeba mai mugun hali kawai, yadai gama lalataki yagano wadda ta fiki a birni ya aure”.

      “Wannan magana ai zaune take baba yalwa, tunda iyayensa suka bijirema wannan auren ai nasan hanyar kuɓuta suke nema”. ‘Cewar Rashida dake ƙoƙarin dama kunun tsamiya itama na saidawa ne’.

      Baba yalwa ta kyaɓe baki tana sauke tukunyar taliyarta a kasa, “To ai idon Ubanta ya rufe ya kasa gane haka rahida, saboda ita ƴar mai ce ba'ason ɓacin ranta, muna nandai maga yanda za'a ƙare kuma ai”.

     Nanma dariya matan suka sanya, kowa yashiga jifan Ummu da magana mara daɗi.

      Ummu dai batace komaiba, ta ɗauki ruwan ta nufi sashen Hanne matar yayansu ta juye mata ruwan ta fito, ganin sauran yaran duk bazasu komaba itama saita nufi sashensu ta ajiye bokitin tana cire hijjabinta daya jiƙe da ruwa, yayinda ƙasan zuciyarta ke ƙuna da tausayin kanta. Tabbas ƴaƴa da yawa marayu sukan tsinci kansu a gararin rayuwa fiyema da nata, maraicin rashin uwa maraicine mai ciwo, sai dai babu yanda bawa ya isa jayayya da hukuncin ALLAH, bayan rasuwar mahaifiyarta riƙonta ya koma hannun kakarsune data haifi mahaifinsu, wato Innayo.

        Kamar yanda na sanar muku tun farko mahaifiyar *_Ummukulsoom_* ALLAH yay mata rasuwa tun tana shekaru Uku a duniya, itace matar Malam buhari ta biyu, ALLAH ya jarabceta da haihuwar ƴaƴa suna wabi, (ma'ana suna rasuwa bayan ta haihu), saida tai haihuwa huɗu ƴaƴan na komawa sanan ALLAH ya zaunar mata da Ummukulsoom, an tayata murna sosai har ALLAH ya sake bata wani cikin, lokacin haihuwarsane kuma ALLAH ya ɗauketa itada cikin gaba ɗaya. Ta tafi tabar marainiyar ƴarta Ummukulsoom.

      Bayan rasuwar mahaifiyar Ummu rainonta ya koma hannun kakarsune, wato mahaifiyar malam buhari innayo, wannan shine dalilin tashin Ummukulsoom cikin tsananin gata, dan innayo batason taji kukan Ummu, idan kuwa taji saitabi ba'asi, daya kasance cikin matan gidanne sai sun fuskanci ɓacin ranta, idan kuwa yaƴansune saita ramawa Ummu.

      Wannan gata da Ummu ke samu fiye da duk yaran gidanne yasaka kowa tsanarta, ko aikane indai Innayo na kusa babu wanda ya isa saka Ummu ko miƙomin. Shi kansa Malam buhari abun na damunsa, dan matansa kullum cikin ƙorafin mahaifiyarsa tafi kaunar Ummu, bata son ƴaƴansu suke. Idan yatari innayo da roƙon taɗan dinga sassauta son da takema Ummukulsoom kodan sauran yaran saita haushi da masifa, har saiya koma yana hurwar bata haƙuri.

        Abin tausayi ga Ummu shine rasuwar innayo lokacin tana shekara tara a duniya, dukda batada girma sosai tashiga damuwa, musamman idan ta zagayo tana buƙatar wani abu ko an daketa tazo kawo ƙara, saita iske ɗaki wayam babu innayo. Haka zata zauna taita kuka tana ƙwala ma innayo kira.

      Wannan halin data shigane ya haddasa tausayinta mai ƙarfi a zuciyar Malam Buhari, gashi dangin mahaifiyar Ummu sun roƙi a basu ita ya hana, dan bayaso ta banbanta cikin ƴan uwanta. Dole suka haƙura suka bar masa ƴarsa.

        Kasancewar sana'arsa bata zaman gida bace ko yaushe sai ya ɗauki amanar Ummu ya damƙama matansa, tareda badata ɗakin uwar gida baba yalwa.

     A gabansa sun amshi wannan amana, harda faɗin ALLAH ya tayasu riƙo.

      Amma malam Buhari na ɗaga ƙafa yakoma wajen sana'arsa sai abubuwa suka canja ga Ummukulsoom, dan kuwa baƙar wahala da tsangwama ta fara fuskanta kai tsaye gasu baba yalwa da ƴaƴansu, kai har dama duk jama'ar gidan. 

         Dukda ƙanƙantarta hakan baya hana a bata uban aikin da yafi ƙarfinta, idan ta ƙiyi kuma a lakaɗa mata duka, ko a saka su Azima sa'anninta su doketa dukda ta girme musu.

     Tun tana faɗama malam buhari idan ya dawo harta fara sabawa tabar faɗa, dan daya koma za'a kuma tsangwama mata fiyema da da.

    Ahaka suka cigaba da zuwa firamare da aka sakasu ita dasu Nusaiba, yayinda suke kuma wayo da banbance dai-dai da akasinsa. Ƙiri-kiri dai Ummukulsoom ke ganin banbanci ga matan Uba, dan zasu yima ƴaƴansu abu amma ita ko kallo bata ishesuba, a tila mata uban aiki amma su Azima na ƙofar gida suna wasansu ko tsakar gida, abinci dai Alhmdllh batada matsalarsa, dan suna bata taci ta ƙoshi, idanma an hanata zataje gidan kakanninta iyayen mamarta taci ta ƙoshi.      

        Ko faɗa tayi dasu Nusaiba koda itace mai gaskiya sai a bata laifi, harma asaka cikin yayyensu wani ya zaneta.

      Idan kaga Ummukulsoom tayi farin ciki to malam buhari yazo gida, a lokacin babu mai cutar da ita sai dai a ɓoye.

       Tun innayo nada rai basiru ɗan maƙwaftan su Ummukulsoom ke tsokanarta da budurwarsa-budurwarsa, hakan bai saka kowa ɗaukar abin da muhimmanciba, dan shima yarone sosai, baifi shekaru biyar zuwa shida yabama Ummu ba, bayan rasuwar innayo halin da Ummu take ciki na wahala ga matan Uba sai Basir kan nuna damuwarsa sosai, idan yaganta tana kuka shine mai lallashinta, idan tace su Nusaiba ne suka daketa saiya rama mata, dan iyayen su Azima sunsha kai kashedi gidansu basiru akan ya kiyayi ƴaƴansu, koda iyayensa sun masa faɗa gobe bazai fasa ramawa Ummu ba idan an cutar da ita.

      Ahaka Basiru yagama firamare shima yabi ayarin yaran garin maza wajen tafiya sakandire, Basiru ƙyaƙyƙyawane sosai, dan ya ɗakko usul na mahaifiyarsa ne data kasance bafulatana, hakanne yasaka yake ɗaukar hankalin mafi yawan yaran garin, sai kiga kowacce tana fatan Basiru ya sota. Hakan na damun Ummu, dukda bawani girmane da itaba, dan soyayyar Basiru ta girmi tunaninta, takan jishi sosai a ranta.

      Rayuwar tacigaba da tafiya a haka har suka kammala firamare, Ummukulsoom na cigaba da fuskantar ƙalu balen rayuwa kala-kala a gidansu, ga tsangwamar ƴan uwanta su Nusaiba dasu Hadiza yaran gidan, duk hanyar da zasubi su dizgata sun sani. Ita dai sai dai tasha kukanta ta share hawaye, randa suka kaita bango itama ta jibgesu, suna dawowa gida iyayensu su kamata su doka.

           Bayan kammala firamare ɗinsu malam Buhari ya yankema zuciyarsa zaiyi ƙundun bala yakaisu makarantar gaba da firamare, wato sakandire (Secondary school).

          Dukda ba'a taɓa hakaba ga ƴaƴan gidan, dan daga firamare ake tsigesu ai musu aure, wasuma basayin firamare ɗin saboda iyayensu basuda sha'awa.

     Amma yayun su Ummu mata biyu da akaima aure, Rabi da Zainaba duk sunyi firamari. Shikuma malam Buhari ƴar sana'arsa dayake fita cikin birni yana ganin yanda yara ke zuwa makaranta sai abun ya birgesa, shiyyasa yay sha'awar saka Azima da Nusaiba da Ummukulsoom da ayanzu sune suka kammala firamare.

        Ummukulsoom tayi farin ciki, dan a koda yaushe Basirunta kance ALLAH yasa abarta tacigaba da karatu, danshi babansa yace bazai masa aure yanzuba sai yaje jami'a, bayaso yay rayuwa irinta yaran garin, auren shekara ashirin. Ummu dai takan sauraresa amma tasan hakan dakamar wuya, tunda sauran yayunsu su Zainaba daga firamare akai musu aure. Sai kuma kwatsam Baba yazo musu da wanan albishir. Aiko da gudu tanufi gidansu Basiru ta sanar masa, daɗi ya kamashi harda rawa agaban Ummu.😂

          Ɓangaren iyayen su Azima kam casukai basu yardaba, haka kawai ƴaƴansu suje su fanɗare, inama laifin wadda sukai anan garin, sudai yaransu sunada mazajen aure, aure suke so ai musu.

       Malam buhari yaja dogon tsaki ya buga rigarsa yabar musu gidan.

       Hakan da yayi ya tabbatar musu da basu isaba kenan, sai hankalinsu ya ƙara tashi, kowacce takai ƙarar malam buhari wajen iyayenta akan aimasa magana, mizaisa yakai musu yara wata makaranta bayan sauran yaran gidanma bama kowa keyin primary ɗinba.

       Maganar tai masifar ɓata ran malam Buhari, ya dage akan babu fashi sai yaransa sunje babbar makarantar sakandiri, su shikenan gidan nasu baza'a samu cigaba ba?, ALLAH ya basu tarin ƴaƴa maza da mata amma yaran maza ma dake sakandire ɗin basufi uku ba, bayan kuma garin ƴaƴa da yawa nayin karatu, harma da matan, saisu gidansu aƙida ta hanasu saka nasu ƴaƴan. To shikam wannan rayuwar ta ishesa hakanan, yanason bama ƴaƴansa ilimi gwargwadon ƙarfinsa, gasu Zainaba nan shekara biyu da aure amma duk sun tsofe saikace ƴan shekara arba'in, kuma ba komai bane sai wahalar rayuwa da rashin wayewar kai na ilimin addini dana zamani.

        Ganinfa Malam Buhari yaƙi tanƙwaruwa dole suka shafa masa lafiya ya saka yaransa makarantar jeka ka dawo ta sakandire dake cikin garin Kudan, dan ƙauyen ɗilau yana gab da Kudan ne.

      Babu irin shige-shigen dasu baba yalwa basuyiba akan karsu Azima suje secondary amma lamari yaci tura, dansu babban tashin hankalinsu ƴar tallar da yaran suke musu suna samo taro da kwabo, yanzunkam babu dama, idan suka fita makaranta tun safe sai bayan azahar suke dawowa, dasunce suyi abu zasuce sun gaji, Ummu ce kawai batada wannan damar, ko tana shigowane akace ga aiki dole tayisa komin gajiyar da tayi.

    Komai dake faruwa yana dawoma malam buhari a kunne, amma sai yay kunnen uwar shegu da batunsu, har iyayen matan nasama ƙin zuwa kiran da sukai masa yayi, danshi yaɗau aniyar insha ALLAHU sai ƴaƴansa sun ɗanɗani zaƙin ilimi.

          Ansha surutai kam marasa daɗin ji akan karatun su Ummukulsoom a gidan, daga baya kowa ya kama bakinsa kuma.

     Ummukulsoom zata iya cewa tafi kowa murna da makarantar, kodan cikama Basiru burinsa, sannan zata samu sassaucin uban aikin datake tiƙa a gidansu da tsangwama, dukda dai tana tare dasu Azima ananma.

      Su Azima kam suna cikin damuwa sosai, dan sufa hankalinsu duk yana kan aure, harsun fara ƴar sayayyar kayan ɗaki da yara ƴammata kanyi ranar kasuwa, amma shine baba yazo ya kawo wanan batun.

         A hankali suka fara sakin jikinsu da sabo da makarantar, harma da yin ƙawaye, Tun su Azima na takaicin wannan makaranta har suka hakura suka fara sabawa, ita dama Ummu ba'ajin bakinta a masu korafi. 

      Sun shiga secondary babu daɗewa Basiru ya zana jarabawar ssce shida sauran yara ɗalibai ƴan uwansa.

      Bayan fitowar jarabawa kuma saiya haye da maki mai ƙyau, dan dama basiru akwai ƙoƙarin tsiya. Babu ɓata lokaci iyayensa suka hau masa shirin komawa zaria da zama, gidan ƙanwar mamarsa, dan mijinta keta ƙoƙarin nema masa gurbin karatu a A.B.U Zaria.

    Sanda komai yagama kammala ya shirya ya tafi, ranar Ummu tasha kuka sosai, su Nusaiba suka sata gaba suna dariya da mata shaƙiyanci, ita dai bata kulasuba.



★.★.★.★.★.★.★.★.★.★.★


    Rayuwa tacigaba da gudu da sauri har zuwa sanda su Ummu suka shiga aji uku na sakandire, bayan sun zana jarabawar jsce.

          A sannan yara ƴammatan gidan su Hadiza iyayensu sukai shirin aurar dasu, kuma duk sa'annin su Ummu ne, Wannan yasaka iyayen su Azima suka tada hankalinsu da bala'in sufa aima ƴaƴansu aure, bazasu yarda yaran gidan duk suyi aure subar nasuba, dan abinda suka kula samarin garin sun fara faɗin ai yaran sunfi ƙarfinsu saboda suna boko.

     Hankalin Ummukulsoom ya tashi matuƙa ganin baba ya amince, ita kuma tanajin daɗin karatun sosai, sannan Basir ɗinta kusan shekara ɗaya da rabi kennan baima zo gidaba, yana Zaria karatu ya ɗauke hankalinsa, tsakaninta dashi sai dai wasiƙa da yake aiko mata idan babansa yaje dubashi saiya bada a kawo mata.

      Badan Malam buhari yaso datsewar karatun su Ummu ba yabada damar samarunsu su turo iyayensu, a kwanaki kaɗan aka kawo kuɗin Azima da Nusaiba, kuma duk ba ƴan cikin ƙauyen bane, Azima cikin Kudan, sai Nusaiba zata auri malaminsu ɗan zaria, za'a kaita zaria kenan.     

       Wannan abu yayma iyayensu daɗi, dan a ganinsu ƴaƴansu sunyi gaba.

       Iyayen Basiru kam haƙuri sukazo suka bada akan sudai basu shiryaba, dan Basiru karatu yakeyi yanzu, idan malam buhari ya amince nanda shekaru Uku babu damuwa, sannan Basiru ya kammala karatunsa, itama tagama sakandire.

       Abin ya taɓa zuciyar malam Buhari, sai yace suje zaiyi shawara to.

     Bayan tafiyarsu yakira Ummu ya sanar mata, sannan yabata shawarar mizai hana ta fidda wani mijin a samarinta, tunda taga sauran ƴan uwanta har an kawo kuɗin aurensu, kuma harda sauran yaran gidan ƴammata za'a haɗa, bazai so ita kaɗai abartaba, yanzu haka nata kawai ake jira a tsaida musu rana.

     Kuka sosai wannan magana ta saka Ummu, dan itadai babu wani saurayi da take kulawa a ƙauyen sai Basiru ɗinta, dan shi kaɗai take tsananin so da ƙauna.     

         Juyin duniya anyi da ita akan ta amince da auren wani saurayi Tanimu da yace yana sonta amma tace itadai Basiru kawai.

      Ganin zata saka kanta a wani hali sai malam Buhari ya yanke hukunci barinta ta koma makaranta da zaman banza da zatayi na jiran Basiru. Wannan abu yamata daɗi, harma fuskarta da yanayinta ya nuna.

    An aje batun Ummukulsoom gefe a yanzu haka, sai shirye-shiryen bikin ƴammatan gidan akeyi watan sallar tsoffi.

      Da baban Basiru yaje dubashi shine yake sanar masa, wannan daliline ya saka basiru zuwa ganin gida babu shiri, Ummu tayi murna da ganinsa, yayinda sauran yara ƴammatan garin suka ruɗe da sake ganin Basirun ya canja fiye da da, yasake zama ɗan gayu, su kansu sauran yaran gidansu Ummu su Hadiza dasu Azima hankalinsu ya tashi, sukazo suka barbaɗama iyayensu zance, dukda takaici ya kamasu babu yanda zasuyi, sai dai sunata ma Ummu fatan tsiya ALLAH yasa anan gaban yace yafasa aurenta.

    Wannan zuwa da basiru yayi kwanansa bakwai, shine yau zai koma makaranta suka tsaya sallama da Ummu ta ɗebo ruwa........


2


   

............Duk hayaniyar yara da matan gidan na sayen taliyar baba yalwa da kunun Rashida Ummu na jiyowa daga sashensu, sai dai ko motsi batayiba balle yunƙurin leƙowa, bata da ko sisi, kuma baba bayanan yana kaduna, tasan kuwa daga Rashida har baba yalwa babu mai bata kayan sana'arsa. Motsin da tajine yasata ɗago idanunta.

     Mariya ƙanwarsu ce ɗauke da robar tanata turiri, da alama taliyace a ciki, ta zauna kusa da Ummu tana faɗin “Umma kinga taliyata, inna ta saimin ta ahirin, nima ina da goma nace a ƙaramin”.

    Cikin murmushin ƙarfin hali da haɗiyar yawu Ummu tace, “Aiko na tayaki murna mariya”.

   Ƴar dariya yarinyar tayi, kafin ta saka hannu a taliyar tana tsakura kaɗan da yarfe hannu saboda zafi. Ummu tace, “Mariya kije ki ɗakko mafici ɗaki saiki fifita, cin abinci da zafi bashida ƙyau ko kaɗan”.

    Mariya ta miƙe tana jan majina da suɗe hannunta, “To Umma tsaremin nadawo, karki bari akuya tacimin”.

    “Bazan bariba insha ALLAHU”.

    Mariya na barin wajen Murja ta shigo itama, zama tayi kusa da Ummu tana cewa “Wai dama kina nan Umma?”.

       “Wlhy ina nan Murja, yau bazaki tallar kunu bane?”.

      “Aina rantse bazaniba alkur'an, kema nazo baki haƙuri akan abinda jama'ar gidanan suke miki, wlhy sam basa ƙyautawa, sun manta keɗin marainiyace, Umma wai miyasa da Basiru yazo baki sake lallaɓashiba kuyi aurenku ki huta da halin banza na mutanen gidannan”.

     Murmushi Ummu tayi, ta muskuta zamanta da miƙe ƙafafu yanda zataji daɗi, “Kai Murja kibar cewa haka dan ALLAH, koyaya banida kamarsu, kumani wlhy yanzu abin baya damuna, maganar Basiru kuma ai ba laifinsa bane, iyayensane sukace saiya gama karatunsa, kuma nima ina son nayi karatu mai zurfi danna taimaki ƙauyennan, kina ganin babu wata fitacciyar yarinya mace a ƙauyenan data taɓa wuce makarantar gaba da secondary fa......”

     Cikin hangame baki murja ta katseta, “Wai Umma tsaya, kina nufin wata bokon kike sha'awar ƙarayi bayan wadda kukayi dasu Azima?”.

      “Murja kinada abin dariya wlhy, to ai bamu gamata ba ma, dan dai an dakatar damune, amma saura shekara uku mugama”.

     “Shekara uku? Kin tsoge sannan Umma, Inaga lokacin haihuwata biyu”. ‘Cewar murja cikin ɗora hannaye duka a kai🙆🏻’.

       Dariya itadai Ummu tahau yi, kafin tabama Murja amsa Mariya ta dawo, dan haka sukaja bakinsu sukai shiru. (Murja tana cikin ƴammatan gidan da za'aima aure, sosai Ummukulsoom takejin daɗin zama da ita, dan tana nuna tausayinta fiye da sauran yaran).


      Har taliya da kunu suka ƙare babu wanda ya kira Ummu yaymata koda tayine, bata damuba, taje ta duba tukunyar tuwonsu taga a kwai sauran gutsatstsari, tsama tayi tazuba miya akai tafita ta ɗumamo a inda su baba yalwa sukai girkin kayan sana'arsu. Babu wanda yace cikanki, itama bata kula kowaba tagama takoma lungunsu tai zaman cin kayanta.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


      Yau takama alhamis ranar da kasuwar Ɗilau keci, da yamma bayan su Azima sun gama hidimominsu sukai shiri tsaf domin zuwa cin kasuwa, tareda aiken iyayensu na sautun abinda za'a sayo musu. Ummu dai na zaune tsakar gida saman turmi, babu alamar ma tayi wanka, hakanne yasaka Murja data fito daga ɓangarensu cikin shirin fita banka mata harara.

    Ummu tai dariya tana dirowa a saman turmin, “Murija mikuma ya faru da harara haka?”.

     “Ban saniba” ‘cewar Murja tana kumbura baki’.

      Ummu ta haɗiye dariyarta da dafa kafaɗar Murja, “Sorry sister, wlhy Baseer ya hanani zuwa kasuwa a zuwannan da yayi, kuma nima sainaga yakamata ace anwuce wajen tuni”.

     “K nifa kidainamin turanci, ƙilama zagina kikayi ban saniba”.

     Cikin zaro idanu Ummukulsoom tace, “Nashiga goma, nifa nace kiyi haƙuri ne, amma ba zaginki nayiba”.

     “Oh, to ai abunne saida bayani, kinsan mu bamusan wannan kwalmaɗe-kwalmaɗen na turawabane”.

    Girgiza kai kawai Ummu tayi tana murmushi, halin Murja sai ita.

      Suna nan tsaye Ummu na gyarama Murja ɗaurinta su Nusaiba suka fito suma cikin gayu, sai wani shan ƙamshi suke da jama su hadiza aji, su adole wayayyune ƴan boko. Kallo ɗaya Ummu tai musu ta ɗauke kanta tana murmushi.

      Azima ta kama yiwa Murja faɗan tana ɓata musu lokaci, sufa zasu tafi su bartane.

   Murja ba kanwar lasa bace, taja dogon tsaki da faɗin “Dalla malama yo ku tafi mana, ko sai akace idan kun tafi basan gane hanyaba? Nifa ba Umma bace da kuka raina, billahillazi danƙarar yarinya zanyi, Aikin banza kawai”.

    Babu wanda ya tanka, dan Murja bata raga musu, idanma dambene jibgarsu take saboda tanada ƙarfinta.

    Ummu tace, “Kedai jeki ku tafi dan ALLAH, kinsan dawani yaji a gidannan sai maganar tazama wani abu daban kuma”.

    Ƙwafa Murja tayi tabi bayansu.

    Ummu kuwa takoma sashensu dantayi koda sharace.


         ★★★★★★★


     Haka rayuwar gidan tacigaba da tafiya, Ummu batajin daɗin zaman amma saboda ta saba ko a fuskarta bazaka ganiba, sai dai idan ankai hakurinta bangone.

    Yauma dai da Ramatu takaita maƙura bayan sun ɗebo ruwa daga rafi sauke ruwan tayi sukahau danbe, aiko taima ramatu jibgar tsiya su Azima ne ƴan rabo.

     Koda suka dawo gida su Ramatu suka zayyane ƙarya da gaskiya, babu wanda yabi ba'asi da maganar murja dake karyatawa tana faɗin gaskiyar abinda ya haɗa.

     Babar Ramatu tasaka lawwali yayan ramatun ya zane Ummu, shiko dama haushinta yakeji tace bata sonshi, yako kamata ya jibga.


       Har bayan magriba Ummu na kukan wannan duka, zataje gidan kakanninta aka hanata, dan matan gidan suna tsoron masifar Inna Laraba yayar mamar Ummukulsoom ɗin.

       Ana tsaka da sallar Isha'i yara ke ihun kiran baban kaduna oyoyo, baban kaduna oyoyo.

    Wani sanyi ya ratsa zuciyar Ummu dan tasan babansune, tana sallame salla ko addu'a batayiba tafito daga ɗakin.

      Fuskarta ta washe da murmushi ganin baba zaune yana shan ruwan da inna Asabe ta kawo masa, ga yaran gidan zagaye dashi suna jiran tsarabar biredi daya saba zuwa da ita.

      Agabansa ta durƙusa tana jiran ya kammala shan ruwan ta gaisheshi, Inna Asabe sai antaya mata harara take da gargaɗi da ido.

     Ummu yitai tamkar bata gantaba, tama sunkuy da kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta.

     Baba daya gama ya kalleta fuskarsa shinfiɗe da murmushi, “A'a Ummukulsoom ɗin baba ce”.

     Fuskar Ummu shinfiɗe da farin ciki ta ɗago tana faɗin “Eh baba sannu dazuwa? Ya gajiyar hanya?”.

     “Alhmdllh Ummukulsoom, ya hutu?”.

     “Baba ai hutu yama ƙare”.

      “Kai kai to lallai yakamata ki koma makaranta kenan, idan lokacin bikin ƴan uwanki yayi saikizo kimusu baici tunda kin dage yanzu makarantar kwana kikeso (boarding)”.

    “To baba nagode sosai, ai lokacinma muna wani hutun”.

       “A to to masha ALLAH, ina sauran ƴan uwan naki?”.

      “Inaga an aikesu ne”. ‘Ummu ta faɗa da sauri saboda uwar harara da baba yalwa data fito yanzu ta maka mata'.

     Tana gama faɗama ta tashi tabar wajen.


       Baba dai ya fuskanci akwai abinda ke damun Ummukulsoom, amma ko a washe gari bai tambayeta ba, saima yashiga mata cuku-cukun transfer zuwa makarantar kwana shida wani malaminsu na firamare batare da ta saniba..

          Bayan kwana uku da hakan yazo mata da albishir, har kuka tayi dan daɗi, yayinta takaici yacika zukatan ahalin gidan. Su Azima sukace sun fasa aure yanzu makaranta sukeso suma.

    Aiko iyayensu suka hayayyaƙo musu da jaraba, harda cewa itama Ummu babu abinda zata samo sai wahala.

     Baba yace, “Can kuganta a ƙwaryarku, lafiya lau yarinyata zatayi ta ƙare da izinin ALLAH”.

     Tsit sukayi kowa yakasa motsi, basuyi zaton shigowarsa ba yanzun, matan ƴaƴa surukansu ko sim-sim kowacce tafara janye jiki tana nufar lungunta.

    Baba ma bai sake tofa komaiba ya raɓa ta gefensu ya shige da itacen girki a kansa, dama daga gona yake ɗauro icce.

      Wannan magana itace ta harzuƙa baba, a washe gari ya saka Ummu ta shirya abinda duk ya dace da wanda baban yakai kuɗi aka shirya mata gidan kakanninta, irinsu ƙuli-ƙuli, yaji, soyayyan Manja da mangyaɗa, gada soyayya dadi sauransu.

      Ganin tafiyar da gaskene sai Ummukulsoom taji duk babu daɗi, tashiga share ƙwalla tana shiga waje-waje yimusu sallama.

     Wasu sumata fatan alkairi, wasuko harda ɗan habaici, itadai bata kulaba, dan duk iyaye da yayye take musu kallo.

         Saida ta biya gidan kakanninta tai musu sallama, gwaggo hinde tsohuwa mai ran ƙarfe hadda ƴan ƙwallanta, dan tun bayan rasuwa ɗahara Ummu take kallo taji sanyi, dan batada yanda zatayine tabarta hannun matan Uba na azabtar musu da ita.

    Ɗari biyar tabama Ummu tana zabga mata addu'a da fatan nasara.


********


      A zaria suka ida sayayyar kayan da Ummu ke bukata, bisaga jagorancin malam Muttaƙa akakai Ummu makarantar kwana ta ƴammata.

     Bayan malam buhari da malam Muttaƙa sunkai Ummukulsoom aka gama duk abinda ya dace da taimakon malam Muttaƙa, sai sukai mata nasiha sanan suka taho suka barota da kwasar sabon kuka, tasha kuka sosai saida taji har kanta na ciwo sannan ta hakura tai shiru. 


     Malam Buhari bai koma Ɗilau ba, kaduna ya wuce, dan yana buƙatar bama garin iska, gakuma hidimar bikinsu Azima dake tunkarowa.


     

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡          


          Ita dai Ummukulsoom zata iya cewa tayi murna da makarantar, kodan cikama Basiru burinsa, sannan zata samu sassaucin uban aikin datake tiƙa a gidansu da tsangwama, dukda dai tana kewar jama'ar gidansu dasu Azima, da daɗi babu daɗi dai ko yaushe suna tare.

        A hankali yau da gobe sai Ummukulsoom ta fara sakin jikinta da sabo da makarantar, harma da yin ƙawaye, yau da gobe har komai ya wuce sukaje hutun farko gida.

    Yaran gidan sunyi murna da ganin Ummu, hakama Murja, sai wasu tsiraru daga matan gida da dama basa cutar da ita, bakuma su hana a cutar da itan.

       A wannan hutuma bata canja zaniba, dan Ummu tacigaba da fuskantar tsangwama ga matan mahaifinta, bata damuba, dan yanzu takuma samun ilimin zaman duniya, ko abu sukai mata basa ganin damuwa a fuskarta, a haka aka shiga shagalin bikin ƴammatan gidan su shida hardasu azima, ranar bikin Ummu tasha surutu wajen jama'a, sai nunata ake da baki idan ta gitta, sannan kuma iyayen su Nusaiba faɗi suke Ummukulsoom tayi kwantai babu miji, iyayen Basiru basa son ta auri ɗansu shiyyasa suka maƙale da karatu yake.

      Daga Malam Buhari har Ummukulsoom basu kula wannan zanceba, saima dangin mahaifiyar Ummukulsoom ne abin ya damesu, dan suma ason samunsu marainiyar tayi aurenta, kodan hutawa da aƙubar matan ubanta, to amma yazasuja da hukuncin ALLAH, fatansu ALLAH yasa hakan shine yafi alkairi.

             Bayan kammala bikin su Nusaiba Ummukulsoom ta koma makaranta ita kaɗai cike da kewar ƴan uwanta kuma ƙannenta, dukda ba shiri sukeba saida taji babu daɗi, Haka dai ta koma makaranta badan taji daɗin hutunba kwata-kwata, saima da baba yazone ƙarshe-ƙarshen zasu komane lokacin biki tasamu sakewa, surutun da aikata mata a taron bikin kuma ya kuma ƙuntata ta.


★.★.★.★.★.★.★


      Haka Ummu tacigaba da karatunta cikin aminci, a bizitin ɗin farko na shigarsu ss2 saiga Basiru yazo mata makaranta, tayi matuƙar farin ciki da ganinsa, tareda mamakin yanda ya canja sosai, yazama ɗan gayu, ƙyawunsa da cikar haibarsa sun kuma bayyana, duk sai taji tama raina kanta, dan nesa ba kusaba Baseer ya tsere mata a halin yanzu. Koda ƙawayentama sukazo gaisheshi tace musu wanda zata aurane casukai ƙarya takeyi, ina ita ina wannan balaraben.

     Itadai dariya tayi kawai, lokacin da zasuje aurenta dashi sa tabbatar da hakan.

     Tun daga wannan busting ɗin kowanne bizitin sai Baseer yajema Ummukulsoom, haɗuwarsu a gidace dai ta ɗanyi wuya, dan duk sanda zaije ganin gida ita tana makaranta, sanda zataje hutu shima yana makaranta.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


*_BAYAN SHEKARA ƊAYA_*


           A wannan shekarar ne su Ummukulsoom ke shirin shiga aji shida, idan kaganta dolene ta birgeka, ta ƙara girma da cika, shiyyasa idan taje hutuma bata yawo kwata-kwata, saboda surutu da ake mata wai tazama Uwar mata a gida babu aure, dan a yanzu haka yaran su azima bibbiyu, Wasuma cikin na uku garesu.

         Takanyi dariya aduk lokacin da aka jefeta da kalmar koda acikin gidansune, musamman idan ta tuna manya-manyan ƴammata dake a makarantarsu, itafa duka-duka shekarun nata sha bakwaine da wasu watanni, amma saboda saɓo ake kiranta uwar mata, lamarin ƙauyensu sai addu'a.

     Tasan abinda yasa ido yay yawa a kanta ita kaɗaice yarinya budurwa da zata kammala secondary, sai yaran gidan mai gari su Harirah, suko bama sa zuwa hutu gida, a hannun yayar mai garin suke zaune a kaduna, shiyyasa babu mai ganinsu balle a ishesu da surutu.

      Wannan hutun dataje gida baba yalwa harda tsareta tana dubata wai ciki gareta, dan taga Ummukulsoom ɗin tayi wata irin cika da buɗewa, ba komai ya kawo hakaba kuwa sai halittar babban jiki da ALLAH ya bata, dan sam Ummu ba siririya baceba, idanma tasamu jin daɗi anan gaba buɗewa zatayi tai ƙiba.

        Sosai zancen cikinnan ya ɓatama Ummu rai, dan haka tai fushi ta koma gidan kakanninta saida tayi sati.

     Dama yanzu bakowanne wahala take juraba, da an takura mata zata barmusu gidanma. Shiyyasa suke cewa idonta ya buɗe taje bariki ta fetsare.


★★★★★


     Ɓangaren Baseer kuma a wannan lokacinne ya haɗu da zankaɗeɗiyar budurwa mai suna Suhaila a makarantarsu, Suhaila ɗiyar manyace, dan babanta nada arziƙi, taso zuwa ƙasar London tai karatun ta, amma sai mahaifiyarta ta matsa akan tayi a gida Nageria. Badan ta soba ta amince, saboda ita kaɗaice mace a gidansu, iyayenta da ƴan uwanta suna masifar sonta. 

       An sama mata gurbin zama ɗaliba anan A.B.U zaria, wanda hakan ne yazama sanadin haɗuwarta da Baseer.

     Tunda ta ɗaura ido akansa ta rikice, dan Baseer cikakken namijine abun so ga kowacce mace, yazama handsome na gaske, ga ƙyau ga tsafta da ilimi, gashi ALLAH yayisa irin mutanennan masu shegen alfahari da taƙama, idan kaga yanda yake yarfa ƴanmata dawani ɗaukar kai saika ɗauka wani ɗan mashahurin attajirine ko mai mulki a Nigeria, bazaka taɓa yarda ya fito daga ƙungurmin ƙauyen Ɗilau baneba.

     Ita kanta Suhaila kallon irinta ƴaƴan masu kuɗi tamasa da farko, musamman yanda taga ƴaƴan manya da ƴanmata masu aji na makarantar dake naniƙe masa yana yarfasu, sannan abokansa duk ƴaƴan manyane, kwata-kwata baya harka da talaka irinsa, nunawama yake yafi ƙarfin saninsu. 

     Abinda yake ƙarama Baseer girma da kima a idanun jama'a shine basirar karatu, ba ƙaramin ƙwaro baneba wajen brain, wannan shine sanadin dayasa ƴaƴan manya ke nane dashi.

       Dukda son Baseer ya mamaye zuciyar Suhaila sai bata tunkareshiba kai tsaye tamkar yanda sauran ƴan matan ke masa, saima suka ƙulla ƴar tsama, data gansa saita shiga tofar da yawu da yatsine-yatsine tamkar taga kashi, kokuma ta bula masa ƙurar motarta. 

     Tun abun baya damunsa harya fara sakashi takaici, yanda ake girmamashi a makarantar da jan mata dayake a ƙasa saboda kyawunsa ace wannan yarinyar tazo tana masa wannan cin kashin?.

     Sai Baseer yafara biyema Suhaila kulum suna cikin faɗa da juna da jifan junansu da baƙaƙen magana. Ahankali sai faɗan nasu yafara komawa shaƙuwa, daganan sai soyayya. 

      Jama'ar makaranta sai dai suka wayi gari sukaga Baseer da Suhaima abokan faɗan juna sun ɗinke sun koma masoya............✍🏻


3


   ...........Yau akaima su Ummukulsoom busting amma ko alamar Baseer ɗinta bata ganiba, sai baba ne yazo mata shi da Inna Laraba, tayi farin ciki da ganinsu tamkar yanda ta saba.

      Baba kasa haƙuri yayi ya tambayeta ina basiru?, dan yasaba duk zuwan da zasuyi anan suke iskeshi ya rigasu zuwa.

    Kan Ummu a ƙasa tace, “Baba bai zoba”.

     Baba yay Murmushi idonsa a kanta, “Karki damu Ummukulsoom, zata iya yuwuwa wani uzurine ya hanashi zuwan, yaron yanada himma, tunda aka kawoki makarantar nan yake ɗawainiya da zuwa dubaki duk bizitin, dukda kuwa shima cikin hidimar nasa karatun yake”.

     Kafin Ummu tace komai Inna laraba ta karɓe da faɗin, “Ai basiru yaron kirkine, ga hankali, banyi zaton zai riƙe alƙawari irin hakaba, musamman yanda naga ya canja yanzu yazama ɗan birni na sosai, ga tsoron zantukan jama'ar ɗilau akan alaƙarsa da Ummu, kowa faɗi yake yafi ƙarfinta yanzu”.

       Dariya Ummu da Baba suka sanya saboda furucin Inna Laraba da tace yazama ɗan birni, furucinta na ƙarshe kuma yasaka zuciyarsu harbuwa, ita kanta Ummu maganar na damunta, tana dannewane kawai dataga babu wani canji daga Baseer ɗin har yanzu..

      Bayan tafiyarsu duk sai Ummukulsoom tashiga damuwa, dan dama a irin wannan lokacin idan sun tafi akan barta da Baseer ɗintane, sukuku tazama gaba ɗaya, daga ƙarshema saitai komawarta hostel, zuciyarta dai namata fatan ALLAH yasa lafiya ta hanashi zuwa, dan ita tafi zargin koma bayajin daɗine.



⚡⚡⚡⚡⚡

       

     Soyayyar Suhaila tai bala'in ɗauke hankalin Baseer ya fara mantawa da wata Ummukulsoom, gidama yaƙi zuwa, ko waya sukayi da iyayensa sai yace karatune ya riƙeshi.

          Soyayya ce mai ƙarfin gaske a tsakaninsu yanzu, abinma saiya baka matuƙar mamaki, zuwa yanzu kam tagama fahimtar shiba ɗan kowa bane, amma hakan baisa taji ta daina sonshiba, dan ƙyawunsa na ɗibarta matuƙa, aganinta shine miji na nunama sa'a, dan kuɗi ba matsalarta bane, zatabi hanyar da zata ginashi ya jiƙe kafin aurensu, yanda ƙawayenta zasuyi respecting nashi 100%.

        Saima ta samu ƙwarin gwiwar buɗe bakin aljihu tashiga kashe masa kuɗi da masa bajinta tamkar hauka, kai kace itace saurayin shine budurwar, babu ɓata lokaci ta koya masa mota, kaya na ƴan ƙwalisa kam kullum cikin saya masa take, a kwana kaɗan yakuma zama handsome na gaske, ƙyawunsa da taƙamar girman kai takuma bayyana, dan Suhaila har barmasa motarta take wajensa ta kwana, ko an tambayeta a gidan tasan ƙaryar da zata shirma.

     A karatunta sosai yake taimakonta, dukda 100L take, shikuma yana shekarar ƙarshe. 

       Daɗin da Baseer ke samu ga Suhailat yasashi kuma mantawa da Ummukulsoom gaba ɗaya balle alƙawarinsu ko soyayyarta, idanunsa sun rufe Suhailat kawai yake gani, ko yaushe suna nane da juna, sai dai idan ta tafi gida, shima zaka samesu suna charting ko waya.

       Wannan ne yasa har akayi Busting ɗin su Ummukulsoom bai jeba, toshi gaba ɗayama ya manta da lamarinta. 

      Sai bayan busting ɗinne innarsa da yake zaune a wajenta ta matsa masa yaje ganin gida, dan ita lamarin Basiru tsoro yafara bata, gaba ɗaya ya canja, baƙin abubuwa idan ta ganshi dasu ta tambayesa saiyace saya yayi, maƙwafta harsun fara dangantashi da Homo saboda anga ya zama babban yaro dare ɗaya.

       Hankalinta sai ya kuma tashi itada mijinta, dan  sun rasa sana'ar ubanmi yake da yakema kansa hidimar kuɗi, sai daga bayane ta fuskanci mike faruwa shida Suhaila, hakanne yasata shiryawa taje ta zayyanema iyayensa komai gameda halin da yake ciki.

     Hankalinsu yatashi akan Suhaila zata lalata musu yaro, hakkanne yasasu cewa ta turoshi gida.



Humm Baseer, shegiya naira inji ibro⛹‍♀😂.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


          Ummukulsoom kam batasan mike faruwaba, tananan maƙale da son Baseer ɗinta, burinta tagama jarawarnan dake gabanta ta ssce ta koma gida suyi aurensu, ko wani takaicin ya isheta data tunoshi saitaji zuciyarta tayi sanyi, farin ciki ya ziyarceta. Babbar damuwarta da tasan bazasu sake zuwa hutu gidaba sai sun kammala gaba ɗaya, fatanta ALLAH yasa ya ziyarceta ta tabbatar da lafiyarsa ƙalau dai itakam.      

         Wannan damuwar datanemi sakama kanta sai taso taɓa karatunta, sai da ƙawarta Hafiza isa ta zaunar da ita taimata nasiha, da nuna mata muhimmancin wannan lokacin da suke ciki, bai kamata suyi wasa da damarsuba akan abinda zaune yake yana jiransu, itako jarabawar ta taƙaitaccen lokacice.

      Wannan bayani yasaka zuciyar Ummu saisaita, ta nutsu waje ɗaya domin fuskantar jarabawar dake gabansu tareda fatan nasara, dan tasan maganar Hafiza gaskiyace, auren Basheer nacan na jiranta, wannan kuwa lokaci kaɗan za'ayi a gama, kuma ya wuce kenan.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


        Lokacin da Baseer yaje gida jama'a da yawa sunsha mamakin canjawar daya kumayi, gashi yanzu yawani ɗaurama kansa girman kai ba kowa yake kulawaba, gashi yazo a dalleliyar motar Suhailat kuma data bashi aro, hakanne yasa magana keta yawo agari Baseer yayi kuɗi yana ƙyamar ƴan garin.

       Ran iyayensa a ɓace suka shiga masa faɗa akan rayuwar daya ɗaura kansa a yanzu bamai ɓullewa baceba, inashi ina ɗiyan birni ƴar masu kuɗi, ai *WUTSIYAR RAƘUMI TAI NESA DA ƘASA!*, shidama ga matarsa nan na jiransa.

      A razane ya ɗago idanu yana kallon mahaifan nasa, “Baba matata kuma? Yaushe akaimin aure ban saniba?”.

      Harara mahaifiyarsa ta danƙara masa, tareda masa daƙƙuwa, “Basiru kaci gidanku dan ƙaniyarka, koba a ɗaura maka aure da Ummukulsoom ba ai kasan akwai maganarka da ita a ƙasa ko”.

      Taɓɗijan, shifa saima yanzu da suka ambaci sunan Ummu yatuna da itama, yagaji da jan maganar da faɗan da iyayensa suke masa, dan haka yaɗan murmusa yana miƙewa, “To ai indai maganar Ummukulsoom ce kumabar wahal da kanku inna, tananan ko, badai kun ajiye magana da iyayentaba?”.

       “To ina kuma zaka?”.

   “Baba zan zagaya bayine mana”.


        Tunda Basiru yabar wajen sai inna ta riƙe baki da sallalami, baban Talatu anya kuwa yarinyarnan tabar yaronnan hakannan?”.

       “To mizatai masa? Shashancine kawai irin nasa da ƙuruciya, kana ɗan ƙauye irin ɗilau, talaka fitik inakai ina ƴar masu kuɗi ƴar birni? wannan yana ɗaya daga cikin abinda ke tsoratar da irinmu ƴan ƙauye barin yara suyi karatu, dasunje can idonsu ya buɗe saisu kwashi duniya da faɗi, dukda dai bakowa ke koyo banzan halinnan ba na mutanen birni, amma nasan maganinsa ai, ƙwanannan zanje mu tsaida magana da malam Buhari, bazan yarda ya maidani ƙaramin mutunba”.

      “A wlhy ina bayanka baban talatu, gara dai kam a tsaida magana tunda dai dagashi har ita sunkusa kammala karatunma, ai halaccin da waɗannan mutane sukai mana baici ai musu wannan sakayyarba”.

       “To ALLAH dai ya kyauta, ni bara naje nan gonar bakin tafki na ida kai takinnan, garinnan gab yake da saukar ruwan damuna, yanayi nata ƙara canjawa”.

      “To saika dawo, garikam ai yanata harama”.

        Baseer duk yana jinsu, babu abinda yake ayyanawa a ransa sai tayaya zai yakice wannan banzan auren ya huta, ina mai zankaɗeɗiyar yarinya irin Suhaila, ga kuɗi ga ƙyawu zai yarda a ƙaƙaba masa wata baƙauya wadda iyakarta secondary, shima da ƙyar ta harhaɗa, shifa saima yanzu ya fahimci bason Ummukulsoom yakeba, tausayinta kawai yakeyi dama can, rashin wayewar kaine da sanin menene soyayya ya hanashi fahimta. Amma yanzu kar yake kallon komai, degree fa zai haɗa, abinda kaf ƙauyen ɗilau wani bai taɓa yiba saishi, ai dolene ya kuma jama kansa girma a ƙauyennan, jama'r ciki su ƙara fahimtar *WUTSIYAR RAƘUMI TAI NESA DA ƘASA!* tsakaninshi dasu fa yanzu.




Hummm.🚶🏻‍♀☹


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


       Su Ummukhoolsum na gab da gama jarabawa aka kai kuɗin aurenta daga gidan su Basiru batareda shi yasan hakanba, sosai Malam Buhari yaji matukar daɗi da farin ciki, yayinda zuciyar matansa kamar tayi bindiga dan baƙin ciki, koda wasa basa fatan Basiru ya auri Ummukulsoom, babban burinsuma tadawo da ciki.

    Koda malam Buhari ya fahimci hassada ƙarara a fuskokinsu baice komaiba sai girgiza kai da nema musu shirya, baisan mi Ummukulsoom ta tare musuba a gidan da a kullum basa ƙaunar cigabanta, saikace wata sa'arsu ko kishiyarsu.

       Ba wai ranar aurenta da Baseer aka tsaidaba, sundai kawo kuɗin gaisuwa domin su tabbatar har yanzufa suna nan, sun ajiye magana bayan dawowar Ummu da kammala karatun Baseer nanda wata biyar sai a tsaida ranar aure kai tsaye.


      Shidai Baseer da baisan hidimar da akeba kwannasa biyu ya tattara ya koma saboda zasu fara exam shima..


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

      Rayuwa ta cigaba da turawa cikin aminci, Yayinda su Ummu keta zana jarabawa, zuciyarta kuma na maƙale dason Baseer ɗinta, saboda son faranta masama taketa ƙoƙarin ganin tayi abun arziƙi.

 

         Hakama Baseer sunata exam, soyayyarsa da Suhaila nata ƙara ƙarfi, ahankali har sunansa da hotunansa sun baje gidansu Suhaila, sai dai ta ɓoye musu shiba ɗan kowa baneba.

     Koda yayartama taga hotonsa saita rikice da koɗashi tana tambayar Suhailat ɗan wanene a ƙasarnan?.

     Dariya kawai Suhailat tayi, tana faɗin “madam kedai kiga photo kawai, baruwanki da ko ɗan wanene, idan kuma ƴar bayan katanga kike shirin minfa”.

      Dariya Amrah tayi tana dukan kafaɗar, Suhailat da faɗin, “Banza kawai, ɓarauniyar saurayi kika maidanima ashe?”.

      Kwashewa sukai da dariya har mom nasu dake gefe tana saurarensu.

      Suhailat tace, “To ai duniyarce yanzu saida tsaro”.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


       Komai kaga farkomshi to yanada ƙarshe, a yau ne su Ummu suka kammala jarabawarsu, kowannensu kagani yana cikin farin cikin gamawarsu da baƙin cikin rabuwa da juna, sunata musayar lambobi da adireshi.

     Itadai Ummu number wayar baba taita badawa, sannan kanta tsaye take bada address ɗin garinsu, aganinta minene abin ɓoyewa, tushenta shine abin alfaharinta koda kuwa gidansune kawai a ƙungurmin daji, shiyyasa take mamakin wasu ɗaliban dakan zauna suyita sharara ƙarya gidansu kaza da kaza, to randa ALLAH ya ƙaddara zuwan wani kuma yaga ba haka bane sai kaji kunya kenan?.

      Haka dai sukaita sallama da juna har lokacin zuwan baba da yazo ɗaukarta. Ta ƙarasa bankwana ga waɗanda basu tafiba, suka kamo hanyar gida tanata kuka baba na lallashinta.


         Bayan sun iso gida taɗan samu tarbar arziƙi darajar suna tare da baba, ko kaɗan yanzu lamarinsu baya damunta, aganinta ma sun cancanci uzuri.

       Tana samu taci abinci tai wanka saita fice gidan zuwa gidan kakanninta, gwaggo Hinde taji daɗin ganin Ummu, sai godiya takema ALLAH tana ƙari, “ALLAH nagode maka da wannan boko na Umma ya ƙare, kema kizo kiyi aurenki mu huta da surutun jama'ar garinnan, gashinan su Azima harda yaransu bibbiyu, Ramatu da Atine ma cikin na ukune dasu”.

      Murmushi Ummu dake cin gyaɗar da Gwaggo Hinde ke saidawa tayi, sannan tace, “Ohni Gwaggo, irin wannan murna haka, to ai konayi auren nasan Basiru zai barni naciga da bokon, dannifa insha ALLAH saina zama lauya”.

     Galala Gwaggo Hinde tayi da baki har zaninta na neman kwancewa, ta tattaro abinta ta ɗaure tana ajiye kwanon shanruwan hannunta da zata damawa Ummu fura, “Kekuwa Umma anyi lalatacciyar yarinya, yo banda shegantaka miye kuma abin birgewa a bokon? Inama laifin abinda kika samu? Kaf garinan fa dagake sai ƴaƴan maigarine kuka gama wannan bokon, ke da ALLAH can ki maida hankalinki ga gidanan an fara gina miki a faƙon amare”.

      “O ni kuji Gwaggo, to waya faɗa miki shi karatu ana gamashi, ilimi ai kogine, sannan damai neman arziƙi da ilimi bakiji ance basa ƙoshiba? Kuma dan nayi aure sai akace bazan nema ilimin addini dana zamaniba? Haka zamuyita zama babu wani cigaba a garinmu? Nasan Baseeru zaiyi farin ciki da burina shima?”.

     Baki Gwaggo Hinde ta taɓe tareda faɗin, “Ke kikaga zaki iya keda Basirun, shima gashinan anata surutu agari yayi kuɗi yana wulaƙanta mutane, wannanfa karon dayazo amotafa yazo garinan dalleliyama kuwa”.

      “Mota kuma Gwaggo? To shi dake karatu ina kuma ya samu mota?”.

      “Ina zan sani nikuwa, wasu mutanenma marasa tawakkali harsun fara cewa yankan kai ya fara”.

    Babu shiri Ummu ta kwashe da dariya, haka tashiga dariya ba ƙaƙƙautawa, saida Gwaggo ta ɗauki abu ta bugeta dashi sannan ta tsagaita daƙyar, “Kai Gwaggo wlhy dolene aringa cemana gidadawa mu ƴan ƙauye, shikenan wai da mutum yayi arziƙi sai ace yankan kai yakeyi? Toku wama yace muku wai ana yankan kai ɗin da gaskene?”.

       “To Umma ai karkiga laifinmu, mi muka sani da duniya ke ciki?, duk wani abu da zamani yazo dashi mutumin ƙauye sai yaje birni yake ganinsa, idan antashi zaɓen shugabanni da mutanen ƙauye akeyi, amma dasun ɗare madafun iko saikiga bazasu kuma tunawa akwai wasu masu numfashi a jejina ba, duba kigafa wutar lantarki ta gagari ƙauyennan, masu waya kullum suna hanyar zuwa Kudan kai caji, saima kwanannan ne akace balarabe jikan tasalla yasayo injin wuta (Genretor) yafara cajin dashi, kuma waya ɗaya wai Murtala guda, yo inba sana'a kakeba kullum ina zaka ɗauki Murtala (20) guda ka miƙa wai dan kawai aimaka caji”.

      Cikin sanyin Murya da takaici Ummu tace, “Gwaggo ai duk irin waɗannan abubuwan muke dubawa mu dage sai munyi karatun, girman ƙauyennan bai dace ace irin waɗannan cigaban bamu dashiba, ba wuta, babu hanya mai ƙyau, idan ka hawo mashin zaka shigo garinnan ko zaka fita hanjin cikinka tamkar zasu zazzago dan gwazazzabai, ga talauci ya addabemu, ƴar makarantarnan ta gaba da primary ankasa mana, kullum saimunje cikin Kudan, wlhy da ace za'ayi secondary a garinnan iyaye dayawa zasu samu kwanciyar hankalin saka ƴaƴansu karatu, mufa yandama kikasan ba'a ƙasarnan mukeba, kuma mafi yawan ƙauyukan Nageria suna fuskantar waɗannan matsalolin, shiyyasa wani lokacin bancika ganin laifin shugabanni ba, saboda wasu sun fito daga ƙauyukane, suntashi babu mai taimaka musu abaya, shiyyasa dasun sami madafin iko suma saisu fara tsula tsiya da riƙo da kalmarnan ta malam bahaushe *Wutsiyar raƙumi tai nesa da ƙasa*, gwaggo mu kanmu talakawan mun kasa gyara jiyanmu, tayaya muke tunanun shugabanni zasu gyara mana yau ɗinmu, ƙananan yara irinmu masu tasowa mu amfanu da gobenmu jibi tazama ta ƙanenmu, kowa yazo burinsa yayi ɓarnar datafi ta ɗan uwansa”.

       ”Wlhy hakane Umma, shiyyasa wataran kike birgeni akwai zancen hankali idan kinso”.

      Dariya Ummu tayi tana kwanciya a gadon Gwaggo Hinde, “to nidai bara na miƙe a gadon ƴan gayunki Gwaggo karki tadani sai dare, dan ni yauma anan zan kwana”.

     “To kihuta lafiya”. ‘Gwaggo hinde ta faɗa danta kula Ummu na fashin salla ne’.


        Bayan Ummu tasha barcinta ta tashine Gwaggo kemata bayani gameda kawo kuɗin gaisuwar aurenta da akayi daga gidansu Basiru, ance saisun kammala karatu za'a tsaida magana, to yanzu gashi ALLAH yakawo lokacin, tasan kuwa za'a tada maganar kenan.

     Sosai Ummukulsoom taji daɗi, amma saita danne bata nuna a gaban Gwaggo ba, saima rufe fuska da taita famanyi najin kunya.

     Saida taga Gwaggo tafita tsakar gidan taita jin daɗinta da godiya ga ALLAH itama takusa mallakar masoyinta cikar burinta a matsayin miji.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡.


           Tunda Ummukulsoom tadawo bata sami zaman yini ko ɗayaba a gidansu na Babban gida, kullum cikin yawon gaida ƴan uwa da abokan arziƙi take da yayyenta da ƴan uwanta na ma'auri, harma da dangin mahaifiyarta dake garin.

     Yau dai gidan Murja taje, suna tsakar gida itada surukarta suna ɓarar gyaɗa Ummu tai sallama.

    Idanu Murja ta gwalalo na mamaki, kafin ta miƙe cike da zumuɗi tana faɗin “A'a a'a lale marhabun da manya-manya maganin ƙanana-ƙanana, maraba marhabun lalale”.

      Murmushi Ummukulsoom tayi tanamai jin takaici a ranta, Murja dukta canja ta fara komawa tsohuwar ƙarfi da yaji, shekara uku kacal da aure, wai ahakanma ita tanajin daɗi saboda mijinta yana zuwa neman kuɗi legas, kuma yana iyakar ƙoƙarinsa wajen yimata abu, dan bashida wani nauyi mai yawa a kansa, babansa ya rasu, mamarsace kawai a gidan sai Murja da yaranta biyu saikuma ƙannensa mata biyu suma duk sunyi aure. Ummukulsoom ta ƙarasa gaban Lamunde surukar Murja ta durƙusa har ƙasa ta gaidata.

    Da fara'a Lamunde ta amsa tareda mata bangajiyar gama karatu.

     Ummukulsoom tace, “Alhamdulillahi” tana miƙewa.

     Kamar idon Lamunde zai faɗo haka tabi bayan Ummu da kallo, tana ganin sun shige Lungun Murja dake a katange saita riƙe haɓa tana faɗin “Ohni Lami, yarinya tazama Uwar mata a gida babu aure, kanada wannan agabanka ai ko barci mai daɗi kabar yinsa”.

     Su dai su Ummu basusan tanayiba, sunacan hira ta ɓarke a tsakaninsu bayan murja ta ɗeboma Ummu ruwan tulu mai sanyi, tareda ɗaukar ƙalli ƙaƙau ɗinta na saidawa da takeyi ta ajiye gaban Ummu wai tasha iya shanta.

    Dariya Ummu tayi tana ajiye kofin silba datasha ruwa, “wato tawajena kina nan da hali baki sauyaba ko? Yo nama wannan abun cin tuwo ai yau a hanyar bayi zan kwana, wai ina yaran nawane?”.

         “Shi wannan ɗan (ɗanta na fari, bata faɗar sunansa saidai tace wannan ɗan😂) yana gidan innarsu karime, da yaranta sukazo ɗazu ya bisu, Amadu kuwa yanzunan su Lance suka fita fashi gidanmu”.

     “Ok ƙwarai na gamu dasu, kuma naga Rayya da goyo amma dayake hijjab ta saka nama zata ko ɗan Hadiza ne”.

      “A'a Amadu ne, kuɗin ƙalliƙaƙau dasukaimin talla suka kawo, yanzu mikike so na dafa miki? Kinsan ku ƴan gayune ba komai za'a bakuba”.

     Hararta Ummu tayi tana faɗin “A'a ƴan mayu ba ƴan gayuba, ni kinsan komi kika bani cizanyi wlhy”.

     “To shikenan bara afara sayo miki awara gidan tinenen haruna, dan awararta akwai daɗi, dama yau fate muka tashi da sha'awaryi na tsaki, amma tunda kinzo bara adafa hinkafa”.

       “A'a wlhy kuyi fatenku, ni namafi sonshi ai, to kodai munsamu na ukune?”.

      Harar Ummu Murja tayi tana shafa cikinta, “Na Ukun lafiya Umma, duka watan Amadu nawa? Dana bani ai, wlhy banida komai, kawai dai sha'awace jiya naje gidan sunan Safare aka wawashe faten bamu samuba, nikuma na saka abin araina shiyyasa nace yau saimuyi, Inna kuma tace itama tanaso”.

       “ALLAH sarki, haihuwa ta nawa Safare tayi kuwa?”.

    “Ta huɗuce, kinsan ɗanta na biyu komawa yayi ai, yanzu Ukune a raye”.

       “Wayyo ALLAH ya amfana waɗannan ɗin”.

    “To amin, bara na leƙa nan maƙwafta naga ko ade na nan tasayo awaran”.


      Yini guda yau Ummu a gidan murja tayisa, sukasha hirarsu ta zuminci ga fate mai daɗi datai musu, sai bayan isha'i Ummu tabaro gidan.

     Tazo tasha masifa wajen baba Yalwa, wai tatafi yawo batazo ta tayata aikin tuwoba bayan tasan batajin daɗi yau da atini ta tashi.

    Itadai Ummu haƙuri tabata tai shigewarta ɗaki, babama yana zaune yana saƙar tabarma Uffan baiceba.


         Ummukulsoom tacigaba da zaman jiran dawowar Basir, yayinda aketa mata surutun girman datayi, abun na damunta da bata haushi, shiyyasa Gwaggo hinde kullum cikin nema mata maganin baki take, shi kansa baba abun na damunsa, dan haka yasamu mahaifin Baseer akan su tsaida magana a saka rana kodan surutun mutane.

    Baban basiru bai musaba, suka kuma kawo kuɗin sallama aka tsaida biki wata takwas, amma idan komai ya kimtsu kafin wata takwas ɗinma za'ayi a huta kawai, yanzu dai dawowar Basiru ake jira.

    Hankalin Ummukulsoom daduk wani mai ƙaunarta ya kwanta saboda saka ranarnan, baba ma yasamu ya fara shirin tattarawa zai koma kaduna wajen sana'arsa.

    Ummu ta naniƙe akan zata bisa taje ta gaisa Innarsu ƙanwar baba dake kaduna tana aure.

    Bai musaba yace ta shirya, itama ta huta da surutan mutane.

     Wannan tafiya ta saka su baba yalwa takaici, har suka kasa jurewa saida sukayi tsegumi.

    Basu sami amsaba daga baba, ya ɗauke ƴarsa suka nufi kaduna abinsu...........✍🏻


4


   ...........Kasancewar basuyi fitar wuriba sai gab da magriba suka isa cikin kaduna, koda mota ta ajiyesu a kawo sai suka hau napep zuwa Tudun wada anguwar su Inna Harira ƙanwar baba.

    Ita dai Ummu babu abinda take sai kallon hanya, dan wannan shine zuwanta na uku da wayonta dai.


        Gidane madaidaici mai jan murfi baba ya tsaya, ya tura ƙofar suka shiga, a soro ya tsaya yace Ummu tashiga sannan.

     Da sallama Ummu tashiga gidan, budurwar dake a tsakar gida tana kwashe kayan shanya ta amsa mata, duhun magriba ta rufa, gashi babu wuta shiyyasa bata fahimci waneneba, tace,

     “Wacece dan ALLAH?”.

     Murmushi Ummu tayi, dan ta fahimci Azizah ce ɗiyar Inna harirah, dukda dai taɗan jima bata gantaba tun bikinsu Azima. Cikin tsokana Ummu tace, “Ƴar yankar kaice”.

     Maganar saita bama Aziza dariya, dan haka ta sagale kayan da tafara kwashewa a igiyar tare da takowa inda Ummu take a hanyar shigowa.

     Wani ihun murna Aziza ta saka tana faɗin “Kan bala'i Ummukulsoom! Tab wlhy badan fuskarki bata canjaba da ban ganeki ba, sannu da zuwa keda wa?”.

     “Nida Baba ne”. ‘Ummu tafaɗa tana nuna zaure da hannu’.

       Inna Harirah data idar da salla ta leƙo tanama Aziza faɗa, “Wai Aziza kanki lafiya kuwa? da mangaribar ALLAH kiringa kira mana bala'i a cikin gida? Keda wace Ummukulsoom ne?”.

      “Yi Haƙuri mama, wlhy daɗine yasani faɗa ban shiryaba, Ummukulsoom fa ta ɗilau, hardama baba buhari”.

    Da sauri Inna harirah ta ida fitowa daga ɗaki tana gyara ɗaurin zani, “Da gaske ɗiyatace yau agidan? Ina yayan shima?”.

    “Aiko dai itace wlhy mama”.

     Ummu dai dariya taketa musu, yayinda shima baba yay sallama ya shigo.

      Murna sosai takuma kaurewa, dan Inna harira taji daɗin zuwan Ummu, dama kullum cikin yima baba tsogumi take akan rashin barin yaransa zuwa wajemta sosai, mazan sunfi zuwa.

      Alwala baba yayi yatafi masallaci, Ummu ma haka tayi tata agida. 

       Sai da suka nutsu bayan baba ya dawo da malam ɗanjuma baban Aziza sannan aka samu nutsuwar zaman gaisawa da taɗin zuminci. Ummu dai bata iya saka baki sai an sakota, saima Aziza dake  zungurinta idan taji tayi shiru.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


           Ɓangaren Baseer kam Alhmdllh shima yagama jarabawarsa, a yanzu haka satinsu ɗaya kenan, amma yaƙi tafiya ɗilau, wai sai yayi bautar ƙasa (NYSC) ɗinsa sannan yahuta gaba ɗaya kenan.

      Innarsa bataja maganarba, ta shirya taje ɗilau ta sanar musu da yanda sukayi da Baseer, aiko mahaifinsa ya shirya da kansa yabita zaria n, saida yayma Baseer tsiya ta fitar hankali sannan yashirya suka koma ɗilau da baba, babban baƙin cikinsa ma baiyi sallama da Suhailat ba saita waya.

    Abin mamaki tunda Baseer ya dawo ɗilau ya nane a gida baya fita balle kai tunanin zai nemi hanyar gidansu Ummu yaje ganinta. Hakan da iyayensa suka ganine ya sasu zaunar dashi sukai masa bayani gameda aurensa da Ummukulsoom da har an tsaida rana.

    “Baba an tsaida ranafa? Miyasa ba'a bari nadawo anji ta bakinaba? Wlhy ni zanmafa cigaba da karatunane na mastas (masters)”.

      “Kai kasan wani masta basiru, aure dai mun ajiye rana kuma babu fashi, tun watan jiya ma an fara ginin gidanka a faƙon amare”.

      “Inna ban ganeba, ni aka farama gini a garinnan? To na ƙasa kona siminti?”.

     Wane shege kabama kuɗin sayen simintin da za'ai maka ginin bulo da bulo? Basiru wlhy karka kaini wuyafa, bar ganin muna lallaɓaka, kai bazaka dawo cikin hankalinka bane waishin? Wane irin ruɗi duniya da ganga sheɗanne ke buga maka? Banda rashin hankalima inakai ina yarinya ƴar birni ƴar masu kuɗi? Kai kanama ganin iyayenta zasu bakane......?”

      “ALLAH baba zasu bani, naga idan na auri Suhailat kumafa zakuji daɗinnan, dan ɗaukeku zanyi na maida binni.”

     “dalla rufama mutane baki shashasha kawai wanda baisan ciwon kansaba”.

       Shiru basiru yayi yana ɓata ƙyaƙyƙyawar fuskarsa fara tas.


          A ranar da yamma ya shirya yaje gidan su Ummukulsoom, bawai dan taji daɗiba kodan shi yana ɗokin ganinta, a'a soyake yaje yaja mata dogon gargaɗi akan tace ta fasa aurensa, dan yasan hakanne kawai zaisa iyayensa su barsa, soyakema yakoma zaria gobe bazai iya zaman ƙauyennan ba wlhy.

     Koda Baseru yaje ya aika yaro kiran Ummukulsoom sai yaron yace ai bata nan, jiya suka tafi kaduna itada Baba.

      Shiru Basiru yayi takaici na cinsa, haka yabaro ƙofar gidan yanata wani ɗaɗɗaure fuska shi adole mai aji, ko magana wani yay masa a hanya sai dai ya ɗaga hannu yana wani basarwa. Can yakoma bayan gari tafkin da jama'ar ƙauyen ke ɗibar ruwa, yasamu waje ya zauna yana tunanin mafita, ganin wankin hula zai kaishi dare ya yanke shawarar shiryawa yaje zaria koda yini ɗayane ya gana da abokansa su Areef.

     Da wannan shawarar yadawo gida yana shaidama innarsa ashe Ummu taje kaduna?.

         “Au kaduna taje? Ko shiyyasa ɗazun a gidan raɗin sunan Amina Rashida ke cemin ƴata antafi birni?”.

     “Aiko dai inna, nima duk sainaji babu daɗi daban sametaba, inaga gobe idan ALLAH ya kaimu zanje kaduna na yini da yamma saina dawo?”.

      ”A gaskiya ina bayanka kaje, yanda kusan shekara ɗaya kenan baku haɗuba yakamata kaje, itama zataji daɗi”.

     Kallon Inna yayi a kaikaice yana murmushi kawai dashi kaɗai yasan fassarar kayansa, kafin daga bisani ya amsa mata da “to inna”.

      Washe gari kam kamar gaske Baseer yay shiri yace musu yaje kaduna, baba harda bashi kuɗin mota, nanko zaria ya yada zango, ko gidan innarsa baijeba yanufi gidansu Najeeb abokinsa.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡ 


        Ummukulsoom taji daɗin zuwanta kaduna sosai, balle ga Aziza da suke kusan sa'anni, komai tare sukeyi abinsu, Baba ma washe gari yabar gidan, dan dama ba'anan yake zamaba idan yazo, yanada masaukinsa saidai ya leƙo su gaisa.

      Kwanan Ummukulsoom tara a gidan ranar Aziza take ce mata gobe zata koma gidan aikinta, iyalan gidan Alhaji Sufiyan sun dawo daga tafiyar da sukayi.

       Ummu dake kwance tana karatun novel ta tashi zaune tareda ajiye buk ɗin, “Ban ganeba Aziza, aikinmi kuma kikeyi?”.

     Murmushi Aziza tayi tana cigaba da gugar kayanta da takeyi da dutsen guga na gawayi, “Ummukulsoom kinsan rayuwa irinta yanzu ba'a zama, ballemu rayuwa ta birni bakamar taku ta karkara ba, nauyi yayma baba yawa shiyyasa bayan munyi candy naga da zaman banza gara ko wani abun naɗanyi, akwai makwafciyarmu tana nema ma yara gidan aiki shinefa namata magana ta samarmin gidan Alhaji Sufyan, da ƙyar baba ya yarda nafara, itama mama saida naita roƙonta wlhy, nakan musu share-share da goge-goge sai kula da yaransu, duk wata dubu goma sha biyar”. 

       Cikin zaro idanu Ummu tace, “Aziza dubu sha biyar fa? A waɗannan ƴan ayyukan kawai?”.

       “Wlhy kuwa Ummu, shiyyasa suma su baba suka barni, kuma ga alkairi da wataran haka kawai za'ai miki, yanzu haka ɗan anko da ƴan abubuwa na kwalliyar ƴa mace basai na takurama su baba suminba, da kuɗina nakeyi”.

       “A to nima kam ba'a barina baya wlhy Aziza, ni ɗinnan da kina gani an saka ranar biki, ga baba nauyi yamasa yawa shima kuma bawani ƙarfine dashiba, kinga insha ALLAH kafin dai na koma gida wlhy nasamu abin taimakonsa”.

     “Hakane wlhy Ummukhoolsum, kuma tundama bikin ansaka da nisa basai kiyi zamankiba har sai lokacin ya matso, kinga ƙya tara ko yayane”.

       Haka sukaita tattauna maganar, Aziza nakuma wayar mata dakai gameda aikin. Daga ƙarshe suka sanarma Inna harira.

     Shiru Inna harira tayi tana nazarin maganar tasu, dan wannan kam dole ta tuntuɓi yayanta, idan ya amince babu komai sai Ummu ta fara zuwa.

       Da daddare Baba yazo gidan bisaga kiransa da Inna harirah tayi masa a waya, bayan sunyi hirarsu ta zuminci saita zayyano masa zancen aiki da Ummu tace zatayi.

     Da farko dai cayay a'a, saida Inna harira tai masa bayani na gamsuwa sannan ya fahimci maganar, saima ya amince kai tsaye, yace “Harira to babu laifi, yanzune na fahimci zancen naki, idan ita Ummukhoolsum ɗin taga zata iya sai tayi, fatana dai ALLAH ya karesu daga sharrin wasu ƴaƴan manyan na rashin tarbiyya”.

      “To amin yaya, ai lamarinnema yanzu basai ƴaƴan manya ke lalata yaraba, ƴaƴan talakawanma taƙadirane, fatanmu dai ALLAH ya karesu aduk inda suka tsinci kansu”.

     “To Amin ya rabbi harira”.


***********


       Washe gari inna harira da kanta tashiga gidan Rahine taimata bayani a samawa Ummu gidan aiki dan ALLAH, amma na mutanen kirki irin gidan da Aziza ke nata.

       Baki Rahine ta washe tana faɗin, “Wlhy faɗuwa tazo dai-dai da zama, dama maƙwaftan gidansu Alhaji Sufiyan ɗin suna neman mai aiki kuma budurwa kamardai Aziza, kuma suma basuda damuwa, aiko yau ɗinnan ta shirya sainaje na nunata, ALLAH yasa a dace, ina mai tabbatar miki maman Aziza yarinyar zataji daɗin zama gidan Alhaji Mahmud Ajiwa, tsohon sojane mutumin kirki wlhy”.

     Murmushi Inna harirah tayi tana cewa “To Alhamdulillahi, babu damuwa bara na tura miki ita kuwa”.

        “To tayi maza tazo kuwa mutafi, dan ba'a sakaci da irin wanga dama kar wasu su rigamu”.


        Sosai Aziza tai murna dajin gida kusa da kusa zasu ringa aiki, koba komai zasuga juna kullum.

     Itama Ummu taji daɗin hakan, dan haka tafara shiri kamar yanda Inna harira ta sanar mata.


★★★★★★★


      Ummukulsoom na zuwa ta iske har Rahine tagama shirinta itama, dan haka suka fita zuwa gidan aikin.

       Tunda mai napep ya tsaya Ummukulsoom ta saki baki da hanci da idanu tana kallon katafaren gidan, “Oh ALLAH mai rahama mai jinƙai, kiga gini tamkar baza'a mutuba, saima ka ɗauka ba hannune ya ginaba”.

    Dariya Rahine tayi saboda a fili Ummukulsoom tayi maganar, “Kinga muje ciki, keda zakiyi aiki acikinsa miye na santi tun yanzu?”.

      murmushi Ummu tayi tabi bayan Rahine.

       Sai da suka gaisa da mai gadin soja sannan sukai ciki, Duk tsoro ya kama Ummu ganin soja, arayuwarta tana bala'in tsoron soja da ɗan sanda wlhy, kuma batasan daliliba, itadai suna mata kwarjinine kawai.

        Rahine ta katsema Ummu tunani da faɗin, “Kinga Ummukulsoom zauna a gaban Fulawarnan nashiga na shaidama hajiya zuwanki sannan”.

      Ummukulsoom ta amsa da to.

       Kusan mintuna talatin da shigar Rahine saigata taleƙo ta yafito Ummukulsoom da hannu alamar tazo. Tashi Ummu tayi ta nufeta, dama zaman dukya gundureta saboda sojan mai gadin can da take hangowa.

        Da ƙyar numfashin Ummu ya daidaita saboda ganin daular dake cikin falon da suka shiga, ga wata hamshaƙiyar mace dukda shekaru sunja gareta hakan bai hanata cake gayuba tamar zata biki. Duk zumuɗin Ummu na zuwa gidan aiki sai taji jikinta yayi sanyi, ta zauna a ƙasa tamkar yanda taga Rahine tayi. Muryarta har ƴar rawa take tace, “Hajiya ina yini, mun sameku lafiya”.

       Jitai ba'a amsaba, saita ɗago kai ta kalli hajiyar azatonta bataji baneba. Amma sai tayi karo da idon Hajiya na ƙare mata kallo sama da ƙasa. Kanta ta maida ƙasa ta sunkuyar.

     Cikeda isar masu ƙasaita Hajiya Jamila tace, “Minene sunaki?”.

      Ummu ta haɗiye wani yawu daya daskare a maƙoshinta kafin tace, “Ummukulsoom”.

     Kusan minti biyu kafin hajiya tace, “Ba laifi Rahine, tayi, dan nakula tanada ƴar wayewar kai bakamar kidahumar yarinyar da kika kawo ranarba”.

     Rahine ta washe baki tana faɗin, “Alhmdllhi hajiya, amin afuwa da kawo waccan ɗin, ita wannan ai tayi karatu bakamar waccanba”.

     “Yayi” kawai Hajiya jamila tafaɗa tana jawo handbag ɗinta dake gefenta, ƴan dubu-dubu ta jawo aciki tana miƙama Rahine,

      “Ga wannan dubu talatinne, ashirin kuɗin aikinta, biyar kuma ki ɗauka, biyar ɗin kije da ita a wanke mata kai daduk abinda ya dace, kinsan banason ƙazanta hakama yarana, zuwa gobe sai tazo tafara aikinta ko jibi, dan inaga gobe zan yini gidan bikine?”.

      “To hajiya ALLAH ya saka  da alkairi, ya ƙara buɗi, kidaɗe kina zamani Uwargida kuma Amarya agidan Alhaji”.

    Ummukulsoom dai najinsu hajiya ko uffan bataceba, saima yunƙurin miƙewa da takeyi.

    Hakanne ya saka suma suka miƙe suka fito, mamaki nacin zuciyar Ummukulsoom, shin tunkanma ta fara aikin har anfara biyanta albashi kenan?.

        Kasa daurewa tayi, bayan sun shiga napep tace, “Baba wai kenan tunma kafin mutum ya fara aiki suke fara biyansa kuɗi?”.

      Dariya Rahine tayi, “Ai Ummukulsoom kaɗan daga halin kirki na Alhaji Mahmud Ajiwa kenan, kinga wannan albashin data baki? To abinda ya bata na tabbata ya ɗara hakan, amma babu komi ko hakama Alhmdllhi, kafin wani lokaci saikiga kin tara arziƙi, kedai kawai ki kwantar da hankalinki, duk abinda suka nuna basaso karkiyi”.

      “Insha ALLAHU baba zan kiyaye, dan wlhy ni yanayin matarma saiya saka jikina sanyi, sainaga kamar tanada wulaƙanci?”.

      “Ummukulsoom kenan, karki saka wannan a ranki, kedai kawai kiyi abinda ya kaiki, idan har baki shiga hurumin taba bakida matsala da halinta insha ALLAH, yarinyar dana kaimusu kwanaki ƙazamace, shiyyasa suka koreta, kuma karki ɗauka ke kaɗaice mai aiki a gidanfa, a'a akwai wasu, sai dai basa bari su shigar musu sashe, kekuma aciki zakiyi musu aiki bakamar sauran ma'aikatanba”.

       “ALLAH sarki, to ALLAH ya bamu sa'a baba Rahine”.

     “Amin ƴarnan”.


Da wannan firar suka ƙarasa gida, sosai inna harira tai farin ciki da har anfara bama Ummukulsoom albashi, nan take takira baba ta shaida masa. Yace ta adana mata kuɗinta shi babu abinda zaiyi dasu.

      A ranar Rahine ta ɗauki Ummukulsoom takaita shagon saloon domin a wanke mata kai daduk abinda ya kamata wanda hajiya bazatayi tsogumiba.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


          A ɓangaren Baseer kuwa shima ya isa zaria, inda suka samu zama shida shaƙiƙan abokansa uku, Najeeb, Areef da Abdull.

     Abdull dake saman mota zaune ya kalli Baseer dake gefensa yace, “My guy wai ina kaje ka maƙalene anata harka babu kai? Lokacifa yayi da zamu afka camp”.

       Cikin takaici Baseer yace, “Bazaka ganeba Abdull, ina cikin tsaka mai wuyane wlhy, nima hankalina duk yana Camp ɗin”.

     “Mike damunkane?” 

Cewar Areef dake cikin mota amma yabuɗe murfin ya zuro ƙafafunsa waje duka, Najeeb na zaune daga sama shima.

     Numfashi Baseer ya sauke yana jan tsaki, “Wato akwai wata yarinya tun muna ƙanana haka nake tsokanarta irin budurwata-budurwa ta ɗinnan, so ayanzu fa shine su dad suka wani dage wai saina aureta, harma sunkama kai kuɗi an tsaida ranar aure”.

     A tare su Najeeb sukace “Aure!!?”.

    Kansa ya ɗaga musu zuciyarsa nakuma harzuƙa.

       Abdull yace, “Haba guy dole kayi baƙi ka rame, to kai yazakayi da Suhailat ne?”.

     “Ai ba ya zaiyi da Suhailat zaka tambayesa ba, cazakai dama yanason yarinyarne amma yake yaudarar Suhailat?”.

      Harara Baseer ya danƙarama Areef mai maganar, “Areef banason iskancifa, a zancena nace muku tun tana ƙarama nake tsokanarta, kuma tana ɗan shan wahalane a gidansu shinefa nake nuna tausayinta, tosukuma su mom nalura sun ɗauka wani sonta nakeyi har yanzu, mafita nazo kubani ba surutan banzaba guys”.

       Dirgowa Najeeb yayi daga saman mota yadawo kusa da Baseer yana dafa cinyarsa.

     “Bas kawai ka nuna musu kaifa ba sonta kakeba kanada wadda kakeso, ai dai ba aima namiji auren dole naga”.

      “Bazaka ganeba Najeeb, dad ɗina shegen taurin kaine dashi, yanzu dana nuna banayi zaima iya aurota ya ajiyemin kokuma yay fushi dani, adai canja wata shawarar”.

             Tsaki Abdull yayi duk suka kallesa, yace, “Nifa ina takaicin iyaye irinsu dad ɗinnan naka, sai suyita abu kamar basu gama wayewaba, ni shawarata kawai yarinyar zaka samu kaja mata dogon gargaɗi, kokuma mu saceta mu ɓoye, saimuga wadda za'a sakaka ka aura”.

      Kwashewa sukayi da dariya suna tafawa, Baseer yace,

     “Ai matsalar shine batanan tayi tafiya, kuma bansan ainahin inda takeba, kai Areef minene shawararka?”.

     “Ni gaskiya duk shawararku bataiminba, abinda kawai nake gani inhar kanason Suhailat kace tafito kuyi aurenku, ko a gidanka saita cigaba da karatunta, sukuma su momcy idan sunga kadage ga mata kakawo duktaurinsu sai sunyi laushi, kaidai kadage akan ra'ayi ɗaya”.

    Shawarar Areef tayifa, amma gameda dagewa su dad karyayi haka, yabisu ta siyasa kamar yanason aure, sauran shawarar matakin da zaka ɗauka agaba zan faɗa muku”.

      Duk sun amince da shawarar Najeeb ta ƙarshe, dan haka sukabar zancen ahaka.


          Baseer bai koma Ɗilau ba a ranar, saima wajen Suhaulat yaje makaranta sukasha hirarsu har dare, sannan ya tafi gidansu Najeeb ya kwana.

       Da safe ƙanwar Najeeb tazo kawo musu breakfast taga Baseer, rikicewa tayi sosai, dan baƙaramin ɗaukar hankalinta ƙyawun Baseer yayiba, aranta faɗi take dama ana samun indiyawa a cikin hausawa haka?, samun ƙyawawa irin Baseer acikin hausawa sai an tona, itadai ana cewa mutum tara yake bai cika gomaba to zata rantse Baseer yacika cif, dan bataga abin kushewa ko kaɗanba a jikinsa (niko nace tawajen a haline bai cika gomanba ai😂).

       Tsaf Baseer yalura da kallon ƙurillah da Nehal kebinsa dashi, shiyyasa yaketa kuma kamewa yana basarwa, yasan ƙyawun da ALLAH yamasa ba ƙaramin kankaro masa mutunci da kima yakeba wajen Al'umma, shiyyasa yake alfahar da ƙyawun nan nasa, dan shine ƙarfin ikonsa”.

     Nehal dai ta zurma kam akan son Baseer, saidai kunya tasata yin kawaici, yayinda ƙasan ranta ta ɗaura aniyar saita mallakesa matsayin mijin aurenta kota halin ƙaƙa.............✍🏻


 

NO. 5


            Washe gari Ummulsoom da Aziza sukai shirin tafiya wajen aikinsu, inna harirah tai musu nasiha akan su kare mutuncin kasu, tareda doguwar addu'ar kariyar ALLAH.

         Da yamma suka wuce, Aziza tashiga gidan Alhaji Sufiyan Rahine da Ummukulsoom suka shiga gidan Alhaji Mahmud Ajiwa.

         Sun daɗe suna sallama a ƙofar falon kafin a zo a buɗe musu, matashiyar budurwace da zata girmar Ummu kaɗan, amma a mamakin Ummukulsoom sai taga Rahine ta rissina tana gaidata, kuma a haife ta haifi wandama yafi budurwar.

       Itakam sai yamutse-yamutsen fuska takeyi tamkar taga wani kashin safe. A ɗage tace, “Daga ina?”. (Kuma tasan Rahine).

       Rahine ce ta iya bata amsa yanzuma, dan Ummukulsoom tanada sauƙin kai, amma tatsani wulaƙanci a rayuwarta da raini, shiyasa tun abinda hajiya jamila tai musu jiya ya tsaya mata arai.........

      Tunaninta ne ya katse lokacin da Rahine ta zungureta, ta sauke numfashi da kallonta, dan batasan ya aka ƙareba saidai taji Rahine tace “mu shiga ciki”.

        Dukda Ummukulsoom bata saniba zata iya cewa yau duk yaran gidan na nan, dankuwa harda wadda ta kirasu ƴammata biyu tagani sai yarinya da bazata gaza 12years ba, sai saurayi wanda shine zasu iya shekaru dai-dai da Ummu ɗin, sai kuma budurwar da zata iya kai shekaru ashirin da shida, amma yau babu hajiya a falon.

        A ƙasa su Ummu suka zauna daga can bakin ƙofa, ko kallo basu ishi yaranba, daga masu latsa waya da laptop sai masu kallo a tv. Ganin Rahine ta gaishesu itama Ummu saita gaishesu.

     Sau ɗaya suka amsa, shima basu dukabane ba. zaman kusan mintuna ashirin sukayi kafin Hajiya jamila ta sakko daga saman bene, yaudai babu kwaliya jikinta, amma tana sanye da wata doguwar riga (Arabian gown) datasha duwatsu sai walƙiya takeyi, gawani ƙamshi mai daɗi.

      Zama tayi kusada ƙaramar yarinyar fuskarta babu walwala, amma idonta nakan su Ummukulsoom tana ƙare mata kallo taga anmata gyaran da tace?.

      Daga Ummu har Rahine gaidata sukayi, ta amsa sau ɗaya kafin ta ɗora da faɗin, “Kindai faɗa mata aikinta a gidannan ko?”.

        “Eh to hajiya bankai ga sanar matanba kam”.

       Yatsine Fuska hajiya jamila tayi tana maida kallonta ga Ummukulsoom, “Aikinki a gidanan shine gyaran ɗakina da duk na yaran gidannan, sai falon sama, kokuma nace mikima sama gaba ɗaya ke zaki ringa gyarawa, dan ahaka dai na yaba da hankalinki, bansan kuma mike rankiba, babu ƴar aikin dake hawa mana sama sai wadda muka yarda da ita, amma mafi yawanku saiku ƙare da mana sace-sace, to yarage ruwanki ki riƙe amana ko kici”.

      Idon Ummu ya ciko da hawaye, muryarta naɗan rawa tace, “Insha ALLAHU hajiya zaki sameni mai riƙe amana da riƙo da gaskiya”.

      “ALLAH yasa, dan masu aikinnan muna fukaine, farkon zuwa suyita sinne kai tamkar mutanen arziƙi, amma dasunsha jar miya idonsu ya buɗe sai raini wlhy Momcy”. ‘Babar budurwarce mai maganar a ƙufule’.

     Tana kai aya sauran yaran suka kwashe da dariya, wadda ta buɗe musu ƙofa tace, ”

      “Kai aunty Ummayya”. 

 Dariya taɗanyi itama sannan ta taɓe baki.

       Hajiya jamila ta katse zancen yaran da faɗin, “ki kama kanki, ko jaririn gidanan abin girmamawane, karkiga kin girmi wasu aciki kice zaki takasu, neman arziƙi kikazoyi a gidansu, babu talakan da zaizo ya ƙun tatamin yara. Kalli abinda zan nuna miki”.

      Idon Ummu cike da ƙwalla ta ɗago ta kalli hajiya Jamila data fara nuna yaran da ɗan yatsa tana faɗar sunayensu.

      “Wannan sunanta Ummayya, wannan Aneesa, wannan Bassam, wannan Buhayyah, yarage naki ki kira sunansu gatsal kezaki sha wahala a wajensu”.

     Kai kawai Ummu ta jinjina mata ta maida kanta ƙasa, dan talura wannan gidan basusan daraja da kimar ɗan adamba. Kuma ba wani abu ke ruɗar tunaninsu ba sai dukiyar da ALLAH ya azurtasu da ita.

     Bayan Rahine ta wuce tabar Ummu aka kira wata mai aikin mai suna Halima, itama babbar mace ce, amma yanda yaran kemata magana babu girmamawa ya bama Ummu mamaki da tsoro, ita akace taje da Ummu sashensu.

    Tashi Ummukulsoom tayi ta bita sashen masu aikin dake can baya, Halima ta nunama Ummu ɗakin da zata zauna ita kaɗai, sai dai bazata iyaba, tanajin tsoro. dan haka tace, “Bah-bah dan ALLAH idan babu damuwa ki haɗani da wani, wlhy tsoro nakeji kwana ni kaɗai”.

     Murmushi halima tayi, tace, “to ƴarnan idan babu damuwa ki dawo ɗakina, dama nabaki ɗakinne dan karna shiga haƙƙinki”.

     

       A ranar dai Ummu bata fara aikiba, sai washe gari da safe, sunayin sallar Asuba Halima tace suje, mamakine ya kama Ummu tace,

    “Bah-bah ina zamuje da farar safiyarnan?”.

     Dariya Halima tayi tana gyara ɗaurin ɗan kwalinta, “Ummukulsoom kenan, ai zancen hutu kuma ya ƙare daga gareki, koda yake ke aikinkima da sauƙi, ɗakin su Bassam ne ma dake zuwa makaranta kaɗai zaki gyara da sassafe, shima yagama bana sai Buhayyah kawai, amma dolene kije ki gyara falon sama dana Hajiya dana Alhaji da wuri kafin su fito”.

     Ummukulsoom bataja zancenba ta miƙe suka tafi tana mai tausayin talaka a ranta.

        Tunda tahau sama takuma jinjina arziƙi na mutanen gidan, itadai tana aiki kamar yanda Halima ta nuna mata zuciyarta na santi. Tsaf ta gyara falon kafin ta koma na hajiya ta gyara sannan na Alhaji shima, dukda tama lura baya gidan.

    Bayan ta kammala ta sakko, ta iske ladi ta gyara na ƙasa tsaf itama.

     Bata zaunaba taje can baya inda Halima tace zata sameta, wanke-wanke ta iske tanayi, ta zauna tana tayata, dukda Haliman tace ta barshi.

     Bayan jama'ar gidan sun tashine Ummu tabi ɗakunansu na barci tana gyarawa, tadai gurzu da aiki kam, dan duk inda sukaso yarda kaya sukeyi, itadai ta kammala a gajiye ta rarrafa sashensu namasu aiki taje taɗan kwanta ta huta tunda ta karya dama itada halima.


 ★★★★★


       Wannan shine tushen fara aikatau ɗin Ummukulsoom a gidan Alhaji Mahmud Usman Ajiwa.

        Dan matsaloli kam tana fuskantarsu bila a dadin, da gaske halayyar mutanen gidan basa ƙaunar talaka ya raɓesu koda ƴan uwansune na jini kuwa, tasha ganin baƙi sunzo daga can garin Ajiwa tushen mai gidan a wulaƙantasu idan bayanan, amma idan yana gida za'a saka ƴan aiki su tarbesu, sannan shikam zai tarbesu da musu lale mar'habun cikin mutunci, ko kaɗan bashida damuwa, abinda kawai ta lura dashi baida sakin fuska, ko yaushe fuskarsa a tamke shima, rana ɗaiɗaice zakaga fuskarsa da fara'a, sai kuma idan ƴan uwansa sun kawo masu ziyara, koda yake ita Ummu ma baifi sau uku zuwa huɗu ta taɓa ganinsa ido da idoba, shima bawani kallonsa take iyayiba sosai.

       Matarsa kuwa da ƴaƴansa ko kaɗan basa haɗa sabgarsu da wanda bai dashi, dan tsantsar wulaƙanci suna ganinsa su ma'aikatan gidan, ƴar ƙaramarsu ma Buhayyah da Ummu ta girmeta sosai bata ɗagama ma'aikatan gidan ƙafa ko kaɗan, komai tsufanka kai mata kuskure zata iya danƙara maka zagi, inma ta kama da mari fuskarka tasha yatsu kuwa.

    Inhar kaga gidan ya nutsu masu aiki sun sami ƴancin kansu to Alhaji Mahmud yana gida, sai kuma sauran ƴan aikin sunce akwai ɗansu na biyu a gidan da suke kira Yaa Amaan, shima yaran gidan na mugun tsoronsa, hatta da Ameer wanda ke bi masa a cikin maza shakkarsa yake, kuma hajiya Jamila na masifar sonsa.

    Itadai Ummu tunda tazo gidan bata taɓa ganinsa ba, dan ance soja ne, ya gaji aikin babansa ne, yanzu haka yana zaune a garin legos, dama tun fil azal ba'a gidan ya tasoba, hannun mahaifiyar Alhaji Mahmud ya tashi harya girma, bayan rasuwartane ya dawo gidan da zama.

     Ameer ma bawani zaman gidan yakeba sosai a farkon zuwanta, sai cikin satinnan take ganinsa kulum-kulum.

    Sai kuma wata da suke kira Aunty Nurse, sunanta na gaskiya Jalilah, itace ke bima wanda yake zaune a legos ɗin, abinda Ummu ta gaza fahimta shine, tanada aurene kokuwa bata dashi? Dan babbace sosai babu laifi, zata iya kai shekaru talatin.


★★★★★★

          

      Yauma tayi matuƙar nisa a tunaninta taji an shureta da kafa, firgigit tadawo hayyacinta, Ameer dake tsaye a kanta ya watsa mata harara.

     “Ke dan uwarki bakiji ana kiranki baneba?”.

      “Dan ALLAH kayi haƙuri yaya Ameer, wlhy ban jibane”.

     “Mtsoww” yaja dogon tsaki, yana wuceta, “kije ki wankemin toilet, kuma koda wasa kar hannunki yakai kan wani abu nawa a ɗakinnan, toilet kawai nace ki wanken”.

     “To yaya”. Ta faɗa a sanyaye tana miƙewa ta nufi sashen samarin gidan.

     Shiko ko saurarenta baiyiba yanufi motarsa.

       Iya tsaruwa ɗakin Ameer ya tsaru, sai kamshin turarensa daya shafa ke tashi, kamar yanda ya sharɗanta mata kullum iya toilet take wanke masa, sai idan yana a ɗakinne ya tsaya a kanta tai masa gyaran ɗakin gaba ɗaya, shi buƙatarsa shine karta taɓa masa duk abinda zai iya ci, a cewarsa ƙyanƙyaminta yakeji.

      Aduk lokacin da ake jifanta da mugayen kalamai zuciyarta kanyi zafi da ɗaci, harma ta faki ido tai kuka da tausayin talaka bawan ALLAH.

    Tsaf ta wanke toilet ɗin yana sheki da ƙamshi, tafito kenan taci karo da Bassam ya fito daga ɗakinsa, dagashi sai gajeren wando da best, kallo ɗaya tai masa tai azamar janye idonta, dukda Bassam zasu iya sa'anni dashi hakan bai hanata rissinawa ta gaidashiba, dan hakan dokar Hajiya Jamila ne, tace dolene su girmama koda jaririne dake gidan.

    Cikin ɗaukar kai da shan kamshi Bassam yace, “K jeki ki cema kuku akawomin breakfast yanzunnan, sannan ki dawo ki gyaramin ɗakina”.

      “To”. Ummu ta amsa masa kanta a ƙasa zuciyarta na kunar wannan ƙasƙanci.

       Kamar yanda ya umarceta haka ta nufi kicin, Jud kuku nata aikin haɗa abincin rana da raira waƙarsa irin tasu ta coci, yana ganinta ya faɗaɗa murmushinsa da faɗin “Umikusmu kaine?”.

      Ƴar dariya tayi, saboda yanda yake faɗar sunanta abun na matukar bata dariya, harta gaji da gyara masama, ta gyara tsayuwarta tana faɗin “Nice Oga Jud, sannu da aiki”.

     “yawanka Umikusmu, mikake buƙata ne?”.

     “Uhum dama yaya Bassam ne yace na karɓa masa breakfast ɗinsa”.

     “Humm, kice oga Bassam an tashi, to gashi anan bayanki, dama na haɗa ina shirin gama wannan aikinne na Madam Buhaya ne”.

     Cikin toshe baki Ummukulsoom tace, Oga Jud bafa Buhaya ba, Buhayyah”.

     Dariya shima yayi yana kai hannu zai taɓata, sai kuma yay saurin janyewa saboda kallon data watsa masa.

    “Oh sorry Umikusmu, ina mantuwane baka so”.

     Batace masa uffanba ta ɗauki breakfast ɗin Bassam ta fice.

    Yawu ya haɗiye yana binta da kallo harta fice, sosai Ummukulsoom ke birgeshi, sai dai tun a ranar farko data fara aiki a gidan ya tabata ta taka masa birki da gargaɗi, hakanne yasashi shakkarta, koya kai hannu zai taɓata daya tuna saiya janye yana bata haƙuri.

       

      Ummukulsoom kam tana kaima Bassam abincin ta shiga bedroom ɗinsa tahau gyarawa, ya tile uban kayansa a kan sofa, kusan kullum saitayi bautar gyara masa drower, amma hakan bazai hana gobe idan ya tashi ɗaukar kaya ya watsosu kasa gaba ɗayaba, saika rantse makahone shi. Ranta duk a ɓace ga gajiya ta kammala tsaf, ta fito falo ta iskeshi yana waya cikeda taɓarar shagwaɓa data zame musu jiki shida Buhayyah autar gidan....

       “Yaa Amaan Please mana, wlhy ka tambayi momcy ma........”

     Ƙitt aka yanke wayar, hakanne ya sakashi wurgi da ita sai a goshin Ummukulsoom dake tsaye tana jiran ya kammala ta sanar masa ta gama gyarawa.

    Da azama ta dafe goshin saboda azabar zafin da taji......

    Cikin daka tsawa Bassam yace, “Dalla malama fitarmin anan banza ƴar matsiyata jinin talauci, kin wani zauna kina sauraren wayar da nakeyi”.

     Jikin Ummukulsoom na rawa ta fito, ga hawaye na kwarara a idonta, ga zugin da goshinta ke mata. Can bayan wasu flowers ta maƙale tasha kukanta da tausayin kanta, yaron da zasu iya shekaru ɗaya da shine yake maidata tamkar wata ƴarsa ko ƙaramar ƙanwarsa Buhayyah, a kullum wasu masu kuɗin suna ƙara banbanta tazarar dake tsakanin talaka da mai kuɗi, sun manta da duk ALLAH ne ya haliccemu yakuma banbantamu ƙabila daban-daban, jinsi daban-daban, wani bayajin yaren wani, sannan yay masu kuɗi a cikin talakawa, ya fidda talakawa a cikin masu arziƙi, bakuma dan wani yafi wani yay hakanba, a'a wannan buyarsace da ikonsa, sai dai hakan bai hana masu kuɗinmu ruƙo da kalmarnan ta malam bahaushe *WUTSIYAR RAƘUMI TAI NESA DA ƘASA* ba.

    Bayan tasha kukanta tai azamar share ƙwalla saboda kiran da ladi ke ƙwala mata, tasan bai wuce ace wata bautar bace ta taso. Haka suke wuni kullum a gidan tamkar ƴaƴan bayi.

 


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


     Washe gari Baseer yasamu Suhailat a school yay mata magar aurensu. Shiru tayi tana kallonsa da nazarin maganarsa, kafin taɗan murmusa tana gyara zamanta. “Love miyasa kake buƙatar muyi aure yanzu? Ka manta cewa yanzune zanje L200 ma ni? Dady na bazai bari ba, dan kaf yaran gidanmu mata babu wanda yataɓa aure daga degree ma wlhy, ni a yanda na tsara aurenmu sai nako haɗa degree ɗinane, time ɗin kaima kaga kagama masters naka, sainasa Dady yasama maka aiki muyi aure muci gaba da karatunmu”.

      Baseer ya haɗiye takaicin daya tsaya masa amaƙoshi daƙyar yana kallon Suhailat tamkar ya maketa, duk kuɗin da ubanta ya tara bazatama ce dadynta yabashi wani abuba saidai ya nema masa aiki dan raini, da ƙyar ya danne zuciyarsa a fili yace, 

     “Bara na fito miki a mutum to, Dad ɗinane yakeso na auri wata yarinya da tun muna ƙanana nake kulawa da ita da tausayinta, shikuma ashe duk zatonsu sonta nakeyi, zancen da nake miki yanzu haka an tsaida mana ranar aure ni da ita k.......”

     Wata zabura Suhailat tayi tunkan baseer yakai ƙarshen zancensa, tace, “Love! Kaikuma shine ka yarda ko mi?”.

    “No, bance miki na yardaba, amma rashin yardar tawa shine aurena da ke, dan haka yaya kika gani? Kin shirya zuwa kicema iyayenki aure kikeso kokuwa nama nawa iyayen biyayya bayan kin kammala karatun sai kizo ata biy.....”

     Hannu tai saurin sakawa ta danne masa baki tana faɗin “ALLAH ya kiyaye nazo ta biyu a gidanka wlhy”.

      Zame hannunta yayi daga saman bakinsa yana murmushi da kallonta, “To sarkin kishi naji, yanzu nabaki kwanaki bakwai naji ƙwaƙwƙwarar amsa daga gareki”.

     Cikin tura masa baki gaba da kumbura fuskar zancen kishiya da yay mata tace, “Naji zanje na faɗa”.

     Ƙasaitaccen murmushi ya saki, ya matsa da bakinsa kusa da nata yana faɗin kona ɗan sha bakinnan?”.

     Harararsa ta ɗanyi tana matsawa baya, “Love na faɗa maka hakan bazai taɓa faruwaba har sai munyu aure, niba sauran ƴan matan yanzu bane masu bama samari jiki ana romance nasu, nafison ka aureni don ALLAH badan sha'awa ba, dan haka kabarmin zance irin wannan mara ma'ana”.

     “To Usataziya na daina”.

     Banza Suhailat tai masa, dan dama duk lokacin daya nuna yanason taɓa jikinta ko kissing ɗinta tana nuna masa ɓacin ranta, dukda ta taso gidan arziƙi hakan bai sakata lalacewaba, dan mahaifansu tsaye suke akansu wajen tarbiyyarsu, dukda kuwa ita kaɗai suka haifa, su Amrah da sauran mata biyu da dadynsu ya aurar duk ƴaƴan ƴan uwansane ya riƙe tun suna ƙananu. Amma su huɗu iyayensu suka haifa kacal, maza uku yayyaenta sai ita auta kuma mace.

     Ganin tahau sama yashiga lallaɓata, dan inbai wasaba wannan fushin ta tayinsa kenan dan kawai yace yamata kiss. Shiyyasa wani lokacin sai yayta ganin kamar bata wayeba. Bai bartaba saida yaga ta huce sannan ya koma gidansu Najeeb.

        Yau ma tararwa yay Nehla zaune a harabar gidan tana jiransa, kuma basarwa yay yana shaƙar iska da busarwa, harga ALLAH yarinyar ta haɗu itama, kuma yana ɗan jinta a ransa, amma bazai bata fuskaba yanzu sai nan gaba yasamu Suhailat a hannu sosai.

     Da ƙyar ya amsa sannun datai masa ya wuce sashen Najeeb yana taku tamkar mai ƙyamar ƙasa.

    Tamkar idon Nehla zai faɗo tabisa da kallo tana haɗiyar yawu dakuma tsarkake sunan ALLAH da yay wannan ƙyaƙyƙyawar halitta, dan baseer yawuce mijin novel komai, ashe marubuta novels ba ƙarya sukeba akwai ƙyawawa acikin hausawa?.


   Nidai nace, “Hummm, Nehla aikifa ya sameki kekam”.


★★★★★★


          Kwannan Baseer uku a Zaria sannan ya shirya komawa Ɗilau badan ya soba, dan kwata-kwata shifa baya buƙatar zaman ƙauyennan yanzu.

         Koda ya huta babansa yadawo gona ya iske ya dawo faɗa yayta masa, shida yace zaiyo yini shine har kwana uku, yanzu dan abin kunya gidan surukan yaje yayta kwana kenan?.

      Baseer yace baba kenan, ai bamma jeba bare naji kunyar, amma a fili sai yace, “Baba ayi haƙuri, munyi kewar junane nida Ummukulsoom ɗin”.

      “To mara kunya naji”. ‘cewar baba’.

     Dariya Baseer yayi yana gyara kishin giɗarsa a tabarma.

        “Baseer yakamata ka shirya gobe muje gona ka tayani da ƙarasa aikin girbinnan, kagafa ance masu jajayen shanun nan sunfara zuwa”.

     A razane Baseer ya kalli baba mai maganar yana tashi zaune sosai.

    “Baba gona fa kace?”.

“Eh itafa nace, sai akai yaya”.

      “Babu komai baba, Amma wlhy ni nama mance yanda ake riƙe fatanya balle laujen girbi”.

     Galala baba yayi da baki yana kallon baseer, bakinsama yayi nauyi yagaza furta komai, sai Innarsa ce tasamu ƙarfin halin faɗin, “Baban talatu wlhy nangaba idan mukayi sake Basiru cazai mu ba iyayensa baneba, halayyar da yaronan ya aro tafara bani tsoro nikam”.

      Yanzunma baba kasa cewa komai yayi sai kallo da yake bin inna da Baseer dashi kawai.

      Ganin haka baseer yace, “Inna nifa ban aro halin kowaba, indai aikine inada kuɗi zan ɗauki masuyi na biyasu”.

    “Banaso Basiru, bar kuɗinka kasha shayi da ƙwai da daliyar yara (indomie) kaji”.

       “Kamar kasan kuwa can yafi kauri baban talatu, dan tunda yadawo gidannan banda fura bantaɓa girka abinci yaciba, dakace ga abinci zaice ya ƙoshi, inata damuwa dako baida lafiyane, saida yay tafiyarnan naje ɗakinsa zan ɗakko kwanon dayasha fura na iske farantai da kofunan idi mai shayi na bakin yara”.

       Murmushi kawai baba yayi baice uffanba ya miƙe, saida ya doshi shiga bayi sannan yace, “ALLAH ya shiryeka Basiru”.

      “Amin baban talatu”.

Basir kam bakinsa ya taɓe yakoma ya kwanta yana cigaba da laguda wayarsa da yake charting da Suhailat, dan ƙauyen Ɗilau basuda matsalar Network Alhmdllh...........✍🏻


NO. 6


         Abin duniya ya ishi Suhailat, tarasa yanda zata tunkari mahaifinta da zancen aurenta da Baseer, hakanne yasata samun yayansu na biyu, dan yanada masifar sauƙin kai. Nutsuwa tayi sosai a gabansa alamar akwai magana a ranta.

      “Ke auta wai lafiyarki kuwa?, kinzo kin tasani gaba tamkar wata marainiya, mike damunki?”.

        Ƙasa takumayi da kanta, kafin a hankali tace, “yaya idan na faɗa zaka taimakeni?”.

      “Insha ALLAHU dear sister, faɗa min idan zan iya”.

       “Yaya dan ALLAH ka fahimceni, wlhy ba rashin kunya baceba ko son zuciya dan ALLAH, yaya Nu'im wlhy aure nakeso, dan ALLAH ka taimakeni”.

     Tsura mata idanu yayi ko ƙyaftawa babu, dan maganarta ba ƙaramin mamaki ya bashiba, da ƙyar ya iya jawo wasu kalamai bisa harshensa.

     “Aure kuma Auta? Karatunfa to?”.

    “Yaya zan cigaba a gidan mijina, kai shedane bana wasa da karatuna, Wlhy ko Mami nakasa tara da maganar nan, dan ALLAH ka taimakeni, kasan indai mace ta furta buƙatar aure to wlhy akwai matsala kenan.”

       Ajiyar zuciya ya sauke tareda gyara zamansa, yace, “Shikenan Auta, insha ALLAH zanma daddy magana, yanda mukayi dashi zakiji insha ALLAH, fatana dai ki kare mutuncin kanki kamar yanda su Aliya sukayi aure lafiya kema kirabu damu lafiya”.

     “Insha ALLAHU Yaya, nagode sosai”.

     Murmushi yayi yaɗan bubbuga kafaɗarta sannan yatashi yabar gurin.


*_BAYAN SATI HUƊU_*


      Suhailat nata sauraren taji wani yamata maganar amma sai taji shiru, a gefe kuma kullum Baseer ciki. takura mata yake da maganar, ita harma tagaji da bashi haƙuri.

     Ranar tana shirin kuma tunkarar yayanta Nu'im da maganar sai gashi daddy yama aiko an kirata. Sosai ta tsorata ganin dukkanin yayunta maza ga mami ga daddynsu.

      Zama tai can gefe tamakar munafuka, ta gaidasu jikinta nata tsuma.

     Fuskar daddynsu babu alamar wasa yace, “Suhailat wane saƙo kika bada abani wajen Nu'im?”.

      Tuni idanun Suhailat sun cika da ƙwalla, muryarta na rawa tafara magana cikin in ina.

    “D..dda...y p..lea..se kayi haƙuri dan ALLAH, wlhy nakasa jurewane kawai”.

      “Suhailat kenan, yaushe kikama canja haline ban saniba? Ganin kina karatu yanda ya kamata yasa ban maida hankalin bincikenki akan mikike aikatawa a makarantaba, amma tun randa Nu'im yakawomin maganarnan yasani bin cikarki, shi yaron dake hure miki kunnen kije ki faɗa masa nace ban shirya aurar dakeba yanzu. Kuma daga yau kika sake tarar wani a gidannan da wannan maganar kinsan yanda ake ɓalla rake? To haka zan ɓallaki, naima ƙasusuwanki filla-filla su rabu da tsoka, shasha kawai, kima rasa wanda zakiso sai ɗan talaka baƙauye ma, wanda ya girma a daji, nasan ƙyansa ke ruɗarki tashi kiba guri”.

      Jikin Suhaila na ɓari ta miƙe tafito tana hawaye, harga ALLAH tana bala'in son Baseer ɗinta, babbar matsalarta kar a aura masa wadda yace, dan itako tanada kishi mai tsanani, musamman a kansa, bata fatan koda magana ne ta buɗe ido ta gansa tareda wata mace inba itaba, tasan in ya auri wata zata iya mutuwa sanadin bugun zuciya.

    Yini guda a ɗaki tayisa tana faman kuka, takira Baseer ta sanar masa yanda akayi, shiko yashiga zugata dacemata to shifa zaiyima iyayensa biyayya kamar yanda taiwa nata ta haƙura dashi.

    Wannan kalma ta sake bata tsoro tareda kashe mata waya da yayi, takuma rikicewa sosai.


          Tun daga wannan Ranar Suhailat take cikin damuwa, tabar samun Baseer a waya kwata-kwata, kuma yana cikin Zaria a binsa, dan tuni yabaro ɗilau bisa bijirewar dayayi shifa zaije yayi bautar ƙasarsa, ganin zai tara musu ƙasa baba yace ya tafi, shinefa ya haɗo kayansa yayo gidan innarsa Zaria.

        Wasa-wasa lamari yay tsamari ga Suhailat, dan makarantama tafara rage zuwa, dukta rame tafita hayyacinta, mamin su da Amrah da sauran yayunta sunyi lallashi harsun gaji taƙi saurarensu, shima kuma daddynsu yaƙi saurarenta, dukda halin data saka kanta ciki yana damunsa kuwa.

      A haka aka cigaba da tafiya har tsawon watanni biyar, zuwa lokacinfa kwata-kwata Suhailat tama bar zuwa makaranta, idan ka ganta saikace mai ciwon ƙanjamau, idan ta kira Baseer a waya saiya gadama yake ɗauka, idanma ya ɗaga ɗin yata yaɓa mata magana na lissafa mata kwanakin aurensa dake matsowa tsakaninsa Ummukulsoom.

    Wannan ne yakuma susutar da Suhailat.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


        Ummukulsoom ma dai nacigaba da aikinta, zuwa yanzun duk wulaƙancin da za'ai mata bata kuka, idan tagama duk abinda tasan zatayi saitai tafiyarta gidan Alhaji Sufiyan da Aziza ke aiki, susha hirarsu, matar gidan na birgeta, dan kuwa su sunsan mutuncin ɗan adam, macece mai kirki, idan kaga yanda sukema Aziza zaka ɗauka ƴar uwarsuce ta jini.

    Itama Aziza idan ta samu lokaci takan shigoma Ummukulsoom ɗin, dukda a harabar gidan take tsayawa bata shiga gudun wulaƙanci. Duk ranar juma'a sukanje gida su gaida Inna Harira kuma, anan Ummukulsoom kan samu ta gana da babanta idan yana kaduna baije ɗilau ba.

     

    Yauma Ummu na falon sama tana aikin gyarawa saboda ƴan uwan hajiya jamila da sukazo aka saukesu acan, tana cikin yin Morping hajiya Jamila tafito daga ɗakinta ta zauna a falon, zamanta baifi na minti biyuba Aneesa ta shigo tana hawaye jikinta duk a sanyaye, gaban Hajiya Jamila ta durƙusa tana faɗin “Momcy Please dan girman ALLAH karki faɗimishi, kiyi haƙuri, wlhy Yaa Amaan kasheni zaiyi idan yaji zancennan”.

      A ƙufule Hajiya jamila tace, “Yo ina sauran ji kuma Aneesa, Dad ɗinku ya faɗa masa, yakira Ummayya kuma ɗazunnan ta zayyane masa komai saboda tanajin tsoro, kinsan dai halinsa sarai, k.......”

     Ring ɗin da wayar hajiya Jamila tayine yakatse zancen nata, ta kalla screen ɗin wayar, *Fodio* yafito ɓaro-ɓaro, Aneesa ma data leƙa tagani tuni jikinta yafara mazari tana kuka da roƙon kar Hajiya Jamila ta ɗaga dan girman ALLAH.

      kukan Aneesa yasaka sauran ƴan Uwanta fitowa, kowannensu yayi tsumu-tsumu babu mai motsi. Mamakine ya kama Ummu, takuma lafewa, dan ta lura an manta tana falon, wanene wannan saikace dodo? baya kusa amma ake masa irin wannan mugun tsoron?, duk rashin Kunyar Aneesa dasu Buhayyah kalli yanda sukai mugun laushi, tunanin Ummu ya katse ganin Hajiya jamila zata ɗaga wayar saboda kira da aka ƙarayi dan kiran farko ya yanke......

       Yanda Hajiya Jamila take magana damai wayar zaka fahimci tsantsar ƙaunar da take masa, yanayin fuskarta kaɗai ya isheka amsa. Lokaci da tace, “Aneesa! Gata nan”.

       Sai Aneesa ta miƙe zumbur tana ja da baya jikinta na ɓari, Hajiya jamila ta rufe sifikan wayar da hannu yanda bazaiji abinda zata cema Aneesa ba, a hankali take faɗin,

     “Wlhy Aneesa ki rufama kanki asiri ki amshi wayarnan babu ruwana, hakan dazakiyi shine gagarumin laifi a wajen Fodio dan kinsan yatsani hakan, sabodake kawai zai iya baro legos yazo Kaduna yau ɗinnan, yarage naki kuma”.

      Ummayya taima Aneesa nuni data amsa..

     Durƙusawa Aneesa tayi gaban Momcy ta amshi wayar, bakinta na rawa tace “Assalamu alaikum yaa Amaan!”.

       Ai bata gama rufe bakiba sukaga tayi wata zabura wadda tasaka sauran yaran suma ja da baya, Buhayyah kuwa zuwa tai ta ƙanƙame Momcy.

     Ummukulsoom kam sai ta kuma zama status ai, toshi wannan ana tsoronsa a waya, inaga ya bayyana a fili? Abinci tacigaba da bama idonta, aranta tanajin alhakintanema ya kama Aneesar, dan yau cin kashin datai mata da safe karema bazai shinshinaba....

     Aneesa taci gaba da faɗin “Wlhy tallahi yaa Amaan kuskurene, amma na rantse maka bazan sakeba, wlhy yabani abune a lemo barci ya kwashen........”.

     Zabura takumayi batakai ƙarshen zancenba.

     Ummukulsoom jitake inama tanajin miyake faɗama Aneesar take wannan mazarin, dukfa tajiƙe da uwar zufa dukda garin bama zafi akeba.

    Yana yanke wayar Aneesa ta faɗa jikin momcy tana faɗin “Nashiga Ukuna momcy, wlhy cayay gobe Sani yakaini legos, dan ALLAH Momcy ki hana, wlhy gawata zai maido miki nasani”.

      Ita kanta Hajiya Jamila ta shiga damuwa, tace, “Aneesa saboda wannan nake faɗa muki a kullum ku a lura da abinda kukeyi a waje, yayanku yasaka masu sakama duk wani motsinku ido amma bakwa fahimtar yaren da nake muku, kema kinsan tunda ya hau dokin zuciya indai Fodio ne bazai fasa abinda yay niyyar mikiba, inma bakibi Umarninsa kinje legos ba wlhy zai iya ajiye aikinsa na wuni ɗaya yazo garinnan danya gurjeki”.

     Kuka sosai Aneesa keyi, dan tasan duk abinda Momcy tafaɗa hakane.

     Ana haka Ameer yashigo shima, ganinsu cirko-cirko yasashi faɗin “Kukuma Lafiya kuwa?”.

        Bassam ne ya sanar masa Yaa Amaan ne.

     Wata yar zabura Ameer yayi yana dafe ƙirji, “Mi akai masa kuma? Kudai yarannan akwai jazama mutane bala'i, munsamu *DAMISA* tai barci, wani cikinku halan ya taso mana ita?”.

     Ummayya tace, “Wlhy kuwa yaa Ameer Aneesa ce, nifa har daɗi nakeji dayay kusan shekara baizoba, gashinan ta ɓallo mana ruwa, yace gobe isa yakaita legos”.

      A firgice Ameer ya waro idanu waje, yace, “Legos!!?, Aneesa ALLAH ya jiƙanki, wlhy gobe da sassafe zan wuce Abuja, dan inaji a jikina Yaa Amaan yana gab da shigowa kaduna kuwa”.

      Ummayya tace, “Wlhy yaya Ameer nima kano zanbi aunty Nurse nayi hutun sati biyu”.

    Sum-sum Ummukulsoom tasamu tabar falon kafin wani yaganta, hakanne yasa batasan ya ƙarshen zancen ya ƙareba.

     Washe gari dai tunda safe taga Aneesa ta ƙaramin akwai tana kuka Isa driver ya ɗauketa a mota sun tafi.

      Wannan lamari ya tsayama Ummukulsoom a zuciya, dan yafi kwana uku yana mata yawo a rai da mamakin wane wannan *Yaa Amaan ɗin da sukema laƙabi da suna Damisa?* dama duk rashin kirkin yaya Ameer dasu Ummayya akwai wanda suke shakka har haka bayan mahaifinsu?.

      Satin Aneesa ɗaya a legas saigata tadawo wujiga-wujiga, dukta rame tayi baƙi, dukda Muguntar da takema Ummu saida taji tausayinta da tunanin komi yay mata haka?.

     Tadawo babu jimawa saiga likita yazo dubata wai inji Yaa Amaan.

     Indai taƙaice muku zance saida Aneesa ta kashe sati biyu tana jiyya a gida, dukta zama wata shiru-shiru a gidan.

      Wannan lamari yakuma firgita Ummu, addu a take ALLAH yasa itadai harta bar wannan gida bama zata haɗu da wannan Yaa Amaan ɗinba.

      

      Haka rayuwa tacigaba da matsawa, yayinda bikin Ummu ke ƙaratowa, A kullum Ummu cikin lissafin kwanakin bikinta take da Baseer ɗinta, ga tsananin kewarsa da take, rabonda ta gansa a idonta kusan shekara biyu kenan, har Alla-alla take kwanakin bikin suzo, yanzu hakama an faɗama su hajiya Jamila nanda wata ɗaya Ummukulsoom zata bar aiki za'ai mata aure.

    Randa Rahine tazo tana faɗama hajiya maganar auren Ummu Alhaji Mahmud yana gida, kuma yana jiyosu dayake yana ƙaramin falonsa na hutawa.

       Dukda bawani kallon tsaf yakema yarinyarba ya lura tanada nutsuwa, sannan batada hayaniya, yana kuma gamsuwa da gyaran sashensa da takeyi, danshi mutumne mai bala'in son tsafta, shiyyasa tunda ya lura matarsa da ƴaƴansa ragwagene sai bayajin ƙyashin biyan a ɗauka ƴan aiki a gidan, ko nawa Hajiya jamila tafaɗa yakan bada indai yana dasu.

        Inda ta shine da sunbar Ummukulsoom karsu mata aure, dan tun randa yataɓa jin hirarsu da Aziza akan karatu ya ƙudirci taimakon yarinyar yasata tacigaba da karatu, to ashe kumama akwai zancen aure akanta. 

     Daga nan yaci gaba da sabgarsa bai sakebi takan zancenba gaba ɗaya. Dan ko kaɗan baya shiga wata sabga da batashiba shikam.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


       A ƙauyen ɗilau kuwa tsaf iyayen Baseer suka kammala masa gininsa da akeyi a faƙon amare, ginine na ƙasa irinnna ƙauye, amma sam ko sau ɗaya bai taɓa zuwa ya leƙaba, danshi dariyama su baba ke basa, waye zai zauna a wannan gidan? yoshi bama gidanba ko garin baya fatar zama cikinsa wlhy.

         Hakama lefe su inna sun dage suna siyan ɗai-ɗai dama suna tarawa, gakuma gudunmawa da dangi suketa kawowa, dan haka zuwa yanzu Alhmdllh, abinda ba'a rasabane kawai ya rage a ida haɗawa, sunma jinkirtane basu sayaba saboda wajen wata uku da aka ƙara akan wata takwas ɗin farko, yanzuko da biki yazo gab wasu awakin Basiru dana inna aka haɗa aka kai kasuwa aka sayar, talatuwa yayarsa da ƙanwar inna dake zaria suka shiga kasuwa suka haɗo sauran abinda ya dace da akwatunansu guda biyu, sai basket na riyo da ake zuba kayan yara a ciki.

    Yanzu kam sudai biki kawai suke jira abinsu.



★★★★★★★★


       Ɓan garen baba Ummukulsoom ma Alhmdllh kamar yanda ya ƙoƙarta yayma su Azima kayan ɗaki itama Ummu yamata dai-dai ƙarfinsa, harda ɗan gadon ƙarfenta na mutunci, yasan ba uwa garetaba, dan haka yasai katon ɗin samira biyu blue yakai gidan Gwaggo hinde yace a ajema Ummu, albarka Gwaggo hinde taita saka masa, dukda itama sunata sayen ƴan abubuwanan itada sauran ƴaƴanta ƴan uwan mahaifiyar Ummun.

       Acan kaduna ma ƴan kuɗin da Ummu ke tarawa na aiki inna harira ta cire wasu taɗan saya mata su kuloli dadai abubuwan da suka dace na amfani irinnan birni.

    Zuwa yanzukam Alhmdllh ranar biki kawai zamu iya cewa muke jira ta kowanne ɓangare, saidai fa banda ango, danshi nasa hangen daban.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


             Kwata-kwata Suhailat tagaza lafiya, ta jefa kanta a bala'i bisa ga jagorancin Baseer dake zugata a gefe yana tunzura mata wutar kishi a ranta, saboda ya fahimci tana tsananin sonshi ga kuma kishi da take dashi mai tsanani shima.

    Yau har takai Suhailat a asibiti ta kwana.

        A jiya da daddare yakirata yake shaida mata saura sati ɗaya ɗaurin aurensa da Ummukulsoom, shine ta yanke jiki tafaɗi a sume. Aka kwasota zuwa asibiti.

      Biris daddynta yay da lamarin, danshifa komi zatayi bazai aura mata ɗan talakawa ba. Yau da ace wani ɗan mai kuɗi ta kawo irinsa wlhy saiya aura matashi, yasan konan gaba bazata sha wahalaba, tsakaninta da wanda take ƙulafucin kuwa *Wutsiyar raƙumi tai nesa da ƙasa* tama gaji ta haƙura.

       Mahaifiyarta kam tashiga damuwa matuƙa, hakama ƴan uwanta.

    Har asibitin Baseer yaje ya duba ta, yay ta zubama su mamin ladabi, harda hawaye yake sharewa wai na tausayin Suhailat.

            Hakan da yayi, sai ƴan uwan Suhailat sukaji ƙaunarsa a ransu, danfa sosai ya nuna damuwarsa akan lamarin kamar mi.


       Bayan kwana biyu da faruwar haka likita yayma daddyn Suhailat magana akan zuciyar yarinyarsu tana cikin haɗiri, dan daga yanzu inhar wani abu na firgici ya kuma samunta makamancin wannan zuciyarta zata buga su rasata gaba ɗaya.

     Wannan magana da mamin Suhailat tajiya yasata zaman dirshan tanama daddy kuka da roƙonsa yabar Suhaila ta auri yaron da takeso, indai batun talauci ne ALLAH bai hanashi abinda zai taimaki yaronba.

     Dayake shima hankalinsa a tashe yake baija zancenba ya amince, dan yana tsananin son Suhailat, ga yayuntama maza duk sun matsa masa da roƙo akan yay mata abinda ta keso dan ALLAH.

      Shi da kansa yayma Suhaila albishirɗin ya amince ta auri Baseer, gani sukai kawai ta rungume daddy ta fashe da kuka, duk sai tausayinta ya kuma kamasu, ALLAH ya jarabceta da soyayya mai ban tsoro, wanima saiya ɗauka ƙarya take, itako harga ALLAH son Baseer take tsakaninta da wanda ya halicceta.

     Itace ta matsa akan ta warke a sallamesu, shima likita fahimtar da yay tasamu maganin ciwonta saiya basu sallama suka dawo gida a daren.

      Bata iya haƙuriba, sai da ta kira Baseer a daren ta shaida masa, yanda yanuna mata tsantsar farin cikinsa ne yakuma dasa sabuwar ƙaunarsa a ranta, gani take shima yana tsananin sonta da ƙaunarta fiyema da yanda take masa, dan anbata labarin kukan dayazo yayi tana kwance a asibiti.

     Da kansa ya tsara duk matakan da daddynta zaibi wajen shawo kan babansa shima, dan yanzu haka bikinsa da Ummukulsoom kwanaki biyar kacal yarage, shirye-shirye kawai sukeyi. 

     Hakan yaso birkita zuciyarta, amma yashiga kwantar mata da hsnkali saɓanin da da saidai ya rura zuciyarta da ɓacin rai.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


         Kwanaki biyarne kacal suka rage bikin Ummukulsoom da Baseer, zuciyar su baba yalwa tamkar zatayi bindiga, sai daifa babu yanda suka iya da ikon ALLAH, dan haka suka zuba na mujiya kawai. 


★★★★★★


       Yau Ummu zata baro kaduna, ma'aikatan gidan Alhaji Mahmud Ajiwa su Jud duk sun shiga damuwa, dan Ummukulsoom yarinyace mai shiga rai, batada damuwa, kakan zauna tsawon lokaci da ita bakace gashi tamaka kazaba, sukansu ƴan gidan zukatansu duk babu daɗi, dan Ummu tayi juriya da halayyarsu ba kaɗanba, gashi duk abinda sukace tai musu babu wani ja'inja takeyinsa komai gajiyar da tayi, sai daifa aransu sukejin babu daɗin, amma a fili basu nunaba.

     Bayan ta kammala shirinta taje kiranda Alhaji Mahmud yay mata.

    Durƙushe take agabansa yana mata nasiha akan rayuwar aure, hawaye kawai take sharewa da hijjabinta, tareda jin ƙaunar dattijon mai adalci da ɗaukar kowa ɗaya, gashi yana mata nasiha tamkar mahaifinta, daga ƙarshe yay mata doguwar addu'ar zaman lafiya, sannan yabata wani abu a ✉ dabatasan ko mineneba, yace, “Gobene zaki tafi can garinku ko?”.

     Kai Ummukulsoom ta ɗaga masa tana share ƙwala.

    Yace, “Ok, insha ALLAH driver zaizo ya kaiku can ƙauyen yaganomin, dan insha ALLAH zan halarci ɗaurin auren inhar wani uzuri bai dakatar daniba, ALLAH ya sanya albarka yabaku zaman lafiya, ko anan gaba kike buƙatar taimako kizo gidannan kanki tsaye, dan kema kinzama ƴar uwa kodan wahalta mana da kikayi, dan komi mai gida zai biya ma'aikaci bai gama biyansaba, ALLAH yay miki albarka, kodai kaduna kika shigo kidinga daurewa kina zuwa ayi zuminci”.

     Ummukulsoom na share hawaye tace, “To baba, nagode ALLAH ya ƙara girma da lafiya mai amfani”.

    ”Amin ɗiyata nagode nima”.

 Sauran ma'aikatan sunsha kuka da Rahine tazo tafiya da Ummu, tareda kawo wata yarinyar da zata maye gurbin Ummukulsoom ɗin.


     Koda suka koma gidan Inna harirah ma ba zama sukaiba, dan itama Aziza tataho gida saboda bikin Ummu da zasu tafi.

    Duk abinda zasu tafi dashi suka kimtsa saboda jin Alhaji Mahmud yabasu mota ta kaisu.


★.


      Yau da biki ya rage saura kawana ukune su Ummu suka nufi ɗilau a motar da Alhaji Mahmud yabada akaisu............✍🏻



NO. 7


           Mahaifin Suhailat yay shiri tsaf shida babban ɗansa yayansu Suhailat suka nufi ƙauyen ɗilau, babu abinda kecin zuciyarsa sai takaici, wai ƴar cikinsa, jininsa ce zata auri wanda yafito daga wannan ƙungurmin ƙauyen da ko hanyar kirki basuda shi, Wlhy badan ciwon da akace yanama Suhaila barazana ba babu yanda za'ai ya amince da wannan shirmen nata.

     Tunda suka shiga cikin ƙauyen ransa yakuma ɓaci ƙololuwa, hakadai ya danne da ƙyar, da tambaya suka isa gidansu baseeru, banda kallon raini babu abinda dadyn Suhailat kema gidansu Baseer shida Mika'il, yama akai wanda ya fito a wannan banzan gidan yasamu kuɗin karatu? har yaje ya ganarmasa ɗiya?, koda yake ance mutanen ƙauye kuɗine dasu amma shegen maƙo baya barinsu suci.

       Koda baban Basiru yafito yaga waɗannan baƙi a jibgegiyar mota duksai ya rikice, yama rasa ina zai ajiyesune.

      Dadyn Suhailat dake cika yana batsewa yace, “Kaga malam kaimu daga cikin gida, dan wannan maganar ta sirrice”.

     Jikin baban Basiru na rawa yace, “To to Alhaji ayi haƙuri, kushigo, bismillanku”.

     A cikin gidama inna tasha mamaki, dardumarta da baffanta yaje makka yakawo mata tsaraba shekaru kusan ashirin ta ɗakko, dan bata fito da ita kwata-kwata, bayan an saka musu tabarma sai aka shimfiɗa dardumar a sama, amma dukda haka sun zaunane kawai bisa ƙyanƙyami cewar daddyn Suhailat.

     Baseer daduk yasan da zuwansu saigashi ya shigo, dan dama yana laɓe a bakin gari yana kallon shigowar su Daddyn Suhailat.

     Maganin daya amso wajen wani malami na rufe bakin iyayensa da malamin yace saisu daddyn Suhailat sunzo zaizo ya barbaɗa a gidan, da tun jiya ya binne wata laya a tsakkiyar murhun gidan dukdai na rufe bakinne,  ya zaro maganin a aljihunsa, cikin hikima yaringa zubda maganin a ƙasa kaɗan-kaɗan, tabbas innarsa ta lura ƙurar wani abu na fita a hannun Basiru, sai dai bata kawo komai arantaba.

    Kamar yanda malamin ya faɗa maganin na ƙarewa su inna da baba suka shaƙa sai duk tunaninsu ya juye, suka kuma ganin Dadyn Suhailat yamusu wani mugun kwarjini, hakama Basiru.

               A dake Daddyn Suhailat yafara magana, saikace yana gaban ƴaƴansa ne ko ɗaliban makaranta, sai wani faman mazurai yakeyi.

     “Bisaga Nacin ɗanku na liƙema ƴata harta kamu da ciwo, munyi-munyi ta rabu dashi hakan ya gagara, dukkan abinda takeso mukuma zamu iya mata domin samun lafiyarta, dan haka mukazo akan maganar aurenta da ɗanku, na farko dai yarinyata bazata iya zaman ƙauyennan ba gaskiya, balle rayuwar talauci dabata taso tagani ba. Zanbama ɗanku gidan da zasu zauna, da motar hawa, nakuma bashi aiki, komai na hidimar bikin na ɗauki nauyi, sannan Suhailat bazata taɓa rayuwa da kishiyaba, sai kusan yanda zakuyi da wadda kuke shirin haɗashi da ita”.

         Takaici da baƙin ciki sun cika zuciyar Inna da Baba fam, amma bakinsu da fuskarsu yagaza nunawa, sun rasa dalilin hakan kuma, shi kansa Basir maganar daddyn Suhailat ya ƙona zuciyarsa, amma ayanzu bazai nunaba sai ƙudirinsa ya cika a kansu sannan...........

      “Kunyi shiru, ko bakuda abin faɗane bayin ALLAH?”. Cewar mika'il.

      Da sauri baba yace, “To Alhaji duk yanda kace ai haka za'ayi ALLAH ya sanya alkairi yabada zaman lafiya, indai maganar auransa da waccan yarinyane an barsa, yanzuma zanje na sanarma mahaifinta”.

       “Muna jiranka kaje ka sanar musu kadawo, muma saimu bama ɗanku abinda mukai masa alƙawari, sannan mu tsaida maganar auren”.

       Baba ya amsa da “To” yatashi ya fita, dolene yabaka tausayi, jikinsa sai rawa yake tamkar wani almajiri gaban ubangidansa, Inna kam banda suya babu abinda ranta keyi mata, tarasa mike damunsu itada baban talatu, anzo ana wulaƙantasu a gidansu, akan ɗansu amma sun gaza ɗaukar wani mataki.

    Baba na fita yasa gefen rigarsa ya share hawayen da suka gangaro a kumatunsa, wanda kwata-kwata yama rasa dalilinsu.

     A ƙofar gida baban basiru ya iske baban Ummu yanajin redio shida wasu dattijai biyu, saida suka gaisa cikin mutunci sannan baban Basiru yaja baban Ummu gefe ɗaya dan yay masa bayani, amma saiya kasa sai inda-inda yakeyi. 

     A dai-dai wannan lokacin motar su Ummukulsoom ta tsaya, hango babanta dataine yasakata ɗokantuwa da fitowa taje gareshi, dukda kuwa kwanansu 6 kacal da rabuwa yataho gida.

     Tunda Baban basiru da Babanta suka hangota sai hankalinsu ya koma kanta, kowanne fuskarsa washe da murmushi, a zukatansu suna ambatar kalmar masha ALLAHU, dan ganin Ummu ta kuma cika da buɗewa alamar duk inda take bata cikin wahala, tana gab da isa gaban su baban, Basiru da Daddyn Suhailat da Mika'il yayanta suma suka iso. Dan basiru ne yacema daddyn Suhailat yakamata yaje da kansa, babansa zai iya kasa faɗama baban Ummu sun fasa auren, shikuma ba son Ummu yakeba daman.

       Babu wani dogon tunani a maganar, daddyn Suhailat ya amince suka biyo bayan baba.

      Tunda Ummukulsoom ta hango Basiru sai takejin zuciyarta na wani tsitstsinkewa, babu abinda takeyi sai ƙara tsarkake sunan ALLAH da yay wannan ƙyakykyawar halitta, lallai ta more da samun miji abinso ga kowa....

    Basiru kuwa kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa, dukda harga ALLAH yaji wani abu ya soki ransa gameda canjawar da Ummu tayi gaba ɗaya, sai dai kuma kuɗi sun rufe idonsa, burinsa kawai yagansa da gida da motar da daddyn Suhailat ya ambata masu, idan yasamu wannan daga baya yazo yabama Ummukulsoom haƙuri ya aureta, yasan zatai masa Uzuri......

      Bayanin da Daddyn Suhailat kema baban Ummukulsoom gatse-gatsene yaja hankalin dayawan mutanen wajan, dan cikin hargowa yake faɗin, “Malam munzone mu sanar maka Baseer ya fasa auren ɗiyarka, dan bama su daceba, ina wannan ƙyaƙyƙyawar halittar ina matar data fito daga wannan ƙungurmin ƙauyen, ka nemawa ƴarka mijin aure kawai”.

  

      Babu wanda yasan miya faru, kawai ganin Ummukulsoom akai a ƙasa wanwar ta yanke jiki ta faɗi, Aziza ta fasa ƙara da kiran sunanta.

     Kafin kace mi matan ƙauyen sun fara turuwar fitowa, hakama tsirarun maza dake a ƙarƙashin inuwa suna hira.

     Baban Basiru kasa jurewa yayi, ya sulale yabar wajen yana hawayen da baisan dalilinsuba, yana zuwa gida yace Inna ta shirya subar garinnan.

     “Baban talatu kayi haƙuri dan ALLAH, basai munje ko inaba, tafiyarmuce zatasa acigaba da zarginmu akan wannan lamari, narasa mike damunmu nikam yau?”.

    Kasa magana yayi yashige ɗaki abinsa.

     Koda su Basiru sukaga Ummukulsoom ta faɗi suma sai suka bar wajen, duk dama su su daddyn Suhailat basu san ita bace amaryar, ko gida ƙin komawa yay yabi daddyn Suhailat akan ya karɓo keys ɗin gida dana mota da za'a bashi.

    

      Driver n daya kawo Su Ummukulsoom ne yasa aka sakata amota suka nufi zaria aka kaita asibiti.

      Tuni ƙananun magana sun baje ƙauyen ɗilau, yayinda zukatan wasu daga jama'ar gidansu Ummukulsoom tamkar su zuba ruwa a ƙasa susha, har gari ya ɗauki zance, yayinda aka sauya maganar gaba ɗaya daga gidan su Ummukulsoom. Wai ciki tayo a binni shine basiru yace ya fasa bazai auri ƴar iskaba.

      Tunfa magana na yawo wasu na ƙaryatawa har tafara tasiri akace Baseru yajiyo zsncen cikin Ummu ne tuni, wai wandama yay mata cikinne ys kawota a mota, shi Basiru bai fallasa asirin zancen bane sai yau da yaga Ummu da ƙwartonta bayan kuma saura kwana uku ɗaurin aure yarage kacal.

      Dangin mahaifiyar Ummu wannan magana ta rikitasu iya matuƙa, sai kuka sukeyi, musamman ma Inna laraba, mashin tahau zuwa garin Kudan, dagacan tashiga motar zaria tabisu asibiti bayan takira baba a waya ya faɗa mata asibitin da drivern da su Ummu sukazo dashi ya kaisu.


           Alhaji Mahmud yagaji da jiran Isa Driver zasu tafi Abuja, amma shiru babu labarin Isa, gashi lokaci yana ƙurewa, shikuma meeting gareshi na tsoffin ma'aikatan tsaro da za'ai a Abujar domin shawarwarinsu gameda halin da ƙasa ke ciki.

     Ransa a ɓace ya ɗauki waya yay kiran Isa yana masa faɗan ina ya tsaya nanda zaria ace har yanzu bai dawoba? Bayan yasan shi yake jira kuma.

       “Kayi haƙuri Alhaji, wata matsalace aka samu gameda auren yarinyar dana kawo......” ya kwashe kaf abinda yagani ya shaidama Alhaji Mahmud, ya ƙara da faɗin, “Kuma abinda zai baka mamaki Ranka ya daɗe Alhaji Hussain Abba ne fa”.

      Cikin tsantsar mamaki Alhaji Mahmud yace, “Isa Kana nufin Alhaji Hussain Abba dai dana sani na nan anguwarmu?”.

     ”Wlhy kuwa shi yallaɓai, kasan mutuminnanfa bashida kirki dama, akwaishi da alfahari da dukiya, namarasa ina yaron ya sonsa? Kokuma ƙyawun yaronne ya ruɗi Alhaji Hussain ɗin har yayma ɗiyarsa kamunshi?, ni nama zatafa bashida sauran yarinya mace dukya aurar”.

        A tsawace Alhaji Mahmud yace, “Wannan bai dameniba, ina mahaifin yarinyar?”.

     “Gasunan cikin tsantsar tashin hankali yallaɓai, dan yarinyar bata farfaɗoba har yanzun”.

       Alhaji Mahmud ya dafe kansa zuciyarsa na wata irin tafasa da hanƙoro tamkar zata fito, (damashi akwai baƙar zuciyar tsiya, anan Fodio yay gado tamkar jinin kutare haka suke🙊⛹‍♀), yace “Haɗani dashi”.

       Isa yasan ran maza ya ɓaci, dan haka bai kuma tofa komaiba yaje inda baban Ummu ke tsaye yana sharar ƙwalla a kaikaice yabashi wayar.

     malam Buhari bai musaba ya amsa ya kara a kunnensa.

        Sama-sama suka gaisa Baba na mamakin wanene....?

    Cikin katse tunaninsa Alhaji Mahmud yace, “Nasan baka sanniba bawan ALLAH, amma hakan bazai hanani neman alfarma daga garekaba, kasa a ranka kawai ni ɗan uwankane musulmi wanda aduk inda kake zai kare mutuncinka da kimar ka kasantuwarka mai daraja, ni ne mutumin da yarinyarka tai aiki a gidansa, yanzu driver ke sanarmin komai akan abinda yafaru tsakaninka da mijin da zata aura? Idan har ka amince dani bazan cucekaba balle yarinyarka inason gabani aurenta, kuma banaso a canja ranar ɗaurin auren, kamar yanda kuka tsara wannan juma'ar nakeso ayiɗin”.

        Gaban baba ya faɗi, dan dagajin muryar mutumin ba yaro baneba, tayaya zai bashi Ummu kuma, amma dukda baba a tsorace yake dajin muryar Alhaji Mahmud, dan dagaji kasan anyi barden namiji a zamaninsa, sannan yanada matuƙar zafi babu alamar ɗaukar raini a lamarinsa, ajiyar zuciya baba ya sauke, batare da tunanin komaiba yace, “Alhaji na amince, ALLAH ya sanya albarka acikin wannan aure”.

     Daga canma sai Alhaji Mahmud ya sauke ajiyar zuciya yana jinjina halin dattako da ƙundunbala irinnan Malam Buhari, yace, “Ɗan uwa nagode da wannan karamci naka ƙwarai da gaske, dukda baka taɓa ganinaba amma ka aminta dani batareda ja'injaba, namaka hakane danna gwadaka dama, amma bani zan auri yarinyarka ba, yarona Fodio nake nemama aurenta dake aiki a garin legos yanzu haka, dan soja ne”.

      Share ƙwalla baba yayi wani sanyi na ratsa ransa, dan dama ya amincene saboda bashida wata mafita, ga Alhaji Mahmud ya ɗauresa da jijiyar wuyansa, amma jin bashi bane mai aurenma sai baba yace nikeda godiya Alhaji, dan koba komai dariyar maƙiya zata zama kuka, sannan hawayen marainiya bazasuci gaba da kwaranyaba, ALLAH yasa hakane yafi alkairi”.

      “Amin ya rabbi, insha ALLAHU zuwa gobe zan shigo garin, yanzu dai zanje Abuja ne”.

      Godiya baba ya ƙara masa sannan suka yanke wayar kawai.

       Wannan magana tadan sanyaya ran baba danasu Inna laraba, bayan kamar a wa ɗaya dayin haka kuma Ummukulsoom ta farfaɗo, saidai sunmata allurar barci danta sake samun nutsuwa.

             Baba ya sanarma Inna laraba halin da ake ciki, hakanne yasata kukan daɗi itama, koba komai Ummukulsoom zata samu sauƙi, dan kuwa wannan matsalar kaɗai ka iya hanata samun miji a ciki da bai ɗin ƙauyen ɗilau, danma basusan ƙurar data tashiba bayan barowarsu ƙauyen na jifar Ummukulsoom da akeyi da kalmar cikin shege.🤦🏻‍♀


★★★★

 

         Duk wayar da Alhaji Mahmud keyi hajiya jamila na zaune, hakanne ya saka hankalinta ƙololuwar tashi, jinin jikinta na neman daina zagayawa. Cikin tsantsar firgici ta kalli Alhaji Mahmud daya ajiye wayar, “Abban Fodio nifa ban fahimtaba?”.

      Wani kallon banza ya watsa mata, saboda har yanzu ransa a ɓace yake, da ƙyar yabuɗe baki yace, “Ai yanzu zaki fahimta uwar rashin haƙuri, yarinyar datai aiki a gidannan tatafi jiya akan za'ai mata aurene mijin ya fasa, nikuma nace a ɗaura da Fodio...”

     Zabura tayi tana dafe ƙirji, “Haba Abban Fodio, karasa wadda zaka zaɓa masa sai ƴar talakawa wadda ta fito daga ƙauye tazo aikatau a gidansu?”.

      Baiyi mamakin jin hakan daga garetaba, dan a halayyar jamila sai dai yabama wani labari, kansa kawai ya girgiza ya miƙe, dan idan har yace biye mata zaiyi zaima iya lakaɗa mata duka agaban ƴaƴantane, ya watsa mata harara yana nufar ƙofar fita da faɗin “Idan na aura masa ita kisaka ya saketa take a wajen taron ɗaurin auren”. Daga haka yay ficewarsa kawai.

      

     Saida ta tabbatar yafita sannan tashiga zabga bala'i ɗanta bazai auri ƴar aikiba, banbaminta yajawo hankalin yaranta sukazo suka zagayeta suna tambayarta lafiya?.

      Cikin tsantsar takaici da tsanar Ummukulsoom tace, “Wai Dad ɗinkune zai aurama yayan ku yarinyar data bar gidannan jiya?”.

       Idanu duk suka zaro waje, Ummayya tace, “To wlhy Asiri taima Dad, kuga munafukar yarinya sum-sum da ita tazo tasha jar miya da shayi, itakuma nata salon cin amar kenan?”.

       Aneesa ta karɓe da faɗin, “Yo ai dama ɗan talaka bai iya samun wajeba, mi yaa Amaan zaiyi da wannan karabuti ɗin, wlhy Wutsiyar raƙumi tai nesa da ƙasa, mukaɗaima mun isheta”.

      Dariya Bassam ya sanya, duk suka juyo suka kalleshi, ya ɗage kafaɗa da faɗin “Ku miye naku na damuwar?, indai Yaa Amaan ne ubanta zataci a wajensa, saita gwammaci mutuwa tai da zama da wannan”.

          Harara hajiya Jamila ta zuwa masa, tana faɗin, “Dalla malam rufama mutane baki, ubanmi kasani daga shu'umancin mace, shi dad ɗinku sauƙinne dashi? Amma ta iya cusa masa hakan a ransa ta asiri. Duk yanda kuke tunanin Fodio baya ɗaukar raini zata iya binsa ta ƙarƙashin ƙasa kamar yanda tabi dad ɗinku ai”.

      “Hakane kuma wlhy Momcy”. Cewar Buhayyah.

      Aunty Nurse dake zaune tana saurarensu ƙala bataceba, saima cigaba da danna wayarta da takeyi, zuciyarta na mamakin halayyar ƴan gidansu da basa canjawa sai dai ƙaruwa, su dai basu zasu zauna da matarba, amma sunbi sun gallabi ransu, yanzu daka nufi faɗama momcy gaskiya ta nemi ɓata maka ranka, dan hakama ita tazaɓi yin shiru.

         Miƙewa Aunty Nurse tayi tana faɗin, “Nidai Momcy shawarar dazan bada shine abi komai a sannu, kunsan dai halin dad, karku jawo abinda zai hana kowa zaman lafiya a gidannan”.

      Maganarta duk ta shigesu, dan suma sunsan basu isa ɗaga murya agaban dad ba.

     “Momcy maganar Aunty Nurse fa gaskiyace, inaga kawai ki kira Yaa Amaan ki sanar masa kafin dad ya faɗsa masa, ki zugasa karya karɓi auren”. Ummayya yace mai maganar.

     Kai Momcy ta jinjina saboda gamsuwa da maganar Ummayya. Ta jawo waya tafara kiran Yaa Amaan amma saitaji busy, tunda taji hakan kuwa tasan yana cikin aikine, dole ta haƙura bata sake kiransaba dan tasan inya zama free zai kirata da kansa. Amma dukda haka saita rubuta text massage ta tura masa duk dan kar dad ya rigata😂😝.


    ★★★★


  Alhaji Mahmud kam wani abokinsa ya kira dake Abuja, yace yasaka abuga masa katin ɗaurin aure yanzu kafin ya iso, ya tura masa abinda za'a saka a katin, yayi hakane saboda yanason fara raba I.V ɗinne tun awajen taron nan nasu.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


      *_WASHE GARI_*


  Washe gari Alhaji Mahmud yazo Asibiti a Zaria ya samu baba, dan daga Abuja ya wuto nan bai tsaya kd ba, a jiya kuwa yayta raba I.V ga abokansu yana basu haƙuri akan abinne yazo a ƙure, amma dukda haka sunce zasuzo insha ALLAHU.

      Ya tausayama halin da Ummukulsoom take ciki, kwana ɗaya dukta zube, babu abinda takeyi sai kuka, danma da likita yaga ta takura kanta saiya danna mata allurar barci, dan taƙi sauraren kowa lallashin da ake mata, ita kaɗai tasan tarin ƙaunar da takema Basiru, a yanzuma sai takejin ƙaunarsa fiye da ko yaushe a rayuwarta.

      Baba da Alhaji Mahmud sun gama yanke komai, dan ba karamin ƙwarjini Alhaji Mahmud Ajiwa yayma baba ba, mutum kirki dashi, sai daifa ya lura a kwai tsare gida, dan tunda yazo gurin baba baiga haƙorinsa ba da nufin dariya, fuskarnan sam babu wani fara'a, a sojansa yake na gaske dukda yayi ritaya ma tuni.

     Komai na asibitin Ummu Alhaji Mahmud ne ya biya, kafin yay musu sallama ya koma Kaduna dan tsara abinda ya dace. harya zo yatafi Ummukulsoom bata saniba tana barci.

          

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


       Tunda ya shigo falon Buhayyah da Bassam dake dariya suka nutsu, Ummayya ta ajiye wayar hannunta itama suka haɗa baki wajen masa sannu da zuwa.

     Fuskarnan kamar ko yaushe babu walwala ya amsa, sun ringa sun saba da yanayin mahaifinsu na rashin fara'a da ɗaukar raini, dan haka bamasa damuwa da wannan.

      Shima ya tambayesu ya gidan? Tareda batun sunje islamiyya (kasancewar shi bai yarda yaransa su dogara da boko ba kawai) kame-kame suka fara, saboda basuje ɗinba, dama ita Ummayya sai yana gida take zuwa, dan acewarta ta girmi zuwa islamiyya yanzu, saboda ta girma

     Dukda ya fahimci basuje ba sai bai ce dasu uffanba ya haura sama abinsa, dan yanzu yanada wani uzirin.

        Yasan Hajiya Jamila bata gidan shiyyasa bai nemetaba, dan tace zataje gidansu yarinyar ƙanwarta ta haihu, to ƙila tare da Aneesa suka tafi dan baigantaba.

      Saida ya watsa ruwa sannan yadawo falo ya zauna yana shawara da zuciyarsa akan ya sanarma Fodio maganar auren koya barsa saidai yaji an ɗaura?. Tunda dama yamasa gargaɗin ƙarshe akan yakawo matar aure amma shiru kakeji tamkar malam yaci shirwa.


WANENE ALHAJI MAHMUD USMAN AJIWA?


NO. 8


      Alhaji Mahmud Usman ɗan asalin jihar katsinane a ƙaramar hukumar Ɓatagarawa, cikin garin Ajiwa aka haifesa, anan ya girma haryay karatunsa na secondary, tun bashida wayo shi mutumne dama maison aikin soja, mutane da yawa sukance yadace da aikin, saboda rashin fara'a da yake da ita tun yana ƙaraminsa. Hakanne yasaka mahaifinsa fatan cika masa burinsa, cikin amincin ALLAH kuwa sai komai ya tafi dai-dai yanda ya kamata, dankuwa Mahmud yazama soja bisaga taimakon wani bawan ALLAH da mu'amular kasuwancin audiga ya haɗa malam Usman mahaifin Mahmud ɗin dashi.

         Wannan shine tushen dawowar Mahmud cikin garin kaduna da zama, anan kuma ALLAH ya haɗashi da Jamila ɗiyar Alhaji barau daya taimakeshi, dukda yanayin rashin fara'a na Mahmud tace taji ta gani, haka dama take fatan mijinta ya kasance, koba komai mata saji shakkar kawo masa wargi🤣.

      Ilai kuwa sai maganarta ta tabbata, dan komin son da mace kema Mahmud tsoron tunkararsa take saboda fuska babu wasane shi, bayan aurensu a cikin jaji suke zaune, babu jimawa saiga ciki ya bayyana ga jamila, sosai tayi farinciki, amma saitaga kamar Mahmud baiyiba.

     Hakan ya tashi hankalinta, takasa daurewa ta taresa da maganar, abunka da zuciya a kusa yako sheƙa mata mari, cikin faɗa yace, ”Amma Jamila bakida hankali da tunani, tayaya ALLAH ya azurtani da kyautar da babu dukiyar dake iya sayenta a duniya ki dangantani da wanda baya farinciki? Shin rawa kikeso nazo nayi agabanki sananm kisan ina murnane”.

     Jikinta na ɓari tace, ”A'a” sannan ta durƙushe gabansa tana hawaye da bashi haƙuri, bata taɓa tunanin zancenta zai fusatashi irin hakanba, halayyar Mahmud kulum ƙara bata tsoro take, dan saida sukai aure takuma fahimtar shi murɗaɗɗen mutumne mai bahagon fahimta, kokusa mutumne da bayason wasan banza, gashi magana kaɗan take fusatashi, sannan baka isa canja masa ra'ayinsa akan abinda yay niyyaba, tundaga wannan ranar bata kuma tunkararsa da makamancin maganar nanba, tacigaba da rainon cikinta, gwargwadon iko yana bata kulawarsa, hakama abinda ke cikinta.

     A kwana a tashi ALLAH ya kawo watan haihuwarta takoma gidansu cikin garin kaduna. Batafi kwanaki huɗu da komawarba ALLAH ya sauketa lafiya ta santalo ƴarta mace. Mahmud yayi murna sosai, sai dai bazaka taɓa ganin hakan daga fuskarsaba, hidimar dayake da mai jego da jaririyace amsar, dukdama a lokacin bawani ƙarfine dashiba, da ɗan albashinsa ya dogara da taimakon iyayensa kuma.

    Ranar suna yarinya taci suna Saliha, amma suna kiranta da (Ummi) saboda sunan (mahaifiyar Mahmud kenan). 

     Bayan arba'in jamila tadawo jaji suka cigaba da rainon ƴarsu Ummi. Watan Ummi takwas a duniya ALLAH yakawo wani cikin batareda jamila ta shirya zuwanshiba, gashi yazo mata da laulayi sosai, harma yafi cikin farko wahal da ita, ga Ummi bata isa yayeba, hakan saiya tada hankalin jamila ga zugar ƙawaye ƴan bani na iya, tako tada hankalinta akan zata zubar da ciki.

      Ran Mahmud yakai ƙololuwar ɓaci ya korata gida ta huta, mahaifinta kuwa ya goya bayanshi yabata rashin gaskiya. Hankalinta yatashi matuƙa, dan biris Mahmud yayi da lamarinta yacigaba da sabgoginsa ma, duk wata kuma zai aika mata da kayan abinci, amma bazataga idonsaba, gashi a lokacin babu zancen waya😂.

      Ta gurzu iya gurzuwa wajen iyayenta da kewar Mahmud, (kaji iyayen ƙwarai) saida tai laushi sosai, cikinta ya shiga wata takwas, dama an karɓe Ummi daga wajenta, dan kartasha ciki, tuni an yayetama.

     Cikinta na wata takwas Mahmud ya maidata gidansa dake cikin jaji, ammafa takuma ganin canjin da babu ƙofar kawo masa raini. Itama saita kama kanta tana taka tsantsan dashi dan a zauna lafiya, bata fatan kuma komawa gidansu dan tasha baƙar wahala, mamanta batai mata da sauƙiba, ballema baba dako gaisuwarta daina amsawa yayi.

     Saida Cikinta yacika wata goma sha ɗaya sannan ta haihu, kowa ya zura ido yaga ƴan biyu saboda uban girma da cikinta yayi amma sai sukaji tsit, sai guda ɗaya aka santalo musu namiji ƙato mai kama da Mahmud tamkar anyi kaki an tofar.

     A wannan karonma tasha hidima, dan albashinsa yaɗan matsa saboda girma daya ƙara samu a gidan soja, gakuma kasuwanci dayaɗan fara taɓawa shida wani abokinsa.

        Ranar suna yaro yaci Usman, amma saboda sunan mahaifin Mahmud ne suke cemasa (Fodiyo). Sai kuma  saboda sauran jama'a sai Jamila ta haɗa masa da *AMAAN!*.

     Wannan karon ma bata sauya zaniba, watannin Amaan bakwai shi baima cika takwas ɗinba saiga ciki, lokacin sunje hutun ƙarshen shekara Ajiwa, surukan da masu dattako, iya na ƙyalla ido taga Jamila da wani cikin saita karɓe Amaan tahana a bashi nono, lokacinne kuma Jamila ta fahimci wani cikinne da ita, tasha kuka a ɓoye, dan bata yarda oga Mahmud yaganiba gudun rikici. Amma harga ALLAH wannan saurin ɗaukar ciki kamar wata akuya yafara bata tsoro, gashi babu damar ta tanka Mahmud ya saka uwarta a waƙa.

    Haka ta haƙura, bayan hutunsu ya ƙare suka taho aka baro Fodio a Ajiwa badan jamila tasoba, ko kaɗan bata fatan tanayi wata a ƙauyen balle ace kuma ɗanta zai zauna can din-din, saidai batada wani ƙarfin ikon magana. Gashi dama Ummi tana gidansu, sai suka kuma dawowa babu yaro ko ɗaya a gabansu, garama Ita Ummi ana kawota ta kwana biyu anan.

      A wannan haihuwarma Jamila saita haifo ƴarta mace, wadda taci suna Ai'sha, amma suna kiranta Jalilah (Aunty Nurse) saboda sunan mahaifiyar Jamila Mahmud ya saka. 

      Bayan haihuwar Jalilah kam saita ɗauki mataki akan maganin tsara haihhuwarta, bisaga planing na gargajiya da wata ƙawarta taimata hanya, Mahmud baisaniba kuma, sannan daya fahimci tanayin bai tanka mataba  ya cigaba da sabgar gabansa, yanzu kam saida ta yaye Jalilah saiga wani cikin, shima bawani mugun tsira baneba, dan Jalilah shekararta ɗaya da rabi aka yayeta, wannan karon kam kuka hardana baƙinciki Jamilah tayi, kenanma maganin baya aiki? Dan ita sotai saitayi irin shekara huɗunnan kafin ta ƙara, amma hakan bata samuba.

      Shima wannan cikin ta haifeshi lafiya yaci suna Isma'il, (Ameer) saboda sunan mahaifin jamila ne aka saka.

    Adai taƙaice haka haihuwa tacigaba dama jamila kusa da kusa, bayan Ameer tai Ummayya, sai Aneesa, sai Bassam, sai kuma auta Buhayyah. 

     Tun bayan haihuwar Ummayya jamila taso tsaida haihuwa, saidai sanin halin mijinta yasata nutsuwa ta hakura dajan addu'ar ALLAH ya iyakance mata.

    To dayake ƙwayayen basu ƙareba saida alƙawalin ALLAH ya cika tai haihuwarta takwas cif, maza uku mata biyar.

       Ummi dai kam tazama ƴar gidan kakanni, dan ba a maido musiba, kawaici kuma ya hana Mahmud tambaya. Hakama Fodiyo duk rashin ƙaunar zamansa a ƙauye da Jamila keyi acan ya rayu, dan yazama ɗan gidan Iya. inma zaka tambayesa su wanene iyayensa zaice maka iya da baffah.

      Abinda zai baka mamaki babu abinda Amaan yabaro na halayyar mahaifinsa, rashin fara'a da zuciya a kusa, rashin shiga sabgar mutane daduk halin mahaifinsa da kuka sani.

     A garin Ajiwa ya rayu haryakai aji 6 na primary, yana tsaka da zana jarabawar ƙarshe ALLAH yayma Baffa rasuwa, wannan rasuwa ta girgiza mahmud da Amaan sosai, hakama iya,

      Bayan komai ya lafa Fodio yagama exam ɗinsa, Mahmud yace sai iya ta shirya ta dawo kaduna da zama.

     Takoyi tsalle ta dire tace bata dawowa kaduna itakam, a haifeta a ajiwa ta tashi anan har aure zuwa tsufa dan babu mijinta yanzu ace tabar tushen ta, sam wannan kam bamai yuwuwa bane.

    Babu yanda Mahmud baiyiba tadawo tunda babu ran baffa, amma sam tace bata dawowa. dan dole yabarta taci gaba da zama ƙauyen Ajiwa abinta.

     Tunda Mahmud ya sanarma jamila iya taƙi yarda ta dawo kaduna sai murnarta ta koma ciki. Dama can ba dawowar Iya bane damuwarta, ta ɗanta takeyi, danta ɗauki son duniya ta aza akan Fodio, da anyi magana tace tausayinsa takeyi saboda yana rayuwa a ƙauye, wannan yasa da akace zasu dawo kaduna take nuna masa tsantsar murnarta da kulawarta, sai kuma murna ta koma ciki.

       Kula da hakan da Mahmud yayine yasashi shareta kamar bai fahimtaba, akuma lokacin yaymusu gini a cikin gari suka dawo da zama. Dan yanzu yazama babban soja.

     Rayuwa tacigaba da tafiya har fodio ya kammala secondary school nashi a ƙauyen Ajiwa, a time ɗin iya ta kwanta jiyya itama, shine mai kula da ita, duk da shima Alhaji Mahmud kullum yana bisa hanya, daga ƙarshema ya maidota asibiti a abuja, kwananta huɗu ALLAH yay mata rasuwa. 

     Duk wanda yaga Fodio a wannan time ɗin dolene ya tausaya masa, dan shi kallon mahaifiya yakema Iya, ko wasan jika da kaka basayi daman.

      Wannan shine sanadin dawowarsa kaduna. Yaran gidan su Ameer dama sunsan baya wasa dasu, dan ko hutu yazo sukai masa shirme mazgarsu yakeyi tamkar ALLAH ya aikoshi, balle yanzu daya dawo zaman gidan dindindin. Wata soyayya ta musamman hajiya jamila ke nunama fodio, saika rantse shine tafara haifa, hakan da Alhaji Mahmud ya lura dashine yasashi ɗauke Fodio ya sakashi a N.D.A *(Nagerian Defence Acadamy)* gudin rabuwar kan ƴaƴansa, dan ƙaunar da jamila ke nunama fodio shaiɗan zai iya ɗarsa wani abu a zukatan sauran yaran suga kamarsu bata ƙaunarsu haka, jamila taita kuka ita ɗanta bazaiyi soja ba.

     Mahmud bai kulata ba saboda batayi a gabansa, dan haka ya nuna baimasan tanayiba, da anyi hutu kuma Fodiyo bayason zama kaduna sai Ajiwa, dan da can ya saba, kuma su ya sani.

           Rayuwa taci gaba da matsawa Amaan ya kammala N.D.A, akai posting nashi jihar Delta, bayan wasu shekaru a Delta aka maidashi Legos. Shine har yanzu yake zaune acan.

      A yaran gidan Ummi tayi aure harda yaranta, hakama Aunty Nurse, sai dai ita bata taɓa haihuwa ba, uwar miji tasaka mijinta ya saketa ya ƙara aure bayan kuma suna son junansu, wannan shine dalilin zamanta a gida yanzu, dukda ma ba ko yausheba, saboda a kano take aiki dan can tayi auren kafin ta fito.

      Amaan ma shekaru uku da suka wuce an saka masa biki da wata yarinya Safiyya, ɗiyar ƙanwar Alhaji Mahmud ce, dama haɗasu za ayi auren zuminci, bikinsu baifi saura wata biyu ba tayi haɗarin mota itada wata yayarta ta rasu, sai da mutuwarnan ta taɓa Amaan sosai, dan dukda haɗashi aure akai da Safiyya yarinyar ta kwanta masa arai saboda nutsuwarta, tunda kuma aka saka bikin bai taɓa tsayawa da ita kona second 1 ba da sunan zanceba, inama ta ganshi, ita tsoronsama takeji saboda zaneta daya taɓayi itada Aneesa wani hutu da tazo gidansu, shikuma time ɗin yana gida. Bayan rasuwarta bai kuma zancen aureba, sai lokaci-lokaci shi Alhaji Mahmud kan masa, shikuma ya nuna baya kula ƴar kowa, daga bayama sai ya tattarshi ya ƙyaleshi da batun auren.



 wannan shine tarihin gidan Alhaji Mahmud Ajiwa a taƙaice👌🏻.



*_MUNDAWO LABARI_*⛹‍♀


        Hajiya Jamila bata haƙuriba da daddare takira Amaan, nanma bai ɗagaba, saida ta yanke sannan ya kirata, gaisuwa sukayi, dukda dai banajin miyake faɗa daga can.

      Cikin damuwa ta zayyane masa halin da ake ciki, bansan miya faɗa mata daga canba naga ta miƙe tsaye cikin cagwaron ɓacin rai tana faɗin “Kana nufin harya kiraka ya sanar maka? Kaikuma ka amince ka karɓi auren ƴar talakawa wadda tai aikatau a godanku?”.

    Taɗanyi shiru alamar saurarensa, Alhaji Mahmud dake bayanta tsaye yacika yayi fam da ɓacin rai ya zare wayar daga kunnenta, hakanne yasakata juyowa a firgice tana kallonsa, ko inda take bai kallaba ya maida wayar a kunnensa yana faɗin, *“Uthman!* Ka tabbata idan Uwarka ta saka ka bijiremin akan wannan auren saidai ka nemi wani uban amma ba Mahmud ba, idan kuma kakaini bango wlhy saina janye lamunin danai maka kazo ɗaurin aurennan dole, koda zaka rasa aikin nakane kuwa”. Yana gama faɗa ya wurgar da wayar ƙasa yana nuna hajiya jamila da jikinta ke mazari, dan yanda yake a fusacennan kaɗan daga aikinsa yay mata duk abinda zuciyarsa ta bashi. “Wlhy Jamila kinji na rantse, idan har kikayi wasa akan aurennan zan saki nadamar da baki taɓa tunaniba”. Ya juya ya fice abinsa, dama yazo suyi magana ne akan auren, amma tunda ta zaɓi komai sai dai ta gani zai bi da ita ta hakan kuwa.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


          Yau tunda Ummu ta farka daga barci take faman kuka da zuba sambatun ambaton sunan Basiru karyay mata haka, wlhy tana tsananin sonshi.

       Sambatunta dai na yau yafi na kullum, doctor da y'an uwanta sai lallashinta sukeyi amma taƙi sauraren kowa. Haushine ya gama cika zuciyar Inna laraba, a harzuƙe ta daka mata tsawa da yunƙurowa tamkar zata maketa, 

     “Dan uwarki kimana shiru kona zauneki, shin Basiru shine autan maza halan a duniya? Yace yafasa aurenki sai me? Ko akace masa shikenan har duniya ta tashi bazaki samu wani mijinba? Aranda yace yafasa d'in aranar ALLAH yabaki Wanda ya fishi komai.............”

        A matuƙar razane Ummukulsoom ta ɗago ta kalli innar tata jin wai tasamu wani Mijin. To wanene? a kuma ina? Ita dai tasan bata kula kowa a kaf faɗin ƙauyensu sai Baseer ɗinta, a birni kuwa wani baitaɓa cewa yana sontaba, saima tsana da tsangwama da taita fuskanta a wajen uwar ɗakinta da ƴaƴanta, to inba sadaka baba yay da itaba ta inane zata samo Mijin aure cikin kwanaki biyu rak da fasa aurenta?........

     Zainaba yayarta da itama ke a dɗakin ta washe baki tana dafa kafaɗarta, “Ummu wlhy karkiji wasa, Alhajin da kike aiki agidansa yanajin abinda ya faru yace yana nemama ɗansa aurenki, yanzu haka goben dai za'a ɗaura miki aure babu fashi......”

      Ba tare dasun Ankara da halin da Ummu tashigaba kawai sukaga ta tuntsuro a gadon kawai.

     Atake Zainaba ta fasa ƙara, sauran ƴan uwa dake a waje suka antayo ɗakin da gudu, yayinda tuni likita shima yagama rikicewa.

         Daƙyar aka korosu waje dan samun damar bama Ummu taimakon gaggawa, dan takuma sume musu. Sosai hankalin kowa yake a tashe ga tsananin tausayin yarinyar da ta taso babu uwa a duniya, ga cutawar matan Uba, gakuma bala'in daya haye Mata a rana tsaka na rashin mssoyin data kwallafa rai a kansa yaci amanarta gab da cikar burin mallakar junansu.


        Hankalin likita yatashi sosai, dan jinin Ummu yaƙara hawa sama, da ƙyar suka samu sukai Mata allurar barci, komai saiya kuma susucema mahaifinta da ƴan uwanta, babu wanda bayajin tsananin tausayinta, ranarma haka suka kuma yini a asibitin, dan sai yamma lis Ummu takuma farkowa.

    Ba'abar kowa yashiga inda takeba sai babanta. Ya zauna kusa da ita yana rikƙo hannunta cikin tausayawa, “Haba Ummukhoolsum! Ɗita ki kwantar da hankalinki kinji, kizama cikin mutane masu haƙuri da karɓar ƙaddara aduk yanda tazo musu”.

        “Baba na karɓa ƙaddara, kuma na godema ALLAH, amma dan ALLAH karku had'ani aure da d'angidan Alhaji, wlhy matarsa da ƴaƴansa basason talaka ya raɓesu, shine kawai mutumin kirki, sannan indai Ameer ne ya tsaneni, ko taɓa Abu nayima a gidan to baya amfani dashi wlhy, dan ALLAH ka tausayamin baba, wannan gidan yafi ƙarfina, *WUTSIYAR RAƘUMI TAI NESA DA ƘASA!*, akwai babbar tazarar nisa data banbantani dasu, garama kayi sadaka dani ga wani acikin ƙauyenmu, namaka alƙawarin zan zauna na kwantar da hankalina baba”.

        “Yanzu ma Ki kwantar da hankalinki Ummukhoolsum, nima nasan sunfi ƙarfinmu, amma wlhy kunyar Alhaji da halaccinsa yasa naji bazan iya watsa masa ƙasa a idoba, domin shi da zuciya ɗaya yake sonki, kumani ba Ameer yacemin sunan yaronba, kamar *Fodiyo* yacemin”.

       Zaro idanu sosai Ummukhoolsum tayi, kafin ta ɗaura hannu aka ta fashe da sabon kuka, “Na shiga uku ni Ummukhoolsum tawa ta ƙare, dodon gidanma kenan gaba ɗaya ai baba. baba kana nufin Wanda naji suna cema *Yaa Amaan!?”.*

     “Ummukhoolsum ban saniba nima, yadai cemin ɗansa Fodiyo dake a birnin legas da zama”.

     Da sauri Ummu ta diro daga gadon jiyyarta ta durƙusa gaban babanta tana kuka, “Baba dan ALLAH kace masa a'a, wlhy indai ɗansa dake legas ne nama ƙarajin abun yafi ƙarfina, wannan ba shigata baceba, baba ni bamma sanshiba, a tsawon shekara ɗaya danayi a gidan ban ta6a ganinsaba, amma wlhy duk ƴan gidan tsoronsa sukeyi, dan sunce bashida mutunci ko kaɗan, yamafi Yaa Ameer ɗin, da wani yayi abufa a gidan akace za'a faɗama Yaa Amaan saikaga sun ruɗe da shiga tashin hankali,  baba kuma sojane fa, dan girman ALLAH baba karka basuni, nidai wlhy na haƙura da aurennan ka taimakeni baba”.

    Sosai tabashi tsananin tausayi da dariya, duktabi ta rikice dagajin sunan mutumin ma da ba ta6a gani tayiba, ya kamo hannunta ya maidata saman gadon, “Haba Ummukhoolsum ki kwantar da hankalinki dan ALLAH, bai kamata mu watsama Alhaji ƙasa a idoba har mak'iya su sami damar yimana dariya, kidubafa yaronda tun kuna ƙananu kuke tare yazo rana ɗaya ya gujeki akan kuɗi, kodan wannan takaicin bai kamata muyi sake da damar da ALLAH ya sake bamuba, domin inaji a jikina yamiki sauyin alkairine Ummukhoolsum, Alhaji yawuce haka a garemu....”

         “Baba ni kaɗai nasan tashin hankalin danake hangowa a zamana wannan gidan, wlhy baba akwai babbar Matsala, Alhaji ne kawai mutumin kirki sai aunty nurse, amma wlhy sauran duk mugayene, basa ƙaunar talaka ya raɓesu ko kaɗan....”

      “Ya Isa haka mana Ummukhoolsum, naji Zan duba kwanta ki huta hakanan kinji”.

     “Baba to za'a fasa ɗin?”.

       “Karki damu zanma Alhaji magana kinji, yanzu dai ki kwantar da hankalinki, kinga likita yace jininki ya hau sosai”..  

       “To baba Na kwantar, amma dan ALLAH kacema likitan ya sallamemu mu koma garinmu, ni nama warke gaba ɗaya”.

      “To shikenan zansa a sallamemu, kwanta ki huta kinji”.

    Bata musa masaba takoma ta kwanta tana share hawayenta.



★★★★★★★★★★


        Washe gari da sassafe aka sallami su Ummu suka koma ɗilau, dama shi baba tun jiya da yamma yakoma saboda shirye-shiryen ɗaurin aure.

      Sai kallon Ummu ake ana ƙus-ƙus na gulma, kowa burinsa yaga cikin da akace tayo, wasu kuma casuke ai cikin aka zubar a asibiti. A cikin gidansu ma duk zuba mata idanu sukai tamkar wata mujiya, dan baba bai sanarma kowa za'a ɗaurama Ummu aureba gobe sai mazan gidan, dayake ALLAH yasa masu hankaline suma sai sukaƙi faɗama matansu, sai bayan dawowar su Ummukulsoom daga asibiti inna harira ta sata tai wanka, ta bata abinci taci da magani tasake kwanciya tana cigaba da kukanta mara sauti Aziza da Murja na lallashinta.

      A tsakar gida kuma inna Harira ta fasa maganar ɗaurin auren Ummukulsoom da za'ayi bayan sakkowa massalaci, kallan kallo aka koma a tsakanin matan gidan, yayinda kuma suke dariyar gatsatsa a gefe da tambayar juna to wanene mijin? Ko ɗan inna harira ne Murtala?.

     Babu dai mai basu amsa, suka cigaba da gutsiri tsomarsu har lokacin da ƴaƴansu suka fara shigowa da gudu cikin gida suna faɗin wai motoci nata shigowa garin, tun suna ɗaukar maganar ƙaryar yara har suma suka fara jin garin ya ɗauki hayaniya da ƙarar motoci, abinka da ƙaramin ƙauye yo. Sai kuma ga baba yashigo yanata tattara tabarmi shida sauran mazan gidan.

      Sai kowa tashiga tambayar mijinta wai mike faruwa?. Sukuwa mazan amsarsu ɗayace ƴan ɗaurin aurene.

     Idan sunce ɗaurin auren wa? Basa samun amsa.


       Ummukulsoom dai barci yakuma ɗauketa batasan hidimar da akeyiba kwata-kwata, ita tama zata baba yasa sun janye kamar yanda yace mata. 

       Gari ya ɗauki ɗumi, amma anrasa taron mi akeyi ƙofar gidansu Ummu, wasu suce ɗan siyasane yazo, wasu suce malamaine sukazo wa'azi, ga kuma harda sojoji, kowa dai yarasa matsaya.

       Tun a wajen sallar juma'a akaji baƙon muryane ke limanci, saboda cikin baƙi yau wani yaja sallar Juma'a a babban masallacin garin. 

     Ana idar da salla kuma aka shiga sanar da ɗaurin aure, mutane kam duk sai suka nutsu domin jin ƙwam.

       An ɗaura auren *Ummukulsoom Buhari ɗilau* da angonta *Lieutenant Colonel Usman Mahmud Usman Ajiwa* akan sadaki mai tsoƙa.

      Sabon magana yazo Ɗilau kuma, gari ya ɗauki zance malam Buhari ya saida ƴarsa.........🙆🏻😨🤦🏻‍♀😂



NO. 9



         Baseer yana gidansu Suhailat yana hutawarsa hankali kwance, duk da ya kula jama'ar gidan suna masa wani kallon raini-raini, Suhailat ce kawai ke tareda tsantsar farin cikin kasancewarsa a gidansu, yau dai yakasa haƙuri yamata ƙorafi suna zaune a harabar gidan suna shan iska.

      Cikin tsareta da idanu yace, “Love niko wani abu na damuna da zaman gidannan naku”.

    Itama hankalinta ta maida gareshi cikin nuna kulawa, “Miyake damunka ne Love!?”.

     “Sai nake ganin kamar ba kowa ke sona a family nakib.....”

    Saurin saka hannu tai ta rufe masa baki tana girgiza kai, “Haba Love, wace irin maganace wannan? Wlhy kowa yana sonka, ahankali zakaga sun saki jiki dakai, kasan har yanzu akwai rashin sabo, amma ka faɗamin wanene baya sake maka a cikinsu?”.

     Hannunta ya zame daga kan bakinsa yana kuma ɓata fuska, “Suhailat ko daddynki bayasona, dan kawai ya faranta mikine ya amince na aureki”.

      Murmushin ƙarfin hali tamasa, dan tasan tabbas daddynta baya ƙaunar wannan auren nasu, amma batason shi ya fahimci hakan, ta dafa hannunsa tana kallon fuskarsa dake kuma dulmiyata a ƙaunarsa, “Love Daddy yana sonka, yanajin haushine saboda katsewar karatunmu ni da kai, amma zuwa nan gaba kaima zaka fahimcesa, dan yanda yake sona kaima haka yake sonka”.

    Badan ya yardaba ya ɗaga mata kansa kawai, daganan suka shiga hirar shirye-shiryen bikinsu.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


          Garin ɗilaufa ya kuma ɗaukar sabon zance akan ɗaurin auren Ummukulsoom, harma wani bayajin zancen wani. Yayinda jama'ar da suka halarci ɗaurin aure suka fara barin garin.

    A cikin gida kuwa zuba ido ake aga ango ya shigo gaida iyaye kamar yanda aka saba, amma sai sukaji tsit, nanfa abu yazama abun kace nace har ran inna laraba ya ɓaci matuƙa tahau zazzaga tsiya cikin taro, da faɗin ai badai dole sunga angoba, idan sun daka ransu a inuwa shekarama kwanace indai mijin Ummukulsoom ne zasu gansa duk daren daɗewa.

      Wannan hayaniyace ta tashi Ummu a barci.

    Da ƙyar ta iya haɗa bayanan masu tsogumi waje ɗaya, harta fahimci abinda ke faruwa, jikinta rawa kawai ya farayi, dan ƙafafunta suna neman gaza ɗaukar gangar jikinta, ta zame a hankali ta zauna tana sharar ƙwala da tunanin miyasa baba bai karɓi uzirintaba ya yarda ya aura mata mutumin da kowa ke tsoro......

      Tunaninta ya katse saboda kiran da inna harira ke mata, ƙwallanta ta share kafin ta miƙe tafito bakin ƙofa inda Inna harira ke tsaye.

      Inna harirah dake kallonta tace, “Sako hijjabinki zaki gaisa da baƙine”.

    Komawa tayi da baya, ta ɗauki gyalen Aziza dake aje a tabarma jikin ts duk a sanyaye. Inna Harira ta kama hannunta suka fito tsakar gida, kanta a ƙasa ta kasa kallon mata dake cike da gidan ƴan biki da ƴan gulma. Gashi dama sun zuba mata ido tamkar yau suka fara saninta.

        Soron gidan malam Habu inna harira ta kaita.

      Alhaji Mahmud ne zaune a tabarma shida wasu abokansa biyu shaƙiƙai, sai Ameer dake tsaye gefe yana cika da batsewa, dagani kasan yazo ɗaurin aurenne dan tilas.

    Ummukulsoom ta durƙusa a gabansu ta gaishesu muryarta na rawa, ga hawaye na zuba danma gyale ya kare fuskar.

      Duk sun amsa mata cike da kulawa, tareda addu'ar zaman lafiya da samun zuria ɗayyiba, suka ɗora da saka mata albarka itada mijin nata da bata saniba, bakuma taga alamar yazoba.

     Alhaji Mahmud yataso yafito waje yana kiranta. Tasowa tai ta biyoshi, can gefe suka koma inda babu jama'a, amma dukda haka saida aka saka musu ido har wasu na zargin koma shine mijin?.

      Shi dai Alhaji Mahmud ko a jikinsa, fuskarnan kuma babu fara'a tamkar ko yaushe. Ya kallli Ummu dake durƙushe a gabansa,

     “Kiyi haƙuri ɗiyata, kizama cikin mutane masu karɓar ƙaddara aduk yanda tazo musu, insha ALLAHU zakiyi farin ciki a ƙarƙashin jinina, ki manta da komai daya faru a baya, ki fuskanci sabuwar rayuwar da zakiyi yanzu. Mun gama magana da mahaifinki da a yau zamu wuce dake, amma saboda wasu ƴan dslilai muka bar tariyar taki sai satin sama idan ALLAH ya kaimu, aidaita haƙuri da rayuwa kinji, zan aiko Isa da saƙo zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu, tashi ki koma ciki, ALLAH yay miki albarka”.

      Kai kawai ta iya kaɗa masa, kafin da ƙyar tace, “Amin Dady, na gode da karamcinka gareni, ALLAH ya ƙara girma da lafiya mai amfani, ya sakanka maka da mafificin alkairi”.

      Karo na farko danaga yayi wani ɗan guntun murmushi wanda saika saka masa ido zaka fahimci yayisa, idonsa a kanta yace, “Tashi kije ciki, muma wucewa zamuyi yamma tayi”.

     Nanma kanta ta ɗaga masa tamiƙe tana tangaɗi da ƙyar ta iya isa inda Inna harira ke jiranta.


      Tunda Ummukulsoom ta koma ciki saita ƙunshe kanta a ɗaki tana cigaba da tunanin yanda rayuwa zata gudana a gidan Alhaji Mahmud, yanzu haka tana kula yanda Ameer yake jifanta da kallon ƙyama da tsana, ta rasa miyasa Alhaji Mahmud yagaza fahimtar wutsuyar raƙumi tai nesa da ƙasa tsakaninta da ɗansa, sannan baba yagaza fahimtar ita abinda take hangowa. 

     Har yamma tana ɗaki, sai ƴan biki dakan leƙo su gaisa irin ƙawayensu da sukai rayuwar yarinta, waɗanda mafi yawansu a yanzu idan ka gansu saika ɗauka yayun Ummukulsoom ne, wasuma tamkar sun girmeta sosai, su Azima kansu dake aure a birnin duksun wani tsofe mata a ido, dan Azima ma fama take da ƙaton ciki na huɗu yanzu haka.

    Zuwa yamma su Murja suka saka waƙa a redio sunaji ana kwasar rawa da guɗa, tareda shewa da dariyar yaran mata.

       Sune ma sukaje suka kinkimo Ummukulsoom daga ɗaki dole ta fito tsakar gidan dake cike da  mata, saboda anan inna laraba ke karasunta matsayin Uwar ƴa tunda babu mahaifiyar Ummukulsoom a duniya.

      Ga ƙatuwar tukunyar tuwo masara fari ƙal anata tuƙi, sai miyar taushe da kunun zaƙi da zoɓo, duk dai dangin mahaifiyar Ummu ne sukayi dan itama tayi farin ciki, karkuma tayi kukan rashin Uwa.

     Cigam ɗin dasu Murja suka siyo itadasu Aziza sukazo kan Ummu suna zuba mata suna tiƙar rawa, wai cingam ɗin shine matsayin kuɗin liƙi.

      Batare da Ummukulsoom ta shiryaba tasaki murmushi tana ture murja dake callara mata buɗa a kunne, yayinda Aziza da Nusaiba da Hadiza ke zuba mata cingam.

     Manyan iyaye irinsu baba yalwa da gayyar ƴan biki suna kallonsu, wasu kuma na aikin abinci, yayinda wasu ke gulmarsu group-group, irinsu baba yalwa kuwa danne zukatansu kawai sukeyi, dan wani sashe na murna wani sashe na baƙin ciki.

      Har dare kusan tara gidan anata kujiba-kujiba irinta biki, yayinda wasu ke kwasar ƙafafunsu suna wucewa gida ana barin ƴan uwa irinsu Murja da suka cigaba da cashiyarsu.

    Itadai Ummu tunda tagudu ɗaki sallar magriba bata sake dawowa ba ma. Sai wajen tara da rabi yunwa ta isheta ta leƙo kozata hango Aziza, amma tagaza ganinta, danma garin ƙwanyar yake da hasken farin wata kasancewar yau daren sha biyar.

     Ruwa ta ɗiba a buta tanufi bayi, tafitone ta hangi Murja can gefe tana wankema ɗanta Amadu kashi tana masifa saboda a wando yayi.

      Ƙarasawa Ummu tayi taimata dundu a baya, Murja ta ɗago tana sosa wajen zatai masifa saitaga Ummukulsoom ce.

      “Kai kai wlhy dama ance ƙashin amare ƙwarine dashi, amarya karki ƙarasani kijama mijina salalan tsiya”.

     Ummu ta harareta tana ɗaukar Amadu daga gabanta ta ƙarasa ɗauraye masa jikin da butar hannunta, cikin dusashshiyar muryarta da kuka ya dishe tace, “Kindawo nan kinama yaro mugunta, ALLAH ya isarmu”.

      “ALLAH Umma bazaki ganeba, tunfa ɗazun nace yaje ya hau fo amma yay kunnen uwar shegu dani, dan wulaƙanci da wayonsa yay kashi a wando, dashi zanji koda Sa'a?”.

      Ummu data kammala masa ta ɗaukeshi a hannu tana faɗin, “ƙila to baiga fo ɗinba, kinacan kina tiƙa rawa zaki nutsu ki bashine, mizan samu a gidannan inci nasha magani, yunwa nakeji”.

     “Tab aiko sai tuwo, kuma kinsan yagama hucewa, ba ɗazun naga Halima da kwanoba tace kezata kaima fura inji baba furera?”.

     Ɗan yamutsa fuska Ummu tayi tana gyara tsayuwa, “Kinsan bancika damuwa da furaba Murja, kuma lokacin banajin yunwa, da Jummai tashigo itada kishiyarta naga ƴarta nata kallon kwanon shine nace ta zauna tasha”.

      “A to lallai bakida mankai, to yanzu da furar haki ce kumafa? Ke bakisan shegan son banzar Jimmai ba ashe, itada bata wuce tayi duk gidan data shiga saboda shegen kwaɗayinta datayi sallama ake kife kwano da murfi”.

    Karo na farko da Ummu tai dariya har haƙoranta suka bayyana tunda tadawo garin ɗilau, “Kai Murja ALLAH ya shiryaki, nidai samomin ko tuwon ne naci dan ALLAH”.

     “A'a ba ayi hakaba amarya da cin tuwo, bara na mayi ango tunda baya kusa, ina zuwa naba Kamilu ya siyo miki shayi wajen idi na bakin yara”.

      Duk kiran da Ummu take mata akan karta bada bata sauraretaba, ta karɓi Amadu daga wajenta dantaje ta saka masa kaya.

      Ummukulsoom ma wuce yaran dake rawa tayi takoma ɗaki, bayan yunwa ma har wanka tanada bukatar yi kodan nauyi da jikinta yay mata, rabonta da wanka tunna safe bayan sun dawo a sibiti, da yamma ma dazata canja kaya daga alwalar la'asarne tashafa mai ta canja kayan.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


           Su Alhaji Mahmud sun iso kaduna gab da magriba, baima shiga gidaba ya tsaya masallaci, saida yay har sallar isha'i sannan ya ƙarasa ciki.

         Duk ƴan uwan hajiya Jamila da sukazo sun wuce, daga ita sai ƴaƴanta yanzu a gidan harda Ummi babbar ƴarsu Aneesa, saikuma ƙannen Alhaji Mahmud su uku da sukazo daga Ajiwa, da wata tsohuwa gwaggonsu. Kasancewar ba sakewa suke a gidanba idan baya ciki duk suna ɗaki, saisu Aneesa dake a falo suna kallo da hajiya Jamila da ƙanwarta Mansura dake aure a kano, dama tun jiya tana gidan, ita keta kuma tunzurata akan ƙin auren na Amaan da Ummu.

      Duk nutsuwa yaran sukai suna masa sannu da zuwa, fuskarnan tashi babu walwala kamar kullum ya amsa, Mansura ma ta gaidashi damasa ALLAH ya sanya alkairi.

         Ganin babu danginsa a falon ransa ya sosu, harya kama kafar benen zai hau ya juyo yana kallon hajiya jamila da gabanta yafaɗi lokaci ɗaya saboda yanda taga idanunsa.

     “Su su Faɗima suna ina? Naji banji motsinsu ba?”.

     Cikin inda-inda hajiya jamila tace, “Sallar isha'i sukashiga yi, da duk muna zaune a falo muna hira”.

      Yasan halinta sarai, kuma yanayinta yasashi sanin karya take, baice uffanba ya ida haurawa yabarta nan tsaye tana binsa da kallo. Saida taga ya ɓacema ganinta sannan ta juyo suka haɗa ido da Mansura suna wani ƙyaɓe baki.


     Koda ta biyoshi harya cire kayansa zai shiga bayi wanka, ko kallonta baiyiba ya shige abinsa, dukda taji takaici haka ta zauna a bakin gado zaman jiransa.

     Wayarsa data fara tsuwwa alamar kira ta kalla, ganin sunan *Fodio* ya sata ɗaukar wayar ta ɗaga kiran.

      Daga can Jarumar muryarsa ta fidda sautin sallama tareda faɗin “Dad kun dawo gida lafiya?”.

    Takaici yasaka hajiya jamila miƙewa tafita da wayar falo dan kar Alhaji Mahmud yaji mizata ce, a falonma saida taje can ƙarshe kafin tace, “Lallai Fodio, nadai lura kai bama ka kishin kanka akan aurennan ko?, ɗazun kuma na kiraka kaki amsamin waya saboda ka maidani ƙawarka”.

         Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke daga can yana lumshe manyan idanunsa daya gada a wajenta, kafin yasa hannu ya dafe kansa, “Momcy Ina yini”.

     “Lafiya lau” ta amsa a ƙufule.

      dukda yaji yanda ta amsa saiya basar yace, “Dad fa?”.

     Cikin gatse tace “Na dafashi na cinye, Fodio banason wulaƙancinka fa na basar da abu, namaka magana baka bani amsaba kana kawo wata tambaya daban”.

      Muryarsa mai nuna tsantsar jarumtarsa daya gada ga Alhaji Mahmud da nutsuwa ya kuma sanyayawa, “Momcy banida abin faɗane shiyyasa”..  

       Haushi ya ƙara kama Hajiya jamila, tace, “Ni wlhy Fodio dama kurma ALLAH yayoka danafi jin daɗin haka, koba komai nasan kurma na haifa, dan iskanci mutum yamaka magana goma ka bashi amsar ɗaya”.

    Rasa abinda zaice mata yayi, sai yace “Yi haƙuri to” abinda kawai yace kenan yay shiru, danshi mutumne bamai yawan magana ba, sunema yake ɗan daurewa yay magana mai tsawo dasu itada dad.

     Jin kamar motsin fitowar Alhaji Mahmud yasata komawa ɗakin da sauri tana faɗin, “Yana wanka, amma gashinan fitowa”.

    Fodio dake saurarenta daga can ya yanke wayar kawai yana sauke numfashi tareda gyara kwanciyarsa a doguwar kujera..

         Alhaji Mahmud baibi takantaba yahau shiryawa cikin jallabiya doguwa.

    Ganin hakan ne yasata cewa, “Fodio ya kira kana wanka, gakuma abinci yana jiranka”.

     Batareda ya bata amsar farkoba yace, “Bazanci abinci ba, akwai fura da muka dawo da ita a ɗiba a dama min”.

     “Fura kuma? Yanzu Abban Fodio duk irin munin ƙauyennan da Ameer ke faɗamin haka zaka iya shan furar da akayo daga can, inama laifin afita asiyo maka mai tsafta wajen Hamza”.

     Wata banzar harara ya watsa mata, ya tsallakota ya fito abinsa.

    Tamkar zata makesa tabiyo bayansa da sassarfa. A falo ta iskeshi yana ƙokarin kiran Fodio. Ganin yanda ya kuma kicin-kicin da fuska yasata ƙokarin ficewa ta cika Umarninsa.

     “Ki turomin su Asiya”.

Wani takaicinne yakuma rufeta, ta amsa da kyar tana fita, gata a gidan amma dan wulaƙanci zaice ta turo masa ƙannensa. Shiyyasa bataso suzo gidan kwata-kwata.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


          Washe gari ma ancigaba da ƴar hidimar biki daba a rasaba, dukda babu ango babu danginsa, zuwa yamma kuma baba yace Ummu ta shirya gidan gwaggo Hinde kakarta zata koma da zama har zuwa rar tarewa. Tayi murna da hakan sosai, dan ta lura zaman gidansu babu abinda zai ƙara mata sai baƙin ciki da damuwar tunawa da basiru, dan habaici da gugar zana kawai ake zuba mata tun jiya akan fasa aurenta da yayi, tun tana hawaye akan ƙananun maganganun harma zuciyarta ta dake tabar jin kukan. Musamman ma dayake Aziza na kusa da ita a ko yaushe tana ɗebe mata kewa.

      Da daddare tareda Aziza suka tafi gidan gwaggo Hinde, dama kayanta dukta tattara ankai can tunda yamma.

      Wannan komawa gidan Gwaggo Hinde da Ummukulsoom tayi yajawo ƴar hayaniya tsakanin Baba da matansa, wai wani munafuncin yake shiryawa shiyyasa yace Ummu takoma gidan kakarta.

    Banza yaymusu yaƙi kulasu, dan ya lura hassada ke cin ransu kawai, da akace an fasa auren Ummukulsoom da basiru ai cikin farin ciki suke, ko jiya da safe dasukaji zancen ɗaurin aurenta da wani basu damuba, saida sukaji labarin yawan motocin da sukazi ɗaurin aure da manyane mutane sannan hankalinsu ya tashi, dukda sunjin daɗin angon baizo ɗaurin aureba.

     Shirun baba yakuma sasu takaici, saisuka zauna da ƴaƴansu su Nusaiba suna gulma. Zainaba ce dama kawai babu ruwanta, dan ita harga ALLAH tana ƙaunar Ummukulsoom matsayin ƴar uwarta Uba ɗaya.


★★★★★


     Komawar Ummukulsoom gidan gwaggo yaɗan sake bata nutsuwa, yayinda gwaggo ta duƙufa gyarata da maganin sanyi, ko yaushe suna tare da Aziza dan suma basu komaba sai randa za'a tafi da Ummukulsoom.

       

     


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


         Kwana biyar da ɗaurin auren Ummukulsoom sai ga Baseer ya danno ɗilau da dalleliyar motarsa fara sol.

     Yawani ƙara ƙyau da ƙiba ɗan zaman dayay na kwana takwas a gidansu Suhailat.

       Sai wani faɗi yake da fankama, yayinda yara suka zagaye motar suna kallo.

     Baba yana zaune a ƙofar gida yana kallonsa, ya gaza cemasa uffan sai ido daya zuba masa ko ƙyaftawa bayayi.

     Gabansa yazo ya durkusa yana gaidashi ido a ƙasa. 

    Baba ya amsa yana faɗin ”Kaiko Basiru ina kashige haka dan ALLAH?,  kana ganin wannan rayuwar ta dace dakai? Kofa sallama bakai manaba kabi mutuminnan saboda yafimu yanzu a wajenka ko?”.

       Ɗan juyawa Baseer yayi gudun kar wani yaji abinda baban nasa ke faɗa, ganin duk taron yarane saiya juyo yana kallon baba cikin ɓata fusaka yace, “Please baba kabari mushiga daga ciki zan maka bayani ai”.

     Kaɗa kai kawai baba yayi yacigaba da rubutunsa da yakeyi a allo. Basir kuma yamiƙe yashiga cikin gida yana ƙunƙunin baba yaƙi ya waye, arziƙi na kiransu amma suna rintse ido.........?


NO. 10


            Inna dake tsakar gida tana surfen ƴar masarar tuwonsu ta ɗago ta kalli basiru batareda ta amsa masa sallamarsaba, harya ƙaraso gareta bata iya janye idontaba, hannunta ɗaya da taɓarya ɗaya kuma tana ƙokarin janye kan akuya dake saka kai a turmin da take dakan, ƙarasowa yay yana girgizama Inna makullin motar hannunsa, fuskarsa washe da murmushi.

     “Innata kuma fa ALLAH ya kaiku matsayin dawani mahaluki bai taɓa takawaba a garinnan”.

    Ɗauke idonta tayi daga kallonsa tacigaba da dakanta tana faɗin, “Nagani kam, yaka baro su baban naka?”.

    Duk da maganar tata ta doki zuciyarsa saboda fahimtar gatse tamasa amma saiya basar ya amsa da “inna suruki dai, iyayena kam ai kune, amma suna lafiya lau, sunce na gaidaku da ƙyau, wani satin zasuzo maganar auren”.

     Inna tasaki murmushin takaici da jinjina maganar a ranta, gidan mazane ke zuwa neman aure, amma su yau ga sabon salo suna gani, gidan mace suna zuwa neman aure gidan namiji.

    Bata sake bi takansaba tacigaba da dakanta, shima saiya miƙe yana mitar ƙurar ƙasa da turmin ke tayarwa zata ɓata masa jiki.

    Ci kanka inna bataceba itadai.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


       Ummukulsoom batada labarin dawowar Basiru ɗilau sai a washe gari, shima Mariya ce datazo gidan take faɗa mata, dan itama tazama budurwa yanzu, sunema ƴammata masu tashe a ɗilau, dukda kuwa shekarunta 14 yanzunema suka shiga js3, amma Ummu tasan daganan ba gaba zasuyiba.

      Sosai zancen dawowar basiru da dalleliyar mota ya tsayama Ummukulsoom a rai, ta ɓoye a bayi tasha kukanta dataje wanka, tasan fidda son Basiru aranta abune mai matuƙar wahala da fama, amma zatayi ƙoƙarin kamantawa koda da kokawane da yaƙin ƙwanji dana zuciya.

      Tsaf gwaggo ta lura da halin da take a ciki saboda taji lokacin da mariya ke sanar mata, amma saitayi tamkar bata gantaba, dan tasan yimata maganar tamkar cigaba da fama mata gyambon dake zuciyartane.

     Zama Ummukulsoom tayi ta rubuta doguwar wasiƙa ta ajiye, da nufin gobe kafin a wuce da ita zata bada akaima Basiru.


★★★★★

  

       Shirye-shiryen miƙa Ummukulsoom kaduna yanata kankama, duk abinda yakamata anmatashi, ƴan gyararraki na jiki gwaggo hinde tamata iya iyawa, maganar kayan ɗaki dai Alhaji Mahmud yace su baba karsuyi komai, dan Ummu ma ba kaduna zata zaunaba, legas zatabi mijinta..


        ★★★★★★


Washe gari sukuku Ummu ta tashi tamkar mara laka a jiki, ita kaɗai tasan halin da take ciki, sai Aziza datasan halin mutanen gidan Alhaji Mahmud, dukda gaskiya itama bata taɓa ganin mijin Ummu ba.

        Aranarma dai baba yazo har gidan gwaggo yasake ma Ummu nasiha shida sauran iyayeta ƙannen mamanta, daga nan yace Ummu ta shirya bayan sallar zuhur taje can gida tama su baba yalwa sallama.

     Da to ta amsa masa tana sharar hawaye.

         Gaba ɗaya sai Ummukulsoom ta daina fahimtar komai dake faruwa a gidan, hatta faɗan dasu gwaggo hinde sukai mata dasu inna laraba da babanta babu abinda ta fahimta, saima nanuƙema Gwaggo himde da tayi akan itafa sai da ita indai anason taje.

     “Haba Ummukulsoom kiyi haƙuri mana, kinga yanzu an yanke da mutum biyar kawai za'aje, insha ALLAHU namiki alƙawarin idan ƙura ta lafa zanzo naga matsugunninki kinji”.

     Ummu na kuka tace, “Nidai Gwaggo ban yardaba”.

       “Karki yarda ɗin dan Ubanki, ke koma banzar halayyar matan ubanki bazaisa kiji ɗokin barmusu gidanba yau suci baƙin halinsu suda ƴaƴansu, ga cin fuska da basiru yay mana, amma ubangiji ya nuna masa shine gatanki, ni tashi muje ki canja kaya konayi kutufon lahadi bakwai dake”.

      Jikin Ummu na ɓari tabar jikin Gwaggo tabi Umarnin Inna laraba, dan itace mai masifar.

        

    Ƙarfe biyu dawasu mintuna Ummukulsoom da Aziza suka fito daga gidan gwaggo tana sharar ƙwalla, yayinda su inna laraba kebinsu a baya, dan bazata sake dawowa gidan gwaggo ba, daga can gidansu za'a wuce da ita kaduna.

     Babu abinda zuciyarta keyi sai lugude da dukan goma-goma, saboda dole sai sunbi ta ƙofar gidansu Basiru, fatanta da addu'arta ALLAH yasa karta gansa.

       Sai dai kuma addu'arta bata karɓuba, dan tana karyo kwana dashi tafara tozali, ta sauke manyan idanunta bisa ƙyaƙyƙyawar farar fuskarsa ta asalin jinin fulani, hakan yai dai-dai da ɗago tasa fuskar shima suka haɗa ido, daga ita harshi saida gabansu ya faɗin, Ummu ta sakar masa wani murmushin takaici daya zauna bisa ransa tamkar zane akan dutse. shine yay saurin janye nasa yana wani tamke fuska tamkar yaga mutuwa, danshi fa har yanzu babu wanda ya faɗa masa an ɗaura ma Ummu aure, to baya mu'amula da kowa a matasan garin, dan gani yake shi yafi ƙarfinsu, Inna da baba kam ma ko kallon arziƙi basa masa, daga amsa gaisuwarsa basa daɗawa basa ragawa, hakan kuma bai damesaba, a cewarsa idan sukaga kuɗi zasu sakkone.

      Ummu kam ƙoƙarin haɗiye hawayenta takeyi da wani bahagon ƙududu daya tokare maƙoshinta, saida suka ɗan gotashine ta zaro takardar data rubuta a hijjab ɗinta tabama Aziza da nuna mata basiru da hannu tai gaba.

     Fahimtar da Aziza tayi ne yasata amsa takoma baya tana tamke fusaka dan bama ta buƙatar basiru ya kawo mata raini, ita ƙyansa bawai ruɗarta yayiba.

     A saman motarsa dayake ƙokarin buɗewa ta ɗora masa tana jifansa da harara, “Gashinan inji Ummukulsoom ”.

    Bata jirayi amsarsaba tai gaba saboda kusantowar su inna laraba, bayanta yabi da kallo cikin takaici, wlhy data tsaya da sai ya kifa mata mari, cikin jan tsaki ya ɗauki takardar ya jefa a mota yashiga yana faɗin “baƙauyar banza, dama kinbar wahal da kanki wajen rubutamin wasiƙa, dan ayanzu dai tsakanina dake *Wutsiyar raƙumi tai nesa da kasa*. ban ƙiba zuwa nan gaba ƙila na dawo gareki kema ki dandali arziƙi”.

      Shi kaɗai yake sambatunsa a mota ya na tuƙi, dan zaria zaije.

       

      Haɗuwa da basiru ba karamin miki ya tadama Ummukulsoom ba, shiyyasa kwata-kwata bata fahimtar faɗan da ƴan uwan baba suke mata, itadai tana saurarensune kawai.

      Gab da la'asar motoci uku sukazo na ɗaukar amarya, dan babane yacema Alhaji Mahmud ba mutane da yawa bane zasu rakota, shi soyayma akaita da safe baƙi su juyo da yamma.

    Amma sai Alhaji Mahmud yace sam bazai yuwuba, saisun kwana itama kowa yasan ƴar gatace.

       Bayan an idar da sallar la'asar ne aka fito da Ummukulsoom dake kuka tamkar ranta zai fita, mata sai leƙe suke ta katanga, marasa haƙuri kuwa sunfito tsakar santa inda yara suka baibaye motocin ɗaukar amaryar.

    Mota ɗaya kayan Ummukulsoom aka loda, na gara da wanda zata iya buƙata da kayan sawarta, ɗaya kuma mutum huɗu suka shiga, uku mata namiji ɗaya cikin yayunta.

     Ɗayar motarma mutum biyu sai ummu ta Uku, sai aziza a gaba.

      Kamar haɗin baki yara suka fara raira waƙar amarya ta bankwana, hakan saiya kuma janyo hankalin mata suka makalƙale katangu suna kallo har motocin ɗaukar Ummukulsoom suka lula.


★★★★★

   

      Ganin basiru ba ƙaramin tsayama Ummukulsoom yayi a raiba, har suka ɗauki hanyar kaduna tana kuka ƙasa-ƙasa na tausayin kanta, shikenan yau tabar ahalinta gaba ɗaya tatafi gidan aure, gidan Aurenma inda akafi ƙarfinta, kallon lamari take tamkar wani almara ko film.   

        Abu ya haɗe mata goma da ashirin, kukan rabuwarta da tushenta da mahaifinta datafi ƙauna fiye da kowa da dangin mahaifiyarta, kukan rabuwa da masoyinta basiru wanda alamu sun nuna da gaskefa sun rabu har abada, yaya zatayi da ɗunbin so da ƙaunar da take masa kenan?, ga rashin jin daɗin jiki, sai fargabar sake sabuwar rayuwa a gidan Alhaji Mahmud, ga tsananin tsoro da firgici idan tama tuna wata aura?, dawa zata zauna?.

          Kwata-kwata tarasa jinta da ganinta dama dukkan tunaninta har suka bar garin zaria, tunma tana jin fitar iska sama-sama har idonta ya rufe ruf taji ɗif sai duhu daya mamaye jinta da ganinta.


        

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


            Momcy zaune a ɗaki itada ƙanwarta Mansura da bata wuceba, sai Ummi babbar ƴarta.

       Kallo ɗaya zakai musu ka fahimci duk ransu a ɓace yake, Mansura ta sauke numfashi tana janye tagumin da tayi.

        “Aunty Jamila ga shawara, nifa a ganina kibi gargaɗin da mijinki yay miki, dan kinfi kowa sanin halinsa. Mu tarbi amarya tamkar ranmu babu komai, idan zata wuce legos ɗin nan ne zamu samu damar gudanar da shiri na gaba kuma”.

         “Hum mansura kenan, da kinsan yanda nakejin wani baƙin ciki akan aurennan na Fodio da bakice na danne zuciyata na tarbi shegiyar yarinyarnan da danginta ba, amma kuma ba a ƙin ta mutane inji masu ida magana, minene shirin namu na gaba?”.

      “Yauwa auty, abinda dama nakeson ki tambaya kenan, bayace nanda kwana biyu za'a kaita wajen Amaan ɗinba?”.

      “Eh haka yace”.

“To Aunty anan ne kekuma zaki lallaɓasa akan kinaso kuje duka gidan rakata, zaki samu damar ganawa da Amaan ɗin kema, idan kun tashi tahowa abaro masu Ummayya da Aneesa su zasu ƙarasa mana sauran aiki su hana tsinanniya zaman lafiya, tunda ba koyaushe Amaan ke a gidaba dama”.

      Ummi da tun ɗazun batace komaiba tai saurin faɗin, “Wlhy shawaran ki yayi Aunty Mansura, Momcy mubi wannan shawarar”.

        Numfashi Momcy ta sauke, tace, “Shikenan ALLAH yasa mu dace, yanzu sai a tashi afara shirya abincin tarbar amarya, suma dangin nasa ai musu magana, dannifa nama ƙagara akawo maryar gobe su kama gabansu, duk sunzo sun cika mana gida”.

      Baki Mansura ta taɓe tana miƙewa, “Aini kinama min ƙoƙari wlhy, ni bama zan ɗauki wannan iskancinba dangin miji suzo su taremin agida a hanani rawan gabar hantsi, komai nayi da mijina da ƴaƴana idonsu nakai”.

      Ummi ta haɗe fuska dan zuciyarta ta sosu da maganar ƙanwar mahaifiyar tata, koba komai dai aisu dangin mahaifintane, kuma sune adonta. Tashi tai ta fice tabar musu ɗakin, duk suka bita da kallo mamaki.

    “Tofa, Wai Ummi haushi taji? Tafison dangin Ubanta akanmu kenan?”.

      Momcy kasa cewa uffan tayima ita, dama wannan halin Ummi ne, tatsani a kushe dangin dad nasu, ta nan ɓangaren suna shan saɓani da Momcy ɗinsu, dan itakam tana son dangin mahaifinta.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

  

        Sun isa cikin kaduna gab da magrib, Alhaji Mahmud na a harabar gidan zaune yana alwala, direba ya danna hancin motar cikin gidan bayan sojan mai gadin ya buɗe musu gate.

         Inna laraba ce ta fahimci halin da Ummu take ciki na gushewar tunani, dan haka takamo hannun ta fiddota a mota tana mata magana ƙasa-ƙasa.

     “Haba Ummukulsoom dan ALLAH ki kwantar da hankalinki, insha ALLAHU lafiya zakiyi zamanki, ALLAH yana tare dake ɗiyata”.

    Guntun murmushi kawai Ummu tayi, zuciyarta nawani irin suya da luguden tsoro tamkar zata faɗo ƙasa, ƴar hayaniyar mutane dake tunkarosu yasata gyara gyalenta sosai takuma rufe fuskarta tana haɗiye hawayenta.

      Dangin Alhaji Mahmud ne na Ajiwa da sukazo biki, shine suka fito tarbar amarya saboda isa yaleƙa ya sanar musu, ganin Hajiya Jamila da ƙawayenta basuda niyyar hakan da danginta saisu sukaga yakamata su nuna halin dattako da cikar mutuncin ɗan uwansu. 


    Yanda dangin Alhaji Mahmoud sukema su Inna harira lale marhabun sai farin ciki ya kamasu, dansu basuyi zaton hakanba, musamman ma Altine matar ƙanin baba da Inna laraba da gidan Alhaji Mahmud ya rikitasu, sai yanzu Inna laraba tafara fahimtar abinda Ummukulsoom ke nufi da mutanen sunfi ƙarfinsu.

        Alhaji Mahmud daya kammala alwalarsa saiya miƙe zai fita masallaci. Ya kalli Ameer daya shigo yanzu da mota, da alama daga wajen aiki yake, janye idonsa yay daga kan Ameer dake tunkaroshi ya maida ga ƴan uwansa, cikin ƙannensa ya yafito ɗaya da hannu.

     Da sauri taje gareshi tana faɗin “Yaya baƙi sun iso kuma, To ALLAH ya sanya alkairi ya bada zaman lafiya, yasa abokiyar arziƙinsace”.

       “Amen” kawai yace ya gyara tsayuwarsa, “Amina mike faruwa naga kunbar baƙin anan?”.

     “Babu komai yaya, yanzu muke shirin shiga dasu ciki, saidai bamusan inane za'a saukesuba, dukdama naga basu da yawa”.

      “Ina ita jamilar?”.

“Tana ciki yaya, munga direba yazo ya sanar da isowarsu amma babu wanda ya motsa a cikinsu shiyyasa mukaga yadace mu mufito”.

        Tuni fuskarsa takuma nuna alamar ɓacin rai, kallon Ameer yay daya iso, cikin harshen turanci yace yaje yakira masa hajiya Jamila”.

     Ummu da Aziza kawai sukaji miyace, dukda ita Ummu ma bawani can sosai takejin turancinba.

     Minti baifi Ukuba saiga Hajiya Jamila ta fito cikin kwalliya, fuska ta saki ganin Alhaji Mahmud tsaye a wajen, “Baƙi sannunku dazuwa, Rakiya ashiga dasu ciki mana tsayuwarmi kuke anan?”.

     Kallom mamaki duk sukai mata da jinjina makircinta, sunsan dai dantaga yaya su ne take wannan barikacin.

      Inda yake can gefe tsaye ta nufa, “Abban Fodio gani, ina bayi isa yashiga yana sanar da isowars....”

    Wani banzan kallo yamata na kinma rainamin hankali.

    Hakanne ya saka zuciyarta lugude.

      Cikin kaushin murya yace, “Wlhy Jamala ki kama kanki, karki bari haƙurina yaje bango akan lamarinnan fa”.

       “Haba Abban Fodio kayi haƙuri dan ALLAH, kagama gashican ana kiran salla karka makara”.

      Baikuma cemata komaiba yanufi hanyar fita.

      Taɗan harari bayansa kafin tajuyo gasu Ummukulsoom tana washe haƙora saikace gaske.

     

         Abin mamaki su Ummukulsoom suka sami tarba ta mutunci gasu Hajiya Jamila, wannan abu yabama Ummukulsoom mamaki, dukda dai ta zargi kodan baƙin ido tayi hakan? Dakuma ganin Alhaji Mahmud yana gida.

        Dan gidan babu laifi yacika da dangi da ƙawayenta.

     Aziza ma abin ya ɗaure mata kai over, tarasa ya da zata fassara wannan tarba da akai musu, suko su Inna Laraba basusan dawan garinba, sai suketa jinjina kirki irinna jama'ar gidan.

     Abinci mai rai da lafiya aka baje musu, saida sukaci suka ƙoshi sannan suka fara shirin sallar magrib da aketayi, Ummu dai taƙi cin abincin, tundama suka shigo kwance take abinta, sai kunun aya da Inna Harira ta takura matane tatashi tasha, dama tana fashin salla, dan haka koda suke ta alwala ita bama ta motsaba daga kwancen da take.

     Bayan hajiya jamila da Aunty Nurse Ummukulsoom bataga kowaba a yaran gidan har suka kwanta barci.



★★★★★★★★


      Da safe ma abinci mai ƙyau aka basu, sukaci suka ƙoshi kafin suɗan ƙarama Ummu faɗa suka hau shiri, dan sosuke suje gidan Inna harira su huta zuwa gobe su koma ɗilau kamar yanda ta roƙi alfarma.

     Bayan sun kimtsa aunty Nurse tazo taimusu rakkiya falon Dad kamar yanda yabada Umarni, sun gaggaisa dayima juna godiya, tareda addu'ar sanya albarka ga auren.

    Yayinda Momcy dake gefe ke murmushin yaƙe, dan takaici ya kumeta jitake tamkar ta makesu.

     Mota yabada akaisu gidan Inna harira, zuwa gobe isa yaje ya maidasu ɗilau.

    Cikin mutunci aka rabu, yayinda Ummu ke kwasar kuka tamkar numfashinta zai fita, Aunty Nurse taja hannunta zuwa wani sashe can gefe idan ka wuce nasu Ameer, tunda tazo gidan kusan shekara ɗaya bata taɓa shiga ɓangarenba, saima lokaci-lokaci ta lura ake buɗeshi a gyara, ita tama zata ba'a amfanin komai aciki...........



NO. 11


  .............Tamkar sokuwa haka takebin kowacce kusurwa na falon da kallo, komai dake cikinsa silba ne, sai ɗai-ɗaikun abubuwa bulu....

    Yanda take bin falon da kallone yabama Aunty Nurse dariya, ta murmusa tareda kamo hannun Ummukulsoom suka zauna a kujerar farko.

      “Ummukulsoom nan shine sashen mijinki, anan zaki zauna kafin ki wuce, duk kayanki suna nan ankawo tun ɗazun kinji”.

        Kan Ummu a ƙasa ta  amsa da “To Aunty” duk da kuwa tsorone fal ranta, taya zata iya kwana ita kaɗai anan?.

    Miƙewa aunty Nurse tayi ta fita, zuciyarta na tausayin Ummu da yanda zata rayu da yayan nasu mai bahagon hali tamkar mahaifinsu.

    

     Ummukulsoom ta daɗe wajen zaune tana tsiyayar da hawayen tausayin kanta da kewar ahalinta dake damunta, ga dai jiyanta ta wuce da ƙalubalen rayuwa kala-kala, gata a yau ɗinta a wani bigiren da ita kanta takasa fassararsa, to kenan yaya gobenta zata kasance kuma a ƙarƙashin fadar sarki mai cikakken iko irin mijinta dako ganinsa bata taɓa yiba sai jin labarin tsantsar mulkinsa da tsagwaron barazana ta kasaitattun maza.

       Duniya babban gida, mai cikeda abubuwan ƙawa da tsoro harma da firgici, zuwa yanzu takuma yarda RAYUWA tana tafiyane da JARABAWA, idan yau ta wuce da nata salo, gobe saitazo ɗauke da nata itama, babu kuma wani hannu daya isa goge rubutun da yazo a alƙalamin ƙaddara, shiyyasa masu iya magana sukance duniya rawar ƴammata, to lallai rawar ƴammatan ce kam.

      Tafi zaman awa ɗaya a wajen kafin tasami yunƙurawa da ƙyar saboda kiran sallar azhar da aka ƙwalla. 

     Kuma baje idanu tayi tana ƙarema falon kallo a karo na biyu, komai a tsare tamkar na mace, sai dai babu hoto ko ɗaya alamar mamallakin sashen baya buƙata, dan ita ko a falon sashen su Momcy taga hoton kowa a gidan amma banda nashi, a fili ta furta “Toko baya hoto ne?”. taɗan taɓe baki da ɗage kafaɗa alamar shiya sani.

      Tamkar munafuka ko mai shirin sata tana gudun a kamata haka ta laɓaɓa zuwa ƙofar da aunty Nurse ta nuna mata matsayin bedroom ƙwara ɗaya tal dake sashen, ta ɗora hannunta jikin ƙofar ta murɗa a hankali kafin tafara leƙa kanta tamkar zata ganoshi. Sai kuma ta ida shigewa gaba ɗayanta.

    Bedroom ɗinma tamkar falon haka yake, dan shima ɗauke yake da Silver and blue color ɗin komai, saman gadon babu bedsheets katiface kawai sai filos suma babu riga. Taɗanbi ko ina da kallo sannan tanufi toilet, nanma dai masha ALLAH, Sai dai babu komai na amfani kamar irinsu sabulu da sauran tarkace na bayi kamar yanda tasan nasu Ameer suke, itadai tai alwala tafito tai salla.

    Tana idarwa Aunty Nurse tashigo itada Buhayyah dake ɗauke da tire, sai kumbura baki take alamar ansata kawowa tilas ne.

    Idon Aunty Nurse Buhayyah ta faka ta dallama Ummukulsoom harara kafin ta dangwarar da tiren zata juya.

    Ummukulsoom tai ɗan murmushi tana haɗiye abinda ya tsaya mata a maƙoshi, yayinda Aunty Nurse ta dakama Buhayyah tsawa da faɗin, “K dan Ubanki dawo nan, ita sa'arkice da bazaki gaidataba”.

    Tamkar Buhayyah zata rushe da kuka tace, “Ina yini” cikin yamutse fuska da harar Ummukulsoom ƙasa-ƙasa.

     Ummu tace, “Lafiya lau Aunty Buhayyah”.

     “Aunty Kuma? Buhayyah kike cema Aunty? To aiko kar bakinki yay kuskuren faɗa gaban yaa Amaan, inba hakaba zai haɗa ke da ita ya kakkarya wlhy”. Ta maida kallonta ga Buhayyah daketa wani huhhura hanci, “kekuma kika tsaya mana a kai, ki buɗe Wadrobe ki ɗakko bedsheets ki shinfiɗa a gadonnan”.

     Buhayyah zatai magana Aunty Nurse ta watsa mata harara. 

    Babu shiri tayi shiru tabi Umarninta, ɗakko bedsheets ɗin tayi tana ƙoƙarin shinfiɗawa tamkar zatai kuka.

    Ana haka saiga Bassam yashigo shima yana kumbura tasa fuskar, ledar hannunsa ya miƙoma Aunty Nurse daga ƙofar ɗaki. “Aunty Nurse gashi”.

     “Humm nizan taso na amsa kenan, to ka wuce kasaka kowanne inda ya dace a toilet, banzayen yara kawai, duk kugama iskancinku yanzunan yaa Amaan zaiji komai wlh.....”

       Gabb!!

    Da sukaji yasakasu waigawa su duka.

     Bassam ne yakusa kifewa ƙasa saboda jin aunty Nurse tace saita faɗama Yaa Amaan. 

      Gaban Aunty Nurse yazo ya tsugunna, itama Buhayyah haka, suka fara mata magiyar roƙon dan ALLAH tayi haƙuri.

      “Kunsan da haƙurin kukema mutane iskanci?, yanzu ita sa'arkuce? Ko kai Bassan danake tunanin zakuyi sa'anni dagani Ummukulsoom tabaka watanni, balleke Buhayyah, idan zaku dawo hankalinku ku dawo, dan yanzu matar Yaa Amaan ce ba ƴar aikinkuba, inkuwa bazaku gyaraba kunsan halinsa sarai, kune zakusha wahala wlhy, kutashi kuban waje”.

     Su dukansu duk sun zama kalar tausayi, dan sunsan kaɗan daga aikin aunty Nurse ta sanarma yaa Amaan ɗin.

      Hakan da sukai sai Ummukulsoom takumajin tausayin kanta, wannan shi wane irin mutumne to? Takan kai maƙurar tunanin wajen fasalta wannan yaa Amaan amma saita kasa, ƙwaƙwalwarta tagaza, mutumin da baya kusa ana masa irin wannan mugun tsoron ina ita da zatayi rayuwar aure dashi, lallai tana tsaka mai wahala itakam. Basiru ya sakata a ramin kura, dan dabai fasa aurentaba daduk hakan bata faruba, da yanzu sunacan cikin aminci da farin ciki.......

     Tana ta tunaninta harsu Buhayyah suka kammala komai, aunty Nurse ta tasa ƙeyarsu suka fice.

       Abincin taɗanci sannan ta kwanta saboda ciwo da kanta ke mata.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


        Washe garin kawo Ummukulsoom shima daddyn Suhailat yaje ɗilau suka tsaida magana da baban Basiru, wannan karonma sai sha musu ƙamshi yake da yaɓa musu magana, amma sun gaza ɗaukar mataki saboda sihiri na cinsu, wata ɗaya kacal aka tsaida na bikin, su Baba basu damuba, tunda dai babu abinda zasuyi, dan haka basuja zancenba suka amince.

     Daɗi tamkar zai kar Basir, dan jinsa yake a sama can ƙololuwa, shifa yanzu ya wuce da tunanin kowanne banza.

    Kafin kacemi ƙauyen ɗilau ya ɗauki labarin Baseer mai ƙashin arziƙine, wai zai auri ɗiyar mashahurin mai kuɗi a birni. Wasu masu hankali da tunsninsu yafara dawowa hanya sukance dama saboda ita ya yaudari Ummukulsoom kenan? Magan ganu dai kala-kala nata zagaye ɗilau da kananun ƙauyuka maƙwafta.

     Koda Malam Buhari yaji labari Murmushi kawai yay baice komaiba,  a washe gari ma ya shirya yabaro garin domin komawa ga sana'arsa.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


      Ɓan garen Suhailat ma tana cikin tsantsar farinci, kallo ɗaya zakai mata kuma ka fahimci hakan daga gareta, kwana biyu da tsaida bikin suka tafi dubai itada Amrah da maminsu haɗo mata kayan lefe dana ɗaki.

   Abin yabama baseer haushi, danshi yazata dashi za'aje Dubai ɗin haɗo kayan🤣😝. Sai kawai Suhailat ta kirasa da daddare tana faɗa masa gobe fa zasu wuce.

     Yace, “Ina kuma Love?”.

       “A'a, Love yada tambaya irin haka? Dubai mana haɗo kayan lefe dana gidanmu”.

       Da ƙyar ya iya haɗe abinda ya tsaya masa a maƙoshi yana fisgo magana, “Kina nufin har kunsami visa?”.

      “Eh mana, jiya da ƙyar daddy yakuma jajircewa yasamo mana, dama tawace taso bada matsala, amma yanzu komai normal, karka damu ba daɗewa zamuyiba, sannan komai zan fara turo maka idan yamaka sai a ɗauka”.

       Jiyay tamkar ya mannama ubanta zagi, amma ya danne yace, “Uhum, ni bara naje su Najeeb na jirana, idan kun sauka mayi waya”. Baijira amsartaba ya yanke wayar yanajan dogon tsaki.

       Yagama zubama su Arfaan ƙaryar zaije dubai haɗo kayan auren Suhailat shida daddynsa da Suhailat ɗin, shine zasuyi masa wannan wulaƙancin, shi yanzuma mizaice dasu Abdull ɗin idan sunga bai tafiba? Ko kashe wayarsa zaiyi yay tafiyarsa Ɗilau kawai yay kamar kwana goma saiya kunna yace musu ya dawo?.

      Haka yayta juya maganar a ransa har Nehal ƙanwar Najeeb ta iso wajen.

     Ƙamshin turarenta ne yasashi ɗagowa ya kalleta.

        Murmushi tamasa, yayinda shikuma yaɗan basar yana wani shaƙar iska da ƙyar. Gaidashi kawai tayi tai shigewarta gida.

    Ya bita da kallo yana lasar laɓɓa, baiso ta tsaya iya gaisuwaba, dan ya ƙagara ta furta masa kalmar so itama, sai dai yakula yarinyar kamar tafi Suhailat iya jan aji.....

     “Bas! Mikake leƙe hakane wai?”. ‘Arfaan yafaɗa yana dukan kafaɗarsa’. 

    Firgigit yadawo hankalinsa yana jan tsaki, “Babu komai my guy, inasu Najeeb ɗin mu wuce”.

    “Gasunan zuwa, kasan iyayin Abdul, wai kaya yake canjawa”.

     Baseer yaɗan taɓe baki yana miƙewa tsaye.


     Daga can kuwa Suhailat bata kawo komai a rantaba ta ajiye wayar da tunanin cikin uzuri yake ƙila.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


             Ummukulsoom bata farkaba sai da aka kira sallar la'asar, alwala tayo tai salla, tiren abincin da aka kawo mata ta ɗauka ta nufi sashen su Momcy zuciyarta na dukan ɗari-ɗari na tsoro. Ta can ƙofar baya tabi tashiga kicin. Jud nata ƙoƙarin haɗa abincin dare yana raira waƙarsa ta sabo.

    Yana ganinta ya hau washe baki tareda risinawa yana faɗin “Madam good Everning”.

      Ummukulsoom taɗan hararesa da wasa, “Oga Jud yau kuma nice Madam ɗin?”.

       Cikin hausarsa dabata fita da ƙyau yace, “Ai kama wuce Madam, kai Momy ne, kana matsayin matan Boss Amaan nefa yanzu, Walayi ka more Madam Umikusmu, dan Boss Amaan ya haɗufa, sune mazan da ƴammatan yanzu ke rubibi fiye da kuɗi. Damma shi mutumin kirkine baya harkar mata, amma da kinsha go slow walayi......”

     Ummukulsoom ta katse Jud da faɗin “Nidai Oga Jud bar wannan zancen, inasu baba Halima suke ne?”.

       “Suna ciki Alaji ya kirasu, kinsan yau ana bada albashi, nima na amsa nawane tunda safe”.

       “Oh to Congrat oga jud”.

     “Thanks you so much Ma!”.

     Yafaɗa a matuƙar girmame.

    Murmushi kawai Ummukulsoom tayi tafito ta koma sashenta. A hanya tagamu da Ameer, ko inda take bai kallaba dukda gaidashin da tayi. saima tsaki daya ja mata.

    Gwiwarta a sage takoma masaukinta tana neman sassaucin wannan sabuwar rayuwa a wajen Ubangiji.


        Ita kaɗai taita rayuwa a sashen cikin kaɗaici har dare, tsoro ta faraji dan haka tayanke shawar zuwa nemo ɗan tayen kwana, tana ƙokarin fita aka ƙwanƙwasa ƙofar, ɗan firgita tayi, amma saita danne zuciyarta ta buɗe tana addu'a a ranta, ganin baba Halima ɗauke da tiren abinci yasata saurin karɓa tana faɗin “Baba da kanki? Dan ALLAH kibar kawowa, ai gara ki kirani na amsa”.

     Ƴar dariya baba halima tayi, “Ai girmankine yanzu hakan, kodan mutuncin Yaa Amaan a girmama matarsa, balle kema yarinyar kirkice Ummukulsoom”.

       “Baba kishigo to”.

 “Wai rufamin asiri Ummukulsoom, kaf ma'aikatan gidannan babu wanda ya taɓa shiga sashennan, yaa Amaan bayaso, duk ƙyuyar yaran gidannan nakin aiki sune ke gyara masa sashensa ko yana gari ko bayanan, kedai sai da safe kawai”.

      Idon Ummukulsoom ya ciko da ƙwala, a fili tace “Na shiga Ukku ni Ummu. wlhy baba tsoron kawana nakeji anan ni kaɗai, dama yanzu zanje nemanki ki tayani”.

     ”Ummukulsoom bar wannan maganarma kar wani yaji, ki daurema zuciyarki, babu abinda zai sameki wlhy, bara na tafi kar wani cikinsu ya ganni anan azata wani abun muke kitsawa kinji, ki aje zuciyarki waje ɗaya babu abinda zai sameki da yardar ALLAH”.

      Baba Halima na tafiya Ummukulsoom ta rushe da kukan tausayin kanta, wannan wane irin gidane haka?.


★★★★★★


        A daren yau inhar barci ya ɗauki Ummukulsoom to ɓarawone, gaba ɗaya a tsorace take, ko yaya taji motsi sai taji kamar kanta akayo, sai gabannin asubahi tasamu tai barcin, hakanne yasata makara har sai da Aunty Nurse tazo ta tasheta.


        Momcy nason zuwa tama Ummukulsoom tatas amma Alhaji Mahmud ya kafa ya tsare, dan yana gida babu inda yake fita sai massalaci saboda bayajin daɗin jikinsa kwana biyunan, shiyyasama yaɗan ja tafiyarsu lagos.

    Shikuma gama fahimtarta da yayine yasashi jamata dogon gargaɗi itada ƴaƴanta akan Ummu.

     Wannan yasa Ummu samun zaman lafiya a kwanaki huɗun nan, sai idan tazo gaishesune aita dalla mata harara, sai dai babu damar aci zarafinta, dan kullum da safe saita shiga ta gaidasu, hakama da yama zata shiga dagaan tadawo sasheta tai zamanta, bata da aboki hira sai tv.

     Akan tafiyarsu kuwa tsaf yagama fahimtar shirin matar tasa shiyyasa ya saka mata ido, koda ta tuntuɓesa da batun binsu lagos rakkiyar Ummukulsoom Shiru yay mata, saida ta sake maimaita masane yay mata wani kallon data sha jinin jikinta kafin ya ɗauke idonsa akanta.

      “Jamila wai dan ALLAH yaushene zakiyi hankali ki tuna kin girma?, babba dake mai mazgegen ɗa kamar Fodio da Ameer amma har yanzu baki gama sanin ciwon kankiba, ke yamzu idan ance kije rakkiyar suruka saikije?”.

        Ɓata fuska tayi tana hura hanci, “To Abban Fodio naga kaima dai zuwa zakayi ai ko”.

       “ALLAH ya shiryeki to tunda ni nazama kishiyarki”.

    Da kallo ta bisa tamkar zata fasa kuka, haryaje ƙofarsa ya juyo yana kallonta, “Saura kuma kice zaki kirashi, inma kinyi to kinyi a banza, ranku zai ɓacine dagake harshi ɗin”.

      Kasa cemasa uffan tayi, dan yakai ta iya wuya ainun yau wlhy, amma kuma yagama fuffukarsa saita raba wannan auren, dan bazata taɓa barin jininta zama da ƴar aikiba amatsayin mata, jinin natama irin Fodio datake ƙauna fiye da sauran ƴaƴanta.


      Da daddare Dad yasaka aunty Nurse ta kira masa Ummukulsoom, kanta a ƙasa ta durƙusa ta gaidashi cike da ladabi.

      Da kulawa ya amsa mata dukda dai fuskar tasa babu fara'a kamar kullum, yace, “Ki shirya ɗiyata, insha ALLAHU gobe zaki koma wajen mijinki, dukkan kayanki yanzu kije ki fiddosu da asubahi isa zaiyi gaba da matar da zata ringa ɗan miki ayyuka, mukuma zuwa yamma zamubi jirgi insha ALLAHU”.

       UMMU ta haɗiye hawayen da suka cika mata ido da ƙyar, kafin tace, “To baba nagode, ALLAH ƙara lafiya”.

     “Amin” ya amsa mata, kafin yace tashi kije abinki.

     Kanta ta jinjina masa tana share hawayenta cikin dabara, sannan ta miƙe ta fito.

     A falon ƙasa ta iske Momcy zaune itada Aunty Ummi, gabanta ya faɗi, ƙafafunta na rawa ta ida sakkowa a benan, cikin risinawa tace, “Sannunku mommy”.

    Babu wanda ya amsa mata a cikinsu, dan haka ta ƙara maimaitawa a karo na biyu, nanma basu amsa mataba, sai aunty Ummi ce tace “k zonan dan Uwarki”.

    Rintse ido Ummu tayi taɗan buɗe, saboda zagin ya shigeta, bata jama mahaifiyarta addu'aba taja mata zagi.

    Gabansu taje ta durƙusa tana danne kukan dake neman ƙwace mata.

       “Munafuka, wane shegen boka kika kaima sunan dad ɗinmu haka?”.

      A razane Ummu ta kalli aunty Ummi tana girgiza kanta, dan bakinta ya gaza furta komai.

    Momcy tace, “Badake ake maganaba! Kika zuba mana waɗannan munafukan idanun?”.

     Ƴar zabura Ummu tayi tana fashewa da kuka, “Wlhy Momcy babu wajen bokan da naje, bamma taɓa zuwa wajen boka ba wlhy, ƙaddarace kawai hakan, ku yarda dani”.

       “To, wato ƙaddara ce? To kinji Momcy ƙaddara ce”.

     Ƙwafa Momcy tayi tana dungure kan Ummu, “Dan Ubanki zakiga ƙaddara kuwa, da ƙafafunki saikin nemi gidan Ubanki indai Fodio ne, tashi kibama mutane waje baƙauyar banza”.

     Kafinma Momcy ta rufe baki Ummukulsoom ta bar wajen, haka ta fice tana kuka da tausayin kanta.

    Baba Halima data gants tajata can wani lingu tai mata nasiha akan halin surukarta da dangin mijinta, takuma kwantar mata da hankaki.

    Wannan ne yabama Ummu ƴar Nutsuwa hartaje ta fiddo musu kayan Isa ya loda a mota, danshi tafiyar asuba zaiyi.


*_Washe gari_*


              Ƙarfe Shida na yamma Ameer yakai Ummukulsoom da Alhaji Mahmud airport, tasha kuka kafin subar gidan, Momcy harda mata nasihar munafunci agaban Dad, data faki ido kuma ta danna mata harara, har harabar gidan suka rakota, saida tashiga mota sannan suka koma ciki zuciyar Momcy tamkar zatai bindiga, nanfa tashiga ƙokarin kiran Fodio amma wayar na nuna mata Number busy. Takaici yakuma kamata tamkar zata fashe.

  

       A airport su Ummu sukai sallar magriba, tanata kalle-kalle da tsarkake sunan ALLAH, a tsawon rayuwar bata taɓa ganin jirgi a ƙasa ba sai yau, bata kuma shan mamakiba ma saida suka shiga zasu tafi.

    Ita dai rumtse idontama tayi, dan jitai cikinta na juyawa tamkar zatai amai lokacin da jirgin zai tashi. Wai ita Umma ƴar ƙauyen ɗilau ɗinnan, marainiya mara gata da galihu a cikin gidansu, itace yau zaune ɗane-ɗane a jirgi, ALLAH mai girma da ɗaukaka, mai yin yanda yaso a lokacin da yaso, ko wa zata tarar kuma a matsayin miji? Oho, ta haɗiye ƙwallar idonta tana karanto addu'ar daduk tazo bakinta saboda zuciyarta jitake tamkar zata wantsalo ƙasa dan firgici............✍


NO. 12



        *_LAGOS STATE_*


       Tunda Jirgi ya sauka a filin jirgin *Murtala Muhammad international airport* Dake birnin Lagos zuciyar Ummu ta ƙara ƙarfin gudu da tsitstsinkewa, wani irin ruɗani ke kuma mamaye illahirin jikinta da kuzarinta, ƙarshen tika tiki tik, yaune dai zataga wannan jan gwarzo abin firgici ga ahalin gidan Alhaji Mahmud Ajiwa.

       Wani ɓarin zuciyarta kuma na mamakin legas ɗin da taji matasan garinsu masu zuwa neman kuɗi suna cewa kwana biyu ake a hanya kafin azo shine su suka isa a lokaci ƙalilan haka?. ALLAH mai iko da rahama kenan.......

     Tuntuɓen data kusanyi ne ya saka Alhaji Mahmud dake gabanta faɗin “Kula mana”.

    Kanta tai saurin jinjina masa tana damke handbag ɗinta sosai cikin hannu ta, sanye take cikin doguwar riga baƙa mai kyau da aunty Nurse tabata a yau ta saka, sabuwace dal tasha adon duwatsu sai ɗaukar ido takeyi, ɗan kwalin rigarne aunty Nurse ta naɗa mata saboda yanada girma sosai, sai farar handbag madaidaiciya da takalmanta marasa tudu, jikinta na fidda sirrin ƙamshin humra da inna harira ta haɗa mata a kayan gudunmawa, sai turare mai daɗi ƙamshi, tayi ƙyawun da duk wanda ya kalleta saiya sake kallo, dukda kuwa babu wata kwalliya a fuskarta bayan fauda da lipsgloss data ɗan shafa shima dan kar lips nata su bushe ne.

     Kanta a ƙasa take bin Alhaji Mahmud a baya, saboda haske daya haske airport ɗin tamkar rana.


★★★★★

          

          Fitowar su Ummukulsoom daga jirgin yay dai-dai da isowar motocin su Yaa Amaan biyu cikin airport ɗin, yaɗan kalla agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa yana jan siririn tsaki.

      Attahir babban abokinsa kuma amininsa ya kallesa yana faɗin “Please ya isa haka mana Ajiwa, ai gamu mun iso akan lokaci, tunda yanzu ma suke fita a jirgin”.

       Uffan baice masaba, dama Attahir yasan ba amsar zai samuba, dan a halayyar Amaan sai dai yabama wani labari kuma.

     Fita sukayi saboda buɗe musu ƙofa da akayi.

      Attahir da idonsa ya sauka akan Alhaji Mahmud yay saurin cewa, “Alhamdllh ga Dad canma”.

       Amaan ya ɗaga manyan idanunsa daya gada ga Momcy yana kallon inda Attahir ya nuna, numfashi yaɗan sauke kafin yataka ahankali yabi bayan Attahir da tuni yanufi Dad yana masa oyoyo.

     Dad yace, “Yauwa Attahir, da kanku kukazo tararmu haka?”.

      “Ai dolene Dad, yau da kanka a lagos aiko zama bai ganmuba, sannunku da zuwa”. ‘Ya ƙare maganar da kallon Ummu da kanta ke a ƙasa’.

     Kafin tasamu damar bashi amsa gabanta yay wani irin faɗuwa saboda jin wata nutsatstsiyar murya mai cikeda izza ta ambaci, “Dad barka da zuwa”.

     “Yauwa Fodio, kuke da sannu da muka taso  akan aiki”.

    Numfashin Ummu yay sama yay ƙasa kafin tasamu jarumtar fisgoshi da ƙyar, lallai tana bukatar kallonsa amma tagaza hakan, gushewar jinta na wucin gadi yahanata jin amsar daya bama mahaifinsa. Da ƙyar tasamu damar satar kallonsa shida abokin nasa dake gefenta yana ƙara jaddada mata kalmar sannu da zuwa,

     Sanye yake da wando fari tas dogo sai baƙar t-shert da akai rubutu da manya haruffa a gabanta kamar haka. *_NICE HANDSOME_*.   

           Alhaji Mahmud ya nunama Amaan Ummukulsoom da hannu yay gaba abinsa inda yaran sojoji biyu ke tsaye jikin motocin da sukazo dasu.

      Yaɗan rausayar da kansa yanabin bayan mahaifinsa da kallo, cikin wani irin yanayi ya zuƙi isaka ya fesar daga bakinsa, kafin ya sauke idonsa akan Ummu dake tsaye tamkar an dasata a wajen, baiwaniga fuskarta sosaiba dan haka ya janye idonsa yana harar Attahir daya bar wajen shima yana dariya ƙasa-ƙasa.

     Siririn tsaki yaja yafara taku cikin bajinta na masu isashshiyar lafiya da jarumta zuwa gabanta.

       Babu zato Ummukulsoom Sai tsinkayar muryarsa tayi daf da ita.

       “Sai an kaiki motar ne?”. ‘Yafaɗa cikin kausasa murya mai fidda fusata’.

      A razane Ummu ta ɗago ta kallesa tai azamar maida kanta ƙasa saboda ganinsa gabanta gingirin gin, tafara ƙoƙarin Haɗiye abinda ya tokare ƙofar maƙogwaronta tana matsawa baya kaɗan, cikin in ina tace, “I..n..a y..ini”.

      Sai da yaja numfashi tamkar bazai amsaba sannan yay taku biyu yana faɗin, “Lafiya”.

       Kawai yace yana yin gaba abinsa.

       “Innalillahi.... Ummu tashiga maimaitawa tanabin bayansa da sassarfa, yayinda jikinta ke rawa tana tafiya tamkar zata zube ƙasa, ta tabbata da takalmi mai tsinine a ƙafarta babu abinda zai hanata faɗuwa. Dukda kwaɗayin ganinsa da take ta kasa kallon koda bayansama, harta dai samu ta cin masa inda yake tsaye agaban Ash color ɗin motar dake bayan wadda Dad ya shiga.

     Hannunsa daya zuba a aljihun farin wandonsa kawai ta iya satar kallo, ga wani tsoron ganin matasan sojojin dake shigarta, a rayuwarta tana tsoron soja da ɗansanda, gashi kuma ALLAH ya jarabceta da auren ɗaya a cikinsu.........

     Cikin risinawa matasan sojojin suke gaidata, da nuna mata ƙofar motar da ɗaya ya buɗe mata.

       Karon farko data ɗaga kai ta kalli fuskarsa, amma abin mamaki sai taga bama ita yake kalloba kwata-kwata, azamar janye idonta tayi.

      Attahir yay murnushi mai sauti yana faɗin “Amaryarmu Bismillah, shiga mota”.

   Kanta ta ɗaga masa dayin guntun murmushi takarasa tashiga motar.

       Amaan dake jinsu amma yay tamkar hankalinsa baya kansu ya zare hannunsa ɗaya daga aljihu yaɗan shafi girarsa tareda takawa ɗayan ɓarin motar da Ummu ta shiga shima ya shiga bayan an buɗe masa.

      Ummu dake ƙoƙarin dai-daita rawar jikinta sai kawai taji mutum ya zauna gefenta, ɗauke numfashinta kawai tayi gaba ɗaya tana dafe ƙirjinta. Itakam inhar haka zuciyarta zata cigaba da tsoron mutuminnan tashiga uku kenan, tariga ta sakama ranta tsoronsane tunkan ta gansa, shiyyasa yau takasa dai-daita kanta gaba ɗaya, ko nutsuwar kallon fuskarsa tama kasa samu.

      Shikam kansa ya jingina da kujera ya lumshe manyan idanunsa masu matuƙar haske, ƙasan zuciyarsa kuwa mamakin Dad yakeyi akan zaɓa masa wannan ƴar yarinyar sa'ar ƙanensa Bassam matsayin matarsa ta aure.

       Ko motsin arziƙi takasa yima a motar, takoma can jikin murfin mota ta takure, kasancewar Attahir motar da Dad ke ciki ya shiga sai tasu motar tai tsit, driver n sojan ne kawai keta aikin tuƙinsa, yayinda Ummukulsoom keta faman baje ido tana kallon hanya da jinjina garin Legas ɗin. 

     Yau dai gata a legas, garin da ake faɗin ya tara kowanne shege da shegiya, masu arziƙi da masu neman arziƙin......

       Wayarsa tai wani ɗan tsuwwar data katsema Ummu tunaninta.

    Idonsa ya buɗe tareda ɗan karkatowa jikin Ummu ya zaro wayar a aljihun wandonsa. Ba ƙaramin hargitsawa cikin Ummukulsoom yayiba saboda jin kafaɗarsa naɗan gogar gefen hannunta, ga ƙamshin turarensa yakuma shige mata har ƙofar maƙoshi.

     Zamansa ya gyara sosai ya ɗaga wayar saboda ganin sunan Attahir.

    “Lafiya?”. ‘ya faɗa acan ƙasan maƙoshi’.

    Ummukulsoom bataji abinda aka faɗa masa daga canba, taga dai ya ajiye wayar yana faɗama driver “Junaid samu waje ka tsaya”.

     Ita Ummu ma batai zaton direban yaji maganar tasaba, amma saitaga ya samu waje ya tsaya inda ya dace.

     Kafinma a buɗe masa shi harya buɗe da kansa ya fice, Ummukulsoom ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana gyara zamanta, dan a matuƙar takure take, ta ƙagara suje inda zasu.

       Attahir ma fitowa yay yana nufo Amaan da shima motarsu ya nufa.

      “Ajiwa! kuma lallaɓasa muji kozai haƙura yaje ɗin, danfa yadage sai dai a kaisa hotel”.

       Bai bama Attahir amsaba ya raɓa ta gefensa ya nufi motar inda Dad ke ciki. 

   Dad dake kallonsu ya buɗe motar ya fito fuskarnan a haɗe tamakar ko yaushe, ”Shi Attahir ɗin ya kasa shine ya turoka ka titsiyeni?”.

      Amaan ya girgiza kansa amar A'a, yaɗan shafi girarsa da ɗanyatsa yana gyara tsayuwa, da ƙyar ya fisgo maganar da yakesonyi, “Dad Please, kasan kanada masaukifa, yaza'ai ka kwana hotel?”.

      “Nasan inada masauki Fodio, amma kamar yanda na sanarma Attahir wannan karon bazan kwana a gidanka ba, da da yanzu akawai banbanci, koka manta kanada iyaline?”.

       Kansa yaɗan dafe ya lumshe idonsa ya buɗe, dan yau anata sashi yawan magana, dama idan kaji doguwar maganarsa to Dad ne, amma ko oganninsa na wajen aiki suna masa complain akan rashin yawan magana. “Dad dan ALLAH karkace haka, amma indai hotel ɗin kakeso saimuje can mukwana mu duka”.

      Babu shiri Alhaji Mahmud yaɗan fiddo ido yana kuma tamke fuska, “Fodio yaushe zakai hankali? Da matar taka zakaje a kwana hotel?”.

     Shagwaɓe fuska yaɗanyi yana rausayar da kai da shafar girarsa da ɗan yatsa, “To Dad muke gida”.

     Alhaji Mahmud ya girgiza kansa idonsa akan Fodio, ya tabbata yakai ƙololuwar gajiyawa da magana, danma shine, amma da wanine datuni ya shareshi yabar bada amsa. Yasan kaf halayyarsa Fodio ya ɗaukko, amma rashin son maganarsa yayi yawa, dan yakan gaskata maganarnan ta bahaushe dakance *ɗan gado harya zarta*. To lallai Fodio yagaji komai nasa amma harya zartashi ta ɓangaren shegen miskilanci.

      Ganin iskar hadarin dake ɗaure da garin tafara tasowa yasaka Dad haƙura ya koma mota.

      Ajiyar zuciya Amaan ya sauke, dan ya tabbata Dad ya haƙura zai bisu, da kansa ya rufe masa motar kafin ya juya ya kalli Attahir dake tsaye gefe yana latsa waya.

     ”Attahir?”. ‘Ya kirayi sunansa cikeda ƙosawa da magana’.

     Ɗago ido Attahir yay ya kallesa, ganin Dad amota yasakashi fahimtar komai ya dai-daita, tahowa yay, yayinda shikuma Amaan yakoma mota.

     Ummukulsoom dake ƙare masa kallo tacikin motar tun ɗazun tai azamar ɗauke kanta tana dai-daita zamanta, babu abinda zuciyarta keyi sai tsarkake sunan ALLAH da ya halicci wannan bawa mai kamala da tarin Nutsuwa, sosai yake kamanni da mahaifinsa, yayinda ya ɗakko fari da manyan idanu na mahaifiyarsa, ita wannan tagamu dashi a hanya bata sanshiba wlhy bazatace masa bahausheba, ba komai zaisa hakanba kuwa sai ƙirar jikinsa, lallai ya cancanci xama soja tako wanne fanni, gaskiya yafi dukkan ƴan gidansu ƙyau, danshi ya ɗakko kamannin Dad and Momcy dukya haɗa, ga kwarjini kuma da ALLAH yay masa, ta tuno Baseer ɗinta ƙyaƙyƙyawan bafullace fari tas, zaifi Amaan ƙyawun fuska, amma Amaan yafisa kwarjini da cikar haiba, sannan yafisa ƙyawun sura da dirarriyar ƙira da nutsuwa, isa, ƙasaita, dukya dama Baseer ya shanye, yanda yakema taƙama da wannan ƙyan nasa idan yazo Gaban Amaan dolene ya raina kansa, iyakaci yay kurin finsa fari da dogon hanci. Anata ganin kuma tsantsar ƙyawu bashi ake kira ƙyauba, komin ƙyawun mutum akwai matakan da saiya cikasu yake ƙayatar da mutane da kwarjinin barazana, to irinsu Amaan koda basuda ƙyau kwarjininsu ke girmama barazanarsu a zukatan jama'a......

     Ita kaɗai taketa saƙawa da kwancewarta har suka shiga cikin *_DODAN BARRACK_* bata saniba. Sai tsayuwar mota taji kawai da motsin fitarsa batareda yace mata Uffanba.

     Tana shirin Buɗewa aka buɗe mata, dukda darene Barrack ɗin akwai wuta, dan haka Ummu taɗan samu damar kallon iya inda idonta zai iya zuwa. A yanda dai ta kula inda suke na manyane, dan tsaf yake da manyan gidaje masu ƙyau tamkar ba a cikin barikiba, bakajin motsin komai sai haushin karnuka, saikuma mutane ɗai-ɗai dake shawagi........



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


       Suhailat dai ta wuce tabar zuciyar Baseer dajin haushinta, koda ta kirashi a washe garin isarsu ƙin ɗagawa yayi, dukda kuwa saida ta turo mssa massege akan sun sauka lafiya, amma ya gaza kiranta.......

     Kiran data sake masane ya sakashi jan dogon tsaki yana hararar wayar, sai da takusa tsinkewa ya ɗsga tare da dai-daita muryarsa tamkar mai barci.

      Daga can tace, “O love kayi haƙuri, bansan barci kakeba na tadaka wlhy”.

     “Babu damuwa Babie kun sauka lafiya”.

     “Lafiya lau, bayanma baka kiraniba saini na nemeka”.

     “O sorry Love, wani uzurinefa infaɗa miki yay mugun riƙeni, amma kina raina tamkar rubutu bisa dutse”.

     Suhailat tai murmushin jin daɗi tanajin ƙarin ƙaunarsa a ranta, cikeda shauƙi tace, “Ok Love ya wuce, kabuɗe data naturo wasu kaya ka duba mana idan sunyi, idan basuyiba sai a canja”.

         “Kina nufin harkun fara sayen kaya?”.

      ”Eh mana, to miza'a jirane? Somuke muyi mu gama mudawo, kasan akwai shirye-shirye da yawa da ba'ayiba”.

      “Hakane kuma, bara na duba ɗin”.

    Daga haka suka yanke wayar, daɗi yay mugun kama Baseer, irin wannan aure ai yayi, kana kwance abinka ana maka hidima, danma yakula muguntace dasu, yanzu ƴar dubai ɗinnan da dashi akaje ai zaifi ƙayatarwa ko, amma babu komai, zai fanshene, bara dai agama bikin.........✍🏻



NO. 13


..........Gidane da komai za'ace Alhmdllh, dan saika rantse da mace aciki, komai tsaf kuma ƙal, ga ƙamshi mai daɗi yana tashi.

        Zama Ummukulsoom da Dad sukayi, yayinda Amaan yanufi wata ƙofa Attahir na binsa abaya.

     Mintuna kaɗan suka fito suma suka zauna suna sake gaida Dad cikin girmamawa.

   Shima cike da kulawa yake amsa musu da tambayar aikinsu.

     Bayan kammala gaishe-gaishe Amaan ya sake miƙewa yana faɗin “Dad bara na saka maka ruwan wanka kai salla, kafin Su Abbas sukawo abinci”.

     “A dai akai ɗiyata ɗakinta tasami nutsuwa, ni ba baƙo baneba, Attahir ma ya rakani”.

       Ɗan yatsa yasa ya ɗan shafi girarsa kawai, bai iya sake cewa komaiba har Dad da Attahir suka nufi wata ƙofa dakecan gefen falon.

     Ummu dai na zaune duk tana saurarensu kanta a ƙasa, ya ɗan kalleta yay gaba batareda yace mata komaiba, itako dukda tana kallonsa ta ƙasan ido ƙin motsawa tayi, yayi wajen taku biyar ya tsaya cak jin bata biyoshiba, ya kasa ɗaga baki yace mata ta taso, yakuma ƙi juyowa ya kalleta.

      Karo na farko da abinsa yabama Ummu haushi, ta miƙe tana kumbura fuska batare da itama ta tanka masa balle ya samu amsa.

    Gaba yay tabisa a baya saikace wata munafuka, yanzu kam ta fara fahimtar dolene su Aneesa sukejin tsoronsa, mutum babu fara'a babu walwala, magana ma wahala take masa, ita kam dai takula yamafi Dad tsauri da tsare gida.

       Ɗakine Babba, wanda da alama ma sabbin kayan gado aka saka masa, dan sai ƙamshin sabon fenti ke tashi, gadonma babu zanen gado, sai katifar da ko leda ba'a cirewa ba, hakama bedsheets ɗin yana cikin ledarsa ba'a fiddashiba.

       Da ƙyar ya iya buɗe baki yace, “Nan ne ɗakinki”.

   Kai kawai ta ɗaga masa, amma bata amsa da bakiba.

   Hakan sai ya sakashi waigowa ya kalleta, dai dai ta ɗago ido zata saci kallonsa. Karaf idonsu suka shige cikin na juna, da hanzari ta janye tai ƙasa da kai.

    Idanu ya ɗan lumshe ya buɗe yana taɓe baki, kafin ya raɓa ta gefenta yafice abinsa.

     Cikin dabara tabi bayansa da kallo harya fice, ta sauke ajiyar zuciya tana taɓe baki itama da bin ko ina na ɗakin da kallo.

   Komai Ash color ne a ɗakin, idonta ya sauka akan akwatuna pink dake gefe guda shida sabbi fil, mamaki ya ɗan kamata, ta taka zuwa gabansu jikinta har rawa yake ta ajiye handbag ɗin hannunta a gefen gadon tabuɗe ɗan ƙaramin saman akwatunan. Littatafaine na addini, sai Qur'an da abin sallah mai ƙyau.

    Jikinta a sanyaye ta maida ta rufe tana mamakin akwatunan minene kuma?.....

    Batada mai bata wannan amsar, dan haka tanufi ƙofar data gani a ɗakin wadda take kƴautata zaton toilet ne.   

         Sosai Toilet ɗin yamata ƙyau shima, sai dai ba a ajiye komai ba na amfani a ciki, alwala kawai tayi ta fito tai sallar Isha'i.

       Idar da sallarta babu daɗewa saiga matar Attahir, itama bawata babba baceba, dan yaronsu ɗaya Ahmad, Ummu ta tarbeta da fara'a tana karɓar tiren hannunta data haɗoma Ummun abinci.

      Hafsat wayayyar macece mai yawan fara'a, gata ƙyakykyawa masha ALLAH, tun Ummu na sissine kai harta fara sakin jikinta da Hafsat saboda janta da hira da take tayi, cikin mintuna ƙalilan sabo yashiga tsakaninta da Ummu.

      Ahmad kam ai yana jikin Ummu. Hafsa itace tabuɗe bedsheets ɗin ta shimfiɗa a gadon, tareda buɗe akwatunan ta fiddo mata duk abinda zata buƙata kamar su sabulan wanka mai turare da kayan barci dadai sauransu.

    Ta ɗaga wata rigar barci mai azabar ƙyau pink tana kallon Ummu da murmushi, “Amaryarmu gaskiya wannan ya kamata yau asama angonmu, dan dakansa yaɗau rigar barcinnan dukda dai bai buɗe ya ganiba lokacin”.

     Ummukulsoom tai ƙasa da kai tana murmushi da mamakin maganar Hafsat na cewa da kansa ya ɗauki rigar barcin, dan ƴar ɗigilace, gata shara-shara.

    Fahimtar hakan da Hafsat taine yasata dariya, “Karkiji wasa wlhy, dashi mukaje muka haɗo lefennan, duk abinda ya tare masa gaba ya ringa kwasowa, ni dariya ma ya bani, sai da naima Abban Ahmad magana sannan ya dakatar dashi nafara nuna abinda za'a ɗauka. Ai wannan miji naki kam saikin dage kin maido manashi mai fara'a amarya, dan ALLAH ya kukeyi idan yaje wajanki hira? Dan ni tunda mukai aure da Abban Ahmad kusan shekara biyu kenan zan iya rantse miki ban taɓa ganin haƙoransa da sunan dariya ba”.

     Rasa abinda Ummu zatace tayi, dan ta fahimci itama maman Ahmad ɗin batasan auren ɗori ɗafini akai mata da shiba, sai kawai tai murmushi tanama Ahmad wasa”.

      “Nifa kibarjin kunyata, danni ƙawarkice ehe”. ‘Cewar maman Ahmad tana rufe akwatunan da miƙewa’.

     Toilet tashiga ta aje mata komai na amfani inda ya dace, tasake dawowa bedroom ta shirya kayan kwalliyar da turarirrika akan mirror.

    Ummukulsoom dai nata wasa da Ahmad abinta tanacin abincin da maman Ahmad ta kawo.

      Bayan Maman Ahmad ta kammala itama ta dawo ta zauna kusada Ummukulsoom suna ɗan hirarsu a nutse. Bata sake jin ɗuriyar su Amaan ba sai kusan sha ɗaya na dare, lokacin hadari yafara tasowa gadan-gadan.

     Amaan yay sallama a ƙofar ɗakin batareda ya shigoba, amsawa sukai yaɗan leƙi kansa yana faɗin, “Maman Ahmad Attahir na jiranki”.

     Baima jira ta amsa ba yabar wajen.

      Ummukulsoom ta ɗakko mata Ahmad dayay barci ta rakota, sun iske har harsun fice dan haka suma sai suka fito inda Amaan da Attahir ke tsaye iskar hadari na kaɗasu.

     “A'a amarya dakanki kika fito cikin wannan iskar? Kamata yay ai kar'a sake ganin idonki a waje sai nan da wata biyu haka”.

     Murmushi Ummukulsoom tayi tana miƙama Maman Ahmad dake bama Attahir amsa Ahmad ɗin, shi dai Amaan uffan bai ceba, dukda kuwa yana tsaye a wajen yana jinsu dama kallonsu, dan ƙasa-ƙasa yaketa bin duk wani motsin Ummukulsoom da ido, so yake yaga mi Dad yagani a tattare da yarinyar da har yaga dacewarsu takai suzama miji da mata......

    Yayyafi aka fara, dan haka su Attahir sukai musu sallama suka nufi gidansu dake gabansu Ummu kaɗan, dan gida baifi goma bane a tsakaninsu.

        Daga shi har ita babu wanda ya motsa a wajen bayan wucewar su Attahir, ƙarfi ruwan ya farayi yana jiƙasu, ganin bashida niyyar motsawa sai Ummu tawuce sim-sim ta barshi a wajen tsaye.

      Da kallo ya bita harta shige, kafin ya lumshe idonsa ya buɗe yana shafar girarsa da ɗanyatsa.

      Koda Ummukulsoom ta shiga saita laɓe a jikin Window tana kallon ikon ALLAH, zai taho kokuwa sai ruwan yagama sauka a kansa?. A mamakinta sai taga ya cigaba da tsaiwa a wajen ruwa na jiƙashi, tsawon mintuna kusan goma ruwan yayi ƙarfi sosai yay masa jalaf, dan farar rigar jikinsa dukta manne masa, ganin yanufo hanyar shigowa yasa Ummu kwasa da gudu tanufi ɗakinta, sai da ta zauna sai gudun nata yasata yima kanta dariya ita kaɗai.

      Tundaga nan bata sakejin motsin kowa ba, ga ruwa ana shekawa sosai, ALLAH ɗaya gari banban kenan, a gida arewa dai sanyi ake zubawa, sai gashi yau tazo lagos kuma ana ruwa, lallai baka sanin mi duniya take ciki saika baro yankinka, tunani taitayi kala-kala, harta kwanta, can ƙasan zuciyarta kuma cike da kewar babanta da ahalinta na ɗilau tareda Baseer daya faɗo mata a rai. Daga ƙarshe dai saida tai kuka zuciyarta ta rage nauyi kafin barci ɓarawo yasamu damar saceta.


  ⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


        Kwanan su Suhailat goma cif a dubai suka dawo Nigeria da kaya niƙi-niƙi, dan tunkan su taho da kwana huɗu suka turo kayansu.

      A washe garin dawowarsune ta kira Baseer dake ɗilau a waya tana sanar masa sun dawo, sakin jikinsa yay sukasha hira, da mata alƙawarin gobe zaizo kaduna wajenta.

    Murna tayi sosai tareda masa addu'ar zuwa lafiya.

   

      Duk wayar da yake da Suhailat agaban inna dake bakacen geron fura data surfa yakeyi, amma tai biris dashi tamkar batajiba, saida ya aje wayarne daga inda yake a kishingiɗe a tabarma yace, “Inna kinji Suhailat sun dawo jiya”.

      A lalace Inna tace, “ALLAH sarki, to sannunta da zuwa”. Daga haka taja bakinta ta tsuƙe taci gaba da bakacenta. Shima bai sake magana ba yakoma chart dasu Abdull. Kamar an tsikareshi ya ɗago ido ya sake kallon Inna,

    “Inna wai miyasa naga an dawo da waɗancan akwatinan?”.

       Kamar bazata tanka masaba sai kuma tai murmushin takaici tana miƙewa da harhaɗe kwanukan datai aikin, “Tunda kace bazaka auri ƴarsuba mizasu yi da kayanmu, sun kuma aurar da ita gamai bukatarta, idan sun ajiye kayan wazai saka?”.

     Mamaki shinfiɗe a fuskarsa yace, “Wai Inna kina nufin Ummukulsoom tayi aure?”.

     Cikin gatse Inna tace, “A'a sun ajeta sai bayan kayi naka tukunna”.

       “ALLAH yabaki haƙuri  inna ba baƙar magana na nemaba, amm to yaushe ma akai hakan ban saniba? Ko wani ƙaton ƙauyen suka samu?”.

       “Kaje ka bincika mana”.

    Shiru yay bai sake maganaba, saima baki daya taɓe alamar su suka sani yacigaba da chart ɗinsa.


*_Washe gari_*


      Da hantsi ya shirinsa tsaf ya nufi kaduna wajen Suhailat. Tarba yasamu mai ƙyau agareta, yini guda suna a tare, ta kwaso masa akwatuna yagani, sai santi yake da yaba ƙyansu. Suhailat na fita kawo masa abinci yay sauri ya ɗauki hotunan komai tare da kansa cikin style kala-kala, atake ya turama Su Abdull cewa gafa kayan lefe Mom nashi ta haɗo a dubai, jiya ta dawo.

     Rikicewa sukai sunata santi, Areef yace, “Bas gaskiya wannan karon kazo ka kaimu mu gaida Mom, bai dace ace muna tare kusan 3years ba amma kaƙi kaimu gidanku, bayan kuma mu duk kasan namu gidajen”.

      Tashi yay zaune da sauri saboda ganin maganar Areef ɗin, jikinsa har rawa yake ya rubuta musu, “Karku damu guys zakuje gidanmu, kunsan dai anan wajen ƙanwar Mom ɗina nake, gashi masifaffene mijinta da ita kanta, amma zakuje Abuja tushena insha ALLAH”.

     Nan take suka shiga maida masa reply ɗin “ALLAH ya kaimu lokacin”.

    Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya rufe data ɗin, kansa ya dafe da takaicin Areef, duk cikin abokansa shine ya cika nacin akan saiya kaisu gidasu, shikuma ya zula musu ƙarya cewa a abuja iyayensa suke, anan zariya gidan ƙanwar Mom nashi yake, sun taɓa zuwa gidan Innarsa anan zaria, dayake gidansu mai ɗan ƙyaune dan mijinta nada hali dai-dai gwargwado sai bai damuba, amma saida ya zinliƙa musu karyar wai Dad nashine ya sayama su Innar tashi gidan ma. Suko duk sun yarda dashi saboda ƙyawunsa da tinkaho kesakasu ɗaukarsa ɗan manya, kuma sun haɗu da shine a time ɗin yana tare da Suhailat tafara sakar masa ƴaƴan banki.

      Suhailat bata san miya faruba tadawo suka cigaba da hirarsu hankali kwance.


★★★★★★


        Tun daga ranar shirye-shiryen biki suka cigaba da gudana, sai dai a gidan su Suhailat kawai hakan ke faruwa, dan a ɗilau hankalin Baba da Inna kwance yake, sun dai san ɗansu zai aure, amma tunda ba'a buƙatar komansu an raina miye nasu kuma, sai su zuba ido suga yaya wasan zai ƙare.

       Tun bikin na sauran sati ɗaya Baseer ya tattara kayansa ya koma Kaduna ya tare a hotel da  Suhailat ta kama masa ɗaki da kanta, dan haka suma su Najeeb sai suka dawo nan suka tare kawai.

    Hidimar biki aka shiga sosai, sai dai kuma babu ahalin Baseer na gaskiya a ciki, dan yanajin kunyar nunasu saboda ƴan ƙauyene. Amma gudun kar suji kunya suka samo wata hajiya Hamida ghana amatsayin sojan haya mai amsa sunan mom ɗin Baseer, itace ta samo musu dangin da zasu dinga wakiltar kowane taro matsayin dangin Baseer kuma.

   Hakan kuwace ta faru, tun aranar kamu dasu hajiyar Dubai akayi amatsayin dangin Baseer, ko lefe ma ana saura kwana hudu biki su aka kaimawa suka kuma kawowa gidansu Suhailat amatsayin lefe harda key ɗin mota.

      An cigaba da biki har ranar da aka ɗaura auren Suhailat da angonta Baseer, wanda yay shar cikin shadda fara tas. Ɗaurin aure dai su Baba sunzo hardama baban Ummu ma ya halarci ɗaurin auren, sai daifa su ƴan kallo suka zama, dan wani Daddyn Suhailat yasa a matsayin wakilin Baseer, dan haka ƴan ɗaurin aurema suka ɗauka shine mahaifin Baseer ɗin.

     Abin yay matuƙar ƙona ran baba, amma saiya danne bai nunaba, sai idon mutane ya faka ya share hawayensa da babbar riga, ƴaƴa biyu kawai suka mallaka a duniya, daga Talatu sai Basiru, sun saka basiru yay makaranta bisa shawarar mijin innarsa ta zaria, sai kuma danya zama mai taimakon kansa da ƙauyensu, amma sai abin yazama ba hakaba, dama wannan shine dalilin da su mutanen ƙauye ke gudu wajen barin ƴaƴansu suyi zurfi akaratu, kowa na tsoron ɗansa ya aro baƙon halayya da sukan kira na yahudu da nasara. Da wannan takaicin baba yakoma dilau, ko inna baiba labarin yanda akaiba ya bar abinsa a zuciya. 


Ango da amarya ansha kyau an gaji, musamman a wajen dina, ƙawayen Suhailat duk sun rikice da ganin handsome ɗin data samu na kerewa tsara da zagayen ƙasashen duniya, ga nera kamar yanda ta sanar musu, ansha shagali kam yanda ya kamata, dan nera ta koka iya kokawa, daga karshe aka miƙa amarya Suhailat ɗakinta dake a ƙaton gidan da mahaifinta ya bama Baseer. Wanda shikuma baseer ya mannama abokansa ƙaryar Dad ɗinsane ya saya masa anan kd saboda yanason zama anan fiye da Abuja.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

      

           Barcin da Ummukulsoom bata samu bane yasata makara, sai wajen 7 ta tashi, salla tayi cikin taraddadin yinta a makare, bayan ta kammala ta gyara ɗakin dukda babu wani dattima, wanka tayi ta shafa mai, sai dai kuma babu kayan sakawa, tsaye tayi cikin jimamin yanda zata samu kaya, dan ta lura su isa basukai ga isowaba ƙila, dabarar buɗe akwatunan lefen nata da maman Ahmad tace tayi, cikin amincin ALLAH saita samu dogayen riguna a ciki, wata jaa ta ɗauka ta saka, rigar tamata ƙyau sosai, gashi tai mata ɗas tamkar an gwadata, dan Ummu ba siririya baceba, hargitsin bikinnan ma ne dai yaɗan sakata ramewa, motsin dataji ya yawaita a falone da maganganu yasata leƙowa.

      Mamakine ya kamata ganin Dad dasu isa direban dayayo gaba da kayanta, sai kuma wadda aka haɗosu tare da zata ringa taya Ummu ƴan ayyuka kamar yanda Dad yace.

       Fitowa ta idayi, tazo gaban Dad ta durƙusa ta gaidashi. 

     Da kulawa ya amsa mata dukda dai fuskar babu walwala, tariga ta saba zuwa yanzu da wannan yanayin nasa. Gaidata su Isa ma daketa shigo da kayan sukayi, ta amsa tana musu sannu da zuwa da tambayar hanya.

       “Hanya Alhmdllh auntynmu, ai tunma jiya muka iso, sai dai lokacin ruwa ya sakko dole muka nemi mafaka”.

    Ummu tace, “ALLAH sarki, sannunku da zuwa”.

        

         Dad ya kalli agogon dake falo sannan ya kalli Ummukulsoom, “Ɗiyata tadomin mijinki, danni nagama shirina jirgin ƙarfe goma zanbi”.

       Gaban Ummu ne ya faɗi, tuni damuwa ta mamaye fuskarta, sai dai kuma ta kasa cewa komai ta miƙe zuciyarta na ɗar-ɗar ɗin tsoro, itafa koma ɗakin nashi bata saniba.

    Corridor ɗin dataga yashiga jiya shida Attahir ta nufa zuciyarta nata bugawa da sauri-sauri. Ƙofar ɗaya ta iske cikin Corridor ɗin, tai tsaye takasa koda ƙwanƙwasawa,  taja kusan seconds 10 kafin ta fara ƙwanƙwasawar a hankali, saida tai haka har sau uku amma ko motsi batajiba, ɗora hannunta tai a handle ɗin ƙofar tana rimtse ido, tamkar wadda tazo sata haka ta leƙa kanta bayan ta tura ƙofar, ALLAH ma yasota bata da ƙara.

     Kwance ta hangosa saman ƙaton gadonsa ruwan hanta a rigin gine ya rungume filo dogo, gadonma farin bedsheets ne a shinfiɗe, yana sanye da wandone 3queater fari tas shima a jikinsa da best itama fara, fuskarnan fayau da annurin da ko idonsa biyu bazaka sameta a sake hakaba. Rasama abinda ya kamata tayi tai, sai kawai ta zaɓi juyawa ta sanarma Dad bai tashiba....

      “Mikike buƙata?”.

Muryarsa ta daki kunnenta babu zato. A matukar firgice ta juyo ta kalli gadon, a mamakinta saitaga yana a yanda tashigo ta iskeshi, saurin janye idonta tayi da matuƙar mamakinsa, kenan duk abinda take yana kallo, muryarta na rawa tace, “Dad ne yace dama na maka magana ya shirya zai wuce”.

     Manyan Idanunsa da suka ƙara girma saboda barci ya buɗe ahankali yana kallonta, batareda ya tankaba ya tashi zaune ya zuro ƙafafunsa alamar zai sauka.

    Fita Ummu tayi tana kuma jaddada mamakinta akan halin wannam mutumin.


      Kodama ta dawo falon saita iske Attahir yazo harda Ahmad, ga kulolin abinci alamar breakfast yakawo musu.

     Saida ta sanarma Dad yana zuwa sannan suka gaisa da Attahir ta ɗauki Ahmad daya baro jikin Dad ya nufota tamkar ya ganeta, dan yaron akwai wayon tsiya masha ALLAH.

      Bayan Ummukulsoom ta ɗauki Ahmad saita nufi komawa ɗakinta, da sauri taɗanja baya saboda karo da suka kusanyi dashi, ya sako blue ɗin t-sheat a saman 3queater ɗin wandonsa. Ganinsa yasaka Ahmad fara zamewa daga wajenta yana miƙa masa hannu.

      Gani tai kawai ya miƙo masa hannu alamar ɗaukarsa shima, babu yanda ta iya dole ta miƙa masa shi, wajen ƙoƙarin ɗaukarsa hannunsa ya gogi ƙirjinta.

    Saurin matsawa tayi saboda jin abinda batai zatoba, shi kansa saida zuciyarsa tai wata irin harbawa, amma a fili saiya kuma tamke fusaka yana barin wajen tamkar ba ayi komaiba.

      Tunda ta shige bata sake fitowa ba har Maman Ahmad tazo, itacema tabiyota da breakfast ɗin.

         Sai da Attahir ya kira wayar maman Ahmad akan Ummukulsoom tazo sannan tataso ta fito.

     Dad da Yaa Amaan kaɗai ta iske a falon zaune, kansa a ƙasa alamar nasiha ake masa.

     Guri Ummukulsoom tasamu ɗan nesa dasu zata zauna, amma sai Dad yay mata nuni da kusa da Amaan dake zaune a kujera 2seat.

       Bata zauna a kujerarba dai ta zauna a ƙasa kusa dashi sai dai  akwai tazara a tsakaninsu.

        Dad yay gyaran murya yana gyara zamansa idonsa a kansu. “To Alhmdllh da ALLAH ya nunamin wannan rana, Fodio ga Ummukulsoom nan matarka dana ɗaura muki aure, bakuma komai yaja hankalina dayin hakanba sai ƙyawawan halayya dana lura tana dasu, ina mai ƙyautata maka zaton samunta fiyema da yanda kake zato, ina fatan zaɓina bazai zama abin wulaƙantarwa daga gareka ba, idan kayi haka kuma ka tabbata ni kaimawa, dan na yarda da tarbiyyar daka samu ɗari bisa ɗari”.

       Da ƙyar ya iya dai-daita kansa yace, “Insha ALLAHU Dad, ina godiya, ALLAH yaƙara nisan kwana”.

       “Amin” Dad ya amsa yana maida kallonsa kan Ummu da kanta ke a ƙasa tana share hawayen da batasan dalilin yinsuba.

     “Ummukhoolsum!”.

“Na'a Baba”. ‘Ummu tafaɗa muryarta na rawa’.

        “Ga mijinki nan Fodio, ina fatan zaki kwantar da hankalinki kimasa biyayya, karnaji wata matsala kinji, ALLAH ya baku zaman lafiya da da zuria ɗayyiba mumina”.

      kai Ummu ta ɗaga tana hawaye, bakinta yagaza furta komai. Dad ya kara musu nasiha sannan ya miƙe yana kallon agogon hannunsa. 

      “Kunga bara na wuce naga ina neman makara, ALLAH yabada zaman lafiya”.

    Mikewa Fodio yay shima, sai yanzu Ummukulsoom ta lura ya canja kaya ashe.

     Ummu naji na gani Dad da sukazo tare ya tafi ya barta, ɗaki takoma tana kuka, maman Ahmad taita lallashinta da mata nasiha. Harsu Amaan suka dawo daga rakkiyar Dad bata gama sakin jikintaba.

     Wajen sha biyu maman Ahmad ma tai mata sallama ta koma gida ɗora girkin rana..........✍🏻


NO. 14


.............Farin cikin da Amarya Suhailat da  angonta Baseer ke ciki yau bayyanashi ɓata lokacine, a wannan dare dai kam babu ɗaga ƙafa saida ya amayar da kwaɗayinsa na kusan shekara biyu, tun tana biye masa da marmarin soyayya harta koma jamasa ALLAH ya isa.😹

     Da safe dai ya zage yanata lallaɓa kayarsa da riritata, yayinda itako taketa langaɓe masa, ko ruwa saitace saiya bata abaki, ita bazata iya shaba jikinta ciwo yake. Haka taita zuba masa taɓara a wannan yini.

      Da daddare yanemi sake morewa takoce bai isaba, yo kasheta zaiyi, daya matsa mata da magiyama kuka ta saka masa da ɗaukar waya wai zata kira Daddyn ɗinta.

       Da sauri ya warce wayar yana bata haƙuri da faɗin shifa da wasa yakeyi,  baki ta tura gaba tana jan bargo da juya masa baya. Dole ya haƙura ya kwanta shima ya rungumeta yana haɗiye kwaɗayinsa dan dole, amma harga ALLAH yaso sake ɗanɗanawa. (mijin Hajiya sai haƙuri to🤣).



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


             Ƙarfe kusan biyu maman Ahmad ta sake aiko musu da abinci, Ummu na ɗaki ƴar aikin maman Ahmad tazo, A'i da suka taho da isa kawai ta iske zaune a falon tana kallo, rissinawa tai ta gaisheta dan A'i babbar mace ce sosai.

       “Aunty ce tace akawoma aunty Amarya”.

      Miƙewa A'i tayi tana faɗin “Tofa bara na kira miki ita”.


        Ummu na zaune ta idar da salla A'i tai sallama.

     Ummu ta amsa tareda bata izinin shigowa.

      tunda A'i ta shigo takebin ɗakin Ummukulsoom da kallo a kaikaice tana jin jina kai, lura da hakan da Ummu tayi yasata katseta da faɗin “Baba lafiya dai ko?”.

     “A babu komai uwar ɗakina, dama wata ƴar budurwace ta kawo abinci wai inji ko auntyn ta”.

       Miƙewa Ummu tayi tsaye tareda zame hijjab ɗin jikinta tana cewa, “Inaga maman Ahmad ce, ita bata gajiya tun jiya take ɗawainiya damu”.

       Ƴar dariya A'i tayi tana ficewa, Ummu ma ta biyo bayanta.

     Mai aikin Maman Ahmad ta gaidata cikin girmamawa, sannan tace “aunty amarya ga abinci inji aunty tace a kawo muku”.

      Fuskar Ummukulsoom ɗauke da murmushi tace, “Kice mata nagode sosai, ya sunanki?”.

     “Aunty Sunana Zubaida”.

   “Masha ALLAH Zubaida kice nagode kinji”.

       Bayan fitar Zubaida Ummukulsoom ta buɗe kulolin, abincine mai kyau yanata tashin ƙamshi, A'i sai leƙa kai take nason ganin minene itama?. Ummu ma batasan tanaiba, tafara kwashe kulolin tanufi dani dataga sunci abinci ɗazun. Tashi A'i tai ta tayata suka kai.

   Ana cikin haka saiga Yaa Amaan ya shigo, ita Ummu ma sai yanzu tasan baya gidan.

     Zubewa A'i tai tana gaishesa, ko kallonta baiyiba ya wuce cikin falon tareda amsa mata da “Lafiya”.

       Duk da zuciyar Ummu na rawa haka ta tako zuwa cikin falon tana masa sannu da zuwa.

     Fararen idanunsa ya ɗago yaɗan kalleta tareda janye idonsa lokaci ɗaya.

      Dukda bai amsa mataba saita sake daurewa tace, “Ga abinci maman Ahmad ta aiko dashi”.

       “Kuci kudai, zuwa ƙarfe takwas ina son ganinki”. ‘ya ƙare maganar da miƙewa ya wuce abinsa’.

     Kallo kawai Ummu ta iya binsa dashi a sace, hakama A'i dake laɓe a dani tana taɓe baki da naɗar gulma.

     Ummu ma data mance da ita ko kallon inda take bataiba tai wucewarta nata ɗakin itama.   

     A'i na ganin duk sun shige saita zaro wayarta dake saƙe a zani jikinta har ɓari yake, da sauri ta nufi ɗakin da aka bata ta zauna tana ƙokarin kiran Momcy ta fesa mata gulma, dan dama dalilin turota kenan danta sakama su Ummu ido kafin su Ummayya suma suzo.

      “Hajiya kun wuni lafiya?”.

     Daga can ta amsa mata cikin isa.

     Tsayuwa A'i ta gyara cikin kwarewa a gulma tace, “Uhm hajiya ai wannan ogan nawa nakula jan gwarzone sojan gaskiya, dan yarinyarnan kam bazataji da daɗiba a gidannan, kofa kallon arziki bata ishesaba wlhy, yanzunnan tagama masa iyayi da feleƙe akan abinci amma da kinga yanda yawani dizgata saima tabaki tausayi, kofa kallonta bayayi hajiya”.

       Wata ƴar dariyar mugunta hajiya jamila tayi daga can, “Nagode miki dakawo min labari mai daɗi A'i, dama ni na yarda da Fodio yarinyarnan sai taci ubanta a wajensa kafin kuma ya koro musu ita da jan kati, aiki na kyau A'i, adai cigaba da sakamin ido, nanda sati biyu su Aneesa ma zasu taho”.

         “To hajiya, insha ALLAHU zaki cigaba da samun bayani daki-daki kuwa daga gidan soja”.  


★★★★★★★★


          Ummukulsoom bata sakejin ɗuriyar Amaan a gidanba har akai sallar magriba, tana zaune tayi tagumi da tunanin ahalinta taji sallamar maman Ahmad, cikin mamaki ta ɗaga kai tana dubanta, mamaki ya ƙara kamata ganinta cikin kwalliya sosai.

      “Amaryarmu ya da kallo haka? Tashi maza kiyi sallar isha'i tunda gatacan ana kira, ga mai kwalliya zatai miki”.

     “Kwalliya kuma maman Ahmad tami?”.

      “Idan Ana salla ba'a magana amarya, kedai tashi kawai”.

      Babu yanda Ummu ta iya dole ta mike ta kabbara salla, Maman Ahmad tashiga buɗe kayan data shigo dasu  a leda tana bubbuɗewa. 

        Bayan Ummu ta idar maman Ahmad tace “zakiyi wankane?”.

      Cikin shagwaɓa Ummu tace, “A'a maman Ahmad yanzufa nai wanka”.

    Hafsat tayi dariya da riƙe haɓa, “Tofa amaryarmu ashe shagwaɓaɓɓace, kinga adana abunki sai Amaan na kusa”.

      Juyar dakai Ummu tayi tana murmushin jin kunya, har mai kwalliya ta shigo bata sake yarda sunyi magana da Maman Ahmad daketa kuma tsokanartaba.


★★★


      A ɗakin Amaan ma yanacan Attahir ya tsaresa akan saiya tashi ya saka wasu kaya daya kawo masa, suma dai na sojojine amma ba irin wanda suke fita aiki da suba.

      Haɗe fuska Amaan yakumayi yana harar Attahir, kafin ya janye idanunsa ya maida kan tv yana faɗin “Attahir kasanfa banason takura, wlhy harka fara samun ciwonkai, ina zamujene wai?”.

      “Nidai koma mizakace jekaita cewa, kamin alfarma katashi ka shirya, insha ALLAHU zaka gani ai, wlhy abune mai muhimmanci, kasan dai bana maka kalar wasannan ai, musamman danasan bakason fita ko ina idan 8 tayi sai dole”.

     Wani nannauyan numfashi ya sauke yana jan siririn tsaki, yakuma harar Attahir yana mikewa da jefar da wayarsa akan gadon dayake kwance da, “Banza kawai sarkin takura”.

       “Nadai ji bakomai”. ‘Attahir yabashi amsa yana ma bayansa gwalo’.

      Bayi yashiga kusan mintuna goma ya fito yana kuma tamke fusaka, sai da ya ɗakko best da boxer a Wadrobe ya juyo yana harar Attahir, “Dalla malam tashi ka fitarmin, Ko a gabanka zan shirya ne?”.

     Dariya Attahir yay yana miƙewa da faɗin, “Rufamin asiri, ni a suwa da kallon ƙato na shiri a gabana? Wannan sai Ummukulsoom”.

       Da sauri Amaan ya miƙa hannu zai damƙoshi, amma Attahir ya fice da ɗan gudu yana dariya.

     Amaan yay ƙwafa kawai yana lumshe ido da buɗewa daya zame masa jiki.


    Cikin mintuna kaɗan saiga maman Ahmad ta fito riƙe da hannun Ummukulsoom dake sanye da wata haɗaɗɗiyar doguwar riga sky blue, ta mata ƙyau sosai, an naɗa mata dark blue ɗin ɗankwali dayay mugun zama a kanta, tayi kyau harta gaji, babu wanda zai mata kallo ɗaya ya yarda Ummukulsoom ce ta ƙauyen ɗilau maima su Baba yalwa bauta.

     Attahir yaɗan zunguri Amaan dake ƙoƙarin ɗaura agogo, yayi ƙyau cikin Uniform kalar green shima,  kayan sunyi masifar zauna masa a jiki tamkar an hakiccesa dasu.

    Ɗago ido yay a fusace zaima Attahir masifa, danya fara kaisa bango da takurarsa, karaf idonsa ya sauka akan Ummukulsoom dake tsaye kusada Maman Ahmad kanta a sunkuye ta kasa kallon kowa. Haɗiye maganatsa yay cikin sarƙewar yawu, yay saurin ɗora hannunsa a baki saboda tahowar wani munafikin tari dabai shiryawa zuwansaba.

     Juyar dakai Maman Ahmad tai tana danne dariyar dake neman ƙwace mata da ƙyar, shiko Attahir saida ya dara kaɗan, kafin ya ɗauki ruwa ya tsiyaya masa a glass cup ya miƙa masa”.

     Harara ya dalla masa ya karɓa ya shanye yana kuma satar kallon Ummu da itama take kallonsa a sace, Sosai yay mata ƙyau, lallai ya cancanci zama soja tako wanne fanni, da'ace zata iya bashi shawara datace yayta zama da Uniform ajikinsa a kowanne lokaci.

     Ajiye kofin yay ya fice tamkar baiga komaiba, dariya Attahir yay yana kuma girmama halin abokin nasa, shi yasan abinda yafima haka zai aikata, amma yanaji a jikinsa komai zai wuce tamkarma ba'ayiba, dan irinsu Amaan basu iya shagala a soyayya ba, daga lokacin data kamasu saisu koma tamkar wasu bayin mace.

        A'i na laɓe tana kallon duk abinda ke faruwa, ƙwafa tayi tafito sosai bayan taga Amaan ya fita. Cike da ladabi tace, “Anguwa za'a ne Uwar ɗakina”.

     Su duka kallonta sukayi, kafin Ummu tasamu damar bata amsa Attahir yace, “Zamuje wani wajene, zuwa 12 haka zasu dawo insha ALLAH”.

    “To ALLAH ya tsare”. ‘Tafaɗa tana kuma satar kallon Ummukulsoom ɗin’.

    Amsawa sukai da amin suka fice abinsu da barinta da ƙududun baƙin ciki da gulmar dake cinta. Jikinta har ɓari yake ta dannama Momcy waya ta fesa mata zance.


     Ran Momcy a ɓace takira wayar Amaan danson jin ina suka nufa?.

    Lokacin Ummukulsoom na ƙokarin shiga Motar da aka buɗe mata inda tun fitowar Amaan ya shiga.

    Ko motsi baiyiba dukda jin wayarsa na ring, Ummu data zauna ta saci kallonsa ta gefen ido, a mamakinta sai taga yanajin wayar amma ya share.

    Kauda kanta tayi gefe da roka masa ALLAH shiriya a zuciyarta.

      Suna fara tafiya ya maida kansa ya jingina da kujera ya lumshe idanunsa yana shaƙar daddaɗan turaren Ummukulsoom na haɗin khumra.

    Tafiyarsu ta ɗanyi Nisa taji muryarsa mai cike da amo na faɗin “Abbas mu shiga wajen nan”.

      Satar kallonsa Ummu tayi ta gefen ido, amma sai taga har lokacin yana kwance jikin kujerar idonsa a lumshe, aranta tace toshi wannan zuciyarsace idonsa halan?. Bata da mai bata amsa dan haka ta tsaya sauraren miza'ayi a wajen.

         Abbas daya gama parking ya juyo ya kallesa, cikeda ladabi yace, “Sir mun tsaya”.

      Batareda ya buɗe idoba ya miƙa masa ATM card ɗinsa yana faɗin “Shiga wajennan kasamo gyale dark blue”.

       Amsar ATM ɗin Abbas yay ya fita, yayinda Ummu tama kasa fahimtar maganar tasama gaba ɗaya.

     Shi kansa Abbas bai fahimtaba, amma gudun yin laifi saiya kasa tambaya ya buɗe motar ya fita.

    Ganin su Attahir ma sun faka saiya nufi motarsu danya tambaya.

     “Abbas lafiya kuwa naga kun tsaya?”. ‘Attahir ya faɗa yana fitowa daga tasu motar’.

      “Sorry Sir!, Boss ne yace nashiga nan nasayo gyale dark blue, nikuma nakasa ma fahimtarsa wlhy”.

      Attahir ya haɗiye dariyarsa gudun yin abun kunya gaban yaransu su Abbas, nuni yayma Abbas da hanya alamar suje to”.

    Cikin sunkuy dakai da girmamawa Abbas yabi bayan Attahir.

     Mintuna kaɗan suka fito hannun Abbas ɗauke da jikka ƙarama mai ƙyau🛍.

      Saida ya shiga mota sannan ya miƙama Amaan.

       Koda ya karɓa saiya ɗora saman cinyar Ummu batareda yako kalleta ba balle tasamu arziƙin ƙarin bayani.

     Kallonsa taɗanyi, cikin dauriya tace, “Yaya miza ai dashi?”.

      Da gefen ido ya kalleta yana maimaita kalmar yayan data faɗa a zuciyarsa, toshi yaushene yama zama yayanta?.

    Sharewa yay yaki bata amsa, dan haka itama ta tsuke bakinta.

      Babu wanda ya sake magana a motar har suka isa inda zasuje bisa jagorancin Attahir.

       Wani hotel ne mai aji a cikin anguwar tasu ta da babu yawan hayaniya, Sojojine birjik zagaye da Hotel ɗin, ga motoci a zube ko ina, tsoro yakuma mamaye zuciyar Ummu ganin sojojin........

     Bata kammala tunaninta da neman amsaba taji an buɗe musu ƙofa. Ganin yaƙi koda motsi sai ita tai yinƙurin ficewa abinta.

      Harta zira ƙafa ɗaya taji an cafkota da wani lallausan hannu, juyowa tayi a firgice danson ganin wanene haka?.

      Gabanta ya faɗi ganin hannunsa riƙe da tsintsiyar nata hannun, sannan yana nan zaune yanda yake ido kuma a rufe. Sai kawai ta maida kanta ta sunkuyar, dan wannan faɗan kam yafi ƙarfinta.

      Jin Attahir ya kuma cewa, “Amaryarmu fito kinji”  saita kuma yunƙura zata fita.

       Wata irin figowa yay mata data haye saman jikinsa gaba ɗayanta, take jikinta ya fara ɓari, kafin tagama fahimtar manufarsa ta tsinci kakkausar muryarsa cikin kunnenta yana faɗin “Idan har ƙafarki ta taka wajennan ahaka babu mayafi saina lallasaki wlhy”. Yana gama faɗa ya tureta daga jikinsa ya fice abinsa.

       Daga Attahir har maman Ahmad galala sukai suna kallon ikon ALLAH, dukda kuwa basuji miyake faɗa mata ba.

        Da ƙyar Ummu tasamu damar haɗiye yawun daya toƙare maƙoshinta, ganin mutane ta danne firgicin data shiga da ƙyar tana ƙokarin buɗe jakar daya ajiye a jikinta. Ganin mayafi kalar ɗan kwalinta saita shiga ƙokarin buɗeshi daga leda.

     Maman Ahmad data ɗan fahimci lamarin nasune ta leƙo motar ta amshi mayafin ta buɗema Ummu shi, daƙyar take danne dariyarta da mamakin Amaan, tace, “Amarya angon nakifa na lura akwai kishi, wlhy ina bayansa, konine bazan yarda kishiga wajennan ahaka ba”.

      Kasa fahimtar ta Ummu tayi, dan ƙwaƙwalwarta bata gama dawowa daga ruɗanin data tafiba har sannan. Bayan ta kammala yafa mayafin ta fito da taimakon maman Ahmad.

      Ɗan kama hannun da ango kema amarya shi ƙinyi yayi, yadai tsaya suntafi a jere su Attahir na binsu abaya da gayyar sauran abokansu sojoji.

     Shigarsu ƙaton hall ɗin dake dinɗim da duhu ne yakuma tsurar da Ummu, taɗan matsa jikinsa batareda ta shiryaba. Yana ƙoƙarin zaro wayarsa ya haska aka kunna hasken fitulun hall ɗin da suka ƙawata adon da akai masa, ɗunbin jama'ar da aka tara suka saki ihu suna masa murnar aurensa, barin jikinsa da Ummu taɗan jingina tayi tana ware idanun mamaki, shikansa sai yanzu ya fahimci abinda ke faruwa, dan haka ya ɗan lumshe idanunsa yana buɗewa akan jama'ar hall ɗin.............✍🏻



NO. 15



.............Gaba ɗaya hall ɗin sojojine da matansu a ciki, hakanne yasa bai iya cewa uffanba yabi Umarnin Attahir dake nuna musu mazauninsu shida Ummukulsoom, amma sai antayama Attahir harara yakeyi ta gefen ido.

         Koda suka zauna ita dai Ummukulsoom kanta a ƙasa tana wasa da hannunta, sai da akai addu'a kafin afara abinda ya tara mutane naɗan jawaban taya Lieutenant colonel Usman Mahmud Usman Ajiwa murnar aurensa tareda yima amarya barka da zuwa, itadai Ummu taji wani, waniko bata fahimta saboda da turanci akeyin duk jawabin.

     Wayarsace ta kuma ring, yay guntun tsaki yana dubawa, ganin Momcy sai abin yabashi mamaki, dan ɗazunfa da rana sunyi waya bayan saukar Dad da daɗewa.

    Ɗagawa yay suka gaisa.

      Daga can tace, “Na kiraka ɗazun baka dagaba, ya nakejin hayaniyane kuma?”.

      “Ba komai Momcy, bansan ke kika kiraba kuma”.

       Gaban Ummu yafaɗi jin ya ambaci Momcy, jitai yacigaba da faɗin, “A'a wani ɗan walimar cin abincine haka oganninmu suka shirya, amma zan kiraki in an tashi”. Bai jira amsarta ba ya yanke wayar.

    Itadai Ummu batako motsaba balle ta nuna masa tama fahimci abinda yake.

       Ancigaba da gudanar  da taro cikin aminci da nutsuwa, dan babu wata hayaniya abinka da manya, yayinda tsakaninta dashi babu wata hira, kowa baki ɓam, anyi wasan takubba irinna bikin sojoji daya birge Ummu sosai, sannan akaci akasha tareda ɗaukar hotuna, saikuma ƙyaututtuka da suka samu da gashi har Ummu.

    Ƙarfe sha biyu saura taro ya tashi lafiya, dama Amaan a matuƙar takure yake, yagaji sosai dukda wajen bawata hayaniya bace dazata damesa, dan bawani yawanema dasuba, gashi kuma babu wata hayaniya.


        Kaf motocin da suka shigo Barrack ɗin dake anguwar Awolawo Road, ikoyi, saida suka raka su su Amaan har ƙofar gidansa, dukda kuwa akwai manyansa sosai dasuka halarci taron harda iyalansu, sai dai dagashi sai Ummu dasu Attahir ne suka shiga ciki, suko sauran kowa yanufi nasa gida.

     Ita kanta Ummu a gajiye take, dan ta ƙagara ta kwanta ta huta da cire wannan rigar, da sauri A'i dake zaune a falon tamiƙe tana musu sannu da zuwa.

      Maman Ahmad ta miƙa mata ledoji da faɗin, “kibama duk ma'aikatan gidannan ɗai-ɗai”.. 

     A'i tace, “To hajiya duk za'a basu, sannunku da zuwa”.

       Shima Attahir ajema su Ummu nasu daya ɗako yayi, dan basuci komaiba a wajen taron, yasan kuma wannan tsarin Amaan ne, koya kuke dashi bazaije wajen tatonka yaci abinciba, koshi da suka zama ƴan uwama lokacin bikinsa da maman Ahmad baicinba saida yazo gida, to gashima a nasan bai ciba.

    Sallama sukai musu suka fice dan dare yayi, gashi a gida suka bar Ahmad dama wajen mai aikinsu zubaidah.

      Da gashi sai ita aka bari a falon, sai A'i dake a laɓe ganin ƙwaƙwaf, kanta aƙasa tanufi hanyar ɗakinta, takunta bai gaza uku ba muryarsa tasata jan birki babu shiri, “Wa kika barma wannan?”.

     Dawowa tayi ta durƙusa a gabansa, leda ɗaya ta ɗauka ta miƙe ta wuce.

    Da kallo ya bita ƙasa-ƙasa harta shige, ya sauke numfashi da lumshe idanunsa yana jingina kansa da kujerar.

     Ƴar dariyar mugunta A'i tayi tashige da alwashin faɗama Momcy da safe dantaji farin ciki.

        

     Ummukulsoom ma koda ta shiga ɗaki saita zube a gado tana mamakin wannan rayuwar, itadai tunda ta taso bata taɓa ganin mai irin wannan halin nasaba,  miskiline irin na gaske ɗinnan, gashi abin ya haɗe masa biyu da aikin sojoji, saidai takula bashida wulaƙanci irinnasu Momcy, koda yake lokaci baiyi dazata yanke wannan hukuncinba, tunda dai kwana ɗaya kacal kenan tayi dashi a gidan. 

     Ta daɗe a wajen tana saƙawa da kwancewa, rabin tunanin dukna Baseer ne da sonsa ya zame mata gyambon zuciya, sai dai tana cigaba da kaima ALLAH kukanta akan ya yaye matashi, tasan badan halaccin Alhaji Mahmud ba da sai dai taƙare rayuwarta a ƙauyen ɗilau babu mijin aure, dan Baseer yariga yay mata fenti mai wahalar goguwa, wannan ƙauyen nasu da inhar aka saki mace take jan tsawon lokaci bata samu mijin aureba, mafi yawama saidai suyi aure a wajen ƙauyen. Ko a mafarkinta bata taɓa kawo Baseer zai mata hakanba akan kuɗi.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


          Su Baseer anata kwasar garar amarci kam, danma Suhailat ɗin raguwace, daya cika matsa mata tahau raki dacewa zata sanarma Daddynta, shiko yakoma bata haƙuri da lallashi.

      Tunda suka tare agidan ba ai sharaba, abinci ko kullum daga gidansu Suhailat ake kawowa, idan sunci sun ƙoshi bazasuyi wanke-wanke ba, sun tara uban kwanuka a kicin sunƙi su wanke.

     Yauma suna zaune a falo suna hutawarsu, shi yana zaune itako tana kwance a jikinsa suna kalon film.

     Idanunta ta ɗago taɗan kallesa tana yatsine fuska, “Love yaya dai?”.

     Cikin tura baki tace, “Love nifa ice-cream nakeson sha wlhy”.

      “To love, ya kikeson ayi yanzu?”.

     “Mu fita mana”.

 “Amma kina ganin baza'ace kin fara fita da wuriba, kofa sati baki cikaba a gidannan”.

     Wata banzar harara ta zuba masa, “Kaifa na lura har yanzu ƙauyanci ba gama sakinka yayba, an gaya maka munan muna wannan saka idon da tsarin banzar, ni tashi muje ka shiryani mu wuce Please”.

     Maganar ƙauyencin data jefesa dashi ta sosa masa rai, amma saiya danne ya ɗauketa suka nufi sama inda bedroom ɗinsu yake.

     Shiyya shiryata ya shirya kansa, sai dai kuma kayan data zaɓa ya saka matan sunyi ƙanana, ya matso inda take zaune yana taje sumar kansa, “Love in nemi alfarma mana dan ALLAH?”.

     “Tami?”. Cewar Suhailat dake naɗa siririn gyale a kanta.

      Ya ɗan sosa wuyansa yana murmushin yaƙe, “Kayannan ne sai nake ganin kamar sunmiki ƙanana, da da yanzufa akwai banbanci”.

     “Tofa” tafaɗa cikin taɓe baki damasa wani kallon banza, kafin tacigaba da faɗin, ”Sokake na zuba dogon hijjabi uwa wata matar liman? Kaiko in baka ajiye wannan rayuwar ƙauyenba ALLAH zamuyita samun matsala dakai, idan bazaka iya bina a hakaba yi kwanciyarka agida saina dawo”. Taja key ɗin mota da bag tai gaba abinta.

        Cije leɓe yay cikin tsantsar takaici, wai dama haka yarinyarnan take bai saniba, yay ƙwafa tareda binta da ɗan gudu yana ƙwala mata kira.

       Harta tada motar ya fiton gefenta ya buɗe ya shiga, ta taɓe baki da ɗauke kai.

     “Love kawo nai driving ɗin, bai kamata ace kiyiba”.

      Horn tayi mai gadi ya buɗe mata gate, saida ta fice a gidan kafin tabashi amsa, “Bana buƙata, zanja kayata”.

     Shiru yay baikuma cewa komaiba, sai dai ƙasan ransa mamakinta yakeyi, wato lulluɓin biri taimasa da fatar kura akan hallayarta, aiko dai bazai ɗauki rainiba, dolene ta girmamashi a matsayinsa na mijinta.

       Har suka isa wajen shan ice-cream ɗin babu wanda ya sakema ɗan uwansa magana, ita waƙarma data saka taketa bi a hankali, shiko takaicinta yagama kawo masa maƙoshi. 

      A wajen shan ice-cream ɗinma itace tai komai shi yana tsaye zororo tamkar wani yaronta, sai da aka gama haɗa musune tamiƙa masa ya ɗaukar musu suka sami wasu kujeru acan gefe suka zauna sha.

     Sunɗan jima a wajen, yanda taga ƴammata suna kallon Baseer ɗinne ranta ya ɓaci, dan haka tace masa ya tashi su koma gida.

      Murmushi yay danya kula dai kishin kallon da matan ke masane yasata faɗin su tafi, sai yakuma ƙara bada faɗi yana taku ɗai-ɗai danya tunzura zukatan ƴanmatan.

     Yanzunma ita tajasu zuwa gida, sai kumbura fuska take wai ita fushi, da sukazo gida saida yayta lallashinta sannan ta fara kulashi.

       “Wai Love dattin gidannan bai ishekiba ne?”.

       Kallonsa tayi a wani yanayi, “Mikake nufi to? Koni zan gyara?”.

      “A'a bance kezaki gyaraba, amma kibari ƴan aikin da Mami tace akawo suzo hakanan mana”.

      Zaune tatashi daga kwanciyar da tayi tana yatsine fuska, “Kasan mikake faɗa kuwa Baseer? Kana tunanin zanbar wata ƴar aiki mace tarayumin a gida ne? Idanma tunaninka kenan ka canja shawara, sai dai idan maza za'a kawo wlhy”.

      Babu shiri ya waro ido waje da matuƙar mamakinta, “Maza kuma love? Nanfa gidan matar aurene ya za'ai maza suzo suna shigar mana ɗakuna? Idanma sabodani ne wlhy ki kwantar da hankalinki, nifa babu wata mace data isa ɗaukar min hankali bayanke, dagake babu ƙari dan kinriga kin tsare ko ina baki barma wata fili ba”.

      “Eh nayarda da wannan, amma dukda haka babu wata ƴar aiki da za'a kawo a gidannan”.

      “Amma Love idan ba'a kawoba wazai mana wannan aikin, kedai ba iyawa zakiyiba, kibari ko tsohuwa akawo to”.

       “Tsohuwa? To lallai kanka ya kwance wlhy, ai waɗanan tsoffin sunfi kowa illa a gida, dan jikokinsu suke kawowa ko ƴar ƴar uwarsu, kainifa nagama magana wlhy, idan baka yarda akawo maza ba saidai karinga aikin da kanka”.

     Ba karamin sakin baki yayba yana binta da kallon mamaki harta gama haye benen, wai wannan yarinyar mitake nufi dashine? Tunma kan ayi nisa tafara maidashi tamkar wani yaron gidanta, to lallai zai saitata a hanya bazai ɗau rainiba. 

     Ya daɗe zaune a falon yana saƙawa da kwancewa kafin yamiƙe yanufi kicin ɗin, dan harga ALLAH bayason ƙazanta a rayuwarsa.

     Zagewa yay yafara wanke-wanken, yagama tsaf yagyara kicin ɗin yadawo falo, ina faɗa muku saiga Baseer yagyare gida tsaf yay morping, sai faman riƙe kugu yake na gajiya, Suhailat kam tanacan miƙe a gado tana kwasar barcinta ma batasan bikin dayakeba.


(Mijin Hajiya sai haƙuri🤣zafafa fans na gaisheka da ƙyau😝).



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


                      *_Lagos_*


   Da safe Ummukulsoom tunda tai sallar asubahi tai azkar sai bata kwantaba, ɗakinta ta gyara tsaf sannan ta fito falo, A'i ta iske tana shara, tai mata sannu yayinda itama A'i ta rissina ta gaidata, fuskar Ummu ɗauke da fara'a ta amsa mata, babu inda tasani a gidan ko kicin, dan haka ta zauna tana kallon A'i na cigaba da gyaran falon, sai fira da sukeyi jefi-jefi.

     A'i ta kammala gyaran falon tsaf, dan haka Ummu taje ɗakinta ta ɗako turaren wuta dana ruwa takawo mata aka saka, tareda waɗanda suka gani, dandanan falon ya ɗauki wani ƙamshi na musamman.

      Cikeda bariki A'i tace, “To Uwar ɗakina saura ɗakinki dana oga ko”.

      Murmushi Ummukulsoom tayi, “A'a Baba, wannan zan dinga gyarawa insha ALLAH, aikin ai sai yay miki yawa”.

     “A wane yawa Uwar ɗakina? Shifa aka turoni nayi, indai bazaki iyaba zan dinga gyarawa”.

      Ummukulsoom ta girgiza kanta alamar a'a, dan bata manta maganar baba halima datace ko acan bai yarda ƴan aiki su shigar masa sasheba sai ƙannensa.........

    Motsin da taji a bayantane ya katse mata tunani ta juyo da hanzari, shine sanye cikin kayan training ash, zubewa A'i tai tana gaidashi, ya amsa sau ɗaya yay gaba abinsa.

      Sanyi ƙalau jikin Ummu ya ƙarayi, gashi ko gaisheshinma ita bata samu damar yiba.

      A'i tace, “Uwar ɗakina bara to na gyara nawa ɗakin nima”.

    Kai kawai Ummu ta iya ɗaga mata, A'i na barin wajen ta sauke ajiyar zuciya da saƙa wasiƙar jakinta, ta bisa ta gaidashi kota bari saiya sake fitowa? Tarasa matsaya, dan haka tacigaba da zaman falon.

      A'i ma dake laɓe gajiyatai da tsaiwa takoma cikin ɗaki ta zauna tana neman Number Momcy a waya ta fesa mata labari harda na jiya.


         Ummukulsoom na nan zaune kusan awa ɗaya saigashi ya fito sanye cikin Uniform, yayma Ummukulsoom masifar ƙyau, dan haka ta shagala da kallonsa batareda ta saniba.

     Bakinsa yaɗan taɓe yana lumshe idanunsa ya buɗe a kanta, kafin ya zauna kujerar dake kusa dashi.

       Anan Ummu ta dawo hayyacinta, ta zamo daga kujerar tana gaidashi.

      “Lafiya” kawai yace, takula wannan shine salon amsa gaisuwarsa dai, bata tashi a ƙasanba shikuma bai miƙeba, magana yakeson yi amma yakasa buɗe baki. Kusan mintuna biyar suna a haka kafin ya fisgota da ƙyar, “Maman Ahmad zatazo anjima ta nuna miki tsarin gidan, akwai maiyin abinci dazai dawo anjima”.

       Yanda yay maganar a dunƙule sai Ummu ta gaza fahimta, amma dukda haka saita ɗaga masa kai kawai alamar amsawa, yakuma jan wasu seconds ɗin kafin yacigaba da faɗin “Naje Abuja ni”. Yana gama faɗa ya miƙe.

     Kan Ummu a ƙasa tace, “ALLAH ya tsare ya saukeka lafya”.

     Akan laɓɓansa ya amsa yana ƙoƙarin ficewa, harya kai ƙofa sai kuma ya tsaya yaɗan juyo ya kalleta batareda ya iya cewa uffanba.

     Mikewa Ummu tayi ta nufosa, danta lura kiranta yakesonyi amma bakinsa ya gagara hakan, zata risina yay mata nuni data miƙe tsaye, mikewar tai, saidai kanta a ƙasa ta gaza kallonsa.

     “Akwai kuɗi a ɗaki, idan Desmond yazo kibasa yayo cefanen duk abinda ake buƙata”.

    Bai jira cewarta ba ya fice abinsa.

       “Ni Ummukulsoom naga takaini, wanene kuma desmond ɗin?”.

    Babu mai bata amsa dan haka takoma ciki bayan taji tashin mota alamar sun tafi.

     A'i dai nacan ɗaki zaune batasan mike faruwa ba, dan batayi zaton fitowar Amaan a wannan lokacinba.

     Ɗakin nasa Ummukulsoom tayi yunƙurin zuwa ta gyara saiga ƴar aikin maman Ahmad yauma takawo musu abinci, godiya tace tai mata ita kuma tanufi ɗakin nasa danta gyara.

       Yanzu ne tasami nutsuwar yima ɗakin kallon tsaf, komi Coffer Color ne, yayinda bedsheets yakasance fari, hakama labulaye, ƙamshine mai daɗi ke tashi tamkar ba ɗakin namiji ba, gashi babu wani tarkace ko kayan hauka irin nasu Yaa Ameer datake shan wahalar gyarawa. Tsaf tazage ta gyara ko ina ta bajeshi da ƙamshi har toilet ma, ta jinjinama tsaftarsa gaskiya.


★★★★


      Sun gama karyawa babu jimawa saiga maman Ahmad, sosai Ummu tai murnar ganinta, bayan sun gaisa maman Ahmad ta zagaya da ita lungu da saƙo na gidan, tareda nuna mata komai dalla-dalla, suna cikin zagayen ne Desmond kukun gidan yadawo, dama yaje duba mahaifiyarsane da batada lafiya shiyyasa su Ummu basu iskeshiba a gidan.

     Yayi matukar murna daya iske boss ɗinsa yayi aure, dan shi bai faɗa masaba, Ummukulsoom dai aranta tace da matsala kenan, dan desmond bayajin hausa sai turanci da yarensa na ƴan Calaber, sai ƴar haukar hausarsa dayake ƙwaɓowa itama tsinta yake wajen Amaan idan sunayi da Attahir ko waya.

      Kuɗi ta ɗakko masa kamar yanda Amaan ɗin yace, ya amsa yanufi kaduwa cefane cikin matuƙar ɗokin wannan mata ta ta boss.

      Har yamma maman Ahmad na gidan tana kuma koya mata abubuwan daduk ya dace, tareda bata shawarwari, dan ta lura Ummukulsoom tanada bukatar koyan abubuwa, itakuma harga ALLAH yarinyar tashiga ranta sosai. 


        Da daddare Desmond yay musu girki kamar yanda yay musu na rana dama, ita kaɗanma ta iya tsakura ta kwanta, dan sosai kewar babanta ke damunta, gashi matsalar ma ko Number sa bata riƙeba, data amshi ko wayar maman Ahmad ce ta kirasa sun gaisa.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

              *_KADUNA_*

     

           Koda Suhailat ta tashi taga aikin da Baseer yayi sai abunma yabata dariya, ta kallesa cike da tsokana tana faɗin “Lah ashe Love ɗin nawa ya iya aikin mata, aiko kahutar da kuɗin Daddy wlhy”.

     Takaici ya hanashi amsa mata ma, yay hayewarsa sama ya barta tana tuntsurar dariya, a ranar yini guda iskancin dataita masa kenan.

     Washe gari su Najeeb sukazo musu yawo, yini guda a gidan sukayi suna shan hira, abinci ma sai sawo musu akayi, dan Suhailat dai bayi zataiba, gidanma yau da safe Baseer ne yaɗan gyara inda zai iya, amma dayaga tashiga barci da rana yayta zulama su Areef ƙarya🤣😝.

        Washe garima dai baƙin sukai, ƴan uwan Suhailat sukazo su Amrah, ranar dai Baseer sai barmusu gidan ma yayi yafita gararanba agari dan babu inda ya sani, su Najeeb kuma duk ƴan Zaria ne.

     A wajen yawonsa yasamo budurwa mai suna Lubna, yarinya ƙyaƙyƙyawa ƴar manya, Number ya amsa amma shi yaƙi bata tashi, yace mata idan ya kirata ta gani.

     Sosai Lubna tamutu akan Baseer, shiko sai fankama yake da huruwa yana basarwa.

     Sanda ya dawo gida su Amrah sun wuce, hakanne yasaka Suhailat yin fushi tanata masa masifa itafa bazata ɗauki wannan yawonba gaskiya. Haƙuri yayta bata dan daya fara mata ƴar masifa irin shi miji ɗinnan saita ɗauki waya zata kira Daddynta, dole yakoma lallashinta da bata haƙuri sannan ta saukko sukacigaba da ƴar soyayyarsu.

      

      Haka rayuwar tasu take tafiya ba a daidaiba, dan kuwa Suhailat ke acting a gidan like miji, shiko yazama mijin hajiya, sai abinda tace takeso ake a gidan, randa suka cika sati biyu saiga kuku daddynta ya turo mata, abin ya matuƙar sosa ran Baseer, sai dai kuma babu damar magana kan ran Suhailat ya baci.

    Ƙiri-ƙiri ta hanashi fita, idanko ma yasamu ya fitan minti talatin yay yawa take danna masa kira ya dawo gida, yaukam ma dazai fitan motarsa babu mai catai yaje yahau napep, dan batada kuɗin bashi yasha mai.

      Dole sai haƙura yay da fitar kuwa, dan harga ALLAH bazai je ya hau napep ba da ajinsa da komai😹⛹‍♀............✍🏻



Mungode kwarai da gaske da lamuninku, waɗanda suka kiramu sukai mana gaisuwa da waɗanda sukai mana ta chart, harma waɗanda basu manaba duk mun gode ALLAH yabada ladan zuminci. Shikuma ALLAH ya gafarta masa ya yafe masa da dukkan iyayenmu da al'ummar musulmi tundaga zamanin ANNABI ADAMU har kawo yau😭🙏🏻, ALLAH ya ƙara mana haƙurin rashinsu, Muma ALLAH ya wajabta tsoransa a zukatanmu ya ɗauki ranmu muna masu imani da soyayyar MANZON ALLAH (S.A.W)😿, ALLAH ya gafarta mana baki ɗaya



NO. 16


..........Matan Barrack ɗin sunata shigowa ganin Ummukulsoom amarya, Hausawa da ƙabila, waɗanda basajin hausa iyakarta dasu gaisuwa, saikuma taita murmushi.

       Da yawansu sukan ƙunshi gulmar mamaki a ransu, basu taɓa zaton ganin matar Ajiwa yarinya irin hakaba, sun zata zasu gata wata babba irin sa'arsa ɗinnan.

       Ummu dai bama tadan sunaiba, damuwar gida da tabon da Baseer ya barmata arai sune maƙale a ranta, duk da dai tana ƙoƙarin cire Baseer ɗin da ƙarfin tsiya.


         Yau ma dai bayan ta tashi barci ta kimtsa ɗakinta da jikinta, fes ta fito cikin doguwar riga ta shadda ruwan gwaiduwar ƙwai, kayan sun mata ƙyau dukda babu wata kwalliya atare da ita, daga fauda sai lipsgloss data saka, sai ƙamshinta mai daɗi dake tashi a jikinta.

     A falo ta iske A'i na faman Morping, suka gaisa cikin girmama juna tamkar gaske, Ummu dai batada matsala da A'i, saima yabon halayenta da takeyi, girmamata kuma takeyi sosai kasancewar a haifema zata iya haihuwar kamarta.

     Bata zaunaba ta wuce dani danta karya. A'i tabita da ido tana wani taɓe baki, itafa harma tafara tsarawa kanta ƴarta zata kawo gidan itama a dama da ita, idan da rabo sai aci wannan daular duniyar da ita tazama matar soja. dan tun randa tazo gidan tai tozali da Amaan taji a ranta sun dace da ƴarta, dan Aina'un tata ƙyaƙyƙyawace san kowa ƙin wanda bai samuba.

      Ummukulsoom dai batasan hidimar da A'i keyiba ma ita, anutse tai breakfast ɗinta ta taso tadawo falon da A'i kesa turaren wuta. Kasancewar babu nepa saita kwanta cikin kujera tana tunanin rayuwa da sauyin da take zuwa dashi akowacce rana.

        Cike da salon iya bariki A'i tazo ta zauna a falon ƙasan carpet, “Uwar ɗakina barci ake?”.

     Ɗago ido Ummu tai ta kalleta tana murmushi, “A'a baba, idona biyu wlhy, natafi tunanin duniyane kawai”.

      A'i tai ƴar dariya da gyara zamanta, “hakanma yanada ƙyau Uwar ɗakina, amma nikan idan ban shiga hurumin daba nawaba da munyi wata magana”.

     Zaune Ummu ta tashi sosai, cike da girmamawa tace, “Baba ke uwace a gareni, duk abinda kikaga yadace kimin magana na gyara ko nayi karkiji komai kimin”.

     “Gaskiyane Uwar ɗakina, ALLAH dai yay miki albarka. Dama akan mijinki ne wlhy, nakula kamar babu wata shaƙuwa a tsakaninku, sai kace ba auren soyayya kukaiba?”.

       Murmushin takaici Ummu tayi idonta akan A'i, “Humm Baba kenan, kusan hakane gaskiya, dan saida aka kawonima mukasan juna”.

      “Irin auren mutan da kenan, muma ai duk shi akai mana kuwa uwar ɗakina, irin wannan auren ai anbar yinsa yanzu saboda zamani ya canja, amma karki damu, duk shawarar data dace zan baki yanda zaki kama mijinki kuwa yamafi waɗanda sukai auren soyayyar”.

      Ƙasa Ummu tayi da kanta saboda kunyar A'i.

     “Barjin kunyata Uwar ɗakina, sosai zan karantar dake indai nice, sai daifa na lura waccan uwar mijin taki ba mutuniyar kirki bace ba”.

      Da sauri Ummu ta ɗago ta kalleta, kafin ta fara waige-waige a falon cike da tsoron kar wani yaji maganar da A'i tayi, ganin babu kowa yasata maida kallonta gareta, murya ƙasa-ƙasa tace, “Baba wannan maganar mubarta dan ALLAH, Momcy uwace a gareni kuma ni bata taɓa min wani abu mara ƙyauba”. 

       Ji A'i tai kamar ta make Ummukulsoom, dan recoding take a wayarta, sotai Ummu ta saki baki suyi gulmar Hajiya Jamila, amma takula wanna yarinyar shegen wayone da ita, sai tayi da gaske zata ɗorata a network, a fili kuwa saita washe jajayen haƙoranta tana muskuta zamanta kusada Ummu, “Uwar ɗakina ai maganar gaskiya dolene ayita, amma tunda baƙya buƙata anbar zancen, yanzu maganar miskilin mijinnan naki akwai hanyar dazan miki a bidashi ta ƙasa kisameshi ram a hannu”.

      Wani irin tsargawa cikin Ummukulsoom yayi na tsoro, dan kuwa A'i na rufe baki Yaa Amaan na shigowa cikin falon.

       Duk sai sukai tsiru-tsiru alamar rashin gaskiya.

     Shikam ma bai kula da suba, dan waya ya shigo yanayi, hakanne yasaka Ummukulsoom sauke ajiyar zuciya ta miƙe zuciyarta na addu'ar ALLAH yasa baiji zancen nasuba.

     Taɗan saci kallonsa tana gyara tsayuwa, sanye yake da wandon Uniform sai farar t-sheat data kamasa sosai, hakanne yasaka ƙirar dirarren jikinsa bayyana fili.

      Kallon Ummu yay sau ɗaya shima ya janye idonsa yana cigaba da wayar da yake cikin harshen turanci.

      A'i kuwa tuni ta miƙe tabar falon jikinta na ɓari kamar gaske, a ƙasan ranta kuwa taso ma Amaan ɗin yajisu, danya fara zargin Ummukulsoom.

      Ganin A'i tabar falon saiya zauna yana cigaba da wayar.

     Desmond kuku ne yafito hannunsa ɗauke da ƙaramin tire ya ɗoro ruwa da glasscup.

     A table ɗin gefen kujerar da yake zaune ya ɗora tiren, yana ƙoƙarin ɗaukar ruwan ya buɗe Ummukulsoom tai masa alamar daya barshi, dan ta tuno nasihar kakarta Gwaggo hinde da tace *_Umma karki zama cikin mata masu yima miji rowar ruwa, a duk sanda mijinki yashigo gida kifara tarbarsa da sannu sai ruwa ya biyo baya, hakan zaisa aduk lokacin dayaji ƙishi koda yana a wajene saiya tunoki, wannan ma mallakace mai daraja da mace zataima mijinta babu boka babu malam, balleke da akai muku auren haɗi_*.

       Babu musu Desmond ya miƙa mata ruwan cikin rissinawa irin ta girmamawa, dai-dai lokacin da Amaan ya ajiye wayar yana kuma ɓata fuska.

     Gaisheshi desmond yayi, kafin yabar wajen da hanzari gudunma Boss laifi.

        Ummukulsoom kam ida buɗe ruwan tayi ta tsiyaya a cup ɗin, har ƙasa ta durƙusa ta bashi tana faɗin “Sannu da zuwa, ya hanya?”.

      Manyan idanunsa Farare tas ya ɗago daga kallon wayar ya sauke a kanta, kafin yaɗan lumshesu ya kuma buɗewa akanta. Batare daya amsaba ya ɗaga mata kansa kawai da miƙa hannu zai karɓi ruwan data miƙo masa.

      Tattausan hannusa ya ɗora akan nata batareda yay niyyar hakanba, da sauri Ummu ta ɗago idanunta ta kallesa,  shima dai-dai ya ɗago nasan akanta.

     Kallon ido cikin ido sukaima juna, ya janye nasa idon cike da basarwa tamkar ba ai komaiba, dukda kuwa har yanzun hannun nasa nakan nata.

     Ita ta fara yunƙurin janyewa a kasalance, kafin shima ya janye yana ƙara haɗe fuska sosai, yakai ruwan bakinsa ya fara sha sukaji ana ƙwanƙwasa ƙofa.

      Ita kaɗai ta waiga ta kalli ƙofar, shiko ko motsi baiyiba, saima kofin ruwan daya ajiye ya miƙe zai nufi ɗakinsa.

         A'i dake laɓe tana kallonsu ce ta fito har tana tuntuɓe tanufi ƙofar ta buɗe, ƙyaƙyƙyawar mace fara tas ce a tsaye.

     A yatsine ta kalli A'i kafin tai mata nuni da hannu alamar ta matsa mata a hanya.

    Matsawa A'i tai numfashinta na fita da go slow, “wannan kuma wacece haka?”. Tai tambayar a zuciyarta.

      Duk wannan abun dake faruwa a idon Ummukulsoom ne dake tsaye itama a inda Yaa Amaan ya barta.

     “Hi babie”. ‘Budurwar ta faɗa tana ɗagama Yaa Amaan dake ƙokarin ida shigewa ɗakinsa hannu’.

      Sai dai harya shige abinsama.

    Ummukulsoom dai da A'i na tsaye suna kallon ikon ALLAH, dan ita shigar dake jikin matarma take ƙarema kallo.

    Sanye take da dogon wando jeans da jar t-sheat, ta cusa rigar a cikin wandon, sai siririn belt ɗin da aka tsuke wandon dashi kalar jaa, sai sweater wadda da alama tasakane dan gayu ba sanyi ba, gashin da Ummu ke ƙyautata zaton na dokine ta ɗauresa a tsakkiya yana reto ta yana gyale siriri.......

      Maganarta ta kuma katse Ummukulsoom daga kallon head to toe ɗin da take mata.

       Desmond take ƙwalama kira alamar dai ita ƴar gidace.

     Cikin hanzari desmond ya fito yana amsawa da “Ma”. Amma sai yay turus ganin mai kiran nasa, a wani yanayi na firgici yake baza idanu  a falon da leƙe-leƙe.

       Ranta a ɓace take magana cikin harshen turanci da nuna Ummu, “Waɗannan fa?”.

      Dukda Ummu batajin turancin sosai taji wannan, dan haka tai shiru taji amsar dazai bata.

     Jikin desmond na ɗan rawa yace, “yi haƙuri Ma, banida hurumin baki wannan amsar, sai dai Boss”.

       Harara ta zuba masa tana jan ƙwafa, kafin tace, “Jeka kawomin abinsha kaje ka sanar masa zuwana”.

    “Ok Ma”. ‘Ya faɗa cikin risinawa’.

    Ba komai Ummu ta fahimta ba a zancen nasu, bare kuma A'i da ba'asan komai ba, amma hakan yamata daɗi, addu'a ma take a ranta ALLAH yasa karuwar mai gidance, sai dai koda hakan ta kasance sai ƴarta ta shigo gidannan, dan zuwa yanzu kam ta fahimci ALLAH ya kawota gidanne danta sama ma ƴarta matsuguni badan taima Hajiya Jamila leƙen asiriba.

        Gaba ɗaya itako Ummukulsoom ranta a dagule yake, tasan ba kishi baneba, abune mai kama da tsoro ke shigarta, dan itadai ba sonsa takeba balle taji kishinsa, ko zataji zafi sai dai taji akan darajar igiyar aure dake a tsakaninsu, dakuma takaicinsa na ɗan musulmai mai aikata zina inhar hakanne tsakaninsa da matar, dankan wannan ai sai dai ta kirata mata, tunda ko a ido kasan zasuyi sa'anni da Yaa Amaan ɗin.......

     Dawowar desmond ce takuma katse tunaninta.

     Matarkam dako kallon su Ummu batayi ta amshi lemon da Desmond ya bata tana cigaba da danna faskekiyar wayarta.

 

          Desmond ya kalli Ummukulsoom cikeda damuwa ya nufi hanyar ɗakin Amaan.

     Hakan saiya ƙara saka jikin Ummu yin sanyi, saima tabar falon tanufi ɗakinta itama, dan batason ganin abinda zaisa kimarsa da darajarsa ta zube a idonta.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡  


        *_KD_*


     Kwance yake ɗai-ɗai a ƙayataccen falon nasu sanyin A.C na ratsasa, ga kwalin lemo da glasscup a gefensa, idonsa akan waya yanata faman zuba murmushi, kallo ɗaya zakai masa ka fahimci charting yakeyi da masoyiyarsa.

      Wata ƴar zabura yay tareda dunƙule hannu yana faɗin “Yes! Itama ta afka” sai kuma yay azama dafe bakinsa da hannu yana waige-waige a falon, ganin babu alamar kowa ya sauke ajiyear zuciya yana rimtse ido, yasan idan iya bala'innan Suhailat ta jisa ai yau babu mai barci a gidan lafiya, dama ganin tayi barcine yasashi fitowa falo da sanɗa.

     Wayarsa ya ɗauka yacigaba da Charting da Lubnar sa hankali kwance.


        Cikin barci Suhailat ta lalubi Baseer amma sai taji filone a gabanta, kuma matsowa tayi tana lalubawa babu alamarsa a wajen, da ƙyar ta buɗe idonta tareda laluben bedside drawer ta kunna fitila, ganin babushi dai da gaske sai tai tunanin kodai yana bayine, hakanne yasakata maida idonta ta rufe batareda ta kashe fitilarba.

      Kasa komawa barcin tai ta tsaya jiran fitowarsa. Minti uku, huɗu, har aka kai sha biyar babu alamarsa, sakkowa tai a gadon ta nufi hanyar bathroom ɗin tai knocking tareda kanga kunnanta, sai dai kuma tsit babu alamar motsin ruwa, murɗa ƙofar tai ta buɗe ta leƙa, wayam babushi.

       “To ina kuma yaje?”. Ta faɗa cikin riƙe ƙugu da cije lip”.

      Fitowa tai, falon sama ma dai wayam, cikin ruɗani tanufi ƙasa, tunkan ta ida sakkowa ta hangoshi kwance bisa doguwar kujera.

      Wata irin hasala zuciyarta ta farayi, dan haka tafara sauka benen a hankali cikin sanɗa.

     Gaban Baseer ya faɗi saboda jin motsi, da sauri yakai dubansa ga matakalar benen saiya hango Suhailat na sakkowa, ai babu shiri yay azamar goge Number Lubna dayay save da suna Lukman Ɗilau daga kan WhatsApp folder ɗin, yay azamar fitowama gaba ɗaya yakoma folder ɗin Qur'an tareda yin fuska tamkar baiji motsintaba.

    Suhailat data lallaɓo a hankali saboda son ganin miyake? dan zuciyarta kai tsaye tabata amanarta yakeci, sai taga Qur'an yake karantawa, wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke tareda faɗawa jikinsa.

    Yiyai kamar baisan da zuwan nataba, yay wata zabura zai ƙwala ihu ta toshe bakinsa da hannu tana faɗin “Love nice fa”.

      Ajiyar zuciya ya sauke tare da janye hannunta, “Kai Love wlhy kin bani tsoro matuƙa, yaushe kika sakko?”.

     Shagwaɓe fuska tayi tana kuma manne jikinta da nashi, “Ba kaineba ka gudo ka barni, sai kawai na farka babu kai”.

      “Sorry Love ɗina, barci naji na kasayi, shinefa nace bara nayi ko karatun Qur'an ne, gudun karna hanaki barci da hasken waya shinefa nadawo nan. Amma amin hukunci dai-dai da laifina”.

       Murmushi tamasa da ɗora goshinta a nasa, “Yanzu ko zan hukuntaka Love” ‘ta ƙare maganar da manne bakinsu tana bashi wata sumba mai ƙyau’.

       Badan yasoba ya biyemats, kafin kacemi sunyi zurfi tun a falon, daƙyar ya iya ɗaukarta suka koma sama zuciyarsa na mamakinta, wato yanzu data fara gogewa a harkar saiya fahimcima tafisa jaraba, dan lamarinta harya fara bashi tsoro, saida suka gama soyewa fa ya sakko falon chart da Lubna, amma yanzu kuma ƙiri-ƙiri ta nuna ƙari takeso.

       Haka dai ya miƙa wuya bori ya hau kafin su koma barci.


*Washe gari* da safe saƙon Daddynta yazo akan maganar komawarta makaranta, idan kuma batason A.B.U Zaria tafaɗa inda takeso a maidata.

          Baseer dake zaune a dani suna breakfast yaga fara'arta tai yawa tana danna waya, farfesun kifin da yake sha ya ture gefe yana maida hankalinsa a kanta sosai, “Love tasamune shin?”.

      Batareda ta kallesa ba tace, “Kusan haka”.

     Tasowa yay ya dawo kusa da ita ya zauna, shima yana leƙa wayar bayan rungumeta da yay.

     Kallonsa ta juyo tayi tana ƴar dariya, “Wai kasan me?”.

    “A'a saikin faɗa babie na”.

       Kuma ƙadandaneshi tayi cikin tsantsar so da ƙaunarsa, “Daddy ne yace yaushe zan koma makaranta? Idan kuma banason Nigeria nafaɗi duk inda nakeso zai kaini yanzu tunda inada aure”.

      Wani farin cikine ya ratsa Baseer, shima kuma ƙanƙameta yayi, “Kai amma naji daɗi love, yanzu ke wata ƙasa kika zaɓa mana?”.

       Sakinsa tai tana kallonsa a ɗage, “Ban gane wace ƙasa na zaɓa manaba? To ni da wa?”.

      “Keda wa kuma Love? Ni da ke mana, kinada wanda yafini a yanzune?”.

       “Tab inadashi mana tunda ga family na, ni nama faɗa masa banason ko ina, dan ni kaɗai yace, niko bazan iya tafiya ko inaba na barka a 9ja kaci amanata”.

       Wani malolone ya tokare maƙoshinsa, amma ƴar iskar yarinyarnan tama rainashi wlhy, jiyake kamar ya naɗa mata na jaki kozai rage ƙududu, amma saiya daure ya danne yana murmushin yaƙe wanda yafi kuka ciwo, “Haba Love wace irin maganace wannan kuma? Please kishi yabar rufe idonki ki daina tunanin zanci amanarki, kuma idanma karatun yakama a fita ƙetare ai tare zamu tafi, basai nai masters ɗinaba acan nima, mukuma zarce da Honeymoon ɗinmu”.

       Dariya sosai Suhailat takeyi tana nuna Baseer daya cika yay fam, daƙyar ta iya tsagaitawa tana dafa kafaɗarsa, “Oh Alhaji Baseer nawa ka tanada na tafiyarto?”.

      Takaicine yafara lulluɓe ganinsa, yay luuu da idanu kafin ya buɗesu da ƙyar yana haɗiye busashshen yawun daya kasa wuce masa a maƙoshi, tashi yay yabar mata dining ɗin yahaye sama.

      Baki buɗe Suhailat tabisa da kallo, sai da yakai rabin steps ɗinne tace, “Ikon ALLAH sai kallo, to waikai haushi kaji? Kaida bakada ko sisi kazauna mini tsarin banza harda wani Honeymoon ko uwarmi, to lallai kacika ɗancin bati, aimaka ciki ai maka goyo harda zanin ɗaurawa, kama daɗe bakaji haushinba, kajimin   baƙin bawa mai jiran ALLAH zai kawo”.

     Sarai Baseer yajita, dan haka ya juyo a fusace zai nuna mata asalin color ɗinsa saikuma ya kasa saboda gargaɗin zuciyarsa da tace “Da sauran time”. Murmushin dabai shiryaba ya sauke, yace, “Love na gode da gori”. Ya juya yacigaba da hayewa.

      Sai kuma Suhailat taji babu daɗi, miƙewa tai da sauri ta hawo saman daɗan gudunta.

     Isakeshi tai kwance kan gado ya rufe fuskarsa da filo.

    Jikinsa ta haye tare da zare filon, ya ɗago fuska zaiyi magana ta haɗe bakinsu.

    Duk yanda yaso ƙin bata haɗin kai ya kasa.

     

     Bayan sun sami nutsuwa haƙuri taita bashi harya sauka, kafin suje suyi wanka tare cikin farin cikin da Baseer iya fuska yakeyinsa.


★★★


        Da yamma Suhailat tashirya ta tafi gida, hakan yabama Baseer damar bajewa a kan gado cikin bedroom suna shan hirar soyayya a waya da Lubna.

    Yayi zurfi sosai har baiji motsin shigowar motar Suhailat ba, harda shigowarta bedroom ɗin nasu.......😬🤫😆⛹‍♀




⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡ 


        

          Desmond yay knocking a ƙofar Amaan tamkar yanda ya saba, sai dai shiru ba'a buɗe masaba, sake yi yay har sau biyu nanama babu amsa.

     Harya yunƙura zai bar wajen yajiyo muryarsa da ƙyar yace, “Shigo”.

     Kasan cewar yakan ɗan jefa masa hausa wani sa'in saiya fahimci abinda yake, dan haka ya tura ƙofar ya shiga.

       Amaan daduk zatonsa Ummukulsoom ce yana kwance a bakin gadonsa ido lumshe, da alama kuma duk Knocking da Desmond yakeyi yanajinsa, tsabar miskilanci ne ya hanashi amsawa.

      “Sir! kanada baƙuwa”.

Cikin rashin zaton desmond ne Amaan ya buɗe idanunsa, kamar bazai tankaba saikuma yace, “Waye?”.

     “Sorry sir! Aunty Bukky”.

   Kuma haɗe fuska yay tamkar bazai tankaba, ya lumshe idanunsa ya buɗe a kansa, yace, “Bukky?”.

      “Yes sir”.

Hannu ya ɗaga masa alamar yaje.

    Har desmond yakama handle ɗin ƙofar zai buɗe muryar Amaan ta dakatar dashi.

     A kausashe yace, “daga yanzu karka sake shigomin ɗaki, duk abinda kake buƙata ka sanarma matar gidan tazo ta sanarmin, idan bata falo kajirata harta fito ko ni idan na fito”.

      “Sorry Sir”.

      Uffan baice dashiba ya maida idanunsa ya sake lumshewa, bamashi da alamar tashi yafita ganin baƙuwar tasa.

       Yaɗauki tsawon mintuna goma kafin yatashi zaune yana jan tagwayen tsaki, mai makon ya fitama saiya hau zame kayan jikinsa alamar wanka zaije.


      Tun Bukky na jiran Amaan da marmari harta fara ƙosawa, sai dai kuma tariga tasan halin wulaƙancinsa da baƙar shariya wanda akullum take faɗin Hausawa nadashi.

      A'i dai na nan laɓe sotake sai taga ƙarshen wasan, desmond kam tuni yakoma kan aikinsa, dan ƙokarin shiryama Amaan abinci yake tunda baisan da dawowarsa ba.

      Ummu kam tana ɗakinta kwance, dukda kuwa zuciyarta sai tunzurata take akan takoma falon taga mizai faru tsakanin mijin nata da baƙuwar. Wani kuma sashe na hanarta akan ƙazantar da baka ganiba tsaftace, ita dai ta ƙyautata masa zato yafi alkairi agareta..........


NO. 17


  .............Sai da yagama komansa hankali kwance sannan ya fito sanye cikin wando 3quarter da ta t-sheat baƙa, sai slipper baƙaƙe masu taushi a ƙafarsa. Ko kaɗan fuskarsa babu fara'a, hannayensa duka suna cikin aljihun wandon.

      Ƙamshin turarensa ne ya fargar da Bukky dake kwance a kujera kamar tasamu gidanta.

       Ta tashi zaune da hanzari tana faɗin “Babie!”.

      Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke idonsa batareda ya amsata ba, ya zauna saman kujera 1seat ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tareda ɗora dukan hannanyensa a hannun kujerar.

       Cikin muryarnan tasa mai cike da miskilancin gwarzantaka yace, “Miya kawoki gidana?”.

       Mamaki ƙarara a fuskar Bukky, ta miƙe tareda nufoshi, amma saiya ɗaga mata hannu alamar dakatarwa da maimaita maganarsa akausashe.

     “Bukky nace miya kawoki gidana?!”.

     Jatai ta tsaya zuciyarta na fara hasala da salon wulaƙancinsa, murya a dasashe tace, “Ajiwa miyasa kake sha'awar wulaƙantani a duk sanda nazo gidanka?”.

      Lumshe idanunsa yay ya buɗe akanta, wani kallon banza yay mata daga sama zuwa ƙasa ya taɓe baki da ɗage kafaɗa alamar oho miki, kafin ya ɗauki wayarsa ya hau dannawa hankali kwance.

       Dai-dai nan kuma Ummukulsoom ta fito dan duk azatonta baƙuwar tama tafi, amma saita ganta tsaye kamar mai shirin danbe, yayinda boss Amaan ke zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya yana danna waya .

        Juyawa Ummu tai da sauri da nufin komawa, amma sai Bukky ta katse hanzarinta ta hanyar nunata tana faɗin “Ita kuma wacece wannan?”.

        Banza yay mata, yaƙi ɗagowa balle yaga wacece ɗin, dukda dai zuciyarsa na basa yarinyar da aka kawo gidance amatsayin matarsa, danyaji ƙamshin munafikin turarentan nan dayake gab da hanata sakawa.

        “Ajiwa! magana fa nake maka”.

     Tamkar bazai ɗagoba sai kuma ya ɗago ɗin, kallo ɗaya yaymata itada  Ummukulsoom ya ɗauke kansa yamaida kan waya yana faɗin, “Kunne keji, kuma yajiki, sanin ita wacece kuma ba matsalarki bace”.

       “Tabbas ba matsalata bace ba, amma kai zata zama taka, Ajiwa kenan, ai bai kamata ka ɓoyemin ka kawo mace gidakaba, koka manta zancenka Na karshe kafin rabuwarmu?”.

         Wani banzan kallo yamata yana juya manyan idanunsa dake kunshe da tsanarta, yaja wani siririn tsaki, kansa ya maida jikin kujera ya kwantar yana lumshe idanunsa, dan zuciyarsa tafara zuwa maƙoshi.

      Haushi yakai Bukky Bango da dizgatan dayake agaban Ummu da A'i data hango a makale, dukda kuwa tanada tabbacin bajin turancin sukeba, cikin shirmensu Na yarabawa da tsantsar gogewa a bala'i ta tafara girgiza jikinta, “Ajiwa kasanifa zan iya tada barrack dinnan tsaf da jama'ar dake cikinta inhar abinda aka sanarmin akanka ya tabbata, Dan alkawarine inhar bazaka aureniba to Baka Isa zama da wata maceba kuwa ko ita wacece a matsayin mata” ta kalli Ummu dake tsaye har yanzu, “Ke kiramin ƴar iskar yayarki dan yau koni ko ita a gidanan”. 

      Bakomai Ummu take fahimta a zancen nasuba, saboda duk wannan bala'in da turanci akeyinsa, sai dai kiran yayarta datace tayi yabata mamaki, wato ita batakai akirata maceba ashe, karon farko arayuwarta dataji wani fushi da sha'awar tsiwar rashin ragi, dan haka ta zubama Bukky harara ta ɗauke kanta”.

      “Heeey” tafaɗa cikin dirga tsalle tana nuna Ummukulsoom da dafe baki, “Ajiwa ni wannan yarinyar take harara danna aiketa?”....

       Kansa daya fara masa nauyi saboda hayaniyata ya dafe, kafin ya dago a zafafe ya nunata, “Wlhy Bukky idan kika bari naje bango akanki zan ragargaza ƙasusuwanki ne a gidannan, halan kin mance dawa kike magana ko? wane Warning nai miki akan zuwa gidana last time?”.

         Tsalle takuma dirgawa ta dire tana nuna Ummu, “Warning ɗinka na banza, da kace karna sake zuwa maka gida baka bukatar mace, su kuma waɗan nanfa? wai inama banzar matar takane? Tafito inba tsoroba”. ‘taƙare maganar a gadarance, tana hararar Ummu tamkar wata kashi’. 

       Idanunsa ya lumshe ya bude a kanta, yayinda tuni suka canja launinsu Na farare tas zuwa Dan jan hasala, Sai dai bakinsa yagaza cemata Uffan...

       Itama Ummu tana buƙatar taji amsar dazai bata akan matarsa da taketa ambata. 

        A'i ma dake a labe har yanzun ko gajiya bataiba, burinta taji amsar dazai bama Bukky, taga kuma zai nuna Ummu amatsayin matar tasane?, dan bakaramin dadi tajiba da jarabar Bukky ta dawo kan Ummu, babban fatanta Bukky ta naɗama Ummu dukama danta kula akwai alaƙa mai ƙarfi tsakaninta da mai gidan, dukda shi sai basarwa yakeyi.

       

        Sosai Bukky ta hango wata wutar bala'i daga idanunsa, tasan wanene Ajiwa akan zuciya da tsantsar rashin daukar raini, saidai kuma sam baya son hukunci cikin fushi, da wannan damar take amfani a yanzu take zuba iskancinta a gidan,  amma hakan bazaisa ta tafiba sai taga wacece matar tasa? dan kuwa tana zamanta a Abuja wajen sister ɗinta aka kirata ana sanar mata yayi aure, shiyyasa tazo lagos babu shiri, saidai kuma ita bataga matarba........

      Tunaninta ya katse ganin ya tashi zai koma dakisa, hartana kokarin taune harshe wajen azamar dakatar dashi,

        “Waini ko kana nufinma wannan abarce matar auren taka?”. Tai maganar da nuna Ummu.

        Cak ya tsaya, sai dai bai juyoba, bayason hasala kansa da yawane gudun karya karya yarinyarnan, amma tai wasa daga gidannan saidai a wuce da ita asibiti.

     Yunkurawa yay zai cigaba da tafiya tasha gabansa cikin tsantsar cika bakinsu Na yarabawa, “Ajiwa maganar nake, nace wacece matarka?”.

         Ɗan yatsansa yasa ya shafi girarsa da lumshe idanunsa ya bude a manta, “Bukky inaga kin manta wanene Ajiwa ko? Ina ɗaga miki kafane bisa wani dalilina.........”

       Saurin katseshi tayi, “Bana bukatar ɗaga kafarka Ajiwa, inkaga nabar gidannan sai ka sanarmin wace banzar yarinyace wanan ɗin?”.

          “Banza? Matar tawa ta aure kike kira banza?”.

         “heeeeey!! Matarka!!? A hakan!?, Wannan jinjirarce kake kira matarka a gabana Ajiwa? Lallai yau na sake tabbatar da halin hausawa, dama anfada min naki ji”.

       “Ko kina bukatar tabbatarwa ne Yoruba girl?”. 

     Wata banzar dariya ta tuntsure da ita tana kamo hannun Ummu zuwa gabansa,  ta fincike rigar Seawater din jikinta tana fadin, “kalleni da kyau banga abinda banfi wannan jaririyar yarinyarba da har bakinka ke iya kiranta matarka a gabana”.

          Raɓasu yay zai shige ɗaki batareda ya kalli ko ɗaya a cikinsuba “Kin makaro, dan abun ba'a jiki bane wawuya kawai”. Yay maganar tamkar bashine yayba.

      Hankaɗa Ummu tayi, tai baya kamar zata faɗi amma saita faɗo jikinsa.

     Tasss!! sukaji Saukar ƙarar mari a fuskar Bukky batareda kowa yaga ya akai yayishiba.

      Tuni gani dajin Bukky ya tsaya, yayinda falon yay tsitt saboda firgicin da suka shiga har A'i.

     Babu shiri Ummu da jikinta yahau mazari takuma shigewa jikinsa tare da ƙanƙamesa tamkar ita aka mara.

     Wutar kan Bukky data ɗauke na wucin gadi bata gama dawowa aikiba Amaan ya finciko Ummu datai shirin barin jikinsa zata gudu ya maidota ya matseta a kirjinsa tareda Dora bakinsa akan nata batareda tunanin komaiba.....

      “Eeeeeeehyyyyyy Me!!! Ajiwa!!!” Bukky tafaɗa cikin kwala ihu tareda buga wani uban tsalle ta zube ƙasa irin zaman ƴan bori.

    Daga canma A'i hannu ta aza bisa kai da fadin “Ni jikar Haƙilu, kajimin tantirin yaro zai kashemin sauran ganina”.

    Ihunsune ya fiddo Desmond daga kicin a guje, ya waro ido shima yana komawa da sauri ya labe bayan kofa yana wani mazari da jiki irinna iya shege ganin Boss da kansa yana cika aiki.

        Bukky dai saijuye-juye take a ƙasan tiles tana ɗora hannu aka da yarfarwa, ga hawaye na kwarara da majina a fuska, yayinda idonta yakasa daina kallon Yaa Amaan dake kissing ɗin Ummu a salon daya fara canjawa daga bata haushi zuwa wani yanayin daban, tun tanayi da yarabanci da turanci harta koma Igbo, catake Chiiii!!!, Chineke God woooooh!!!.....

      Oga Amaan dake shagulgula ai ko motsi baiyiba, tuni ma shi yabar duniyar dasu Bukky suke, ya lula sabuwar duniya dabai taba lekawaba a rayuwarsa sai a mafarki, Ummu kam da jikinta ke bari cikin tsantsar rudanin abinda batai zatoba, baikuma taba faruwa a kantaba sai hawaye takeyi, tsoronsa ya hanata yunkurin yin koda mitsi na nufin kwatar kai......

         Bukky ganinfa zata halaka akan bugun zuciya saitay Kansu ta fara jan Ummu daga jikinsa....

       Sai a lokacin Amaan ya dawo hayyacinsa,  hannu ɗaya yasa ya hankaɗa Bukky baya, kafin ya janye Ummukulsoom daga jikinsa itama yaykan Bukky yana fincike belt ɗin wandonsa, idonsa yay jajur duk farinnan ya bace, gashi sun wani zama kanana saboda tsantsar fusata.

     Ba Bukky da yake dukaba hatta da Ummu kuka take, A'i kanta jikinta yafara mazari...

     Desmond ma dayasan halinsa baƙaramin ruɗani ya shigaba, dan bai taɓa tunanin haukar bukky ɗin zai hasala boss irin hakaba yau.

         Dai-dai nan Attahir yashigo falon hannunsa dauke da briefcase ya kawoma Amaan daya manta a wajensa, kuma takardune masu amfani aciki, yasan zai iya nemesu a yanzuma saboda akansu aka turasu Abuja.

        Ihun dayake jiyowa tunkan ya shigo ya tada masa hankali, badai ƴar mutane Ajiwa kema wani abuba, har tuntuɓe yake wajen shigowa falon, turus ya tsaya ganin Bukky ce, sakin briefcase din yayi yay azamar shan gaban Amaan tareda ƙoƙarin riƙe belt ɗin hannunsa.

       Hankaɗe Attahir yay cikin daka tsawa yace, “kabarni na koyama wannan dabbar yarinyar hankali, yau saita faɗamin idan niɗin sa'antane dan ubanta”.

          Tsantsar fitina kawai Attahir ya karanto a idon Amaan, daƙyar ya riƙe belt ɗin daga hannunsa yana faɗin, “A'a Ajiwa Please, dan ALLAH kayi haƙuri kabarta haka, idan ita batada hankali kai kana dashi ai”.

         Amaan ya zubama Bukky harara da sakin belt ɗin da Attahir ya rike, ya nunata da yatsa cikin kakkausar murya da fushi yace, “yanzu kin kuma tabbatar dani din jinin hausawan ne? Kinkuma tabbatar da cewa itadin tafiki komai ko? Wawuya kawai, minti 3 kacal nabaki kibarmin gidana kafin naimiki abinda sai an kwasheki a Ambulance wlhy”. ‘yay maganar dakuma yin kanta tamkar zai sake duka, amma sai Attahir ya taresa da azama.

      Ƙwafa yay kawai ya fice daga falon.

      

      Kuka Bukky take tana faɗin saita halaka Ummu wlhy, yau saita ƙona Barrack ɗin gaba ɗaya sannan ta kashe kanta dashi kansa kowama ya rasa.

     Yanda take kuka haka Ummu ke kukan dabatasan daliliba, dan batajin abinda Bukky ke faɗa saboda da yarabanci takeyi.

      Da ƙyar Attahir ya fidda Bukky daga gidan, tanata rantsuwar saita halaka Ummu ayau tunda ta rabata da Amaan.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


*_KD_*


         Da sauri Suhailat ta fisge wayar hannunsa tana fadin Maci amana kai da wa?”.

         A matukar firgice Baseer dake rigin-gine ya juyo tareda wantsalowa daga gadon, muryarsa har zuga take wajen fadin “Banason shashanci Suhailat, Lukman n........”.

         Tuni takai wayar kunnenta, batareda ta saurareshiba, “Ai sainaji wace jakace kake waya?. Hello! Wace ƴar iskace ke mai waya da mijina”.

     Jin ba'a amsataba ne yasata saurin Ciro wayar daga kunnenta ta kalla, Ashe tama katse kiran wajen hanzarin amsa, sai dai kuma ganin ansa Lukman Dilau ne yasata sauke numfashi da maida kallonta ga Baseer daya hangame baki alamar ya sadakar tashi ta Kare.

      “Love sorry please, wlhy nazata da mace kake wayane”.

    Wata irin ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke jin ALLAH ya rufa masa asiri a karo Na biyu, yay azamar canja launin fuskarsa zuwa fishi, “Wlhy Love ban taba zaton waɗannan halayyar daga garekiba? Dama yardar da kikaimin kafin aure ta karyace?.......”

       Da sauri ta saka hannu ta rude masa baki tana faɗin, “Nacefa kayi hakuri Dan ALLAH”.

        Tureta yay yatashi irin a fusace ɗinnan yafito daga dakin, yayinda itakuma tabiyoshi da gudu tana kwala masa kira.

      Duk yanda taso ya saurareta yaƙi, saida ya garata son ransa sannan ya saurareta

      “Suhailat tsakanina da ALLAH bazan ɓoye mikiba nagaji, miyasa kika ɓoyemin halayenki ne kafin aurenmu? Wace irin rayuwar aure mukene tamkar kece mata nice miji?.......”

        “Laifinkane Baseer”.

 “Laifina kuma? Miyasa yazama laifina Suhailat?”.

        “Katashi kanema aiki, duk namijin dazai zauna gida mace ke masa komai duk soyayyar dake tsakaninsu dolene darajarsa ta zube, badan naci zarafinka na faɗaba, shawara na baka, saboda a yau anjefeni da gori akanka wanda ya sosa zuciyata, bakomaine ya jawo hakanba kuma sai soyayyarka dake raina, a kullum dangina kallo suke tsakanina dakai *Wutsiyar raƙumi tai nesa da ƙasa*, soyayyar danake maka nikuma ta hana idona ganin hakan, duk abinda kaga ina maka inayinsane dankasan ciwon kanka, nagama maka babban yaƙi tunda har muka mallaki juna matsayin miji da mata”.

      Baseer dake tunani da amsar maganarta hundred percent ya jinjina kansa, “Lallai gaskiya kika faɗa Suhailat, kuma na gamsu da jawabinki wlhy, nakuma miki alƙawarin kawo canji nan bada daɗewa ba”.

    Farin cikine ya kamata, dan tana sonsane tsakaninta ga ALLAH saɓanin shi daya saka taura biyu a bakinsa.

  

     Tun daga wannan zama sai rayuwar gidansu Baseer tafara canjawa, dan a washe garin da hakan tafaru ya shirya yaje ɗilau.

       Iyayensa sunyi mamakin ganinsa, amma sai babu wanda ya nuna hakan, suka shiga tambayarsa iyali.

        Ko kaɗan rashin hankalinsa bai barsa fahimtar iyayensa fushi suke dashiba, baimayi wani zaman minti talatin a gidanba yafice zuwa ƙauyen da malaminsa yake anan kusa da garinsu.

     Har yamma lis bai baro garinba, dan duk w

[1/28, 1:18 PM] 💞Noorinnissa💞: ani ƙula-ƙula saida ya tabbatar anyi akan Suhailat da mahaifinta dama duk ƴan uwanta sannan yataho.

    Dole a ɗilau ya kwana, washegari tunda farar safiya yafar garin tamkar korarre.


★★★★


      Ya iske Suhailat bata gida, dan ita babu tsarin tambayar fita agareta, hakan sai ya bashi damar yin ƴan binne-binnan sa da barbaɗe-barbaɗe.

       Ance tsafi gaskiyar maishi, to lallai Baseer ya gazgata hakan, dan kuwa yasamu yanda yakeso akan Suhailat da ahalinta, zuwa yanzu kam shike juya gidansa da ƙarfin iko na mazajen ƙwarai, yayinda tuni mahaifinta yabasa babban matsayi a kamfaninsa wanda kowa yay mamakin hakan, amma saninsa matsayin surukinsane mijin tilon ƴarsa sai babu wanda ya iya tankawa.

      Lallai duniya ta samu ga Baseer, yakuma cika da ƙara ƙyau, sai mulki yake zubama Suhailat, ga laulayin ciki data fara batareda ta shirya hakanba. Sai dai kuma koda wasa batai yunƙurin zubdawa ba, saboda tana son babynta.

     Haka tacigaba da karatunta ga laulayi, Baseer kam ya manta dawani cigaba da karatu, aganinsa duk abinda zaiyi karatun a kansa yariga ya samu, kasancewarsa mai kaifin basira saigashi yagama fahimtar abubuwa mafiya yawa na kamfanin daddyn Suhailat.

      Yakan zagaya ɗilau ya gaishesu lokaci-lokaci............✍🏻


NO. 18



..........Bayan Barin Bukky gidan Attahir yashiga neman inda Amaan yake, dan yasan yana cikin barrack ɗin babu inda yaje.

       Saida yaɗansha wahala kafin ya samoshi can wani waje inda babu kowa zaune a saman farar kujera idonu a lumshe ya ɗora ƙafafunsa a tebir ɗin gaban kujerar yana kaɗasu alamar har yanzu a sama yake can ƙololuwa, har Attahir ya iso wajen bai motsaba, dukda kuwa yaji motsinsa, kuma yanada tabbacin shine saboda wajen bama kowa ke zuwansa ba sai irinsu, shi kansa Attahir ɗin sanin idan ransa na a ɓace yafison waje mara hayaniya yas yay tunanin zuwa wajen dubashi.

      Tsawon mintuna uku yana tsaye akansa amma baida alamar nuna yasan da zuwan nasa.

    Attahir yaɗan girgiza kansa yana guntun murmushi, Ajiwa mai abin mamaki, ubangiji mai hikimane daya halicci bayinsa iri-iri mabanbanta halayya, da a labari akace masa akwai masu irin kalar halin Ajiwa saiya ƙaryata, saboda baitaɓa ganin mutum miskili mai zuciya irinsa ba, ko mahaifinsa da ake ganin taurinsa Ajiwa ya takashi ya shanye.......

      “Malam ka tashimin aka”. 

       Murmushi Attahir yay yanajan kujera shima ya zauna, ”Oh dama kasan da zuwan nawa amma ka shareni?”.

     Banza Amaan yay masa yaƙi bashi amsa. Sai dai hakan bai damu Attahir ba, saima numfashi daya sauke yana kuma kallonsa sosai, “Ajiwa miyasa ka daki Bukky? Bayan na sanka da tsanar wannan halayyar ta dukan mace?”.

      Shiru yay tamkar bazai tankaba yanzuma, harma Attahir ɗin ya fidda tsammani sai yaga ya buɗe idonsa dasukai jazur akansa.

    Kallo ɗaya yayma Attahir ɗin ya maidasu ya rufe, sai da yaja wasu seconds kafin yace, “Miyasa baka tambayeta ba ita?”.

      “Kasan bazata faɗamin gaskiya ba ai, ni namayi mamakin ganinta  musamman idan na tuna irin rabuwar da kukayi”.

      Nanma shiru bai tankaba, shima kuma Attahir ɗin bai sake maganaba har tsawon wani lokaci, saikuma ya cigaba da faɗin, “Ajiwa Bukky ba karamin so take makaba wlhy, ni dama nasan dawuya ta iya rabuwa dakai, wancan lokacinma fushin da tayine yasata nisantarka, mizai hana kawai ka cire komai a ranka ka aureta kodan gudun karta cutar da matarka ta hanyar da bamu zataba”.

      Cikeda wata irin fusata ya buɗe idonsa akan Attahir, “Amma bakada hankali, Attahir harkai kake faɗamin na auri yarinyar data nemi yimin fyaɗe, tadawo tana roƙona akan nai divergent ɗinta babu igiyar aure a tsakanina da ita saboda ita dabbace karya. Idan wannan maganar banzarce ta kawoka wajen tashi barnan”.

      “Yi haƙuri nabar maganar, to amma miyasa ita Ummukulsoom bazaka karɓeta a matsayin mataba kamar yanda ka karɓa a gaban Dad”.

     Wata banzar harara yaa Amaan ya zubama Attahir yana jan tsaki, kafin yamiƙe da nufin bar masa wajen. Saurin riƙosa Attahir yayi yana faɗin “Ajiwa ka tsaya muyi magana mana”.

      “Dalla malam sakeni, nakula yau hankalinka baya cikin kanka”.

      “Ni wlhy garau nake, kaima kuma kasani tunda ba shaye-shaye kataɓa gani inaiba, nakan rasa gane halinka wani lokacin wlhy Ajiwa, halayyar Bukky yasaka jin bazaka aureta ba dukda ɗumbin son da take maka, tun kana shareta harka karɓeta, yanzu kuma yarinyar nan da Dad ya aura maka ni banga aibunta ba, kanada damar ɗorata aduk makarantar da kakeso inma kasancewarta ƙaramane batai makaba ko rashin zurfin ilimi, kaga nanda shekara biyu zuwa uku sai kaga anwuce wajen tamaka yanda kake buƙata, dan girman ƴa mace baida wahala musamman idan tanasamun kulawa mai ƙyau da kwanciyar hankali, wlhy kai kanka idan ka kusanta zamanka da mace zaka rage wannan baƙar zuciyar taka, kasamu nutsuwa fiye da zatonka, ka kai age ɗin da kake buƙatar mace ƙololuwa, amma kake azabtar da kanka akan wani ra'ayi naka mara dalili......”

      Fisge jikinsa yayi tareda jan tsaki da harar Attahir ɗin yana faɗin, “Banza kawai, kai yaushe nataɓa cemaka ina buƙatar macen? To bana sonta kuma bataiminba, amincewa Dad dakake magana kuma kaima kasan bana taɓa jayayya dashi, karɓa daban, hakama amincewa daban, karka sake sakomin yarinyarnan a shirmenka”.

      “Idan baka amince da itaba miyasa ka daki Bukky akanta yau?”.

     “Shaƙeni na faɗa maka mana”. Yana gama faɗa ya canja wajen zama zuwacan nesa da Attahir.

     Dariya Attahir yayi yana binsa da kallo, a fili yace, “Ajiwa kana raina wacece mace, namaka alƙawarin inhar ina cikin masu tsawon rai saina sakaka kaso zaɓin Dad fiyeda tunanin duk wanda ya sanka, kwanannan zamu fara wasan kuma”.


       Shidai Amaan baisan alwashin da Attahir ke dauka a kansaba, dukda kuwa yaji dariyar da yayi da buga table alamar tabbatar da alwashinsa.

       Attahir bai bisaba, sai waya daya ɗauka yakira Abbas akan ya sanarma Desmond yabashi ya kawowa Amaan ɗin abinci inda suke, danya fahimci baici abinciba.


★★

     Koda Attahir ya fita da Bukky sai Ummu ma tanufi ɗakinta tana sharar ƙwalla, itafa harga ALLAH tausayi Bukky tabata, sannan tana son sanin mike tsakaninsu haka?.

      Kwanciyarta ta gyara akan gadon zuciyarta nakuma tsorata da lamarinsa, yanzukam taƙara fahimtar miyasa ƙannensa ke shakkarsa, idan har zai iya buɗe ƙwanji ya lakaɗama budurwa da suke soyayya duka irin haka inaga ƙannensa ko ita da aka cusamawa akan dole?.

      Laɓɓanta ta shafa da tuna abinda yay mata, wani abu takeji na sauka a zuciyarta mai kama da shakku da tsoro, tasan yayi hakanne dukdan yabama baƙuwarsa haushi, amma harga ALLAH batai zatoba. “Ya ALLAH kasaka sanyi da salama a zuciyar mutuminnan, idan har a haka zanyi rayuwa dashi nashiga uku kenan wlhy” ‘tai maganar tana sharce hawayen dake gangaroma fuskarta’.

     Har yamma takasa fitowa, salla kawai ke tashinta da tayi sai ta koma ta kwanta, koda wasa bata fatan haɗuwarsu, dan yau abu biyune a tsakaninsu, kunya da tsantsar tsoronsa.


       A'i kanta wannan lamari ya firgitata, yo ashe Alhaji Mahmud ga babban magaji daya zartasa nan, wannan jarababben yaron ai zai iya halaka mutum idan ya shigar masa hanci, itako ina ita ina kawo Aina'u wannan gidan, yanda take da shegen rawar kantanan yaje ya halaka mata ɗiya, to amma kuma harga ALLAH fa burinta na ƴarta ta auresa yana nan zaune daram a ranta, dan dama a kullum burinta ƴarta ta auri miji na kece raini kamar yanda ƴar kishiyarta ta aura, to ga damar kuma tasamu sai dai wannan jarababben mutum haɗa inuwa dashi  haɗarine.......

    Wayarta datai ring ce ta dawo da ita hayyacinta, ganin Momcy ce saita ɗauka da hanzarinta. Cike da girmamawa ta gaidata.

    Daga can Momcy tace, ”A'i yau najiki shirune, bayan kuma Fodio yacemin yadawo tun ɗazun”.

     “Ki gafarceni hajiya, ai yau abin faɗarne akwai ban takaici wlhy....”

    Cikin katseta Momcy tace, “baruwanki da takaicinsa, kamar yanda na faɗa miki koma miye akayi ki sanarmin”.

    “ALLAH ya huci zuciyarki to, dama dai watace tazo bayan dawowarsa...........”

    Tsaf ta kwashe komai ta sanarma Momcy hatta da kissing ɗin Ummukulsoom da kaɗan ya hana zuciyar Momcy bugawa, tashiga zabga masifa akan dolene tasaka Fodio sakin Ummu kwanannan, dan wlhy baza'a haifa mata jika daga tsatson ƴar aikiba kuma ƴar ƙauye, ai garama ya auri Bukky ɗin koba komai ɗiyar manyace mai aji da ƴanci.....

           Ummayya da Aneesa da suka shigo suka isketa suka shiga tambayarta, jin abinda ya farune sai suka shiga tunzurata suma suna cewa asiri Ummu taima yayansu, taya za'ai wannan ƙazamar yarinyar harta birgesa yace zaiyi mata kiss?. Ummayya harda ƙaƙaro amai wai ƙyaƙyamin haɗa baki da yayansu yay da Ummu.

      Suma kansu da ba'ai a gabansuba gulmar A'i tasakasu yini da takaici, gashi Momcy nata kiran yaa Amaan yaki ya ɗaga.



ALLAH ya rabamu da sa kai a uku.

⛹‍♀⛹‍♀, surukai da dangin miji kuma kanku faɗa akan sakama ƴaƴanku ido da matansu, babu abinda ke janyowa sai hana sukunin zukata wlhy.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


          Yayinda Suhailat ke fama da karatu da laulayin ciki, Baseer nacan soyayya tai ƙarfi tsakaninsa da Lubna, sam Suhailat batasan mike faruwa ba, koda ta sani a yanzu batada wata fawa ɗin ɗaukar mataki, dankuwa asirin da yay mata yay masifar yin tasiri a jikinta, saboda sakacin addu'a dayin ibada akan lokacinta, ga azabar laulayima dake addabarta, sauƙintama ƴan aiki daya kawo ya tile a gidan, wanda ba son zamansu takeba saboda kishinsa, sai dai batada baki yin magana a halin yanzu.   

         Maganar Baseer hartaje gidansu Lubna, nanfa saiya ƙara haukacewa saboda ganin mahaifin Lubna yafi na Suhailat kuɗi nesa ba kusaba, gidan da sukema kawai abin kallone, dan wata duniyace guda mai zaman kanta.

      Dayake saida yayma Lubna da mahaifinta shiri na musamman sai babu wata jayyaya family ɗinta suka karɓesa hannu biyu,  dukda sun tabbatar sun fisa komai na game da dukiya da alfarma.

        *Alhaji Wada barma* ya bama Baseer damar turo iyayensa, dan acewarsa so yake ya aurar da Lubna kasancewar ta kammala karatunta, shikuma mutumne dake riƙo da aƙida tasa, da ƙyarma ya amince Lubna tafara jami'a a gida, sauran yayyenta duk iyarsu secondary yay musu aure, agidajensu suka cigaba da karatunsu.

        Sai da ya gama tanadar iyayensa na bogi kamar aurensa na farko sannan ya shirya yaje ɗilau ya sanar musu zai ƙara aure.

    Tsantsar mamaki ne da al'ajab suka bayyana a fuskar iyayensa da ƴar uwarsa talatuwa, baba yashiga masa faɗa akan hakan, dan aganinsa yin fushi da Basiru yanzu ba nasu bane, garama sujawosa a jiki da masa nasiha ƙila ya dawo hayyacinsa.

    Tsare-tsaren gaskiya da ƙarya ya zauna yayta musu har suka amince, tareda masa addu'ar fatan alkairi, ba komai yasa sukai hakanba sai masa talala akan canja salon dawo dashi hanya idan yanada rabon hakan.

      A wannan karon iyayensa bama suje ɗaurin aurenba, dan kaf garin ɗilau bayansu babuma wanda yasan Basirun zaiyi aure, su baba sunƙi sanarma kowa.

     

      Ba tareda Suhailat tasan komaiba aka shiga shagalin bikin Baseer da amaryarsa Lubna.

     Abinda Suhailat kawai ta lura dashi shine canja mata daya farayi, datai magana kuma ya hau kanta da masifa dacewar shifa babu lallai babu tilas saisu rabu.

     Baƙaramar girgizata zancen rabuwarnan tasu yakeba. Tun tana ɗaukar lamarin wasa harya fara taɓa rayuwarta. Shiko ko'a jikinsa, dan ta amaryarsa Lubna yake.

     Haka akasha bikinsa da Lubna, tareda raƙwashewa da ƙwallewa batareda dangin Suhailat ko ɗaya ya saniba, abokansa na su Najeeb kansu abun basu saniba tunda a kano amarya take.

       Dama tun ana saura sati a ɗaura aurenne Baseer yayma Suhailat ƙaryar zaije lagos wani aiki daya shafi kamfani, amma ko daddynta bayason ya sani har sai ya kammala.

     Son da take masane yasata aminta dashi, tai masa addu'ar dawowa lafiya harda rakkiya zuwa mota dukda tana fama da kanta kuwa.

       Koda yabaro gidan saiya hau tuntsura dariya da faɗin “Kai anya a duniya akwai wawaye irin mata kuwa? Da anyi magana suce sun fika wayo, to shidai baiga wayonba, dan gasu yana garawa tamkar sitiyarin motarsa a hannu, shiko lallai ƙyau yamasa rana, dan gashi yazama jarin tara dukiya ta hanya mai sauƙi batareda shan wahala ba” wata dariya yakuma bushewa da ita “Lubna kema kin shigo tarkon Baseer, ALLAH ya kawo wata mai tsautsayin a next target”.

     Harya ƙarasa kano aranar yanata haukarsa a mota shikaɗai.


    Bayan biki aka kai masa amaryarsa gidansa daya saya da kuɗin Daddyn Suhailat.



⛹‍♀⛹‍♀Humm su Baseer samarin shaho.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


             Hankalin mahaifiyar Bukky ya matuƙar tashi saboda a yanda ta dawo gida.

       A ruɗe suka shiga tambayarta abinda ya sameta?.

     Tsaf ta zauna ta zayyane musu komai akan auren Amaan da dukanta dayay akan matarsa.

      Cikeda masifa yayanta ya miƙe, “Yanzu kingane mi muke sanar miki akan halin Hausawa, kin zauna kin mutu akan akansa saikace shine kaɗai namiji a duniya, idan ƙyawunsa ke ruɗarki acikin yarenmu akwai waɗanda suka fishi komai, idan dan yana sojane akwai waɗanda suka fisa komai a gidan soja wanda Dady zai iya samo miki, ƙilama asiri yay miki, dan hausawan nan sun iyayi dama, mutanen da babu abinda suka iya sai auren mata suna sakinsu........”

     “Bolaji ya isheka haka, ƴar uwarka nacikin damuwa maimakon ka taimaketa saikaita cimata mutunci?”.

     “Niba mutuncinta nake ciba Mom, gaskiya nake faɗa mata tunda ita takasa ganowa kanta”.

      “To anji, jeka kawai”.

 Baki ya taɓe ya fice daga falon haushin ƴar uwarsa nacinsa a rai, shi dama can yatsani wancan guy ɗin, dan ƙiri-ƙiri aka hanashi wani gurbi a gidan soja saboda shi.

 

     Yana fita Maman Bukky ta kalleta tana faɗin “Kinga dear bar Bolaji kinji, indai har akan Amaan ne bar zubar da hawayenki, dagashi har matar tasa zasu gane kuransu, kamar yanda bai aurekiba itama bazai zauna da itaba”.

    “Mom da gaske kike?”.

  “Yes dear da gaske nakeyi, daddynku ma yana dawowa zan sanar masa komai, nasan zai ɗauki mataki a wannan karon, dama kece kika hana a faɗa masa abinda yay miki wancan lokacin, amma a wannan time ɗin tunda haukarsu na sojoji ya ɗebesa harya dakeki saiyayi dana sani kuwa”.

      Rungumeta Bukky tayi tana dariyar jin daɗi, “Nagode mommyna, shiyyasa nake sonki, komi ranki yabaki kima shegiyar matarsa, nikuma inason ya mutu akan sona duk abinda yamin harna baya saina ramashi”.

      “Duk za'ai masa, gobenan zanje wajen babalawo na Obada”.

    Daɗi sosai ya kama Bukky hardasu rawa, dan tatsani Ummu sosai a ranta, dama saboda ƴar yarinyarnan yaketa mata wulaƙanci ashe tuni, ai yanzu kam saiya zauna da ita tagani.



🙍🏾😟


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


       Yaa Amaan bai dawo gidanba sai kusan 10 na dare, babu kowa a falon sai tv da keta aiki, daga A'i har Ummukulsoom tsoro ya hanasu fitowa, abincin darema sai ɗiba Desmond yay yakai mata ɗaki.


     Wayarsa daya manta a falon ya ɗauka a saman table ɗin dake gefen kujerar, babu wanda ya motsata duk da ya lura an sake gyara falon, a falon ya zauna yana danna wayar, kira yagani rututu a kuma duk na Momcy yafi yawa, daga ƙarshe yaga harda saƙonta.

     Cikin dafe kai ya buɗe massege ɗin nata.


      _Fodio nakiraka kaƙi ɗagamin waya saboda ka maidani ƙawarka ko?, kokuma mace ta rufe maka ido._


       Rumtse idonsa yayi sosai, zuciyarsa na wani bugawa da sauri-sauri saboda ƙarin wani sabon ɓacin rai da yaji, harma shi Momcy kecema mace ta tsonema ido, yaushe yarinyar takai ajin zama mace dahar zata makantar dashi su, datasan yanda ya tsani aurennan ma da ko a mafarki bazatai wannan tunaninba, ya karɓetane saboda bazai taɓa iya jayayya da mahaifinsa ba, zamanta kuwa a gidan akwai gaɓar da yake jira ta barsa, dan a tsarinsa bayason auren ƙaramar yarinyar dako 20years bata cikaba, haba wannan ai solon jan rainine, ya zauna da sa'ar ƙaninsa Bassam matsayin matar da zata iya ganin ƙarshen girmansa, ko a mafarki baya fatan wannan mummunan al'amarin. tsakaninsa da ita *Wutsiyar raƙumi tai nesa da ƙasa* wlhy.

      Wani takaici yakuma taso masa saboda tuna abinda yay mata ɗazu a dalilin waccan jakar yarinyar Bukky, saidaga baya yamafi jin zafin kissing ɗinta da yayi akan haukarda Bukky tazo tai masa a gidan.........✍🏻



NO. 19



...........Ƙiri-ƙiri haɗuwa a tsakaninsu tayi wahala tsawon kwana biyu, dan ko motsinsa taji bata fita falon, akwana biyunnan kuma a gida yake kusan yini, shiyyasa daga ita har A'i babu mai sukunin zuwa zaman falon, kowa da nasa dalili, garama A'i takanyi asubancin fitowa ta gyara ko ina dukdan gudun karsu haɗu, sai dai fa yini take leƙensa ta Window idan yana zaune a falon.

          Wannan takura kantan da tayi saiya haddasa mata yawan tunani da kewar gida mai tsanani, kaɗan-kaɗan saikaga tana share hawaye, ga maman Ahmad shiru bata shigo gidanba.

     Kwana uku suna wannan ƴar wasan ɓoyar, ana huɗune ta fiskanci kamar babu motsinsa a gidan har yamma.

     Bata tambayi Desmond ba, dukda kuwa yana kawo mata abinci da lokacin cinsa yayi.


      A'i ce taɗan fara walwala a gidan data fahimci yayi tafiya, a ha kali saita ringa jawo hankalin Ummu ma, dukda kuwa badan ALLAH take hakanba, dan kawai bin ƙwanƙwanton tane takaima Momcy gulma ta waya.

     Da yamma suna zaune a falon suna kallo saiga Maman Ahmad, sosai taji daɗin ganinta, da cewa tayi fushi.

    Dariya Maman Ahmad tayi tana kwantar da Ahmad dayay barci, “Ayi haƙuri amaryarmu, kinsan jiki da jini, ga makaranta muna Exam”.

        “ALLAH sarki, ashe karatu kikeyi?”.

    “Wlhy kuwa amarya muna ɗan taɓawa, kema ai kamata ma yay ki koma makarantar”.

    Murmushi Ummu tayi kawai, aranta tana tunani wanene zai biya mata kuɗin makaranta itako, to koma takardunta bata karɓoba balle.

     Sun cigaba da firarsu har zuwa yamma, a cikin firarne Ummu kejin wai Amaan ashe yana Yobe state ne shida Attahir, abin ya matuƙar bata mamaki, amma sai bata nunama maman Ahmad bata saniba, dankuwa ta tuna da gargaɗin Gwaggo hinde akan riƙe sirrin miji koda ace ƙuntata maka yakeyi.


*BAYAN SATI BIYU*


         Satin su yaa Amaan biyu a barno suka dawo, lokacin Ummu na falo kwance barci yaɗan figeta, A'i ma uwar gulma tana kicin wajen desmond suna hirar kurame, acewarsa yana koyan hausa, itama tana koyan turanci😆.

        Da sallama ciki-ciki ya shigo falon, ƙal yake da tsafta tamkar yanda yake buƙatar ganin kayansa, ga ƙamshin turare mai daɗi yana tashi.

     Batareda ya lura Ummu dake kwanceba ya zauna a falon yana sauke numfashin gajiya tareda kallon agogon fata dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa, ya kuma furzo huci tareda kwantar da kansa jikin kujera yana lumshe manyan idanunsa dake cike da gajiya. Kusan minti huɗu yana a haka, sai dariyar su Desmond dayake jiyowa sama-sama, idonsa ya buɗe a hankali sai suka sauka akan Ummu dake kwance tana barci hankalinta kwance.

        Duk yanda yaso janyewa saiya kasa, saima kallonta daya farayi tundaga ƙyaƙyƙyawar fuskarta zuwa matashin ƙirjinta, baki ya taɓe tareda cigaba da binta da kallo daki-daki. Cike da takaici ya sake maida idanun ya rufe, yama za'ai ace wannan ƙwailar yarinyarce matarsa, yaushema ta gama zama mace dahar ake tunanin dacewarsu?, ƴar ƙibarma daya lura tana da itace ta taimaketa, amma da siririyace da baƙaramar ƙwaila za'aiba a wajen, a ƙyawun fuska kam ya yarda tanadashi bakin gwargwadon iko, hakama kalar fatarta babu laifi, ƙirjinne dai babu alamar abun arziƙi, dolenema yasan abunyi game da wannan yarinyar kam, yanason bi ta hanyar da bazai ɓatama Dad raiba ya rabu da ita, Momcy kam dama kullum fatanta da gargaɗinta akansa kenan.

     Yakai mintuna talatin a falon kafin ya miƙe da nufin ƙarasawa ɗaki yaɗan huta.

        Duk basusan da dawowarsa gidanba saida yafito zashi sallar magriba, mamaki duk saida ya kamasu, desmond ya zube ƙasa yana bashi haƙuri akan baisan ya dawo baneba.

    Hannu ya ɗaga masa, murya can a ƙasan maƙoshi yace, “Haɗamin wani abu nayi azumine”.

    Bai jira cewarsaba ya sa kai ya fice abinsa.

    A'i dake bayansu a ranta tace, ba dole kai azumiba kasamu bakin ƴar mutane ka taune ranar.

        A fili kuwa sai jaddada masa barka da dawowa take yaƙi ko kallonta, sai hannu daya ɗaga mata kawai ya ida ficewarsa.

     Ummu naɗanjin motsinsu daga ɗaki, amma taƙi fitowa, ko kaɗan bamata sha'awar haɗuwarsu ita kam.

         Koda ya dawo sallama a falo ya zauna yay buɗa baki, amma baiga gilmawar yarinyar dako sunanta bai riƙeba shikam, hakan bai damesaba, dan aganinsa lafiya ke ɓuya. Sallar isha'i kawai ta tadashi, daya dawoma falon ya cigaba da zama har kusan 10:30pm, kafin ya tattara inasa-inasa yay ciki.


        Washe garima harya fita wajen aiki baiji motsin Ummu ba, saikuma abun yaɗan tsaya masa arai, baya fatan aikata abunda mahaifinsa zaiyi fushi dashi, karya zam yarinyar ko batada lafiyane?. Hardai yadawo gidan kusan 11 na dare abin na a ransa, hakanne yasashi nufar ɗakinta kai tsaye, dan gidan yayi tsitt babu motsin kowa, alamar sunyi barci.

     Tsaye yay yana tunanin idanma yashiga mizaice ya kawoshi?, amatsayinta na ƙaramarsa bata fito ta gaisheshiba dukda yasan taji motsin dawowarsa sai shine ma zai nemeta. Siririn tsaki yaja tareda lumshe idonsa ya buɗe yana shafar girarsa, harya juya zaibar ƙofar saikuma yakuma dawowa yana jan wani tsakin.

    Handle ɗin ƙofar ya murɗa tareda leƙa kansa, tsakkiyar gadon ya hangota kwance cikin doguwar riga ruwan madara, ya ɗan sauke ajiyar zuciya tareda jan ƙofar ya rufe mata bayan ya fito.

     Duk abinda yake Ummu na kallonsa, dan idonta biyu, da farkoma tsoro taji, amma ganin shine saita koma mamakin miya kawosa? Ganin bai maganaba ta maida idonta ta rufe da cigaba da tunaninta na nemawa rayuwarta mafita.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

   

           Baban Bukky na dawowa mamanta ta sanar masa komai.

    Murmushi yayi yana gyara zama cikin harshen yarabanci yake faɗin, “Babu wani babalawo dazakuje wajensa, kubarni dashi, dan akwai harƙalla a tsakaninmu, dama yaron yana neman wargaza mana wani aiki dukda kasancewarmu a samansa, lallai inada tabbacin da biyu ya dakarmin yarinya, sai dai wannan shine kuskure mafi girma daya tafka a rayuwarsa”.

        Dukda bataso ya dakatar dasuba taji daɗin nuna fishinsa akan hakan, takumasan zai ɗauki mataki kamar yanda ya faɗa.

     Bukky ma dake laɓe tana saurarensu ta gamsu takumaji daɗi, sai daifa ita sam ba Amaan kawai takeso ya ɗanɗana kuɗarsaba harda matarsa, dan haka ta yanke shawarar zuwa ita kaɗai wajen babalawo ɗin batareda iyayenta sun saniba.


  ★★★★


      Washe garikam batareda sanin kowaba a gidan ƙawarta Amo tai mata rakkiya wani ƙauye wajen bokanta.

    Dukkan bayani daya dace tai masa akan baƙar muguntar da takeson aima Ummu.

       Ƴan bincike-bincikensa na bokaye yayi kafin ya ɗago ya kalleta, “Madam maganar gaskiya yarinyarfa akwai tsari jikinta tunma tana ƙarama kakanta yayi, dan alamu sun nuna dukkan zuri'ar mahaifiyarta suna tare da wannan tsarin a jikinsu, kowanne asiri bazai kamasuba sai dai ƙaddarar ALLAH da babu mai gogeta a kundin mutum”.

      Cike da damuwa da takaici Bukky tace, “Yanzu kana nufin koma mizan mata bazai yuwuba kenan?”.

     “Gaskiya bazai yuwuba, sai dai ki bani dama zan sake binciken wata hanyar, nanda wani lokaci saiki dawo”.

     Godiya tai masa suka taso suka dawo, Amo nata kuma tunzurata, harda cewa zataje taga matar ta Ajiwa.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


     Ɓangaren Momcy ma hankalinta yakasa kwanciya gaba ɗaya, burinta kawai tayaya zata raba auren Ummu da Amaan, amma sam ta rasa, gashi kullum cikin lasar takobin hakan take.

    Duk da Alhaji Mahmud na lure da ita bai taɓa maganaba, baima kuma nuna mata yasan anaiba.


★★★★


      Haka dai rayuwar taci gaba da tafiya yau da daɗi gobe sai haƙuri, a zaman Ummukulsoom da Yaa Amaan babu wani canji, danba harkarta yake shigaba, hasalima baya haɗa sati guda a jere yana gidan, yanayin yawan tafiye-tafiye wanda Ummu batasan ina yake zuwa ba dan ko sallama sai randa ya gadama yake musu, wani lokacin kuwa sai dai taji a bakin desmond ko maman Ahmad.

    A kwana a tashi aurensu yashiga watanni shida dayi, har yanzu kuma A'i uwar gulma nakai rahoto wa Momcy.

      Yayinda itakuma take ƙarajin tsanar zaman Ummu da ɗanta tareda neman hanyar rabasu cikin sauƙi.

    Taso su Ummayya suje legas amma Dad ya hana ƙiri da muzu.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


        Ɓangaren haji Baseer ma dai a wajensa komai yana tafiya yanda yakeso, yasha amarcinsa da Lubna yanda ya kamata, yayinda ita kuma take masa biyya fiyema da zatonsa.

    Hakanne yasakashi kuma jin Suhailat fita a ransa, dan haka yashiga mata salon wulaƙanci kala-kala.

    Tun Suhailat bata fahimci komaiba harta fahimta, saboda yawan tafiye-tafiye da yakeyi, tun tana dannewa hardai ta tambayi Daddynta ko Baseer yanayine a ƙarƙashin company? Daddy ta yace ko kusa ba haka baneba, shi kansa baisan ina Baseer ɗin yake yawan zuwaba, dan a duk sanda zaiyi tafiya cemasa yake yaje ɗilau gaida iyaye sa.

        Sosai hankalin Suhailat yay mugun tashi, tashiga bin ƙwaƙwƙwafin Baseer, daga ƙarshe tagano ashe aure yay basu saniba, harma amarya nada ciki ƙarami.

     Ai a wannan dawowa dayay tsiya ta ɓarke tsakaninsa da Suhailat, wadda takaiga ya shashsheƙa mata mari ga tsohon ciki. 

       Tako dage ta rama marin dayay mata, nanfa suka harƙume dukan juna saboda bashida hankali, tsautsayi ya sakashi doke ɗan cikin nata tako zube a wajen tana kuka.

    Shikuma a fusace yake faɗin, “Ya saketa saki uku, kuma ALLAH ya isa tsakaninsa da ita”.

      A wannan lokacin Suhailat batashi takeba kam, ta azabar datake ciki take, ga jini yafara zuba mata.

     Hankalin ƴan aikinta yatashi matuƙa, kukun gidan yakira Mahaifinta ya sanar masa.

   

     Lokacin da mahaifin Suhailat sukazo gidan tadaɗe da fita hayyacinta saboda jini dake zuba. Basubi takan komaiba suka kwashe zuwa asibiti.

         Suhailat tasha wahala sosai kam, aranar kuma ta haihu bakwaini, yaron ko awa ɗaya baiyiba ya rasu.

    Tsinuwa dai kam Baseer ya shata ga dangin Suhailat, saidai koma ƙeyarsa basu ganiba, dan aranar da abun ya faru aranar yabar kaduna zuwa ɗilau,  ya kwashe Inna da baba wai zai kaisu zaria, aiko ya gudo kano dasu tareda canja layin da dangin Suhailat suka sanshi dashi.

     Sudai su baba sunmasa tambayar duniya yaƙi faɗi musu gaskiyar abinda ya faru, sai ƙarya daya zauna ya tsara musu akan wai wasune suke son cutar dashi, idan kuma basu samesaba su zasu nema ai.

      Hankalin baba ya matuƙar tashi, dan bayason tashin hankali shikam, shiyyasa lamarin basiru ke bashi tsoro sosai, yaron bayajin magana ko kusa ko kaɗan, dan sudai shine jarabawarsu.


    Kamarko basiru ya sani ya gudu dasu baba, dan koda mahaifin Suhailat yasa aka nemeshi bashi a kaduna saiya tura ƴan sanda su kama iyayensa, yasan hakan zaisashi zuwa da kansa ai dole, sai dai kuma sunje babu su Inna a ɗilau, kowa yakance baisan ina sukajeba, dan ko talatuwa ƴarsu batasan da tafiyar yasuba, dayakema ba'a ɗilau take aureba, tanacan wani gari a katsina.

     Mahaifin Suhailat yay alwashi nemo Baseer aduk inda yake, amma sai Suhailat ta dakatar dashi ta hanyar cewa ya barsa, dakanta zatai wannan ramuwar, kamar yanda ya yaudareta ta hanyar zanba itama ta hanya mai sauƙi zata ladabtar dashi, duk da tasan itama akwai kuskurenta na bijirema iyayenta, tun farko sun nuna basaso amma ta dage saishi saboda soyayya ta rufe idonta bataji bata gani.

       Sosai take roƙonsu gafara bisa hakan. cikin tausaya mata suka yafe mata, tareda mata gargaɗin ta kiyaye gaba.

    Murmushi kawai tayi mai ciwo, dan ita zuwa yanzu ko ba'a bata shawaraba ita maibama kantace, ba soyayyaba ko mazama basa burgeta zuwa yanzu, dan duk tamusu kuɗin goro akan yaudara.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


           Tun Baseer na tsorace da nemansa da yasan mahaifin Suhailat zai iya yi harya sami nutsuwa ganin shiru, bayan lafawar komai yabar su baba suka koma ɗilau saboda takurawar da sukayi akan sabawa da sukai da can ɗin.

       Shiko saiya cigaba da rayuwarsa da gimbiya Lubna cikin soyayya da amincin datai masa har ranta........✍🏻


NO.  20



...........Haka rayuwar taci gaba da tafiya a gidan nasu Ummu, babu mai shiga harkar wani tsakaninta da Yaa Amaan, iyakaci randa suka haɗu ta gaisheshi, idan ya gadama ya amsa koya ɗaga mata hannu yay gaba, idan basu haɗuba kuwa ko oho, baruwansa da tanada lafiya ko akasin hakan.

     Abin na damunta matuƙa, ga kewar ahalinta da a kullu yaumin take a ciki, sai dai batada wata hanyar jinsu koda a wayane, dan batada number ɗin kowa, idanma tana dashi ina waya?, dama wannan rayuwar ta gudarma kanta tun farko, amma sai Baba ya kasa fahimtarta, tayaya ɗan gayu ɗan boko ɗan manyan mutane irin Yaa Amaan zai so ƴar ƙauye irinta, mai karatu iya secondary school? Bayan ƴaƴan manyanma dake amsa sunan ƙwarya tabi ƙwarya a tsakaninsu basu isheshi ko kalloba saboda tsabar murɗin hali, to bare ita kuma karan kaɗa miya, Inhar Baseer da suka rayu tare a gari ɗaya, matsayi ɗaya, zai gujeta bayan ALLAH yay masa wani nasibi to lallai kuwa ɗan gayu kamar Amaan bazai taɓa ya sota ba.

       Waɗannan tunanin sune suka zame mata abokan rayuwa, sai A'i dake jin daɗin halin da take ganin Ummu ɗin itada uwar ɗakinta Momcy, idan kaga walwalar Ummu to maman Ahmad ce tazo gidan, dan bata wani sakama desmond sosai, shi kansa yana girmamata tamakar yanda yake girmama wanda ya ajiyeta, dukda kuwa ya girmeta sosai.


★★★★


     Yau ta kasance laraba, haka kawai Ummu ta tashi zuciyarta babu daɗi, ga damuwa irinta kewa. Zaman ɗakinne ya isheta yau dai tafito harabar gidan dantasha iska, sanye take da doguwar riga ta atanfa, saboda ƴar ramar datai sai rigar tai mata burun-burun, saɓanin da datake cikata fam.

       Tayi nisa sosai a tunani har motarsa tashigo bata saniba, tunda suka shigo a kanta ya sauke manyan idanunsa, gajeran tsaki yaja kafin ya fito bayan Osin ya buɗe masa motar, shifa inma ba ganinta yayba mantawa yake da ita a gidan, garama idan yaga tsohuwar da suke tare wadda sam matar batai masaba ne yakan tuna da akwai mace matar aurensa wai a gidan.

           Sanye yake cikin kakin sojoji, sun masa ƙyau sosai dukda babu hula a kansa, fuskarnan tam babu alamun fara'a, tamkarma yana tare da damuwa.

       Takunsane ya ankarar da Ummukulsoom da batasan da shigowar tasaba, tai azamar ɗago kanta tareda sauke idanunta a kansa batareda ta shiryaba.

    Ba ƙaramar faɗuwa gabanta yayiba ganin ya kafeta da mayun idanunsa yana mata kallon sama da ƙasa, tamkar munafuka haka ta taso ta nufoshi tana masa sannu da zuwa, kallo ɗaya zakai mata ka fahimci kamar a firgicema take.

    Bai ko amsaba yay gaba abinsa yana sakin wani siririn tsakin ƙasan maƙoshi, hakan saiya kuma sanyaya jikin Ummu har hawaye na cika idanunta.


      Koda yashiga bai zauna a falonba, ya zube saman lafiyayyen gadonsa yana sauke wani nannauyan numfashi, dolenema yabi shawarar mahaifiyarsa koma yace Umarninta, anzo gaɓar da dolene sai yarinyarcan tabar gidansa, duk yanda Momcy ta tsara masa haka zaiyi, yasan wannan hanyarce kawai zata sakashi rabuwa da Dad lafiya batareda yaɗau zafi a wannan lamarinba.

     Ya lumshe idanunsa ya buɗe a hankali, kafin yatashi zaune sosai ya jawo drowa ɗin gefen gadon ya fiddo wani madaidaicin note book da pen, shiru yay tsawon lokaci yana kallon takardar, zuciyarsa na masa gargaɗi akan kar yayi haka, yayinda watacan ke angizashi akan hakan shine kawai mafita, ya saketa kawai, yarinyar bata dace da shiba, mizaiyi da baƙauya mara zurfin ilimi, ƙwaila.

     Kansa ya dafe tareda rumtse manyan idanunsa da ƙarfi, saiya koma ya kwanta ya cillar da biron yana jan wani tsakin mai ƙarfi.

   Dai-dai nan wayarsa ta fara ring, yay burus da ita harta tsinke aka sake kira, tsakin ya kumaja da ƙosawa da kiran, kafin ya cirota a aljihu ya buɗe idanunsa, Momcy ce, dan haka ya kirata saboda na biyunma ya tsinke.

       “Yaya Fodio ka rubuta mata?”.

      Numfashi ya sauke a hankali, murya a daƙile yace, “Momcy wlhy na kasa, sai nake ganin tamkar bamma dad adalciba, tamkar na wa.......”

     “Dalla yimin shiru shashasha shanyayye kawai, wlhy ban taɓa sanin kai ba jarumi bane sai yanzu Fodio, shin kodai kaima son nata kake?.”

     “Haba Mom, ni wlhy ban taɓajin son yarinyarnan a rainaba, mitake dashi da zan sota? Kawai na karɓetane a matsayin zaɓin mahaifina zuwa wani lokaci, da gudun saɓa masa, banaso ya kalleni mara biyayya a garesa”.

        “Yo aiko kayi masa biyayya shima ya sani, tunda aka ɗaura maka aure batareda jin ra'ayinka ba, aka kuma kawo maka yarinyar ka karɓa batare da bijirewaba, Fodio nagaji da gutsira magana akan wannan banzan auren naka, wlhy a wannan karon idan har baka saki yarinyarnanba saina tsine maka........”

     A matuƙar firgice ya tashi zaune, “Momcy!”.

       “Eh kirani da kyau, wannan shine umarnin ƙarshe dazan baka wlhy kaji na faɗa maka”.

      “ALLAH ya huci zuciyarki, indai maganar sakine an gama, gobe zansa a kawota”.

     “Ina? Kasata a mota tanufi ƙauyensu badai nan gidanba, kuma ida ya tambayeka dalili kasan yadda zaka kare kanka, karkuma sunana ya fito a ciki”.

     “To” kawai yace mata ya yanke wayar.

    Hakan ba ƙaramin ɓata ran Momcy yay ba, itakam lamarin Fodio har tsoro yake bata, ta tabbata da yanason wannan yarinyar komi zatai bazai saketaba, ai tagodema ALLAH da zuciyarsa bata sotaba.

    

       Koda ya kashe wayar saiya kasa rubuta sakin, har aka kira sallar magrib yana saƙawa da kwancewa, saida yafito zaje massalacine yanufi ƙofar ɗakinta, batareda knocking ba ko sallama ya tura ƙofar ya leƙa kansa.

      Idonsa karaf akan ƙirjin Ummu dake ƙokarin saka riga, yayunda itakuma tai saurin duƙewa ƙasa ta rufe jikinta.

     Wani tsaki yaja dahar zuci Ummu ta jisa, kafin a matukar hasale ya buga ƙofar ya shigo sosai yana wani harare-harare, “K ki haɗa dukkan abinda kika san nakine a gidannan”.

    Iya abinda kawai yace mata kenan ya juya ya fita abinsa zuciyarsa na tsantsar takaici da ganinta, yatsani ƙwailar mace, dukda baya neman mata, bai taɓa zina ba a rayuwarsa, a tsarinsa shine ya auri cikakkiyar mace wadda tako ina ta haɗu, yatsani koda a bokansa yaga sun auri ƴar yarinya marar cikar halitta, shikam ganinma yanda take a shafene yakuma sakajin zuciyarsa tsanar zama da ita, lallai maganar Momcy gaskiyane, tsakaninsa da yarinyarnan *wutsiyar raƙumi tai nesa da ƙasa.*


     

      Ummu dai ya barota cikin ruɗani, lokaci ɗaya jinta da ganinta suka gushe, da kyar ta iya ƙarasa saka rigar takoma bakin gado ta zauna tareda rabga tagumi, gaba ɗaya tunaninta ya gama tsayawa cak, tama rasa yazata fassara umarnin nasa.

      Har akai salla a masallacin Barrack ɗin aka sallame bata motsaba a wajen, saida isha'i ta kawo jikine ta iya yunkurawa dakyar tai salla tana hawayen da tun ɗazu basuzoba sai lokacin. Koda ta idar bata zaunaba, tsaf tashiga haɗa kayanta kamar yanda ya faɗa, tanayi tana hawaye, duk abinda ta iske a ɗakinma ta haɗashi waje ɗaya, hatta da kayan lefenta dako ɗayama ba'a ɗinkaba, sai dogayen riguna dana barci dataita sakawa, suma duk ta maidasu a akwatin. dan tasandai labarin gizo baya wuce na ƙoƙi, tunda dama ɗazun ta ritsa A'i na waya da Momcy.

      Komai ta haɗa abunta waje ɗaya, sai dai harta kwanta bai sake shigowa ba, dukdama barcin nata rabi da rabi ya zama.



*_Washe gari_*


    Ta idar da sallar asubahi ya shigo ɗakin hannunsa ɗauke da takarda guda biyu, ko kallonta bai yiba ya ɗorasu akan mirror tareda jingina da jikin mirror ɗin, murya a matukar daƙile yace, “Banida lokacin miki dogon bayani akan komai, sai dai kawai nace miki kisan maganar da zaki faɗama Dad akan zamanki a gidannan, karkuma ki kuskura sunana kona Momcy yafito a ciki, bakikai maceba balle har zuciyata ni Usman Majmud Usaman ta soki, banason ƙwailar mace mara zurfin ilimi, na sakeki saki ɗaya, wannan kuɗin kiyi amfani dashi, ga driver can yana jiranki a waje”.

       Ko motsi Ummu batayiba harya gama jawabinsa, saima kafesa da ido datai tamkar tasamu magiji, tana masa kallo irin wanda tunda tazo gidan bata taɓa nutsuwar masaba koda a sace, harya ficema bata dawo hayyacintaba.

        A'i da yau takejinta fayau tashigo ita da desmond da baisan abinda ke faruwaba, sudai ance kawai suzo su fidda kaya.

     Dukkan kayan da Ummu ta haɗa suka shiga ɗiba suna fita dasu, hatta da akwatunanta na lefe dayace su ɗaukar mata saida suka fiddasu.

       Saida suka gama fidda komaine tadawo hayyacinta, wasu hawayen baƙin ciki suka gangaro bisa kumatunta, lallai ta yarda *Namiji ɗan kunama ne* miyasa maza sukeson wasa da *ZUCIYARTA DA RAYUWARTA NE?*, Basiru ya kaɗa nasa taken, yau ga Amaan ya karɓi garayar, a hankali ta miƙe zuwa gaban mirror inda ya ajiye takardun biyu, ta farko ta taɓa taji mai kuɗince, dan haka saita ajiye ta ɗauki ɗayar tareda gyara tsayuwarta tana bin kanta da kallo a cikin madubin.

     Wani malalacin murmushi ta saki tareda share hawayen dake bin kumatun nata dukda basu daina fitaba, ta nuna kanta da take kallo acikin madubi tana magana cikin kakkausar murya da hasala irin wadda ba'a taɓa sanin tana da itaba, tace,

      “Minene narasa na mace dahar maza suke neman maidani cingom?, kowa ya tauna zaƙin ya ƙare saiya yadda matsayin amfanina ya kare, Basiru ka yaudareni alokacin da nake buƙatarka, kaci zarafina a cikin garina na haihuwa saboda kasamu ƴar masu kuɗi mai zurfin ilimi, nayi kuka, nayi ciwo saboda sonka dayayma zuciyata illa. Usman Mahmud Usaman ni Ummukulsoom Buhari ka kira da ƙwaila, marar ilimi, dukda nama iyayena biyayyane na aureka badan nima naji sonkaba, to lallai a wannan karon ban dace da zama mace mai rauni akan tozarcin ƴaƴa mazaba, ban cancanci sake bama wani namiji damar cin tuwo a kainaba, anyi biyu ba za'a sake na ukuba, na ɗauki alwashin zame muku *_WUTSIYAR RAƘUMI_* daga kaina bazaku sake raina ɗiya mace ba, zan tabbatar muku da cewa ɗiya mace ma mutumce tamkar kowa, zan tabbatar muku cewa dukiya ba ita bace ta banbanta tsakanin mutane, zan tabbatar muku da cewa Duk abinda *_ƳAN BIRNI SUKAI ƳAN ƘAUYEMA ZASUYI MAFIYINSA_*, kalmarka daka sanarma karuwarka cewa *_ABUN BA'A JIKI BANE_* tabbas ni Ummukulsoom Buhari ɗilau babban gida saina tabbatar maka da ita inhar ina numfashi a doron duniya, saina zamarma mazaje masu irin halayyarku *RAINA KAMA..!!*” ta faɗa da naushin mirror batareda tunanin komaiba.

    Ko takan hannunta dake jini batabiba ta figi takardar ta fice tareda bangaje A'i dake tsaye a bayanta, sai dai zuwanta kenan bataji dukkan alwashin Ummukulsoom ba.

      Galala A'i tabi Ummu da kallo baki a hangame, “Tofa, kekuma sakin da sabon salo yazo miki na nuna rashin tarbiyya? Eh lallai keko jar miyar dasamun (desmond🤣👍🏻 ) da wainar ƙwai ta ratsaki, to wlhy bazan bi motarkuba ta kasuwa zanje na hau, garama mu rabata hanya tun anan karkije ƙaramin haukarki ya sakaki shakeni”.

      Oho Ummu batasan tanaiba, shi kansa boss Amaan dake zaune a falon yana jiran fitowarta ko kallonsa bataiba ta fice abinta, shima bakinsa ya taɓe tareda ɗage kafaɗa alamar matsalartace. Dan baya buƙatar ɓata ransa a kanta, a ganinsa batakai matsayinba, dadai babu Dad a tsakaninsu lallai saiya koya mata tarbiyya da girmama manya.


       Dukkan kayan Ummukulsoom dana A'i angama lodasu a mota, danhaka Ummu tashige mota abinta tana koƙarin danne wutar dake ruruwa a ranta ta tsananin fushin da bata taɓa tunani ko sanin tana da itaba, tabbas tasan tun a kuruciyarta ta tsani wulaƙanci, amma sam batada zafi ko hayaniya, saidaifa daga wannan ranar tayi alƙawarin shafe babin wancan tarihin ta maye gurbinsa da jarumta.


       Desmond harda kukansa saboda ganin Ummu zata tafi, dukda baisan ainahin abinda ke faruwarba sai da A'i ta sanar masa cikin ƙwarewa a gulma, da ace shi wanine a igadan daya bama boss shawarar karyay wannan gangancin, dan shidai harga ALLAH Ummukulsoom tamasa, yarinyar akwai nutsuwa da sanin darajar mutane.

        Yasan ogansa murɗaɗɗen mutumne na bugawa a jarida, amma sam baida wulaƙanci shima, shiyyasa bai taɓa tunanin hakan daga garesaba, kodai A'i ƙarya ta faɗa masane?.

     Har Motar su Ummu tafice a gidan bayan A'i ta shiga tana habaice-habaice desmond yana wajen tsaye yana hawaye..


        A yaune Ummu ta tabbatar da zargin da tadaɗe tanama A'i na sakama zaman aurenta ido da ɗaukarta CID ɗin Momcy, koda taketa sakin magana a motar dajan Driver da hira murmushi kawai ummu tayi, ita kallon uwa take mata darajar girmanta, hakanne zaisa tabarta da halinta, duniyace zata koya mata hankali, ba itace a gabantaba a halin yanzu....


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


        Attahir baisan mike faruwaba har washe gari, da yaje Office ya iske maganar turasu ƙasar Seria ta tabbata, kuma harda sunan Amaan da kowa bai taɓa tunaniba.

    Hankalinsa tashe ya nufi office ɗin Amaan ɗin,  shaƙuwarsu ta sanya baya neman ison shiga Office ɗinsa, dan haka sojan dake tsaye a wajen yay salute nashi tareda ƙamewa sannan ya buɗe masa ƙofar ya shiga.

    Lafiyayyen Office dayaji abubuwan more rayuwa gwargwadon iko.

         Kwance yake cikin kujera ido a lumshe, sai faman girgiza ƙafa yake alamar akwai abinda ke damunsa.

      Attahir dayaja wasu mintuna a kansa ya sauke ajiyar zuciya, kafin ya zauna gefensa jiki a matuƙar sanyaye.

     Dukda yanajin motsinsa da tabbatar dashine hakan baisa ya ko motsaba.

       Cikin tsantsar damuwa Attahir ya kirayi sunansa.

     “Ajiwa”.

Shiru bai amsaba, baikuma motsaba tsawon wasu mintuna, kafin ya buɗe manyan idanunsa da suka ƙara girma dayin ja na alamar ɓacin rai ko rashin samun isashen barci, ido kawai ya zubama Attahir amma bakinsa yamasa nauyi.

      Attahir ya kallesa tareda sake gyara zama yana fuskantarsa, shi duk tunaninsa akan maganar turasu Seria ɗinne, dan haka cikin kwantar da murya yace,

      “Ajiwa dan ALLAH ina roƙonka ka janye makaman yaƙinka akan mutanennan, sunfimu fawa a matsayin manyanmu, sun fimu sanin kowanne irin tuggu dake a gidan soji, sun fimu ƙarfin iko a wajen shugabanni, katina kaifa yanzu mai iyaline, dukda ba zaman fahinta kukeyi da matarkaba zata fuskanci babban ƙalubale idan wani abu ya sameka, muma haka, familyn ka ma haka, ma.......”

         Dakatar da Attahir yay cikin ɗaga masa hannu, ya tashi zaune shima sosai, babu abinda yake sai sauke tagwayen ajiyar zuciya na alamar yana tareda tsantsar hasala da fushi,

      “Attahir wlhy kaji na rantse maka bazan janyeba, tabbas duk abinda ka lissafa sun fini, amma bazan zuba idanu aitamana illaba ta ƙarƙashin ƙasa, a kullum ɗaukar yaranmu ake aikin soji, amma sai illatamu ake ta ƙarƙashin ƙasa, daga yaye yara basu wani ƙware a yaƙiba, basu gama fuskantar a ina sukeba sai a ɗebesu akaisu dajika wai su bada tsaro, sai ai amfani da rauninsu aje a saka musu bama bamai ko a buɗe musu wuta duk su mutu, kaga an ɗiba yara sama da miliyan ɗaya zuwa daji da nufin yaƙi kafin wata uku idan ka duba zakaga basufi guda 100 suka rageba, sauran duk an kashesu, sai a dawo kafafen yaɗa labarai ana farfagandar ƴan ta'addane, shin wai ƴan ta'addarnan basa ƙarewane Attahir? Kowa yasan a ƙa'idar yaƙi sai kakai shekaru goma sha a gidan soji kafin a turaka, amma mu a ƙasarmu ko kaɗan ba haka baneba, bakuma komai ke janyo hakanba sai amfanuwa da manyanmu keyi ta wannan hanyar, kuɗaɗen da ake fitarwa kullum akan matsalar tsaroce basaso a dakata, Attahir idan har zamu cigaba da saka ido waɗanan abubuwan na faruwa baka tunanin wataran sai anrasa matashi ko ɗaya daga yankin arewa a gidan soji? Akumayi amfani da wannan damar acigaba da haddasa mana masifa akawo sojojin suyita kashemu suma tunda kullum burin ƙarar damu ake dama, tabbas ina mamakin yanda wasu manyanmu ƴan yankinmu suka zaɓi saida mutuncinmu akan dukiya, Attahir dukiyafa mai karewa, wadda idan yau ALLAH yace saikazo gareshi a matsayin gawa dolene katafi ka barta, wlhy turani wata ƙasa da a kai bashine yake nufin sunci galaba a kainaba, kona mutu a wannan yaƙin da aka turani za'a haifi wanda ya fini....” Magana yake amma hawaye na kwarara a idonsa saboda tsantsar kaiwa ƙarshe da zuciyarsa tayi a ɓacin rai.

     Hakan saiya kuma ɗagama Attahir hankali, Yau Ajiwa daya sanine ke kuka a gabansa saikace wani mace, lallai zuciyarsa takai ƙololuwa a matuƙar ɓaci kuwa.

    Saurin riƙe masa hannu yay alamar lallashi,

        “Ya isa haka dan ALLAH Ajiwa, kukafa kakeyi, abinda tunda nake a rayuwata ban taɓa ganiba”.

      “Humm Attahir bazaka gane bane, bazaka gane yanda zuciyata kejiba akan zalunci kala-kala da al'ummar mu ke fuskanta, bazaka gane ya nakejiba idan na tuna ɗunbin zalinci da tauye haƙƙi da wasu a shigabanninmu ke mana, sai yaushene zamuji daɗin ƙasarmu? Sai yaushene zamu sami ƴanci a ƙasarmu? Sai yaushene yankinmu zai samu kwanciyar hankali? A duk sanda aka tare wancan bala'i saikaji wanda ya fisa ya ɓullo, miyasa a yankinmu kawai waɗannan abubuwan suke tasirine Attahir?”.

         “Gaskiyane Ajiwa, maganarka tana a kan hanya wlhy, saidai yazamuyi tunda mafiya yawan masu madafun ikon riɓaɓɓu sunfi yawa, sannan mu kanmu talakawan zukatanmu babu ƙyau, rashin gaskiya da zalintar junanmu kawai mukasa a gaba, ALLAH dai ya gayaramu gaba ɗaya muda shugabannin. Ajiwa ya maganar matarka? Zata koma kaduna ne kokuwa zaka barta anan?”.

          “Hummm” yaa Amaan ya faɗa cikin tsantsar takaici yana maida manyan idanunsa ya lumeshe, bai sake cewa uffanba har zuwa wani tsawon lokaci kafin yaja siririn tsaki da faɗin “Ni banida wata mata yanzu, dan na maidata gida yau”.

      “Ajiwa saki kake nufi komi? Kasanko mi kake faɗa?”.

      Idanunsa ya buɗe tareda zuba ma  Attahir harara ya maida idanun nasa ya kuma lumshewa yanama Attahir nuni da ƙofa alamar ya fice masa.

     Ko kaɗan Attahir bai yarda da zancenba, dukda basu taɓa irin wannan wasar da Ajiwan ba, ko sallama bai masaba ya tafi cikin sassarfa.

     Wayar maman Ahmad yakira akan taje gidan Amaan ta duba masa Ummu.

    Amma sai tace tana makaranta.

      “Kinga Please, ko lecture kuke kifita kije ki duba tana nan?”.

     “Ban gane tana nanba Dadyn Ahmad?, wace irin maganace wannan kuma?”.

      “Hafsat Please, banason jan magana jeki dan ALLAH, daga baya mayi wannan”.

    Da “to” kawai ta amsa masa ta kashe wayar...........✍🏻



NO. 21



............Sosai hankalin maman Ahmad ya tashi jin bayanin desmond, dan haka ta kirayi Attahir ta sanar masa tana hawaye, harga ALLAH tana ƙaunar Ummukulsoom, amma lallai ta jajantama Amaan bisaga wannan gangancin da yay.

     Kasa magana Attahir yayi gaba ɗayasa, tsawon mintuna biyu kafin ya yaneke wayar yana haɗiye wani ƙududun takaicin Ajiwa a maƙoshinsa.

        Kiran Maman Ahmad yay yace ta haɗashi da desmond.

    Bayan desmond ya karɓa yay masa tanbayoyi akan direban daya ɗauki su Ummu, duk bayanan da yake buƙata ya sameshi garesa, dan haka ya kashe wayar tareda neman Abbas daya kawo direban, shine yabama Attahir Number ya kirasa.

    Bayan sun gama tattaunawa ya yanke yana nazarin akan tarar Alhaji Mahmud da zancen tareda abinda yake shiryawa, baisan yaya zai fahimcesaba, tunda yana tunanin anya Amaan zai iya faɗa masa?.

    Ganin bai samu mafitaba sai kawai yakoma Office.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


          Yini guda yau Dad yana gida bai fitaba, sai dai ya kaɗaice kansa acan baya daga harabar gidan yana harkar business ɗinsa ta lap-top, ya daɗe a wajen kafin ya tattaro kayan ya dawo cikin gida.

    Gidan shiru babu kowa, yaran duk suna makaranta, dan Bassam ma yacigaba da karatu tun tafiyar Ummu babu daɗewa.

      A falon ƙasa ya zauna danya ɗan huta, wayarsa dake gefe tai ɗan wani motsi alamar shigowar saƙo ya kalla, ganin sunan Fodio yasashi ɗauka ya buɗe saƙon.

      Ƙurama wayar ido yay yakasa koda motsi saboda firgici da saƙon ya ƙunsa, tare da tsantsar al'ajabi da tsaurin ido irinna Fodio, ya maimaita saƙon yafi a ƙirga kafin ya adanashi inda wanima bazai ganiba.

     Ana haka Momcy ta sakko cikin kwalliya, yanayin fuskarsa yasata faɗin “Abban Fodio lafiya kuwa?”.

      Wani kallo yamata tareda ɗauke kansa kawai, yasan tasan komai dake faruwa, dan yanaji a jikinsa itace ta saka Fodio a wannan hanyar, dan haka ya shirya binta ta inda bata zata ba.

     Duk iya bin kwakwkwafi na Momcy bataji abinda takeson jinba, saima ta fara zargin ko fodio ƙarya yay mata bai saki yarinyarnan ba, tashi tai tabar falon takoma sama tana neman wayarsa, sai dai kuma bai ɗagaba kusan kira uku, haushi yakuma hasalata, dan ta ɗauki alwashin a wannan karon inhar Fodio ya bijirema umarninta saita janye son da take masa gefe ta saɓa masa.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


      Lokacin da su Ummu suka iso cikin kaduna ƙarfe ɗaya na dare ya wuce, linƙis take da zazzafan zazzaɓi a jikinta, dan hannunta da tajima ciwo ya mata nauyi sosai, ga ciwon kai saboda kuka da tasha.

     Tasha mamaki sosai ganin Attahir ya taresu, sai dai ƙala kasa cemasa tayi, sai idanu da takebinsa dashi, idan san samuntane daganan kawai su wuce ɗilau, dan ko sha'awar zama gidan inna harira batayi itakam a wannan karon, ƙauyen can da ake cin zarafinta a kansa take sha'war komawa da burin yin rayuwa.

        Attahir ne yay musu jagora zuwa wani katafaren gida da Ummukulsoom ta gaza fahimtar inane, sai dai gidan shiru babu hayaniya alamun jama'ar cikinsa sunyi barci, amma a mamakinta saiga kusan mutum uku sun fito tarbarsu, babbar mace mai tsananin kama da Attahir sai matashiyar budurwa da zasu iya zama sa'anni da Ummu, sai saurayi wanda kallo ɗaya zakai masa kasan ƙanin Attahir ɗinne.

     Tarba sukai musu ta mutunci da girmamawa, harda A'i uwar gulma.

    Matar da kanta ta kama hannun Ummu sukayi cikin gida, sai jera mata sannu da zuwa takeyi.

      Ummu nata mamakin kirkin mutanen gidan, ko kaɗan basuda wulaƙanci, lallai ga inda Attahir ya gado ƙyaƙyƙyawan hali ashe, sai dama-dama ake da ita babu wani ƙyanƙyami ko nuna isar su wasune, ta tuna gidansu yaa Amaan iyayen alfahari da tunƙaho.

     A ɗakin budurwar akaima Ummu masauki, dandanan ta haɗa mata ruwa mai zafi dan tayi wanka.

       Godiya Ummu tai mata sannan tashiga wankan, tana wanka tana kuka, haka dai ta gasa jikinta sannan ta fito.

    Tun fitowarta Bilkisu ta lura da hannun Ummu. 

     “Amma kamar hannunki da ciwo ko?”.

     Kallonta Ummu tayi kafin ta kalli hannun tareda yin guntun murmushin takaici, “karki damu, bawani ciwo bane mai yawa”.

    Hannun takamo tana kallonsa da faɗin, “Wannan kam ya wuce ƙaramin ciwo, kallifa yanda tafin hannunki ya yayyanke, kinga ga kayan barcinan ki saka bara na dawo”.

      Ummu bata iya cewa komaiba, sai binta da kallo datai harta fice, ajiyar zuciya taɗan sauke kafin ta ɗauki kayan barcin wando da riga masu ɗan kauri ta saka, tana ƙoƙarin saka hula taji sallamar yarinyar tareda Attahir. saurin jan ɗan kwalin kayan data cire tayi ta yafa a jikinta, dukda kayan ba matseta sukaiba kuwa.

        Kallo ɗaya yay mata shima ya kauda kansa, yayinda budurwar kuma ta ajiye ƙarmin tire mai ɗaukeda kofin shayi da madai-daicin cake a gefe. 

    “Yaya bara na akarɓo maganin wajen Ummy”.

    Kansa ya ɗaga ɗaga mata kawai ya zauna a kujerar data kasance guda ɗaya a ɗakin.

      Ummu dai na tsaye tana saurarensu, sai dai kallo ɗaya zakaima fuskarta ka fahimci bata tareda walwala.

     Attahir ya furzar da huci yana faɗin, “Bismilla ki zauna mana”.

    Bata musa masaba ta zauna a bakin gadon tana haɗiye hawayenta, maganarsa ta sata ɗago ido taɗan kallesa.

     “Shine ya jimiki ciwo a hannu ko?”.

    Kanta ta girgiza masa tana juya idanunta saboda hana hawayen da suka tara zubowa, amma hakan bai hanasu fitowarba, bakin gyalen tasa ta goge, “Bashi ya jimin ciwoba Abban Ahmad”.

     Kansa ya iya girgizawa kawai, yace, “Ok, kiyi haƙuri Ummukulsoom, ki ɗauki hakan a matsayin ƙaddara, dare yayi yanzun, zuwa da safe zamu tattauna insha ALLAH, kisha wannan tea ɗin bilkisu zata kawo miki magani, dan ALLAH ki fidda komai a ranki, ki kuma saki jikinki a gidannan, domin ke ba bare baceba”.

       Kanta ta ɗaga masa tana kuma share ƙwallarta, “Nagode sosai Abban Ahmad, amma kayi haƙuri, zuwa yanzu babu inda nake kwaɗayin zama irin ƙauyenmu, kuma yadace mahaifina yasan matsayin aurena a yanzun”.

       “Wannan tilas ne ai Ummukulsoom, dolene baba yasan komai, maganar ina zaki zauna kuma duk zamuyi magana daga baya”.

       Nanma kanta ta jinjina masa.

     Bai bar ɗakinba har Bily takawo maganin, suka saka Ummu tasha tea ɗin dukda taƙii cin cake ɗin, magani tasha yay musu sallama ya fice.

       Gajiyar datai a hanya ce tasaka barci saurin ɗauketa, dukda sunsha kokawa tsakaninsa da damuwarta kafin barcin yaci nasara akan damuwar tata.


        A washe gari da safe saida Ummu ta makara sallar asuba, bily kuma taƙi tashinta.

      A gaggauce tayo alwala tafito, dan ƙarfe takwas saura, bayan ta gabatar da sallar tai addu'a tana kuma tariyo abinda ya faru a jiya, kusan iyanzu duk sun baro cikin Barrack ɗin.

      Ganin dukkan kayanta a ɗakin sai mamaki ya kamata, ta kasa fahimtar ma'anar hakan, ita duk tunaninta gari na wayewa zasu ɗauki hanyar ɗilau, kallonta ta maida ga Bily dake ƙudundune a bargo tana barci, Ummu ta sauke nannauyar ajiyar zuciya kawai.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


            “Honey wai meke damunkane kwana biyunnan?”.

     Baseer dake kwance ɗai-ɗai a gado yana danna waya ya ɗago idanu ya kalli Lubna mai maganar.

     “Mikika gani?”.

“Ba komai, kawai dai naga kamar kacika maida kanka busy a kwana biyunnan, bakason zama a gida, idanma ka zauna kata danne-dannen waya kenan”.

     Idanunsa ya janye a kanta ya maida kan wayarsa, “Kece dai kikaga hakan, amma ni nasan babu wata canjawa danai”.

    Shiru tai kawai tana kallonsa, tama kasa cewa uffan.

    Tsawon mintuna suna a haka kafin ta miƙe tabar bedroom ɗin.

    Bayanta ya raka da harara yana taɓe bakinsa, a yanzu kam ko kaɗan bata birgesa, bakaramin haushinta da takaici yakeba idan ya kalli ƙaton cikin gabansa, ya tunano zabgegiyar yarinya jinin kanuri Fannah ɗinsa, yarinya mai zamani mai lokaci a zuciyarsa, tuni soyayya tai ƙarfi a tsakaninsu, harma mahaifinta yace ya fito, burinsa ƙarshen watannan ya tura kuɗin aure, dan bayason bikin ya wuce nanda wata biyu, hotonta dake wayarsa ya latso yana kallo, wata nutsuwa da ƙaunarta tareda sha'awa wadda itace ƙarfin son na rinjayar zuciyarta, yarinyar komai yaji kam, dan akwai halitta mai ƙyau.

     Tsawon lokaci yana kare mata kallo lungu da saƙo ta hoton, kafin ya rufe yana zamewa ya kwanta.

      Lubna kam bata sake shigowa ɗakinba, kwanciyarta taje tayi a ɗayan ɗakinsu kodan ta hutama ranta.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


       Sai da su Ummukulsoom sukazo yin breakfast sannan takejin ashe A'i ta wuce gida tun ɗazun, ita kaɗaice a gidan yanzun, suna cin abinci amma banda ita, sai tsakura take kaɗan-kaɗan.

     Lura da hakanne yasaka Ummi mahaifiyar su Attahir janta da hira tareda lallashinta akan taci, duk sai kunya ta isheta, dan haka taɗanci abincin.


    Kammalawarsu babu jimawa Attahir ya fice akan zaije ya dawo yanzun.

      Addu'ar dawowa lafiya sukai masa, itama Ummi ta shirya tafita wajen aiki kasancewar ita likita ce.

      Daga Ummu sai Bily aka bari a gidan, Zaid ma yafice wajen nasa aikin.

         Kamar yanda Attahir yacema Bily ta ɗaukema Ummu kewa haka ta dake taita janta hira, dukda bata amsawa iyakarta murmushi ko e ko a'a.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


           Koda Attahir ya fita gidan su Fodio ya nufa, a falon baƙi akai masa masauki, dan haka hajiya jamila batasan wanene baƙonba, Jud ya kawomasa ruwa da lemo. Babu daɗewa da fitarsa saiga Dad dayasan da zuwansa ya shigo, fuskarnan babu fara'a tamkar kullum.

     Zamowa Attahir yay daga kujera ya koma saman Carpet yana gaidashi. Cike da kulawa Dad ya amsa da tambayarsa wajen aiki.

     Attahir yace, “Alhmdllh Dad”.

      Kujera ya nuna masa alamar ya koma ya zauna, amma sai Attahir ɗin yace, “A'a Dad nanma ya isa”.

         Attahir sai juya maganar da zaiyi yake a ransa, amma ya kasa, saikace shine Fodio ɗin, lura da hakanne ya saka Dad gyara zamansa, “Attahir bakinka da magana, sai dai bansan mikake son ɓoye minba? Inhar maganar abokinkace karkaji komai, yama rubutomin text massege a jiyan, ina tsumayen isowar Ummu ɗinne kawai,  ɗazun da safe tsohuwar dataje ta tayata zama ta iso gidannan tareda driver, shine yame sanarmin dama tana tare dakai, Saƙo ɗaya zan baka kabama abokinka Attahiru, yayi yanda yakeso, nima saiya jira lokacin dazan masa yanda nakeso, duk duniya ban haifi ɗan dazai jayayya daniba wlhy, ni nafisa tsaurin ido dagashi har uwar tasa data sakashi, idanma shine ya aikoka ka sanar masa bana buƙatar kowa akan wannan maganar”.

      jikin Attahir sai tsuma yakeyi jin Dad a matukar fusace yake magana, yakuma kasa da kai yana kwantar da murya, “Wlhy Dad ba Amaan bane ya turoni, hasalima baisan nabaro legas ba a yammacin jiya, amma amin afuwa bisa yin gaban kaina da nayi, nayi hakanne gudun kartace zata wuce garinsu a daren dan bansan shiyama sanar mukuba”.

       “Babu komai Attahiru, hakan dakai ba laifi baneba, yanzu ina ita Ummukulsoom ɗin?”.

      “Tana gidanmu na barota, dama nafara zuwane akan wata shawara”.

     “To to ina saurarenka wace irin shawarace?”.

      Shiru Attahir yay yana juya zancen, kafin yace, “Dad dan ALLAH kayi hakuri akan abinda Amaan yayi, karka nunamasa fushinka dan zai taɓa rayuwarsa sosai, mubi ta hanya mai sauƙi wajen nuna masa kuskurensa kawai, sannan mizai hana Ummu ta koma makaranta ita kuma”.      

        Shiru Dad yay yana kallon Attahir tareda nazarin maganarsa, yaɗan nisa yana kaɗa kansa, “Shawararka mai ƙyauce Attahiru, shikam dama ai bazan taɓa masa maganarba daman,  maganar karatunta kuwa zan zauna da mahaifinta muyi magana, dan dama naso takomane tana ɗakinta, a yanzu kam bamuda hurumin hakan tunda bata a ƙarƙashin ikonmu”.

       “Eh gaskiyane Dad, sai kuma maganar zamanta a gidan namu”.

        “Eh to wannan kam ka bani lokaci, dan nafison tadawo kusa dani kam, amma zuwa anjima zanzo gidan itama na ganta insha ALLAH ”.

      “To Dad nagode sosai, ALLAH ya ƙara girma da lafiya mai amfani”.

      “Amin ya rabbi Attaru, nine da godiya ai basa zamowarka aboki na ƙwarai, ALLAH yay muku albarka, shima ALLAH ya shiryesa”.

“Amin Dad mun gode, ALLAH ya huci zuciyarka, bara naje ni, shima Amaan ɗin a satinnan zaizo kd ɗin ai”.

       “Ok babu damuwa”.


Attahir ya koma gida zuciyarsa na cigaba da takaicin Amaan, sai dai a ransa yanajin cewar yanzune za'a fara wasan, fatansa ALLAH yabasu tsawon rai na dawowa lafiya daga inda zasuje kawai, ALLAH yasa ita kuma Ummukulsoom karta basu kunya.........✍🏻



NO. 22



............A falo Attahir ya iske Ummukulsoom da Bily suna hira, dukda dai bily ce mai firar Ummu tana dai tayata da murmushi da e ko a'a ne, dan tunani gaba ɗaya ya hazuciyarta sukuni.

      Sannu sukai masa ya zauna cikin kujera yana amsawa, da ido yayma Bily alamar ta tashi. Murmushi kawai tayi ta miƙe zuwa kicin.

      Attahir ya tattara dukkan hankalinsa akan Ummu da kanta ke ƙasa tana wasa da yatsun hannunta, “Ummu ina fatandai komai lafiya? Gidan namu yana miki daɗi?”.

       Murmushin da baikai cikiba tai masa, kafin tace, “Komai Alhmdllh, kuma gidannan namin daɗi, musamman dattakon jama'ar gidan da ƙyawawan halinsu abin alfahari da koyi, sai dai kayi haƙuri, ina bukatar tafiya gida kodan iyayena susan halin danake ciki”.

     “Hakane, kema kinzo da magana mai ƙyau, amma kiyi haƙuri kiɗan bamu lokaci, dan Dad ma yace zaizo anjima. Dan ALLAH in tambayeki mana”.

      Kaɗan ta ɗago kai ta kallesa ta maida, “Ina saurarrenka”.

       “Please iya ina karatunki ya tsaya?”.

       “Secondary ne kawai”.

    Da tsantsar mamaki yake kallonta, “Wai Ummukulsoom dama kinyi karatu har zuwa secondary?”.

      “Eh Abban Ahmad ”.

Wani daɗine ya kama Attahir, danshi duk zatonsa Ummukulsoom bata wuce primary ba, a lallai aikin nasu mai sauƙine, cike da zumuɗi yace, “Kin amshi result nakine?”.

        “A'a gaskiya bankai ga karɓaba”.

     “Wannan mai sauƙine ai amaryarmu”.

    Karan farko da wannan sunan ya sosa zuciyarta har fuskarta ta nuna, Attahir dayaga yanda ta ɓata fuska sai yay murmushi yana miƙewa.

     Babu zato Ummu taji yace, “Ayi haƙuri bazan sake faɗaba, daga yau Ummukulsoom kawai”.

       Kunyace ta kama Ummu, dan batai zaton fuskarta ta tona asirin zuciyarta baneba.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


               Cikeda farin ciki ta shigo gidan nasu, dan daga kano take, turus taja ta tsaya a bakin ƙofar tana sauraren labarin da A'i kebama Momcy, wasu hawaye masu zafi suka gangaroma fuskarta batareda ta shiryama hakanba.

      “Momcy lallai kinyi kuskure mai girma”.

     Daga A'i har Momcy da basusan da shigowar aunty Nurse ba suka juyo  da sauri suna kallonta. Da hannu Momcy taima A'i alamar ta tashi taje, miƙewar kuwa tayi ta fito, amma saita maƙale jin gulma.

    Aunty Nurse taci gaba da takowa cikin ɗakin tana share hawayenta, “Yanzunan Momcy rayuwar ƴarki bata zama isharar kiyaye ƴaƴan wasuba kenan? Momcy da kanki kika saka Yaa Amaan sakin matarsa, miyasa? Mita tare miki ne? Kin manta raɗaɗi da ɗacin da kikaji a lokacin da Muzaffar ya sakeni bisa tursasawar mahaifiyarsa? Kin mance kukan da mukayi ni da ke da ƴan uwana? Zamana a gida matsayin bazawara baisa zuciyarki raunin tausayama yarinyar da bata tsare miki komaiba Momcy, acikin ƴaƴanki mata kaf ɗinmu Aunty Ummi ce kawai zaune gidan miji, gani ga Ummayya ga Aneesa ga Buhayyah dako yanzu aka mata aure saita zauna amma har kikaba shaiɗan damar ingizaki maida ƙaramar yarinya Bazawara, Momcy nasan kinyi amfani da ƙarfin ikonkine akan Yaa Amaan saboda kinsan bazai taɓa bijire mikiba, amma lallai shima ya tabbata saiyayi dana sani wlhy, kuma yayi asarar mace wadda inada yaƙini a raina bazai taɓa samun koda kwatankwacintaba.......”

      A zafafe Momcy ta daka mata tsawa, “Jalilah! Wane irin banzar fatane wannan, wlhy ki kiyayeni”.

       Ƙin amsawa Aunty Nurse tayi tama juya ta fice daga ɗakin, ko kallon A'i dake laɓe bataiba dukda kuwa ta ganta, akwatinta taja ta fice takoma motarta tabar gidan, dan yau tamaji gidan nasu gaba ɗaya ya fice mata a rai, duk kayan farin cikin data kwaso sai taji bata sha'awar juyesa anan kwata-kwata, gidan kakanninta ta tafi waɗanda suka haifi Momcy, saidai ƙin faɗa musu abinda ya faru tayi.


      Dukda jikin Momcy yayi sanyi da kalaman Aunty Nurse hakan baisa taji zata iya barin Ummukulsoom ta rayu da ɗantaba.


 ★★★★


     Duk abinda ke faruwa tsakanin Aunty Nurse da Momcy Dad na jinsu daga falonsa, murmushi kawai yayi wanda yakan daɗe arayuwarsa bai yisaba, musamman irin wannan dahar hakoransa farare tas suka bayyana, koda ya fito domin tafiya zuwa gidansu Attahir baiko kalli hanyar ɗakin matar tasa ba ya fice abinsa, su kansu yaran wasu a ciki suna falo zaune wasu kuma na ɗakunansu. Hannu kawai ya iya ɗaga musu koda suka gaisheshi.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


             Gidansu Attahir Isa direba ya kaisa, dukda kuwa yasan mahaifin su Attahir ɗin baya ƙasarma, amma ya kirasa sun tattauna akan batun Ummu kasancewarsa abokinsa tun barowarsa Ajiwa, kasuwanci ma tare sukeyi abinsu.

        A falon Alhaji Abubakar akai masa masauki, kasancewarsa ba baƙo bane a gidan.

       Ummi ta fara shiga suka gaisa, tareda tattaunawa itama akan batun Ummu ɗin, kafin atura masa Ummukulsoom.

      Tunda ta shigo falon sai kawai taji wasu hawaye na neman ɓalle mata, a gaban Dad ta zube a ƙasan carpet ta fara gaidashi cikin rawar murya.

     Shima tunda ta shigo idonsa na kanta, wani tausayinta na ratsasa.

     Yay ɗan gyaran murya yana kuma maida hankalinsa a kanta sosai, “Ummukulsoom badai kuka ba?”.

      ƙasa tai saurin yi da kanta hawayen na sakkowa.

     Nannauyan numfashi Alhaji Mahmud ya sauke, kafin yace, “Yanzu ba lokacin kuka baneba ɗiyata, lokacin sanin ciwon kaine, ni na haifi Fodio amma bazan taɓa hanaki damarkiba domin maida masa murtani, bana buƙatar jin abinda ya rabaku a yanzu, fatana kizama jaruma wajen neman abinda yake tunanin kin rasa kinji”.

         kanta ta ɗaga masa alamar amsawa tana share kwallar data zubo mata, “Baba to dan ALLAH inason komawa gida, kodan su baba susan halin da ake ciki suma”.

         “Ummukulsoom kenan, bazance miki a'a ba, bakuma zance miki eh ba, sai dai albishir dazan miki shine, Babanki yasan komai, dan ɗazun da rana mun haɗu dashi agidan innarki mun tattauna”.

      Cike da mamaki ummu ta kalleshi, cikin suɓucewar harshe tace, “Amma baba shine baice na koma gidaba”.

       Sosai ya kalleta shima yanzu, “Ummukulsoom ba komawarki gidane matsalarba, mutuncinki shine abin dubawa, kindai san miya faru kafin aurenki da Fodio, idan kin koma a matsayin bazawara wace kalar dariya kike tunanin za'ai miki da mahaifinki a wannan ƙauyen? Dama akwai masu jiran irin wannan ranar a gareki, waɗanda a kullum suke jifar babanki da kalmar saidaki yay gamasu kuɗi, ke yarinyace, sai nan gaba zaki fahimci abinda muka hango miki, ki kwantar da hankalinki kicigaba da zama anan gidan, yanzu haka an fara bincika miki makaranta”.

       Wani ɓangare na zuciyar Ummu a ƙuntace yake, wani gefen kuma yayi farin ciki da komawarta karatu, dan aganinta shine farkon tsanin nasara a alwashinta. Godiya ta shiga yima Alhaji Mahmud, yayinda kaunarsa keta ratsa ranta, samun irin waɗannan a cikin al'umma abune mai matuƙar wahala, irinsu Dad  sune jagororin masu kishin ƙasa da al'ummarsu na gaskiya, da ace irinsune suka yawaita a yankinmu da bamuyi kuka da attajiraiba da shugabanni.

       Dad yaji matuƙar daɗi ganin Ummu tabasu haɗinkai, ya saka mata albarka sosai kafin yay musu sallama ya tafi bayan yabata kwalin waya sabuwa fil da wasu ƴan kuɗi.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


           *_SABUWAR DUNIYA_*


       Dole mu kira wannan ƙaddara ta Ummukulsoom da suna sabuwar duniya, dan kuwa tazo mata da sauye-sauye na haƙiƙa, a sati ɗaya kacal datai gidansu Attahir harta fara canjawa, dan kowa a gidan ƙoƙarin canja damuwarta yake da farin ciki, Ummi tajata a jikinta sosai tamkar uwa mahaifiya, Bily kam amsa suna biyu takeyi, ƙawa kuma ƴar uwa, Attahir ya zama yaya hakama Zaid, saiko Uwa Uba Dad da Abba mahaifin su Attahir da tun dawowarsa gidan yaji wata tsantsar ƙaunar Ummukulsoom, tareda girgizar zuciya dayaji ainahin sunan garin da Ummukulsoom ta fito, ya daɗe yana maimaita sunan garin *ɗilau* a ransa, sai dai kuma ya haɗiye komai batareda yabar kowa ya fahimtaba.

        Abinda yakuma saka Ummu sakin jikinta da gidan shine zuwan Maman Ahmad, dan Attahir ya kawosu gida har sai an koma yajin aiki, sai kuma ga Aziza da Inna harira sunzo gidan ganin Ummu, daɗi ya kama Ummu matuƙa, harda kukanta kuwa, yini sukai a gidan ranar, Ummi tace a bar Aziza ta kwana biyu.

    Hakan yakuma sakama Ummu ƙaunar Ummi da ahalin gidan su Attahir gaba ɗaya.

     Haka suke haɗuwa ɓangaren maman Ahmad susha hirarsu idan Ummi ta wuce wajen aiki, Abba dama bai cika zamaba saboda yanayin business ɗimsa, hakama Zaid aiki kan hanashi sukuni, Attahir kuma tunda sukazo yanata cuku-cukun amso takardun Ummukulsoom a Zaria, dan so suke itada Bily su wuce makaranta, itama shekararta ɗaya da kammala secondary, saidai result ɗinta baiyi ƙyauba saida ta gyara a wannan shekarar.

        Yaa Amaan har gidan yazo ya gaida Ummi kamar yanda ya saba, dan shima yazo yin sallama gida akan tafiyarsu.

        Har yazo yatafi ma Ummu na barci a ranar, saida ta tashine Maman Ahmad ke sanar mata da Bily, baki ta taɓe tai tamkarma bata jisuba, dan ita a halin yanzu baya gabanta.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


              Tunda Amaan yazo kd yake samun gata ga Momcy kamar yanda ta saba a duk lokacin da yazo garin, inda sukuma su Bassam suka shiga tsantsar takura hatta da Ameer, ko kaɗan babu mai ƙwaƙwƙwaran motsi na jin daɗi, sai rayuwar gidanma ta canja, ƴan aiki suka sami ƴancin kansu dan babu mai musu kallon banza hatta da Momcy.

      Ko a fuska Dad bai nunama Yaa Amaan abinda yayba na sakin Ummukulsoom, baima bashi fuskar tado masa zancenba, abinka ga ɗan gado, shima saiya basar tamkar bai aikata komaiba, saima Momcy dake zungurarsa da zance, amma sam yaƙi biye mata, ko sau ɗaya yaƙi cewa komai game da zaman Ummu gidansa balle sakin nata.

      Momcy tasan zaimayi abinda yafi haka, dan hallayar Fodio sai dai du'ai kawai.

     Kwanansa goma a kd shida Attahir suka koma legos cikeda addu'ar ƴan uwansu da iyayensu.

      Ranar saboda jin daɗin tafiyarsa su Aneesa har ƙaramin perty suka haɗa, dama ga Dad baya nan yana Ajiwa shida Ameer, shi kansa Fodio saida yaje, dan yana matuƙar ƙaunar garin sosai.

      Momcy ce kawai taji kewar tafiyar ɗan nata mafi soyuwa a gareta, dan ranar yini tayi a gidan tamkar mai zazzaɓi.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


        Komai da ake buƙata na takardun Ummukulsoom Attahir bai tafiba saida ya kammalasu, yabarma Dad neman makarantar dasu Ummu ɗin zasu tafi.

         

*_BAYAN GAMA IDDAR UMMU_*


           Rayuwa mai juyi da sauyi, akwana a tashi kuma baida wahala a wajen ubangiji, musamman a wannan zamanin da babu abinda yakai lokaci gudu da sauri, zuwa yanzu tabon dake cin zuciyar Ummukulsoom yafara dasashewa, a da kam kullum dare sai tayi kuka,  ahankali tafara sabawa da sabuwar rayuwa tareda janye duk wani ƙududun mazaje biyu dake ranta tamkar rubutu bisa dutse.

       Rayuwar Ummu agidansu Attahir abin birgewa, hankalinta saiya kuma zama waje ɗaya bayan ta gama idda taje gidan Inna Harira ta kwana biyu sun gana da babanta, nasiha yay mata mai ratsa jiki tareda ƙarfafa mata gwiwa akan burin Alhaji Mahmud na tayi karatu, dan shima da farko bai yardaba, saida Dad yay masa bayani na gamsuwa sannan ya fahimci lallai a yanzu karatu shine gatanta, dan haka ya amince hundred percent.

       Ummukulsoom ta murmure sosai, jikinta ya fara dawowa, zuwa yanzu batada zumuɗin daya wuce su fara karatunsu, dan Islamiyyar data shiga inda Bily keyi saita kuma zaburar da ita amfanin ilimi, tareda jin ƙarfin gwiwar cikar burinta tunna farko tana ɗilau.

       gaba ɗaya ta shafe babin Amaan balle wani Baseer a ranta, takuma dunƙule maza tamusu kuɗin goro a yanzu, Dad da mahaifinta da Abba sai ko Attahir ne kawai sukaciri tuta mai girma a ranta.


       

★★★★★★


          Yau ta kasance asabar, shiyyasa kowa yana gida, maman Ahmad ma bata koma legas ba saboda makarantarsu basu koma yajin aiki ba har yanzun, su kansu su Ummu can ake jira su koma a samar musu, kasancewar Ummi batada ƴan aiki sai wata dattijuwa mai wanke-wanke kawai sai suka zage suka gyara ko ina tamkar yanda suka saba.

      Bily dake Morping ta riƙe ƙugu tana faɗin wash ALLAH na, ALLAH bayana kamar zai cire”.

     Baki Buɗe Ummukulsoom take kallonta, kafin tace, “Oni Ummu, wai Bily ke wace iriyar raguwace? Morping kawai kikema raki irin haka?”.

     Hararan wasa Bily ta mata tana zama a hannun kujera, “ALLAH bazaki ganeba Kulsoom, kefa shaidace akan wahalar da muka shawo jiya a kasuwa”.

       “Kai babie nan kina bani pepe wlhy, yanzu nan har ɗan yawon jiya yakai a kirashi wahala? ALLAH ya bama Yaya Zaid haƙuri dayayta yawo da kayan nauyi a hannu, kinga muyi sauri wlhy time ɗin islamiyya zai ƙure”.

       “Kai nifa yauma kamar karmuje islamiyyar nan wlhy, dama Ummi ta yarda muje gidan su Aziza musha weekend ma........”

       “Mu kuma kubarmu shiru a gidan dagani sai Hafsat ko? Anƙi wayon”.

    Da sauri suka juyo jin maganar Ummi dake fitowa daga ɗakinta.

      Dariya sukayi suna durƙusawa suka gaisheta, ta amsa cike da fara'a tana kallon yaran nata tamkar tagwaye, ita badan karta zula ƙaryaba da tace har kama tame gani Ummukulsoom nayi da Bily da maigidan.....

     Bily ce ta katse tunanin Ummi da faɗin “Please Ummin mu, kingafa ga yaya Zaid ma yana gidafa, muma muɗan miƙe ƙafa muga gari dan ALLAH”.

       “Bily duk daɗin bakinki ƙyayi ki barni, indama yinine sainace kuje, muma sai muyi tafiyarmu gidan Hajiya yaya”.

      Da sauri Bily tace, “Mun yarda koma yini ɗinne ko Ummukulsoom ”.

       Murmushi Ummu tayi tana gyaɗa kai alamar amsawa.

      Ummi tayi dariya tana faɗin “Ok, saiku shirya Zaid ya kaiku, amma islamiyya fa? Bilkisu banason baƙin yawonki yasaki faramin wasa da karatun yarinya”.

     “Kai Ummi ALLAH a'a, itamafa tanason zuwa”.

      Cike da tsokana Ummu tace, “Nidai a'a banaso Ummi, muje islamiyyar mu kawa......”

    Cikin wani tsalle Bily ta isa gaban Ummu tareda rufe mata baki da hannu alamar karta ƙarasa.

     Dariya Ummi da Yaya Zaid dake shigowa suka sanya musu.

      Yaya Zaid ya ƙarasa wajen cin abinci yana faɗin “ALLAH Ummi karki bari Bily ta koyama Ummukhoolsum baƙin yawonta da tamkar anmata ƙauri da ƙafafun kare”.

      Baki bily ta turo gaba tana kallon Ummu, “Yanzu kin yarda ashiga tsakaninmu kenan?”.

      Dariya Ummu da Ummi sukayi, Ummu tace, “Inafa zan yarda, ai ko saɓani haka ya ganmu ya barmu tawajena”.

       “To aiko saidai kufita anguwar a Napep” cewar yaya zaid yana musu harar wasa.

      Ummi dake ƙarawa inda yake tace, “A'a ba ayi hakaba Yaya Zaid, gwiwar autocina bisa ƙasa, sun tuba”.

      “Ummi karki nemar musu alfarma, gara kibarsu su ɗana suji, dama ni inada gun zuwa”.

      Ummukulsoom tai saurin cewa, “Yi haƙuri Yaya Zaid, karmuje a sake irin ta wancan karon muka ɓata”.

       “Ai hakan shine dai-dai daku ma”.

      Haka suka cigaba da hirarsu suna shirin yin breakfast har maman Ahmad ta shigo itama, da gudu Ahmad ya nufi Ummi kasan cewar kakar tasa na matuƙar sonsa.

         Itama zama tai suka cigaba da breakfast ɗin har suka kammala Ummu da Bily suka gyara wajen, kafin kowa yanufi ɗaki ya shirya.

         Ummi da maman Ahmad ne suka fara tafiya gidan hajiya yaya suka bar su Bily na jiran fitowar yaya zaid a harabar gidan. 

    Tunda ya fito idonsa nakan Ummukulsoom da tai ƙyau cikin sket da riga na shadda pink, sai dai kuma ta saka hijjab mai hannu, dukda babu kwalliya a fuskarta sai tayi ƙyau sosai.

    Ɗauke kanta tayi dan batason yana mata wannan kalon, shima sai yay murmushi kawai yana musu nuni dasu shiga mota.

      Da sauri Bily ta shige baya ta kulle, hararta Ummu tayi ta buɗe gaban ta shiga badan tasoba.

      Ta mirror bily tai mata gwalo, dan tasan ta tsani zaman gaban mota dama.

        Yaya Zaid na tafiya yana jan Ummu da hira, itako iyakarta murmushi, dama bata sakin jiki dashi inba taga Ummi a wajenba, har ƙofar gidan su Aziza ya kaisu, daɗi ya kama Aziza sosai da inna harira. Bayan Zaid ya shiga sun gaisa komawa yay ya barsu nan.........✍🏻


NO. 23



...........Yau kam sunsha shargallensu agidan inna harira, dama Aziza yaya lafiyar giwace itama, har dare suna gidan, baba yazo suka gaisa bayan sallar magrib.

      Da zai tafi saita bisa soro dansu ɗan tattauna.

          “Baba dan ALLAH ku amince naje Ɗilau, wlhy ina kewarsu sosai”.

      Baba dake zaune a tabarma yay ƴar dariyarsu ta manya, “Ummukulsoom kenan, indai ɗilau ce zakije, kibari su Alhaji sugama shirin karatun naku, dan dama munyi dashi sai kin kammala iddarki, tunda dai yanzu kin kammala nasan da kansa zaimace kije ɗin”.

     “Hakane baba, amma ya jikin Gwaggo hinde ɗin?”.

      “A jikin Gwaggo kam Alhmdllhi wlhy, ta murmure dan talatar satin can data wuce mun haɗu da ita wai zataje tsinkar gyaɗa gonar babanki Ayuba, harma naita faɗa akan bai kamataba, amma sai tacemin itace tace zataje saboda likita yace take ɗan motsa jikinta”.

       “ALLAH sarki gwaggo, to ALLAH ya ƙara musu lafiya, amma baba ai batasan aurena ya mutuba ko?”.

      “Haba Ummukulsoom, ya za'ai a sanar mata da wannan maganar banda dai wautarki ta ƙuruciya, ai ba abune na daɗiba kinga, balle ita dake fama da jikin tsufa”.

       “Hakane kuma baba, ALLAH yasa mudace”. ‘Ummu tai maganar cikin share hawaye’.

       “A'a Ummukulsoom, nifa wannan kukan bana sonshi, idan akai haƙuri komai mai wucewane, saikiga yazama labari tamkar baima faruba, a rayuwa kowanne bawa da tasa ƙaddarar, ki ɗauka keɗin taki kenan, idanma kikaji ta wani saikiga ai ke takin ba komai baceba”.

      “Hakane baba, insha ALLAHU zan kiyaye”.

    “Yauwa ko kefa ƴar albarka, ni bara natashi naje, dan gobe idan munkai da rai asubanci zanyi”.

     “To baba ALLAH ya tsare hanya, a gaishe mana da kowa”.

     “Amin dai Ummukulsoom, duk zasuji ”.

     

     Har baba yay musu sallama ya tafi Yaya Zaid bai ƙarasoba, sai wajen tara saura yazo, ko shiga gidan baiyiba, waya yayma Bily akan su fito waje.

        Aziza ta rakosu har ƙofar gida, bayan su. gaisa da yaya Zaid suka ɗau hanya, itakuma ta koma gida abinta.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


              Lubna shiru zaune a falo ita kaɗai sai masu aikinta, ta zuba tagumi tana tunanin wai ina Baseer yake zuwane ne, a ƴan kwanakinnan takan rasa ina yake zuwa duk bayan kwana biyu, na farkoma saida yay kwana tara, ita dai a saninta sai kanada kishiyane kowa gidansa daban miji ke wannan asha ruwan tsuntsayen, itako ba kishiyace da itaba balle tace.....

       Motsin da taɗanjine ya sata waigowa da sauri, shine sanye cikin ƙananun kaya tamkar yanda ya saba, cike da zumuɗi tai masa sannu da zuwa.

     Amsawa yay tare da tambayarta jikinta da gida, tai murmushin yaƙe da amsa masa, hakan da yake mata yake sakata samun nutsuwa koda zuciyarta ta fara mata rawa a kansa.

      Da kanta ta taimaka masa yay wanka dukda ƙaton cikin dake gabanta kuwa, bayan sun dawo falo suka baje suna ƴar hirarsu.

    Kiran da ya shigo wayarsane ya saka Baseer saurin ɗaukar wayar ya danne ƙarar, Lubna ta ɗan tsura masa idanun tuhuma, “Babie ka ɗaga mana”.

      Murmushin yake yay mata, “Lah karki damu Hafiz nefa”.

     Murmushi tai tareda ɗauke kanta, shima haka, kusan minti biyu sai aka sake kira, nanma yay azamar danne ƙarar. miƙewa Lubna tai ta bar masa falon, dan ta lura bayason ɗaga wayar a gabanta.

     Da yake baseer ɗan barikine na gasken gaske sai yama kashe wayar gaba ɗaya, Lubna dake laɓe taga kozaiyi wayar harta gaji da tsaiwa ta dawo falon suka cigaba da zamansu, da zaije masallacima a gida yabar wayar yanda zata kuma yarda dashi ɗari bisa ɗari.

    Sosai kam hakan yay tasiri a zuciyar Lubna.


    Shikam yana fita ya ciro ƙaramar wayarsa ya kira fannah, “Oh babie sorry kinata kirana wlhy barci yaɗan kwashenine, kinsan matafiyi”.

      “ALLAH sarki babie na ya gajiyarka ya aikin?”.

       “Alhmdllh babie na, sai daifa kewarki tareda kewar lallausan jikinki da ƙamshinki”.

      “Karka damu, indai wan nanne nakane ai dear, bara na barka ka huta anjima mayi waya mijina abin alfaharina”.

      “Ok amaryar ƙamshi ki huta lafiya kinji”.

      “Insha ALLAH” Ta faɗa tana kissing wayar.

    Murmushi yayi ransa fes, duniya sabuwa yake jinsa, yasan da Lubna ta fahimci yayi auren nan da sai anyi uwarwatsi, dan ya gama lura tafi Suhailat kishin masifa, shiko baya buƙatar rabuwa da Lubna a yanzu, dan yana amfanuwa da mahaifinta fiye dana Suhailat, zaitabin hanya mai ɓullewa da wani bazai taɓa fahimtar yayi aureba balle har wani a family ɗin Lubna ya sani.



★★★★★

  

    Kwansa biyu a gidan Lubna ya ballaƙa mata karyar zuwa gaida iyayensa a kaduna, bata damuba, dan dama yana irin hakan, kuma tasan iyayensa acan suke, tunda itama kanta acan ɗin suka fara haɗuwa.

      Yana barin nan sai gidan daya kamawa amaryarsa Fannah haya, wadda duka-duka auren nasu bai wuci sati ukuba kacal.

     Yanda su Suhailat suka mutu akan son Baseer haka Fannah ma ta mutu, sosai take bashi kulawa da tattali, banbancinta dasu Lubna ita mahaifinta ba mai kuɗi bane sosai, amma gwargwado sunada rufin asiri, ƙarfin soyayyarta a zuciyar Baseer kam sha'awa ce, dan Fannah mace ce har mace, akwai diri ɗan gaske dako wanne irin namiji zaiso samun matarsa haka, ga uwa uba ƙyaƙyƙyawace jinin shuwa ɗan asali.

        Tarba tai masa ta musamman, kasancewar tunda sukai aure wannan ne karo na biyu dayay tafiyar kwana huɗu, iyakacinsa kwana dayane a matsayin aikin Office, nanko gidan Lubna yake zagayawa itama yaɗan kare yawa.


       Haka rayuwar tasu taci gaba da tafiya batareda sun fahimci wa suka auraba, garama Fannah idan taga abinda bai mataba takan tanka, wataranma har suyi faɗa da baseer ɗin, daga baya kuma yadawo su shirya.

      A haka har ALLAH ya sauki Lubna lafiya ta haifi ƴarta mace ƙyaƙyƙyawa mai tsananin kama da baseer, sosai yay farin ciki da wannan babie, sai dai abinda zai baka takaici babu ko mutum ɗaya daga dangimsa na jini, sai iyayensa na bogi dayay amfani dasu wajen aurensa, sukansu su Inna sai a hoto sukaga ƴar, amma hakan bai hanasu saka mata albarkaba da addu'a, dansu har yanzu bama susan ba Suhailat bace uwar ƴar, a tunaninsu har yanzu itace matar tasa, lamarin baseer yabar ɓata musu rai, sun zubamasa idone kawai.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


            Ummukulsoom ce farkon fita a motar, tai gaba tabarsu, shi Zaid ma dariya ta bashi, yasan duk dan karsu kasance su biyune take wannan abun.

           A falo ta iske su Ummi da suma basu wani jima da dawowar ba, Ahmad yazo yana mata oyoyo ta ɗaukesa tana shillawa.

     “Ku yanzu dama haka ake yini?”. Cewar maman Ahmad.

     Dariya Ummu tayi itama tana zama gefenta, “Kai aunty, kuma da alama fa yanzune kuka dawo, muma dan yaya Zaid baije da wuri baneba, Ummi fa?”.

        “Ummi tanada baƙo, suna falon Abba”.

     Kafin Ummu tayi magana su Bily ma suka shigo. Yaya Zaid dake kallon Ummukulsoom yace, “Hajiya bamu ɓataba, muma man gane hanya”.

     Murmushi kawai Ummu tayi ta ɗauke kanta, yayinda maman Ahmad take binsu da kallo baki buɗe, dan itakama tafara fahimtar akwai wata a ƙasa. Bily kam data saba gani dariya kawai tayi tana zama ɗauke da Ahmad.

      “Wai Aunty Hafsat kallon mi kike mana hakane?” cewar yaya Zaid.

      “Babu ko ɗaya Uncle, sai daifa ina bada shawarar abi a sannu kar ai karo da muruci, dan ramin damisa ba wajen wasan yara baneba”.

      “An samu matsala Aunty Hafsat, kinsanfa ni bawani gane wannan hausa cikin hausar nakeba”.

     Bily tace, “To balleni kuma yaya Zaid”.

      Ummukulsoom dai kam tsaf ta fahimci maman Ahmad, shiyyasa ta miƙe tama bar falon, a ganinta bada wannan amsarma ɓata lokacine, tarasa yanda zata hana mamana Ahmad dangantata da Yaya Amaan, mafi yawancin lokacima itace ke tuna mata sunansa, dan itakam tama manta da har sunan nasa, kamar yanda takeda tabbacin ita dama baima san natanba.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

       

      *_Gidan Alhaji Mahmud_*


        “Mun shiga uku Momcy, mike damun Dad ne, ina zamu samo mazan aure a wata biyu kacal? Wlhy Momcy kaf samarina babu maimin zancen aure”.

       “Toke kinama da Samarin Aneesa, ni nace mi, banda Huzaifa wanene ke zuwa wajena, Huzaifa kam iyayensa wlhy bazasu masa aure yanzuba”.

     Momcy na zaune ta zuba tagumi tareda zubama ƴaƴan nata idanu, abin duniya duk ya isheta, tarasa gane kan Abban Fodio a kwanakinnan, sai fito mata da salon abubuwa yake waɗanda ita kaɗaice ke fahimtarsu, yanzu daga Aunty Nurse ta samu miji shine yace Ummayya da Aneesa ma su fidda gaba ɗaya zai haɗasu ya aurar.......

     “Momcy magana mukefa”. ‘Aneesa tafaɗa cikin girgizata’.

      Cikin sauke ajiyar zuciya ta dawo hayyacinta, “To ni Ummayya mikukeson nace muku? Kunsan dai wanene mahaifinku da abinda duk ma zai iyayi, amma kubari zan gwada, ina zuwa”.

       Fatan samun nasara sukai mata, ta miƙe ta fita zuwa falon Dad.

    

      Zaune yake a falo yana danna Lap-top, yana waya kuma, hajiya jamila taji daɗin samunsa cikin walwala, gefensa ta zauna harya kammala wayar yana faɗin Alhmdllh, ALLAH kabani tsawon ran sauke wannan nauyin”.

     Da “Amin” hajiya jamila ta amsa, duk da bata fahimci komaiba a zancen nasa.

     Juyowa yay ya kalleta yana gyara zamansa, “Lafiya dai ko?”.

      “Lafiya lau Abban Fodio, dama dai akan maganar yaran nanne”.

     Ɗaure fuska ya kumayi sosai, “Waɗanne yara kenan?”.

     Tuni zuciyarta ta fara hautsinawa ganin yanda ya koma mata, cikin in ina tace, “Su su Ummayya, kayi haƙuri ka kara musu lokaci”.

      “To, to, saboda ga mijin hajiya Jamila ko? Jamila wlhy ki kiyayeni, ina tarakine kawai, idan kika bari nakai bangon da zan amayoki bazakiji da daɗiba, wlhy kinji na rantse duk wadda bata kawo mijiba a watanni biyunnan danace saina aura mata duk wanda yaymin, har shima Ameer ɗin, niba shashasha bane dazan zauna naita tara ƴaƴa a gida manya-manya babu aure, ko Buhayyah ta samu miji bayan kammala secondary ɗinta aure zan mata, dan haka wannan shine gargaɗi na farko, kuma na ƙarshe tsakanina dake, karki sake zuwamin da wannan batun, ina buƙatar ɗakunan da suke ciki dan mai zama cikinsu tana gab da shigowa”.

     Wani irin duka ƙirjinta yayi, ta waro idanu waje cikin tsantsar firgici, “Abban Fodio ban gane maganarka ta ƙarsheba wlhy”.

     Miƙewa yay tsaye tareda kwasar tarkacensa yana faɗin, “Ai bazaki taɓa ganewaba tunda kinacin kan kifi”.

      Tamkar sha katafi haka tabisa da kallo, manyan idanun nan da Amaan yay gado tamkar zasu zubo ƙasan carpet ne, jinta yay wani diimm, hakama ƙwaƙwalwarta tai jingim bata aiki gaba ɗaya, sam saita daina fahimtar komai, dukda wani gefe na zuciyarta na faɗa mata bafa abinda take tunani baneba.


        Sam a kwana biyunnan gidan ya sauya, saika ɗauka ko Amaan ne yazo, amma ba hakan baneba, dafin umarnin Dad ne kecin kowa a zuciya, idan ka ɗauke Aunty Nurse dake cikin farin ciki da shirin Dad ɗin, dan itace tabasa wata shawarar a cikin shirin nasa, bama tai zaton zai ɗaukaba ashe ya amsa.


       Ana cikin wannan yanayin a gidan saiga admission ɗin su Ummukulsoom ya samu, sai dai kuma a Rivers state ne, University of port harcourt suka samu, hakan bai damu Alhaji Mahmud ba kam, dan a ganinsama canne Ummukulsoom zatafi samun wayewar kai kasancewarta cikin ƙabilu daban-daban, zata samu ilimin zamantakewa da jama'arda koda ba kabilartaba.

       A ranar yakira Abban Attahir ya sanar masa, shima yayi matuƙar murna da hakan.

     Babu ɓata lokaci aka hau yima Ummukulsoom da Bily shirin tafiya port, duk da ita a ranta tana tunanin yaya zasu rayu a inda basusan kowaba, gashi ita koɗan turancinma bawani iyawa tayiba, danma Bily na nuna mata wasu abubuwan a zamanta gidan, sai karatunta na islamiyya, tana bukatarsa matuka, dan babu wani ilimi dazai tasiri ga rayuwar ɗan musulmi idan babu na addini a cikinsa.

    Kasa daurewa tai taima Bily tsokacin maganar, Bily kuwa ta samu Ummi da zancen ba tareda Ummukulsoom ta saniba.

    Murmushi Ummi tayi tanajin ƙarin ƙaunar Ummukulsoom a ranta, haka takeson mutum ya kasance mai sananin ciwon kansa da martabar addininsa.

      “Karku damu Bilkisu, zanyi magana da Abbanku saimuga yanda za'ai gameda islamiyyar taku, idanma wani malami za'a samu sai a sama muku acan, dan namaji kamar bacikin makaranta zamu zaunaba”.

     “Tofa, ba cikin makarantaba Ummi, to wajenwa muda ba dangi garemuba acan ɗin?”.

     “In banda shirmenki Bilkisu ko babu dangi ai akwai abokan arziki ko, mudai jira muji yanda za'ayi ɗin, kudai yanzu ku kammala shirin tafiyar taku ɗilau ɗin”.

     “Aini Ummi kinma tunamin, kinsan kuwa yanda na ƙagu muje garin nan nasu Ummukulsoom? A rayuwata inason naganni a inda ban saniba, musamman ma ƙauye wlhy”.

         Dariya Ummi tayi tana girgiza kai, “Hajiyar zumuɗi kenan, koda yake Ummu mafa na lura tana cikin tsantsar farin ciki, tana dai dannewane kawai, yarinyar tanada nutsuwa sosai wlhy, shiyyasa a kullum take sake shigemin rai, narasa miyasa Abbanku yace karna kaita wajen Hajiya yaya?”.

      “Wlhy nima Ummi abinnan na bani mamaki, nasan kuma Hajiya yaya batada matsala, tanada son jama'a zakuma taso Ummukulsoom sosai”.

       “Karmu damu, na tabbata akwai nashi dalilin shima ai”.

      “Hakane kuma Ummi, yanzu dai bamu kuɗin mutafi wankin kan kar rana tayi, nadsan Ummukulsoom ma tagama wankan yanzu”.

      “Duba a bag ɗincan da nadawo aiki ɗazun ki ɗaukar muku dubu biyar, sai ai muku har ƙunshi ko, dan sonake taje tsaf”.

      “Hakane Ummin mu, shiyyasa nake ji dake barci da ido biyu”.

       “ALLAH shirya minke Bilkisu, kindai maidani kakarki wlhy”.

      Dariya Bily ta fita tanayi da faɗin “Ni na isa Ummina.


         Ummukulsoom na zaune gaban Mirror tana rolling gyalen doguwar rigarta Bily ta shigo.

        “Hummm kaga ƴammatan yaya Zaid, irin wannan ƙyau haka”.

     Harara Ummu ta ɗago ta zabga mata, amma batace komaiba, Bily ta kwashe da dariya tana jingina da mirror ɗin, “Miye na hararata to? Kin zata ban harbo jirginku baneba shin?”.

      “Bakida man kai wlhy Bily, a'a garinmu kika harbo ba jirginmuba, idan kin shirya muje, idan kuma bazaki jeba nai gaba”.

       “Oh ga maganata ta fito, bama kwaso na biku dama ai, to duk tsiyarku sai naje”.

    Dariya Ummukulsoom tayi, ta ɗauki bag ɗinta tana faɗin “Ki sameni wajen Ummi parrot”.

       “Nice parrot ɗin?”.

“Kinmafi Parrot ai Bily”.         

          Bayan Bily ta gama shiryawa ta samu Ummukulsoom a wajen Ummi suna hoto, shiga tai itama akayi da ita sannan suka fita zuwa sashen maman Ahmad da itama taketa shirin komawa legas, amma anan zatabar Ahmad wajen Ummi, tare suka tafi wankin kan.

      Sai yamma lis suka dawo gidan, ammafa sunyi ƙyau sosai, barema Ummu datai kitso, sai fuskar ta ƙara fitowa fes da ita, dukda baza'ace takuma zama wata cikakkiyar maceba amma jikinta ya murje sosai, fatarta tayi wani irin ƙyau da kwanciya saboda bawani yawo takeba, kallo ɗaya zakai mata ka gamsu hankalinta a kwance yake, batada wata damuwa sai wadda ba'a rasaba.

     Hankalin Ummi saiya sake kwanciya dataga yanda Ummukulsoom ɗin tai ɗas, koba komai ƴan garin nasu bazasu taɓa samun hanyar yin ƙananun maganaba, dan babu wanda zai kalleta bai sake kalloba.


*_Washe gari_*


            Washe gari saiga Aziza itama, dan tare zasuyi tafiyar zuwa Ɗilau.

       Tsaf suka fito kamar ka sacesu ka gudu, haka kawai Ummukulsoom saita tsinci zuciyarta da fargaba, amma saita danne dan a yanzu bata buƙatar halin tsoro a rayuwarta, burinta akomanta ta zama jaruma, su ukune kaɗai zasuyi tafiyar, sai yaya Zaid dazai kaisu ya dawo, dan 1week zasuyi su dawo.

     Sunyi sallama da maman Ahmad, itama insha ALLAH gobe zata wuce Lagos ɗin.


         tunda suka tafi a motar Aziza da Bily ne kawai ke fira, sai Yaya Zaid dakan ɗan saka musu baki idan yaso, amma sam Ummukulsoom kamar bata ma a motar, sai kallon hanya take abinta, shirun natane dai kan ɗan saka yaya Zaid janta da hira lokaci-lokaci shima, a haka har suka isa Zaria, tsaraba ya ƙara musu ta kayan marmari sannan suka hau hanyar ɗilau bisa jagorancin Ummukulsoom.........✍🏻



NO. 24



..........Babu abinda ya sauya mata a garin a kusan shekara ɗaya da bata ciki, sai dai gine-gine da aka ƙara na jar ƙasa alamun dai matasan garin sunsha aurarraki, sanin babanta na gida yasata nunama Zaid hanyar da zata kaisu babban gida, yara saibin motar suke da gudu dukda basusan wanene a cikiba.

       Sai suka bama Ummu tausayi, duk wanda ya rayu a ƙauye yasamu wani cigaba dolene ya tausayama waɗanda suke a ciki, bawai dan suna cikin ƙunciba ko koma baya na rayuwa, a'a sai dan kawai suna rayuwane tamkar shugabanni sun manta dasune, ka shekara goma bakaje ƙauyenkuba idan kaje saika tarar babu wani canji da aka samu, idan kayi wasama saikaga ankuma samun taɓarɓarewane.

        Tunda Ummukulsoom suka fito yaran dake binsu sukai cirko-cirko suna kallonsu, hakama manya dake cikin inuwoyi zaune ana zaman gulmar mata sai duk suka zubo musu ido.

     Mariya ce data dawo daga ɗibar ruwa rafi tai tozali da Ummukulsoom, cikin ƙaraji tace, “La'ila, yaya Umma”.

       Hakan da tayine ya fargar da waɗanda basu gane Ummu ba, Ummu na kiranta amma tuni tayi cikin gida kai rahoto.

     Kafin kace mi an zagaye su Ummukulsoom har mata na leƙe ta katanga kowa burinsa yaga Ummukulsoom yata komane.

    Itako sai zuba musu murmushi takeyi, fuskarta a washe take tarbar kowa.

     Duk sun ɗauka Zaid ne mijinta, dan danan aka bashi masauki, Ummu tashiga matuƙar mamakin tarbar da suka samu gasu baba yalwa, kafin kacemi ƙauyen ya ɗauki zuwan Ummukulsoom. Ƴan gidan kam sai kawo musu abinci ake da fura, sunci iya abinda zasu iya ci, Bily sai daɗi takeji, harga ALLAH garin yamata sosai.

      Da yawan ƴan gidansu Ummu jikinsu yayi sanyi da ganin yanda Ummukulsoom ɗin takuma canjawa, ta murje tayi ras da ita, saidai fa dukda hakan sunata ƙananun gulma wai babu komai (Ciki🤣).

         

     Lokacin da Ummu ta fito zasuma yaya Zaid rakkiya gidan Gwaggo hinde ya gaisheta sai mata ke leƙensu ta katanga, oho sudai basusan anaiba, gashi abindama zai ƙara ɗaukar hankalinka, da Ummu suka tafi jere da Zaid ɗin, Bily kuwa da Aziza suna gabansu, duk Aziza ce da shirinnan, dan fatanta karsu bada wata ɓaraka da wani zai fahimci Ummukulsoom batada aure yanzu.

     Shiko Zaid da hakan yay masa daɗi sai jan Ummukulsoom yake da hira akan mizai shirya musu kafin su dawo na tafiya makaranta, wannan ne yasata biye masa harda murmushin dake narkar da mazan garin.


      Gwaggo hinde na tsakar gida a garken dabbobi tana basu ruwan tsari su Ummu sukai sallama, dukda an sanar mata da zuwansu saida taji wani irin daɗi, sai dai kuma a lokacin da take ma su Ummukulsoom lalale marhabun sai idonta ya sauka akan Zaid dake shigowa a ƙarshe, gabantane yay tsananin faɗuwa, tai kasaƙe tana kallonsa baki a hangame.

       Daga Bily har Ummu har Aziza duk juyawa sukai suma suna kallon abinda Gwaggo hinden ke kallo,  ganin Zaid sai duk suka juyo gareta.

        Ummukulsoom ta karasa inda take taɗan girgiza hannunta, ”Gwaggo! Kin ko baƙya murna da zuwan nawa na koma?”.

     Ajiyar zuciya Gwaggo hinde ta sauke, kafin tai murmushi tana canja zancen da faɗin, “Sannunku da zuwa amarya, kumuje ciki mana, angona lalale marhabun (tazata Zaid ne mijin Ummu itama).

         Zaid da duk yasha jinin jikinsa da kallon Gwaggo hinde yay murmushin yaƙe yana amsata.

      Koda suka zauna a tabarmar da Gwaggo hinde ta samusu gindin bishshiyar mangwaro dake gidan sai bin Bily da Zaid take da yawan kallo a sace, Ummu da Zaid ne kawai suka lura da hakan, amma dai basuce komaiba duk da shima Zaid mamakin kamannin Gwaggo yake da Abbansu, sai dai ita tsufa daya kamata.

      Bayan an gaggaisa sukasha ruwan da Gwaggo ta ajiye musu sai aka hau ƴar hira, musamman tsokanar Ummu da gwaggon keyi akan ina zatakai jiki?, watanni kaɗan hartayi irin wannan canjawar, Mi Zaid ke batane? Itama a kawo mata nata kar kishiya tafita a wajensa.

      Dariya kawai Zaid kema Gwaggo dajin wani nishaɗi a ransa, inama ace zancen Gwaggo zai tabbata daya zama cikin masu sa'a, saidai gefen zuciyarsa na mamakin shin Ummu ta taɓa aurene? Dansu babu wanda yama taɓa sanar musu komai akan dalilin zaman Ummukulsoom gidansu shi da Bily, dukda ita bily takanji maman Ahmad na ambatar sunan Amaan ɗin bata taɓa sanin matsayinsaba a wajen Ummu, bama ta zata yaya Amaan na gidansu Buhayyah ba.

        Sunsha har zuwa biyar na yamma Zaid yayma gwaggo alkairi suka rakoshi har mota tanata saka masa albarka da fatan saukarsa lafiya, anan aka sauke kayan su Ummu tareda tsarabar gwaggo yatafi cikeda kewar Ummu da Bily, tareda alwashin dawowa ya kwana garin dan yamasa daɗi sosai.

     Su Ummu kuwa nan suka dawo suka cigaba dashan hirarsu, sai dare taje babban gida itada Aziza, dan Bily maƙalewa tai wai ita tana gidan Gwaggo suje su dawo.

      Acan su Ummu sukasha hirarsu da baba saida suka farajin barcine suka dawo gidan Gwaggo, dan baba cayay su kwana acan safi samun sakewa.

       Gwaggo kuwa tanata jan Bily da hira cikin hikima, dan ganin Zaid ya tada mata wani tsohon tabonta, hakama kamannin Ummu da Bily wanda saika daɗe tare dasu zaka fahimci hakan.

      Bily batasan dawan garinba, duk tambayar da Gwaggo tai mata itadai kai tsaye take amsa mata harsu Ummukulsoom suka dawo gidan.  



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


          “Wow ga wata kaya fa alhaji tana tunkaromu”.

       Baseer dake zaune a mota yana latsa waya ya ɗago ido a sace yana kallon zankaɗeɗiyar yarinyar fara tas, motar da aka buɗe mata ta fitoma kawai abar kalloce.

    Karon farko a rayuwar Baseer dayaji son mace na gaskiya a ransa bayan Ummukulsoom, ya cije leɓe da ƙarfi yana binta da kallo harta shige wajen hutawar.

       Hafez sabon abokinsa da shima yake binta da kallo sake da baki ya sauke sassanyar ajiyar zuciya yana maido kallonsa ga baseer daketa kokawa da busashshen yawu a maƙoshi.

       “Bas abari ya hucefa”.

      Da ƙyar Baseer ya iya faɗin “Abokina shike kawo rabon wani, amma muja aji”.

     “Aji kuma? Yo kai mace ne? Ai irin waɗannan ina faɗa maka idan bakai ka tayaba saika ƙaraci haɗiyar yawunka ko kallo baka ishesuba, kaidai tashi muje kawai”.

      Fitowa Baseer yayi bayan yakuma fesa turare tun a mota ya goge fuskarsa sosai, nufar wajen sukai shida Hafiz suna tafiya ɗai-ɗai tareda basarwa dan shima Hafiz ɗin masha ALLAH ƙyaƙyƙyawane.

       Tunda suka shigo wajen suke baje ido amma ko alamarta basu ganiba, nanfa suka shiga zagaye-zagaye amma babu ita, fitowa sukayi waje sai sukaga motar tatama babu.

      Kowannensu yay tsirmai-tsirmai da idanu sunma rasa a yanda zasu fassara abun, kamar ance Baseer ya ɗaga ido saiya hango motarsu can saman titi, da sauri ya bugi kafaɗar Hafiz ya nuna masa motar.

      Ido Hafiz yaɗan zaro, “Bas wai yaushema ta shiga  motar to?”.

        “Ƴar dariya Baseer yay, “Wato kasan mina fahimta kuwa?, ba wajennan ta shigaba, wancan shagon ɗinkin ta shiga kasan akwai ƙofa tacan baya, wannan kuma kamar ba kowa yasan da itaba”.

       “Kumafa maganarka gaskiyace wlhy Bas, yanzu yaya za'ai kenan?”.

        “Wai kai tsayama dai, sonta kake komi?”.

       “Sosaima ko” cewar Hafiz.

      Wata banzar harara Baseer yay masa yana faɗin “bakada mankai wlhy, kwana nawa bikinka ya rage da Aysha, wannan kayanace”.

           Hafiz yace, “Babu komai saina barmaka, amma wlhy nakamu fa”.


       Tun wannan gani da Baseer sukaima wannan budurwa hankalinsa ya kasa kwanciya, kullum cikin tunanin ina zai ganta yake, ahaka suka shiga shagalin bikin Hafiz.

        Ranar Dinner ana tsaka da raƙwashewa saiga yarinyarnan yagani, itama kuma tun shigowarta wajen da Baseer ta fara tozali dake zaune kusa da ango.

        “Meenal wai mikike kallone haka?”.

     Sassanyan murmushi tayi tareda juyowa ta kalli mai maganar, “Zakiyya na macene, dan ALLAH kalla guy ɗincan”.

     Kallon tsaf Zakiyya tamasa tana jinjina kanta, banga laifinkiba babie, komai yaji kama, sai dai irin waɗannanfa mata bazasu barki ki hutaba saboda bibiyarsa”.

      “Karki damu Zakiyya, indai nasamu zan adana yazama nawa ni kaɗai”.

      “Nasan zaki iya kam, amma batun rashin son zama 9ja fa?”.

      “Saina fara bincike a kansa, idan mai bine saimu tafi, idan kuma sai an bisa babu matsala zanyi manage”. 

      “ALLAH ya taimaka ƙawata, batun ƙulla alaƙa fa?”.

      “Ga katina ki bashi, idan yazo da wulaƙanci to lallai ɗan manyane, idan ya karɓa da hannu biyu zamu sama masa ajin karatu”.

      Dariya zakiyya tayi kafin ta maida kallonta ga Baseer, ita kanta badan ƙawarta tayi shigar sauriba data shiga daga ciki, amma babu komai, ai akwai bayan katanga.

        A wajen liƙine Baseer da Meenal suka haɗu, sunama amarya da ango sai suka koma yima junansu kowanne na jifan ɗan uwansa da murmushi, tun a wajen alaƙa tafara ƙulluwa, musamman da amaryar Baseer ta gabatar musu da Meenal matsayin yaya.

      An tashi taron biki lafiya tareda alaƙa mai ƙarfi tsakanin Baseer da Meenal.




⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡.


             Sosai su Ummukulsoom kejin daɗin ɗilau, sai faman zaga gari suke suna yawo, gidan murja kam ai nanne gidan hutawarsu, tai musu wannan tai musu wannan, Ummu na ƙaunar Murja sosai, dan zumincinsu akwai shaƙuwa acikinsa na haƙiƙa.

       Kwanansu huɗu a ɗilau sukaje wajen Nusaiba itama, hakama Azima, bakaramin rikicewa da sauyar Ummu sukaiba, sukam duk sun fara zama wasu mama, musamman ma Azima daba jin daɗin zaman takeba yanzu saboda kishiya, tausayinsu saiya cika zuciyar Ummu, takaraji. ƙarfin gwiwa akan nutsuwa taci gaba da karatunta.


       Gaba ɗaya kwanansu takwas a ɗilau Yaya Zaid yaje ya kwasosu suka dawo kaduna.

       Ummi tayi murna da ganin yaran nata, dama tanata kewarsu, ga maman Ahmad itama ta wuce tuni.

     Suma dai dawowar tasu duksai ta kasance ta shirye-shirye, duk abinda zasu buƙata angama kimtsa musu shi, Ummi duk sai taji kamarma ta hanasu tafiyar, amma dai tanason babies ɗinta suyi karatu kuma ai.

        Ana gobe zasu tafi Dad yazo gidan, haɗuwa sukai shida Abba sukai musu nasiha mai ratsa jiki akan su kare mutunci su, karsuyi wasa da addininsu dansunje ciki. kabilun da addini ya banbantasu, su zama ƴaƴa nagari, suje suyi abinda yakaisu shine abinda aka turasu.

       Sosai su Ummukulsoom sukaita share hawaye, danda kallon abun sukeyi kamar wasan yara, ashedai tafiyar ta gaskece..

     Da daddare yaya Zaid yakaisu gidan inna harira sukai mata sallama, canma kamar karsu rabu da Aziza sukaji, sai kusan 11 suka dawo gida..........✍🏻


NO. 25



        ...........“Abba fodio wai dan ALLAH har yanzu kana akan bakanka gameda aurensu Ummayya?”.

      Yi yay tamkarma bai jitaba, hankalinsa kwance yake kallon labarai a NTA.

     Ta sake maimaita maganar a karo na biyu.

      Wata lalatacciyar harara ya zabga mata yana kuma tamke fuska, “Jamila! Amma dai kinsan halina ko? Kinsan banason rainin arziki ko? Tom kici gaba”. Yay kwafa yana miƙewa yabarta a falon.

     Tsan tsar tashin hankaline yakuma bayyana a fuskarta, a gaba ɗaya kwanakin nan batada wani dogon sukuni, ba auren su Ummayya bane kawai damuwarta harda maganar buƙatar ɗakunansu daya tofa, tama rasa a yanda zata fassara zancen nasa, dan tunaninta da fassararta mugun abu yake bata, wato Alhaji Mahmud zai ƙara aure. Zabura tai tsaye tana faɗin, “kai ina bama haka baneba, da zaiyi dayayi tun munada ƙuruciya”. Gaba ɗaya ta susuce. Mansura ƙanwarta ta kira, amma saitace mata ta jirayi zuwanta ƙarshen satin sama, dan yanzu maigidanta yana gari.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


       Su Ummu sai shartar hawaye ake itada Bily, sunbi sun kanainaye jikin Ummi suna mata shagwaɓa, Abba da suka bashi dariya saiya murmusa yana faɗin, “Autocin Ummi ayi hakuri, wannan shine ake kira da neman ilimin ko a birnin sin, fatanmu dai ku kasance masu nasara, nanda wasu shekaru muga lauya da ma'aikaciyar banki a gidanmu”.

     Murmushi duk sukayi masa, suna ɗaga kawunansu da share hawaye.

      Yaya Zaid dake musu dariya ya miƙe yana faɗin, “ALLAH yabamu haƙuri muda aka tura wata ƙasa tsawon shekaru, ALLAH Abba kubar ƙara shagwaɓasu ma, dan tafiya port dolene yau, muna dawowa muci daɗinmu dagani sai my Ahmadi na, ko my boy”. Yaƙare maganar da jawo Ahmad jikinsa.

     Hararsa Ummi tayi tana nuna masa hanya, Ummukulsoom da Bily kuwa suka kumburo baki suna kuma matso hawaye, hakan saiya saka Abba dariya, ya kama hanyar fita yana faɗin, “Kunga kufito jirgin da zamubifa ya kusa tashi”.

      Miƙewa sukai har Ummi suka fito, dayake duk gidan zasuyi musu rakkiya, Abba ya kama hannun Ahmad da shima yay laƙe yana kallonsu dukda bai fahimci miza'ayiba.

    ko a mota yaya zaid sai tsokanarsu yake, amma sunƙi kulashi, suna lafe a jikin Ummi abinsu.


★★★★★


        Karo na biyu Ummukulsoom a jirgi, saidai wannan lokaci yazo da cigaba, dan zuciyarta tsaye take babu wani ƙauyanci ko tsoro a ranta, hirarsu ma sukeyi itada Bily a hankali.


      Jirginsu na sauka suka sami tarba ta musamman daga abokin Abba Mrs Alabo, ɗan asalin Abiloma L.G. ne, yaren Calaberi ne na asali.

     Tare yake da iyalansa, matarsa mai suna Miss Ibiso, sai ƴaƴansa Uku, akwai babbar budurwa mai suna Blessing, sai mai bimata namiji Dakubo, sai kuma matashiya budurwa kamarsu Ummu mai suna Peace.

           Kwasarsu sukai zuwa anguwarsu dake Bony street hausa line, anguwar ta burge su Ummukulsoom, babu wata hayaniya, gata tsaf, gidane madaidaici mai ƙyau da ƙayatarwa, dankuwa daka gansa kasan an kashe ƴan canji, komai abin birgewa, dan danan aka cikama su Ummu gabansu da abinci da kayan ciye-ciye.

     Yanda Abba ke fira da Mrs Alabo Zai tabbatar maka da akwai sanayya mai ƙarfi a tsakaninsu, hakan saiya birge Ummukulsoom da bily, tuni suma suka saki jikinsu da yaran, sai daifa Bily ce mai maganar, Ummu bakomai take fahimtaba kasancewar turanci sukeyi.


           Bayan sun huta sai suka shirya zuwa makarantar, duk abinda ya dace akuma yimusu Abba saida yayi, kafin su dawo gidan Mrs Alabo akan ranar Monday su Ummu zasu fara lectures, Ummukulsoom dai kallon abun take tamkar wani mafarki ko almara, sai dai tana ƙarfafa zuciyarta bisaga raunin dataga tana neman faɗawa.

        A ranar Abba da Ummi da yaya Zaid da Ahmad suka juya, har airport suka sake rakasu, saida sukaga tashinsu suka dawo gidan.

       A ranar dai kam su Bily sunyi baƙunta kasancewar akwai rashin sabo, amma yanda Peace taketa shige musu a jiki sai suka fara sakewa, gashi kuma duk jama'ar gidan basuda matsala, duk da kasancewarsu ba musulmai ba hakan bai hana su Ummukulsoom yin ibadarsu cikin kwanciyar hankali ba.


        A kwanaki Uku kacal su Ummu suka gama zama ƴan gida, sun saki jikinsu sosai, yin komai suke tamkar gidansu.

       A ranar Monday kuwa tunda wuri sukai shirin tafiya makaranta, kasancewar itama Peace Can takeyi bama ta daɗe da farawaba sai suka samu ƙwarin gwiwar tafiya hankali kwance.

      Daga Bily har Ummukulsoom shigar dogayen ruguna Arabian gown sukai, ta bily baƙa da adon stones honey color, ta Ummukulsoom ma baƙa da adon fararen stones, sosai sukai ƙyau, saikace tagwaye, haske kawai Bily zata gwadama Ummukulsoom.

      Peace data fito cikin dogon wando da t-sheat sai taita kallonsu, dansun birgeta sosai, hakanma saiya sata komawa ta ɗakko siririn gyale ta kawo wai itama sumata irin rolling ɗin dasukayi da gyalen jallabiyarsu.

      Ummukulsoom ta karɓa tamata, dama ita tama bily ma.

        Dakubo Yayan Peace Shine ya ɗaukesu amota zuwa school, dama shima canɗin dai yakeyi, yanama shekarar ƙarshene shi.

     Suna tafiya Peace Na nuna musu abubuwa, suko sai ware ido suke suna kallo da haddacewa.


      *_BABU NAKASASHSHE SAI KASASHSHE_* Cewar Ummukulsoom data tsinci kanta a gaban lecturer cikin hall yana zuba musu lecture, ba abu ɗaya zasu karanta ba itada Bily, dan kowa akwai burinsa, a ganinsu kuma hakanne zai basu damar maida hankali akan abinda ya kawosu.

      A ranar sai 5pm sukabar school suka koma gida, tun a mota kowa kebama ɗan uwansa labarin abunda akayi peace nata musu dariya musamman yanda Ummukulsoom ta dage tana haɗo turanci, dan acewarta ahakane zata iya har tayi kamar kowa wataran.

     Sun iske gidan babu kowa, Mom da Blessing Sunje Choch, Daddy kuma bai dawo aikiba.

      Kai tsaye ɗakinsu suka nufa, kowa yashiga warware gyalen kansa, kafin Ummukulsoom tai saurin shigewa bathroom tana dariya akan zata rigasu yin wanka.

        Suma cikin dariyar suke faɗa mata zasu ramane, ta ɗauka yau ranartace.

        Gaba ɗaya yau cikin nishaɗi Ummukulsoom take, kallo ɗaya zakai mata kuma ka fahimci hakan, koda sukai waya da Ummi bayan sun idar da sallar magriba saida ta fahimci haka, shiyyasa itama sai taji zuciyarta takuma sanyaya akan kewarsu.

          Suna ajiyewa Yaya Zaid shima ya kira yay musu fatan alkairin farawa a sa'a, Abba dai bama ya kasar.

    Saiga Maman Ahmad ma takira, hira da itane yajasu tsawon lokaci, dan sunata bata labari daki-daki, yayinda take kuma ƙarfafa musu gwiwa musamman Ummukulsoom dakeda tabo a zuci.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


            Cikin wani murmushin iya bariki Meenal take kallon Baseer dake gabanta, ta juya idanunta cike da salo tana tauna cingam yana bada ƙara ƙass! Ƙasss!!, “My Boo kenan, aini duk abinda naso bana masa ruƙon sakainar kashi, karkasha mamaki akan son danake maka, sai daifa a aurenmu akwai sharaɗi mai girman gaske”.

     Cikin faɗaɗa murmushinsa yace, “Minene sharaɗin?”.

       “Banason zama da kishiya, banason yaudara, banason ƙarya, banason ha'inci, idan harka kiyaye wannan zan mallaka maka dukkan kaina da dukiyata harda ragamar iko dani”.

       Saida ya jinjina maganar sosai kafin yay murmushi, “indai wannan ne bakida matsala dani, dukna ɗauka kuma insha ALLAHU zaki sameni yanda kikeso”.

      “To Alhmdllhi my Boo, abu nagaba shine karabu da dukkan ƴammatanka, sannan bayan munyi aure bazamu zauna a Nigeria ba, yanzu haka bikin Aysha ne ya kawoni dole, sai kuma haɗuwa dakai daya riƙeni gam, kamar yanda nasar maka Abbana shine Ambassador na Nigeria a ƙasar Frace, so kuma dama can acan kusan muke gaskiya tunkan hakan ta faru, amma idan baka ra'ayin zama can nimai haƙurice mu rayu anan ɗin....”

      Da sauri Baseer yace, “Haba dear, mizai hana nabi zaɓinki, wlhy ni na amince koma inane muyita tafiya kawai”.

      Wani tsadajjen murmushi tai masa tana faɗin, “Ok, kayi ƙyan kai kuwa, sai dai gaskiya zamanmu bazai wuce shekaru biyu ba zamu dawo Nigeria kawai, badan komaiba sai dan cikar wani buri na mahaifina, dan yanason neman takarar gwamna”.

     Wani daɗine yakuma ratsa ransa, dan haka ya murmusa tareda cewa “ALLAH ya tabbatar mana da hakan”.

     “Amin My Boo, so yanzu dai nabaka dama akan ka tsara yanda komai zai kasance, nima insha ALLAH zan tsara na turama Abbana dukkan bayanan”.

        Nanma murmushi yayi, kafin su mike tayo masa rakki har mota, bayan ta buɗe masa ya shiga ta manna masa kiss a kumatu.

     Idanu ya lumshe wani daɗi na ratsa ransa, lallai yanzune aka dace ashe, dakam kansa a tukunya.


        Gaba ɗaya Baseer ya susuce akan Meenal, babu abinda yake sai tunani akan ya sanar mata gaskiyane kokuwa ya ɓoye? gaba ɗaya Lubna da Fannah sun gaza gane kansa, ita Lubna ma ana tsaka da wannan sauyawar ta Baseer babban tashin hankalin rasuwar mahaifinsu ya risketa.

     Wannan yasakata tattara komansa ta watsar, rashin mahaifinta ya taɓa dukkan rayuwarta.

     Zuwan Baseer biyu gidan yabar zuwa, danshi a yanzu ta matsalarsa da Meenal yake, yagama yanke hukuncin sanar mata da komai gameda asalinsa, maybe hakan zaisa tafi sakin jiki dashi da ƙaunarsa, danshi harga ALLAH son gaskiya yake mata babu nufin yaudara ko kaɗan a ransa.


      A haɗuwar da sukai ta yau ya zauna yasanar mata komai gameda asalinsa, saidaifa baice mata ya taɓa aureba.

     Ta jinjina zancen ƙwarai da gaske a ranta, amma saitaji tama samu ƙwarin gwiwar aurensa.

     A washe gari Baseer yakama hanyar Ɗilau.

      Babu wanda yay mamakin zuwansa a cikin iyayensa, dansu yanzu kam lamarinsa sun maidashi gefe.

       Bai samu zama dasuba sai dare, dukkan abinda yazo dashi gameda aurensa da meenal ya fayyace musu, sannan ya sanar musu ya rabu da Suhailat saboda yaga danginta ba mutanen arziki bane, yakuma roki su yafe masa bazai sake aikata kuskuren da yayba a farko na wofantar dasu, a yanzu tsakaninsa ga ALLAH yakeson meenal take sonsa, shiyyasama ya sanar mata gaskiyar shiɗin wanene.

      Duk da baba bai aminta dashiba ya jinjina zancesa sosai a rai, dan haka yace indai hakane to ya tattaro ya dawo gida, sannan zai tura da kansa zuwa nan auren meenal din, inhar aka wulakantasu to lallai yasani wlhy bazai auretaba, idan kuma ya bijire musu a wannan karon to zasu sallamasa gaba ɗaya.

      Duk da jikinsu yay sanyi da kalamansu ya amince da hakan, dan wlhy a wannan karon jiyake idan basu aminceba zai iya barin duniyarma gaba ɗaya.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


           Ummayya da Aneesa sun kawoma Dad miji kamar yanda ya umarta, shiko ya amsa tareda shiga yin bincike akan mazajen nasu, shidai baiga wata matsalaba a wajen samarin nasu, dan haka yabasu damar turowa.

     Cikin ƙankanin lokaci komai ya kammala, aka tsaida ranar biki dai-dai da ɗaurin auren Aunty Nurse.


     Momcy na murna zata aurar da ƴaƴanta, sannan tana fargabar kalmar dad ta jiran daki, danma dai Mansura nata dannarta da nuna mata tabisa ta makirci.

     Dad duk yana lura da halin da take ciki, amma yay biris da ita yashiga hidimar fita kunyar ƴaƴansa.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


          Su Ummukulsoom ƴan jami'a, karatu ake babu kama hannun yaro, yayinda suke ƙara samun ilimin zaman duniya da zama da jama'a. Zuwa yanzu kam turanci yafara zama bakinta, dayake akwai kaifin ƙwaƙwalwa ga burin na neman cikar alwashinta, kasancewarta mace mai murjajjen jiki saita kuma ƙara ɗan buɗewa, tai wata ƴar kuɓul-kuɓul da ita, kayan da Yaa Amaan yakira na ƙwaila suka fara cikowa ɗas.

     Koda yaushe tana waya da kowanta, Babanta, Aziza, inna harira, Gwaggo hinde idan baba yaje ɗilau, hakama ƴan uwanta inhar baba na ɗilau, Ummi, Maman Ahmad, yaya zaid danma shi bata wani sakar masa jiki saboda a salon da yake zuwa mata.


     

 ⛹🏻‍♀️ Ummukulsoom ɗinmu ta mutunci acigaba da gashi🤣👍🏻



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


         Shagalin biki a gidan Dad ya kankama, dankuwa nanda kwanaki Huɗu za'a ɗaura auren yaya Ameer, Ummayya, Aneesa da aunty Nurse.

     Kowa kagani yana tare da farin ciki, sai dai Hajiya Jamila nata kam akwai rauni, tanata dai yaƙe a fuska.

       Duk wani abun ƴan gata shi ake musu, hakanne yasakasu jinsu a sama.

        Duk wasu bidi'oi anyisu, kasancewar su Momcy ƴan abama bidi'a haƙintane babu algus🤣.

         Ummi ma duk tana halartar bikin, hakama yaya zaid daya kasance abokin Yaya Ameer.

       Ranar ɗaurin aure aka ɗaura na aunty Nurse sannan Ummayya sai Aneesa. Zuwa sallar zuhur aka ɗauro na Ameer shima da tasa amaryar.

        Aranar aka kai amare ɗakunansu bayan an halarci dinner ɗin da Yaa Amaan ya ɗauki nauyin yi dukda baya ƙasar, wayama saiya shari wata biyu basuyi da waniba saboda yanayin da suke ciki a ƙasar Syria, sunata fama da ƴan ta'adda abin babu sauki.

        Aunty Nurse ce dai bata tareba sai bayan kwanaki biyar da gama nasu Ummayya, batawani yi taroba, mijinta Abdul-hakeem yazo ya ɗauketa bayan Dad yay musu nasiha mai ratsa jiki da addu'ar zaman lafiya, sannan yayma ƴarsa rakkiya har gidanta itada mijinta a garin Abuja.


     Zuwa yanzu dai gida yadawo tsitt, daga Momcy sai Dad da Buhayyah, Bassam ma ana gama biki yakoma Kano makaranta.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


         Ɓangaren Baseer ma zamu iya cewa burinsa ya cika, dan kuwa a wannan karon iyayen Meenal sunsha banban da sauran surukansa, tarba ta girmamawa sukaima su baba da sukaje masa neman aure, hakanne yasaka zukatansu kwanciya waje ɗaya har aka tsaida ranar ɗaurin aure.

          Wata ɗaya da Sati biyu na cika aka ɗaura masa aure da Meenal ɗinsa ƴar mutan katsinawa, wadda acan aka ɗauro auren.

        Lubna da Fannah da basusan abinda ke faruwaba saidai sukai karo da text massege nashi kowacce da zanen saki biyu.

     Lallai sun tsinci kansu a matuƙar tashin hankali, dan aranar Fannah a asibiti ta kwana, Lubna kam ai ba'a magana, ga tabon rashin mahaifi gana Baseer, duk Number sa data sani saida aka nema, amma dukya karya layukan, tashin hankalin rashin mahaifinsune ya hana yayyenta maida hankali ga matsalar Baseer ɗin, kowa yayta lallashinta, ga yarsu daya barmata.


        An ɗaura aure da kwanaki biyu Baseer suka ɗage paris shida amaryarsa Meenal.

      A wannan karon kam hankali baba da inna yaɗan kwanta, hakanne yasa basu damu da tafiyar ta baseer ba, fatansu dai ALLAH yasa dattakon iyayen Meenal yazama silar nitsuwarsa waje ɗaya kawai............✍🏻



NO. 26



............Rayuwa ta cigaba da shuɗawa, yau da gobe kayan ALLAH, tun ana ƙirgen kwanaki har aka koma sati, aka koma wattanin da suka ƙulla shekara, kafin wani dogon zango saigasu Ummukulsoom da shekaru huɗu a makaranta, karatu yayi nisa sosai, yayinda nasarori da ƙalubale ke ƙaruwa, to dama rayuwa ta gaji haka, dolene wataran ayi kuka wataran takaici wataran al'ajabi wataran kuma dariya, abinda kawai ke saka nutsuwa a zuciyar bawa shine haƙuri da karɓar ƙadda ta nasara ko faɗuwa, godiya ga ALLAH alokacin daya baka koda kaɗanne, rintse ido daga hangen nasama ka kula da wanda bai kaikaba, karɓar da hannu biyu daga nasarar sa'a ko faɗuwa, dan duk wanda yashigo duniya yasa a ransa makarantace ita, lokacin da wancan ke zuwa aji na gaba sannan wani ke dawowa baya maimaita ajin kokuma barin makarantar baki ɗaya.

       Ummukulsoom tayi imani da waɗannan ƙalubalen a rayuwarta shiyyasa ta kwantar da hankalinta wajen maida hankali ga karatunta na boko dana islamiyya da Dad yazo da kansa ya sama musu. dan masu iya magana kance komai iliminka idan baka neman wani to lallai zaka rasa gaba ɗaya, kokuma kazama a jerin masu kafa tasu gidauniyar ta ɓata bisaga bigiren yarda da kai.

     Ƙwarai da gaske Ummu ta canja a shekarunnan, danta sake girma da cika, a wanda ya santama ya ganta a yanzu idan ba faɗa maka akaiba bazaka shaidata ba, ga wata nustuwa da hankali data ƙara, tareda aji irinnan manyan yara masu aiki da tarbiyyar addinin islama.

     Duk da kasan cewarsu acikin mafi rinjayen waɗanda ba musulmiba hakan baisa sun zubar da kimarsu da daraja ta ƴaƴan musulmaiba, basa shigar banza balle ballagazanci da sunan wayewa, akoda yaushe cikin taka tsantsan suke wajen girmama addininsu da al'adarsu, sun riƙe abinda yake nasu da hannu biyu, yayinda suka rintse idanu daga wanda bai dace dasuba ko bai zama mallakinsuba komai daɗinsa ko samun farin ciki daga garesa.

     Wannan rayuwar tasu saita fara tasiri a zuciyar Peace, tana mamakin dama haka musulmai keda ƙyaƙykyawar mu'amula ashe? Gasu mutane masu gaskiya da ƙarfafa kai, aduk lokacinda wata ƴar matsala ta shigo a karatunsu takan damu, amma saita su Ummukulsoom suna faɗin haka ALLAH ya ƙaddara, maybe wani tushen nasarace yasaka ubangiji jarabtarsu danyaga imaninsu, mai makon taga rauni tattare dasu sai taga tarin tawakkali da ƙarfin gwiwa.

       A ɓangaren ibada ko a ina suke lokacin salla yayi saisun sami wajen daya dace sunyita, ɓangaren mu'amularsu da maza akwai tsari, babu sakin fuska babu cuɗanya ta jiki sai dai da kuskure, Dakubo yayantane a gida ɗaya suke kwana suke tashi amma ko zama kusadasu basa bashi fuska balle taɓasu, sannan dukkan wani nau'in abinci ko nama da addininsu ya hanesu ci basa cinsa a gidan koda an girka, duk wani taro na shagala dasu jama'ar gidan zasuje su Bily basa  binsu, tasha roƙonsu su rakata Choch dan kawai jan ra'ayinsu amma saisu sami hanya mai sauki su waske mata, samari da yawa sukan nufesu da kalmar so ko ƙawance amma basu taɓa tozartasu ko cin zarafinsu ba, ta hanya mai sauƙi suke fahimtar dasu karatune yakawosu port ba soyayya ba, duk yanda wani shaiɗani yaso mu'amulantarsu sukan nemi tsarin  ALLAH da sharrinsa da gujema dukkan abinda zai ruɗesu da faɗawa tarkonsa.

       Rayuwarsu a wajen bata hanasu saka hijjab ba, bakuma ta ruɗesu saka farce a hannayensu ba ko ƙara gashin doki a kansu, daduk abinda addinin islam ya hanesu dashi, ako ina kuma basajin shakkar nuna su musulmaine bare jin kunya.

     Sunyi ƙawaye sosai yare daban-daban, sukan nema sani akan karatunsu ga wanda sukasan ya fisu, hakama wanda sukafi idan ya nemi taimakonsu sukan masa.

     Waɗannan kaɗanne daga nasarori dasu Ummukulsoom suka samu da cigaban rayuwa.

      A duk sanda suka sami sukuni kuma sakanzo gida suyi kwanaki su koma, hakama su Ummi sukanje su ziyarcesu aduk sanda suka sami ƙyaƙyƙyawar dama, kullum cikin musu nasiha suke da ƙara musu ƙwarin gwiwa tareda tsoratar dasu bijirema ALLAH da gangan saboda ruɗin duniya da tunanin ALLAH bazai kamaka ba wataran.

        Haka rayuwar taci gaba da matsawa har suka kusa shefe wata shekarar, a yanzu haka watanni ƙalilanne suka rage musu kammala karatunsu, musamman ma Ummukulsoom, dan ita bily ma tana gab kasancewar ba tsarinsu ɗaya baneba.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


       Shekarar su yaa Amaan huɗu cikin ta biyar suka dawo ƙasarsu ta haihuwa, dukda kasancewar yaƙine ya kaisu akwai cigaba tattare da tafiyar tasu mai yawa.

     Ƴan uwa da abokan arziƙi sunyi farin ciki matuƙa da ganinsu, tareda godiya ga ubangijin daya basu ƙwarin gwiwa da nasara.

          

          Lokacin da Attahir sukaje dubasu Ummu shida maman Ahmad ba ƙaramin mamaki ya shaba da ganin Ummukulsoom gaba ɗayanta ta canja, sai jinjina kai yake da sake girmama sunan ALLAH, wlhy koshi da ace a hanya yagamu da ita bazai taɓa shaidata ba, komanta ya canja tazama big girl ta gaske.

     Baisan wata dariyar shaƙiyanci ta kufce masaba lokacin da Amaan ya faɗo masa a rai.

         Lallai yana tausayin ƴan maza, ashe lokacin wasan yayi, dan angama gyara filin ga ƙwallo ga ƴan kallon wasa harma da alƙalan wasa a gefe.


      Cike da zolaya ya kalli Ummu yana faɗin “Ummukulsoom baki tambayeni ina mutuminba?”.

       Fararen idanunta ta ɗago ta kallesa, cikin muryarta mai sanyi da tarin nutsuwa tace, “Yaya Attahir wanene mutumin kuma?”.

       Murmushinsa ya faɗaɗa sosai yana kuma kallon ƙyakykyawar fuskarta, “Lallai na kuma yarda ƙanwata ta girma, to tundama kin mantashi bara na tuna miki, abokina Ajiwa”.

      Cikin halin ko in kula tace, “Yaya kenan, shida ba sallah ba yaza ai nai saving nashi a memory na dan gudun kiyayewa, shiba azumiba balle yazama cikin rubutattun ayukana na wajibi, mai riƙewa da adalci shike riƙe zuciya, mai ƙyautatawa da nasibi shike zane a dutse tamkar ruwa mai yaɗuwa a ƙorama, duk wanda kura ta koroshi a tafiya to ka tabbata bazai sake bin hanyarba, idan kaga an riƙe to ɗayan biyune, mosoyin na gaskiya, ko malami mafi kulawa akan ɗalibi, dan ba a taɓa mantawa da abubuwa uku, mutuwa, hisabi, makoma, tsoron ALLAH kesa a tuna mutuwa, Imani kesa a tuna makoma, ƙyaƙyƙyawan buri kesa a tuna alajanna, shikuma baya jerin ko ɗaya aciki, mizaisa yazama abin tunawata”.

        Kai Attahir ya jinjina cikin fadaɗa murmushin fuskarsa, lallai duk bulalar daka raina itake zanar ciki da bayanka kaji zafi har ƙarkashin zuciyarka, Ajiwa lokacin yayifa, ga wuri ga kuma waina, ƴan kallo saiku ƙara shiri.



       ⛹🏻‍♀️lallai zamusha kallo na haƙiƙa🤣😝



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


           “Fodio kana jinafa amma kaimin shiru ko?”.

      Manyan idanunsa daya gada a wajenta ya buɗe a kanta, cikin muryar nan tasa mai amo da izza yace, “Momcy bansan mizan cemiki ba nikam, danni ban shirya auren ƴar kowaba”.

     Harara ta zabga masa tareda watsa masa daƙƙuwa, “kaci gidanku Fodio, mikake nufi? Ba zakayi aureba a rayuwarka komi?”

     Numfashi ya firzar tareda lumshe idanunsa ya buɗe a kanta, sai dai yaƙi cewa komai.

      “Wai miye ka tsuramin waɗannan idanun?”.

    Karan farko da ya saki murmushin gefen baki wanda na tabbata da wata macen yaymawa saita kuma sumewa, bayi yakeba shiyyasa idan yayi saiya kasance na musamman, ita kanta Momcy da ta haifesa saida ta hangame baki, “O ALLAH, Fodio dan ALLAH karinga koda murmushi ne a rayuwarka, ba ƙaramin ƙyau yake makaba wlhy, amma ina daɗi ko yaushe fuska ɗinke kamar wanda aka haifa mala'ikun rahama basa kusa”.

     Kansa kawai yaɗan dafe amma baice mata komaiba, yakuma maida fuskar ya ƙara haɗewa.

    Dad dake bayansu tuni, yaɗan girgiza kansa kafin ya ida shigowa falon da sallama ciki-ciki kamar yanda ya saba.

     Duk amsawa sukai, Hajiya Jamila dake kallonsa a ranta ayyanawa take “Oh ni jamila, wannan wane irin mutane ALLAH ya haɗani dasu, nikam nama ƙagara Bassam ya kammala karatunnan yadawo ko haƙoransa na rinƙa gani naji daɗi, amma kana tare da waɗannan ai dole ka zata kullum wani nasu ke mutuwa”.

    Sudai basu san tanaiba, dan Amaan ma tashi yay yafice abinsa, dama abinci yazo ci, bayan yagamane yaɗan kwanta a falon yana hutawa kasancewar yanzu gidan nasu babu hayaniyar kowa, daga Momcy sai Dad, saiko idan ƴaƴan aunty Ummy su zo, yarinyar Ameer ma ba kawota akeba sai dai idan uwarta tazo gidan, hakama Ummayya yaronta sai tazo take zuwa dashi, Aneesa kam yanzune take da cikin, itakuma Aunty Nurse tana abuja abinta da ƴaƴanta tagwaye itama data haifa duk maza, inba zuwa taiba ba ganinsu akeba. Sai ƴan aiki wanda kuma dokace shigowarsu sashen musamman da ayanzu Yaa Amaan ɗin yana a gidan.


         “Abban Fodio wai kana ganin haka zamu cigaba da zubama Fodio ido bazai yi aureba kenan? Ga ƴan uwansa kowanne har da ɗansa ko ƴarsa a gabansa, ko Buhayyah akaima aure yanzu haihuwa zatayi itama”.

     Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa, bai tankaba baikuma sake kallontaba.

     Jigum tai tana kallonsa, ranta duk a jagule, a tsawon shekaru huɗunan gaba ɗaya Alhaji Mahmud ya canja mata, ya daina hira da ita, abinci ma saiya gadama yake ci, baya shawarar komai da ita, komai saidai taga yayisa batareda yace da ita uffanba, ko dawowar Fodio dukda yasani ƙin sanar mata yayi, sai dai kawai ta gansa, hakama tafiyar Buhayyah makaranta, lamarin na matuƙar damunta sosai, ta bashi haƙuri yace ya haƙura amma yaƙi sake mata kamar da, ga kaɗaici da take fama dashi a gidan, haka take yini kamar wata mayya, dawowar Fodio ma bawani rage mata kaɗaici tayiba, tunda ba zama yake suyi hiraba sai yaso. Garama idan su Ummayya ne sukazo, sukuma Dad ya kafa musu dokar sai da ƙwaƙwƙwaran abu zasu zo masa gida.......

     Ganin zai tashi tai saurin miƙewa itama tana marairaice murya, “Haba Abban Fodio dan ALLAH ka saurareni mana, wlhy rashin auren yaronnan yana damuna, kar muna nan sake da baki ya saka kansa a halin neman mata”.

      Bakinsa ya taɓe yana rabawa ta gefenta zai fice, “Ashe kina tsoron ya nemi matan kika sakashi rabuwa da wadda ALLAH ya halatta masa? Saiki dage ki masa aure na ƙwarya tabi ƙwarya ga ƴaƴan manyan mutane cike da gari, ai baikamata ma kizo guna neman shawara ba uwar ɗa”.

       Sosai zancensa ke tsitstsinka zuciyarta, wai har yanzu zancennan yana ransa kenan? Miyasa Abban Fodio keda riƙo irin haka? Abu kusan shekara biyar yakasa goguwa a ransa, yarinyarma ƙila yanzu tagama rakwaɓewa a ƙauye, yanzu hakama tayi haihuwa ƙila tafi huɗu. Jagwaf ta koma ta zauna a kujera yayinda zufa ta jiketa, kardai Abban Fodio yace ya cire hannunsa akan lamarinsa, hakan ba karamar masifa bace a gareta, dan bazata iya tanƙwara Fodio ba ita kaɗai sai da taimakonsa, musamman akan abinda bashi yace yana soba, shegen taurin kasa daya gada a gurinsa shine babbar damuwarta dashi. 

    Ta matuƙar daɗewa a wajen tana saƙawa da kwancewa, yayinda maganar mahaifiyarta ke kuma girgiza ranta, *“Jamila kinyi kuskuren saka Usman ya bijirema mahaifinsa akan aƙida mara amfani, to kisanifa wlhy wataran kezai bijiremawa, dan ƙofa kika nuna masa ta daina muku biyayya akan dukkan abinda kuka ɗorasa akai, kekanki kinsan shegen murɗin halin wannan yaron da taurin zuciya, ko bayan ba raina saikin tina wannan maganar a lokacin dakikaso tankwarasa akan umarninki ya kasa tankwaruwa”*.

     Ta taune leɓe da karfi tana faɗin “Ina hakanma bazai yuwuba mama, babu ɗan dazan haifa a cikina ya isa mijirema umarnina, sakin yarinya danasa yayi kuwa ai nafi mahaifinsa gaskiya, dan kowa yana bukatar cigaba a rayuwa baci bayaba, dolene na zaɓama Fodio matar aure da kaina a wannan karon inhar bashida zaɓin kansa”.

       Wani murmushi Dad dake jiyota daga bedroom ɗinsa yayi, ya jinjina kansa.


     Duk yanda Momcy taso Dad yabata haɗinkai a kan matsalar rashin auren Fodio ya watsar da ita yaƙi saurarenta, yakumaki yima Amaan ɗin maganar.

        Shima Yaa Amaan a satin yaje Ajiwa, kwanakinsa uku ya dawo, a ranar bai ƙwana a kd ba yanufi Lagos shida Attahir dan ana musu nema na gaggawa.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

   

            Haka rayuwar taci gaba da tafiya su Ummukulsoom suka fara jarabawar ƙarshe, gaba ɗaya ta gama tattara hankalinta can, fatanta nasara kawai daga ita har Bily.

          Yanzu hakama dukkan jama'ar gidan suna falo suna hira, sai dai banda Ummukulsoom dake zaune a ɗakinsu tana karatu, tana jiyo dariyarsu daga ɗakin har bily. Mafi yawan lokaci haka take batason yawan hayaniya yanzu, tafi bukatar kaɗaice kanta tai nazarin littatafansu na islamiyya kokuma na boko, wannan halayyar tata kansa mutane da yawa ɗaukarta mai tsananin ɗaukar kai, sam kuma ba haka bane, saika mu'amulanceta zaka fahimci halayyarta mai ƙyau.

          Haka kawai taji sha'awar kiran maman Ahmad su gaisa, tai dailing Number nata tare da sakawa a Hans free taci gaba da duba buk ɗin gabanta, sam Number taƙi shiga, hakanne yasata tunanin kiran Yaya Attahir maybe yana gida......


            Zaune suke da Attahir a Office suna tattaunawa akan maganar ƙarin girma da ake shirin musu, sai dai shi Amaan manyan nata masa zagon ƙasa saboda wani dalili nasu,  kiran Bily ne ya shigo wayar Attahir dan haka ya ɗaga yana faɗin “To autar Ummi ko accaunt yay ƙasane?”.

     Amaan dake zaune na saurarensa amma baice masa komaiba, har Attahir ya daga suka gaisa ya tambayeta ina bestie ɗinta?”.

      daga can bily tace, “Tana ɗaki yaya, kasanta ba gajiya da karatu takeba, ina aunty Hafsat da abokinka Yaa Amaan?”.

     “Ai haka akeso gara ku dage ku sami results masu kyau, Auntynku na gida, Ajiwa kam gamu a tare, zaiki gaidashi ne?”.

      “Wai yaya barshi, wanda a filima ko gaidashi kai bai amsawa da kyau inaga a waya, kace ina gaidashi dai”.

     “A'a ba ayi hakaba kedai gashi ku gaisa”.

    Kafin Bily tace wani abu Attahir ya mikama Amaan wayar yana mikewa da faɗin, “Autar Ummi ce zata gaisheka, bara naje toilet”.

       Uffan baicema Attahir ba, amma yakai wayar kunne da nufin amsawa, saboda bazai iya ƙin jinin Attahir ba, ballema Bily tanada hankali yarinyar.

      A lokacin da Yaa Amaan ke ƙokari kai wayar kunnensane Bily kuma daga can ta yanke saboda tsorata, dan harga ALLAH bazata iya yin waya dashiba.

    Jin wayar ta tsinke ne yasashi jan karamin tsaki yana niyyar ajewa kira ya shigo, screen ɗin ya tsurama ido, *_My Sister_* da ya gani, ya sashi tunanin ko bily ce ta sake kira, dan haka tana gab da tsinkewa ya ɗaga tareda saka wayar a kunnensa yakoma jikin kujera ya lafe yana lumshe idanu.

        daga can Ummu tai murmushi jin Attahir ya ɗaga, cike da nutsuwa tace, “Assalamu alaika yayana!”.

      Wani irin yarrr Amaan dake saurarenta yaji, babu shiri ya buɗe lumsassun idanunsa yana jawo numfashi da ƙarfi, karan farko a rayuwarsa da sautin muryar mace ta sashi jin wani yanayi, baki ya buɗe zai amsa daga can Ummu daduk ta ɗauka Attahir ne ta katseshi cikin shagwaɓa da faɗin, “Yayana yau ƴar shiruce abin, shikenan namayi fushi”.

      Yanzunkam da ƙarfi ya rumtse idon tareda haɗiye tsargawar da zuciyarsa ke nemanyi, sanin inhar tacigaba da magana zai iya cutuwa yasashi saurin katseta kar a samu matsala, can ƙasan maƙoshi yace, “Kina lafiya? Ya karatu?”.

     Gabantane ya faɗi itama, jin muryar dabata yaya Attahir ba, tace, “Ya ALLAH, bawan ALLAH ina mai wayar?”.

      Sosai ya buɗe idanunsa akan Attahir daya fito daga bayin dake cikin Office ɗin, batareda ya bata amsaba ya ajiye wayar yana faɗin, “Kai malam da wace uwar iyayi ka haɗani?”.

     “Uwar iyayi kuma?" Attahir ya faɗa yana karasowa ya ɗauki wayar, idanu ya waro ganin Ummukulsoom, baisan dariya tazo masaba, yay azamar danne bakinsa tareda ɗora wayar a kunne yana faɗin, “Sorry Autar Ummi bana kusane ykk?”.

        daga can Ummu tace, “ALLAH yaya Attahir harna fara tunanin faɗar baƙar magana, wanene wannan ya ɗaga wayar yanata mutane gwalli kamar wani mace?”.

     “Tofa anzo wajen, bar wancan batun, minene labari?”.

     “Babu komai, kira nai mu gaisa kawai dama ka kuma haɗani da Aunty Hafsat”.

      “Im yanzu dai kika faɗi gaskiya, kindai nema Number kawarki baki samuba kika kirani, to ina wajen aiki idan na koma zan kira”.

      “To yaya na gode, ammafa hasashenka ba gaskiya bane”.

    Bata jira cewarsaba ta yanke wayar cikeda takaicin wanda yafara ɗaga mata waya........✍🏻


[2/21, 9:08 PM] ❣️Noor-ur-Rahman❣️: *_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_* 


*_Daurin boye_*

_safiyya huguma_

*_Buri daya_*

_mamuhgee_

*_Wutsiyar rakumi_*

_billyn Abdul_

*_Kai min halacci_*

_Miss xoxo_

*_Sauyin qaddara_*

_hafsat rano_



*08030811300*

*07067124863*


                   *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*

  


*_NO. 27_*



   ............“Wai lafiya kaketa zabgamin harara Ajiwa? Naga kaika ɗaga wayarnan da hannunka bani na bakaba, to miye laifina da zakaita watsamin waɗannan mayun idanun damin tsoki?”.

       Yanzunma tsakin yaja tareda ɗauke itanunsa daga kan Attahir, takardun gabansa ya tattara waje ɗaya yamike ya fice daga Office ɗin.

     Da kallo Attahir ya bisa yana dariya ƙasa-ƙasa.

     Dukda yaji dariyar ta Attahir bai kulasaba ya fice abinsa yana jin wani irin takaicin da baisan daliliba.

          Sosai Attahir ya kwashe da dariya yana dukan tebir ɗin gabansa, “Ajiwa manyan ƙasa”. Ya faɗa  Shima tare da miƙewa ya fice abinsa.


       Koda ya koma gida har dare abu kamar wasa yaƙi barin ransa, duk yanda yaso yakice muryar yarinyar aransa ya kasa, wannan wace irin masifa ce haka, Bily da aka haifa a gabansu itace har take neman zamema ransa matsala (duk ɗaukarsa bily ce), “Mtsoww anyama banzannan Attahir bashi ya shirya ba?”. Yay maganar a fili cike da takaici.

       Tun fa yana ɗaukar lamarin da sauƙi harya zame masa abin tunani lokaci-lokaci, harma zuciyarsa na buƙatar sakejin muryarta, sai dai tsabar baƙin miskilanci yahana koda a fuska ya nunama wani.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


        Ɓangaren Ummukulsoom kam tuni tama manta da wani batun wayar da sukayi, dan karatunta taci gaba dayi harsu Bily suka shigo, sun ɗan taɓa hirarsu daga nan suka kwanta.


★★★★


          Su Ummukulsoom sun cigaba da Exam cikin aminci da fatan nasara, kulum cikin kaima ALLAH kukansu suke tareda ƙwazo a exam ɗin, ahaka suka kwashe watanni har yau gasu ALLAH ya kaisu ga nasarar gamawa, ranar Ummu tasha kukan daɗi, duk da dai tanada sauran karatu na shekara ɗaya a gabanta kafin tazama Barrister ta gaskiya.

        Ansha shagalin bikin yaye ɗalibai, wanda ya kayatar ya ajiye tarihi, Ummukulsoom tana ɗaya daga cikin ɗaliban dasuka sami ƙyauta aword na ɗalibai mafi ƙwazo, hakanne yasaka Dad matuƙar jin farin ciki, dan shida Abba da Ummi yaya Attahir, Yaya Zaid, maman Ahmad suka halarci taron, kowa yanata saka musu albarka tareda taya murna.

       Aranar suka baro port harcourt cikeda kewar su Peace wadda taita kuka, dan ba ƙaramar shaƙuwa bace mai yawa ta shiga tsakanin wannan ahali dasu Ummukulsoom, shiyyasa bazasu taɓa mantawa da suba, dolene su dinga kawo ziyara a kai akai kamar yanda suma sukayi alƙawarin kawo musu.

     

     Koda suka dawo KD ma wata ƴar kwarƙwaryar walima Abba da Dad suka shiryama su Ummukulsoom bayan sati biyu da dawowarsu, bawani uwar gayya akaiba, maƙwaftane sai kuma makusantansu da dai wanda baza'a tasaba.

         Tun safe su Ummi basu zaunaba, dan shirye-shiye suketayi na abincin da za'aci da sauran kayan maƙulashe Zuwa ƙarfe biyu na rana iya waɗanda aka gayyata suka fara isowa, harda Hajiya Momcy itada Buhayyah da tazo hutu, yaukuma shine karon farko da zasu haɗu da Ummukulsoom a gidan, dan duk zamanta a gidan hajiya jamila bata taɓa zuwa ta isketaba.

       Zuwa kusan Uku saiga Inna harira tare da Aziza, sam Momcy bata wayi Aziza ba, kasancewar itama ta kara girma yanzu, sannan ko acan da bawani farin sani Momcy tai mataba, tunda kota shiga gidan wajen Ummu ba sakar musu fuska takeba.

      Aziza ɗakin su Ummu ta shige inda mai ƙwalliya take shiryasu.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


               “Attahir ka takurama rayuwata fa da yawa”.

      “kaine kaja na takura makan ai Ajiwa, katashi ka shirya Please, 4pm fa za'a fara walimar nan, gashi kuma har 3:12pm yaushe ka gama shirinka har muka tafi dan ALLAH,  a dai gaban Abba ka amsa zakaje balle yauma ka shikama mutane rashin arziƙinka daka iya  kaƙi zuwa”.

      Banza yay masa yaƙi amsawa, shi yama rasa wane abune ya shiga kansa harya amsa zuwa kd a weekend ɗinnan, da ba'a takura masa da wannan kayan takaicinba.

      Miƙewa yay yashige bedroom ɗinsa yabar Attahir kaɗai a falo.

     Gwalo Attahir yayma bayan Amaan yana faɗin ɗan rainim wayo sai kaje dai insha ALLAH.

      Shidai baisan yanaiba, kasancewar bai wani jima da wankaba yasashi ƙokarin shiryawa, harya ɗakko ƙananun kaya saikuma ya maida yana jan ƙaramin tsoki, Dad yasha masa gargaɗi saka manyan kaya a duk lokacin da irin wannan abun ya taso, kansa ya dafe yana mai tsirama kayansa idanu, shi yama manta rabon da yasakama jikinsa manyan kaya, dama sai in zaije Ajiwa ne kokuma ranar juma'a, saiko in tafiya ta haɗashi da Dad dole, yana shiri yana kuma ɓata fuska saikace dole.


       Kamshin mayen  turarensa ne ya saka Attahir ɗagowa ya kallesa, a hankali ya furta “Masha ALLAH a saman laɓansa saboda ganin ƙyawun da Yaa Amaan yay masa, yau dai kam ya fito a asalin bahaushensa ɗan asali ba sojan Nigeria ba.

      Sanye yake cikin shadda gizna ƴar gaske kalar bulu mai duhu, ɗinkin zamani dogon wando da riga mai gajeren hannu, kasan cewarta babu wani tsawo, kaɗan rigar ta wuce ɗuwawunsa, ɗinkin ya zauna masa ɗas dai-dai da halittarsa, yayin da ƙyawun haiba da kwarjinin musulinci ke yawo bisa kamilalliyar fuskarsa ma'abociya tsare gida.

     Hularsa zanna ce a hannunsa ko kari bai mataba, sai agogon fata baƙi da yake koƙarin ɗaurama tsintsiyar hannunsa, ya sake tsuƙe fuska saboda kar Attahir ya tasashi gaba da tsiya kamar yanda ya saba idan yaga yasa manyan kaya.

       Fahimtar hakan da Attahir yayine yasashi yin ƴar dariya yana mikewa, “Oh ALLAH, Ajiwa ina roƙon ALLAH yasa kar wankannan naka ya tafi a banza, ALLAH yasa yau dai kayi kasuwa wata ta kyasa, mun gaji da zawarcin dakakeyi wlhy”.

       Idanunsa ya lumshe ya buɗe akan Attahir tareda ciza lip nashi alamar zan kamakane.

      Attahir yakuma sanya dariya, “To miye na fusatar?, kowadai yasan kai bazawarine yanzu wlhy tunda ka taɓa aure malam”.

      Ƙin kulasa yay ya nufi hanyar fita yana gyara karin hularsa, Attahir ya kwashe da dariya, yasan ya kaisa maƙura shiyyasa yagaza bashi amsa, shika ɗaine ke iya taɓa Ajiwa fiyema da haka a zauna lafiya, dan suna matuƙar ƙaunar juna, shikaɗai yake iya sanin damuwar Ajiwa ko sirrinsa, kamar shima Ajiwan ne kawai ke iya sanin nasa sirrin da damuwar.

     Fitowa yay shima dan yasan yanda yakaisa bango kaɗan daga aikinsa ya tafi ya barsa a gidan. Ilai kuwa, iskewa yay isa na ƙokarin buɗe masa mazaunin driver alamar shinema da kansa yau zai tuƙa motar, abinda kakan daɗe bakaga yayiba.

     Buɗe gefensa yay da sauri ya shiga.

    Amaan ya Kashe Motar yana kallon Attahir cikin harara, “Malam kasanifa bazan tuƙa ƙaton banza ba”.

       “Kam bala'i Ajiwa wai nine ƙaton banza?”.

      “Inba ƙaton banzaba uwar miye? Dalla fitarmin a mota kaje ka hau taka da kazo a ciki”.

      “Anƙi a fitan, idan kaga dama ka zubar dani a hanya bazawari kawa.....”

     Naushin ya kawoma fuskar Attahir yay saurin kaucewa yana dariya, “Tab yi haƙuri mazan fama, miyay zafi zaka juye fushin gwairantakar ka a fuskata kaima matata asara da amaryar dazan ƙaro”.

      “Mtsoww banza na mamajo”. Amaan yafaɗa yana tada motar.”

         “Uhm babu komai, nadai fi bazawari tuzuru mara aure mai kwannan shago da filo a ƙirji”.

      Wani lalataccen murmushi ya saki yana girgiza kai, Attahir na latsasa yanda yaso, shi kaɗaine kemasa irin hakan baiji komaiba, saboda tsantsar ƙaunar da yake masa a rayuwa, bai sake kulashiba har suka ɗau hanyar gidansu Attahir ɗin, saima karatun Qur'an daya sanya a motar.

    Hakanne yasaka Attahir shima yaja bakinsa yay shiru yana sauraren karatun.

     Har suka iso gidan bakinsu bai saɓaba, kasancewar harabar gidan babbabace sai basu ajiye motar a wajeba suka shige ciki...


★★★★★


        Su Ummukulsoom kam suna ɗakinsu, duk hidimar tarbar zuwan baƙin da akeyi basu fitoba, sunsha ƙyau itada Bily cikin golden color ɗin gown ta Material, ɗinkin ya zauna musu a jiki ƙwarai da gaske, ɗan kwalinma da aka naɗa musu akai golden, kai komai nasu kalar golden ne, danma ƙiri-ƙiri Ummukulsoom ta hana ai mata kwalliya mai yawa a fuska, hakan yasaka itama Bily cewa ai mata ƴar dai-dai, amma hakan bai hanasu yin ƙyawuba sosai.

          Ƙyawun dasuka shane ya sanya Aziza dagewa tanata zuba musu hotuna a waya dukda Ummukulsoom nata kaucewa bataso.

        “Waike Ummu mike damun kankine? Dalla malama ki tsaya na ɗauki hotuna son raina?”.

     Harara Ummukulsoom ta zuba mata, taja gyale zata yafa Bily ta riƙe, “Malama wlhy baki isaba, dagani harke babu wanda zai saka wani gyale”.

        “Amma dai bily sanin kankine bazan iya fita hakaba ko?”.

      “To sannu matar liman, aiko dole ki iya, naga bawani taron maza bane balle kice, daga iyayenmu sai yayyenmu sai ƙanne da ƙawaye.......”

      Kafin Ummu ta bata amsa tajiyo Ummi na kiranta, dan haka ta sakarma Bily gyalen tarefa yin ƙwafa ta fita tana amsawa.

       “Woow autata kece haka kamar zan kaiku gidan aure?”.

     Hannu Ummukulsoom tasa ta rufe fuska tana faɗin “Kai Ummi”.

      “ALLAH kuwa kin ganki kuwa kamar na sace na ɓoye”.

     Kuma rufe fuskar tayi tana dariya ƙasa-ƙasa, Ummi ta rungumeta tana kuma yaba ƙyawun da Ummukulsoom ɗin tayi, yarinyar akwai sura mai ƙyau, hannunta ta kama suka nufi ɗakinta.

     Sarƙoƙine masu ƙyau da abin hannu guda biyu a kan gadon da Ummi ta ajiye, ta zaunar da Ummukulsoom gefe tana nuna mata, “Ummuna zaɓi wadda tai miki anan”.

    Cike da tsatsan so da ƙauna Ummukulsoom ta kalleta, tuni wasu hawayen farin ciki sun taru mata cikin fararen idanunta, a hankali tace, “Ummi mizan saka muku dashi ku tabbatar daku na dabanne a zuciyata da rayuwata, Um......”

     Cikin ƙatseta Ummi ta ɗaga mata hannu, “Ki ɗaukemu matsayin iyaye kawai ya wadatar damu Ummukulsoom, karna sake jin makamancin wannan a gareki kinji, inajinki araina kamar yanda nakejin su Bily, inhar bazasuyi tunanin mana ramako da haihuwarsuba kema karki taɓa tunanin yin hakan, tsakanin iyaye da ƴaƴa babu ramako sai jinƙai”.

     “Hakane Ummi, ALLAH yay muku sakamako da Aljannah, yabamu ikon muku biyyaya da jin ƙanku”.

     “Amin ya rabbi dear, wacce kika ɗauka na saka miki?”.

      Ta gabanta kawai ta nuna, dan sarƙokin duk sun haɗu, babu wacce tafi wata.

    Ummi da kanta ta sakama Ummukulsoom sannan ta fita ta kira Bily itama, tuni suka ƙara haskawa da wani mugun kyau, ga turare da Ummu ta kuma feshesu dashi tana ƙara gwarzanta ƙyawun da sukayi.

     Hanasu fita Ummi tayi tace su zauna a ɗakinta tana zuwa.

    Da to suka amsa mata, suka zauna suna ƴar hirarsu da Peace a waya suna bata labarin abinda ke faruwa, itako sai jaddada musu take ai mata video ɗin komai a tura mata.

   Sunata mata dariya kuwa.


      Duk wanda ya dace ya iso yazo, gidan yacika da ƴar hayaniya kaɗan musamman ta ƙananun yara dake wasa.

   Hakan ne yasaka Amaan jin bazai iya zama ba a wajen taronba, dama tunda suka iso yana falon Attahir zaune, sai yanzune suka fito, dukda kowa ya nemi mazauni fitowarsu Ummukulsoom kawai ake jira dasu Dad sai yaki zama.

       

     Ummi da kanta tazo ta fita dasu Ummukulsoom, nanfa kallo ya koma sama, kowa sai maimaita masha ALLAH yake a ransa, Momcy da zuciyarta ta gama narkewa akana ƴammatan da suka gama haɗuwa ayyanawa take a ranta lallaifa Fodion ta ya samu matar aure acikin waɗannan carkwaɗa-carkwaɗan ƴaƴan, yanzune zatai masa cikakken aure na ƙwarya tabi ƙwarya tamkar yanda mahaifinsa yay mata gatse.

      Inda aka tanada dominsu suka zauna.

     Zaid daya cika fam da kishi akan Ummukulsoom ne yay addu'ar buɗe taro, yau itace ranar da yaci burin sanarma Ummukulsoom sirrin zuciyarsa na tsawon shekaru biyar da wasu watanni da yaketa dako.

       Ita kanta Ummukulsoom jitai dukta takura saboda kallon da samarin abokan su Yaa Zaid ɗin ke musu na ƙurulla, sai faman bankama duk wanda suka haɗa ido harara takeyi, itafa gaba ɗaya harkar soyayya ko samari haushi suke bata yanzun.

     Aziza ce ta taso a nutse ta kawo mata waya da Baba yay kira, danshi bai samu zuwaba yana ɗilau.

    Karɓa Ummukulsoom tayi ta miƙe domin keɓewa gefe guda ta amsa.

      Tacan baya sashen Yaya Attahir ta nufa, dan daga canne kawai bazaka iya jin hayaniyarba.

 

          Zaune yake tacan bayan ɗakunan sashen Attahir inda bayajiyo hayaniyar sosai, wajen Attahir ya gyarasa sosai saboda hutawa, kansa jingine da kujera ido a lumshe ya tafi duniyar tunani.

      Sautin takun mutum ya fara jiyowa kafin zazzaƙar muryar ta mai fita da nutsuwa, sosai gabansa ya faɗi danjin muryar da bazai taɓa mantawaba, ya tabbata ko a cikin barci ya jita saiya gane balle a zahiri. Ya kuma buɗe hancinsa yana zuƙar mayataccen ƙamshin Khumra daya haɗu da turare a jikinta.

     Dukda ƙwaɗayin ganin mamallakiyar muryar da yakeyi hakan baisashi yin ko motsiba balle buɗe idanu saboda tsabar miskilanci da jin kai.

     Sam Ummukulsoom bata lura da mutum ba a wajen, dan haka take kuma narke murya tana zubama Baba shagwaɓa akan rashin zuwansa walimar, sannan babu ko ɗaya daga cikin yayunta da yazo, danma Inna harira da Aziza na nan.

      Kasa jurewa da zuciyarsa tayine,  yasakashi Buɗe idanunsa a hankali, akan bayanta data juya masa ya sauke, yanda rigar ta fita da ainahin surarta ne yasaka numfashinsa yin sama yay kasa saida yay kokawar tarbosa ya haɗiyi yawu dake neman daskare masa da a ƙirji, sam duk yanda yaso ɗauke idonsa ya kasa, babban burinsama ta juyo yaga wacece ita....

     Isowar Zaid wajen batareda Ummukulsoom ta fargaba yasata tsorata ta ɗan zabura tana yanke wayar.

    Saurin riko hannunta Zaid yayi ganin zata zube ƙasa saboda tuzguɗewar da takalman ƙafarta sukayi kasan cewarsu masu tsini..

    Tai azamar son fizge hannunta ta dafa flowers ɗin dake wajen, dan bata buƙatar yaya Zaid ya taɓata, sai dai kuma aka samu akasi ɗayan takalmin ma ya tuzguɗe tai baya zata faɗi gaba ɗayanta.

     Shi kansa baisan lokacin daya baro inda yake zauneba yazo yay azamar fisgota ta faɗo jikinsa saboda ganin Zaid na shirin haɗata da jikinsa danya bata taimako daga faɗuwar da take shirin yin.

      Da ƙarfi Ummukulsoom ta rumtse idanunta saboda takaicin faruwar abinda take gudu fiyema da zatonta, sai dai abinda ya ɗaure kanta sam ba ƙamshin turaren Yaya Zaid take shaƙaba, jikinma yasha banban dana yaya Zaid ɗin zata iya cewa. 

    Ƙoƙarin janye jikinta tayi yay saurin fara tureta yana haɗe fuska fiye da ko yaushe, kafin yaja siririn tsaki batareda ya ko kalli fuskartaba ya raɓa gefenta yabar wajan yana harar Zaid dake tsaye kamar gunki yana kallon ikon ALLAH daga Yaya Amaan, shi sam baiga sanda yazo wajenba, sai Ummukulsoom daya gani kwance a ƙirji sa.

        Baki hangame Ummukulsoom tabi bayansa da kallo, cikin takaicin tsoron da Zaid yazama silar bata tace, “Shikuma wannan dangin tsakar daga ina? Waya bashi lasisin taɓani ma?”.

     Dukda yayi taku kusan biyar a tsakaninsu hakan bai hanashi jin abinda taceba, dan haka ya tsaya cak furucinta na dukan ƙahon zuciyarsa da ƙarfi....

     Azamar saka hannu Zaid yayi a bakinta jin zata kuma wani magana, ya ja hannunta suka shige ƙofar kicin din Maman Ahmad dake a wajen.

      Hakanne yasa koda Amaan ya juyo domin ganin wannan tsagerar yarinyar sai yaga shigewarsu ciki kawai, da ƙarfi ya rumtse idanunsa tareda shafar girarsa da ɗan yatsa ya yarfar da hannun.........

      “Ajiwa dama kana nan naketa nemanka?”.

       Haɗiye abinda ya tokare maƙoshinsa yayi sannan ya buɗe idanunsa dake a rumtse da harsun fara canja launi.

       Attahir da yay maganar ne ya kuma kafesa da idanu saboda mamakin yanayin daya ganshi, “Ajiwa lafiya kuwa?”.

        Batare da yasan maganar ta subuto daga bakinsa ba yace, “Yaushe Zaid yayi aure ban saniba?”.

       “Aure kuma? Zaid ɗinne zaiyi aure baka saniba? To miyasama kamin wannan tambayar?”.

        Fahimtar kato ɓarar da yake nemanyine yasakashi maidama Attahir amsarsa da harara ya raɓa gefensa yabar wajen.

     Da kallo kawai Attahir ya iya binsa, yayinda yake juya kalmar auren Zaid ɗin da Amaan yayi a ransa, yaɗan ɗage kafaɗa da taɓe baki alamar shiyya sani yajuya shima yabi bayansa.


       Su Ummukulsoom kam na shiga ta ture hannun Zaid dake kan bakinta tana fusge hannunta, “Yaya Zaid dan ALLAH kabar min irin haka banaso wlhy”.

         “Yi hakuri Ummukulsoom wlhy nima bada niyya nayiba, gani nai zaki ƙwanto mana ruwa haka kawai, kinsan kuwa wanene kike  jifa da kalmar dangin tsaka?”.

       Cikin halin ko in kula tace, “Oho yaya Zaid, nidai koma wanene ai gaskiya na faɗa, haka kawai yakama mana tsaki wani yace ya taimakeni? Ya barni na faɗin mana ai dai jikinane, ALLAH ya isana ma taɓanin da yay wlhy”.

       Sosai Zaid ya waro idanu yana hangame baki, sai dai kuma tai gaba ta fice binta tana gyara zaman ɗan kwalinta ranta duk a dagule, dolene ta cire kunya ta takama Zaid burki bisaga take-takensa da take gani, dan bazataso yazama sahun farko a cikin jerin mazan da zata ja a ƙasa ba kodan mutuncin ahalinsa a idonta.

     Binta da kallo yay harta fice, ya dafe kai tare da zubewa cikin kujerar falon, shikam baisan wane irin so yakema yarinyarnanba, amma sam takasa fahimtarsa tunba yauba, dukda iyakar iyawa yana yaɗa manufofinsa a zahiri gareta.


       Ummukulsoom kam na fita taci karo da Maman Ahmad data taho kiranta saboda ana bukatarta a wajen.......



Idan ka ga mutum yana tsarguwa da shiga cikin jama'a, shi maha'incine, idan kaga mutum yana fushi a wurin jayayya to maras hujja ne, idan ka ga mutum yana faɗa, ba shi da abin faɗi. Mai gaskiya mmba ya tsoron jama'a. Mai hujja ba ya fushi. Mai abin faɗa ba ya faɗa!.


NO. 28



   ..........Duk yanda yaso hana kansa zama wajen taron zuciyarsa sam taƙi aminta, burinta kawai taga a bincinta, shi kansa yana buƙatar ganin mamallakiyar muryar, danya fahimci tsagerace ta gaske.

     Daɗin daɗawa kuma tunda ya ɓillo da Dad ya fara tozali, yay masa wani kallo wanda yasan bai wuci gargaɗi ba akan ƙauracema zama wajen taron da yay.

      Tafiyarsa ya cigaba dayi a hankali har Attahir yazo ya iskoshi, babu wanda yacema wani uffan suka ƙarasa inda dama aka tanada dominsu.

      Zamansu baifi da minti biyu ba Ummukulsoom da Maman Ahmad suka dawo wajen suma, sai dai fa yanzu Ummu ta yafo gyale a jikinta. Hakanne ya saka Bily dan ƙara mata harara dayin ƙwafa alamar zan kamaki.

       Duk hidimar da ake a wajen taron Amaan yaƙi kallon kowa, sai faman latse-latse yake a waya, amma kunnensa yana a wajen gaba ɗaya.

      Ummukulsoom ma dai hankalinta baikai gareshi ba, sai Zaid daya addabi rayuwarta da kallo shida wane dake kusa dashi wanda take ƙyautata zaton Ameer ne, dama taga Momcy da Buhayyah a wajen tuni, amma sam bata kawoma ranta ganin Amaan ba.

       An basu damar yin ɗan jawabi a taƙaice itada Bily, dan haka Ummukulsoom ta fara miƙewa kamar yanda aka umarceta.

       Tunda ta miƙe idanu suka sake yawa a kanta, duk sai taji jikinta yayi sanyi, dan haka idanunta suka gaza kallon kowa.

          Da sallama ta fara kafin addu'ar fatan alkairi ga waɗanda sula halarci taron tayasu murnar, sannan ta fara jawabi mai ratsa jiki a sanyaye.

      Tunda tai sallama jijiyoyin jikinsa suka saki, kasa cigaba da latsa wayar yayi, yatasa da wane sihiri yarinyarnan take aiki a cikin muryarta.....

      Ummu taci gaba da faɗin, “Alhamdullahi ala kulli halin, Ubangijina shine ya dace na fara gode masa, dan shi mai ni'imane mai kuma rahama mai jinƙai, mai badawa ga wanda yaso akuma lokacin da yaso, ba wayonka yakesa ya bakaba hakama ba ƙarfin iko ba, ka gode masa alokacin daya baka sannan ka gode masa idan ya hanaka, bai kasance azzalumin sarkiba balle ragon tunaninka ya baka cewar rashin sonkane yasashi hakanaka, kokuma kaida ya bamawa kai tunanin kafi kowane acikin al'ummarsa shiyyasa ya baka, ilimi baiwace, dukiya jarabawace, mulki ƙalubalene, Aljannah rahama ce, iyayena ya yayyena da ƙawayena a zatonmu wannne mafi alkairi a cikinsu?. Da ace ALLAH zai ɗauke maka kowacce ni'ima, ya azurtaka data ilimi da nasarar aiki dashi, yay maka albishir da ƙyaƙyƙyawar makoma shin bazakafi son hakaba?. Akwai miliyoyin halittun Ubangiji waɗanda basu da aljihu, ba asusun ajiya ko a banki. Amma ba su daina cin arziƙi ba. Ƙwantar da hankalinka, arziƙinka yana nan ba zai wuce ka ba. Nemi halaliya, don ba ka wuce arziƙinka. Saurin nema ba ya kawo samu. A wata maƙabarta aka rubuta cewa, “Ba za a kawo ka nan da kuɗi ba, amma kana iya aiko su kafin ka zo”. Kenan ya dace mai arziki ya yalwata arziƙinsa da alkairi tunkan ya tsinci kansa a kabari, mai ilimi ya yalwata iliminsa wajen aiki dashi da fargar da waɗanda basu saniba tunkan ya tsinci kansa a kabari, mai mulki ya yalwata mulkinsa da adalci tunkan ya tsinci kansa a kabari, talaka ka yalwata talaucinka da bautar ALLAH, tunkan ka tsinci kanka a kabari, dan abinda ka shuka shi kaɗaine zaka tarar a makomar da ita kaɗaice gidanka na gaskiya. Da ace kowane mai arziƙi irin zuciyar Dad da Abba da Ummi ke garesu da bamu tsinci a halin da mukeba a yanzu, ku ƙafafune, sannan bangwayene, bayane goya marayu harma da masu iyayen, ƙyawawan halayyarku ya koyamin abu uku, *Kƴautata zato, kar kai kuɗin goro ga al'umma wajen jifansu masu zukata da hallaya iri ɗaya, ƙyautatawa na ƙasa dani da tausayinsa*  harshena bashida kalaman miƙa godiya a gareku, sai dai naita muku addu'ar fatan alkairi kuda a halinku har randa numfashine zai yanke, Dad da Yaya Attahir kune fitilata mai haska gabana da bayana, kune........!”.

     Kukane ya sarƙeta ta kasa cigaba, dan haka Ummi ta taso tazo ta rungumeta itama zuciyarta na karyewa da kalaman Ummukulsoom, ba Ummi kawai ba, da yawan jama'ar dake wajen kalamun Ummukulsoom sun girgiza zuciyarsa.

       Dad ne da kansa yafara tafama Ummukulsoom, kafin duk wajen ya ɗauki tafi, yaya Amaan daya kasa koda ƙwaƙwararn motsine kawai yakasa yin tafin, danshi ba hanunsa ke tafinba zuciyarsace ke tafawa tareda dukkan magudanar jininsa da kowacce jijiya dake kai saƙo tsakanin zuciya da ƙwaƙwalwa, karan farko da mace ta birgesa, karan farko daya tabbatar da mace duniyace mai koyar da mutanen duniya ilimi, karon farko da darajar mace ya girmama a idsnunsa fiyeda da dacan da mahaifiyarsa kawai yake kallo da irin wannan darajar bayan salihan mata da suka gabata irinsu nana Aysha, a tunaninsa matan ƙwarai masu hikima sun ƙare, a tunaninsa kowacce mace dake a wannan duniyar mara tunanice, a tunaninsa kowacce mace dake rayuwa a yanzu mara hangen nesa ce, ashe sam ba haka bane.......

    Girgizasan da Attahir yayine ya sakashi dawowa hayyacinsa, ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana kuma tamke fuska ganin jin abinda Attahir ke faɗa masa.

      “Haba malam irin wannan kallo haka? Kodai ƙanwata tayi satar zuciyane?”.

     Harara ya balla masa tareda jan siririn tsoki yana lumshe manyan idanunsa tareda ƙokarin dai-daita tangaɗin da tunaninsa keyi, ina su Attahir suka samo wannan yarinyar? Dan shidai baisanta ba agidan sai yau?.

       Ummukulsoom kam da ƙyar Ummi ta lallasheta tai shiru, tasa tishu ta gyara mata fuskarta sannan ta maida ta mazauninta suna sauraren jawabin bily dame faɗin “Nikam ai banida sauran abin faɗa, ƴar uwata tagama faɗar komai daya dace, sai dai fatana ALLAH ya bamu ikon amfani da shawarwarinta, yakuma sakama iyayenmu da alkairi duniya da lahira”.

    Da amin aka amsa, tareda tafa mata itama.

          Su Dad suma sunyi jawabi mai ƙyau dake ƙara nuna martabar zancen Ummukulsoom, kafin su da kansu sufara bada ƙyautar da suka shiryama ƴaƴan nasu guda biyu, wanda kuma aka gayyaci Amaan amatsayinsa na yaya shida Attahir su bada.

      Jiyay tamkar yace bazai yiba, amma sam bashida ikon yin wannan jayayyar.

     Haka ya tashi zuwa wajen shida Attahir, sai dai fa fuskarnan tana nan yanda kuka santa.

      Koda ya amsa micrephone ɗin domin yin jawabi na jinjina gasu Ummukulsoom kamar yanda Attahir yayi, sai ya rasa abinda zai ce, kusan sakanni goma kafin ya lumshe idonsa ya buɗe, tareda kai hanni yaɗan safi girrarsa, ganin Dad ya kafesa da idone ya sashi kuma rumtse idanu, shikam yaga ta kansa, gashi duk ƴan wajen sun watso masa idanu, abinda ya tsana a rayuwarsa kenan (kallo), da ƙyar ya fisgo magana saboda taɓasa da Attahir yay alamar yace wani abu.

          “Sun cancanci jinjina, ALLAH ya sanya albarka ga abinda aka samu, yakuma sakasu yin aiki dashi damu baki ɗaya”.

     Kowa da Amin ya amsa, tareda ƙara jinjina miskilanci irin nasa, duk abin faɗa dake a wajen shi iya abinda zai faɗa kenan.

     Shi kansa Dad saida ya girgiza kai yana murmushi, ya tabbata wannan jawabin an kaisa maƙurane shiyyasa yayisa har kusan kalmomi 80, “ALLAH ya shirya ka Fodio”.

      Ƙasa-ƙasa Attahir yace, “Ajiwa kayi abunkai, tunda kakusa faɗar kalma 90”.

     Hararsa yayi amma bai tanka ba, danshi yama ƙagara yabar gidan gaba ɗaya.

        Tunda ya fara jawabi Ummukulsoom ta tsargu, sai dai bata buƙatar gaskata shine din koba shi bane, dan haka ta hana idanunta ɗagowa tama kallesa.

        Koda akazo wajen bada ƙyautar haka kawai Ummukulsoom ta tsinci kanta a wani irin yanayi na tsinkewar jini, ƙin yarda tayi ta kallesa yayinda shima yaso tilasta kansa ƙin kallon fuskar kowannensu.

     Sai dai kuma aka samu akasi, bayan karɓar ƙyautar akai musu hoto ba tareda kowa ya kalla ɗan uwansaba, sai Attahir dake kallonsu yana murmushi mai ɗauke da ma'anoni da dama. 

    Bayan yin hoton ta juya zata koma wajen zamansu itada Bily bazar ƙasan gyalenta ta maƙale a zoben sa na azurfa batareda ko wannensu ya lura ba, saida tai taku uku ta tsaya cak saboda jan dataji amma gyalenta.

     Shima da yaji an fisgi hannunsa saiyay saurin ɗago ido, hakan yay dai-dai da juyowar Ummukulsoom domin son ganin abinda ya riƙeta. Atake idanunsu suka shige cikin na juna.

      Atare zukatansu sukai wata irin harbawa, yayinda wani fushi yazo maƙoshin Ummukulsoom ya tokare saboda ganin wanda bata taɓa tsammani ba, a ranta take furta “dama shine?”, samun kanta tayi da danƙara masa hararar data nemi wantsalo zuciyarsa ƙasa saboda tasirinta a gareshi batareda yasan daliliba.

    Shi sam bai ganeta ba, yay saurin tattaro yawun dake neman gujema harshensa ya haɗiye da ƙyar kafin ya janye manyan idanunsa cike da basarwa da takaicin tsagerancinta, ya cire bezar gyalen ya bar wajen jijiyoyin jikinsa na saki gaba ɗaya.

     Itama juyawa tai tabar wajen a wani irin yanayi da ita kanta takasa fassarawa.

       Attahir da abin nasu ya tsaya masa a rai kasa daurewa yay sai da ya dara, hakama Dad da komai ya wakana akan idonsa, sauran mutane da basuda ilimin sanin komai kam basu kawo komai a ransuba, dan bama kowa idonsa yakai ba, Dad ya fahimci Fodio bai gane Ummukulsoom ba, itakuma ya lura ta gane Fodion, hakan yamasa daɗi sosai kuwa(🤣👍🏻Dad ɗinmu na mutunci tarkonka ya ɗanu).

      Har taron ya tashi lafiya tsakanin Ummukulsoom da Amaan sai aka koma ƴar satar kallon juna, idan suka haɗa ido a bisa kuskure ta dan ƙara masa harara, shikuma hakan saiya saka zuciyarsa fusata.

       itakuma ya lura ta gane Fodion, hakan yamasa daɗi sosai kuwa(🤣👍🏻Dad ɗinmu na mutunci tarkonka ya ɗanu).

      Har taron ya tashi lafiya tsakanin Ummukulsoom da Amaan sai aka koma ƴar satar kallon juna, idan suka haɗa ido a bisa kuskure ta dan ƙara masa harara, shikuma hakan saiya saka zuciyarsa fusata.

         Haka dai taron ya tashi lafiya, kowa yatafi da tsarabar da zuciyarsa ta samu, wasu burin mallakan waɗannan ƙyawawan yaran ma shine a ransu, musamman abokan Zaid irinsu Ameer.

     Hakama tsakanin Amaan da Ummukulsoom...........


Duk yanda ka yi sai wani ya zageka. Manta da mutane ka yi komai yanda ya kamata.


     Yafema wanda ya cuce ka ni'ima ce. Tuna abin baƙin ciki da damuwa wahala ce. Manta alkairi butulci ne.



        NO. 29


..........“Bestie wai duk gajiyarce haka?”.

          Guntun Murmushi Ummukulsoom dake kwance a kan gado tun ɗazun tayima bily mai maganar tareda miƙewa zaune tana ɗan sauke numfashi.

       “Wlhy Bily kin ganninan kaina kemin ciwo kaɗan-kaɗan, nasan dai bai wuci wannan hayaniyarba, kina ganin yanda Aziza ta baje”. Tai maganar tana kallon Aziza da tuni tai barci.

       “A kwaifa gajiya, yaukam ansha bidiri, yanzu danaje ɗakin Ummi take cemin Yaya Amaan ma ya aiko mana da ƙyautar kuɗi dubu ɗari mu raba”.

      Duk da Ummukulsoom ta fahimci wa bily take nufi saita ɗan yatsine fuska, “Waye kuma haka?”.

          “O ashefa kina buƙatar ƙarin bayani, wanda ya bamu ƙyaututtuka shida yaya Attahir, shima yayanmune ai, ɗan gidan Dad”.

       “ALLAH sarki, to kin gode. Kinga bara na haɗo ko tea nasha yunwa ta fara gallabar rayuwata”.

      “Maganinki kenan ai, tunfa ɗazu nakawo tuwo da zafinsa amma kikace kin ƙoshi, kuma kikace na gode ke baki godeba kenan?”.

       “Indai kin gode nima kamar na godene kinji bestie, bara dai naga mike a kicin ɗin, dan sai yanzu nake dana sani, yanzu kuma idan nace zanci zai takuraminne dan dare yayi”.

        “Gara dai kisha tea ɗin kawai, saiki haɗa dako wani abune”.

     ”Ok ina zuwa”.

 Gyale ta ɗauka ta yafa akan riga da wandon kayan barcinta ta fice, ba kowa a falon kowa gajiya ta sakashi yin tiɓis, dama duk baƙi sun kama gabansu tunda ba wani taron biki bane ko suna. Tea ɗinta ta haɗo ta dawo ɗaki tasha kafin tasha magani su kwanta.


         Washe gari ma haka suka tashi a matuƙar gajiye, amma haka suka daure suka gyara gidan tsaf ko ina ya ɗauki haske da ƙamshi.

      Kafin su kuma komawa ɗaki susha barcinsu yanda ya kamata.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


               “Fodio ya maganar mu ne? Ina muka kwana ina muka yini?”.

        Ci gaba yay da yin breakfast ɗinsa hankali kwance, kafin ya ɗago manyan idanunsa ya harari Buhayyah da itama tame breakfast ɗin, dan a dining suke su uku, Dad ne kawai babu.

       Fahimtar dalilin harar tata da yayne yasata miƙewa ta kwashi kayan break ɗinta tabar musu Dining ɗin, dama duk zamansa ya takuta.

      Momcy batace komaiba, dan shifa dama ƙa idarsace wannan, ko hira bayason yi gaban ƙannensa, garama Aunty Nurse taci wannan darajar.

        “Tunda ka koreta saika bani amsa”.

       Shiru yay nanma bai tankaba, sai laɓɓansa da sukaɗan motsa alamar yanason maganar fitarta ce wahala a garesa, saida yaja wasu seconds kafin yay ɗan gyaran murya da cirar tishu ya goge bakinsa, “Momcy kenan, nifa ban ganiba har yanzu?”.

      Kallon mamaki ta tsaya masa tana kurɓar tea, “Ban gane baka ganiba? Ita matar auren film ce da har saika gani?”.

        Alamar gajiyawa da maganar ya nuna a fuskarsa kafin ya lumshe idanunsa ya buɗe a kanta, “Momcy Please bar wannan batun, ni yauma zan koma?”.

       “Barin batu kam ai baima tasoba Fodio, dan aure dolene kayisa nan kusa, Dad ɗinku fa zuba mana ido yay yaga yanda zamu kwashe, kaga ko ai yakamata muba mara ɗa kunya ko. A ganina yarannan biyu na gidan Alhaji Abubakar mizai hana ka zaɓi ɗaya”.

      Baƙaramin waro mata manyan idanunsa yayiba, tareda kafeta dasu batareda ya fargaba.

      “Nidai ɗauke waɗannan idanun naka a kaina kaji”.

     Karan farko data bashi dariya, dan haka fuskarsa taɗan nuna alamar sakewa, amma fa ba murmushi yayba, saikace ba gunta ya gajesuba.

       “Bakace Komaiba?”.

“To Momcy banida abin faɗar ne, kibani lokaci zan duba na gani to”.

      “Zaka duba ko zaka zaɓa”.

         Tashi yay tsaye yana faɗin, “To zan zaɓa” dan shikam yagaji da surutun.

        Da kallo ta bisa tana maijin ƙarin ƙaunar ɗanta har cikin ranta, wataran halayyarsa ta bata haushi wataran kuma tai mata daɗi.



 ★★★★

 

          Koda ya koma sashensa sabon shafin tunani ya buɗe, dama a cikin yanayin ya kwana, haka kawai ya tsinci zuciyarsa da daskarewar harbawa, baisan minene daliliba, abinda kawai ya iya fahimta shine yawan tuno kalmarta ta *“Shikuma wannan dangin tsakar daga ina? Waya bashi lasisin taɓani ma?”* da karfi ya rumtse idanumsa, furucinta na sukarsa, yarasa miyasa yarinya ƙarama irin wannan kalamanta sukai tasiri a ransa?, hararar da tai masa bayan bazar gyalenta ta maƙale masa ya mugun tsaya masa a rai itama, dolene ya ɗauki mataki akan yarinyar, dan zuciyarsa bazata iya ɗaukar raini daga kowaba.

     Haka yayta saƙawa da kwancewa shi kaɗai, tareda juya zancen Momcy.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡



            “Yaya Attahir wai dan ALLAH da gaske kake mu shirya?”.

       “Oh Bily kin rainani wlhy, na taɓa muku irin wannan wasanne? Ina Ummukulsoom?”.

         “Tana ɗaki kwance, amma ba barci takeba”.

      “Ok, tom kuyi maza ku shirya, Dan hafsat ta shirya tuni”.

          “Kai godiya cikin kd babban yaya”.

      Murmushi kawai yay yana girgiza kai, baisan randa Bily zata bar rawar kaiba shikam, halin autanci sosai yake tasiri a jikinta.

       “Madam tashi ki shirya”.

      Ummukulsoom da barci ya fara ɗauka ta ture hannun Bily dake bugunta tana faɗin, “Dalla malama ki bari, wai miyasa kekam a rayuwarki kike baƙin ciki kiga mutum na hutawa”.

        “Hhhhh yarinya zakiga baƙin ciki, Yaya Attahir ne yace mu shirya ya kaimu wani waje muga gari”.

         Buɗe ido Ummukulsoom tai tana kallonta, “Dan ALLAH da gaske kikeyi?”.

     “ALLAH kuwa karkiji wasa”.

     Tashi Ummukulsoom tai cike da jin daɗi, dama zaman gidan ya isheta, sun saba da yawon fita makaranta.

       Shiryawa tai cikin siket da riga na atanfa, kasancewarta mace mai cikar halitta sai sukai mata ɗas, tai ɗaurinta ture kaga tsiya, wanda ya bayyana gashinta dake a tsaka tsakin tsawo, baƙi siɗik saboda gyaran da yake samu, yanzu haka babu kitso, amma a gyare yake  tsaf,ga ƙamshi mai daɗi na tashi saboda kayan ƙamshin da ake turareshi dashi a koda yaushe. Bata cika son kwalliyar shirmeba a fuska tunma tana ƙauye, sai abun yay tasiri a gareta har zuwa yanzun.

        “Bily Please ina gyalenmu ƙalar Ash ɗinan?”.

       “Tab babban aiki, ai inaga gyalennan kam yayi datti, kinsan ranar walima ɗinmuncan shina ɗaura akai mukaita aiki, kuma ba ai wankiba”.

       “Amma dai kin gama dani, yanzu wanne zanyi amfani dashi kenan?”.

    “Ki saka yellow ɗinnan mana, shima zai zauna sosai ALLAH”.

     Kallon kanta tai a mirror, kafin taja gyalen ta jingina da kayan, ganin zai shigane saita fesa masa turare.


    “Woow Autocin Ummi irin wannan ƙyau haka?”.

     Murmushi su Ummukulsoom sukayi saboda tsokanar yaya Attahir ɗin da maman Ahmad, Zaid kam ya kafe Ummu da ido ko ƙyaftawa bayayi, hakanne yasa taƙi kallon inda yake, da tasanma tafiyar da shine da wlhy bata amsa zuwaba, shaf ta manta yau weekend yana gida, kuma koda sun barta a gidan bazai mata daɗiba, dan Ummi da Abba sunje Niger state duba wani yayanta da baida lafiya.

     Koda suka fito sai Yaya Attahir yace su shiga Motar zaid, shi matarsa kawai zai ɗauka, Ahmad kam yana tare dasu Ummi.

    Ko kaɗan Ummu bataso hakanba, amma saita basar kawai, gashi Bily tai saurin shigewa gaba.

         Koda suka fice a gidan duk yanda Zaid yaso Ummukulsoom ta saka baki a hirarsu ƙi tayi, sai taso ma take murmushi, maida dukkan hankalinta tayi ga latsa waya, shi dai Zaid har mamakinta yakeyi, anya batada aljanu kuwa? Yarinya Sam batsan soyayya ba?.

      Oho ko kaɗan Ummukulsoom batasan yanayiba, ita zuwa yanzuma sotake ta leƙa ƙyauyensu taga yaya lafiyar jama'a, dan shekara ɗaya kenan bata jeba kuma duk shekara idan sunzo ƙarshen shekara take samu ta leƙasu koda kwana ɗayane itada Bily, yanzu kuwa kafin ta koma makaranta ya kamata ta leƙa kam ko sati biyu tayo.......

      “Hajiyar tunani saiki fito mun iso”.

     Ajiyar zuciya Ummukulsoom ta sauke kaɗan, kafin ta kalli Zaid dake maganar tsaye ya buɗe mata mota, ita saima abun yasata murmushi, “Yaya zaid kenan saikace wata sarauniya?”.

      “Ai ke Kinmafi ƙarfin sarauniya Babie”.

     Murmushi ta kuma masa, batareda ta bashi amsa ba ta fice daga motar shikuma ya rufe yana shakar daddaɗan ƙamshinta mai narkar dashi.

        

     Sosai Ummukulsoom ke kuma ware idanu tana kallon gidan, ko shekaru nawa zata ɗauka bata zoba bazata mantashi ba, yana nan yanda ta sanshi, sai fenti da aka canja masa, saiko tsarin flowers ɗin gidan, ta haɗiye wani abu mai kama da hasala a maƙoshinta, tareda saurin dannesa da tarin alkairin mai gidan, kodan alfarnar Dad bazataki alfahari da zuwa gidanba.

       Da sallama suka shiga falon da komai na cikinsa ya kasance baƙon ganin Ummukulsoom, dan duk ba wanda ta sani baneba, ko ina ƙal yake da tsafta, a wannan fannin kam tasan Momcy gwanace, batason ƙazanta ko kaɗan, sanyin AC ne kawai ke ratsa falon sai ƙamshin turaren wuta. Tsit gidan babu yawan hayaniya kam yanzun.

      Bily takuma kwaɗa sallama, daga kicin muryar wata dattijuwa ta amsa.

     Idanu Ummukulsoom ta kafe ƙofar kicin ɗin dashi dan taga wazai fito, burinta kawai taga baba halima.

    Ilai kuwa itace, amma ta ƙara manyanta, cike da girmamawa take musu sannu da zuwa.

    Tausayinta ya kama Ummukulsoom, ALLAH sarki rayuwa, wato talaka shidai haka rayuwarsa a mafi yawan lokuta take ƙarewa, ka taso cikin wahala, idan haka ALLAH ya ƙaddara maka saikaga harka girma a cikinta, Baba halima ta cancanci ta huta, amma sam hakan bai samuba, batason bayyana mata kanta kam a halin yanzun, dan a ganinta lokaci bai yiba.

     Itace da kanta ta hau saman benen, dama tun can da ita kaɗaice keda wannan lasisin, saiko wadda suka ɗauka domin musu aikin gyaran saman.

    Babu jimawa saiga Momcy ta sakko cikin kwalliya.

    Ganin su Ummukulsoom ne baƙin yasata rikicewa da musu lale mar habun, “Haba dai ya zaku zauna anan kuma ƴaƴana? Kunga kutaso ku hawo sama dan ALLAH.

       Baki Ummukulsoom taɗan taɓe a kaikaice, kafin tabi bayan su Bily da har sunyi gaba itada maman Ahmad.

      A falon Sama ma komai baƙon Ummu ne, sai kallon falon take tana tuna baya, tamkar batai bauta a cikinsaba, ALLAH sarki rayuwa, ni'imar ALLAH da bance wlhy, hakama ikonsa akan kowa dabanne, karkaga kana shiga haƙƙin ɗan uwanka koda da mummunar maganace ko zagi ka ɗauka ALLAH bazai jarabcekaba, shi buwayine gagara misali, yakan yafe laifin a tsakani sa da bawansa, amma fa baya yafewa tsakanin mutum da mutum, to bakasan ta hanyar da ALLAH zai sakankama wanda ka cutamawa ɗinanba, sannan kaikuma bakasan ta ina zai jarabceka da haƙƙin wanda ka ƙuntatawarba, yau dai gata tazo gidan Momcy ba'a Ummu ƴar aikiba, ba'a ƙasƙantaciyar dasu suke ɗaukaba, sai dai ALLAH kuma ya toshe saninsu da fahimtarsu ta yanda suka gaza ganeta.

    Dan danan aka cika musu gabansu da kayan motsa baki, Hajiya jamila tamkar zata goyasu dan tsabar ɗoki.

    Hakama Buhayyah data fito daga ɗakinta jin hayaniyarsu.

        Suna tsaka da gaisawa kira ya shigo wayar Momcy, ɗagawa tayi cikin murmushi tana faɗin, “Yaya dai Fodio?”.

    Basu san wace amsa daga can ya bataba, sundaiji tace, “Ok to babu matsala bara a kawo musu”.

          Kallon Ummukulsoom tai dake a kujerar farkon shigowa a kaikaice, yarinyar tafi dacewa da Fodio ɗinta, saboda tafi Bily cikar halitta dukda suna mata satar kamanni, taɗanyi gyaran murya da kallon Buhayyah.

    “Buhayya keda diyata kuje ku kaima su yayanku abin motsa baki da lemo”.

     Buhayyah taɗan ɓata fuska, dan itakam ta tsani aikin yaya Amaan, kafin ka gama yakusa cinyeka da harara, amma babu yanda ta iya saita miƙe tana kallon Ummukulsoom dake kusa da ita, Auntyna dake zamuje ko?”.

        Tamkar Ummukulsoom ta danƙara mata zagi haka taji, dan duk tana saurarensu amma tayi kamar bata fahimta, murmushin yaƙe tai a fili tana faɗin, “Babu damu muje”.

       Momcy dake kallon Ummukulsoom cike da birgewa tace, “Yi haƙuri ɗiyata, daga zuwa an saki aiki, yayan nakune sai a hankali, bayason ƴan aiki su masa komai”.

     “Lah babu damuwa Momcy ”. ‘Cewar Ummukulsoom a wani yanayi’.

    Itako Momcy daɗi taji, saboda itadai yarinyar komai nata birgeta yake, akwai jan aji sosai, irin yanda take fatan matar Fodionta ta kasance komai Ummu ta haɗashi.

     Ummukulsoom da Buhayyah kam tuni sun fice, kicin suka nufa suka karɓi Kayan da Jud ya haɗa, Ummu sai kallonsa take, amma sam shi bai ganeta ba, yana nan bai canjaba, hakama wulaƙancin su Buhayyah ga ƴan aiki, dan yanda takema jud ɗin magana dolene ya baka tausayi, saikace wani ƙaninta ko ɗanta, a gadarance take bashi Umarni.

       Koda suka fito Buhayyah sai sukar ƴan aiki takewa Ummukulsoom, amma sam taƙima tanka mata, hakanne ya saka Buhayyah ɗan kallonta, taga Ummukulsoom tayi kicin-kicin da fuska babu alamar sauƙi.

    Buhayyah a ranta ayyanawa take “kin cancanci jan aji wlhy, dan komai kina dashi najan ajin, ni saima naji kin kuma burgeni, inason huɗɗa da masu aji” a zuciyarya taketa surutannan, Ummukulsoom kam tama ɗauke kanta daga gareta tamkar ba a tare suke tafiya ba.

     A ƙofar falon suka tsaya Buhayyah ta  ƙwanƙwasa. Babu jimawa aka buɗe musu suka shiga.

           Shine a kujerar farkon shigowa falon, Ummukulsoom ta danna ma bayansa harara kafin taima falon kallon tsaf, komai shima an canja hatta da fentin sashen, sai dai mayataccen ƙamshinsa da ta sani tun fil azal yana nan nane da sashen, koda sukai sallama Attahir da Zaid sun amsa amma shi ko motsi baiyiba balle ya ɗago ya kallesu, sai aikin latsa waya yakeyi hankalinsa kwance.

      Tsabar iya neman faɗa irin na Ummukulsoom da zata wuce sai ta taka masa ɗan yatsan ƙafarsa ta wuce. Zaid yayma Ummu murmushi tarefa mata signal da ido alamar sannu da aiki.

    Ɗauke kanta tayi kamar bata gansaba, ta ajiye tiren hannunta.

     Buhayyah ce ta fara wucewa Ummukulsoom na binta a baya, batareda taga sanda ya motsaba kawai tajita a ƙasa ya taɗeta.

     “Wayyo Ummina”. Ta faɗa a hankali saboda shigar azaba da ƙashinta ya fuskanta na ƙafa.

      Duk kanta Yaya Attahir da Zaid sukayo suna tambayar lafiya? Hakama Buhayyah, amma gogan naku ko motsi baiyiba balle ya kalleta.

     Attahir ne yaɗansha jinin jikinsa, ya kalla ƙafarsa tareda auna inda Ummukulsoom ta faɗi, tabbas yaji a ransa Ajiwa ne ya aikata tsiyar, amma ya fuske tamkar bai aikataba.

       Sai abun ya ɓatama Attahir rai, a ganinsa mi Ummu tai masa dazai mata wannan muguntar, ransa a ɗan ɓace yace, “Ajiwa wai garin yaya hakan ta faru? Naga a gabanka ta faɗi?”.

    Yiyay tamkar baiji mi Attahir ɗin ya faɗaba, sai da ya mula da kansa sannan ya ɗago manyan idanunsa farare tas ya sauke akan Attahir da shima ya ɓata fuska. Bakinsa yaɗan taɓe tareda maida kallonsa ga Ummukulsoom dake kuma narke murya tana kuka, wanda da gani kasan harda shagwaɓa da sheri ganin Attahir ya nuna fushinsa akai🤣............✍🏻



Kada jin daɗin wani ya tsonema ido. Ba ka san abin da ya rasa ba kafin ALLAH ya ba shi ni'imar da yake cikin ta. Kada dammuwarka ta tada hankalinka. Ba ka san alherin da za ta jawo ma ka ba. Haƙuri maganin zaman duniya.



NO. 30


............Bakinsa ya kuma taɓewa tareda kauda idanunsa daga kanta.

      Zaid da yakejin kukanta har cikin ransa yay saurin kai hannu ga ƙafarta amma sai carab Amaan ya riƙe hannun.

     Dukansu idanu suka zubama hannun nasu, kowa baki hangame, hatta da Ummukulsoom saida ta tsaya da kukanta tareda hangame baki tana kallon hannunsa dake riƙe da na Zaid, kafin ta maida kallonta ga fuskarsa.

     A tamke take sam babu alamar sauƙi, sannan kuma ya ƙi kallon kowa har Zaid ɗin, yakumaƙi sakin hannunsa.

      Attahir ne yay gyaran murya ganin abin zai canja salo, “Ƙanwata jawo baya kinji inga ƙafar”.

      Matsawa Ummukulsoom tai shirinyi fuskarta ɗauke da mamaki amma sai taji an riƙe ƙafarta mai ciwon.

        Saurin kallonsa tayi, sai ta ga ya saki hannun Zaid ɗin, ƙafar tace yanzu kam a hannunsa......

    Tunaninta baije ƙarsheba ya matsa ƙafar sosai sai da tayi ƙara tareda ƙan ƙame hannunsa ta fashe da kukan gaskiya kam yanzun.

    Ture hannunsa Attahir yayi da sauri yana faɗin, “Wai kai Ajiwa mike damunka ne haka?!”.

        Zaid kam da Buhayyah idanu suka rumtse saboda tausayin Ummu, dolene ka fahimci taji zafi, dan da alama taji ciwo a wajen, matsawar da yay kuma yabama ƙashin wajen damar dai-dai ta.

       Amaan da yasan Attahir ya fusata, kuma komai zai iya faruwa a tsakaninsu sai bai tankaba yama miƙe yabar falon.

      Saurin binsa Attahir yayi, dan ya shirya suyi koma miye, bayason zalinci mara dalili, abinda ya fuskanta kawai Ajiwa ya gane wacece Ummukulsoom shiyyasa yake neman magana, shiko a wannan karon bazai ɗaukaba wlhy, dan jinta yake a ransa tamkar Bily da Zaid.

       Ganin sunbar wajen Zaid da abin duniya ya damesa yakuma yunƙurin kai hannu ga ƙafar Ummukulsoom.......

       Cak ya tsaya daga yunƙurin shiga bedroom ɗinsa, cikin kakkausar murya yace, “Wlhy Zaid idan har ka aikata sai na ɓata maka rai, kubar falon nan kaida Buhayyah”.

      Kasa aikatawar Zaid yayi, dan yasan halin Yaya Amaan farin sani, amma zuciyarsa na mamakin miyasa yake son shiga rayuwarsa shida Ummukulsoom?, ko dai sonta yake shima?.

     Buhayyah kam tuni ta fice dan tasan ƙarshen zancen inma tayi taurin kai, dama darajar su Ummukulsoom dake falonne ya bata damar sakin jikinta.


       “Wai kai mika ɗauki kan kane? Mi kake taƙama da shine a rayuwa?!”.

      Ummukulsoom ta faɗa a matuƙar fusace, dan zuwa yanzu bata shakkar yasan itaɗin wacece, bazata ɗauki wannan rainin hankalinba.

         Tsaƙi yayi ya ƙarasa shigewarsa batare da ya bata amsaba....

      Dukda azabar da ƙafarta ke mata miƙewa tayi ta fice, zuciyarta na wata irin tafasa da kuma kumbura....


           “Ajiwa mikenan kakeyi? Kaga kana neman haddasa raini tsakaninka da yarinyarnan ko”.

       Murmushi Amaan yayi, irin wanda duk tsantsar shakuwarsu da Attahir yakan jima bai ganiba, dukkan hannayensa biyu zube suke a aljihun wandonsa 3quarter, gaban Attahir yazo ya tsaya sunama juna kallan kallo tamkar wasu zakaru, ya lumshe idanunsa ya buɗe akan Attahir dake hararar sa fuska a ɗaure.

      “So kake ka san dalilina? To ba yanzuba, sai dai lallai ka gargaɗeta ta kiyayi shiga lamarina, inba hakaba da hannuna zanta karyata ina ɗorata, inga ƙarshen fitsara”. Yana gama faɗa yaɗanja baya daga gaban Attahir.

     Katsesa Attahir yay da faɗin,

       “Ajiwa ba maganar wasa nake makaba anan,  banga mi yarinyar nan ta makaba, karka bari akanta saɓani ya shiga tsakaninmu”.

       “Attahir karka azamin ciwon kai Please, kaje ka fara bincikarta kafin kazo kanamin surutun banza”.

      Tsaki Attahir yaja tareda hararsa ya fito daga bedroom ɗin.


       A tsakar gida ya iske jama'ar gidan cirko-cirko, ga Ummukulsoom gaban Dad tana hawaye zaune a farar kujera.

    Kallo ɗaya yayma fuskar Dad ya sunkuy da kansa, dan lallai ransa a ɓace yake.

        Momcy dukta rikice, sai tafa hannaye take, tanason nufar sashen Amaan amma tana shakkar Alhaji Mahmud.

     Sashen Amaan Dad ya nufa ransa a matuƙar ɓace.

         Tunda Dad ya shigo falon Amaan da fitowarsa kenan daga bedroom ɗinsa yasha jinin jikinsa, amma kasantuwarsa ɗan gado akan dakiya sai bai nunaba ya hau faɗin, “Dad lafiya kuwa?”.

      Cikin hargowa Dad yace, “Ban saniba, Mi yarinyar can tamaka kaji mata ciwo a ƙafa!?”.

      Kansa ya dafe cike da tsantsar takaici, ɗan abunda ya mata har yakai na a hau kansa irin haka?.....

      “Fodio da kai nake, banason iskanci fa?”.

      Idonsa harya fara canja Cala, da ƙyar ya iya furta “Dad ni minai mata to?”.

        Dad ya yunƙuro zaiyi magana Momcy data shigo tai azamar tararsa da faɗin, “Abban Fodio dan ALLAH kayi haƙuri, mubi a hankali”.

     “Anƙi abi a hankalin kekuma, in banda iskanci da tsabagen zalunci daga zuwan yarinyar gidan ziyara saiya kama cutar da ita, kai wai a rayuwarka bakajin daɗine idan bakai zalunci ba? To wlhy wannan yazama farko da ƙarshe da ko harar banza ka sake mata, shashasha kawai mai baƙar zuciyar tsiya. Ke kuma ki gargaɗi ɗanki ya kiyayi taɓa yarinyarnan, akanta zan iya saɓa masa wlhy”.

    Fuuuuu Dad ya fice yabar musu sashen.


       Kafe ƙofar da Dad ya fice yay da kallo, yakasa koda motsi daga inda yake tsaye, akan wannan yarinyar Dad kemasa waɗannan kausasan kalaman? Bayan kuma itace taja yay mata hakan........

      Ita kanta Momcy kalamansa sun girgizata, to ita yarinyar wacece ita da har yake tada jijiyar wuya a kanta?.

       “Fodio wacece ita wannan ɗin? Dan na fahimci daga kai har Alhaji kunsanma wacece kenan?”.

      “Momcy ni ban santaba”.

        “To in bakasan wacece itaba miyasa kai wannan gangancin? Miya haɗaka da ita?”.

      Kallonsa ya maido akan Momcy amma ya kasa bata amsa. sanin ransa a ɓace yakene ya saka Momcy kama hannunsa ta kaishi har rukunin kujerun dake falon, ya zauna. Itama zama tayi gefensa, “Fodio kayi wauta, yarinyarnan dama itace nake fatan kaje ku daidaita, gashi tunkan aje ko ina kafara ruguzamin shiri, dan ALLAH Fodio ka rage zuciyarnan taka......

      “To amma Momcy sai kawai na zauna ƙaramar yarinya taitamin rashin tarbiyya.”

      “Wane irin rashin tarbiyya kuma Fodio? kai yaushema ka santa da zakace haka?, irin waɗannan yaranfa abun tattaline, Ko dai ka santa ɗin da gaske kuna ɓoyemin ne?”.

       Idanu ya tsura mata kawai, yana maimaita kalmar tattalin data ambata a zuciyarsa tareda rarrabe ma'anoninta a ransa.


         A tsakar gida kuwa Baba Halima ce ta duba ƙafar Ummukulsoom, dan ta iya gyara, sai taga ashe targaɗene kawai tayi a ɗanyatsa, kuma ya maida ƙatsin lokacin daya matsa ƙafar, magani taje ta ɗakko ta shafa mata, a ranta tana mamakin halin Amaan, shikam yama zarta mahaifinsa murɗaɗɗen hali, ina daɗi daga zuwan yarinya gida kai mata wannan ganganci haka in banda dai ƙarfin hali.

      Bily tayi zuru-zuri, sai tsoron Amaan ɗin ya kuma kamata itakam.

      Ana gama gyarawa Ummukulsoom tace itadai gida zataje gaskiya, Dad bai hanaba yace suje ɗin.

       


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


           *_Birnin Paris_*


      Dur ƙushe yake a gabanta tamkar ɗa mai neman gafarar mahaifiya, ya rame ya lalace matuƙa gaya, tamkar ba Baseer ɗinnan ba ɗan ƙwalisa mai bama mata pepe, babu wannan kwarjinin da cikar haibar da kwanciyar hankali ke samarwa.

      Hawayen dake tsiyaya a fuskarsa wasu na bin wasu ya share, ya kuma gurfana a gabanta yana roƙo, “Dan ALLAH hajiya kimin aikin gafara, wlhy tallahi ƙarfina ya ƙare bazan iya ba, dan ALLAH ki bani dama na sawwaƙe miki na koma ƙasata wajen iyayena da kika nisantani dasu tsahon shekara Biyar, wlhy nayi nadama.........”

      “Wlhy bakayi nadama ba Baseer, dan har yanzu baka gama magantuwa ba, baka kai ƙarshen littafin rarrabe shu'umcin maceba.......”

      Muryar da bai zato ba ta katse masa zancensa, a matuƙar rikice ya juyo jikinsa na wani irin ɓari da rawar mazari, cikin tsantsar tashin hankali da gushewar tunani ya furta *“Suhailat!!”* saiya sulale wajen a sume kawai. 


         Suhailat dake tsaye a bakin ƙofa ta tako cikin tsantsar ƙasaita zuwa gaban Baseer dake kwance wanwar a ƙasa, murmushi mai ƙayatarwa tayi kafin ta maida kallonta akan Meenal dake tsaye itama fuskarta ƙawace da lallausan murmushi, hannu suka bama juna cikin kashe idanu......😬


           🙀🙆🏻‍♀️ Tirƙashi, nasan babban burin kowannenku sanin mikuma ya maida Baseer haka bayan barinsa ƙasarsa ta haihuwa🤔🙆🏻‍♀️, to lallai yanzune zaku sani kuwa tamkar yanda kuka matsu da cigiyarsa a kullum.😳😉



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


             “Yaya Zaid ya naga Yaya Attahir ya nufi hanyar gidan Hajiya yaya kuma?”.

      “Wlhy nima ban saniba Bily, amma bara dai na kirashi a waya naji”.

          Ummukulsoom na kwance cikin kujera a baya tana jinsu, sai dai kuma bata tankaba, dan dama ta daɗe tana son zuwa gidan Hajiya yaya ɗinnan, amma tarasa miyasa Abba kamar yake ƙin son zuwanta? Ƙyaƙyƙyawan zaton da take masane ya sata bata zargi hakan a matsayin komaiba sai ƙyaƙyƙyawan dalili wanda shine kaɗai ya barma kansa sani.

     Tunanin da tatafi ya hanata jin mi wayar Zaid ta ƙunsa, dan haka taci gaba da tunanin shika-shikan rashin mutuncin datake tanadama wannan azzalumin (Amaan) (maganar gaskiya masoyan Ummu kune bakuda gaskiya a wannan gaɓar😂, dan kuwa Ummu ce ta takalo faɗan dayafi ƙarfinta).


       Bara nayi ta kaina karnasha suburbuɗa a hannun gayu

⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😝


★★★★★★


          Gidane madai daici ammafa mai tsari tamkar ba tsohuwa ke a cikiba, da taimakon Bily Ummu ke takawa zuwa cikin gidan daya ƙayatar da ita.

          Falo tsaf tamkar bana tsohuwa ba, sai ƙamshi ke tashi na musamman.

      Sallamar da suke rangaɗawa wata dattijuwar murya ta amsa daga wata ƙofa.

      Bily ce cikin ɗaga murya tace, “Tsohuwa mai ran ƙarfa kimazafa kinada manyan baƙi yau a gidannan”.

      Hajiya yaya tsohuwa mai tarin dattako ta fito cikin shigar kamala tana faɗin, “Ja'ira mai ɗan karen ƙaudi, kune baƙin nawa?”.

     Zuwa bily tayi ta rungumeta, Hajiya yaya ta tureta, “Bilkisu kinci garinku, karyani zakiyine?”.

     Bily dake dariya tace, “Waceni da wannan gangancin Abba ya ci ƙaniyata”.

         “A'a kice gidanne du gaba ɗaya, Zaidu lafiya naganka yau rai a ɓace?”.

     Duk kallon Yaya Zaid ɗin sukayi, shiko dai yakasa fara'a tun abinda ya faru gidansu Dad ne kecin ransa, yayma Hajiya yaya murmushin yaƙe kawai.

      Duk wannan abun dake faruwa Ummukulsoom ta fita a hanyyacinta, dankuwa tun fitowar Hajiya yaya ta ƙureta da ido baki sake.

       Attahir ne ya fara lura da halin da Ummukulsoom ke ciki, dan haka ya taɓa Hafsat dake a kusa dashi ya nuna mata Ummu...

     Miƙewa Hafsat tayi ta nufi Ummukulsoom da ɗan hanzari ganin tayi baya zata faɗi saboda tsabagen firgici da take a ciki, wannan ne kuma yaja hankalin sauran har Hajiya yaya da ita sam bama ta lura da Ummukulsoom ba sai yanzun........



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


             Tunda suka bar gidan sai ya rasa inda zai tsoma kansa yaji daɗi, miyasa ya aikata mata hakan? Anya kuwa ta cancanci hakan duk da itace ta fara aikata masa laifi? Ya rintse idanunsa da ƙarfi tareda tafe kansa, batareda ya shirya suɓutowar maganar dake kan harshensaba yace,

           “Zuciyata bakimin adalci ba, kin jefani a halin da gangar jiki da ƙwaƙwalwa bazasu iya juraba, ni ban shiryaba! Ban shirya ba nace.....!!!”.

    Ya faɗa a matuƙar harmutse yanajin kansa tamkar zai fashe gida biyu, tun daga randa yaji muryarta komai ya fara canjawa a rayuwarsa, abubuwansa masu muhimmanci dake da alaƙa da gangar jikinsa sun kasu gida biyu wajen yin aiki, *ƙwaƙwalwa da Zuciyar sa* duk sun raba tunaninsa tare da nata, wane irin jarabawace wannan ta sartse mai wahalar fiddawa koda da tsinin allurane. Shika ɗai yasan a halin da yake ciki, miskilancin sane kema damuwarsa hijjabi da fahimtar mutane, duk yanda yaso yakiceta ya kasa, kullum lamarin ƙara ruruwa yake da girmama a duniyarsa.

          Wanene zai tunkara? Wazai fahimcesa? Ta yaya zai fiddo abinda ke ransa? Dad ne yay masa katanga ta baƙin ƙarfe akan dukkan maganar data shafi kalmar aurensa.............✍🏻



NO. 31


..........“Ai ta suma”. ‘cewar Maman Ahmad a matuƙar harmutse, da gudu Zaid ya nufi kicin ɗin Hajiya yaya ya ɗakko ruwa. koda ya buɗe sai Hajiya yaya da itama jikinta ke mazarin rawa saboda ganin fuskar Ummukulsoom ta amsa ta shafa mata a fuska.

    Nannauyan numfashi Ummu ta sauke, kafin ta buɗe ido a hankaki ta saukesu kan hajiya yaya.

    Dukansu numfashi suma suka sauke.

      “Da ana mutuwa a dawo da yau nace mahaifiyata ce ta dawo gareni, duk da a hoto kawai nai mata farin sani ba'a zahiriba. Dan ALLAH yaya Attahir idan mafarki nake ku tadani daga wannan nannauyan barci kafin sauran hankalin da ya rage a ƙwaƙwalwata ya ida tarwatsewa”. 

      Hajiya yaya da har yanzu jikinta ke rawa ta kamo hannun Ummukulsoom cikin nata, idanunta kafe a kan fuskar Ummukulsoom, lallai tanaji a jikinta ko tantama babu wannan yarinyar jininta ce, amma ta yaya ta kasance a cikin family ɗinta bayan babu wani mahaluki daya san inda take tunda ta juyama jiyanta baya, tai wani murmushi mai ciwo, a hankali ƙwallar da suka cika mata ido suka sulalo a dattijuwar fuskarta.

    Hakan sai yakuma saka jikin su Attahir yin sanyi ganin Hajiya yaya na kuka, lallai hakan yana nufin akwai abunda basu saniba kenan.

     Kallon Attahir hajiya yaya tayi, “Attahiru ina kuka samo wannan yarinya?”.

      Numfashi Attahir ya sauke a hankali, kafin ya kalli maman Ahmad da Zaid da Bily yay musu nuni da su fita.

    Harsun yunƙura zasu fice Hajiya yaya ta dakatar dasu, “Kunga ku dawo ku zauna. Kai kuma mushiga ciki”. Tai maganar tana jan hannun Ummu, bin bayansu Attahir yay har bedroom ɗinta.

       Jikin Ummukulsoom yakuma yin sanyi ƙalau, ga ƙafarta na mata zugi dan sai yanzu ma takejin zafin har a zuciyarta.

       A bakin gado hajiya yaya ta zaunar da Ummukulsoom itama ta zauna, Attahir kuma ya zauna a kujerar dake ɗakin mara tudu sosai, an mata itane kawai dan hutawarta.

      “Attahiru ina saurarenka”.

        Guntun murmushi Attahir yayi, kafin yace, “Hajiya yaya da son samune ace Abba yana tare damu, dan nidai shine silar komai, ko dai a kirasu a waya ne?”......

    “Basai an kirani ba gani a kusa”.

     Dukansu ƙofa suka kalla inda Abba ke a tsaye, ya ƙarasa takowa cikin ɗakin, Attahir yay saurin sauka a kujera ya koma ƙasa, itama Ummukulsoom ganin haka sai ta sauka ƙasan.

      Hajiya yaya dake kallon Abba tace, ”Abubakar ina saurarenka”.

     Murmushi Abba yayi, kafin yace, “Hajiya ki gafarceni, ni mai laifine a gareki wajen tone abinda kiketa ƙoƙarin binnewa”.

     Sosai ta kafeshi da idanu, “Abubakar!”.

     “Na'am Hajiya”.

 “Ya akai hakan?”.

“Kiyi haƙuri hajiya, komai na rayuwa yanada sanadi, ni nawa sanadin shine auren Ummukulsoom da Fodio na wajen Alhaji Mahmud abokina. Tun randa Alhaji Mahmud yazomin da zancen ya samawa Fodio matar aure a garin Ɗilau tunanina ya dawo gareki”.

      “Ɗilau Abubakar? Dama acan Usman yayo aure?”.

    “Eh hajiya a canne, bayan munkai kuɗin auren mun dawo nazo na faɗa duniyar tunani, tareda samun ƙwarin gwiwa bisa wasiyyar mahaifina da bai samu damar ƙarasa faɗaba ciwo ya gala baitar dashi,     *(Abubakar mahaifiyarka ƴar wani ƙauyece ɗilau, amma an haramta mata z....)* iya abunda ya faɗamin kenan tari ya sarƙeshi, daga nan kuma harshensa bai sake furta wata kalmaba har ranar barinsa duniya, ban fahimci ƙarshen zancensa ba ko ma'anarsa shiyyasa a koda yaushe nake ɗakko miki hira akan sunan garin, amma sai kikan nunamin ɓacin ranki akan hakan, wannan dalilinne yasani daina miki maganar, sai dai a kullum neman inda zansan garin ɗilau nake, sai a dalilin auren Fodio na sani, ashema kusa take damu. Bayan bikin Fodio ban sake wani yunƙuri akan komaiba, saboda bansan ta inane zan fara ba, amma na kira Attahir akan yay ƙoƙari ya kusanta matarsa da matar Fodio, ƙila kota sanadinta zansan wani abu gameda wasiyyar mahaifina. Ban san fuskar matar Fodio ba, saboda ko a lokacin da tazo gaishemu ranar ɗaurin aurensu fuskarta a rufe take. Babu wani bayani mai gamsarwa dana samu a wajen Attahir kusan watanni shida, sai kirana da yay yake sanarmin saɓani daya shiga tsakanin matar Fodio dashi Fodio ɗin, hakanne yasa nace duk yanda zaiyi yayi tazo gidana ni da kaina saina maidata ga iyayenta, wataƙil ta sanadin haka nima na samu haske a nawa binciken. Wannan shine dalilin dawowar Ummukulsoom gidana, tunda naga yarinyar hankalina saiya kuma tashi, dan tabbas akwai kamanni a tsakaninku, sai mutum ya maida hankali sosai zai fahimci hakan, wannan ne yasa nai duk wani ƙoƙarin ta zauna tare damu domin jifan tsuntsu biyu da dutsi ɗaya, ta samu cikar burinta, nima na samu cikar nawa burin. Zuwan su Bilkisu garin ɗilau rakkiyar Ummu ne ya kuma tabbatar min da akwai ɓoyayyen sirrin da ban saniba game da mahaifiyata, amma gudun ɓacin rankine yasa na hana akawo Ummukulsoom gidannan a tsawon shekarun da tai tare dani, anawa tunanin saina gama gano komai, to gashi kuma ban gama gano komanba Attahir ya kawota”.

         Hawaye sosai Hajiya yaya take sharewa, haka ma Ummukulsoom da duk mamaki ya kamata, itako ashe lallai haukar ƙuruciya na ɗawainiya da ita, dan bata taɓa kawo komai gameda zamanta gidanba, hakama sometimes mutane kance tana kama da Bily, amma bata taɓa gasgata zancenba saboda ita bata ganin kamannin.

         “ALLAH yay maka albarka Abubakar, ba abun kunya yasani ɓoye maka komaiba, bin Umarnin mahaifinane, inason garinmu, inason zuwa cikinsa, inason ahalina dake cikinsa, sai dai wani furuci yay min hijjabi da tsintar kaina a cikinsa”.

     “Sunana Ummukulsoom na yanka”.

     Gaba ɗayansu suka kalli hajaiya yaya da mamaki.

    Murmushi tai musu tareda jinjina kanta, “Ƙwarai da gaske sunana kenan Ummukulsoom, Mu uku mahaifinmu ya haifa a duniya wato malam Ado ba rinji”.

    Da sauri Ummukulsoom ta kalli hajiya yaya jin sunan wanda ta ambata.

    Nanma murmushi Hajiya yaya taima Ummukulsoom ɗin, sannan ta cigaba da faɗin, “Ni ce babba a gidanmu, sai ƙanwata Hindatu, sai autanmu Lirwanu. Muna samun gata a wajen mahaifinmu dan mahaifiyarmu tun a wajen haihuwar Lurwanu ALLAH yay mata rasuwa, kulawar da mahaifinmu ke manace ya saka iyami tsanarmu, wato matar babanmu, a haka muka rayuwa cikin wata bahaguwar rayuwa a hannun Iyami, a wajen baba kawai muke samun sauƙi. Shekarata 12 baba yay shirin aurar dani, dan haka ya bada sadaka ta ga Ɗan-asabe, anyi baikonmu da ɗan-asabe duk da ba sonsa nakeba, amma biyayya ta saka ban musaba.  Bayan baikon mu da sati guda na tafi kiwon dabbobi daji ni da Hindatu kamar yanda muka saba a kowacce damuna, dan anayin ɗaurene, zalincin iyami yasa da ta sai ciyawa gwamma ta sanu kwance dabbobin mu tafi kiwonsu daga safiya har yammaci, randa mukayi gigin dawowa da wuri ta lakaɗa mana duka tace cikin dabbobinta bai ƙoshiba, idan kuma lokacin rani ne bata sakinsu, saidai muje daji muyo musu abinci, hakan ba komai bane face salon ƙuntata mana. A wannan ranar da muma fitane muna tsaka da kiwo sai maciji ya sareni, take a wajen na zube, dan haka hankalin hindatu ya tashi ainun, tashiga kuka da kururuwar neman taimakon wani. Ana haka ALLAH ya kawoshi cikin mota”.

      “Hajiya yaya wake nan?”. Cewar Attahir.

     Murmushi hajiya yaya tayi tana gyara zama, “Attahiru mi kakeci na baka na zuba, ai yanzu zaka sanshi. Ba kowa bane face kakan ku, shine ya taimakeni bai saurari komaiba ya ɗaukeni yasa a mota tare da Hindatu ya nufi Zaria da mu. Ni bamma taɓa zuwa zaria ba sai ranar, ALLAH ya taimaka dafin macijin mai sauƙine, sai aka samu kaina cikin amincin ALLAH, amma dai an kwantar dani a asibitin. Shine ya koma da Hindatu Ɗilau suka sanar da halin da nake a ciki, hankalin baba ya tashi matuƙa, yay ta sakama kakan ku albarka tare da godiya. Amma Iyami gareta ba hakan baneba, ita masifa ma take ina dabbobinta? Sai a sannan kakanku ma yasan abinda yakaimu jeji har wannan lamari ya faru. Gidan maigari baba yakai cigiyar dabbobinta, kaifin yabiyo kakanku su dawo Zaria wajena. Indai taƙaice muku zance shine yayta ɗawainiya da hidimar asibitinmu harna warke, sai dai kuma Ubangiji mai hikimane, dan kuwa shiyya saƙa soyayya mai ƙarfi tsakanina dashi a wannan jiyya, bayan warkewata muka dawo ɗilau, sai ya zamana duk sati saiyazo ɗilau. Hakanne ya tashi hankalin Iyami, dan kuwa ta ɗau alwashin waninmu bazai taɓa samun cigaba ba, yanda bata haihuba a gidan mu da aka haifa sai dai muƙare rayuwarmu a wahala. Ita ta fara fargar da baba wai soyayya nake da Ibrahim. Hankalin baba saiya tashi saboda yana ganin yarigada ya badani, janye waccan maganar kuma tamkar zubar da kimarsa ne, sannan hana Ibrahim ni tamkar butulcine, sai yay yunƙurin datse alaƙar da hanzari, amma kuma sai hakan bata faruba, dan kuwa yana tunkarata danson jin gaskiyar zance na sanya kuka akan nifa lallai Ibrahim nake so, dama kuma banason Ɗan-asabe kowa ma yasan hakan. Da farko Baba kam lallaɓani ya farayi, ganin naƙi saurarensa saiya canja salo saboda zugashin da Iyami keyi. tun anayin abu iya gidanmu harya fito ya fara yawo a garin ɗilau, kowa ya samu abin faɗa. Hakan ya kuma birkita baba ya gaza fahimtar ba laifina bane, zuciyata ce, yagaza fahimtar sheɗancin Iyami. Ibrahim shima yana matuƙar sona sosai, dan kullum cikin zuwa roƙon baba yake amma baba ya baɗe idonsa da toka yaƙi saurarensa. A wani dare sai hindatu ta tadani na rakata banɗaki amma sam naƙi, nace in bazatajeba sai dai tayisa a wando. Ƙyaleni tayi ta fice dukda tanajin tsoro, batafi mintuna uku ba sai gata tadawo, “Yaya, yaya tashi kiga mi Iyami keyi”.

     “Tashi nai zaune da sauri, nace, “Mi Iyamin keyi?”.

     “Ke dai taso ki gani Yaya, dan bayanina bazai gamsar da keba”.

    “Ban musaba na tashi na bita, ta can bayan ban ɗakinmu inda Rumbu yake muka iske iyami tana haƙa rami, laɓewa mukayi ta gama tsaf ta saka wasu layu a ramin, sai da tagama harda yayyafa ruwa ta maida ƙasa ta rufe kafin ta miƙe tana ƴar dariya, “Umma ɗan-asaben ma basamun damar aura zakiyiba balle wani Ibrahim ɗan birni, kamar yanda malam ya sanarmin layunnan na cika kwana goma a ƙasa Ibrahim zaiyi iskanci dake, na tabbata hakan ne zaisa kowa ya tsaneki a ƙauyennan idan kikayi cikin shege, mahaifinki ya tsine miki ya koreki, na gama da babinki, saura Hindatu itama”.

      Gaba ɗayanmu mun tsorata da kalamanta, danni harma na fara hawaye, da ƙyar muka ɗauke numfashi yayinda zata wucemu, a ranar bamuyi barcin sauran darenba daya rage. Washe gari tunda safe muka nufi gidan ƙanwar mahaifiyarmu muka sanar mata abinda mukaji, itama hankalinta ya tashi, dan haka tace mu turo mata Ibrahim idan yazo. Dato muka amsa, cikin amincin ALLAH kuwa washe gari saiga Ibrahim, dayake a lokacin a ɓoye muke haɗuwa, shine na sanar masa da zancen Innarmu. Bai musaba mukaje wajenta. Bayan sunyi gaisuwar mutunci tace, “Bawan ALLAH da gaske kake son ƴata kuwa?”.

      Cike da ladabi Ibrahim yace, “Wlhy Ina sonta Inna, kuma a shirye nake na aureta ko a yanzunnan ne”.

     “To Alhmdllhi, yanzu inaso ka ɗauki Umma kuje garin ɗan-gamau a katsina, idan kunje garin kuyi tambayar gidan Malam Baushi, kuyi masa bayanin komai daya faru, kuce masa nace ya ɗaura muku aure, Ibrahim ga amanar Umma nan, idan kaci ALLAH ya ci taka, karku zo Ɗilau saita haihu”.

    Godiya mukai mata muduka muna kukan jin daɗi, a ranar muka tafi babu wanda yasani har Hindatu, duk yanda Inna tace muyi haka kuwa mukayi, Malam Baushi ya ɗaura mana aure, satinmu ɗaya a can Ibrahim ya ɗaukeni muka wuce legas wajen aikinsa, ban fuskanci matsala a wajen danginsa ba danshi marayane. Ban sake waiwayen garin ɗilau ba, dukda kuwa ina matuƙar kewarsu, sai da na shekara biyar, dan har lokacin ban haihu ba, saida na shekara biyar da wasu watanni nasamu cikin Abubakar, bayan haihuwarsa naso zuwa Ɗilau domin cika alƙawarin inna amma sai wani aiki ya riƙe Ibrahim, dan haka ya bani haƙuri, dan shi burinsa muje tare mu nemi gafarar baba, zamu-zamu tafiya bata yuwuba har na yaye Abubakar, kwatsam kuma saiga wani cikin, ganin haka sai Ibrahim ya lallabani akan nai haƙuri na haihu saimu tafi, ƙilama Baba yafi karɓarmu. Hakance ta faru kuwa, dan saida na haihu tagwaye duk mata sannan muka shirya zuwa ɗilau. Komai ya canja mini daga yanda na sanshi, abubuwa da yawa kuma sun faru, dan ansha tashin hankali bayan nemana da akai aka rasa, a maimakona sai aka ɗaurama Hindatu Aure da ɗan-asabe, baba kuma yace ya barma duniyani, har abada ya cureni cikin ƴaƴansa. Har zuwanmu ɗilau baba na akan bakansa na ƙin karɓata, dankuwa muna fita a mota bai bari nataka koda zauren gidanmu ba yace mu juya, tareda furucin inhar na sake dawowa garin ɗilau ALLAH ya isa bai yafemin ba. 

     Hajiya Yaya ta fashe da kuka mai tsuma rai, wanda yasaka su Ummukulsoom da Attahir harma da Abba kuka suma, da ƙyar Hajiya yaya ta tsagaita taci gaba da faɗin, “Bansan yanda zan fassara muku halin dana shigaba dagani har ibrahim, da ƙyar nasamu wani ya faɗamin inda Hindatu take aure, Lurwanu kuwa na iske ya rasu sanadin zazzaɓi da yayi. Naje gidan Hindatu, muka rungume juna muna kuka, na isketa har tayi haihuwa Uku ita, ƴar da take goyo ma tsakanin haihuwarta da ƴan biyuna kwana ukune, na amshi ƴar saina ganta a langaɓe, hankali tashe na kalli Hindatu da itama take kallona tana kuka.

    “Hindatu miya sametane?”..   

      “Yaya ta rasune yanzunnan, ina kukan mutuwartane ma kika shigo”.

     Sosai hankalina ya tashi nima, na rungume yarinyar a jikina ina hawaye, muna cikin haka saiga ɗan aike daga baba, yace inhar ban zo nabar garinnanba yazo gidan hindatu ya iskeni saiya min abinda ban taɓa tunaniba, kuka na kuma fashewa dashi, na kalli hindatu da itama kukan takeyi.

         “Hindatu dan ALLAH kimin wani taimako kafin nabar garinnan”.

     “Inajinki yaya ki faɗi komiye zan miki”.

    “Hindatu ba kowa yasan ƴarki ta rasuba, dan ALLAH ki bani gawarta, nikuma na baki guda ɗaya cikin ƴan biyu, inason ɗaya a cikinsu ta tashi a garin haihuwata, tunda ni an haramtamin koda zuwa cikinsa, dan ALLAH hindatu ki taimakeni, nasan har abada ba sake haɗuwa zamuyiba”.

    Fashewa tayi da sabon kuka tareda ƙankameni, tace, “Yaya mizai hanani aminta da shawararki, wlhy na yarda, ke kaɗai gareni kaf duniya, gashi kuma ƙaddara ta daɗe da shiga tsakaninmu, mizai sa bazan ji daɗiba idan har kika bar jininki a wajena amatsayin ƴar dana haifa”.

     Nace Na gode hindatu, sauri sauri muka cire kayan jikin Hassana muka maida jikin gawar Ɗahara, na ɗahara muka sakama Hassana, inaji ina gani nataho na baro ƴata hannun ƴar uwata, ko mahaifinta bai saniba, dan baba tozarci bana wasaba ya shigo har gidan Hindatu yanamin dagani har Ibrahim dake mota yana jirana shida Abubakar dake ya yayye. Saida mukazo gida nace masa Hassana ta rasu a madadin gawar Ɗahara ɗiyar Hindatu, damuwar da muke cikice ta kauda damuwar rasuwar Hassana a zuciyarsa, niko inata kewar ɗiyata tunda nasan bata rasuba. Tun daga wannan ranar ban kuma waiwayar ɗilauba, tunma ina kuka harna haƙura, naci gaba da rainon Husaina, bayan shekara biyu Husaina ta rasu saboda ƙyanda da tayi, daga nana Abubakar kaɗai ya rage mana a gabanmu, a legas muka cigaba da rayuwa har Abubakar yakai minzalin aure sannan muka dawo kd, koda muka dawo ban taɓa waiwayen ɗilauba, saboda katangar da Baba yaymin da ita, Har ALLAH yayma Ibrahim rasuwa bayan haihuwar Attahir kuma yanata burin hakan, amma ALLAH yay alƙawarin bazai sake taka ƙasar canba shiyyasa harya rasu bai cika alƙawarinsa na dai-daitani da Baba ba. Wannan shine labarina, inaji a jikina kuma lallai Ummukulsoom tanada alaƙa da ahalina, amma tambayoyin dazan matane kawai zasu bani wannan tabbacin.

      Jikin Hajiya Ummukulsoom ta faɗa ta fashe da kuka, “Hajiya wlhy basai kin tambayeni komaiba, ni ɗin jininki ce, dan kaf sunayen waɗanda kika ambata sun tabbatar min da hakan, Gwaggo hinde kakata ce, itace ta haifi mahaifita Ɗahara......”

     Ɗagota da sauri Hajiya yaya tayi, jikinta har rawa yake tace, “Da gaske kike ƴarnan?”.

     “Wlhy hajiya na tabbatar da hakane kuwa”.

     Fashewa da kuka Hajiya yaya tayi yanzu kam mai ban mamaki da yafi na ko yaushe, tabbas inhar maganar Ummukulsoom gaskiyane to itaɗin jinin ƴartace Hassana data bama Hindatu.

      

     Zaid da Bily dake maƙale a ƙofa suna kuka suma suka kalli juna, cikin kasa-ƙasa da murya maman Ahmad tace, “Ba kallon juna zamu zaunaba, hanyar ɗilau yakamata mu dosa ɗakko Gwaggo hinde”.

     “Maganarki gaskiyane Aunty Hafsat, kumuje kawai, insha ALLAHU daga nan zuwa bayan isha'i na tabbata zamu dawo”.

     A tare suka ɗaga kai tareda juyawa suka fita da hanzari.


      A ɗaki kuwa numfashin Hajiya yaya ne yafara gagarar ƙirjinta, hakane yasaka Abba da Attahir rikicewa, dan tabbas ciwontane ke barazanar tashi.

      Ummukulsoom da batasan komaiba akai tai masifar kuma rikicewa, sai girgiza hajiya yaya take tana kiran sunanta.

    “Attahir maza kira Ummin ku tazo da gaggawa”.

     A rikice Attahir ya amsa da to, tare da zaro wayarsa daga aljihu............✍🏻



GASKIYA HASKE CE. AKASINTA DUHU NE



NO. 32



        *PARIS*


.........Yanda yake kwara rar da uwar zufa ga mutsu-mutsu da ya keta zubawa cikin barci ya bama Meenal mamaki, ta girgiza ƙafarsa yafi sau goma amma bai farkaba, ruwan dake a ajiye a durowar gefen gadon ta ɗauka ta ɗansa a hannu ta yarfa masa akan fuska.

     A matuƙar firgice ya farka yana faɗin, “Suhailat! Suhailat!!”. Tare da rarumo Meenal zai riƙe.

     Duk da ta lura ba a hayyacinsa yakeba saita fusge hannunta.

    Baseer da bai gama dawowa hayyacinsa ba yacigaba da sambatu, “Suhailat dama kece kika saka Meenal ta aureni? Suhai.........”

     Ƙara Meenal ta ƙwala da ƙarfi a saitin kunnensa, hakan yasashi dawowa hayyacinsa sosai, ya waiga yana kallon ɗakin tareda Meenal dake zabga masa harara, ta kumbura tayi fam da kishi, a hasale tace, “Munafuki, ALLAH ya toni asirinka, wacece kuma Suhailat?!”.

         Innalillahi wa'inna ilairirraji'un ya shiga mai maitawa a zuciyarsa, domin dai ya fahimci mafarki yayi ashe, jin Meenal ta fashe da kuka yay azamar dirowa daga gadon yay kanta jikinsa na ɓari, “Please Meenal wlhy mafarki nayi, dan ALLAH ki tsaya ki fahimceni....”

      “Anki a fahimcekan, Baseer ni zaka yaudara? Dama akwai wata mace a ranka amma kacemin baka taɓa son wata mace ba saini?.....”

     “Wlhy gaskiyane Meenal, dan ALLAH ki saurareni na miki bayani, a tsawon shekara biyar da mukayi da ke kin taɓa jin na ambaci sunan wata mace idan ba yauba? Kin taɓa kamani da wata mace koda a cikin waya ne? Haba Meenal”.

      Shiru tai tana kallonsa, dan kuwa maganarsa gaskiyace, tunda sukai aure suke zaune a Paris bata taɓa kamashi da hakanba, dukkan soyayyarsa da kulawarsa akanta yake nunata, ta sauke numfashi tana mai zuwa da ɗan gudu ta shige jikinsa.

     Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana ambaton Alhmdllh. Sai dai dukkan jikinsa a sanyaye yake, wannan mafarkin yay masifar tada hankalinsa gaskiya.......

     Meenal ta katse masa tunani da ɗagowa daga jikinsa tana faɗin, “Ammafa wannan ko wacce shegiyar Suhailat ce da tazo maka a mafarki na tsaneta, nifa koda macen ƙuda bana fatan ta raɓeka balle har asamu shegiyar da zata ziyarceka a mafarki”.

     Murmushi kawai yayi yana haɗiye tashin hankalinsa, “Ai wannanma ba da arziki tazo minba a mafarkin Dear, dan haka karma wannan ya dameki”.

       “Shikenan My boo..., dama fa mun kusa makara, kai maza ka shirya, kasan dai jirginmu 4:30pm zai tashi zuwa 9ja”.

         Kai kawai ya iya ɗaga mata tareda nufar bayi.

    Ko a cikin ban ɗakinma ruwa kawai ya sakarma kansa, ya tsaya yana zuba a jikinsa, yayinda zuciyarsa ta kuma lulawa tunano mafarkinsa.

    Miyasa tunda yabaro Nigeria bai taɓa irin wannan mafarkinba sai yau? Mafarkin fa ya nuna masa Meenal haɗa baki sukai da Suhailat ta auresa, ya rumtse ido da sauri zuciyarsa na tsitstsinkewa, sai kuma maimaita sunan Suhailat yake, shikam dai da ya na da dama da komawa Nigeria ɗinnan da ba'ayi dashiba, duk da yana kewar Innarsa da baba da yayarsa Talatuwa, tsawon shekara biyar kenan tunda sukai aure da Meenal sukazo bai taɓa waiwayar gidaba, koda sha'awa ma baya son zuwansa, yanzun ma zaɓen da akaine mahaifin Meenal yasamu kujerar gwamna shine za'a rantsar dasu zasuje, amma shida Meenal ko wajen zaɓen basujeba, Abban Meenal ya hanasu, a cewarsa yana gudun rikici, bama su kaɗaiba dukkan sauran ƴan Uwan Meenal din dake anan basu jeba.

    Knocking ɗin da tai masane yasashi katse tunaninsa yay sauri yay wanka ya fito, sauri-sauri ta taimaka masa ya shirya, dan Maman Meenal nata musu waya akan sufa ake jira.

        

     Sai da suka kashe komai na kayan wutar gidan kafin su fice zuciyar Meenal fari ƙal, saɓanin ta Baseer dake a dagule da mafarkin da yay, kai tsaye airport suka nufa, inda dukkan ahalin Meenal suke jiransu suma.

     Bayan ƴan gaishe-gaishe aka fara shirin tafiyarsu, sune sunayen farko da aka fara kira, dan haka sune suka fara shiga waje na musamman.

    Gaba ɗaya zuciyar baseer ta kasa sukuni, duk hirar da akeyi ya kasa saka baki, harma yayan meenal ɗin ya fahimta yafara tambayarsa ko bai da lafiya ne?.

     Murmushin yaƙe yayi, yana gyara zamansa, “Lafiya ta ƙalau Bro.. Haneef, kawai dai barcine bai isheniba”.

    ƴar dariya Haneef yayi yana masa jin jina......


         A filin jirgin lagos suka sauka, daga can suka hau jirgi mai zuwa Katsina kai tsaye.

       Wannan shine karon farko da Baseer zaije gidansu Meenal na Nigeria, motoci na alfarma ne sukazo kwasarsu, Baseer sai wani faɗi ake ana buɗawa shi mijin ƴar gwamna🤣.

      Ƙayataccen gidane wanda ya amsa sunansa gida suka isa, sosai komai ke ƙayatar da Baseer, part ɗinsa da ban shida matarsa Meenal, waddama suna ajiye kaya bai sake ganin ƙeyarta ba ta shige cikin ƴan uwanta, zamanne ya ishesa shima ya ce bara yaɗan fita ko tsakar gidane yasha iska. Sai dai yana taɓa ƙofar yajita gam, Meenal ta kullesa, wani haushine ya kamasa, kishin meenal yayi yawa, ya tabbata dan karya fitane tai masa haka, ya furzar da iskar bakinsa yana komawa ya zauna a falon.

     Son da yake matane yake sanyashi shanye duk wani iskanci da take masa, harga ALLAH yana ƙaunarta sosai.


             Bata dawo sashenba sai dare, ta rungumeshi tana faɗin, “I miss you my bobo”.

     “Ƙyace hakafa tunda kin shige cikin ƴan uwanki kin manta dani, danma wulaƙanci harda kulleni”.

    Dariya tayimasa tare da gwalo, “Hhhh bana buƙatar kowa ta ganarmin miji, ai harma a gama taron nan bazakaga wajeba”.

    Baki a hangame yake kallonta, “To inkuwa hakane ki barni na wuce garinmu nima naga su Innata”.

      “Lah wasa nake maka fa, indaima ka fita to sai tare dani”.

     Yanzu kam murmushin yaƙe kawai yay mata bai iya cewa komaiba.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡



           A ɓangaren su Zaid kam da dabara suka ɗakko Gwaggo hinde daga ɗilau, lokacin da suka iso cikin kaduna har tara na dare yayi.

    Kai tsaye gidan Hajiya yaya suka nufa, dan sunsan su Abba ma dai duk suna can, tunda bayan tafiyarsu Abba ya kira yaya Zaid yana tambayar suna ina a rikice.

    Shine yace masa sunje wani wajene amma insha ALLAH zasu dawo a yau, babu yanda Abba baiyi ba dan yasan inda sukaje amma sam Zaid yaƙi faɗa, hakane yasa duk bayan wasu awas sai Abban yakira yaji wane hali suke, sai faɗa yake musu akan fita basu sanarba.

            A galabaice suka iso da Gwaggo Hinde kaduna, dan bata taɓa doguwar tafiya irin hakanba, iyakar yawonta baya wuce Zaria😂.

      Tunda motarsu ta tsaya Ummi da Abba da Attahir suka fito.

     Ganin su Zaid da babbar mace waddama tafi Hajiya yaya tsufa saboda jin daɗi ba ɗayaba ne ya basu mamaki, Attahir daya gaza haƙuri yace, “Kai wai wacece kuka kawo wannan?”.

       “Yaya mu shiga daga ciki, zamuyi muku bayani”.

     Babu wanda ya sake magana, Ummi ta matso ta taimaka musu wajen shigar gwaggo hinde ciki.

       A falo Zaid sai waige-waigen inda zaiga Ummukulsoom yake da hajiya yaya, dukda Ummi ta fahimta sai batabi ta kansa ba, saima shayi da taje ta haɗoma Gwaggo hinde.

     Bily ma da ta matsu taga Ummukulsoom ce ta kasa hakuri itakam, matsawa tayi wajen yaya Attahir a hankali tace, “Yaya Ummukulsoom fa?”.

           “Tayi barci Bilkisu, dan ta fama ƙafarta saboda ruɗewa da tashin ciwon Hajiya, sai da aka sake nemo mai gyara yay mata, shine Ummi tai mata allurar barci danta huta”.

      Cikin damuwa Bily tace, “ALLAH sarki bestie na, ALLAH ya basu lafiya itada hajiya”.

     “Amin bily. Wai wacece wannan?”.

      “Yaya zaku sani, amma kuyi haƙuri ba yanzu ba”.

     Bai sake ce mata Uffanba, haka suma su Abba basu sake tambayarsu wacece Gwaggo Hinde ba, itakuma jigartar datai tasata yin tiɓis, burinta kawai ta kwanta ta huta.

     Hakanne yasa tana kammala shan tea din da Ummi ta haɗa mata saita bata wasu magani tasha aka rakata inda zata kwanta ta huta.

      Suma ɗin Abba cayay su koma gida, shi zai kwana anan shi da Ummi.

        Attahir yace, “A'a Abba, ka gafarceni kuje ku ku huta, ni zan kwana anan ɗin kawai”.

    Bily ma tai caraf tace, “Abba nima dan ALLAH, kaga fa Bestie na nan”.

      Murmushi kawai Abba yay yana girgiza kai, yace, “to indai hakane kai Attahir kuje gida kawai harda Zaid, ita Bilkisu saita kwana dasu, ni da Umminku ma anan zamu kwana”.

      Duk yanda sukaso dole sukabi Umarninsa, suka wuce gida su uku akabar Ummi da Bilkisu nan, ɗakunan dake can gefe Ummi da Abba suka  tafi, bayan Ummi ta kuma duba su Ummukulsoom ta tabbatar babu wata matsala.


*_WASHE GARI_*


       Alhmdllh kowa ya tashi, musamman ma Hajiya yaya da ciwon nata yake tamkar iska dama, Ummukulsoom daice keɗan ɗangyasa ƙafarta, amma dai Alhmdllh batajin ciwo kamar jiya.

    Ummi da kanta ta tashi ta shirya breakfast da zai dace da cin kowa na gidan da taimakon mai aikin hajiya yaya, sai Bily dake ƙoƙarin tsaftace ko ina.

        Tunda garin ALLAH ya waye hankalin gwaggo hinde a tashe yake, burinta taga ta inda Ummukulsoom zata ɓullo, amma taji tsit. Gashi bata zaƙeba ta fito a gidan mutane batasan ina zata dosa ba.

    Tana tsaka da wannan tunaninne Bily ta shigo ɗakin da sallama Ummi na biye da ita.

       Daɗi ya kama Gwaggo Hinde, bayan sun gaisa Da Ummi cikin girmamawa ta ce, “Bilkisu ni banga ƙawar takiba ai har yanzu, ko sai ta gama mini yangane”.

     Dariya sosai Bily keyi, cikin tsokana tace, “Gwaggonmu ta mutunci,   What Are you eating na baka na falling down ne, yanzu zakiga Bestie na harda babban abun mamaki wanda nasan zan samu ƙyauta ta musamman a gareki”.

     “Tofa ƴar nema, ina jiran ganin wannan abun mamaki kuwa”.

     Ummi dai na jinsu tana murmushi kawai, tunaninta ya fara hasaso mata labarin da Abba ya bata a daren jiya, amma dai zatabi yaran nata dan ganin manufarsu, ba zata zama mai musu ƙutseba.

      Bily ta haɗama Gwaggo hinde ruwan wanka mai ɗumi, sai da ta taimaka mata tashiga bayin saboda karta zame a tiles tunda ba sabawa tayiba, dama da asuba itace tazo tai mata jagora tai alwala. Kafin Gwaggo hinde ta fito Bily ta gama gyara ɗakin tsaf ta saka mata turaren wuta tareda ajiye mata man shafawa.


★★★★★


       “Waini bestie ina kiketa shiga da fitane? Nagama kamar baki damu daniba”. ‘Ummu ta faɗa a shagwabe’.

      Dariya Bily tayi tazo tana rungume Ummukulsoom, “Oh sorry dear, in banji ciwonki ba wama zaiji a gidannan, jima nake kamar ya dawo kafata, ai Yaa Amaan yasa ina jin haushinsa wlhy akan wannan abu”.

     Baki Ummukulsoom ta cije tana ƙwafa, amma sai batace komaiba.

         Hajiya yaya duk na jinsu amma sai bata tankaba, dan ranta duk a jagule yake, sosai take ƙwaɗayin son ganin wani nata taji koda labarin ahalin tane, tasan dai kam da wuya ace mahaifinsu nada rai yanzu, sai dai tana tsoron tambayar Ummukulsoom komai a yanzu ma............

        

      “Lah Gwaggo hinde!”. ‘Cewar Ummukulsoom cikin tsananin murna, hakanne ya katsema Hajiya yaya tunaninta cikin tsitstsinkewar zuciya ta ɗago ta kalli bakin ƙofar ɗakinta da Gwaggo hinde ke tsaye bayanta Zaid.

      A zabure ta mike tana nuna Gwaggo hinde hannunta na karkarwa, hakama bakinta, “Hin...hinda....tu kece da gaske?”.

      “Yaya!” ‘Gwaggo hinde ma ta faɗa tana zazzaro idanu tareda ture Ummukulsoom data shige jikinta’.

       Ai tuni ɗakin ya harmutse, babu mai jin zancen wani, Hajiya yaya da Gwaggo Hinde duk sun rungume juna sunata rusar kuka, Abba ma sai sharar ƙwalla yake da babbar riga.

       Bayan wasu mintuna kusan arba'in komai ya natsa, Hajiya yaya na kwaƙume da hannun Gwaggo hinde kamar za'a sake rabasu, har yanzu hawaye yaƙi tsayawa a tsakaninsu, kowanne na mamakin hukuncin ALLAH, musamman ma Gwaggo hinde da ta daɗe kamannin Zaid na rikitata ainun, hakama kamannin Bily da Ummukulsoom.

        Ummi ce cikin lallashi ta lallaɓasu suka ɗanci abinci, tabama hajiya yaya maganinta tasha sannan akai zama na musamman a falon Hajiya yaya, kowa kagani yana cikin wani yanayi na farin ciki da girmama ikon ALLAH mai tsara yanda yaso ga wanda yaso, akuma lokacin da yaso....



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


         Dad daketa zagaye falonsa bayan tafiyar su Ummukulsoom yaji motsi a bayansa, juyowa yay yana kallon Momcy da itama ta kafesa da ido cike da damuwa, ɗauke kansa yay tamkar bai gantaba, saima ya nufi hanyar bedroom ɗinsa saboda daga ita har ɗan nata takaicin ganinsu yakeyi....

     Da sauri ta katsesa ta hanyar faɗin, “Dan ALLAH Abban Fodio kayi haƙuri, mu ɗauki hakan a matsayin kuskure, kasan hakannan da gangan bazai cutar da itab......”

      “K! Jamila ki kiyayeni wlhy, inba hakaba daga ke har Fodio zan saɓa muku a gidan nan, idan ke baki san wacece itaba aishi daya aikata ya sani, dan haka ki fita daga idona kafin na rufe dake a ciki wlhy kinji na faɗa miki”.

      Sosai ta tsorata dashi, dan tasan halinsa balle idan ya fusata, tarasa minene yasashi ɗaukar zafi akan wannan yarinya? Kodai kawai dan kar Fodio ya aure ta ne?.

     A wannan tunanin ta zauna, tasan dai bai wuci yace zai horasa akan yay masa aure ya saki ba, zai dinga bin hanyar da duk tazam ta sanadinsa ya daƙile idan Fodio ya samu matar aure mai dangantaka dashi, musamman wannan da suke da alaƙa mai ƙarfi tsakaninsa da Alhaji Abubakar, tai murmushi tana kallon ƙofar da ya shiga,

     “Alhaji kenan, to ai hanyar ALLAH yawane da ita, insha ALLAHU wannan ɗin sai ta zama matar Fodio, zanbi ta hanyar Hajiya Na'ima (Ummi), sannan nasa Fodio yay farautar zuciyar yarinyar, inhar so ya shiga sai naga ta inda zaka hana, tunda kai baka manta abinda ya wuce a rayuwarka.

     Oho shi baima san ta nai ba.


    Amaan kuwa dake a  sashensa Momcy na fita shima ya hau haɗa kayansa, a yau ɗinnan zai koma Lagos koda ta motane, bazai taɓa barin wannan tunanin yay barazana da ransa ba, danshi shirmema ya ɗauki sosayyar tun tuni, shiyyasa bai taɓa yin taba...............✍🏻



NO. 33



     .........“Yaya kin ɓata ɓat, baba yasa anyi   nemanki daga baya har an gaji, wani yaro Sallau har danfarar sa yay ya saida ƙaramar gonarsa ta bakin fadama ya bashi kuɗin akan wai ya ganki a Legas zai je ya kawo ki gida, amma yaron nan tunda ya tafi bai sake dawowa ɗilau ba sai da baba ya rasu”. ‘Gwaggo hinde ta ƙare maganar da fashewa da kuka’.

     Itama Hajiya yaya kukan takeyi jin Baba ya rasu, “Hindatu kina nufin ALLAH yay ma baba rasuwa?”.

    “Eh yaya baba yarasu tun bayan Auren wannan ƴar (Inna Laraba, bata faɗar sunanta saboda ƴar fari ce), bayan tafiyar ki a zuwan da kukayi baba ya ɗau zafi sosai, ashe Iyami ce ta tunzuro shi, sai da inna haule ta dawo daga tafiyar da tayi katsina, kinsan sanda kukaje baku isketa ba, to bayan dawowarta taji abinda ke faruwa tazo har gida ta sake tambayata, ban ɓoye mata komaiba na sanar mata, itace taje ta samu baba ta warware masa komai har yanda kuka gudu, aiko baba yayta kuka yana dana sanin korarku da yayi, tunda ga nan yashiga nemanki, itakuma iyami ya saketa, amma sam sai ba'a daceba harya kwanta ciwo, kusan shekararsa ɗaya yana jiyya ALLAH yay masa rasuwa, sai dai yace ko bayan ransa aka ganki a shaida miki ya yafe miki duniya da lahira, kema ki gafarcesa keda mijinki”. Kuka sosai Hajiya yaya da Gwaggo hinde sukeyi, sai da ƙyar suka tsagaita, Gwaggo hinde ta nuna Ummukulsoom da itama ke kuka tana faɗin, “Wannan jikarmu ce, ɗiyar Hassana ce data bari, sunanki aka saka mata”.

      Hajiya Yaya ta kalli Ummukulsoom tana murmushi da zirar da hawaye a lokaci ɗaya, “ALLAH sarki, ashe Hassana rabuwar har abada mukayi da ita daga ita har baba, na gwada zuwa ɗilau yafi a ƙirga, amma kalaman baba ke hanani, ALLAH ya gafarta musu, Ummukulsoom zonan kinji”.

     Matsowa Ummu tayi ta shige jikin Hajiya yaya dake hawaye har yanzu, ji take tamkar tana tare da ɗiyarta Hassana.

    Bayan an sake samun nutsuwa Abba yay gyaran murya tareda jaddada godiyarsa ga ubangiji da ban haƙuri ga iyayen nasa, ya ɗora da faɗin, “Ubangiji sarkin hikima, ashe ni ƴata nake riƙo ban saniba, nayi murna da hakan sosai nakuma ji daɗi, a ƙiyasi mahaifinmu ya riga ƴar uwata rasuwa, dan haka tana da gadonsa kenan, dukiyar daya bari yazama ni kaɗaine magajinsa a yanzu hakan ya canja, dole za'a fiddama Hassana haƙinta a damƙasa ga ɗiyata mai sunan Hajiya tunda itace magajiyarta”.

     Ummu na hawaye tace, “Ni dai A'a Abba na yafe maka, ganinku ya fiyemin komai”.

     Murmushi Abba yay yana faɗin, “Mai sunan Hajiya ai haƙƙine, dolene kuma a fitar, ke dai ALLAH yay miki albarka, a yanzu saimu fahimci kuma duk abinda ALLAH ya jarabci bawa dashi badan baya sonsa baneba, na tabbata kinshiga ƙunci mai yawa sanadin matsalarki da Fodio, to ashe wani babban mabuɗin alkairinne ke bibiyar ki, ƙila da hakan bata faruba da wannan sirrin bazai taɓa buɗuwaba, har sai mu bar duniya da tabon a ranmu”.

    “Wannan gaskiyane Abubakar, dolene mu ƙara nuna godiyar mu ga ALLAH, kaima Attahiru ALLAH ya saka maka da alkairi, domin girman da ALLAH ya baka ka riƙe shi, ALLAH ya sake baka wuyan ɗauka”.

     Da amin kowa ya amsa, daga nanfa aka ɓarke hira, zuciyar kowa ƙal da farin ciki.

     Abba kam ai neman Dad yay a waya ya zayyane masa abin farin cikin daya faru.

       Rasama mi Dad zai faɗa yayi saboda al'ajab da farin ciki, a lokacin ya baro gidansa zuwa gidan hajiya yaya.

      Hajiya yaya sai ƙara zuba masa albarka takeyi, domin ƙyautatawar sa akan na ƙasa dashine da ƙyaƙykyawar zuciyarsa ta zama sanadi, da ace bai haɗa Ummukulsoom da Fodio aure ba da duk hakan bata kasanceba. Hajiya yaya sai kuma ƙarfafa musu gwiwa take akan su cigaba da zama masu adalar zuciya, domin hakan basusan alkairin da zai janyoma rayuwarsu ba.

    A dai ta ƙaice ranar saita zama anyi wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan biki a gidan, dan sai dare su Abba suka koma gida, aka bar Gwaggo Hinde da Hajiya yaya suna cigaba da hirar zuminci.

      

      Musalta muku farin cikin da Ummukulsoom ta tsinci kanta a cikima ɓata lokacine, amma kowa ya ganta yasan yau ɗin ta musamman ce, ga albishir da Dad yay mata na komawarta makaranta nanda sati ɗaya, zataje Law school, ta birnin ikko (Lagos) ta ƙarasa shekara ɗayanta da zai tabbatar da ita a matsayin cikakkiyar Barrister..


         Sai daren ranar Attahir yasan Amaan baya ma garin ya koma Lagos, murmushi ƙeta yayi dan kuwa abinda ya gudar mawa zaije ya iskeshi, da Ummukulsoom zasu tafi Lagos, kuma a gidansu zata zauna harta kammala. 



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


               Su baseer ansha shagalin bikin rantsarwa, yaci gayu yanata basarwa sai kace shine ɗan gwamna ɗin, danma Meenal ta kafa ta tsare saboda kar yayma wata mace magana....


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


         Zaune suke a katafaren falon gidansu, ta canja tamkar ba Suhailat matar baseer ba, ta kuma cika da girma dan batafi sati uku da dawowa ƙasarba ma, tana Germany karatu, waya take latsawa hankalinta kwance, yayi da su Mom ɗinta ke kallon labarai.

    Kamar ance ta ɗago sai ta kalli TV jin Daddynta tana kwarzanta bikin rantsarwar dayake shima yaje saboda mahaifin Meenal abokin sane.

    Ƴar zabura tayi tana kuma ware idanunta akan tv n, “Kam bala'i, Baseer!!”.

      Atare Mom da Daddyn ta suka kalleta tareda cewa, “Baseer kuma?”.

       “Ƙwarai kuwa Daddy, wannan Baseer ne ya gama magana a matsayin surukin gwamna, Daddy yaran Alhaji Ɗalha nawane mata?”.

     “Eh to, kamar guda biyu ne, ɗaya ce kuma tai aure shekara kusan biyar data shige, kinsan anyi bikin lokacin bana nan shiyyasa ban jeba sai Salman na wakilta”. 

        “To aiko lallai Abba shegen nan ne Baseer mijin”.

       “Ya zakice haka Suhailat? Tayaya kika san haka?”.

     “Mom ko shekara nawa nayi banga Baseer ba na gansa saina ganesa, Daddy kana da

Invitation ɗin bikin?”.

      “Za'a iya samu Suhailat, amma fa kinsan kusan shekara biyar kenan, ganesa sai ansha wahala”.

     “Daddy bazanji wannan wahalar ba, zanje na duba inda kake tara invitation card ɗinka yanzu nan, dan rayuwar yarinyar tana cikin haɗari, na tabbata itama ba sonta yake ba, kamar yanda yay min zai mata ya gudu”.

     “Gaskiyarki kuma Suhailat, kiyi dukkan binciken daya dace, inhar shine kam ya kamata mu fargar dasu”.

    “Insha ALLAHU kuwa Daddy na, nagode da goyen bayanka a gareni”.


        “Amma Alhaji inaga ya kamata kasan mi Suhailat zata aikata ma yaronnan, kar tunanin ɗaukar fansa ta sakata aikata abinda zamu dawo muna dana sani, kaga dai bikinta kwana kaɗan ya rage, ni dama za'abi ta taune da an barsa kawai duniya ai makaranta ce, zai haɗu da daidai shine a cikinta”.

     Murmushi Daddy yayi yana kallonta, “Karki damu a duk motsinta zan saka idanu, amma batun a barsa ma bai tasoba, dan kingansa fa yanzu a matsayin sirikin gwamna, zuwa nan gaba ina kike tunanin zai kutsa? Sannan bamusan su kuma da wace fuska yaje musu ba, irin waɗanan idan ba'a daƙilesu ba,  suke zamewa al'umma wata babbar fitina yayinda ALLAH ya basu wata dama ta mulkin ƙasa”.

     “Eh to hakane kuma Alhaji, ALLAH dai ya shiga tsakanin nagari da mugu, dankuwa yaron nan ya bar mana tabo mai girma, danma ALLAH ya taƙaita babu rabon ƴaƴa a tsakani”.

      “Wlhy kuwa Hajiya”.


       Yayinda suketa tattaunawa Suhailat nacan tana bincike, ganin zata wahala kafin ta gani saita ƙyale komai ta fito.

       Daddy dake kallonta yace, “Kin gansa?”.

     “A'a daddy, wannan zai zama mai wahala, ga shawara mana”.

      “Ina saurarenki auta”.

    “Daddy muje musu gaisuwar taya murna ta musamman dukkan iyalanka, ta wannan hanyarne kawai zan samu haɗa ƙawance da ita”.

      “Eh to kinzo da shawara, ki bari komai ya lafa zanyi tunani”.

       “Yauwa my sweet Daddy na, ALLAH ya ƙara yawancin kwana”.

     Dariya sukayi shida Mom.

    Itako ta fice zuciyarta fes, lallai Baseer yanzu ne za'ai karon, munafiki kenan mai fuskar zalunci,  mai ƙyan ɗan maciji. dolene ta nemo abokansa su Najeeb, ta hanyarsu tasan zata samu bayanai na musamman insha ALLAH.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


            Wannan karon kam baba har gidan Alhaji Abubakar yazo shida inna harira, daga can suka ɗunguma zuwa gidan hajiya yaya, inda akaita haba-haba dashi, domin kuwa surukine.

     Ya girgiza shima dajin labarin nan, duk da dai yaɗanji wani abun tun da ƙuruciya gameda hajiya yaya, amma kasan tuwar bata garin sai yazam komai an manta dashi, har ƙwalla yay daya tuna da matarsa abar alfaharinsa Ɗahara, wadda ashe sunanta na asali Hassana. 

         Kwana biyu da zuwan baba suka ɗunguma zuwa ɗilau su duka gidan, har hajiya yaya.

     Kuka dai ta shashi, ƙalilanne waɗanda ta sani suka rage a raye, sai waɗanda tabari suna ƙanana, suma yanzu duk sun tsufa da yawansu, dan danan ƙauyen ɗilau ya ɗauki sabon salon labari, su Ummukulsoom kam ansha yawo, dama tana kewar garin sosai, ta daɗe batayi kwanakin nanba.

        

        Komai na tafiyar Ummukulsoom ya gama kammala, dan haka suka baro ɗilau aka bar hajiya yaya acan akan itafa saita more zata dawo. sosai take ɗoki akan ganinta garin haihuwarta, wanda ada aka haramta mata shigarsa a shekarun baya.

     Su dai su Ummukulsoom kd suka dawo sukai shirin tafiya legas.

 


*_Ummukulsoom a birnin ikko karo na biyu_*


        A wannan karonma isowar ,dare sukayi, babu abinda ke fita a fuskar Ummukulsoom sai murmushin takaici, da tuna shekara biyar da wasu watanni da suka shuɗe, ta shigo garin a matsayin matar cushe a wancan karon, ta barsa a matsayin bazawara, yanzu kuma ta dawo cikinsa matsayin mai neman ilimi, fatanta ta fita a matsayin mai tarin nasarar cikar burinta.

      Maman Ahmad dake kallonta itama tai murmushi tana nuna ma Attahir ita.

     Murmushi shima yayi kawai, ya tabbata tana tuno waɗancan shekarun  ne da suka shuɗe.

    Ɗaukarsu akazo yi, Attahir da maman Ahmad suka shiga mota ɗaya, Ummukulsoom da Bily ma suka shiga ɗayar.

       Tunda suka shigo Barrack ɗin Ummukulsoom ta fahimci wasu canje-canje da aka samu masu yawan gaske, su Attahir dai suna nan gidansu data sani, sai dai kayan ciki da aka canja.

     Sam hana dukkan tunani mai alaƙa da tuna baya tai yay tasiri a kanta, ana basu masaukinsu ma itace ta fara shirin barci ta kwanta ba tareda ta nema abinci ba, dan sam batajin wata yunwa.

         Bily ma dai shirin barci tai tazo gefenta ta kwanta suka lula duniyar barci hankalinsu kwance.

 

     Washe gari da safe da taimakonsu maman Ahmad ta gyara gidanta tsaf ya dawo nomal kamar yanda take buƙata, bayan sun kammala breakfast Attahir ya fita ya barsu suna hirarsu.


★★★★★★


       Kansa tsaye gidan Amaan ya nufa da ƙafa, yay sallama a falon da yake tsit babu motsin kowa, ko kaɗan bai kula da Amaan dake zaune a dining yana karyawa ba, shiko tun shigowarsa ya gansa, amma yaki magana, saima ɗauke kansa da yay ya cigaba da cin abincinsa.

    Sai da yaga Attahir zai nufi bedroom ɗinsa sannan yace, “Kai kuma fa?”.

       Juyowa Attahir yay ya kalli dani ɗin, “Oh ashe ga gwairon nan zaune yanacin girkin ƙato”. ‘Attahir ya faɗa cikin jan magana’. 

    Sai a kai sa'a Amaan ɗin bai tanka ba. Kujera Attahir yaja ya zauna shima, “Su Ajiwa masu guduwa, to laifin da kaine yasaka tserowa kana tsoron na maka hukunci ko?”.

        Shi kansa baisan murmushi ya suɓuce masaba, duk yanda yaso ɗaukar zafi da Attahir baya iyawa, ya ɗago manyan idanunsa akan Attahir, “Wai kai bazaka canja bane ba?”.

       Dariya Attahir yayi shima yana kallonsa, “Ajiwa inhar baka canjaba ya za ai nima na canja, shikenan saika gudo ka barmu bayan kuma tare mukaje”.

       “Share kawai Attahir, ya ka baro mutanen kd n?”.

      “Kowa lafiya yake”.

 “To Alhmdllh, ga abinci”.

         “Wa? Kaima kasan wannan ganganne Ajiwa, inada matata na zauna cin girkin ƙato, wannan sai ku gwauraye”.

       “Kai dai ka sani mara mutunci kawai”.

    Dariya Attahir yayi, yasan dai ƙarshen zancen kenan, babu wanda ya sake magana a cikinsu har  Amaan ya kammala cin abinci suka dawo falo, abinda ya shafi aikinsu suka cigaba da tattaunawa, tareda shirye-shiryen ƙarin girman da ake shirin ƙara musu. Koda wasa Attahir bai sanar masa da zuwan su Bily ba.


       ★★★


     Tsawon satin su Ummukulsoom uku a cikin Barrack ɗin ALLAH bai taɓa haɗata da Amaan ba, harma ta fara zuwa makaranta.

       

     Yau ta kasance Alhamis, da wuri Ummukulsoom ta dawo gida saboda lecture ɗin safe tayi, akwai abokin su Attahir Bello matarsa ta haihu, gidansu kuma yana maƙwaf taka da gidan Amaan ne, lokacin da Ummukulsoom ta dawo daga school ta iske Maman Ahmad da Bily sun gama shirin tafiya gidan sunan, ita kaɗai suke jira, ganin zata ɓata musu lokaci sai Ummu tace suyi gaba, ita zata taho tare da Ahmad idan an ɗakkosa daga makaranta.  

     Tafiya sukai kuwa suka barta a gidan ita kaɗai, wanka tai ta zauna taɗanci abinci, tana zaune a falo saiga Ahmad ya dawo.

      Oyoyo tai masa ya faɗa jikinta yana mai jin daɗin ganinta, yaron akwai wayo sosai.

     “Aunty ina su Mama?”.

 “Sun tafi gidan suna Amadina, muma yanzu idan kaci abinci zamuje mu samesu”.

     Tsallen murna ya farayi jin za'aje yawo, itakuma tana masa dariya.

     Wanka tai masa ta shirya sa tsaf yay ƙyau, sannan ta nufi ɗakinsu itama ta shirya baƙar jallabiya da akai mata ado da farin zare dayaji stons, ɗan ƙwalin kawai ta naɗa ta riƙe waya da handky a hannu, sai takalmin ƙafarta fari flat, tayi ƙyau masha ALLAH.

      Kulle gidan tayi ta kama hannun Ahmad suka tafi cikin nutsuwa, tunda ta fito daga gida gungun matasan sojojin suka zuba mata idanu, kowa na yaba halittar ubangiji a ransa, itako ko sashen da suke bata kallaba, tafiyarta take kanta tsaye Ahmad na mata surutu tana murmushi. Ba taɓa zuwa gidan tayiba, amma maman Ahmad tace tai mata kwatance, tareda cewa ko Ahmad tacewa suje gidansu abokinsa Sulaiman zai kaita, kuma ma ai tunda taron suna ake zata gane.

    Tsayawa tai daga tafiyar da takeyi ta kalli Ahmad, “My Amadi wai kasan ina kuwa zamuje?”.

     “Eh Aunty, ba kince gidan su Sulaiman abokina ba”.

     “Yauwa yaron kirki ashe baka mantaba kuwa, muje to”.

     Ci gaba sukai da tafiya, kasan cewar Ummukulsoom taga da ɗan mutane a wajen ɗai-ɗai kuma ga fararen kujeru da aketa shiryawa sai tabi Ahmad kai tsaye inda yake jan hannunta. Dukda ta zauna a Barrack ɗin bazata ƙarar da komaiba tunda a wancan lokacin bawani yawo takeba sosai, sai gidan maman Ahmad, shima zata iya irga zuwanta gidan kuma.


★★★★


         Zaune yake barandar gaban ƙofar falonsa, irin doguwar kujerar nance da akan ajiye a gaban ruwa, sai dai wannan mai taushice kamar nomal kujera, sanye yake da wando 3quarter na kakin sojoji, sai farar t-shet, gaba ɗaya hankalinsa ya tafi ga lap-top din dake a kan cinyarsa.

      Sam Ummukulsoom bata lura da shiba, sai mamakinma jin gidan da tai tsitt babu hayaniya, a ganinta ai bai kamata aji gidan suna haka ba, jitai kawai Ahmad ya ƙwace hannunsa ya shilla da gudu yana faɗin “Big Daddy”.

      Amaan da yaji muryar Ahmad ya ɗago da mamaki, sai idonsa suka sauka akanta, dai-dai itama ta ɗago dan son ganin wanene kuma Big Daddy? Ina Ahmad ya kawosu ne?.

       Tuni dukkan murmushin dake shinfiɗe a fuskar Ummukulsoom ya ɗauke gaba ɗaya, ɓacin ran ganinsa ya maye gurbinsa, gashi ta kasa janye ƙwayar idanunsa daga cikin nata, hakan shima ya kasa janye nasa duk yanda yaso, saima zuciyarsa dake wata irin harbawa da ganinta.............✍🏻



NO. 34


..........Fuska ta kuma haɗewa tana janye idanunta daga cikin nasa, ta fara takowa a hankali zuwa inda suke da nufin kama Ahmad su tafi. Amaan kam sam yakasa ɗauke manyan idanunsa a kanta, sai binta da kallo yake ƙasa-ƙasa da mamakin ina zata je? Sam ya kula bata da tsoro yarinyar nan.

    Mayen ƙamshin turarenta ne ya fargar dashi kusancin da suka samu, ya sauke wata ɓoyayyar ajiyar zuciya yana kuma tamke fuska.

   Ko kallon inda yake Ummukulsoom ba tai ba, ta kamo hannun Ahmad dake laɓe a bayansa zata jawoshi, shima saiya riƙe ɗayan hannun Ahmad ɗin.

     Kallan kallo suka sakema juna kowa fuska babu ɗigon walwa, har ƙasan zuciya Ummu haushinsa takeji.

     “Zamu wuce”. Ta faɗa a kausashe.

       Banza yay mata kamar bai jiba, saida ya shaƙi iska ya fesar sannan yace, “Dani na kawo ki?”.

          Ƙin tankawa tai itama, ta ja hannun Ahmad kawai.

     Ahmad da yake tirjewa yace, “Aunty ni kibarni zan zauna a wajen big daddy”.

     Hannu ta ɗaga tamkar zata makesa, harda cije baki. Ahmad daya tsorata ya ƙankame hannun Yaa Amaan sosai.

    Ba ƙaramin dariya abin yabama Amaan ba, amma saiya fuske ya haɗiye abarsa yana kafeta ta idanunsa, ”Miyasa kika fasa? Ki dakesa mana”.

     Baki ta murguɗa masa  tana wani wulkita idanu da kaɗan ya rage ta wulkice da zuciyar sa, dan gaba ɗaya ƙofofin gashin jikinsa sai da suka buɗe, ya haɗiye yawu da sauri yana janye idanunsa a kanta.

     Ita kam bama tasan yanaiba, sai ƙoƙarin ɗaukar Ahmad ɗinma da take hannu biyu.

     Sam bazai iya jurewa kusancinsu ba, dan haka ya sakar matashi kawai, amma sai Ahmad ya fasa kukan shifa anan zai zauna.

    Bata saurari kukansa ba ta fice abinta.

     Idanunsa ya lumshe tareda kai hannu ya shafi girarsa yana sauke tagwayen ajiyar zuciya, lallai indai wannan shine so to sam bai masa adalciba, dan shikam bazai juraba. Gaba ɗayama jiyay aikin nasa ya fita kansa, dan haka ya tattare kayan ya koma ciki.


      Ummukulsoom kam tana fitowa taci karo da Bily a ƙofar gidan sunan ita da wani saurayi.

      Cikin mamaki tace, “Bestie daga ina haka?”.

    Tsaki Ummu tayi tana dire Ahmad da har yanzu yake kuka a ƙasa, “Ki bari kawai Bestie, wai dan wulaƙanci fa Ahmad ya kama kaimu wannan gidan a matsayin gidan sunan”.

       Bily ta ɗan waro idanu waje tana dariya, “Amma Ahmad ALLAH ya shiryeka, gidan Yaa Amaan ɗinne ya zama gidan su Sulaiman?”.

     “Ai ki barni dashi, yau ba sai gobe ba sai na zanesa, da wani kansa tun na haihuwa”.

      Sosai saurayin da ke tare da Bily yake dariya, shi mamaki ma take bashi, ta dage ita a dole faɗa takeyi, amma kuma muryarta na fitane a nutse kuma cikin amo mai daɗi.

     Sam Ummu ko kallonsa bata yiba itakam tai gaba ta bar wajen, Bily ma dai sai da ta dara, tana binta da kallo, dan ita tunda taji alaƙar dake tsakanin Ummukulsoom da Yaa Amaan tasan sun dace, fatanta kuma komai ya zama normal ta koma ɗakinta.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


              Sosai Suhailat ke bincike akan Baseeru, ba dare babu rana, ta haka ne ta samu ganawa da abokansa su Abdul, da yake duk sunsan da zancen rabuwarta da Baseeru basuyi mamakin komaiba, sai dai canjawar da tai musu.

      Itama sun canja mata ƙwarai da gaske, dan gaba ɗayansu sunyi aure zuwa yanzu.

         Najeeb ne ya fara faɗin, “Mudai a bayan rabuwarku mukejin ƙishin-ƙinshi akan aure yayi, badai mu tabbatar ba dan sam yaƙi yarda mu haɗu dashi, sai bayan aurensa da ƴar gwamnan katsina ta yanzune mukabi diddiginsa har mukasan ashema bayan ya auri Lubnar da muka taɓa ganinsu tare sannan kina amarya amma yace mana ƙawarkice ya kuma auren wata yarinya Fannah, a tare ma ya sakesu da Lubna lokacin aurensa da Meenal ɗin”.

     Mamaki ya kuma danne Suhailat, lallai lamarin Basiru ya gawurta, amma ta ɗauki alwashin nuna masa *WUTSIYAR RAƘUMI TAI NESA DA ƘASA*.

       “To yanzu ta yaya kuke ganin zamu sami Lubna da Fannah?”.

       Abdul yace, “Lubna dai samunta zaifi sauƙi, tunda mahaifinta ba ɓoyayyen mutum baneba, Fannah ɗince dai matsalar”.

        “Hakane, amma inhar mun haɗu da Lubna itama Fannahr zamu sameta insha ALLAH”.

      A tare sukace hakane.


  *Washe gari*


       A washe garin ranar Suhailat tai shirinta na alfarma ta doshi kanon dabo, batasha wata wahalar samun gidansu Lubna da aka bata address ba, hakama bata sha wahala ba wajen masu gadin gidan, kasancewar tace itaɗin ƙawar Lubna ce. Tai kuma sa'a Lubna na gida bata fita ko inaba.

      Tana tsaye jikin motarta Lubna ta fito tare da mai bama fulawar gidan ruwa da yaje ya sanar mata, kallan kallo kawai sukema juna, dan babu wanda yasan wani a cikinsu, sai dai kasantuwarsu wayayyu duk sai suka basar wajen yima juna murmushi.

       Suhailat tace, “Sorry dear, baƙuwa babu sanarwa, baki kuma sannni ba”.

     Murmushi itama Lubna tayi mata, “Babu damuwa, koma dai minene mu shiga daga ciki”.

      “Thanks”. Suhailat ta faɗa a hankali.


         Tunda suka shigo gidan Suhailat ke jinjina tsarinsa, dama tasan ai Basiru bazai taɓa aurar macen da babu manda a gidansu ba, dan shi kaska ne raɓu mai jini.

     Sai da aka gama ajiye mata kayan motsa baki sannan Lubna ta zauna suka sake gaisawa, Suhailat da ke shan lemo ta kalli Lubna da fararen idanunta, “Nasan zakiyi mamakin ganina, gashi baki sanniba, Sunana Suhailat, tun daga kd nayo takakkiya zuwa gareki. Ta sanadin alaƙar da wani banza ya haɗamune nazo nan”.

      “Wake nan?” lubna ta tambaya tana tsare Suhailat da idanu.

    Murmushi Suhailat tayi na takaici, kafin ta ajiye kofin hannunta tana gyara zama, tace,

    “Ba kowa bane face Basiru”.

    Tuni murmushin dake kan fuskar Lubna ya gushe gaba ɗaya, ta yunkura zata miƙe Suhailat ta dakatar da ita ta hanyar faɗin,

      “Ni ya cancanta na fara irin wannan fushin Lubna, amma dana zauna nai tunani sai naga bazai amfaneni da komaiba, domin kuwa zan ƙare rayuwatane inayinsa batare da wanda nakeyi dan shiba ya sani balle yasan na tsanesa, zuwa yanzu ba zuciyar fushi bace a ƙirjina Lubna, ta ɗaukar fansace, wannan dalilinne yasani zuwa gareki domin mu haɗa hannu wajen maida murtanin bashin gaba. Badan Basiru zai gagareni bane ba, sai dan nasan irin tabon daya barmin kema shine ya barmiki, kenan ya dace mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen tabbatar masa da mata ba hularsa bace da zai ɗauka a sanda yaso yakuma aje a lokacin da yaso, amma in babu ra'ayin hakan a tare dake karki damu zan koma, na ida cikar burina, na gode da tarbar mutunci da kikaimin sosai, sai gani na biyu.......”

        “Indai wannan shine burinki nima shine nawa, dan nayi alƙawarin sai Baseeru ya ƙwankwaɗi madarar baƙinciki fiye da wadda ya bani na ɗanɗana, na tsani cin amana, hakama yaudara”. Lubna ce mai maganar a fusace.

    hakan ya saka Suhailat dakatawa daga shirin fitar da takeyi, ta juyo gaba ɗayanta tana kallon Lubna fuskarta shinfiɗe da murmushi, ƙaramin ɗan yatsanta ta miƙa mata, Lubna ta tako har gabanta suka ƙulla tareda sakarma juna murmushi.

      Komawa sukai suka sake dasa hiran basiru da rayuwar da kowa tayi dashi, anan ma Lubna ke sanarma Suhailat ta haihu da Basiru ita, yarinyar tana nan Amal.

       Sosai Suhailat ta tausayama Lubna da yarinyar kanta da batai dacen mahaifiba.

     Sun yanke hukuncin yanda zasu samo Fannah itama, dan daga baya bayan rabuwar Lubna dashi itama takejin ya auri Fannah, a tarema ya sakesu.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


           Tunda ta fito daga lecture ta hangesa tsaye jikin motarsa, sai dai ta yauma ba irin ta shekaran jiya bace, sanye yake cikin suit kalar sararin samaniya, ƙyaƙykyawane ajin farko, sannan ɗan gayu, yau kwanaki huɗu kenan daya fara bibiyarta, sai dai sam taki saurarensa, amma bawan ALLAH yaƙi yin zuciya.

       Ta ɗan sauke numfashi tareda cigaba da takowa inda yake, dan yau taji a ranta zata sauraresa taji da wacce yazo shikuma.

     Sanye take cikin atanfa ruwan fauda siket da riga, sai hijjab ɗinta da kaɗan ya wuce cinyarta mai hannu shikuma ruwan madara, tayi ƙyau sosai dukda kamar kullum babu kwalliya a fuskarta.

    Tunda ta dososhi murmushi ya faɗaɗu akan fuskarsa, yarinyar ta haɗu ta ko ina, kallo ɗaya ta wuce da dukkan tunaninsa, gata da jan aji, dan itace mace ta farko a rayuwarsa da zaice yanata bi tana yarfashi amma yakasa yin fushi......

     “Assalamu alaika” zazzaƙar muryarta ta rangaɗa masa sallama.

      Eyeglasess ɗin fuskarsa ya zare yana murmushi, “Wa'alaikissalam gimbiyar mata, Wannan juma'a tazo min da babban alkairi, ga farin wata gab da ni yana haska min hanya”.

     Basarwa Ummukulsoom tai tamkar bata fahimcesaba, sai ma cewa da tai, “Wai kai bakayin zuciyane?”.

     “Zuciya kuma Babie? Ai akanki ki ɗauka banida zuciya irinta fushi”.

      Murmushi Ummukulsoom tayi ba tare da ta shirya ba, ta ɗauke kanta gefe kawai tana faɗin, “Nifa bana zama inuwa ɗaya da maza”.

    “Babie aini kece inuwa ta, dan ALLAH a tausaya mini abarni na shiga daga ciki, zafin rana na gasani, sanyin kuma da ya kasance ba na inuwarkiba cutarwace a gareni, aji dani raɓar ƙankara tana neman daskarar da jinina”.

      Ɗan kallonsa tayi kafin ta ɗauke idanunta, “Zan duba naga idan ka cancanta”.

     “Yeeees!” yafaɗa yana dunkule hannusa.

    Hakan sai ya bama Ummukulsoom dariya, tai murmushi mai kayatarwa da har ya bayyana jerarrun haƙoranta farare tas.


    Duk yanda taso ƙin binsa saida ya kalameta da daɗin baki ta amince ta shiga motarsa.

     Suna tafiya yana janta da hira game da kanta, a taƙaice taita bashi amsa, yayinda shikuma yake sanar da ita wanene shi kai tsaye.

       A gate ɗin farko tace ya ajiyeta, dan tasan baza'a barsa ya shiga Barrack ɗinba.

     Fitowa yay da kansa ya buɗe mata ta fito, harda wani ɗan sunkuya mata irin na girmamawa, hakan ya sata sakin ƴar siririyar dariya......

 

     Cak numfashin Amaan dake tsaye a ƙofar gate ɗin ya nemi ɗaukewa, tsaye suke shida Attahir da wani abokinsu a wajen, da alama wani abun sukeyi, Attahir ne kawai sanye da complet Uniform a jikinsa da ɗayan abokin nasu, Amaan  kuwa wandonne kawai sai   dark green ɗin t-shert data kamashi sosai.

      Attahir da yaga Amaan ya tsirama waje ɗaya ido fuskarsa na kuma tsukewa sai abin ya bashi mamaki, dan haka ya kalli inda ya ke kallo shima.

     Ummukulsoom ya gani tsaye da ƙyaƙyƙyawan saurayi tana zabga murmushi waya a hannunta tana dannawa, yayinda saurayin shima yake murmushin hakoransa waje yana kallonta, ta mika masa wayar dake tabbatar da tasace, da alama Number ɗinta ta saka masa.

     Attahir ya janye idanunsa daga kansu ya maido kan Amaan da Abokinsu ke tambayar lafiya?, sai dai sam da alama hankalinsa bama ya wajensa.

   Taɓasa Attahir yayi, ya lumshe idanunsa ya buɗe batare da ya kalli Attahir ɗinba, zuciyarsa wani irin zallo take tamkar zata fito waje, ga kansa yay masa wani irin masifaffen nauyi, sam baya fahimtar jawabin abokin nasu.


       Sarai Ummukulsoom taga su Amaan tun lokacin da zata fito a motar Umar, hakan ne yasata biye masa dan ganin yanda gaba ɗaya hankalin Amaan ya dawo kansu, saboda ta sake ƙular dashi harda ɗagama Umar hannu da zai tada motar, bata bar wajenba sai da taga motarsa ta hau titi sannan ta saita kanta ta tako a hankali cikin nutsuwarta zuwa gate ɗin.

    Sai da tazo saitinsu sannan ta kalli inda suke, da Amaan ta fara haɗa ido, amma tsabar wulaƙanci sai catai “yaya Attahir barka da yammaci”.

     Murmushi Attahir yayi yana amsata da faɗin “Yauwa autan Ummi, an dawo lafiya?”.

     “Lafiya lau yayana”. Ta faɗa tana yin gaba abinta tareda watsama Amaan harara, Abokinsu kuwa yabar wajen tunkan ta ƙaraso.

       Ko motsi Amaan kasa yi yayi, dan tabbas ba'a taɓa masa irin wannan rainin ba da Ummukulsoom ta masa yau, shi bama wannanba, Ubanwaye wanda ya sauketa a mota? Dolene ya takama wannan yarinyar birki, inba hakaba wlhy zataja yayta karya ƴaƴan mutane a gabanta....

    Yanda yake fidda numfashi da sauri-sauri ya saka Attahir kallonsa, fushi da tsantsar fusata ya hanga a cikin ƙwayar idanunsa, “Ajiwa lafiya kuwa?”.

      Ƙin takama Attahir yayi, saima yabar wajen gaba ɗaya.

     Attahir yay ƴar dariya yana girgiza kansa, zuwa yanzu kam yagama yarda Ajiwa yagane Ummukulsoom, tsabar miskilanci ne ya hanasa nuna hakan...........✍🏻



NO. 35



...........Tun daga wannan ranar abubuwa suka nemi rikicema Yaa Amaan, yay bala'in sakama Ummukulsoom ido, yayinda ita kuma ta samu hanyar muzgunama zuciyarsa da salo kala-kala, ita duk tana yine saboda fahimtar kamar ya ganeta, duk dama yana yawan tafiye-tafiye shida Attahir, amma dukda haka kowanne motsinta ana sanar masa ba tare da ita tasan ana bibiyar rayuwar taba.

      Karatu kam ta maida hankalinta sosai, fatanta ta samu dukkan nasara, ƙawayenta kam basa wuce abokan karatun ta, duk wanda kuma ya tareta da kalmar so takan nuna masa karatune ya kawota. Ita da Umar kam, kamar wasa sai soyayya da shaƙuwa ta shige tsakaninsu, ita Ummu ma tun tana masa komai da wasa har lamarin yafara shiga jikinta, sai dai wanda ya nutsune kawai zai fahimci shaƙuwace a ranta ba soyayya ba.

    Sai wani lecturer ɗinsu Abdul-wahed shima fa ya kafa ya tsare, Bahaushe ne amma girman lagos, kuma saurayi da dukkan mace tagani saita ƙyasa, sam shima mutum ne da baya harkar mata, ko a makarantar ƴammata suna shakkar kaimasa wargi harma da mazan, amma tunda ya ƙyallara idonsa akan Ummukulsoom sai labarin ya canja salo, tun ana ƴar kallo hardai ranar yasa aka kira masa ita taje ta samesa har office.

       Ita kanta sai da abin ya bata mamaki, dan shi mutum ne da mafi yawan ɗaliban kance yanada shegen girman kai, ita kanta ta jefesa da wannan sunan, amma a yau sai gashi a gabanta yana fara'a da jaddada mata kalmar wai yanason ta zama wata sashe ta rayuwarsa, gaba ɗaya kuma ya ɗaureta da jijiyar wuyanta akan zai jirata har sai ta kammala, sannan kuma bazasu ringa wani mu'amula a cikin makarantar ba, idan yana buƙatar ganinta zaizo har gida ya sameta, shima zuwa gidan ba yanzu ba, sai sun gama sabawa ta waya tukunna.

     kasa koda motsi tayi, harya ɗauki wayarta ya saka Number sa ya kira tasa shima yaga tata.

    Har Ummukulsoom ta dawo gida abin na dama mata lissafi, guy ɗin yakai dukkan yanda mace bata zato, dan harga ALLAH itadai anata tsarin ya haɗu, kuma sai akai sa'a zuciyarta take kai kawo akan lamarinsa.

    Bily dai kasa daurewa tayi saida ta takura mata ta sanar mata damuwarta.

      “Ummukulsoom kuma ke kina sonshi kenan?”.

      Ajiyar zuciya Ummukulsoom tayi, “To ni Bily mizan ce, danfa haɗuwa bawan ALLAHn nan ya haɗu......”

    “Mtsoww, duk haɗuwarsa yakai Yaa Amaan ne, ke nifa ko wannan Umar ɗin haushinsa nakeji, nifa kullum fatana ki koma gidan Yaa Amaan, dan shine yafi dacewa dake ƴar lukutar Ummi”.

    Duka Ummukulsoom ta zubama Bily a cinya, “Kefa banza ce, Amaan ɗin mi, wlhy Abdull ya fisa komai ni a wajena. aini yanzu na wuce da saninsa wlhy, kuma kibar kushemin Umari na, inason kayana, ni saurayi nakeso yanzu ba bazawari ba”.

     Bily ta taɓe baki tana barin wajen, “gwara da kikace a wajenki, Umar wannan kuma matsalarki ce, insha ALLAHU babu wani mai kai kamar kwakwa dazai mallakeki sai Yaa Amaan, da kike ce masa bazawari kema ai itace”.

    Haushi kamar zai kar zuciyar Ummukulsoom, da bily tasan ko sunan mutumin nan batason ji da wlhy bata sake ambatarsa a gabanta ba, sam ta tsanesa fiye da zaton kowa, ganin bily zata fice sai tai saurin maida murtani, “Koda nake bazawara duk wanda ya aura zai tabbatar da sabuwace dal a kwali, shiko ko aure yayi sai matar tace ya taɓa aure, babu kuma wani jawabin da zai mata ta fahimcesa”.

      Haɓa bily ta riƙe tana bin Ummukulsoom da kallo, “Oh ni wai Bestie yaushe kika fetsare har irin hakane?”.

     “Zo na faɗa miki”. Ummukulsoom ta faɗa tana shigewa bathroom.

      “A'a nikam kinfi ƙarfina, bazaki iskantani ba wlhy”.

     Murmushi Ummu tayi daga cikin bayi saboda jiyo maganar Bily.

       


★★★★


    Da daddare duk suna falo suna kallo, Ahmad na gefe yana Homework saƙo ya shigo wayar Ummukulsoom, wayar bily ta miƙa mata, dan tana hannunta tana tura mata wasu apps.

      “K cigaba kawai, maybe ma mara amfani ne”.

       “A'a kedai karɓa, dan A-Waheed ne, inba hakaba na goge wlhy”.

    Warce wayar Ummu tayi da sauri tana faɗin, “ƴar baƙin ciki ashe rabin numfashi nane”.

    Maman Ahmad tai dariya itada Bily, sungafa wannan Abdul ɗin kamar yazo da ƙarfinsa, maman Ahmad batason shiga rayuwarta ne kawai, amma idan san samune kar Ummu tayi soyayya da kowa, fatanta takoma gidan Amaan, amma basuda hurumin cemata hakan, dan yanzu dai tanada ƴancin zaɓama kanta miji ko a addinance.

     Ummu kam tashi tai ta bar falon sannan ta buɗe saƙon. 

  

      _Duniya babban wajene mai yawan al'umma da wasu halittu, sai dai zuciya ta fita faɗi, soyyayya kuma itace al'ummar zuciya, to ni tawa babu kowa a cikinta sai ke kaɗai gimbiyar mata_

           *Naki UMA*.

 

Ummu ta maimaita saƙon yafi sau goma, sai murmushi take zabgawa, tai kissing wayar tana lumshe idanu, hundred percent A-waheed yayi.

     Bata maida reply ba ta share kawai.

      

★★

     Washe gari da taje makaranta koda ya shigo musu class ko a fuska bai nuna yama santa ba balle saƙonsa daya tura, hakan yasa itama ta basar tamkar batama gansa ba, ya gama ya fita abinsa.

      Tun daga sannan Abdul-wahed yazama abokin hirar Ummukulsoom ta hanyar turo mata saƙo a kowane dare, ko fashin hakan bayayi, kullum kuwa akwai salon da massege nashi ke zuwa dashi, kafin aja wani lokaci yagama saye dukkan zuciyarta, sai dai sam maganar fatar baki bata haɗasu idan taje school, kuma bai sake kiranta Office ɗinsa ba, hakama a waya bai taɓa kiranta ba sai dai masseges da kullum baya gajiyawa.

     Da farko abin ya fara damun Ummukulsoom, amma daga baya saita zauna ta nutsu, tareda da yimasa uzuri akan shikuma nasa salon soyayyar kenan, to aiko zata tabbatar masa ta fisa ƙwarewa.

    Duk yawan masseges ɗin da yake mata bata taɓa masa reply ko sau ɗaya ba, hakan kuma baisa ya gajiya ba. Tsakaninta da Umar kuwa suna tare abinsu.


      ★★★★


    Ɓangaren Amaan kuwa zuwa yanzu ko haɗuwa sukai da Ummukulsoom ko kallon inda take ba yayi, dan yakula raini na neman shiga a tsakaninsu, ya maida hankalinsa gaba ɗaya ga aikinsa, bama sa haɗuwa sai lokaci-lokaci, dan makaranta kan hanata yini a Barrack ɗin itama.

      Yau ta kasance litinin, kamar yanda ya saba bakinsa ɗauke da azumi, tun 4pm ya baro office ya koma gida.

     Sanin da Desmond yayi duk mafi yawan irin waɗanan ranakun yakanyi azumi sai yake tambayarsa miza'a masa na shan ruwa.

          Yana falo kwance tunda ya dawo daga sallar la'ar, ba barci yakeba amma idanunsa na lumshe, desmond da tun ɗazu ya ke tsaye yana masa magana ya sake maimaitawa,

     “Boss miza'a girka maka na buɗa baki?”. Yay maganar a ɗarare, dan ya lura a kwanakinnan abu kaɗan ke tunzura zuciyarsa ya hau faɗa.

       Shiru kamar bai jisaba, sai kuma ya sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya tare da furzar da numfashi ya ɗago manyan idanunsa da suka canja launi daga farare zuwa sirkin jaa alamar gajiya na tattare da shi da barci, “Yau kunu nakeso, kaikuma gashi har yanzu ka kasa iyawa, barsa kawai zanje gidan Attahir ”.

        “Ok Boss”. ‘Desmond ya faɗa yana barin falon, zuciyarsa cike da mamakin mike damun boss? A gaba ɗaya kwanakinnan yakuma zama shiru-shiru, rashin son maganarsa ya ƙaru, ga faɗa abu kaɗan zai fara juyema mutum masifa.


       Waya ya ɗauka ya kira Attahir akan yau zaizo nan yasha ruwa, amasa kunun shinkafa da ƙosai na wake.

       Attahir yay murmushi, cike da neman tsokana yace, “ALLAH sarki, wlhy harka bani tausayi, matsalar gwauro kenan ai”.

    Tsaki Amaan yayi yana fadin, “Banza kawai magananne”.

      Attahir ya kwashe da dariya, “Gwarani a magana na tsaya, wanda ya haɗa abubuwan da sukafi nawa fa? Shi minene sunansa?”..  

     “Kasa micrephone mana saika tambaya”. Yay maganar yana yanke wayar tareda jan tsaki.

          Dariya Attahir ya kuma sanyawa yana janye wayar a kunnensa, ya kira maman Ahmad ya shaida mata danshi yana office bai koma gidaba.

       

    Yamma lis Ummukulsoom ta dawo daga makaranta, lokacin su Bily na kicin suna haɗa abinci buɗa bakin Amaan da itama kanta Ummu ɗin, dan tana azuminne itama, amma na ramadan ne da bata rama ba sai yanzu takeyi.

      Bata nemi kowa ba ta shige ɗakinsu itada bily, ruwa ta fara watsawa sannan ta fito, bata wani zaman kwalliya ba, sai mansu mai ƙamshi taɗan shafa sama-sama da ƴar khumra tasa wando da riga masu taushi marasa nauyi, sam kayan basu kama ta ba, dan Ummi ta hanasu saka ƙananun kaya masu bayyana jiki, sai akai sa'a ra'ayin Ummi dana Attahir yazo ɗaya.

    Tana shirin fitowa Yaa Zaid ya kirata, murmushi kawai tai tareda ɗagawa suka gaisa, har tazo falo ta zauna suna wayane, dama ƙa'idane kullum saiya kirata suyi hira, wani lokacin hirar tai tsawo wataran kuma Ummu ta gajarta ta da cewar zatai karatu.

      Ahmad ne da yadawo daga islmiyya ya shigo yana kuka, Ummukulsoom ta yanke wayar tana kallonsa, “Oga Amadi lafiya shigowa gida da kuka kuma?”.

     Zuwa yay jikinta ya zauna, “Aunty”.

    Ta amsa da “Na'am Amadi angon Ummi”.

    “Kinga dai Chizober ce ta dakeni, wai danna bi takan wasansu”.

    “To banda neman rigima Amadi inakai ina taka musu wasa? Kaida ka dawo daga islamiyya maimakon kai maza kazo gida ka kawo ladanka saika tsaya ƙofar gidan su chizober, hakan babu ƙyau kajiko, karka sake, ita kuma zanje na kaima Momynta kashedi idan ALLAH ya kaimu gobe kaji”.

   Cike da murna Ahmad yace, “Eh auntyna, ALLAH ya kaiki maka sau 100”.

    Dariya Ummukulsoom tayi tana faɗin “Amin Ahmadi na”.

     Maman Ahmad dake bayansu tace, “Wai dama kin shigo?”.

    “Wlhy na shigo aunty, tiɓis nake, banason shigowa kicin ɗinnna naga abinci yunwata ta ƙaru shiyyasa”.

      “Hhhh anya wannan azumin zai kai labari kuwa?”.

    “ALLAH aunty zai kai insha ALLAHU saina gamashi, saura biyu fa ya rage yau idan nakai uku”.

    “To ALLAH ya taimaka, shiyyasa nayi nawa da wuri na huta”.

       Miƙewa Ummu tai ta nufi kicin ɗin itama, “Ai kinyi dabara wlhy Aunty, nima a time ɗin muna tsaka da exams ne wlhy, shiyyasa bana ko sittar shawwal banyiba fa, ALLAH dai ya bamu ladan niyya”.

     “Amin” Bily ta karbe tare da ma Ummu sannu da dawowa.


    Suna a kicin ɗin har aka kira sallar magriba, Ummu sai tambayarsu take wai wannan uban abincin da akayi duk wa zai cisa? Ko suma duk shi zasuci matsayin abincin dare?”.

       maman Ahmad tace, “Kusan hakan za'ai, dan bazamu bari kici dadi ki fimu kibaba”.

    Murmushi Ummukulsoom dakecin Dabino tayi, ta ɗauki kofin ruwa tasha sannan ta fice zuwa ɗaki yin sallah. 


★★★★


      Ana idar da sallar magrib suka nufo gida shi da Attahir, Bily kawai suka iske a falon dan tana fashin salla, tai musu sannu da zuwa a zuciyarta tanama Ummukulsoom dariya, ashe Yaa Amaan ne baƙon da Maman Ahmad tace zaizo shan ruwan, lallai yau akwai kallo.

        Shidai Amaan kai tsayema dani ya nufa, dan ba yaune ya fara zuwa shan ruwa gidanba idan yay azumin litinin da alhamis, ba komai ke kawosa ba kuma sai abinci irin namu na hausa, dan desmond ba iyawa yayiba, koya kamanta yi bayayi masa daɗi, shiyyasa inhar yana bukata baya cutar kansa saiya ce maman Ahmad tai masa, itako bata taɓa gajiyawa ba da yimasan.

      Matsowa Attahir yay kusa dashi yana faɗin, “Ajiwa nikam dai bara na watsa ruwa”.

    Kansa kawai ya ɗaga masa ba tare da yayi magana ba, sai ƙoƙarin buɗe kwanikan saman dani din yakeyi hankalinsa kwance tamkar a gidansa.

      Yana ƙokarin zuba kunu a kofi Ummukulsoom ta fito daga dakin tana waya da Umar dake mata barka da shan ruwa, sam bata lura da shiba, sai dai tabbas taji ƙamshin turarensa, hakan kuma baisa ta kawo a ranta yana kusa ba, kujera ta ja ta zauna sunayin sallama da Umar.

      Tunda ta fito shikam idonsa ya sauka a kanta, harta ƙaraso yana mata kallon ƙasa-ƙasa, amma sam babu wanda zai fahimci hakan sai shi da yakeyi, kusan gagararsa zuba kunun yaso yi, sai dai ya dake harta karaso wajen, yanda take magana ƙasa-ƙasa a wayarne yasa baiji mi take faɗaba, amma hakan ya soki zuciyarsa sosai.

    Ajiye wayar Ummu tayi tana murmushi mai sauti, sai dai tana ɗagowa da nufin ɗaukar kunu ta zuba idonta ya sauka a kansa, ya wani basar yana motsa kunun da ya zubama sukari tamkar bai gantaba.

     Tuni fara'ar fuskarta ta ɗauke, a ranta tana mamaki shikuma miyazo yi? Harda yima mutane ɗare-ɗare a dani, aiko ta ɗau alwashin bazata tashiba, dan haka itama ta basar tamkar bata gansaba, ta ɗauki kunun dake gabansa ta zuba tana kuma wani ciccije fuska ita a dole kar a kawo mata raini.

     Duk motsinta yana kallonsa ta ƙasan ido, jira yake yaga zata gaisheshi.

    Kununta ta gama zubawa ta ɗiba ƙosai tare da farfesun kifi ta fuske abinta tanaci hankali kwance, harda ma yanga ta neman magana, babu wanda ya kula ɗan uwansa a cikinsu, sai dai kowanne yana satar kallon ɗan uwan nasa ta gefen ido.

    Saƙo ya shigo wayar Ummukulsoom, hakanne ya sata ɗaukar wayar dan tana ƙyautata zaton A-Waheed ne. Ilai kuwa shine, ta buɗe saƙon kamar haka,

    

    _Safiya ta shuɗe, rana ta gushe, yammaci ya wanzu, alkairin ALLAH yakai gareki ma'abociyar kamewa, barka da shan ruwa._

                *Naki UMA*


     Lallausan murmushi Ummukulsoom ta saki, wanda yakusa sumar da Amaan dake satar kallonta, ya lumshe idanu ya buɗe akanta a hankali.

     Ummu kam da batasan yana yiba reply take ƙokarin maidawa A-Waheed, dan yau taji a ranta zata fara kulashi, jan ajin ya isa haka.


       *Kaima Abincin ALLAH ya tabbata a gareka, tare da alkairin da baya yankewa har ƙarshen numfashi.*

         _Kulsoom_


      Tana gama turawa takuma sakin wani murmushin, jitai kawai an take mata ƙafa da ƙarfi, ta matse fuska saboda zafin daya ratsa har cikin ƙashinta tare da kallonsa, dan tasan sarai shine, kuma yaki ɗaga ƙafar, saima kara murzawa yake tsabar mugunta, ya kuma basar tamkar baya aikata komai.

    Filas ɗin kunu ta ɗauka ta diba kaɗan mai azabar zafi, ba tare da ya kula da abinda ta keba dan waya yake dannawa da hannu ɗaya, ɗaya kuma yana rike da cokalin da yake shan farfesu, ta zuba masa kunun a kan hannun dake riƙe da cokalin.

     Da sauri ya saki cokalin tare da wayar yana janye ƙafarsa akan tata tare da yarfe hannu saboda azabar zafin kunun data shigesa.

   Tuni Ummukulsoom ta mike tabar wajen, ko waiwayensa batayiba ta koma falo dariya nacinta.

         Da kallo kawai ya iya binta yana cigaba da yarfa hannun, wajen har yayi jajur abinka da fari......

      “Ajiwa lafiya?”. ‘Attahir daya karaso wajen ya faɗa yana kallonsa’.

      Sam fuskarsa babu walwala matuƙa, alamar yaji zafin abinda tai masa har cikin ransa, murya a dakile yace ma Attahir ƙonewa yay.

     Hannun Attahir ya kama yana kallo da mamaki, “Ƙonewa kuma Ajiwa? Garin yaya haka? ga wajen haryay ja kamar zai tashi”.

    Baice ma Attahir komaiba, sai zuciyarsa dake ƙara wani kumbura saboda takaici.

    Kira Attahir ya kwalama Ummukulsoom dake zaune a falo, ta amsa tana tasowa tamkar ba ita ta aikata tsiyar ba.

     “Samo ƙankara a kicin”.

    “To” ta faɗa tana harar Amaan da shi bama ita yake kalloba.

       Saida tasha dariyarta a kicin sannan ta kawo ƙanƙarar, ta iske maman Ahmad da Bily ma sun fito, Handkherchief ɗin da Bily ta kawo wanda na Ummukulsoom ɗinne Attahir yace ta amsa ta zuba ƙanƙarar a ciki.

   Saida ta harari Bily sannan ta amsa tayi yanda Attahir yace, Amaan dai duk yana jinsu, amma baiko tankaba, ko sannu dasu maman Ahmad suketa jera masa kai kawai ya ɗaga musu.

     Attahir na shirin amsar ƙanƙarar yay masa sai kawai sukaga ya mikama Ummukulsoom hannun.

    Da wani uban haushi Ummu ta kalli hannun sannan ta kalli Attahir, amma sai yace mata “zauna ki saka masa to”.

     Fuska ta ƙwaɓe tamkar zatayi kuka dan takaici amma sai Attahir ya ɗauke kansa, danshi yaji a ransa akwai abinda ya faru, ba hakanan Ajiwa ya ƙoneba, kuma tunda ya nuna Ummu zata saka masa ƙankarar ya tabbatar akwai dalili, dan yasan halinsa sarai.

        Ganin babu wanda ya goyi bayantane yasata zama idonta cike da ƙwallar takaici, da mugunta ta danna handkherchief ɗin dake ɗigar da raɓar ƙankarar akan hannunsa, amma ko motsi baiyiba dukda yaji zafi kuwa, haka taita danna masa cike da mugunta har ƙanƙarar ta kusan gama narkewa, hannunsa ya janye, batareda kowa ya lura ba ya ɓara mata kunun gaban Ahmad da aka zuba mawa yanzu a hannu itama.

    Tana ƙwalla ƙara yana mikewa cike da basarwa, babu wanda zaice shiɗinne ya aikata.

    Duk kanta sukai suna tambayar lafiya, hawayenta ta goge ta ɗago ta kalli Amaan dake shirin wucewa, kallon ido cikin ido sukaima juna wanda babu wanda bai jisaba har cikin jininsa ita da shi.

      “Maman Ahmad na gode sosai, ALLAH ya raya Ahmad ya kawo ƙannensa masu albarka, Attahir na wuce”.

       Kallonsa sukai, yayinda hankalinsu ke kan Ummukulsoom, bai jira amsar kowa ba ya fice abinsa, hakanne ya saka Ummukulsoom saurin faɗin, “ALLAH ya saka min kuma”.

      Wani murmushin da bai shiryama zuwansa bane ya subuce masa, ba tareda ya juyoba ya karasa ficewarsa.

       Ita da yake ma kunun ya huce nata bai tashi ba, sai dai zafi da yake mata.

       “Ummukulsoom wannan ya tabbatar min da kece kika ƙona Ajiwa ko?”. Attahir ya faɗa yana tsareta da idanu.

      Baki ta ɗan tura gaba tana share ƙwalla, “Yaya shinefa ya fara takani”.

     “Ke kuma sai kika ƙonashi ko? maganinki ai, na kula sam baki gama sanin halin Ajiwa ba, idan har kikace ta wannan hanyar zakibi ki ringa masa abu wlhy wahala zakiyita sha, dan ba raga miki zaiyiba”.

     Ita dai batace komaiba, sai maman Ahmad daketa mata sannu, bily kam tanajin tushen zancen saita hau dariya, dama tayi zargin hakan.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


           Da ƙyar Baseeru ya samu Meenal ta barsa ya tafi ɗilau gaida su baba, yaso suje tare tace, bazataje ƙauye ba wlhy, shidai daya zamarma tilas yaje, sati ɗaya kuma ta bashi kacal.

       Babu tunanin komai ya amince, sai kace itace mijin shine matar.

     Tsananin son da yake matane yasa ko kaɗan baya iya ƙetare maganarta, ga kuma daula daya samu kansa a ciki wadda baya fatan ko a mafarki ta yanke masa.

      Yauma dai kamar ko yaushe yara bin motar sukeyi tamkar yanda suka saba aduk lokacin da bakuwar mota ta shigo ƙauyen, da murnarsa ya shiga cikin gidansu da yagama lalacewa, katangar gaban gidanma ta faɗi sai danni akayi na itacen geza, sai dai kuma jikinsa yay sanyi ƙalau tunda yay sallama a cikin gidan, dan ya iske tashin hankalin baba kwance babu lafiya sosai, dan haka ya rikice, baiko zauna hutawa ba suka ɗakkoshi zuwa zaria asibiti...........✍🏻


*_CIGIYA!_*


_Ɗaliban makarantar ɗanzabuwa da suka ƙare a shekarar 2010 (Zolo) suna cigiyar dukkanin ƴan uwansu da suka kammala suma a wannan shekarar, amma fa ƴan *DAN ZABUWA* kawai, akwai taro da zai gudana ranar 11/3/2020 a cikin harabar makarantar *DAN ZABUWA*, karku bari abaku labari, shekara goma ba kwana goma baceba, gara dai kowa ya garzayo, muga wanda ya koma ƙato😂😝, da wanda yake siriri😉😝, bayan duk da ƙwailayene⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️kar insha suburbuɗa._


     +234 810 999 2578

    *Duk wadda tasan ƴar 2010 ce ɗan-zabuwa saita ma waccan Number magana, ALLAH yasa a dace😃🤝🏻.*

              



*_NO 36_* 



...........Tun da ga randa Amaan yazo gidan shan ruwa basu sake haɗuwa ba, ALLAH dai ya sota wajen da ya sa mata kunu bai tashiba, tunma a daren yabar zafi.

     Yau tana makaranta Baba ya kirata, bayan sun gaisa yake cewa, “Ummukulsoom dama magana nakeson muyi”.

     Nutsuwa ta kumayi sosai, murya a sanyaye dake nuna alamun a gajiye take tace, “To baba ina jinka”.

        “Ummukulsoom baƙya ganin zuwa yanzu ya kamata ki fidda miji kiyi aure kuwa? Tunfa muna ɓoyema mutane akan zamanki babu aure wataran zata bayyana kowa ya sani, niko bana fatan hakan gaskiya, dan maƙiya zasu mana dariya”.

     Idonta ne ya ciko da hawaye, amma ta daure ta haɗiyesu bata bari sun zuboba, ta gyara zamanta tana kuma raunana murya saboda ɗacin da takeji a maƙoshinta har zuciya, “Baba kayi haƙuri, insha ALLAHU zanyi, amma kaga watannine ya ragemin na gama shekara ɗayannan.......”

     Katseta baba yayi da faɗin, “Nasani Ummukulsoom, dan Alhaji Mahmud yaymin bayanin komai, jiya mun daɗe tare dashi akan maganarki, shima kuma ya amince da maganar ki fidda mijin auren, idan san samune dakin kammala shekara ɗayannan sai a kaiki ɗakinki, munyi maganar da Hajiya yaya da Gwaggo hinde da babanki Alhaji Abubakar, kowa ya amince da hakan”.

    Yanzu kam dai kasa riƙe hawayen tayi, suka ziraro bisa kumatunta masu ɗumi, muryarta na rawa tace, “Shikenan baba, insha ALLAHU zanyi ƙokari kodan na saka farin ciki”.

     “Yauwa Ummukulsoom, ALLAH ya albarkaci rayuwarki kinji ko”.

      “Amin ya rabbi baba, nagode”.

      “To masha ALLAH, kukan ya isa haka kinji share hawayen, ALLAH ya baki miji na gari”.

    Murmushi tayi tana share hakawayen, tanason babanta dan shima yana nuna mata ƙauna sosai.

      Bayan sunyi sallama class ta koma, lecture ɗaya ta rage mata, dan haka ana kammalawa tai yunƙurin wuce wa gida jiki a matuƙar sanyaye, dan itakam batasan wazata nuna ba amatsayin abokin rayuwarta.

     Umar yana sonta, itama kuma harga ALLAH bazata ce bai mataba, dan ya haɗu fiye da zaton mai hasashe, sai dai haka kawai batajinsa a zuciya a matsayin miji.

        Zata iya auren yaya Zaid ma, amma sam batajin hakan a ranta, saboda tun fil azal bata ra'ayin yin auren zuminci saboda wani dalili nata.

     “Abdul-Waheed” zuciyarta ta ayyana mata, nannauyan numfashi ta sauke, komai ya haɗa a yanda kowacce mace zatai fatan ya zam mijin urenta, sai dai bai bata damar sanin hallayyarsa ba, a yanda yake mu'amulantar ta kuma sam kamar ba son aure yake mataba, a ganinta kuma halayya itace abinda ma'aurata ya kamata su fara fahimta a rayuwar aurensu kafin maganar ƙyawun fuska ko wani ƙyale-ƙyale ya biyo baya, wannan kuskuren shiyya janyo mafi yawan rikicin aure a wannan zamanin, har ake gaza fahimtar ina aka dosane?..........

     Wayarta dake ring ce ta dawo da ita hayyacinta, ta sauke numfashi tana ƙoƙarin lalubota a cikin bag. Bily ce, dan haka ta ɗaga tana faɗin, “Babie yaya dai?”.

      Daga can Bily tace, “Komai dai-dai, cazan idan baki fito makaranta ba ki jirani nazo sai mu wuce kasuwar muyi gaba ɗaya mu hutu goben kawai”.

    Cike da gajiya ta ce, “Kai Bily, wlhy kin cika matsala, ALLAH na gaji sosai”.

     “Sorry Bestie, ALLAH ki daure kawai muje”.

     “Shikenan, amma ke yanzu kina inane?”.

    “Gani a taxi mana”.

 Yanke wayar Ummu tayi kawai batare da ta ce komaiba, ta samu waje ta zauna zaman jiranta, yayinda maganar baba keci gaba da mata kaikawo a rai.

    Ba tafi zaman minti talatinba saiga Bily ta iso, babu wani ɓata lokaci ta shiga suka tafi.


       Suna cikin kasuwa har 5pm, ga garin yay masifar ɗaurewa da hadari, hakan saiya saka Ummukulsoom ruɗewa, gashi duk taxi ɗin da suka tare saisu ganta da mutane, Ummukulsoom tamkar zatayi kuka, batason ruwannan ya taɓata saboda kanta dake ciwo sosai, ita kanta Bily dukta damu.

     Tafiya suka cigaba dayi a ƙafa suna kuma bincika abin hawan, ga maman Ahmad sai kiransu take, babu wanda ya samu damar ɗagawa, ita kuma acan Attahir nata mata masifa akan tana ganin hadarin miyasa ta barsu suka fita.

        Yayyafin da aka farane ya saka Ummukulsoom ja ta tsaya idonta na cika da ƙwalla, Bily ta kalleta cike da damuwa, ga kaya riƙi-riƙi a hannunsu. 

     “Bestie ya kika tsaya kuma?”.

     “Bily minene amfanin tafiyar tamu, tunda dai harma ruwan ya sakko gara kawai mu tsaya komu samu mafaka”.

       “Ok to mu tsallaka ga wata rumfa can”. Cewar Bily tana kama hannun Ummukulsoom.


         Zaune yake a bayan motar cikin Uniform, kayan sun masa ƙyau sosai, gaba ɗayan hankalinsa nakan lap-top da alama abu mai amfani ya keyi.

     A ɗarare Osin yace, “Sir! Ga wasu da alama suna bukatar taimako”.

     Shiru yay tamkar bazai tanka ba, harma sunɗan gota su Ummu dake ƙoƙarin tsallaka titi ya buɗe baki da ƙyar, “Ka tambayesu idan hanyarmu ɗaya”.

      “Ok sir, thanks you”.

  Bai sake cewa komaiba yaci gaba da abinda yake, Osin ya dawo baya gaban su Bily, kaɗan ya sauke glass ɗin gefensa yay musu nuni da su zo.

    Babu wani batun jan aji Bily tace, “Ummu inaga ALLAH ya kawo mai taimakonmu, saura kuma kice bazamu shiga ba”.

    Hararta kawai Ummu tayi suka nufi motar, Bily ce ta gane Osin, kamar shima da tana matsowa ya shaidata, yay murmushi yana musu nuni da su zagayo su shiga.

      Ummu da batason shiga gaban mota saita tura Bily gaba ita kuma ta buɗe baya ta shiga, Osin na ƙoƙarin nuna mata ta dawo gaba itama amma sam bata luraba.

      Sai da ta rufe motar hancinta ya shaƙo mata ƙamshin turarensa, dukda zuciyarta bata gaskata ba sai da gabanta ya faɗi.

       Shikam duk da yaji an shigo inda yake baiko motsaba, sai ɗago manyan idanunsa da yay a fusace ya zubama Osin harara ta Mirror.

     Osin yasan laifinsa, dan haka yay saurin faɗin, “Sorry sir”.

    Uffan bai ceba ya maida kansa ga lap-top ɗin.

     Bily da taga fuskarsa ta mirror tai saurin dafe baki, “kutt ashe hardashi a motar? Ta faɗa cikin ranta” A fili kuma tace, “Yaa Amaan ina yini”.

      Kamar zai share sai kuma ya ɗago dan yayi mamaki ambatar sunan nashi da tayi. ta Mirror ya kalleta, murya ciki-ciki yace, “Lafiya lau, daga ina kike haka cikin ruwa?”.

      “Yaya kasuwa mukaje ni da Bestie ruwan ya ritsamu saboda mun kasa samun abin hawa”.

        Bai tanka ba, bai kuma kalli gefen da Ummu takeba, dan amsar Bily ta tabbatar masa da itace, dama tun shigowarsu bugun zuciyarsa ya canja salo, musamman da ya shaƙi ƙamshinta.

       Ummu ma gaidashin da bily tayi yasata tabbatar da zarginta akan shiɗinne dai ashe, dan haka taki kallon inda yake, saima ƙokarin duba kayan cikin Handbag ɗinta take taga babu abinda ya jiƙe ko?, ganin komai normal ta ciro wayarta tana dannawa, jitake a ranta da tasan shine bazata shigoba wlhy, hannunsa data kona ranar ta ɗan saci kallo, gabanta ya faɗi, dan ganin wajen harya ɗaye alamar dai ƙunar ta tashi kenan, duk kuma saitaji babu daɗi, dan sam batai masa danta cutar dashi kamar hakaba.

    Ko tari babu wanda yayi tsakanin ita dashi, sai bily da Osin ne keɗan hira har suka shigo cikin Barrack ɗin.

       A ƙofar gidan Attahir Osin ya tsaya.

    Godiya bily tai musu, sai dai Osin ne kawai ya amsa, itakam Ummu uffan bata ce ba.

    Jin Bily ta fita, itama saita buɗe motar zata fita, wani feshin ruwa ya feso mata a fuska saboda ruwa ake tsulawa sosai, saurin dawowa tai baya ta maida murfin ta rufe tana sauke ajiyar zuciya tareda narke fuska kamar zata fasa ihu, musamman data hango Bily da har tana ƙoƙarin shiga gidan, buɗewa tai ta fita da sauri, sanyin ruwan dake jiƙata na shiga kowanne ɓargonta, ko kallon motar bata sake yiba ta shige ciki.

       Kallo ɗaya yayma bayanta ya ɗauke kansa, dan jallabiyar jikinta dukta manne mata a jiki saboda jiƙewa da tayi.

   Ya sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya yana sauke idanunsa inda ta tashi, ɗan kwalin jallabiyarta data zame ta riƙe a hannune ta manta, sai handkherchief.

     Hannu yakai ya ɗaukesu duka yana kallo, ya lumshe idanunsa tareda matsesu a cikin hannunsa, har suka ƙarasa nashi gida yana a haka, saida Abbas ya buɗe masa ƙofar side ɗinsa ya buɗw idanunsa da suka fara canja launi a hankalo, kayansa daya tattare yasa a ƴar jakar gefensa ya fara miƙama Abbas dake tsaye ya buɗe masa Umbrella, sannan shima ya fita, sam shi ba tsoron ruwan yakeba, dan haka yayma abbas nuni daya janye Umbrella ɗin kawai.

     

       Su Ummu kuwa suna shigowa maman Ahmad ta sauke ajiyar zuciya, haka shima Attahir, tambayoyi ya shiga jeho musu a jere sai kace ɗan jarida, sai da sukai masa bayani ne hankalinsa ya kwanta.

     Maman Ahmad kam coffee ta kawo musu mai zafi, godiya sukai mata da sannu, Ummu da gaba daya zuciyarta takuma dagulewa ɗauka tayi ta wuce ɗaki akan zata canja kaya, babu wanda ya hanata ko cemata danmi.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


          A cikin sati ɗaya su Suhailat suka gama binciko Fannah, ita harma tayi aure, amma kasan cewar babban burinta cin uban Baseeru babu musu ta amince da bukatarsu, harma ta fisu ɗaukar zafi akan lamarin.

     Zaune suke a falon Fannah dake aure yanzu haka a Abuja, kowaccensu cikin nutsuwa take cin pizza ɗin gabanta tana ɗora juice, Fannah tace, “Kun gane, bawai na raina shawararku ba, amma sam ku fahimci shifa ɗan halak baya maida bashin gaba da gaba, da soyayya ya yaudaremu, harma ya haɗa da damfara ku a gareku, to muma da ita zamu yaudaresa, yanzu kunga binciken mu ya nuna mana Meenal da ALLAH ya yankama kazar wahalar zama dashi a yanzu tanada shegen kishi, to da wannan kishin nata zamuyi amfani mu tarwatsa shi, abin ƙarin jin daɗi da farin ciki ƴan uwanta basonsa sukeba, shiyyasasuketa zugata tasha magani a ɓoye karta haihu dashi, amma saboda su sakata farin ciki basa nuna tsanarsa a gabanta sai abayan idonta, wannama damace da zamuyi amfani da ita”.

     “Lallai maganarki gaskiyace Fannah, to amma matsalar dai wazatayi soyayyar dashi yanzu?, mudai duk yariga da ya sanmu, rayuwar da mukai dashi ta shakuwa kuma bazai yuwu ace ya gaza ganemu ba”.

       “Hakane kuma Lubna, indai kuma kuna ganin wannan shawarar tayi nima na amince ɗari bisa ɗari, dan kuma wadda zatai soyayya dashi inaga zamu samu, waddama kuwa zatai saurin jan ra'ayinsa”.

     “Wa kenan?” cewar Lubna.

     Murmushi Suhailat tayi tana gyara zama, taɗan kurbi juice ɗin sannan tace, “Yarinyar ƙanwar Mom ɗina Zulfah, yarinyar ta haɗu, sannanfa gogaggace amma bata bariki ba, ina nufin tanada matuƙar wayo sosai”.

    Fannah tace, “Ok to indai hakane Why not musame ta muji”.

     “Wannan mai saukine, dan yanzu hakama tana Abujar nan gidan Aunty Amrah”.

      Babu bata lokaci Suhailat ta dannama Zulfah kira, sunci sa'a kuwa tana hanyar zuwa yawonta wajen shakatawa, dan haka ta canja akalar motarta zuwa inda suke.


     Tunda ta shigo Lubna da Fannah suka tabbatar zata iya, gata ƙyakykyawa kuwa, sai daifa da gani akwai ɗaukar kai, danda da farko ma iyayi zata fara musu, sai da Suhailat tace, “Zanci ƙaniyarki Zulfah, nutsu abu mai muhimmanci yasa muka kiraki”.

     Murmushi tayi cike da basarwa tace, “Sorry Aunty ina saurarenku”.

           A nutse suka zayyane mata komai, tare da nuna mata pictures ɗin Basiru da matarsa Meenal, wanda duk a social network suka samosu, bama wani yawane dasuba, dan Meenal batason ɗora hoton Basiru kar wata ta ƙyasa saboda ɗan banzan kishinta.

      Zulfah ta kalli pictures ɗin ɗaya bayan ɗaya tana wani taɓe baki, a fili tace, “Akwai ƙyau kam, sai dai babu ƙwarjini, lallai zaisan ya haɗu da Zulfy B mai tafiya daidai da zamaninsa, ku kwantar da hankalinku auntys na, indai wannan ƙaramin ƙwaronne wata ɗaya zuwa uku sai yazo gabanku a durƙushe, yanzu dai ina buƙatar mota”.

     “Indai Mota ce ki ɗauki tawa”. Cewar Suhailat ’.

    Murmushi Zulfah tai tana sake kallonsu, “Auntys ba wacce zan hauba, ta kafin alƙalamice wadda zata zama tarko, dan sonake a haɗuwata dashi ta biyu na masa ƙyautarta”.

    Cike da rashin fahimta duk suka kalleta, tai wani far da idanu, “Bazaku taɓa fahimta taba, amma bara na baku satar amsa. Yanzu ba soyayya kawai yake bukata ba, ba kuma kishine kawai zaisa matarsa da danginta fara shakku akansaba, dole sai an ɗorasa a hanyar cin amana, duk da kuwa shi ɗin gwanine wajen iyata, sai dai a yanzu ganin kamar ya hayene yasashi kwantar da kai, to ya kamata mu mu farkar dashi”.

      Basu wani fahimceta ba sosai, amma sanin halinta da Suhailat tayi sai tai saurin cewa, “Babu damuwa za'a nemo miki, babba kuwa”.

      Murmushi tayi tana mikewa, “Hakan yayi, dukkan wani ƙofar raminsa Aunty S ki turamin, zuwa ƙarshen sati idan nagama nazarinsa zan fara aiki a kansa”.

      Da kallo kawai suka bita na mamaki, ƴar ƙarama da ita sai tsaurin ido, gaba ɗaya bazata wuce 24years ba. 



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


         “Bily wlhy ina cikin matsala”. ‘Ummukulsoom dake shirin kwanciya ta faɗa murya a raunane’.

     Tashi Bily tai zaune a tsorace tana kallonta, “Damuwa kuma Ummu, wace iri?”.

       “Humm, Bily ɗazu baba ya kirani ina makaranta, wai lallai saina fidda mijin aure, kuma ina ƙyautata zaton wannan maganarce zata kawo Abba garinnan gobe”.

        “Humm Ummu wannan matsalar tamuce mu duka, dan kuwa hardani a ciki, dan kina makarantane, amma Hajiya yaya itace ta fara kira bayan tafiyarki, na tabbata meeting akai akanmu ni da ke da yaya Zaid”.

    “Wai har shi ma?”. ‘Cewar Ummu tana ƙwalalo idanu waje’.

    “Wlhy kuwa karkiji wasa, ai Hajiya yaya tace, ta kira Number ki bai shigaba ke da yaya Attahir, shinefa ta kira a ta aunty Hafsa”.

       “Na shiga uku Bily ya zanyi? Gara ke kinada Huzaifa a hannu”.

      “Humm wai inada Huzaifa a hannu, kinsan kuwa yaya mukai dashi jiya da daddare?”.

     “A'a ki faɗa ba yaza ai in sani”.

      Cije baki tayi cikin takaici, Ummu wlhy maganar babu daɗin ji, Huzaifa ba sona yake dan ALLAH ba, sha'awata kawai yakeyi, dama yasha min zancen banza ina sharesa, sai jiya ya nunamin asalin wanene shi da manufarsa a kaina, karanta massege ɗinnan kiga”.

    Amsar wayar Ummu tayi ta karanta, gaba ɗaya fuskarta ta nuna ɓacin rai, cike da fusata ta ɗago tana kallon Bily, “Wai da gaske shine ya rubuto?”.

    “Humm Ummu kennan, wlhy shine, ribarmi zanci idan na masa ƙarya, kin riga da kinyi barci a time ɗin, inaga kawai zanba Muhseen dama, dan na lura shikam domin ALLAH yake ƙaunata yanzun”.

        “Dakin birge kuwa Bily wlhy, shawarar da naketa baki kenan tuni amma kikaƙi fahimta ta, saboda son Huzaifa ya lulluɓe ganinki, nifa dama shiyyasa sam bai minba wlhy, amma sai kike ganin kamar kushesa nakeyi”.

      “Ai yanzu kam na gane gaskiya bestie, kuma ko a baya bawai inakin jin maganarki baneba, kawai dai ki ɗauka ƙaddaratace yin soyayya dashi”.

     “Ito hakane kuma, ALLAH ya zaɓa wanda yafi alkairi tsakanin shi da Huzaifan”.

       “To amin aminiya, yanzu ke mikika yanke akan nakin?”.

    ”Ban yanke komaiba Bily, inaga zanma Umar magana”.

    ”Umar kuma? Please dan ALLAH a'a, bawai fa bai cancanta bane, Umar handsome ne sosai, sai dai matsalar gaskiya ya miki yarinta, baifi shekaru uku fa zai iya baki ba wlhy”.

    “Kai bestie bana son sheri, Umar ɗinne baifi shekaru uku ya bani ba? Gaskiya a'a, wannan mazgegen ƙatonne zakice bai ban shekaru fiye da uku ba?, kedai kawai kice bai mikiba, kuma idan ban fiddashi ba bestie wa gareni?”.

    Shiru Bily tai tana tunani, itafa dason samun tane wlhy Ummukulsoom ta koma gidan yaa Amaan, amma sam ta lura su hankalinsu baya akan juna, tarasa miyasa hakan?....

    Kafin tasamu damar bayyana tambayarta a fili saƙo ya shigo wayar Ummukulsoom, kallon wayar sukai su duka, kafin Ummu ta ɗauka jiki a sanyaye, tasan dai bazai wuce A-Waheed ba, ilai kuwa shine, kallon Bily tai da ta tsareta da ido, kafin ta buɗe saƙon.

  

      _Amincin ALLAH ya tabbata a gareki, yau dai zuciya na buƙatar jin motsin ƴar uwarta, kokin bani damar jin sautin muryarki?._

         *_Naki UMA_*


   Sake maimaita saƙon taketa yi, gaba ɗaya ƙwalwar kanta ta gaza ɗaukar komai yanda ya kamata, tsawon watanni Huɗu da fara wannan ƴar wasan ɓuyar tsakaninta dashi, sannan kusan wata uku kenan bama ya a makarantar su, a wani massege daya turo mata yake shaida mata zaiyi tafiya, amma tafiyarsa batada shamaki da ita,  tundaga wannan lokacin bata sake ganinsa ba, saidai kuma babu fashi masseges nashi kullum saisun riski wayarta..... 

      Ring ɗin wayarta ne ya katse mata tunaninta, ta ɗan zabura saikace wadda taga abin tsoro, sai kuma ta ware idanunta akan screen ɗin wayar tana kallon sunansa ɓaro-ɓaro a jiki.

     yankewa tayi ya sake kira, amma har lokacin Ummu ta kasa ɗagawa, ganin ta kusa tsinkewa kuma bata da niyyar ɗagawa sai Bily ta amsa ta ɗaga ta saka mata wayar a kunne tareda sauka a gadon tama fice daga ɗakin, a ranta tanajin haushin wannan Abdul-Waheed ɗin, tanaji a ranta shine zai raba Ummukulsoom da Yaa Amaan, saboda ta kula tana sonshi sosai dukda yana ta faman wasa da hankalinta.....


NO 37


.........Shiru yaki magana, itama kuma ta kasa koda motsawayar dai na ba kunnenta, kusan mintuna biyu sai ya yanke.

    Rumtse idanu Ummu tayi tana mai zubewa a kan gadon daga ita har wayar, ba tare da ta shirya ba siraran hawaye masu ɗumi suka silalo bisa fuskarta.

      Kusan mintu uku da yanke wayar taji shigowar saƙo, biris tayi da wayar ta ci gaba da hawayenta, ahaka barci ya kwasheta saboda matukar gajiyar da damuwa dake tattare da ita.

    Koda Bily tazo ta kwanta ma tayi barci, bargo kawai ta gyara mata itama ta kwanta, dan garin akwai sanyi, ballema su da ruwa da doka.

     

         Da asubahi bayan sun idar da salla wayar ta ɗauka saboda zuciyarta da keta ingiza ta, saƙonsa ta buɗe.

        *_“Ba zaki kaɗai ke amsa suna sarki ba a dokar daji, mata sune manyan sarakan duniya, baku da ƙarfi, amma kuke ƙarama mai ƙarfi ƙarfinsa._*

          _Naki UMA_


   Siririn tsaki Ummukulsoom taja, wanda har bily ta juyo ta kalleta.

     “Kekuma lafiya?”.

“Ba komai”. Ummu ta faɗa tana tashi ta fita zuwa kicin ɗora breakfast kamar yanda ta safa kowacce safiya kafin tai shirin makaranta, sai dai idan taga zata makarane.

    Wayarta Bily ta ɗauka, tana cire security ɗin taci karo da saƙon A-waheed, karantawa tayi tana taɓe baki, ta fito tana fadin, “Ni yau zan kawo ƙarshen wannan wasan yaran naku, banzan mutum kazo sai wasa kake mata da zuciya”.

   Kira ta danna masa, har tai ring ta gama ba'a ɗagaba, ta sake kira, nanma ba'a ɗagaba, kira uku ba'a ɗagaba, cike da haushi ta goge kiran ta maida wayar yanda ta ganta itama ta tashi ta fice tana tunanin ta hanyar da zata haɗu dashi babu Ummukulsoom.

    Kicin taje tana tayata aikin da take na kokarin fere doya.

     “Bestie ƙarfe nawa zaki fita makaranta ne?”.

       Kallonta Ummu tayi sai kuma ta ɗauke kanta, “Yau bani da lecture ko ɗaya”.

        Daɗine ya kama bily, amma sai bata nuna a fili ba suka cigaba da aikin.


★★★

            Wajen 12 na rana Bily tai karyar zataje wankin kai, dan tasan Ummu anan cikin Barrack tafi son zuwa wankin kai, koda ta tambayeta ma sai tace itafa wajen Jenny zataje.

     “ALLAH ya raka taki gona, idan nagama lecture zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu naje wajen Zuhrah na wanke nikam”.

     “Ok” kawai Bily ta fada ta fice.

    Hakan bai damu Ummu ba, dan damuwar da ta dameta daban.

     Kai tsaye makarantar su Ummukulsoom ta nufa, da taimakon wata ƙawar Ummu ɗin Devine Bily taje Office ɗin Abdul-Waheed.

      Bayan tayi knocking ya bata izinin shiga, kansa a duƙe yanata rubuce-ribuce, hakanne yasa Bily bataga fuskarsa ba sosai, ta zauna tana gaisheshi cikin danne haushinta, bai ɗagoba ya amsa mata.

     “Kina da matsalane?”. Yay tambayar yana cigaba da rubutunsa.

     Sai da Bily taja numfashi tare da dankara masa harara sannan tace, “Sister ɗin Ummukulsoom ce ni”.

    Yanzun ma bai ɗagoba, yace, “Wacece haka?”.

     Kallonsa tayi sosai da sosai tana gyara zamanta, “Abdul-Waheed kana nufin bakasan Ummukulsoom da kake turama massege ba”.

     Tsayawa yay da rubutun da yakeyi ya ɗago yana kallonta, “Ba sunana Abdul-Waheed ba, sannan bansan wadda kike magana akaiba”.

      Sosai Bily ta tsaresa da idanu, “Sir dan ALLAH magana mai muhimmanci ce ta kawoni nan”.

       Wani ɗan card ya miƙa mata batare da yace komaiba. Ta amsa ta karanta, *Uswan Mubarak Adam* taga sunansa, kuma hotonsa ne a jiki, ta ɗago ta kuma kallonsa cikin matukar damuwa, “Amma dan ALLAH to kasan ita Ummukulsoom ɗin ne? Dan itama ɗalibace annan”.

       “Gaskiya ban santa ba, danni watannina uku kenan da fara koyarwa anan, amma ita miya faru da itane?”.

      “Babu komai, na gode sosai”.

Kansa ya jinjina mata yana binta da kallo, danshi sam baima fahimceta ba.

        Gaba ɗaya tunanin Bily ya rikice, ko wajen wankin kan batajeba ta wuce gida, a harabar gidan ta iske Ummu zaune tana shan iska.

    Sannu tai mata bily, bily ta amsa tana zama kusa da ita.

         “Bestie dan ALLAH na tambayeki mana?”.

    Kallonta Ummukulsoom tayi alamar tana saurarenta.

      “Abdul-Waheed yana school ɗinku har yanzu?”.

     “Miyasa kikai min wannan tambayar?”.

    “Babu komai, kedai ki amsani”.

     Numfashi Ummukulsoom ta sauke tana girgiza mata kai, ta cigaba da danna wayar tana magana cike da damuwa, “Bilkisu Abdul-Waheed fa sau uku kacal ya taɓa mana lectures ma, sai dai nakan gansa lokaci-lokaci a school ɗin, watanni Uku kuma kenan ya sanarmin zaiyi tafiya”.

    Da sauri bily tace, “menen cikakken sunansa wai nikam?”.

      “Wai bily waɗannan tambayoyin fa?”.

      “Ummukulsoom ki amsani kawai”.

      “Abdul-Waheed Usman Mustafa”.

     Dafe kai Bily tayi, saboda kuma rikicewa da ƙwalwarta ke neman yi, “Ummu nashiga ruɗani”.

    “Ruɗanin mi?”.

“Wanda na tarar a makarantarku yau Uswan Mubarak Adam, shikuma Abdul-Waheed Usaman Mustafa, mai tura miki saƙo a kowanne massege naki yana saka UMA? Baƙya tunanin akwai ruɗani acikin wannan lamarin?”.

     Yanzu kam sosai Ummukulsoom ta maida hankalinta ga bily, ta ajiye wayarta tana kallonta, “Bilkisu warwaremun dan ALLAH, ni kaina ban taɓa damuwa da ma'ar UMA ɗinnan ba sai yau”.

       Murmushin takaici Bily tayi tana sake fuskantar Ummukulsoom, “Fahimtar hakan danai ce yasa aini nafara binciken, sai dai kema nasan karatune ya ɗauke hankalinki, ba wankin kai najeba Ummukulsoom, makarantar ku naje...........”

    Tsaf Bily ta zayyanema Ummu abinda ya faru, har kiran datai ma A-Waheed ɗin bai amsaba da safe.

      Tsaye Ummu ta miƙe ƙirjinta na wani irin kaikawo, tai taku ɗaya biyu sannan ta juyo tana fuskantar Bily, “Bilkisu a tsakaninnan ina ɓoye miki damuwata ne kawai, amma tabbas lamarin Abdul yana cin zuciyata, a yanda yake mu'amulantata zuciyata bataimin adalciba idan har tace zata cigaba da sonshi, sai dai sam nakasa yakicesa a raina duk yanda naso, bai taɓa min abinda ya taɓa zuciyataba irin jiya, Bily ayanzu Buƙatar ganinsa nake ido da ido, sonake ya sanarmin mike ransa? Amma na rasa wace hanya zanbi?”.

      Bily ta mike itama tana dafa kafaɗarta, “Hanya ɗaya ce Ummu.”

    “Wacece bily?”.

“idan har da gaske yake, kisa masa rana yazo gareki”.

     Idanu Ummukulsoom ta tsirama Bily, kalamanta nakai kawo a ranta, itama tun a daren jiya wannan shike mata kaikawo, to tunaninsu yazo ɗaya da Bily kenan, batace ma bily komai ba ta ɗauki wayarta suka koma cikin gida.

    Har dare abin ya kasa barin ranta, kamar yanda ya saba kuwa ɗan halak ɗin sai ga massege nashi.

     Yau ko karantawa Ummu bataiba ta tahau typing massege ta tura masa nata saƙon.

        _Next week insha ALLAHU zan bayyana mijin aurena ga mahaifina tamkar yanda ya buƙata, dan haka kabar wahalar da kanka wajen takura rayuwata da saƙƙonni._

 

    Iya abinda ta rubuta kenan ta tura masa tare da kashe wayar gaba ɗaya.

      Bily bata tambayeta mita turaba, ita kuma bata sanar mataba. 



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


             Kwanan baba uku a asibitin jikinsa yay sauƙi, dama Basiru jinsa yake tamkar akan ƙaya, bayan an sallamesu sun koma gidane Inna kebama Basiru labarin tutsen ciwon baba akan sane, dan kullum suna a cikin damuwa da rashin ganinsa, su summa zata koya ɓatane.

     Haƙuri yayta basu kamar gaske, tareda shaida musu wasu ayyukane suka riƙesa a can.

     Baba dake masa kallon tsaf yana daga kwance yace, “Basiru ka canja wannan rayuwar taka kafin lokaci ya ƙure maka, inaji a jikina akwai abinda kake ɓoye mana, ina tsoratar maka yau da gobe basiru, dukfa wanda ya hau motar ƙwaɗayi zata saukesa ne a tashar wulaƙanci, yanzu yadace ace mace ta jaka wata uwa duniya tsawon shekaru biyar? Sannan ita daya dace ta biyoka gidanka amma kaine ka bita, bata taɓa sanin hanyar tushenka ba a matsayinta na matarka ta aure” Baba yay shiru hana haɗiye wani nannauyan abu daya tsaya masa a ƙirji, idonsa ya kuma kaɗawa yay jazur, yaci gaba da faɗin, “Basiru babu rayuwar dakeda inganci ga bawa irin ka tsaya matsayinka, dukkan wanda zai hangi na sama dashi a rayuwa to katabbata yana tanadama kansane ranar kuka, idan har kana tafiya akan ƙafafunka karka kalli wanda yake a mota, kalli wanda yake tafiya a keken guragu bashida ƙafafun shi, kakuma saka a ranka badan ALLAH ya ƙasƙantar da gurgu bane ya hanashi ƙafa, badan ka fisa bane yabaka ƙafa, badan mai mota ya fiku bane ya bashi abin hawa, zata iya yuwuwa ma wannan gurgun duk ya fiku, ALLAH ya ganar damu gaskiya baki ɗaya”.

     Da amin suka amsa shida inna da talatuwa da itama tazo, kamar gaske Basiru ya ɗauka, dan saida ya ƙara kwanaki uku a ɗilau sannan ya koma katsina..    

       A yanda ya samu tarba daga Meenal kawai sai jikinsa yay sanyi, yasan fushi take dashi, maimakon ya nuna mata ɓacin ransa akan ƙin zuwa duba mahaifinsa da tayi, wanda ko a waya bata taɓa tambayar yaya jikinsa ba, dukda Ya sanar mata yazo ya iske baida lafiya ne, amma saishine yashiga bata haƙuri da lallashinta.

     Da ƙyar ta sakko suka daidaita.


     Kwana biyu da dawowarsa aka shiga hidimar bikin yayanta, sam meenal ta hana basiru sakewa, idan har bata tare dashi to bai isa ya fitaba shi kaɗai, tun abin na bashi dariya da nishaɗi harya fara sosa ransa, amma ko a fuska ya gaza nuna mata, sai cin zuciyarsa yakeyi.

      Yau dai ALLAH ya bashi sa'a ta manta bata kulle ƙofar baya ba ta kicin, dan haka take masa dan kar ya fita, (mijin hajiya kenan🤣😝), duk ya duba baiga keys ɗin motocin taba, ta kwashe ta ɓoye, yaji haushi sosai, harma zuciyarsa ta fara tunanin shima yakamata ya mallaki motar kansa tunda sun dawo 9ja, ƴan kuɗin dake Accaunt ɗinsa kuma bazasu ishesa komaiba, dama waɗanda ya tattarane na su Suhailat da Lubna, aurensa da Meenal kuma ya fahimci kuɗaɗen ba komai bane akan ita abindama take dashi, saiya tattaresu ya sa a banki, sai dai ita kuma Meenal sam tasha banban dasu Suhailat, dan bata masa ɓarnar kuɗi, komai nata kaffa-kaffa take da kayanta, shiyyasa har zuwa yanzu bazaice ga wani ƙwaƙwƙwaran abu daya cizga daga jikinta ba kona mahaifinta.

       Tunda ya fito ya zauna ƙofar gidan Zulfah dake cikin mota take kallonsa, dama tunda aka fara bikinnan take bibiyarsa shida Meenal ba tare da sun saniba, ba kai tsaye take son zuwa garesa ba.

        Kallon Abu da sukazo tare tayi, “broth inaga plan B zamuyi amfani dashi tunda plan A babu ƙofa, dan haka aikinka zai fara fa”

        “Karki samu damuwa muje zuwa kawai”.

    Basiru ta nuna masa, yay murmushi tareda ficewa, murfin ya maida ya rufe mata ya nufi Basiru.

     

       Kan Baseer sunkuye yana danna waya, kallo ɗaya zakai masa ka fahimci akwai abinda ke damunsa, Abu yay masa sallama.

     Ɗago ido yay ya kallesa cike da isa,  amma ganin Abu shiɗinma a haɗe dagani ɗan manyane sai Basiru ya ɗan saki fuska suka gaisa, duk da dai yasan anguwace ta manya da wahala asamu mai ƙaramin ƙarfi dama.

      Ba tare da Abu ya jashi da wata magana ba sukai sallama ya wuce.

    Da kallo Basiru ya bisa harya koma wajen Zulfa dake mota ya buɗe ya shiga suka bar wajen suna dariya.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


              Tsawon kwanaki Uku da tura saƙonnan Ummukulsoom taƙi buɗe  wayarta, gashi Abba yazo da kansa yakuma jaddada musu maganar aure, yauma ya wuce Chaina daga nan lagos.

      A gefe dai Yaya zaid ya dameta da kira ta wayar Bily, tasan bai wuce maganar So ba, ita kuma sam taƙi aminta suyi wannan maganar dashi, daya fara take yanke kiran.

     Shi sam baisan damuwa yake ƙara mata ba akan wadda take a ciki, Muhseen ɗin Bily harsun aje magana akan tura iyayensa......

          Sallamar maman Ahmad ta katse tunaninta, ta janye mata tagumin data rabga tana faɗin, “Ummukulsoom kinada baƙo”.

     “Baƙo kuma aunty Hafsat?”.

     “Eh”.

“To nikuwa banyi da kowa zaizo ba, dan Umar ma yana gombe”.

      Ƴar guntuwar takardar dake hannun maman Ahmad ta miƙa mata, jiki a sanyaye ta amsa, sai dai ganin abinda ke rubuce a jikine ya sata zabura da mamaki.

     *_“Abdul-Waheed!”_*

Haka ma ɗan aiken ya faɗa, gashi can Bily ta buɗe musu falon baƙi, saiki tashi ki shirya.

    Kasa koda motsi Ummukulsoom tayi, to ita daɗi za ta ce taji da zuwan nasa kokuwa haushi?.

   Bata da mai bata amsa, dan haka ta miƙe tamkar wata munafuka, dama bata daɗe dayin wanka ba, dan haka ta canja kayanta zuwa doguwar riga ta atanfa, batai kwalliya ba sam, sai turare da ta ɗan fesa, a ganinta bata buƙatar fentin komai a fuska dan zataje wajensa, dan tagama yanke shawarar zaɓar Umar matsayin mijin aurenta..    


   A falo maman Ahmad ta bata madaidaicin tiren da aka ɗora ruwa da juice sai kofi da dambun nama.

     “Aunty ni dama kin barsa kawai”.

    “Bazai yuwuba ai Ummukulsoom, yau ya fara zuwa, ya cancanci karramawa daga garemu.

     Batace komaiba ta amsa, haka kawai takejin ƙirjinta ya mata nauyi, ga wani rawa da zuciyarta keyi, ta rasa dalili, sai kace yaune zata fara sanin wanene Abdul-Waheed ɗin.

      Bataga bily ba harta fito, dan haka tai tunanin ko tana wajensa, da ƙwarin gwiwar hakan ta ƙarasa ƙofar falon, tai sallama can ƙasan maƙoshi.

    Sam ba'a amsa mataba, inma an amsa bataji ba, dan haka ta harari labulen tana ɗan gyara gyalenta sannan ta shiga da wata sabuwar sallamar.

         Akan bayansa daya juya ta sauke idanunta, Suit ne jikinsa kalar jaa, baisa ta saman ba, ta cikice kawai baƙa sai ƴar karama ta saman, ta ajiye tiren hannunta a hankali, yayinda zuciyarta keta wantsale-wantsale.

    Yanda yanajinta bai juyoba bai kuma yi magana ba haka itama ta samu waje ta zauna ta sharesa, itafa bazata ɗauki wannan isar tashiba sam.

    Kusan mintuna biyu suna a haka, kafin ya juyo a hankali yana takowa tamkar mai gudun aji motsinsa, Ummukulsoom na jinsa amma ta dake taƙi koda motsi itama balle ta saci kallonsa.

      Gabanta yazo ya tsaya cikeda izza, ya harde hannayensa ya zuba mata manyan idanunsa kawai, ganin bazata kallesa bane yasashi saka hannu ya zare wayarta da take dannawa.

    Gabanta yaɗan fadi tabi hannunsa da kallo, sai kuma ta basar taƙi kallon nasa balle ta tanka. Minti biyu ne ya sake shuɗewa, haushi ya fara tasiri a zuciyar Ummukulsoom, dan haka ta miƙe da nufin tafiyarta dan wannan Ummu ɗin bata da bace da maza ke garawa, ta yanzu itace zata gara mazan, inhar bazaiyi maganaba to ita kuma bazatayiba a matsayinta na mace, ballema tamasa sallamar da addini ya wajabta mata amma bataji ya amsaba.

      Taku ɗaya biyu tayi taji an damƙo hannunta.

    Cak ta tsaya tare da juyowa a fusace, “Sakemin hannu!”.

     Shiru bai tanka ba, bai kuma saketa ba.

    A kausashe tace, “Abdul-Waheed sakemin hannu, sannan daga wannan ranar karka sake zuwa inda nake, dama ban taɓa sonka ba, a yanzun ma nazo na tabbatar maka na fidda mijin aurene, karka sake turamin shirmen saƙonka danni ba doll ɗin wasan, yara bace kaji, inada wanda nake S......”

    Fisgotan da yayne ya hanata ƙarasa kalmar SO din da tai niyyar fada, ya turata ta manne da bango, ya kuma dinkareta yanda bazata taɓa kufce masa ba.

     “Duk abinda naso nawane ni kaɗai yarinya, babu wani mahaluki daya isa nai raba daidai dashi koda wajen farautarsa ne..”

    Sosai Ummu ta rikice, ta kalla fuskarsa amma sam ba shi bane, Abdul-Waheed ne dai malamin makarantarsu, to miyasa muryar kuma?....

       Sake kallon hannunsa tayi dan shima zai iya zame mata shaida, sai dai kuma dogon hannun rigar ya rufe, cikin zafin nama tasa dukkan hannayenta ta turashi baya da dukkan ƙarfinta, dan kusancinsu yayi yawa, tsigar jikinta sai tashi yake, ko motsi baiyiba, saima hannayen nata daya riƙe duka ya maidasu baya a matse da hannunsa ɗaya.

    Baki ta buɗe zatai magana ya ɗora yatsansa a baki yace, “Shiiii🤫”. Alamar tayi shiru.

     Ɓam kuwa ta maida bakin ta rufe tana hararsa, shikuma yasa ɗayan hannunsa  akan fuskarsa ya fara zame fuskan saman daya ɗora akan tasa ta ainahi..........✍🏻




*Karki bari ayi babu ke, Abari ya huce shike kawo rabon wani*🤝🏽🤝🏽🤝🏽

Ɗaliban *G.G.A.S.S Ɗan-zabuwa* na cigiyar ƴan uwanta ɗalibai da suka kammala a shekarar *2010 (zolo)*, taron tunawa da juna dazai gudana *11-3-2020* a harabar makarantar ta ɗan-zabuwa. Maza garzayo kar ayi babu ke, shekara goma ba kwana goma bace ba😃💃🏻._

         *_Duk wadda ta kasance ƴar zolon zarto. 🤔kamar haka fa kuke sawa ko my guys?😂,  koda yake ƙwailoli sun zama manyan mata yanzu🤣😝⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️._*

      Anema wannan Number👇🏻

           *+234 810 999 2578*



NO. 38



............Ɗif wutar data haska falon ta ɗauke saboda tasowar hadarin daya gauraye garin, Ummukulsoom ta fisge hannunta jin ya sassauta riƙon da yay mata saboda laluben waya da yake zai kunna fitila, ƙokarin barin falon tayi, dan haka ta fara laluben hanya zata gudu, cikin sa'a ta taɓa ƙofar, sai dai kamar an saita da maido wuta.

     Hasken daya mamaye falonne yasata juyowa jin yana takowa inda take yana dariya.

     “Yaya Zaid?!”. ‘Ta faɗa cike da mamaki da tsantsar ruɗani tana binsa da kallo, gaba ɗaya idanunta sun firfito saboda tashin hankali, mi hakan ke nufi?’.

     Bakinta na rawa tace, “Yaya Zaid kana nufin kaine Abdul-Waheed ɗin?”.

       Murmushi yayi tare da ɗaga mata facemask ɗin daya cire daga fuskarsa.

    Takuma waro idanu tanayin baya tamkar zata faɗi, ALLAH dai ya bata sa'a tai azamar dafe bango, da baya baya ta ringa tafiya har ALLAH ya bata nasarar buɗe ƙofar ta fita da gudu zuwa cikin gida hawaye na ƙwarara a kan fuskarta.

      Dafe kai Zaid yayi yana sauke nannauyan numfashi, ya zube a saman kujerar dake kusa dashi saboda wata hajijiya da yakejin tana neman kwasarsa ƙasa.


        Ummukulsoom na shiga ta faɗa jikin Bily dake falo zaune ta kuma fashewa da sabon kuka, gaba ɗaya Bily ta rikice, sai tambayarta lafiya? Takeyi, amma sam taki magana.

      Motsinsu Maman Ahmad taji dan haka ta fito daga kicin a hanzarce.

     “A'a, Ummukulsoom lafiya kuwa? Yaya da kuka haka?”.

     “Wlhy nima bansan mi akai mataba Aunty, haka ta shigo tana kuka”......

     Shigowar Zaid ce ta katse musu maganarsu, dukansu suka kallesa har Ummukulsoom ɗin dake hawaye, ta miƙe zumbur zata bar falon yay saurin shan gabanta.

       A tsawace tace, “Yaya Zaid baka da abin faɗa mini, a zatona idan kaga wani zaimin hakan haushi zakaji, amm.....”

     Hannu ya ɗaga mata alamar dakatar da ita, “Ummukulsoom ki tsaya ki saurareni, sam ba yanda kike tunanin baneba, bani bane Abdul-Waheed, shi daban ni da ban wlhy kinji na rantse miki”.

     hawayenta ne suka tsaya cak daga zirarowar da sukeyi, ta tsira masa idanu alamar neman ƙarin bayani.

    Da hannu ya nuna mata wajen zama, kamar bazata zauna ba sai kuma Bily ta kamo hannunta ta zaunar, shima zama yayi, Maman Ahmad da Bily suka barmusu falon.

         “Kiyi haƙuri Ummukulsoom banso ɓata miki rai ba sam, nayine dan kawai na gwadaki akan soyayyar da nake miki, dan nasan kin fahimci ina sonki amma kike zillemin, wlhy sam banine Abdul-Waheed ba”.

       “To wanene?”.

Murmushin takaici yayi yana miƙewa tsaye, ta bisa da kallo ranta na ƙara ɓaci, sai da yay taku biyu zuwa uku sannan ya juyo yana fuskantarta.

     “Zuwana na ƙarshe gidannan na fahimci baƙon al'amari daga gareki, na karkatar hankalinki ga wanina bayan Umar kuma, hakan yasani bincikar wayarki ba tare da kin saniba harna samu Number Abdul-Waheed, har office ɗinsa na samesa tareda kora masa gargaɗin ya rabu dake, inba hakaba komi ya biyo baya yay kuka da kansa, naga alamar damuwa a garesa ƙarara, dan har roƙona yayi akan dan ALLAH kar nai masa haka, shi sonki yake tsakaninsa ga ALLAH. kuma aurenki zaiyi, shiyyasa ya barkima ki nutsu a karatunki, har saikin gama yafara fuskantarki. Sam ban sauraresa ba, nakuma ja masa dogon gargaɗi nabarosa, tundaga wannan lokacin nafara tunanin ta hanyar da zanzo miki, saina fahimci kinason Abdul-Waheed sosai, wannan yasani amfani da wannan damar nazo miki matsayin shi saboda maganar aure da baba yay mana, na kiraki yafi a ƙirga muyi magana kinƙi saurarena, saina bincika ta hanyar Bily ba tare da itama tasan manufar hakanba, ita ta sanarmin kina shirin bama Abdul-Waheed dama fa, hankalina ya tashi sosai dan kuskuren danayi shine ban saka Abdul goge Number kiba, kekuma ban goge a nakiba, namanta koda namasa katanga da zuwa wajenki dolene zaku cigaba da mu'amula ta waya fa, kiyi haƙuri Ummukulsoom Please, nasan ni mai laifine a gareki”.

     Wani ƙududun takaicine ya maƙale numfashin Ummukulsoom, dama yaya Zaid ne yay ma Abdul-Waheed katanga da zuwa wajenta? Bawan ALLAH tanata zarginsa da wasa da hankalinta ba tare da ta sani ba, da gudu ta shige ɗakinsu ta barsa nan tsaye ko waigowa batayiba dukda kiran da yaketa ƙwala mata kuwa.

      Attahir dake tsaye bayansu ya kafe Zaid da ido yanason gano gaskiyar zancensa, Zaid dayaji motsi a bayansa ya waiyo suka haɗa ido da Attahir, ƙasa yay da kansa na jin nadamar abinda ya aikata.

     Attahir ya girgiza kansa yana faɗin, “Ya maka ƙyau Zaid, ƙanwarka zakazo kana ma wasa da hankali ko?, ashe dama tun jiya ka shigo lagos amma kamin ƙaryar yaune zakazo ko?”.

      “Kayi haƙuri yaya, nayi kuskure, amma nayi nadama, tunda bata sona kuma na barta”.

    Ƙala Attahir bai ce masaba yay gaba zuwa ɗakin su Ummukulsoom.

    Sai da yay sallama suka amsa sannan ya shiga, Ummukulsoom na kwance jikin maman Ahmad tana kukan takaicin Zaid.

      Bakin ƙofa ya tsaya ya tsura mata idanu, kafin ya saume numfashi ya ƙarasa takowa cikin ɗakin sosai, saurin tashi Bily tai ta basa stool ɗin mirror ya zauna.

        “Ummukulsoom tashi zaune”.

    Babu musu ta tashi zaune tana share hawayenta.

     “Wanene Abdul-Waheed ɗin?”.

     Kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta bashi labarinsa, Attahir dake saurarenta sai jinjina kai yakeyi, “Ummukulsoom kin tabbata kinason Abdul-Waheed a matsayin mijin aure?”.

      Ƙasa ta kumayi da kai alamar jin kunya, hakan ne ya saka Attahir fahimtar tana son nashi.

    Yaɗan murmusa yana miƙewa, “Nima na goyi bayan ki bashi dama, dan nasan da Zaid bai aikata daƙilesa ba da tuni yafara zuwa gidannan, amma nabaki dama kiyi tunanin acikin kwanaki Uku kacal, dan Abba sati biyu nikuma ya bani akanku”.

    Kanta ta jinjina masa alamar amsawa. 


      Yana fita maman Ahmad ta kalli Ummukulsoom da kulawa.

      “Ummukulsoom yanzu ke kinason Abdul-Waheed ɗin?”.

     Kallonta Ummukulsoom tayi tana guntun murmushi, “Aunty idan nace miki bana sonshi nayi ƙarya, sai dai rashin mu'amulantata azahiri da yake shike sakani jin rauni akansa, tayaya zan bashi dama bayan bansan halinsa ba, sau ɗaya kacal muka taɓa maganar fatar baki dashi, daga nan ko'a makaranta muka haɗu bama magana, sam ban fahimci nasa tsarinba nikam”.

        “indai dan wannan ne inaga ba abin damuwa baneba, dan lokaci bai ƙureba a gareku, ayanzu haka zaki iya buƙatar ganinsa, shikuma zaid Abban Ahmad nasan zaimasa magana yaje ya janye gargaɗin da yay masa na hanashi zuwa gareki ko kuwa Bily?”.

       Baki Bily ta turo gaba cike da jin haushi, “Nifa wlhy danma tawani dage ne, amma mizai hana ta koma gidan yaya Amaan, itama hankalinta sai yafi kwanciya wlhy”.

      Harara Ummukulsoom ta makama Bily, rai a ɓace tace, “Bilkisu idan har bason mu sami matsala kikeba kidaina sakomin mutumin nan a lamarina, ni nace mikine sonsa nake ko buƙatar sake zama dashi? Wancanma umarnin iyayene, kamar yanda yace shi da mahaifiyarsa da ƴan uwansa wutsiyar raƙumi tai nesa da ƙasa a tsakaninmu to nima hakance yanzu a gareni, ko ɗauramin shi akayi saina since shi, Abdul-Waheed ɗin dai da baƙyaso dashi zan rayu insha ALLAH ”.

      Baki Bily ta taɓe tama fice daga ɗakin ta barsu tana jan tsaki.

     Itama Ummukulsoom tsakin tayi, ita maman Ahmad ma sai suka bata dariya.


★★★★


        Gaba ɗaya lamarin yazoma Ummukulsoom da ruɗani, dan ita dai da farko sai taga kamar ba Zaid baneba, amma bayanin da yay mata yasata gazgata maganarsa, musamman data turama Abdul-Waheed massege akan tana son ganinsa. saiya bata amsa da,

         *_“Ummuna yayanki yamin shamaki dake, dukda zuciyata na tsananin ƙaunarki, tunda kika turomin maganar aurenki ina cikin tashin hankali mai tsanani, dan ALLAH ki bani damar fuskantar iyayenki._*

     

       Bayan taga wannan saƙon saita sharesa batareda ta masa reply ba, kusan kwanaki biyu da faruwar hakan sai gashi ya kirata, abin ya bata mamaki, dan tunda suke bai taɓa kiranta a waya ba sai yau.

         Ɗagawa tayi jiki a sanyaye, su duka sukai shiru na wasu sakwanni, kafin daga can ya ɗan sauke numfashi murya ƙasa-ƙasa yace, “Assalamu alaiki”.

     Amsawa Ummukulsoom tai zuciyarta na wani irin harbawa, amma saita danne tana saita numfashinta tana gaidashi.

        Yanzunma a taƙaice ya amsa mata, hakan saiya kuma bata mamaki, amma sai ta share itama tai shiru. 

    A haka suka kuma cinye wasu seconds ɗin, harma ta fara tunanin yanke wayar taji yace, “Insha ALLAHU inason zuwa gareki inhar yayanki ya amince”.

     Ɓoyayyar ajiyar zuciya Ummukulsoom ta sauke, maimakon ta amsashi sai kawai tace, “Humm”.

     Sosai yaji Humm ɗinnan har cikin ransa, dan itamafa ya kula ba kanwar lasa bace, sai dai jan ajinta ke ƙara wutar sonta a ranshi sosai...

     Kuma katse shirun nasu yayi da faɗin, “Ban gane Humm ba?”.

     “To mikakeso nace maka nikam? Ni a ganina ya rage naka kazo a lokacin daya dace ko kazo a makare, ni dai a gareni babu fashi wajen bin umarnin iyayena”.

    Daga haka ta yanke wayar tama kasheta gaba ɗaya tanajin takaicin halayyar maza, kowa da kai tamkar giginya da tasa matsalar, taja tsoki tana miƙewa daga gaban mirror ɗin domin sanya kaya, dama wanka tayo tanason zuwa wankin kai ne.

       A gaba ɗaya kwanakin nan maganar auren nan ta dagula mata lissafi, sam batai niyyar yin aure a nan kusaba, amma bazata iya bijirema iyayenta ba, dan baba yamayi ƙoƙari daya amince mata taci gaba da karatunnan, abinda ba'a taɓayi ba a garinsu, yanzu haka da ansan matsayinta a garin da ko ruwa ba'a barta tashaba saboda surutai da za ai ta mata itada baba.


*BAYAN KWANA BIYU*


       Kamar yanda Abdul-Waheed ya alkawarta yay mata massege akan yau zai zo.

      Dan kawai ta baƙanta ran Yaya Zaid da har yanzu bai koma ba ta shirya tarbar Abdul-Waheed, harma fatan Amaan ma ya gansu tare take, dukda ma ita a tsakanin nan gaba ɗaya bata ganinsa, taji dai kamar ranar Attahir na faɗin yaje kaduna.

        Da taimakon maman Ahmad aka shirya masa abinci mai ma'ana mai kuma sauƙi, dan Bily catai batayi, ita gaba ɗaya batason wani Abdul-Waheed, tafiso Ummu ta zaɓi Zaid ko yaa Amaan, rashin dawowar Umar ma ba ƙaramin daɗi yake mataba.

        Shareta Ummukulsoom tayi, suka gama tsaf sannan ta wuce yin wanka, kamar kullum yauma bawata kwalliya ce tayiba, sai dai tayi ƙyau masha ALLAH, ga ƙamshinta mai daɗi tana fiddawa. 

        Huɗu da rabi dai-dai ya turo mata massege akan ya iso, da kanta ta fito ta sanarma Maman Ahmad.

     Maman Ahmad ta kalli bily dake zaune ta saurarensu sai kumbura take, dariyar dake cin ranta ta danne tace, “Yi haƙuri aunty B ɗinmu dan ALLAH ki kaisa falon baƙi kafin ta ƙaraso”.

    Kuma kumbura Bily tayi, “Nifa gaskiya Aunty ki.....”

     “Yi haƙuri Aunty B ɗinmu, ai har yanzu Bestie ɗinki allura ce cikin ruwa ko”.

     “Aunty kuna wani goya mata bayane keda Yaya Attahir za'ace allura cikin ruwa?”.

     “Ai komai sonmu data auri Abdul idan ba mijinta bane bata aurensa wlhy”.

      Dariyar ƙeta Bily ta sanya tana cewa, “Insha ALLAHU ma bazata ƙulluba wannan igiyar” tai maganar tana yima Ummukulsoom gwalo sannan ta fice.

     Hakan saiya soki zuciyar Ummukulsoom, taji a ranta kai tsaye zata bama Abdul-Waheed dama dan kawai ta cusama bily takaici.

  

      Sai da bily ta dawo da kusan minti huɗu sannan Ummukulsoom ta miƙe ta fice ɗauke da tire.

      Haka kawai taji zuciyarta na ayyano mata abinda ya faru ranar tsakaninta da Zaid, saurin kauda abun tayi a ranta tareda karanto addu'a sannan tai sallama.

     Sassanyar muryarsa dake saka Ummukulsoom shiga ruɗani ta ce ta amsa, ta ɗan rumtse idanunta sannan ta shiga.

      Zaune yake ƙafa a harɗe, kansa a sunkuye yana danna waya, ƙamshin turarensa dukta cika falon.

     Sai da ta ajiye tiren sannan ta kuma satar kallonsa, yana sanye da farin yadi mai ƙyau harda hula, sosai yayi ƙyau a asalin bahaushensa, Abdul-Waheed ɗintane tabbas, hakan saiya saka zuciyarta samun nutsuwa, sai dai tana mamakin bugun da zuciyarta ke ɗanyi da sauri-sauri.

         Kallonta yake ta cikin eyeglasess ɗin fuskarsa mai cike da kwarjinin cikar kamala, sam fuskarsa babu walwala.

    Sai dai hakan bai damu Ummukulsoom ba, dan ayanda ta lura dashi haka shima yanayinsa yake kamar Ama..., kasa ƙarasa sunan tayi dukda a zuciyartane kuma.

         Ganin kallon da yake matane yasata cewa, “Ina yini”.

      Ya janye idanunsa daga kanta yay luu har zai lumshe sai kuma yay azamar buɗewa.

   Kaɗan ya rage numfashin Ummu ya ɗauke, dan ba ƙaramin rikita zuciyarta taso shigaba ganin yanda yay da idanu, sai dai buɗewar da yay batare da ya lumshe ba ne ya sa ta saume ɓoyayyar ajiyar zuciya.

       Shi kansa ya kula da halin data kusa shiga, yay saurin kauda yanayin da faɗin, “Ko ba'ai murna da ganina bane gimbiya?”.

     Murmushi Ummukulsoom tayi kawai, amma batace komaiba.

    Ya ɗauke idanunsa daga kallonta yana ɗan furzo iska a bakinsa, “Nasan akwai tarin tambayoyi a bakinki akaina, sai dai nima bazanso kimin suba kulsoom, dama kawai nake buƙata”.

       Batare da ta kallesa ba tace, “Miyasa bakason na tambayeka? Bayan kuma waɗan nan tambayoyin sune abu mafi cin zuciyata a tarayyata da kai”.

     “Nasan da hakan Kulsoom, sai dai sam bansan taya zan baki kowacce amsaba idan kinmin”. ‘ya ƙare maganar yana ɗan dafe kai’.

     Kallon mamaki Ummukulsoom tai masa, dan sosai taga alamun ƙosawa da magana a tattare dashi.

    Ta ɗauke kanta kawai zuciyarta na kuma tsunduma a wasiwasi.

       Shiru duk sukayi babu wanda ya sake tankawa, zuwa can ya kuma kallonta ya janye idanunsa, “Baki ce komai ba”.

       “Humm” ta faɗa kawai tana basarwa, kamar bazata tankaba sai kuma tace, “Bansan mizan ce ba nima, kamar yanda na lura kaima bakinka babu abin faɗa”.

      Lallausan Murmushi taga ya saki a karo na farko, sai dai badan kallonsa takeba ma bazata taɓa fahimtar yayiba, yakai hannunsa a saman ido sai kuma yay azamar waskewa ya dafe kansa...

     Tsira masa idanu Ummukulsoom tayi tsoro na kuma bayyana karara a fuskarta.

       “Ba abin faɗa bane babu, yanda za'a faɗa ɗinne matsalar”. ‘Yay maganar cikin basar da ita’.

       Janye idanunta tayi tana sauke ajiyar zuciya a hankali, “Abdul-Waheed kenan, to ni dai yanzu mike tafe da kai?”.

      Sai da ya gumtsi iska ya fesar yana mata wani kallon ƙasan ido, kafin yace, “Maganar aure”.

      Ta ɗan taɓe baki, “Ai banga alamar hakanba”.

       Idanu ya tsira mata yana kuma ƙoƙarin control ɗin face ɗinsa wajen sakinta, “Ban cika son nuna lamarina a zance ba, ki bani dama ta halattacciyar hanya kawai”.

        “Miyasa da sauri haka?”.

    “Saboda nafi kowa buƙatarki”.

      Murmushi Ummukulsoom tai taɗan basar, “Baka tunanin bakai kaɗai bane a filin dagar?”.

      “Sanin hakan ne yasani tahowa da ƙarfina”.

     “Banda cika baki dai”.

Shiru yay bai amsaba, alamar yakai maƙura.

      “Yakai shiru? Ko dai bazaka iya takararba?”.

      Bakinsa yaɗan motsa, amma yarasa abinda zaice mata, sai kafeta da idanu da yayi.

           “Yawan magana akwai wahalarwa ko?”.

    Da mamaki ya kalleta, karfa yazam kallon ƙitse akema juna? Ya faɗa a ransa. A fili kuma saiya jinjina mata kai alamar A'a.

      Tai murmushi dan ita haka kawaima saiya bata tausayi, wannan kam da a kd suka haɗu babu abinda zai hanata yarda basuda alaƙa da Dad, dan halayyar tazo ɗaya.......

        Katse mata tunani yay da faɗin, “Ba maganar wasa ya kawoniba kulsoom, inason tura iyayena gidanku a satin nan”.

        Kasa amsashi tai, sai zuciyarta ke mata kaikawo akan ta amsashi koko ta ƙara jansa?....

      “Dan ALLAH karkice A'a”. Ya faɗa a hankali can ƙasan maƙoshi.

        “Ai baka ci jarabawa ko ɗayaba”.

    “A jinkirta min ita mana har sai na gama nutsuwa waje ɗaya”.

    “Minene matsalar?”.

“Mahaifiyata nason na auri watanki, bayan kin mamaye ko ina”.

       Kallonsa tai na wasu seconds tare da janye idanunta.

   Yayinda shikuma ya dafe kansa saboda tsantsar ƙosawa yana tsoron kar akai maƙura komai ya buɗe.....

     “Zanyi tunani”. Ummukulsoom ta faɗa cikin katsesa.

     Kansa ya rausayar gefe batare da yace komaiba.

     Ganin hakan ne yasata miƙewa tana faɗin, “Bismillah kaci zwani abu ina zuwa”. Bata jira cewarsa ba ta fice.


     Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke bayan fitarta, ya maida kansa ya jingina da kujera yana lumshe idanu...........✍🏻


*_NO. 39_*



..........Abdul-Waheed dai ya tafi yabar Ummukulsoom da nazari, gashi Bily ce abokiyar shawarar amma ta botsare mata, maman Ahmad kuma yaya Attahir na gida, shiyyasa babu sakewa sosai.

     Kiran da baba ya sake matane ya saka hankalinta tashi, dan kuma jaddada mata maganar yakeyi, hakan yasakata fahimta lallai akwai abinda ke faruwa baba na ɓoye mata, anya ba magar bata da aure bane ya fasu kuwa?.

   Tasan a bakin murja kawai zata iya samun ƙarin bayani, itakuma sai mijinta na gida suke iya gaisawa. Wayarta ta ɗauka ta kirashi, cikin sa'a kuwa ta shaiga. Bayan ya ɗaga daga can suka gaisa, kafin ta tambayi ƴar uwarta.

     Daga can yace, “Kash aiko Umma ansamu akasi, dan jiya-jiya na baro gida yanzu haka ina nan kan hanyar legas, amma itama fa shekaran jiya ta nemeki bamu sameki ba ne saboda natuwak”.

    Cike da zumuɗi, Ummu tace, “ALLAH saiki, lafiya dai ko?”.

    Jimm yayi kafin yace, “Eh to da sauƙi kam, wata dai ƴar magana ce keta yawo a gari akanki”.

    “A kaina kuma? Tami kenan?”.

    Shiru yay kamar bazaice komaiba.

     “Inajinka, karkaji komai ka sanarmin dan ALLAH”.

         Cike da jin nauyinta yace, “Umma kiyi haƙuri, haka aketa cewa wai aurenki ya mutu, randa aka kaiki a washe gari mijin ya sakeki amma shine baba yarufe yaƙi faɗa, kuma wai....”

       Hawayene suka cika idanun Ummukulsoom, haba itakam tayi mamakin azalzalarta da baba keyi a tsakanin nan akan batun aure, bata bukatar jin ƙarshen zancen dan haka kawai ta yanke wayar tana haɗiye kukanta, zuciyarta taf da mamakin ya akai wannan maganar ta fito a ɗilau? Gashi harma an canja salon zancen gaba ɗaya.

          Zafin da kanta ya ɗaukane ba tare da tunanin komaiba ta turama A-Waheed saƙo akan ta amince ya tura magabatansa kawai.

   Tana turawa ta kashe wayarta gaba ɗaya ranta duk a matuƙar dagule.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


          A ɓangaren basiru kuwa tun daga wannan ranar Abu yaketa bin duk hanyar da zata sadashi dashi koda suna tare da Meenal ne, ahankali sai shaƙuwa ta fara shiga tsakaninsu, basiru ya fara sakin jiki da Abu, bakomai yasa Meenal ƙyalesu ba sai fahimtar da tayi shima Abu ɗan masu farcen susa ne, ita haka kawai ma sai taji ya kwanta mata a rai, dan shima yaron babu laifi akwai kala.

          Yau ma dai tare suka fito yawo a motar Abu, danshi baseeru fa inhar bada Meenal zai fita ba koyaushe take bashi mota ba, hakan na ɓata ransa, balle idan ya kalli jibga-jibgan motocin meenal ɗin dake a harabar gidan, ɗan gidan gwamnatin ma ƙiri da muzu saidai taje ita kaɗai shi banda shi, kusan yanzu ma acan take yini ita. 

    Tunma yana nuna mata sha'awar son zuwa tana basar dashi harya haƙura ya ɗauke hankalinsa a wajen badan bayajin haushiba, sai dan kawai yana ƙaunartane da iya gaskiyarsa, sam bayason abinda zai ɓata ranta.

        Wani ƙaton boutique Abu ya kaisu na ƴaƴan manya, kayane na samari ƴan ƙwalisa masu shegen tsada da ƙyau, shi kansa Basiru saida ya rikice da wajen tamkar ba a cikin katsina ba.

       Duk yanda yaso karya ɗauki komai saboda tattalin arziƙinsa bai kaiba sai da Abu ya matsa masa, gudun kar Abu yay masa kallon raini bayan yaga gidan daya masa ƙarya matsayin nasa saiya biye masa suka ɗiba kaya sosai.

    Bayan sun kammala sukaje wajen biyan kuɗi, na Abu aka fara dubawa, ana faɗa masa ya miƙa ATM aka cire.

       Sai kuma oga Basiru, bayan ta kammala dubawa.

     Tace, “Kuɗinka 2.3m... Ne”

     Matar ta faɗa tana kallon basiru dake danna waya ya wani basar sai shan ƙamshi yakeyi, shi a dole babban yaro.

     Wani irin mugun wantsalawa hanjin cikinsa sukai, tuni zufa ta fara tsatstsafowa goshinsa, ya fara laluben aljihu cike da basarwa tamkar yana neman ATM.

     Zulfah dake laɓe tana kallon komai tai murmushin ƙeta tana fitowa cike da takun ƙasaita, ATM ta miƙama matar tana nuna mata kayan basiru,

    “Ki cire kuɗin kayansa”.

      “Ok ma” mai karɓar kuɗi ta faɗa tana karɓar ATM.

      Basiru ya kalli Zulfah yana wani cijewa, “Ji mana hajiya, bana buƙata”.

      Zulfah tai masa wani kallon raini ta cikin eyeglasess ɗinta baƙi dan tasan baya ganinta, sai dai kuma fuskarta ɗauke take da murmushi a zahiri. 

    Ko cikanka batace masaba ta karɓi ATM ɗinta tabar wajen tana ɗaga masa yatsu biyu alamar bye.

       Ƙafafunsa sunyi sanyi ƙalau tamkar an makesa, har Zulfah ta fice daga wajen.

    Abu ya matso kamar baisan komaiba yana faɗin, “Woow, wannan bab ɗinfa my man?”.

    Cike da basarwa basiru ya taɓe baki yana faɗin “ohoma ƴar wahala”.

       Dariya Abu yay a zuciyarsa, afili kuma yace, “Koma dai miye kaci banza, aiba kai kace ta biya makaba”.

     Tsaki basiru yaja kamar gaske, nanko a zuciyarsa jiyake kamar yafara taka rawa, “Kai nifa bazan ɗauki kayannanba, inma na ɗauka ƙyauta zanyi dasu”.

    “Ƙyauta kuma? Dan ALLAH karkayi haka abokina, ka saka abunka tunda dai mu muka zaɓa abinmu ai”.

     “shikenan, ammafa dan kaine zan saka, duk randa muka sake haɗuwa kuma zan bata kuɗinta”.

     “Yauwa to hakanma dai nake ganin zaifi”. Cewar Abu yana matse dariyarsa da ƙyar.

     Kayan aka fidda musu, Zulfah naganin sun fice ta fito ta dawo cikin boutique ɗin.

    Hannu ta bama matar suka tafa tana mata godiya, dama komai sunyisane cikin shiri, kayanma Abu ne yayta nuna masa wanda zai zaɓa bisa ga shirinsu.

    Godiya Zulfah ta sake mata ta fice.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


        *_KD_*


Idanu Dad ya kafe Attahir dasu kafin ya nisa yana gyara zama da maida hankalinsa ga Abba.

     “Humm Attahir kenan, bayan na koreka shine kaje ka ɗakkomin Aminina?”.

       Murmushi Alhaji Abubakar yayi, “To tinda anƙi sauraren buƙatar ɗana badole aje a kinkimoni ba Alhaji Mahmud ”.

      “Alhaji Abubakar ka barni da yarannan, yanzu shi Fodio har idonsa yakai tsaurin da zai aikomin Attahiru akan yasamu matar aure? Bayan kuma a gabanka ya watsamin ƙasa a ido? Toni minene nawa kuma yanzu Alhaji Abubakar?, tunda rayuwar da yaga ya zaɓama kansa kenan basai yayiba”.

      Cikin kwantar da murya Attahir yace, “Kayi haƙuri Dad, wlhy nima da farko naƙi saurarensa sam, amma fahimtar danai yana cikin damuwa sai naga ya kamata na sanar muku”.

      “Attahiru ka barsa ya dawwama cikin damuwarsa da....”

     “A'a ba ayi hakaba Alhaji Mahmad, Kayi hakuri dan ALLAH, Inaga mu ɗauki hakan matsayin ƙaddara kawai, tunda itama yanzu aurenta ma zatayi, tunda harya nuna auren yake sonyi mu sake bashi dama, yanzu dai ai zaɓinsa zai kawo”.

      “Alhaji Abubakar nifa nariga na zare hannu gameda auren Fodio, inhar zai tsufa a haka baiyiba ya rage nasa”.

       “A dai yi haƙuri, kai Attahiru a ina yarinyar da ya ke son take ne?”.

     “Wlhy Abba ban sani ba nima, dan yaki gayamin wacece yake son, duk sanda na tambayesa sai yace min koma wacece zan gani”.

     “Kaji ba Alhaji Abubakar, duk yanda kake zaton tsaurin idon Fodio ya wuce nan, yanzu haka ɗiyar dangin yarabawan ya sake kwaso muku?”.

      Murmushi Abba yayi yana faɗin, “Kai Attahiru tashi kaje, zuwa ƙarshen sati kuzo tare dashi idan zakazo amsar kuɗin su mai sunan Hajiya”.

     “To Abba godiya muke, Dad ALLAH ya ƙara girma, ayi hakuri damu dan ALLAH a gafarcemu”.

      “Yo Attahir da ba'a haƙuri daku ai da tuni kun shiga wani hali, ALLAH ya ƙara shiryawa”.

      “Amin” Abba ya faɗa.


    Bayan fitar Attahir Alhaji Abubakar ya kalli Alhaji Mahmud yana fadin, “Mu cire komai a ranmu dan ALLAH Alhaji Mahmud, mu ɗauki komai matsayin ƙaddara, kuma kaga bayan faruwar abun ya nuna nadamarsa, danma kaine kaƙi bashi dama da wlhy komai ya daidaita”.

       “Shikenan Alhaji Abubakar ALLAH ya shiryesa, amma maganar komai ya daidaita ma ai bata tasoba, yariga da yabar shirin tun rani, shima kuma yasan bana magana biyu, ba gashi ALLAH ya bata wanda ya fisa ba”.

     “Ba mace haka da sauri ba ai, tunda itama sai ƙarshen satin nan zasu kawo kuɗin nata, har yanzu bamuga wanene mijinba, duk da dai binciken Attahir ya nuna yaron mutumin kirkine”.

       “Alhmdllh, ai nama fiso tafara aure kafin shi yayi, dan sam banso maganar auren nasuma ya shigo kusan time ɗaya ba wlhy”.

    Murmushi Alhaji Abubakar yayi, “Aƙara hakuri damu dai to dan ALLAH, kasan ɗan nawane ɗan gado, sai dai shi harya zarta ne kawai”.

    Dariya sukayi irin tasu ta manya.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


      A ranar Attahir ya koma Lagos, dama kuma ranar yazo.

       Basu sami haɗuwa da Amaan ba sai dare, kaf yanda sukayi da Dad ya zayyane masa, buyagin da Dad yay masa naƙin saurarensa sam da farko, da Momcy ma ta saka baki wajen roƙonsa sai abin yaso dagulewa, sai da yaje yakira Abba sannan Dad ya sauraresu, “yanzu dai haka yace weekend ɗinnan mu koma, kasan nima zanje saboda kuɗin auren yarannan da za'a kawo gida”.

           A wani irin yanayi Amaan yake kallon Attahir, ya lumshe idanunsa ya buɗe yana turo iska ta bakinsa, “ALLAH ya kaimu”. ya faɗa da ƙyar’.

      Attahir yay ƴar dariya, “Nifa mamaki kake bani matuƙa gaya Ajiwa, wai kaine kake faɗin da bakinka kanason yin aure yanzu, tuzurancin ne ya isheka halan?”.

     Harara ya dallama Attahir yana ɗauke kansa.

     “Oh hararata ma kake? Ai na gama maka mai wahalar shiyyasa, amma gobema ai ranace”.

     “Ta jibima ta fita, dalla malam tashi kaje ka isheni da magana”.

     “Kutmelesy, Ajiwa ni ɗin? A lallai kaci abinci, wlhy zakasan dani kayi”.

    Murmushi ya saki yana kallon Attahir ɗin, har cikin ransa yana ƙaunar Attahir fiye da tunanin mai hasashe, yana jinsa matuƙa a cikin jikinsa da zuciyarsa matsayin ɗan uwa, amini na hakiƙa.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


           Tsakanin Ummukulsoom da A-Waheed kam yanzu kullum sai sunyi waya, duk dai hirar bata wani kirki akeba, yafi sakewa yay mata magana ta chart, ita da bata damu da charting ba sai yafara zame mata jiki yanzun, ga karatu yasha kanta sosai, saboda suna gangarar ƙarewa.

      Lamarin Umar ne kuma ke ɗaure kanta, yana gombe abunsa ya makale, koda yaushe sukai waya saiya ce mata wani uzurine ya riƙesa, abinda ta fahimta daga garesa dai kam akwai matsala, yana ɓoye matane kawai.

    Ƙyalesa tayi batare da ta takura kanta damuwar ta saniba, sai dai takan shiga damuwa idan ta tuna taya zata fuskancesa da zancen zata auri waninsa ba shiba.


★★★★


    Ranar juma'a sukai shirin tafiya kaduna su duka gidan har Zaid Kamar yanda Abba ya umarcesu, dan za'aje a amshi kuɗin auren su, kuma sosuke su dawo ranar lahadi da safe kodan makarantar Ummukulsoom da Ahmad.

      

★★★★


      “Big daddy!” Ahmad ya faɗa yana fincike hannunsa daga cikin na Ummukulsoom ya nufi Amaan dake fitowa a mota.

         Duk da Ummukulsoom ta fahimci wanene ko kallon wajen bataiba, ta cigaba da danne-dannenta a waya, saima masifa take da zuciyarta akan shikuma waya gayyacesa?.

   Ko da yake ita hakanma ya mata daɗi, ai koba komai zaisha takaici, dan ta ɗauki alwashin saita ƙunsa masa ƙaton haushi, harma Abdul-Waheed zata gayyato ta kaisa har gidansu.

        Shima dai kallo ɗaya yay mata ya janye idanunsa, ko a jirgin ma can nesa dasu ya zauna.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡


        “Alhaji Mahmud nadai sake dawowa”.

     Dad ya kalli Alhaji Abubakar yana murmushi, “To ALLAH yasa ƙyauta kazo kaimin”.

      Dariya Abba yayi, “indai ƙyautace karka damu zan maka da wata bazawara”.

     “A lallai ka iya ƙyauta, amma a wannan shekarun ina mu ina wasu mata, waɗan nan dai sun ishemu ai karasa gwagwarmayar rayuwa”.

       “Gaskiya kam. Akan maganar ɗana ne na dawo, yau kasan zasu iso insha ALLAH, ni aganina tunda har sun bashi izinin tura magabatansa kawai gobe idan ALLAH ya kaimu bayan an amsa na ƙannen nasu kawai sai mukai nasa dana zaidu ko”.

       “Da wuri haka Alhaji Abubakar? Aini sonake ku barshi ya wajigu harma ayi bikin ƴata sannan”.

    “A'a ba'ayi hakaba Alhaji Mahmud, mudaije a ajiye magana, wataƙilama su basu shirya anan kusaba, suko mai sunan hajiya banaso ya wuce wata ɗaya wlhy, tunda kaga wata ɗaya dawasu kwanakine suka rage mata ta kammala karatunta”.

       “To ai ni banida ta cewa tunda ka ɗaɗɗaureni da jijiyar wuya mai ɗa, ALLAH ya kaimu goben”.

    “Amin ya rabbi, nagode sosai”.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


      Koda suka iso kd Amaan isa ne yaje ya ɗaukesa ya wuce gida dashi, sukuma su Attahir Ummi ce da kanta taje ta kwasosu tare da direban Hajiya yaya.

     

     Yau dai kam gida ya kacame da hayaniya, masu shi sun raya shi, adaren sukaje gidan Hajiya yaya, gwaggo hinde ma tana nan dan Hajiya yaya tace bata barinta ta koma, sai dai su ringayin watanni anan kaduna, suje ɗilau ma tare.

    To bayan su Ummukulsoom sun baro su Hajiya yaya acan da ta tashi tahowa sai suka kuma dawowa a tare nan kd, bayan tayi kusan wata uku a ɗilau.

       Basu baro gidan Hajiya yaya ba sai kusan sha dayan dare, suna dawowa gida kowa ya gaji, ma kwanci duk suka nema.

      Cikin barcin da Ummukulsoom ta farane taji wayarta na ring, ɗagawa tayi dan tasan bazai wuce Abdul-wahed ne ba mai kiran.

     Ilai kuwa shine,  Sallama tayi cikin yanayin barci.

    Da ƙyar ya iya controling kansa ya amsa mata, dan gaba ɗaya muryar tata tayi mugun saukar masa da kasala.

     Murya can a ƙasan maƙoshi yace, “har kinyi barcine?”.

      “Eh wlhy. kasanfa a matukar gajiye nake da tafiyarnan”.

       “Lallai ke dai raguwa ce, tafiyar mintuna zuwa awa ɗaya kikema raki”.

     “ALLAH bazaka ganeba”.

         Guntun murmushi yayi daga can, “Ok ki kwana lfy”.

       “Kai sai gobe zaka iso kenan?”.

     “Jirgi ɗaya muka hawo ma” ya faɗa ƙasa-ƙasa.

   Hakan yasa Ummu batajiba, tace, “Kace mi?”.

      “Kinga yi barcinki”. Yay maganar yana yanke kiran.

      Baki ta taɓe kawai ta tura wayar ƙarkashin filon ta gyara kwanciyarta.



*_Washe gari_*


     Tunda suka karya basu zaunaba, gyaran gidan suka farayi aka shiga haɗama baki ɗan abun motsa baki mai sauƙi.

    Da yake suna da yawa dandanan suka kammala komai kowa yay wanka aka zauna zaman jiran isowarsu.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


         “Ni dai Fodio dan kakine kawai, amma yarinyar nan ta gidan Alhaji Abubakar nai maka sha'awarta, to kai matsalarka babu mai tanƙwaraka ne”.

       Fararen idanunsa ya ɗago ya kalleta, “Momcy itama wannan ɗin zaki sota ne”.

      “ALLAH yasa, nidai fatana kar a daɓa irin aurenka na farko”.

    Bai ce komaiba dukda sarai ya jita.

        “Kanajina fa ina magana”.

      “To ni Momcy mizance”.

    Harara ta zabga masa, kafin tayi magana Dad ya sakko cikin shirin tafiya gidansu Attahir.

    Kallo ɗaya yayma Amaan ya ɗauke kansa, “Saika turama babanka Abubakar adress ɗin gidan yace”.

    Kansa a sunkiye yace, “To Dad nagode”.

       Banza Dad yay masa ya fice abinsa, Hajiya Jamila ta taɓe baki tana mikewa tabi bayansa.


     Koda ta dawo daga rakiyar Dad ta dawo falon saita iske Amaan ya gudu.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


             Ƙarfe sha ɗaya da wasu mintuna iyayen Muhseen suka iso, tarbace ta mutunta juna ta gudana a tsakaninsu, abinka da manya dattijan ƙwarai, komai ya gudana cikin aminci, babu wani ja'inja aka tsaida ranar ɗaurin aure jin a shirye suke tsaf, dan atake anan suka bada har sadaki.

      Hakan yayima kowa daɗi, aka rabu cikin sambarka, sai kuma iyayen Abdul-Waheed ake jira.

     Kusan minti talatin da tafiyar iyayen Muhseen amma shiru babu labarin magabatan Abdul, hakanne yasa Abba kiran Ummukulsoom ta kira Abdul a waya ta bama Abba, itako ta samu gudu daga falon.

        Duk zubama Abba dake waya da Abdul-Waheed akayi kowa nasonjin mike faruwa............✍🏻 



NO. 40



..........Abba ya ajiyev wayar yana sauke numfashi, taajiyevxfaɗin akira Ummukulsoom ta shigo da Abdul-Waheed dake a ƙofar gida.

    Itace ta fita tai masa jagora suka shigo, sai dai haka kawai ta tsinci kanta cikin matuƙar sanyin jiki, bayan sallama da gaisuwa babu abinda ya sake shiga a tsakaninsu har suka shigo yana biye da ita.

     Tunda ya shigo falon Dad da Attahir suka zuba masa ido, yayinda Abba shi sam bai kawo komai a ransa ba ya nuna masa wajen zama.

      Abba zaiyi magana Dad ya katsesa cikin tsantsar takaici da ɓacin rai.

       “Kai kaine Abdul-Waheed ɗin?”.

      Cikin mamakin furucin Dad Abba ya kallesa, “Eh wannan shine kam nake gani, dan dashine mukai waya, ke Ummukulsoom ai shine wanda kuke taren ko?”.

    Kan Ummukulsoom a ƙasa ta ɗaga kanta alamar eh.

      Ƙwafa Dad yayi, cike da kakkausar murya yace, “Fodio kai ƙaramin mara kunya ne, tunda iya fuska ka iya canjawa banda gangar jiki, wato ni ban isaba ko? Shine ka koma ta bayan fage kana yaudararta......”

       “Alhaji Mahmud wai mike faruwa? Wannan fa Abdul-Waheed sunansa ba Fodio bane ba”.

    “Humm Alhaji Abubakar kenan, idan ya gama raina muku hankalin sai ya cire Mask ɗin fuskarsa”.

    A matuƙar firgice Ummukulsoom ta kalli inda yake zaune kai a sunkuye, hakama Abba, Attahir kam da tun shigowarsa ya ganeshi takaicine kawai ya gama kumesa, sai dattijai biyu maƙwaftan Abba suma dai abin ya zame musu kamar almara, dan basu fahimci komaiba”.

        Abba ne yace, “Kai ba kace sunanka Abdul-Waheed baneba yaro?”.

      Hannu yakai saman fuskarsa, jiki a matuƙar sanyaye ya zare facemask ɗin da ya sanya, ainahin fuskarsa ta *_USMAN MAHMUD USMAN AJIWA (Amaan, fodio)_* ta bayyana ga kowa.

     Gaba ɗaya Ummukulsoom takasa koda motsi daga inda take a durƙushe, sai kafesa tai da idanu tamkar wani butun butumi.

     Attahir kam kallo ɗaya yay masa ya ɗauke kansa cike da tsantsar mamakinsa, sai maimaita sunansa yake a cikin zuciyarsa tamkar ya samu karatu.

        Abba ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya yana kallon Amaan baki buɗe, “Fodio da kanka wannan aikin haka? Minene amfanin hakan ko ma'anarsa?”.

      Jijiyoyin kansa sunyi ruɗu-ruɗu, hakama idanunsa jajur suke alamar tsantsar damuwa, ya ɗago ido a hankali ya saci kallon Dad, kafin ya maidasu ya risinar yana faɗin, “Abba ku gafarceni, banida wata mafitar data wuce hakan........”

     Cikin katsesa Dad yace, “Tashi kabar falon nan dan ubanka, inba hakaba duk abinda yazo harshena na jefeka dashi wlhy kaine kaja, mara mutunci kawai”.

     Saurin riƙe hannun Dad Abba yayi, “Alhaji Mahmud Please Calm down, mubi komai a sannu dan ALLAH, shima ƙila akwai tashi hujjar....”

    “Hujjafa kace Alhaji Abubakar? Usman bashida wata hujja, kuma koda yana da ita shi yasan har abadan bazata karɓu a wajena ba, wlhy kuma kai masa gargaɗi ya fita a idona, idan yabari nakai bango akan maganarsa da Ummukulsoom narantse da ALLAH har abada bazan sake waiwayarsa ba...”.

    Yana gama faɗa ya tashi ya fice yabar falon.

      Kowa kasa koda motsi yay a cikin falon, Amaan kam yay ƙasa da kai kawai ya kasa koda numfashi mai ƙarfi balle kallon wani.

      Attahir ya fara farga da Ummukulsoom bata a cikin hayyacinta, ya miƙe da sauri zuwa gareta, yana taɓata ta zube a wajen alamar numfashinta baya tare da ita.


    Kafin kace mi komai ya kuma rikicewa, Ummi ta duƙufa akan Ummukulsoom, gaba ɗaya hankalin kowa a tashe yake, musamman Yaa Amaan daya kasa zaune ya kasa tsaye. da ƙyar aka samu numfashin Ummukulsoom ya dawo, sai dai fa dole akai mata allurar barci.      


★★★★


       “Wannan ranar itace naita jiye maka Ajiwa, amma sam sai kaƙi saurarena, saboda shaiɗan na ɗoraka akan kekem ɓera, a zatona aure ya wuce abin wasa a garemu, musamman daya zam wannan wata babbar ƙyautace daga iyaye.

     Bansan dalilinka na dawoma Ummukulsoom ba a karo na biyu matsayin wani, sannan bansan dalilinka na bibiyar rayuwarta ba, sai dai abinda zan sanar maka duk wanda ya baka gurguwar shawarar sakin Ummukulsoom da dawo mata ta wannan hanyar to lallai bai baka ƙyakykyawar shawara ba, dan koni nan bazan taɓa amince maka ba, wannan alwashinane”.

        Attahir na gama faɗa ya barsa tsaye a harabar gidan ya koma cikin gida inda kowa yake jigum-jigum akan lamarin Ummukulsoom.


      Hajijiya yaji tana ɗibarsa, yay saurin dafe motarsa yana sauke wata irin sarƙaƙƙiyar ajiyar zuciya, kansa yay masa jingim, babu wani abu da yake fahimta a halin yanzu, dama yasan dolene wannan ranar tazo kamar yanda Attahir ya faɗa, sai dai sam baiyi tunanin zatazo a juye baneba...

     Mota ya shiga ya tuƙa kansa, ALLAH ne kawai ya kaisa gida lafiya amma badan yasan a wanne yanayi yay tuƙinba.

    Ameer ne da suka shigo kusan tare yazo ya fiddashi daga moto ɗin ganin halin da yake ciki.

    Hannu ya ɗagama Ameer alamar ya barsa kawai, Ameer baiyi musu ba ya sakesa, da kansa ya taka zuwa sashensu Momcy, ba tare da ya amsa gaisuwar su Buhayyah da Bassam dake falon ƙasa ba ya haye sama.

   Da kallo suka bisa kowa baki a hangame, dan sun gansa tamkar baya cikin hayyacinsa.

      Falon Dad ya nufa, Dad dake zaune rai a ɓace ko kaya bai sauya ba yay masa kallo ɗaya yana ɗauke ido. “Usman karka shigo min nan”.

    Cike da mamaki Momcy dake fitowa daga bedroom ɗin Dad tace, “Miya farune Abban Fodio?”.

      Wani banzan kallo ya watsa mata yana ɗauke kansa kafin ya miƙe tsaye hannunsa goye a bayansa.

     “Kamar yanda na alƙawranta ma kaina hukuntaku a yau zan cika insha ALLAHU, Usman badai umarnin wannan yasaka bijirema nawa ba? To ta tattara ta barmin gidana itama, ince dai shikenan, jamila kije na sakeki saki ɗaya.....”

     Ƙara mai ƙarfi da razanarwa Momcy ta ƙwalla.

     Fodio kam tun yana fahimtar kaɗawar iska har komai ya fara masa nisa a kunne da ƙwaƙwalwa da zuciya, a hankali yaci gaba da tsintar kansa a wata duniya dake da banbanci data mutane.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

    

        Komai fa ya dagule musamman a gidansu Amaan, dan bai tashi buɗe idoba sai a ɗakinsa, baisan ya ya akai yazoba, miya biyo baya bayan furucin Dad akan Momcy da shuɗewar abubuwa daga jinsa da ganinsa tare da fitar numfashinsa.

      A hankali ya buɗe idanunsa da sukai nauyi jingim ya saukesu akan Momcy dake zaune gefen haggunsa tana ta faman sharce ƙwalla, sai Buhayyah da Bassam da Ameer daga gefen damarsa suma da alama kukan suka sha, sai Ummayya a kusa da ƙafafunsa itama tana nata.

   Idanunsa ya maida ya lumshe a hankali ƙirjinsa na sake ɗaukar nauyi sosai. Kukan Momcy yafi komai sukar zuciyarsa, yau shine yazama silar guntile igiyar auren iyayensa guda ɗaya bayan kusan shekaru talatin da takwas da ƙullata, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, shi Usman Mahmud ne dai sila da gaske? Sam bai taɓa tunanin Dad ya ɗau zafi har irin hakaba akan lamarin.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


          Ummukulsoom ma dai sai yamma liƙis allurar da Momcy tai mata ta saketa, sai dai abinda zai baka mamaki gaba ɗaya hawaye sun ƙafe a idanunta, sam taƙi kuka alamar zuciyarta a dake take.

    Koda Maman Ahmad ta kawo mata kunun gyaɗa da Momcy tasa aka dama mata karɓa tayi tasha abinta, sannan bily ta haɗa mata ruwan wanka mai ɗan ɗumi. Bayan tayi wankan kaya kawai ta canja ta koma ta ƙwanta, dan tana fashin salla.

     Anan kam hankalinsu yaɗan kwanta ganin Ummu tana cikin nutsuwarta, sai dai halin da Amaan yabar gidan shida Dad yasaka su a cikin jin nauyi.

     Da daddare Zaid yakai Abba gidansu Amaan, dan yanason suyi magana ta fahimta da Dad, amma saiya iske babban tashin hankalin da yafi na farko. Sakin Momcy da Dad yayi, sannan yama bar gidan babu wanda yasan inda ya tafi, saboda harda kaya ya ɗauka.

    Sai kuma Amaan da kowa ya rasa gane kansa a gidan, yaƙi magana ma kowa, sai dai kallo ɗaya zaka fahimci yana cikin matsala ta ciwo da babu wanda yasan na miye. Doctor dai yazo ya saka masa ƙarin ruwa wanda da ƙyarma ya amince aka saka masa.


★★

          Wannan yini dai na Asabar a rashin daɗi jama'ar waɗannan gidaje biyu suka yisa. Shirin da akayi na farin ciki saiya juya zuwa wani al'amari mai rikitar da zuciya da walwala.

     Kowa ya kasa fahimtar dakewar Ummukulsoom, dan sam taƙi nuna abin ya taɓeta a rai, ko shigarta ruɗani bayan ta fahimci Abdul-Waheed shine Amaan, shine yaketa yawo da hankalinta a kusan tsawon watanni bakwai da suka gabata.

       Babu wanda ya matsa mata da tambayar komai a kaf gidan, sai dai kowa kaffa-kaffa yake da ita, musamman ma Attahir da yafi kowa jin zafin Amaan.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡            


       “Wlhy Basiru yau saika sanar min inda ka samu kuɗi har ka sai waɗannan kayan masu tsada haka”.

      Ransa ya kai ƙololuwar ɓaci da Meenal yau, ya ƙura mata idanun sa da sukai jajir saboda cin kashin da take masa tun shekaran jiya akan kayan da suka siyo shi da Abu.

      “Wai Meenal wane irin rainine a tsakanin mu har haka? Ya kullum ina miki abu dan gudun ɓacin ranki amma ke sam baƙya ganin hakan, ni banida hurumin sayen abu sai kinbi ƙwaƙwƙwafina....?”

      “To ya bazanbi ƙwaƙwƙwafin kaba tunda nasan bakada kuɗin sayen abun, idan har ba kuɗina ka ɗiba ba ta ina kake da kuɗin sayen waɗannan kayan masu tsadar tsiya da kaketa sakawa?”.

     “Meenal! Ni kike faɗa ma wannan maganar? Ni ne zan miki sata?”.

    “To waya sani abu a duhu”. ‘ta ƙare maganar da murguɗa masa baki tana dalla masa harara, ta bar wajen’.

     Ko motsi kasa yi yayi, sai ma mamaki dake ƙara girmama a zuciyarsa akan lamarinta, wato dai su mata zumane sai da wuta, ɗaga mata ƙafar da yay tun farkone yajawo wannan rainin a tsakaninsu, yau harshi mace ke kira da ɓarawo dan kawai ta gansa da kaya masu nauyin kuɗi. Da ƙyar yaja ƙafa yakoma saman kujera ya zauna, dan ita meenal tama daɗe da barin gidan.

         Tunda suka dawo Nigeria kamar itace mijin, kullum bata yini a gidan tana gidansu na gwamnati, idanma bata gadama ba saitai kwana biyu acan. Shine ke yini a gida, saboda iskancin tama kulleshi take a gidan, ta wata dabara yake samu ya fita kullum batare da ta saniba. Ko kaɗan bai taɓa zaton haka meenal takeba sai yanzu, dan a tsawon shekara biyar da sukayi a paris babu wannan rainin mai tsanani irin haka a tsakaninsu, duk da dama takan masa wasu abubuwan marasa da ɗi yana shanyewa ne tun suna can.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


          A kwanaki biyunnan misalta tashin hankalin da gidansu Yaa Amaan suke ɓata lokacine.

    Tashin hankali uku ya taso Momcy, barin Dad gidan, sannan duk inda ake tunanin samunsa abun ya gagara, ya kashe wayoyinsa gaba ɗaya.

    Sai sakin da yay mata wanda ko a mafarki bata taɓa tunanin hakanba, duk iya shegen da take masa tun sunada ƙuruciya bai taɓa kwatanta hakanba sam, sai dai yace taje gida ta huta, amma sai gashi yau da rana tsaka, da girmansu ga jikoki ya yanke igiya ɗaya acikin igiyoyin aurensu. 

    Sai damuwar da Fodio yake ciki, wadda ta tabbata itace tushen komai, laifin ta yafi na kowa yawa akan kuskuren daya tafka, duk tunaninta yarinyar ƙauye ta koma tai aure, ashe tana nan tana karatunta a kusa dasu batare da tasaniba, ashema tanada alaƙa mai ƙarfi dasu, ashema ahalinta sunfisu komai, wannan wane irin murɗaɗɗen yanayine ya riskesu a lokacin da basuyi zatoba.

     Ita kanta kwance take rijif babu lafiya, hakan yakuma tada hankalin iyalansu, dan duk yaran suna gida har aunty Nurse da aunty Ummi.

      

        Baya yima kowa magana a gidan, bawai dan miskilanci kawai ba ko jin haushin wani, a'a tsantsar damuwace tattare dashi, ta sanadinsa komai ya rikice a gidansu, kullum cikin yawon neman Dad suke shida Attahir da Ameer da Zaid.

     Abinda ya kuma dagula masa lissafi shine sam Attahir baya ko kallonsa, bayan iyayensa bashida kowa da yake iya sakewa dashi sama da Attahir, Attahir yasan cikinsa fiye da kowa a duniya, shike saukar dashi idan ya ɗau zafi, ya sashi farin ciki idan ya tsinci kansa a damuwa, ya share masa hawaye a lokacin da yaga idaniyarsa na kawo ruwa, amma sai gashi a yau sam baya ko kallonsa, ya juyama komai nasa baya, ko a neman Dad ɗinnan yini suke bakinsu bai saɓa da juna ba. Dama shi inba Attahir ɗinba ba doguwar magana yake da wani ba.


      Yau data kasance rana ta huɗu da faruwar komai Abba ya hasaso inda Dad yake, ya tabbata bayan nan babu inda Alhaji Mahmud zaije kuwa.

     Bai sanarma kowa ba ya saka Attahir tuƙasa suka nufi Ajiwa.

    Ilai kuwa Dad yana a can hankalinsa kwance, koda yaga Alhaji Abubakar sai ya kuma ɓata fuska.

     “Alhaji Abubakar! Karka roƙeni akan abinda bazan iya maka shiba dan ALLAH”.

       Murmushi Abba yayi, “Alhaji Mahmud kenan, ka kwantar da hankalinka bazan roƙeka ba, kamar yanda bazan maka tilas ba, amma sai daifa ka sani, barinka gida ba shine mafita ba, dan ba duka ahalin gidan sukai maka kuskure ba, aganina ka hukunta masu laifin, to mizaisa sukuma sauran kai musu hukunci da ƙaurace musu, nasanka da saurin fushi, amma kai mutum ne mai haƙuri da kawaici komai zafi da yay maka, sam banyi zato daga gareka ba zaka aikata ɗanyen aikin datse igiyar aurenku da hajiya Jamila, da kayi shawara dani dabaka aikata hakanba, mu manyane yanzu Alhaji Mahmud, mun wuce ajin yin hallayar yara ai, dan ALLAH ka tashi mu koma gida, kakuma janye sakinnan, gara kai mata hukunci da wani abun amma ba wannanba....”

      “Alhaji Abubakar bazaka fahimci ƙunar da nake jiba akan lamarin nan, nifa nabama Fodio dama tafi shurin masaƙi akan ya fidda matar aure amma yaƙi, nazo na shige masa gaba akan yarinyar nan da ALLAH yayma rasuwa, ALLAH baiyi zasu rayu matsayin ma'aurata ba ta rasu, kai shaidane nabasa lokaci yakuma hutawa sannan na tuntuɓesa akan batun aure, amma ya nunamin shi bai samu ba, kafin na aura ma Fodio Ummukulsoom saida na sanar masa fa, dukda na isa dashi amma na fita haƙin yaron nan, yakuma cemin ya karɓa, ka tuna ko ɗaurin aurennan zamewa yay yaƙi zuwansa, nakuma barsa duk dan dai a zauna lafiya, na kuma karya ƴancina na ɗauki yarinyarnan da kaina nakai masa har inda yake, yakuma nunamin ya amsa hannu biyu, amma saboda banida daraja a idonsu shine ita ta sakashi ya saketa”.....

     “Alhaji Mahmud ban katseka ba, amma dai karmuyi zargin ita ɗince, ƴaƴane na yanzu ka haifesune baka haifi halinsu ba....”

      Murmushi Dad yayi mai ciwo, “Alhaji Abubakar Jamila itace ta sakashi sakinta, duk da dai shi yaƙi sanarmin gaskiyar abinda ya faru, amma ni na bibiyi komai naji yanda yake, Fodio yanada wani hali na shanye damuwa komai ƙuntatashi da zatayi, ni kaina ba kasafai nake fuskantar damuwarsa ba kai tsaye saina nutsu akan lamarinsa, sannan kaga maganar sakinnan, koda zata kasheshi arai bazai faɗin ainahin abinda ya faru ba da bakinsa, bakomai zai sashi yin shirunba sai dan kar mahaifiyarsa tai baƙi a idona, wannan ne yasa na biyo masa ta bayan gida ai na saketan a gabanshi, kuma dama nayi alƙawarin yanda ta sa ya saki Ummukulsoom itama sai ta ɗanɗani wannan tabon taji inda daɗi, karka ɗauka Ummu ce kawai ke fuskantar wannan bakin halin na jamila, yanzu haka matar Ameer cikin wannan ƙangin take, yarinyar sam bata sakewa a gabanta, shi Fodio zai iya mata kawaici ne, amma Ameer bai iyayi saboda kaf halayyarsa irin tatace, shiyyasa ma bata isa sakashi rabuwa da matar tashiba ko ƙuntata mata, narasa wannan wane irin banzan kishine, ita wanene ya sanya mata ido a nata lokacin? Sannan itama fa tanada ƴaƴa matan a gidan wasu, rayuwar da Jalilah tayi a gidan miji kaɗai bata isa zame mata izina ba ashe? Ka barsu Alhaji Abubakar, sai Fodio ya magantu da bakinsa ya sanarmin miya faru sannan”.

        “Humm sam dai abin baiyi daɗi ba, sannan bata ƙyautaba itakam, dan wannan rayuwace irinta jahilci, duk sonka da ɗanka dolene kabarsa yayi aure, tunda ba kaine zaka auresa ba, amma dan ALLAH kayi haƙuri mu koma, komai fa ya birkice fiye da tunaninka wlhy”.

      “Ka barni kawai anan Alhaji Abubakar, sa gaji su daidaita ne”.

     “Dan ALLAH kar muyi jayayya dakai Alhaji Mahmud, muje koma mi za'ayi sai ayisa a can”.


     Badan Dad yasoba ya kimtsa suka dawo KD a ranar.

      Duk da ya iske dukan iyalan nasa a gida bai kalli kowa ba ya shige ɗakinsa ya sharesu. Har washe gari basu sake ganinsa ba, sai da rana da Abba yakuma zuwa gidanne ya lallaɓashi ya fito falo da ƙyar.

       Babu abinda su Aunty Nurse sukeyi sai kuka da roƙonsa akan yayi haƙuri ya maida mahaifiyarsu.

    Itama kanta hawayen take, dan tama kasa zuwa gidansu ta sanar, amma Abba yaje yay musu bayanin duk abinda ke faruwa akan lamarin, sunkuma ce babu abinda ya damesu, Dad yay musu dai-dai da hukuncinsa, dama saki Ukun yay mata lokaci ɗaya.


      Gyaran murya Dad yay fuskarsa a matuƙar ɗaure, ya sauke kallonsa akan Yaa Amaan da tunda ya shigo falon kansa a sunkuye yake shi kam, duk ya zabge a tsaye, sai haske daya ƙara yay fayau, “Kai da kai zan fara Fodio, kamar yanda mukai dakai a shekaru biyar da wasu watanni da suka shige yanzu zuma shine zan maimaita, inhar wannan matsalar kana buƙatar ganin ƙarshenta to saifa ka sanarmin dalilinka da kuma ainahin abinda ya faru da har ya saka sakin Ummukulsoom, inba haka ba kuwa, hummm”.

       Hankali Momcy yakuma matukar tashi, sai zufa take zabgawa dukda kuwa AC na aiki a falon, ta raba hankalinta biyu wajen kallon Alhaji Mahmud da kuma Fodio.

      Har yanzu kan Yaa Amaan a ƙasa yake, sai da yaja kusan minti ɗaya sannan ya ɗago ya kalli Dad, idanunsa sunyi jajur matuƙa gaya, jijiyoyin kansa kam sunyi ruɗu-ruɗu, da ƙyar ya buɗe baki yace, “Dad ka gafarceni, a duk duniya ina ƙaunar abu biyu fiye da kaina, ina girmama abu biyu fiye da buƙatuna, zan iya sadaukar da komaina saboda abu biyu kuma. Ba komai bane abunnan guda biyu Dad sai kai da Momcy, kamar yanda na roƙeka da farko Dad akan kabar maganar nan a yanzuma ina ƙara roƙonka, dan girman ALLAH abar maganarnan, ka ɗauka ƙaddara ce kawai ta katsa igiyar aurena da ita”. ‘Ya ƙare maganar da dafe kansa da yakejin ya masa nauyi kamar zai tsage gida biyu’.

      Murmushin takaici Dad yayi yana miƙewa, “Kamar yanda ban canja ba a shekaru shida da suka shuɗe a yauma bazan canja ba Fodio, daga yau inhar ka kuma bibiyar Ummukulsoom AL........”

      “Alhaji Mahmud karka ƙarasa dan ALLAH”.

    Abba dake shigowa shida Ummi ya faɗa da sauri.

    Kallonsa Dad yay ya ɗauke kai, “koda ban ƙarasa ba ya tabbata na masa katanga da ita na har abada”. ‘Dad yay maganar yana hayewa samansa’.

     Da kallo duk suka bisa har Fodio dakejin falon na fara juya masa, miƙewa yay dafe da kansa yana haɗa hanya tamkar mashayin giya.

     Ƙarar zubewarsa a wajen ce ta maido hankalin kowa na falon kansa a matuƙar tashin hankali.............✍🏻


NO. 42



..........Duk yanda taso ture tunani kada yay tasiri a ranta hakan ya gagara, har suka kwanta barci sukuku take, ga karatun exam ma kansa ta kasa yau.

         Bily tsaf ta gama fahimtar damuwarta, amma sai batace mata komaiba akan hakan.

    Da safe ko breakfast batayiba ta wuce school, ta samu damar zana jarabawar ne cikin ikon ALLAH kawai, amma ita kanta tasan badan tana tare da nutsuwarta bane.

     Tana fitowa kira na shigowa a wayarta, ta fiddo wayar ta duba, baban tane, murmushi tai sannan ta ɗaga suka gaisa, ta tambayi lafiyar kowa dake gidan.

   Baba yace kowa lafiya lau, sai shirye-shiryen bikin wasu ƙannensu da akeyi.

   ALLAH ya sanya alkairi tayi, da fatan ALLAH ya kaimu lokacin. Sun daɗe suna hira da baba, wadda sam ban fahimci kanta ba, amma nutsuwar da Ummukulsoom tayi tana saurarensa ne zai baka damar fahimtar maganar mai muhimmanci ce a gareta, harda ƴar ƙwallarta kuwa.

     Ko minti biyu batai da yanke wayarba wani kiran ya sake shigowa, ba tare da ta fahimci waneneba ta ɗaga, dan duk zatonta cikin ƴan uwantane na ɗilau.

   Jin muryar babbar mace tai sallama saita nutsu, ta gaisheta cike da girmamawa.

     Daɗi Momcy taji sosai, ta kuma kwantar da murya wajen kiran sunan Ummukulsoom.

    A sanyaye Ummu ta amsa, dan zuwa yanzu ta tsargu da muryar Momcy.

      “Ummukulsoom nasan ba lallai ki saurareni ba, bakuma lallai ki yafeminba nida zuria ta, sai dai hakan bazai hanani roƙonki ba, dan ALLAH ki yafe mana abinda muka aikata a gareki, son zuciyane kawai ya lulluɓe ganina har nake hasashen akwai wani fifiko tsakanin wanda yake dashi da wanda bai dashi, sai dai sam ba haka baneba, jahilci ke saka ɗan adam wannan tunanin da rashin hangen nesa, dan babu wanda yasan gobe sai ALLAH. Da UBANGIJI yaso sai yayi mu iri ɗaya, jinsi ɗaya, yare ɗaya, addini ɗaya, koma duk yayomu mutane, ko dabbobi, ko aljanu, ko itace, ko ruwa. Amma domin saukar da aya agaremu sai ya banbantamu, mutane, aljanu, dabbobi, da wasu halittu dakan zama yankin jin daɗin ɗan adam ko akasin sa, akowace hallita saika samu mace da namiji, wannan rahama ce ta Ubangiji da jin ƙansa. Ba'a dukiya ake gane wanda ALLAH yafi so ba, ba'a ilimi ake gane wanda ALLAH yafi soba, ba'a ƙyawun fuska ake gane wanda ALLAH yafi soba, ba'a ƙyawun nasaba, ko yare, ko jinsi, ko yanki ake gane wanda ALLAH yafi soba, a tsoran ALLAH ne. ALLAH kuma shine kaɗai ke iya banbanta mai wannan zuciyar a wannan duniyar. Zakiga mutum mummuni amma tsiyar da yake tafkawa ko shaiɗan zai shafa masa lafiya, kiga mutum mai addini da yawaita faɗar ALLAH abaki amma shiɗin wakilin shaiɗanne. Wlhy Ummukulsoom nayi nadama irin wadda harshena bazai iya fassarata ba, bakomai yasa hakanba sai ikon da ALLAH ya nunamin akanki, ni na haifi Fodio da cikina, dukda banice na raineshi ba yana ƙarami wlhy nasan halinsa ciki da bai, duk damuwar da Fodio zai yarda wani ya ganta a saman fuskarsa to ki tabbata ba ƙaramin so yakema wannan abunba kuwa, dan ALLAH ki tausaya min, badan na isaba ki karɓi ƙoƙon bararmu a matsayinki na musulma mai zuciyar tausayi da adalci, karki kallemu acikin mutane masu son kansu da yawa, Fodio yana cikin wani hali akanki da fushin da mahaifinsa yakeyi dashi wanda ke kaɗaice mabuɗin warware kowanne sirri ɗiyata, dan ALLAH ki dubemu karmu rasa Fodio. ciwo sai fyaɗarsa yake a tsaye, dan ALLAH Ummukulsoom......”

      Hannu Ummukulsoom tasa ta share ƙwallar data cika mata ido, sosai taji tausayin Momcy irin wanda bata taɓa jiba, kamar ba Momcy ɗinnan bace maiji da kanta, mai tinƙaho da arziƙi, mai kallon na ƙasa da ita abin ƙasƙantarwa, lallai ta yarda Momcy nasan yaa Amaan over.....

     “Ummukulsoom dan ALLAH kinji”. Magar Momcy ta dawo da ita hayyacinta.

      Cikin kwantar da murya mai alamar jin kunya tace, “Wlhy ban taɓa riƙekiba a raina Momcy, kumani na yafe miki, nima ki yafemin dukkan kuskuren dana taɓa miki, da sanina ko akasin haka, dan har abada bazan taɓa daina miki kallon uwa ba, ƙyautatawar Dad agareni ta kore dukan komai na taumashe a zuciyata tunba yanzu ba, ALLAH ya yafe mana baki ɗaya”.

    “Amin ya rabbi Ummukulsoom nagode kinji, ALLAH yay miki albarka, yasa ki gama da duniya lafiya da iyayenki, ALLAH yayta ɗora rayuwarki akan nasara har gaban abadan kinji”.

     “Amin ya rabbi Momcy nagode sosai”.


      Har Ummukulsoom ta dawo gida waɗannan wayoyi biyu sun kasa barin zuciyarta da dukkan fitar numfashinta.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


          Kwanaki biyu dayin haka ranar alhamis daren juma'a suna zaune a ɗakinsu maman Ahmad tazo ta kirasu ita da Bily.

     A falo suka iske Attahir, dama sanin yana gidanne yasasu zamansu ɗaki dansu bama yayansu damar warwasawa ya huta da iyalinsa.

     Zama sukai suna gaidashi, ya kallesu fuskarsa washe da murmushi, “Autocin Ummi kenan”.

   Murmushi duk sukayi kowacce na jin daɗi har cikin ranta.

     Attahir ya katse musu tunani da faɗin, “Ummukulsoom ALLAH yay miki albarka, kin nunawa duniya lallai keɗin ƴar halak ce ta ƙwarai mai girmama alkairi da ƙyaƙyƙyawan tukuyci”.

     Kan Ummukulsoom a ƙasa batace komaiba, Bily kuma sai kallonta take dan bata fahimci komaiba akan maganar.

     Attahir yaci gaba da cewa, insha ALLAHU gobe ƙarfe biyar na asubahi zamu wuce kd, saboda asabar zamu dawo insha ALLAH, na bincika bakida exams gobe idan ALLAH ya kaimu kwata-kwata ko Ummukulsoom?”.

    “Eh yaya, banida ita sai Monday insha ALLAHU”.

    “To ALLAH ya kaimu, kuje abinku dama kiran kenan”.


     Koda suka koma ɗaki sai tunanin mizasujeyi sukeyi. amma sam basu hasaso komaiba.


    Kamar yanda Attahir ya faɗa kuwa hakance ta faru, dan tun 3am maman Ahmad ta tashesu suka kimtsa, zuwa huɗu da rabi suka wuce airport, biyar dai-dai jirginsu ya tashi, sanda suka isa kd kuwa anata sallar asubahi, wasu masallacinma sun idar.

    Anan airport ɗin sukai sallar asuba, kafin masu ɗaukarsu su iso aka wuce dasu gida.

     Suna isowa Bily da Ummukulsoom ɗaki suka shige bayan sun gaisa da Ummi da Abba sukai kwanciyarsu suka koma barci.

   Basu sake sanin wainar da ake toyawa ba sai kusan sha biyu, shima sai da Ummi taje ta tasosu sannan suka tashi kowa na kumbura baki wai barcin bai ishesa ba.

    Wanka sukai suka sakko ƙasa, Mamaki ya kamasu Ummukulsoom ganin Hajiya yaya da Gwaggo hinde a gidan Abba, abinda Ummukulsoom bata taɓa ganiba sam, dan Hajiya yaya idan bada ƙwaƙwƙwaran daliliba bata zuwa gidan sam.

       A falon suka zauna sunata tsokanar Hajiya yaya da Gwaggo hinde, ko abinci tare dasu sukaci.

    Kusan 1:30pm su Attahir suka dawo daga massalaci, mamaki ya kuma kashe su Ummukulsoom ganin Attahir yasha babbar riga ta farar shadda sol, hakama Yaa Zaid da yaa Ameer, Bassam, Abba, baba, Abban Aziza da wasu abokan su Yaya Zaid ɗin.

     Tuni falon ya kacame da gaishe-gaishe tsakaninsu dasu Hajiya yaya, sudai su Ummukulsoom nasu idone.

      Gwaggo Hinde tace, “Yoni banga angon nawa ba, ko yana tsoron nace sadakin yamin kaɗan saiya ƙarane?”.

    Dariya Attahir yayi yana cewa, “A'a fa Gwaggo hinde, aiko miliyan kikace a ƙara zamu sake ƙirgowa, waya yake amma bara na leƙa na shigo dashi”.

        “Wai yaya bikinwa akeyine?”. Cewar Ummukulsoom da Bily cikin haɗa baki.

    Ƴar dariya Attahir yayi yana ficewa ba tare da ya basu amsaba. Mintuna kaɗan sai gashi ya sake shigowa yana gyara hannun babbar rigarsa, hakan ne yasaka ba'a ganin na bayansa. 

    Matsawa yay gefe dan yabashi damar bayyana.

      Yaa Amaan ne sanye cikin ɗanyar shadda fara tas shima harda babbar riga datasha aiki ɗan ubansu Grey color, hularsa kalar surfanin, hakama takalminsa, ƴar ramar dayay da aski saita kuma ƙara masa ƙyau da wani kwarjinin cikar haiba na musamman, wanda hakan nada nasaba da zuwan ranar ta musamman itama.

      A gaban su Hajiya Yaya ya durƙusa yana gaishesu. Gwaggo hinde ce ta daddage ta callara masa guɗa.

    A hankali ya lumshe idanunsa yanajinta har tsakar kansa, sai dai yau sam sai baiji hakan ya ɓata ransa ba, saima wani shauƙi na musamman dake ratsa kowacce ɓular ƙofar gashi dake a sassan jikinsa.

      Ko motsi Ummukulsoom kasayi tayi, sam tunaninta baizo wajenba, batayi zaton za'a sake ɗaura auren da wuri hakaba, ta zata sai ranar su Bily za'a haɗa gaba ɗaya ayi.

    Jiki a sanyaye ta miƙe zata bar falon ganin Bily da maman Ahmad na neman saka rayuwarta a gaba.

     Da kallo ƙasa-ƙasa ya bita harta shige lungun Corridor ɗin dazai sadata da bedroom ɗinsu. Ya sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya yana miƙewa, duk da yana cikin tsantsar farin ciki bazaka taɓa fahimtar komai daga fuskarsa ba, duk da dai yau ba'a matuƙar haɗe takeba, amma shi a ganinsa yau ma fuskarsa washe take kamar gonar auduga a hakan(🤣😝).


       Attahir ne da kansa yaja hannunsa har ƙofar ɗakin su Ummukulsoom, daga nan ya juyo ya barsa wajen tsaye ba tare da yace komaiba.

     Da kallo ya bisa zuciyarsa naji sake ƙaunar Attahir, Attahir da banne a rayuwarsa da zuciyarsa, yasan wannan maida auren nasu duk ƙoƙarinsane, shi kansa bai sanar masa komaiba,  kawai ya sakashi baro legas ne akan zasu halacci ɗaurin auren wani abokinsu, sai da aka ambaci sunansa dana Ummukulsoom ne yasan shi ake ɗaurama aure. Baisan lokacin da hawaye suka cika masa idoba, musamman da idonsa yakai akan Dad da baisan yana wajenba sai lokacin, Dad ya sakar masa wani lallausan murmushi irin wanda ya daɗe bai ganiba daga garesa, rasama yanda zai musalta farin cikinsa yayi, sai godiya yake jerama Ubangiji daya amshi addu'arsa da yake babu dare babu rana.

    Tunda abinnan ya faru bai taɓa fashin azumiba, hakama sallar dare, kowanne dare cikin miƙama ubangiji kukansa yake akan idan auren alkairine a garesu ALLAH ya daidaita komai, idan ba alkairi bane ALLAH ya cire masa ita a zuciyarsa, ya bata wanda ya fisa.....

      “Wai tsoron shiga kakeyine?”. Maganar Attahir ta katse masa tunani.

      Ɗago ido yay ya kallesa, ya kai hannu ya shafi girarsa yana harar Attahir.

    Dariyar ƙeta Attahir ya sanya masa, “Ai dole ka hararenifa tunda na fiddoka a tuzuranci da zawarci Alhaji”.

    Babu shiri Yaa Amaan ya saki murmushi yana yima Attahir daƙƙuwa.

      Salute nashi Attahir yayi ya juya zai bar wajen yana faɗin, “ka shiga dan ALLAH broth, dan su Dad jiranka sukeyi”.

       Baice komaiba baikuma yi yinƙurin shiga ba, sai da Attahir ya juya yabar wajen sanan ya ɗora hannunsa kan handle ɗin ƙofar yay ɗan shiru na seconds goma.

      Da alama dai addu'a ya karanta kafin ya murɗa ya tura a hankali da sallama ciki-ciki.


        Tunda ta shigo ɗakin sai ta hau kukan da ita kanta batasan dalilinsa ba, tasan dai bai rasa nasaba da sadaukarwar da tayi dan kawai ta faranta ma babanta da Dad da kakanninta da Abba da yaya Attahir, tana kwance a kan gado rufda ciki, ta cusa fuskarta cikin filos, hakanne yasa sam bataji shigowarsa ba balle sallamarsa da shi kaɗai yasan yayi kayarsa.

         Manyan idanunsa masu matuƙar haskennan da cikar gashi ya sauke akanta, tundaga ƴatsan ƙafarta har zuwa gadon bayanta yake ƙarema kallo, sanye take da sket da riga na shadda pink, sun mata ƙyau sosai musamman data kasance mace mai cikar halittar jiki.

      Iskar data cika zuciyarsa ya feso ta baki yana harɗe dukkan hannayensa a ƙirjinsa da cigaba da takawa ahankali zuwa gaban gadon.

      Sautin kukanta ahankali da ajiyar zuciya kawai ke tashi a ɗakin, tsaye yay akanta batare da yace uffanba har kusan mintuna uku.

       Ƙamshin mayen turarenta da na jikinsa dana ɗakin ya gauraye ya bada wani irin nutsatstsen kamshi mai tsayawa azuciyar mai shaƙa, ya warware hannayensa tare da zama gefen gadon daf da ita idanunsa ƙyam akanta ko ƙyaftawa bayayi.

      A hankali cikin nutsatstsiyar muryarnan tasa mai cike da kamala da amo yay gyaran murya kaɗan da zata tabbatar mata da zuwansa.

       Ko kaɗan bata kawoma ranta shi baneba, a zatonta yaya Attahir ne, dan haka ta tsaida kukanta tare da yunƙurin tashi zaune sosai.

          Ta janye filon daga saman fuskarta tana yunƙurawa zata tashi, gabanta ya faɗin jin ƙamshin turarensa da tun ɗajun hancinta bai shinshino mataba saboda filo data shige.

       Tayi wani war da idanu na mamakin tozali dashi zaune kusa da ita, saurin ja da baya tai tana haɗe fuska da saurin goge fuskarta.

      Lumshe idanunsa yay a hankali yana wani munafukin murmushi da sam Ummukulsoom bata ganiba ma saboda a maƙoshi kawai yaji fitar sautinsa shi kansa da yay kayansa.......

      “Miye haka zaka kama shigowa mutane ɗaki babu neman izini?”.

       Bai ce mata komaiba, bai kuma janye idanunsa da takeji sun takurata ba akanta..   

    Ta watsa masa harar tare da murguɗa baki ta ziro ƙafafunta ƙasa zata sauka a gadon.

       Ɗauke kansa yay tamkar baya kallonta harta saukan ta nufi ƙofa, ta kama ƙofar ta murɗa zata fita tana cigaba sauke masa harar sai taji gam a kulle, mamaki ya kamata dan tasan dai key ɗin ajikin ƙofar yake basu cireba.

     Ƙarar keys ɗin ta jiyo a bayanta, hakan yasata ta waiwayo inda dakejin ƙarar.

      Shi da kansa yake girgiza Keys ɗin a hannunsa, kamar yasan zata iya guduwa ya zaresu daga jiki ya riƙe a hannu.

     Haushi ya kuma kama Ummukulsoom, a fusace ta nufoshi takai hannu zata warce ya goce gefe, ta bisa ɗayan gefen ya kuma gocewa.

   Sai ta sake kumbura da haushi, “Wai miye hakan kakemin dan ALLAH, kabani key na kama gabana malam”.

      Ƙin tankawa yayi. sai Kuma ɗaga mata key ɗin yayi.

      Cikin harzuƙar da tafi ta da takuma kai hannu da dukkan ƙarfinta zata figa ya tanƙwaɓi ƙafarta da tasa tare da goce hannunsa saita taho gaba ɗayanta ta faɗa jikinsa.

    Kafin tayi wani yinƙuri ya birkiceta ta koma ƙasa shi yana sama, sai dai bai sakar mata nauyinsa ba. 

     Duk da haka saiga Ummukulsoom na sauke numfashi da ƙyar, yayinda zuciyarta tazo saitin maƙoshi ta tokare.

    Shikam lumsassun idanunsa kawai ya zuba ma fuskarta.

      Ganin babu mafita saita sakar masa wani siririn kuka mai tabbatar masa da zuciyarta a kusa take.

         “Malam banason abinda kakemin, wlhy zan maka ihu”.

      “Bismillah” ya faɗa a hankali saman laɓɓansa.

     Iya ƙarfinta tasa wajen tureshi, amma ko motsi baiyiba.

     Ganin hakan babu mafita saita wage baki iyakar iyawarta yanda ta tabbatar wani zaiji ihunta tunda Window ɗin ɗakin ta baya a buɗe yake ta ƙwala ihu.

     Ruf ya rufe mata baki da nasa.............✍🏻



NO. 41


..........Duk yanda za'a musalta halin da wannan ahali suka tsinci kansu a ɗan tsakanin nan ɓata lokacine. Kowannen su hankalinsa a matuƙar tashe yake, musamman yau da har kowa ya iya shaida damuwar Yaa Amaan ƙuru-ƙuru akan fuskarsa, sai dai fa bazaka taɓa iya fahimtar yanayin Dad ba, yanata dai kai kawo shida Abba da Attahir a ƙofar ɗakin da ake bama Yaa Amaan taimakon gaggawa.

     Doctor ɗin dake tare dashi ne ya fito daga ɗakin da aka kaishi Nurses biyu na biye dashi.

    Momcy dake ta kuka tai saurin tasowa tana tambayar Dr ɗin ya jikinsa?, cike da tausayawa ya kalleta, kafin ya ɗauke kansa yana sauke numfashi. 

    “Hajiya sai dai addu'a kawai, ita yake buƙata”. ‘ya ƙare maganar da barin wajen’.

     Zubewa Momcy tai a ƙasa tana kuka, su Aunty Nurse suka riƙeta da bata haƙuri suma suna hawayen, sai dai sam taƙi yin shiru, da alama ma ta fara fita hayyacinta.

    Abba ne ya matso yana bata baki da mata nasiha akan tai masa addu'a bawai kuka ba.

      Kallo ɗaya Dad yay musu ya ɗauke kansa, saima ya fice yabar wajen gaba ɗaya.

  

      Ganin dare ya fara ja Amaan bai farfaɗoba Abba yace su Momcy su tafi gida haka nan, abarma safiya kuma.

     Dagewa Momcy tai akan ita dai abarta ta kwana dashi, Abba ne yayta lallashinta akan tayi haƙuri taje, bazai yuwu mace tayi jiyyar namiji ba.

     Badan tasoba suka tafi. aka bar Abba da Dad da Attahir, Zaid, Ameer a sibitin. 

    Suma duk sai Attahir yace suje gida shi zai kwana.


     Kusan 12 suka tafi har Attahir ɗin dan shima zai canjo kaya ya ɗakko abinda zasu iya buƙata.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

   

          Abba da Attahir da Zaid a tare suka dawo gida.

    Su Ummukulsoom suna falo zaune kowa da hidimar da yakeyi, sarai ɗazun taji ance Amaan baida lafiya, amma bata maida kai akan zancenba, dan a halin yanzu ko sunansa bata ƙaunar a ambata mata.

      Ummi tace, “Alhaji yaya jikin Amaan ɗin?”.

     Zama Abba yay yana faɗin, “To da sauƙi za'ace  Umminsu, sai dai fa gaskiya yaron yana bani tausayi, dan yanajin jiki matuƙa, ni harma na rasa yanda zan fassara al'amarin”.

      “Ya salam, ALLAH ya warware komai cikin sauƙi to, ya farko ko?”.

     “A'a har yanzu dai bai farfaɗo ba, amma Doctor yace babu damuwa a rashin farfaɗowar tashi, shiyyasa muka taho, jininsa ne yay mugun hawa sosai”.

     “Ya ALLAH, ɗan yaro dashi ko iyalanma ba'a ajiye da nisan zango ba ace hawan jini?”.

     Cikin sauke ajiyar zuciya Attahir yace, “Ai Ajiwa ya daɗe da hawan jini Ummi, shi mutum ne da inhar kika iya fahimtar damuwarsa a fuskarsa to lallai abu yakai matuƙar tiƙewa a garesa,   duk abinda kuma za'a cutama wani yaga yana da ƙarfin da zai iya karesa to lallai zai shiga koda shi zai cutu, shiyyasa ko a lokacin da yace min ya saki Ummukulsoom nasha mamaki matuƙa, dan ban taɓa kawo hakan a raina ba wlhy, abubuwan da yake sakama ransa sune suka haddasa masa ciwon, gashi dama shi bamai son yawan magana baneba...”

      Ummi tace, “Babu abinda yafi ƙarfin ƙaddara ai Attahir, tunda har ALLAH ya ƙaddara sai igiyar auren ta tsinke babu wani mai hana hakan koda su a karan kansune, irin masu halayyar Amaan a wannan zamanin ƙalilanne, su bada farin cikinsu dan wani yayi, ALLAH ya bashi lafiya da dukkan sauran musulmai, amma sam abun baiyi daɗiba dai wlhy”. 

      Miƙewa Attahir yay zuwa sashensu, duk abinda zasu iya buƙata ya ɗauka ya koma asibitin


★★


    Amaan bai farkaba sai Washe gari da hantsi, zuwa lokacin duk su Momcy sun koma asibitin, suma su Ummu da maman Ahmad da Bily da Ummi duk suna can.

    Attahir ya fito ya kira doctor suka koma ɗakin tare, dukkan taimakon daya dace shi aka sake bashi.

     Ba'abar kowa ya shigaba sai Abba da Dad, suma kuma basu daɗeba suka fito, saiko Momcy data samusu kuka, itama an barta ta leƙasa na ƴan mintuna.

     Momcy sai ƙara kallon Ummukulsoom take mamaki fal ranta, ko a mafarki akace mata yarinyar datai aikatau a gidansu ce saita ƙaryata tace shirmen mafarkine, lallai ta cutar da ɗanta, dan ko Amaan yanada laifi ta fisa, itace taita cusa masa ƙin Ummukulsoom a zuciya ta hanyoyi da dama bisa ga shawarar ƴar uwarta mansura, ashe batasan ɗanta takema zagon ƙasa ba, wadda kuma take ganin sunfi ƙarfi yau itace tazamar musu wutsiyar raƙumi. Hawaye masu ɗumi suka biyo kumatunta, tasa bakin gyalenta ta share, gaba ɗaya ta kasa ɗauke idonta a kowanne motsin Ummukulsoom, hakama su Ameer sai kallon Ummu sukeyi kowa yana saƙa abinda yazo masa a rai.

    Yayinda kuwa Ummukulsoom ta ɗaukema kowa kai a cikinsu, bayan gaisuwa bata kuma kallon kowa ba sai yaran Aunty Nurse.

    Ganinma kallon yamata yawa ta miƙe da nufin ficewa ta jirasu a waje.

     Lokacin da su maman Ahmad suka fito domin tafiya gida hararta sukaitayi akan abinda tayi.

     Amma sam sai taƙi kallon kowa, sai da akaje gidane kowa ke mata faɗa akan karta sake yin irin haka, babu mai matsa mata akan Amaan, amma gameda lalura da yake ciki ta bar nuna halin ko in kula gaban ƴan uwansa kodan darajar Dad.

   Ta gamsu da wannan maganar, dan haka ko a washe gari ma da sukaje dubashi bayan ta gaishe da Dad ta gaida Momcy dasu Aunty Nurse. yau dai an barsu sun shiga, saidai fa shine ba kowa ya fahimta ba saboda bayajin daɗin jikinsa sosai, bakuma yason hayaniya kwata-kwata.

   

  ★★★★

         A kwana na uku da kwanciyar Amaan asibiti suka koma legos saboda makarantar Ummukulsoom da Ahmad, amma shi Attahir sun barsa anan, dukda haushin Amaan da yakeji bazai iya tsallakewa ya barsa a cikin wannan halinba, ko a jiyyar nan tashi da yake yana bashi dukkan kulawa, sai dai baya masa irin kaffa-kaffa ɗinnan da tsokana sam.

     Sai da su Ummukhoolsum suka biya ta asibitin suma, sai dai fa sam ita ba'a son ranta ba, ko zuwan kullum ɗinnan da sukeyi tana ƙyautata zaton baima taɓa ganinta ba.

     Yau ma sai dama Ummi tai mata jan ido sannan, amma harda hawayenta na haushi.

     Har lokacin da sukaje ma barci yakeyi, tunda yay sallar asuba ya koma barci, hakan yasa ko ma shiga basuyiba.

     Har sunyi niyyar tafiya sai Attahir daya fito daga ɗakin da Amaan ke kwance ya dakatar dasu ta hanyar faɗin su shigo Amaan ɗin ya tashi.

   Jitai tamkar ta rusa kuka, amma yaya zatayi, dole ta dawo da baya tana kuma ɓata fuska suka shiga.

       

      Zaune yake a saman gadon jinyarsa, an saka masa filo ya jingina, ya ɗan rame ba laifi, amma sai ya kuma haske dayin fayau a fuska, kallo ɗaya zakai masa ka fahimci lallai bayajin daɗi sosai.

       Ameer dake haɗa masa tea ya ɗago tare da miƙa ma Attahir, dan inhar bashi ya bashiba baya sha.

     Tunda suka shigo kallo ɗaya yay musu ya ɗauke idanunsa, Bily da maman Ahmad suka matso suka gaishesa da masa ya jiki?.

    Murya can ƙasan maƙoshi ya amsa, ba tare da ya kalli kowa ba.

     Da hannu Bily ta zunguri Ummukulsoom da batace komaiba, Attahir ma ya dalla mata harara.

    Tasan minene laifinta, dan haka ta kumburo baki tana faɗin, “Ya jiki?”.

    Bai amsa ba, sai idanunsa da suka canja launi ya ɗan ɗago ya kalleta, caraf suka haɗa ido, tai saurin janye nata tana hararsa.

   Lumshe nasa yayi a hankali yana kuma haɗe fuska.

    Babu wanda ya sake magana a ɗakin, Amaan yanata shan tea ɗinsa a hankali, Attahir dake zaune gefensa yana ɓalla masa magun guna, da alama jira yake ya gama ya basa yasha.

       Wayar Ummukulsoom ce tai ring, ta lalubota a handbag tana dubawa.

     Wani lallausan Murmushi ta saki ganin Umar rinta.

       Amaan dake kallonta ta gefen ido batare da wani zai iya fahimtar hakanba ya cije haƙwaransa ta cikin baki, haka kawai yaji zafin murmushin nata saboda zargin namiji ne ya kirata....

    “Hallo Umar!” ta faɗa tana ficewa daga ɗakin gaba ɗaya.

   Su duka da kallo suka bita, banda Attahir da Amaan da baka isa fahimtar yana kallon nata ba.  

     Tea ɗin hannunsa ya miƙama Attahir alamar ya ƙoshi, da mamaki Attahir yace, “Wai kana nufin ka ƙoshi?”.

     Fuska ya ɗan yatsine ya ɗaga masa kai batare da yace uffanba, yakai hannu ya ɗiba maganin da Attahir ɗin ya ajiye masa, Ameer yay saurin miƙa masa ruwa da ya kalla.

      Sai da ya gama shan maganin sannan su Maman Ahmad sukai masa sallama tare da addu'ar samun sauƙi mai ɗorewa suka fice suma.

     Lumshe idanunsa yayi zuciyarsa a matuƙar cinkushe, saɓanin da iyayensa suka samu a kansa shine babbar matsalarsa a yanzu, duk yanda yaso kaucema hakan bai tsallake ba, ya haɗiye abinda ya tokare maƙoshinsa da ƙyar, gaba ɗaya ji yake rayuwar ta daina masa daɗi, babu abinda ke saka sa farin ciki a halin yanzu. 


*_BAYAN KWANA UKU_*


           Kwana uku da komawar su Ummukulsoom legos aka sallami Amaan ya koma gida, abinda ya kuma sakashi cikin ƙunci barin Momcy gidan, ƙiri da muzu Dad yace bazata zauna masa a gida ba, duk roƙon da ƴaƴan suke masa yaƙi sauraren kowa.

    Wannan yasa duk suka kasa komawa gidajen aurensu suma, ga jarumin gidan da kan iya tunkarar Dad ɗin shima yayi laushi, dan Dad ɗin yamafi jin zafinsa fiye da kowa, a haka aka cinye kwanaki biyu.

     Dole a ranar lahadin data zagayo kwana takwas da faruwar abun Amaan da Attahir suka shirya suka koma Legos wajen aiki.

     Komai ya kuma canjawa a garesa, ƴar magana ɗaya biyu ma da yakeyi ada yanzu ta gagaresa kwata-kwata.

     Bayan ya gama kimtsawa ya nufi sashen Dad, a falo ya iskeshi zaune yana shan fura da Aunty Nurse ta dama masa, yay ma Amaan kallo ɗaya ya ɗauke kansa.

    Shima kansa a ƙasa yaje gabansa ya zauna, “Dad barka da hantsi”.

     “Barka” kawai Dad yace ya ɗauke kansa;

   Shirune ya biyo baya, ga magana cike da ran Amaan amma bakinsa ya kasa furtawa, sai da yaga Dad zai miƙene yace, “Dad ka gafarceni, ni mai laifine a gareka tabbas, sai dai wlhy bana aikata bane danna nuna maka baka isa dani bane, inhar haƙura da ita da kace nayi zaisa ka dawo da Momcy gidannan na ɗauki maka alƙawarin haƙura da ita, insha ALLAHU kuma bazan sake bibiyar rayuwarta ba, na yarda cewa ƙaddarace ta haɗa mu, itace kuma ta rabamu, sakejin zan iya zama da ita da barinta a yanzu kuma na amsheshi matsayin jarabawa, dan ALLAH Dad kadawo da Momcy”.

    Cifaba da tafiya Dad yayi baice uffanba, sai da yaje gab da shiga ƙofar bedroom ɗinsa ya tsaya, “Inhar ka nisanci Ummukulsoom kamar yanda kai alƙawari to tabbas kaima zaka samu yanda kakeso ga mahaifiyarka, zan saka dukkan idanuna akanka kuma”. Yana gama faɗa ya shige abinsa.

       Yaa Amaan ya sauke wani nannauyan numfashi sannan ya miƙe ya fito, koda ƴan uwansa suka rakosa har mota bakinsa bai saɓa da kowa ba, sai hannu daya iya ɗaga musu kawai.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡

        A ranar suka dawo legos shida Attahir.

     Tunda ya dawo kuma bai haɗu da Ummukulsoom ba, duk wata hanyar da zata haɗasu kowanne ya tosheta tsakanin ita da shi, shi yanayin komaine bisa umarnin mahaifinsa, ita kuma tanayine dan batason ganin sa sam.

        A yanzu haka ta bama Umar damar tura iyayensa gidansu. 



★★★★★

              “Ajiwa wai bazaka cire abinnan a ranka ba dan ALLAH, kusan wata biyu kenan sai zabgewa kake a tsaye, kana kallon kanka a madubi kuwa?”.

         Numfashi ya sauke kaɗan yana lumshe idanunsa, yakai hannu kaɗan ya shafi girarsa, “Attahir kenan, kaine kakemin kallon mai damuwa, amma fa ni bani tare da kowacce damuwa a raina a halin yanzu, Momcy ta koma lastweek, to mikuma zansa a raina?”.

     Murmushi Attahir yay yana faɗin, “Hakane Ajiwa, amma sam kaƙi sakin ranka ai”.

    Ɗan murmushi yayi yana maida idanunsa ya lumshe ba tare da ya ƙara cewa uffan ba.

   Shima Attahir sai ya sakin zancen kawai ya kamo masa wani.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


          A ƙarshen wannan satin Attahir ya shirya zuwa kd na kwana ɗaya.

      Kai tsaye gidansu Amaan ya sauka, yayi farin cikin ganin Momcy ta dawo, sai dai fa da alama har yanzu akwai damuwa, dan ayanayin daya ganta kawai ya isa bashi wannan amsar, komai nata sukuku take yinsa, sam babu walwala a tare da ita, hakama su Bassam dake gida.

    Bayan sun gaisa da Momcy ne ya tambayeta Dad fa?.

     Cikin ɗan yaƙe tace, “Attahir yana baya zaune, kaje can ka samesa”.

     Har Attahir ya miƙe Momcy ta dakatar dashi.

   “Attahir yaya jikin ɗan uwan naka? Nasan daurewa kawai Fodio keyi, har abada bazan yafema kaina ba inhar wannan damuwar takai fodio ƙasa Attahir....” hawaye masu zafi suka gangaro a kumatun Momcy.

   Sosai tsoro ya kama Attahir, ya rikice da bata haƙuri.

    “Attahir babu wani abinda zai tsayar da waɗannan hawayen nawa a irin wannan lokacin, dan girman ALLAH Attahir ka roƙi Ummukulsoom tayi haƙuri ta komawa Fodio, wlhy na tabbata yana sonta, amincewarta ce kawai zata saka Abban Fodio janye katangar da yayma Fodio da ita, wlhy Attahir a yanda nakeji yanzu zan iya haƙura da nawa auren inhar Abban Fodio zai amince Ummukulsoom ta dawo”.

    Kan Attahir a ƙasa idonsa yay jajur ya ɗago ya kalli Momcy, “Momcy kibar faɗar haka, mu cigaba da addu'a, insha ALLAHU komai zai daidaita”.

     “ALLAH ya daidaita Attahir, sannan ka bani Number Ummukulsoom”.

    “Ok gata” yafaɗa yana danna wayarsa, sai da ya faɗa mata ta saka sannan ya fice zuwa wajen Dad.


      “A'a, Attahiru ne a garin namu?”.

    “Eh Dad nine, mun sameku lafiya?”.

    “Lafiya lau Attahiru, ya aikin naku da iyali? Ina kuma ɗiyata Ummukulsoom?”.

     “Alhmdllh Dad, Ummukulsoom na lafiya, yanzu ma akanta nazo wajenka”.

      “To mike faruwa?”.

Kai Attahir ya sosa yana kuma sunkuyarwa, “Dad ka gafarceni, nasan kai mana katanga da wannan maganar, sai dai halin da ɗan uwana yake ciki yasa naji bai kamata nayi shiruba, wlhy Abba Amaan yayi nadamar abinda ya aikata, dan ALLAH kai mana afuwa mun tuba.....”

      “To inbanda abinka Attahiru aini dama ban riƙeku a rai ba ko”.

    “Hakane Dad, amma...”

 “Attahiru! Mubar wannan zancen kaji”.


    Duk yanda Attahir kema Dad magiya sam yaƙi saurarensa, hakane ya sakashi tashi jikin a sanyaye ya tafi ba tare da ya samu yanda yake soba.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


        Washe garin dawowar Attahir Ummukulsoom zaune a harabar gidan daga can baya iskar la'asar na busata tana karatu, kwanaki kaɗan ya rage musu su gama exams nasu, sallamar Attahir ce ta sakata ɗago idanunta ta kallesa.

      “Lah yaya Attahir ashe ka dawo?”.

    Zama yay a gefenta yana faɗin “Eh shigowar kenan, naji gidan shirune inasu Bily?”.

        “Aunty dai taje kitso, Bily kuma a ɗaki na barta tana barci”.

    “Ok to masha ALLAH. Ai dama inason muyi magana tun kusan kwanaki biyu haka”.

    “To yaya ina saurarenka, ALLAH ya jishemu alkairi”.

    “Amin ƙanwata. Dama akan maganar Umar ne, iyayensa sunce zasuje ƙarshen satin nan sukai kuɗi”.

   Kanta a ƙasa tace, “Eh haka yace yaya”.

    Idanu yaɗan tsura mata na wasu sakwanni, kafin yaɗan gyara zamansa, “Ummukulsoom na baki shawara mana?”.

      “Yaya ko Umarni kabani zanbi balle ma shawara”.

    “To na gode, amma ita shawara ra'ayin wanda akaimawace ya ɗauka koya ajiye, musamman idan ta shafi rayuwarsa. Ummukulsoom ina ganin ki sake bama Ajiwa dama a karo na biyu”.

     Sosai ta ware manyan idanunta tana kallon Attahir da shima ita yake kallo.

   Bai jira tace komaiba ya cigaba da faɗin, “Nasan wanene Ajiwa fiye da zatonki, tun bayan rabuwarku dashi na fahimci yana cikin damuwa, sai dai a koda yaushe cikin ɓoyemin yake, lallai yayi kuskure sosai, sai daifa abinda zamu duba babu wani hannu a duniya daya isa goge abinda ƙaddara tazo dashi a littafinmu, haka ALLAH ya ƙaddara a tsakaninku, da Ajiwa baiso karɓar aurenki ba tun farko zai san yanda ya zamewa Dad, sai dai shi mutumne maison bin umarnin iyayensa koda ace zai cutu, Ajiwa na sonki Ummukulsoom, halayyarsa kuma ba girman kai baneba, haka ALLAH ya haliccesa, wlhy duk wani hali da kikasan ALLAH ya halicci ɗan adam dashi babu mai iya canjashi, sai dai ya koyi wani abun, a wannan gaɓar ba kuskuren Ajiwa ya kamata ki kalla ba kota Momcy, Ƙyautatawar Dad da halaccinsa ya kamata mu kalla mu dukanmu, Dad ƙarfin hali kawai yakeyi, dan kaf ƴaƴansa yanason Ajiwa fiye da kowa a cikinsu, ba komai yakawo hakanba kuwa sai ƙaƙarin ƙyautata masa da yakeyi, dan kowacce zuciya nason mai ƙyautata mata, amma saboda adalcinsa a gareki ya haramtama ɗansa ke, bawaifa dan shima baya sha'awar tarayyarku baneba, kawai bayason ya shiga haƙinkine. Saboda ke ya saki uwar ƴaƴansa da sukai aure tsawon shekaru, Na baki damar ki zauna ki tunani akan maganganuna, kamata yay ki koma gidanki ki hukunta Ajiwa da kanki, ba ki barin farin cikin iyayensa dana ahalinsa yaci gaba da tafiyar hawainiya ba”. Yana gama faɗa ya miƙe yabar wajen.

     Ko motsi kasayi Ummukulsoom tayi a wajen, ba komaine ya tsaya mata araiba sai adalcin Dad a gareta, tabbas zatayi wani abu akai, amma ba komawa gidan Amaan ba, ta riga da ta jingine babinsa gefe kuma har Abadan shikam, bakuma tajin zata sake zama dashi musamman zaman aure..........✍🏻



NO. 43


..........A nutse yake sumbatarta, babu wani rawar jiki ko hanzari a tattare dashi. Duk mutsu-mutsun da take bai bartaba sai da yay san ransa, a yanda yake mata kawai zai tabbatar maka da akwai huce haushi, gashi ya danna hannayen duka da nasa babu damar motsawa, ƙololuwar takaici Ummukulsoom tagama kaiwa.

    Tsawon mintina uku suna a haka sannan ya janye bakinsa yana sauke tagwayen ajiyar zuciya, Idanunsa da launinsu ya canja ya ɗago ya zuba mata su, sai taga sun kuma girma da kwarjini, sam bazata jure kallon cikinsu ba.

    Ta kauda fuskarta gefe tana ƙunƙunan ALLAH zai saka mata da koƙarin haɗiye hawayenta.

     Duk da sarai ya jita saiya basar, batare da ya ɗagatanba ya saka mata keys ɗin a hannunta na dama yana matso da fuskarsa daf da tata sosai tamkar zai kuma haɗe bakinsu, duk yanda taso kauda kanta yaƙi bata dama.

    Magana ƙasa-ƙasa tamkar mai raɗa ko mai gulma yana gudun a jisa  yace, “ko zaki sake gwada ihun?”.

      Kamar zata shareshi saita kasa, ta dalla masa harara, Tana sake kumbura fuska da cuno baki.

       “Idanma kin kira mutanen kece da kunya matar Uthman” yay manar da janye jikinsa daga nata gaba ɗaya.

    Ajiyar zuciya Ummukulsoom ta sauke saboda jinta sakayau, aranta sai mita take akan uban nauyinsa.

         Yanajin ƙunƙunan da takeyi amma sai bai tankaba.

      Har tuntuɓe take da ƙafarsa wajen yunƙurin tashi ta gudu, ya bita da kallo ƙasa-ƙasa dariya nacin ransa, amma saiya haɗiye kayarsa ya miƙe tsaye kamar zai kamata, saiya waske yana gyara babbar rigarsa.

      Tuni Ummukulsoom kam taje ga ƙofar bathroom dan ta zata kamata zaiyi, ganin zata shige yace, “Hajiya bani key kar aga na daɗe azata wani abun nakeyi”.  

     Harara ta zuba masa ta shige bayin.

     Murmushi yayi yana kai hannu ya shafi girarsa, dama danta hararesan ya faɗa, harara na mata ƙyau, dan tana sake fiddo da manyan idanunta ne, har wani ƙyallin ruwa zakaga sukeyi, shikuma hakan na matuƙar tasiri agareshi.

      Gaban Mirror ɗinsu ya nufa, ya ɗauki tissue ɗin dake wajen tare da pen yay rubutu kaɗan daga ƙarshen da aka warwara ya maida ya ajiye, sannan ya koma saman gadon ya ɗauki keys ya fice.


          Tunda ya fito falon Attahir ya wani kafesa da kallon tuhuma, sarai ya fahimcesa dan haka  saiya kuma haɗe face ya basar yana watsa masa harara, zama yay suka gaisa da Ummi tai masa ALLAH ya sanya alkairi.

      A saman laɓɓa ya iya amsawa saboda jin nauyinta, kafin ya miƙe suka fice shida Attahir ɗin da dama zaman jiransa yake, Gwaggo Hinde da Hajiya yaya sai tsokanarsa sukeyi.

    Sai Attahir ne ke karesa, amma shi ya gaza cewa komai.

     Suna fitowa Attahir ya tsaya cak yana masa kallon sama da ƙasa, “Ajiwa wai mika aikata kayanka sukai wannan Squeezing ɗin haka? Kamar wanda yay danbe”.

     Hararsa yayi yana ɗauke kai, tareda ci gaba da tafiya yana faɗin, “Shaƙeni na faɗa maka, inma danben nayi miye naka a ciki?”.

     Sosai Attahir ya tuntsure da dariya, “Yanzu kam kasamu bakin min rashin kunya tunda na kaika inda aka ƙaromaka ƙarfi, ɗan rainin wayo nasan maganinka ai wlhy, sai next year zata tare”.

    Juyowa yay ya kallesa, kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru ya cigaba da tafiya zuwa falon baƙi inda ya tabbabatar su Abba na can.

       Attahir ya bisa da kallo zuciyarsa fes, Ajiwansa kenan mai abin haushi da ban mamaki, duk wanda yay masa farin sani yasan yau yana cikin farin ciki, a kan laɓɓansa ya furta “ALLAH ya baku zaman kafiya”.



★★★★★


    Duk da taji ya fita kasa fitowa tayi daga toilet ɗin, gani take kamar kowa yasan miya faru, ta cije baki wani haushi na kuma mamaye ranta, hannunta takai saman laɓɓanta da sukaci ƙaniyarsu, tai ƙwafa da faɗin ƙazantar banza......

    Jin an kuma buɗe ƙofar sai da gabanta yaɗan faɗi, ita duk zatonta shine ya dawo, ta kuma ƙanƙame jikinta tana mannewa da ƙofar.

      Bily data shigo idonta ya sauka akan gadonsu, haɓa ta riƙe tana danne dariyar dake neman taso mata, ta hau waige-waigen inda zata hango Ummu, ganin  babu alamarta a ɗakin saita shiga ƙwala mata kira.

      Ummu dake bayi ta sauke ajiyar zuciya tana buɗe idanunta da dafe ƙirji jin muryar Bily, ƙofar ta buɗe ta fito tana wani cin magani da kumbura baki dan karma bily tazo mata da ƙananun magana.

      Bily dake kallonta ta kwashe da dariya, “Amarsu ta yaya Amaan, mi akaci aka rage a ɗakinne naga gadonmu duk a yamutse?”.

      Kunya ta kama Ummukulsoom tamkar ta nutse, amma saita dake tana harar Bily.

     “Yo miye na hararata? Gadon nan dai da gani Ya...”

    Ranƙwashi mai azabar zafi Ummu tabama Bily akai, ta dafe wajen tana faɗin, “Muguwa kasheni zakiyi”.

    Sosai Ummukulsoom tasa dariya tana ƙarasawa gaban mirror, tissue ta ɗauka da niyyar goge fuskarta data jiƙa kwalli yaɗan kwaranyo, sai taci karo da rubutu. har zata share a tunaninta shirmen Bily ne tayi, sai dai ta tsaya karantawa.

      *_“Duk wayon Amarya wataran ƙirjin ango zata kwana. Amma fa kina ruwa babie, idan kika fito za'aji ƙamshin turarena a jikinki, idan kika canja kaya kuma kowa zai tabbatar ango yay......”_*

      Da sauri ta yage tana dunƙulewa da ƙunƙuni dan kar bily ta gani, sai dai batasan tana a bayanta ba, tarema suka karanta.

    Duk yanda bily taso danne dariyarta ta kasa hakan, dole ta barta ta fito, ta faɗa saman gadonsu tanayi iya iyawarta.

      Ummu ta kuma kumbura da haushi, wani haushin Amaan na kuma ratsata, wlhy mutumin nan ya iya mugunta, ɗan rainin wayo kawai, saiya nemo mai kwana aƙirjin nasa......

       _“Amma fa kina ruwa babie”,_  “hhhhh oh yaya Amaan ɗinmu na mutunci, ashe haka kake dunɗun dunkum ɗinnan bana banza bane, _Ango yay... Me?_ ƙarasa min naji dan ALLAH tawajena”. ‘Bily ta katse mata tunani da shaƙiyancinta’.

        “ALLAH ya isa to” Ummu ta faɗa tana harar Bily ta koma ta sake shigewa bayin badan tasan abinda zataiba, sai sam batason bily taga hawayen da suka cika mata idanu.

      Saboda tsabar jan magana irin na Bily saita bita jikin ƙofar Bayin, “Bestie kar dai wankan manya zakiyi?”.

       Murɗa ƙofar Ummukulsoom tayi da nufin fitowa Bily ta kwasa da gudu ta fice daga ɗakin tana dariya. Itama ƙwafa tayi ta maida ƙofar ta rufe.


★★★★★


       Sosai su Abba suka tasa Amaan da faɗa da nasiha akan a kiyaye gaba, badan mahaifin Ummukulsoom ba da iyayen Momcy dasu Hajiya yaya da Attahir ne duk ya kama kafa dasu, da Dad bai sakkoba har ya amince da sake ɗaurin auren nasu a karo na biyu.

      Daya amince ɗinma cayay sai dai a haɗesa da nasu Bily ne.

       Amma sai Baba yace a'a a ɗaura kawai kodan hankalin Amaan ɗin ya ƙwanta waje ɗaya, yakai maƙurar da ya kamata a tausaya masa kodan mugun ciwon dake tare dashi, suna gudun yaci gaba da takura kansa azo zuciyarsa ta buga a banza, bayan sunada damar share masa hawayensa, kuskurene dai anriga da anyisa, saikuma a tari gaba, ga Attahir dake ta masa fadanci.

     Dukda haka kuma sai da Dad ya kira Ummukulsoom ya tuntuɓeta akan inhar batason Amaan ta sanar masa, shi bazai amince ai mata auren doleba.

    Kunyace dukta ishi Ummukulsoom, ina taga bakin buɗewa tacema dad batason jininsa, cikin in ina tace “Dad na.. Na amin.. ce”. Tai saurin yanke wayar.

      Farin cikin da Dad yashiga aranar bai musaltuwa, dan haka ya amince akan a daura, dama kullum fatansa da addu'arsa kenan, sai dai bayason shiga haƙƙin Ummukulsoom ne kawai.

     To shine fa aka ɗaura auren a yau kamar yanda Hajiya yaya ta bada umarni, shikuma Dad ya roƙeta akan abar Ummu karta tare sai lokacin bikin su Bilyn da bai gaza wata ɗaya ya rageba, zuwa sannan ta kammala karatunta, dan baza'a shiga haƙƙinta ba itama.

    Koma dai yayane shidai Amaan yaji daɗi, sai yaji Baban Ummukulsoom ya kuma daraja da kima a idonsa shida Hajiya yaya, duk abinda ya aikatama ƴarsu sai basu duba ba suka kalli halaccin mahaifinsa. Sosai yay musu godiya, tareda ƙara roƙon Dad ya yafe masa, da alƙawarin insha ALLAHU bazai sake wannan gangancinba, wannanma ƙaddarace.

       A take Dad yace ya yafe masa, shi dama bai riƙesa ba, komai yana masane danya magantu.

    Tashi yay ya rungume Dad yana sake jero godiya.

     Attahir sai dariya yake ƙasa-ƙasa dan kar su Abba suji aci ƙaniyarsa.

      Anja musu doguwar addu'ar zaman lafiya kafin kowa ya kama gabansa.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


             Tunda Ameer da Bassam suka dawo suka sanarma Momcy abinda ke faruwa saita hau kukan daɗi tana sanyama Ummukulsoom albarka. gaba ɗaya ta ƙagara Fodionta ya shigo gidan ta gansa, dan jitake tamkar an maida matashi sabon mutum yau.

        Babu ɓata lokaci tashiga buga waya tana sanarma ƴan uwa da abokan arziƙi abin farin cikin daya sameta.

      Su Baba Halima da sai yanzu sukasan mike faruwa daɗi dukya kamasu, Jud sai son ganin Umikusmu yakeyi, dan tunota yake sonyi randa Amaan yaji mata ciwon nan a ƙafa amma sam zuciyarsa taƙi yarda itace. 

   Cikin mintuna ƙalilan gidan yafara amsar ƴan taya murna na kusa, yayinda su Jud keta ƙoƙarin haɗa abinci mai sauƙi.


     Sai da aka idar da sallar la'asar Dad da Amaan suka shigo gidan, kai tsaye sashen Momcy ya nufa kamar yanda Dad yayi.

     Yana shigowa Ummayya Da Aneesa da Buhayyah sukazo suka rungumesa duk da kowa zuciyarsa a tsorace take da hakan.

    A mamakinsu sai sukaga bai gwalesu ba.

   Momcy tazo duk ta turesu ta rungume yaronta ta gefe.

     Tattausan Murmushi ya saki wanda mutane da yawa da basusan yana yiba suka shagala a kallonsa, Dad ma daya shigo kallonsu yayi yay murmushi yana yunƙurin hayewa sama.

   Momcy ta saki Amaan ta nufi mijinta da hanzari ta rungumesa hawayen daɗi na silalo mata a kumatu, sam ta manta da wasu ƴaƴanta da maƙwafta, burinta ta nuna masa jin daɗinta kozai sakko itama yabar fushin da ita hakanan, dan tunda ta dawo gidan baya kulata, ko magana tai masa daga sallama baya sake amsawa.

    Hannayensa yasaka ya zagayeta dasu shima yanajin farin cikin gane kuskurenta da tayi da wuri, tare da jin ƙaunarta.

    Ƴar ɓoye fuska aka shigayi a wajen su Ummayya, Amaan ma ya sunkuy da kai yana cigaba da murmushin sa, harga ALLAH abin ya bashi kunya. Sai da ya tabbatar sun saki juna harma sun haye sama sannan ya ɗago kansa tare da juyawa zai fita sashensa.


     Wanka yake amma gaba ɗaya zuciyarsa naga Ummukulsoom, abinda ya faru a tsakaninsu kawai yake hasasowa, yakai hannu saman laɓɓansa ya furta ya shafasu, a hankali ya furta“Jan aji, nutsuwa, cikar haiba, kamala....” saikuma yay ɗan murmushi batare da ya ƙarasa ba ya haɗiye sauran a ransa yana ɗauraye jikinsa...

    Koda ya fito sai bai zaunaba saboda jiyo maganar Momcy a falonsa, wando 3quarter ya saka da riga mara hannu yaɗan fesa turare ya fito hannunsa riƙe da wayoyinsa.

       Zama yay kusa da Momcy da tun da ya fito take kallonsa bakinta washe da murmushi na tsantsar farin ciki.

      “Babana Congrat fa, ALLAH ya sanya alkairi ya baku zaman lafiya na har abada, ALLAH ya kawomin jikokina anan kusa”.

         “Amin” ya faɗa akan laɓɓa ba tare da ya yarda sun haɗa ido da Momcy  ba.

        Madai-daicin tiren data shigo dashi ta ɗago tasa a cinyarta, kallonta yay da mamaki, “Momcy wannan fa?”.

    “Kai zakaci Fodio, na kula duk yau baka sakama cikinka abincin kirkiba, koma nace tunda matsalolinnan suka shigo kaima abinci yajin aiki, dan haka ɗura zan maka”.

      “Ɗura fa Momcy?” yay maganar da ƴar shagwaɓa.

       Tace, “Ƙwarai kuwa, yanzun nanma bara ka gani”.

    Duk yanda yaso zamewa akan ya ƙoshi bata barshiba, a baki ta dinga bashi abincin, saboda tsabar son kar yaci saiya ringa mata shagwaɓar wai akwai yaji, shifa ƙirjinsa zafi.

    “Ungo sha ruwa, indai yajine zai kwanta. Duk dai iya langyarenka saika cishi, sonake kafin wata ɗayannan da ɗiyata zata tare ƙibarka ta dawo, ina daɗi akai mata ango ramamme”.

      “Momcy!...” ya kira sunanta a matuƙar sanyaye.

   Eh kirani da ƙyau, ai gaskiya na faɗa, Dad ɗinku ma cayay nazo na saka gaba kaci abinci.

      Zaiyi magana Aneesa ta shigo itada Aunty Ummi. Haɗiye kayarsa yay yana maida fuskarsa babu wasa, dama bawani uban sakewa yay mataba.

     Zama sukai suna kallon ikon ALLAH ana bama yaya Amaan abinci a baki.

      “Lafiya kuka samin ido?”

   Yay maganar ƙasa-ƙasa saboda Aunty Ummy.

       Dariya Momcy da Aunty Ummy sukayi, Aneesa kam ɓoye tata tayi dankar asamu matsala.

         Aunty Ummy ce tace, “Kai da wane idon ka kallemu kasan muna kallonka? Dama cazamuyi mun wuce gidan Abba mu gaishe da ƙanwar tawa”.

    Sosai ya haɗe fuska, dan a zatonsa wani abune daban zai kaisu.

    Momcy ce ta fahimci ma'anar ɗaure fuskar tasa, dan haka tai saurin cewa “Kaga karka kawo komai a ranka Fodio, abinda ta faɗa shine gaskiyar magana”.

      Baice komaiba, amma dai alamu sun nuna ya gamsu.

   Godiya sukai masa suka fice.

  


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


           “Auntys ga dama ta samu, wannan bikin da za'ayi na yayan Meenal ya kamata kusan yanda kukai kuka ƙulla alaƙa da ita, a wannan ranar nima zanyi duk abinda ya dace Numbers namu su kasance a wayar shashashan naku” Zulfah ta faɗa tana wani far da idanu.

   Ranƙwashi Suhailat ta bata, “ALLAH zan ɓata miki rai idan baki nutsu ba, kimana bayani yanda zamu gane”.

     “Kai Aunty wlhy da zafi, minene abin rashin fahimta anan, komaifa a buɗe yake, Auntys L & F dan ALLAH baku ganeba kuma?”.

      Fannah tace, “nidai na fahimceki sosai Zulfah, samun Number sa a garemu dakuma saka tamu a tashi shine mataki na biyu dazai cigaba da girmama saɓani tsakaninsa da ita, amma sai daifa zan sai wani layin dabanne nikam, koma nace kowannen mu ya tanadi sabon layi saboda wannan aikin, muna gamawa mu gimtsesu kawai”.

     “Shawararku tayi hundred percent, sai dai tayaya zamu samu zuwa bikin?”. Cewar Lubna.

      Zulfa tai saurin faɗin, “Ta hanyar Aunty Suhailat mana, tunda nasan za'a gayyaci Daddy dan abokinsane babanta”.

      “Kai amma naji daɗin harkarnan gaskiya, saimu bada himma da shiri na musamman”.


★★★★★


      Sosai su Meenal ke shirin bikin ɗan gata, abin ba'a cewa komai, sam babu mai saka Basiru a sabgar, idan kinga an nemesa wani abu za'a sayo, sai a bashi mota yaje ya sayo, musamman Baban Meenal, motsi kaɗan sai yace a bama Basiru ya sayo masa kaza, tun basiru na ɗaukar hakan girmamawa harya fahimci ƙasƙantar dashi kawai akeyi, duk ma'aikatan gidan ace anrasa ɗan aika sai shi, wannan abu yamasa matuƙar ciwo.

     A haka aka fara gudanar da events, da yake na gidan mata aka fara sai bai halarci ko ɗaya ba, Meenal ma tamasa wahalar gani, tsakaninsa da ita saidai takira tamasa gargaɗi akan ya kula da kansa, wlhy karta ganshi da wata, inko hakan ta kasance wlhy duk abinda ya biyi baya shine yaja.

      Cikin haushi da hasala ya gimtse wayar, dan kiran ma datai masa yanzu kenan, a fili yace, “Wlhy zan koya miki hankaline, bar ganin ina sonki”.

    Oho batasan yanaiba ma ita, dan daga can ta ɗaukama itace ta fara gimtse wayar ba shiba.


        A ranar juma'a su Suhailat suka iso gidan gwamnatin katsina ita da Daddynta dasu Lubna.

    Kasantuwar abotace tunta secondary a tsakanin daddyn Suhailat da Abban Meenal saiyay murna sosai daganin harda iyalansa, da kansa ya kira Meenal a waya ya haɗata da su Suhailat a zuwan ga ƙawaye, dan bazasu wuce sa'anni ba.

     Ganimsu suma fa manyan yarane sai meenal ta amshesu hannu bibbiyu, dama ita ALLAH bai yita mai yawan tara ƙawayeba sam.

           Duk wani motsin Meenal akan idansu Suhailat yake gudana, sunata baza ido suka Baseer yana fantamawa sai sukaga bulum, koma ƙyallinsa basu ganiba acikin hidimar bikin.

        Sai dai cikin sauƙi suka ɗauki Number sa da    Meenal ce kawai tasanta, saboda kuma tai saurin kamashi idan har yanacin amanarta yasa ta bashi kayin tare da shinfiɗa masa dokoki tunda suka dawo.

     Bai musa mataba a lokacin yace yaji ya kuma gani.

          Kowaccensu tai saving Number a wayarta, sauran aiki kuma Abu ne zai ƙarasa musu insha ALLAH.


        Basuga Baseeru ba sai ranar dinner, yana nane da Meenal data hanashi rawar gaban hantsi, gashi ƙyawunsa da gayun da yayi yay bala'in tafiya da ƴammatan wajen.

          Zaune suke a tabiri ɗaya shi da Abu da meenal ɗin, sai su Suhailat dake can bayansu saboda kowacce kujera mutum huɗu ce, kasantuwar Meenal bata buƙatar kowa tare dasu yasa su suke zaune su uku.

        Zulfah dake charting da Abu ta turo masa wani sabon saƙo.

      A kaikaice ya ɗaga kai ya kalleta, tai masa signal da ido.

     Murtani ya maida mata yana gyara zamansa.

       Meenal ce taja hannun Basiru suka miƙe saboda itace takeso ta farama amarya da ango da suka taso liƙi.

     Abu yay saurin janye wayar Basiru dake a saman tebir ajiye.

    Koda basiru ya laluba baiji wayarba sai kawai yabi meenal gudun karta dizgashi, ga Zulfah da tun ɗazun idonsa ya sauka a kanta, yasha matuƙar mamakin ganinta, dama kawai yakeson samu yaji miya kawota wajen? Tanada alaƙa dasu meenal ne kokuwa danshi tazo?.

     Cikin dabara Abu ya miƙama Lubna wayar ta baya, dan itace a kusa dashi.

     Sauri-sauri sukayi duk abinda suke buƙata da wayar, sunyi copy ɗin abubuwa da dama na ciki, sannan suka loda masa hotunan ƴammata, harda wanda yayi da wasu ƴammatan da Abu ne yayta jan ra'ayinsa sukeyi, amma sai baya yarda asa a wayarsa sai iya na ƴammatan kawai.

     Gaba ɗaya Abu ya rikice ganin Basiru da Meenal sun gama sun doshi hanyar dawowa, ya zunguri Lubna da itama taketa yarfe hannu saboda abunda suke Copy ɗin bai gama shigaba.

     Harsun zauna Basiru na laluben wayarsa sai MC ya kuma kiran sunan Meenal, hakan yasa ta kuma miƙewa tareda kama hannunsa suka koma.

    Ajiyar zuciya Abu ya sauke, hakama su Suhailat, bawai dan sunajin tsoroba ne, sundai fi son komai su bisa ta siyasa sai yafi shigar basiru, tunda shima hakan yay musu, bayan sun gama wayar suka goge da handkherchief, ahaka Aby ya amsa shima yaje wajen rawar, cikin hikima ya jefama basiru wayarsa aljihu.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


           Duk da ba kowa yasan da ɗaurin aurenba saiga mutane sunɗan taru. musamman ma dasu aunty Ummy suka ƙaraso, sai gidan ya sake ƴar cika.

      Gaba ɗaya sai Ummu taji ta takura, musamman da Aziza tazo suka sakata gaba itada Bily, dan tsaf Bily ta zayyanema Aziza abinda ta gani, harma da sharri ta ƙara.

    Tun Ummu na tanka musu harta tsaresu.

    Koda su Aneesa suka zo wai gaidata bata nuna musu komaiba, sai dai kuma bata wani sake musu ba sosai.

    Hakan saiya ƙara mata ƙwarjini a idonsu, harma zukatansu suke jin shakkarta, aransu kam ƙiyastawa suke Yayansu ya samu dai-dai shi.

    Inda adane wani yace musu Ummukulsoom ƴar aikin gidansu zata koma haka saisun ƙaryata, su dama suka tashi a birnin, cikin gatan da wayewar da sukeji da ita duk sai suka raina kansu a gabanta, dan ita wayewar tata mai aji ce, bawani rawar kai ko shirmen rashin tarbiyya da rashin wayo, komai nata anutse yake, takan girmama Addininta da al'adarta koda a magana ne fiye da wayewar da mutane ke ɗauka ƴan boko keda ita.

     Sunata zuba hira dasu Bily amma ta share kowa tanata danne-dannen lap-top ɗin Yaya Zaid data amso tana wani bincike, inhar ba wanine ya ambaci sunanta a ɗakinba da sigar tambaya bata ko kallonsu, shima saita zaɓa wanda taga zata iya amsawa, wani kam sai dai tai murmushi kawai ta ɗauke kanta.

       Sun ɗanyi hotuba a waya zuwa gab da magrib kowa ya kama gabansa, sai gidan yay tsit, dan Aziza ma ƙin zama tayi, wai ita kunyar surukai.

       (Sai yau Ummukulsoom takejin zancen ashe yaya Zaid Aziza zai aura, kuma da ƙulla maganar bai gaza wata biyu da wasu satittikaba, gab da za'a kai kuɗinnan ne ma hakan ta faru, ko lokacin da Amaan ya bayyana kanshi da fuskar A-waheed ashe kuɗin Zaid gidansu Aziza aka kaisu, Zaid kuma shiya zaɓi a ɓoyema Ummukulsoom wannan zance bisaga wani dalilinsa can, shiyyasa bata taɓa saniba sai yau).

     Sosai taji daɗin wannan haɗi, koba komai wani zumincin mai ƙarfi ya kuma ƙulluwa tsakanin dangin mahaifiyarta dana mahaifinta.


*_WASHE GARI_*

 

       A yau sukai niyyar komawa amma sai Abba ya hana akan wani dalili, yace su bari sai gobe lahadi saisu koma tunda dai babu makaranta.

     Wannan dalilinne ya saka su Ummukulsoom shan barcinsu suka ƙoshi  har tashin hantsi.

     Ummukulsoom ce ta fara farkawa, gidan tsitt babu wata hayaniya, dama sunsan Abba da Attahir da Zaid zasuje wajen wani ɗaurin aure, Ummi da maman Ahmad kuwa sun fita karɓo kayan gyaran jiki da Ummi keson su Ummukulsoom su fara idan sun koma legos, hakan yasa daga Bily sai Ummukulsoom kawai a gidan........✍🏻


NO. 44


..........Sai kusan ƙarfe ɗaya su Ummi suka dawo gidan, lokacin itama Bily ta tashi suna kicin suna haɗa abincin rana da ƴar hirarsu.

    Ummi data shigo tana faɗin, “Ummm autocina duk kun cika mana gidan da ƙamshi”.

    Dariya sukai suna juyowa, duk sukazo suka rungumeta suna mata sannu da zuwa.

       Sai da ta buɗe komai taga mi suke girkawa sannan ta fita danta watsa ruwa.

     Ummi na fita maman Ahmad ta shigo, dama kunyar Ummi ta sata maƙalewa.

      “Habawa yara, inacan inata tattalin yanda za'a shiryaku amma na dawo ko ɗan ruwa baku kawo minba?”.

       Dariya duk sukayi, Bily tace, “Aunty wai dan ALLAH ina kukaje?”.

         “Gidan wata hajiya ce wlhy, kai-kai angunan nan zasu more fa, yara ina tausaya muku”.

           Kafin su bata amsa yaya Zaid ya shigo. Sannu da zuwa sukai masa.

   Ya amsa yana buɗe firij ya ɗauki ruwa da faɗin, “Wai dan ALLAH baku gama abinci ba? ALLAH yunwa nakeji.

    Cikin tsokana Ummu tace, “Tofa, yaya Zaid kuda kukaje kuka ciwo kajin ɗaurin aure?”.

        “Kajin wahala ba, wanifa ƙauyene can Abba ya kaimu, ni bammasan miye dangan takarsu ba, ko ruwa ban shaba harmuka taho, garama Ameer da Yaa Attahir sunsha fura, dan su dama mayun tane”.

           “Oh wai harda Yaya Ameer kukaje?” cewar Bily.

     “Eh, harma da Dad da yaa Amaan da Bassam fa”.

      “To, to ALLAH ya sanya alkairi”.

     “Amin dai, ammafa naci dariya, kunga angon kuwa? ALLAH Bassam ya girmesa sosai, bai wuce 20years ba”.

         Maman Ahmad tace, “20years fa? Kai Zaid banda sharri”.

     “Wlhy babu wani sharri Aunty Hafsat, bara kiga hotonsa”.

   Wayarsa ya zaro ya miƙa musu bayan ya lalubo hoton, sai mamaki sukeyi, amma banda Ummukulsoom da tai murmushi kawai, dan ita wannan ai ba sabon abu bane a wajen ta, garinsu har ƴan 18 yima aure ake kuma maza.


     Ranar dai yini sukai a gida suna shan hira hankali kwance.

    Sai washe gari da yamma suka koma legos tare da tarin kayan gyaran jiki da Ummi ta haɗasu dashi, sai maganin sanyi da aganinta shine mafi muhimmanci a garesu, garama Ummukulsoom ita ance ta fara shan wasu kayan ƙarin ni'ima dana matsewa, dan ita Ummi duk zatonta Ummu tasan komai tunda dai an kaita gidan miji.

    Sai dai koda suka dawo sai Maman Ahmad bata bataba, dan tasan ita dai yanda Ummukulsoom ta rayu a gidan Amaan a wancan zaman.


    Su Ummukulsoom ba tare suka dawo da Amaan ba, shi sai safiyar litinin ya dawo saboda wani uzuri daya tsaidasa na zuwa Ajiwa.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


           Washe garin litinin da wuri Ummukulsoom tai shirin makaranta, tea kawai tasha a tsai-tsaye, shima sai da Maman Ahmad tai mata jan ido, tana gama sha ta miƙe ta tattara kayanta domin tafiya.

     Sanye take da doguwar riga ja mai taushi, rigar robace, dan haka ta ɗan kama jikinta, amma ba sosai ba, sai dai saboda kasantuwarta mace mai cikar halittar jiki za'ai saurin fahimtar yanda rigar tabi jikinta, gyale baƙi madaidaici ta naɗa a kanta.

     Maman Ahmad nason mata maganar ta canja gyale sai ta shafa'a har Ummukulsoom ta fice.

     Abbas ta iske a ƙofar gidan Attahir tsaye jikin mota.

    Cike da girmamawa ya gaisheta, ita harma abin yaso bata mamaki, sai dai bata ja zancenba tai shirin wucesa.

     “Uhm auntyn mu ai nine zan kaiki”.

     Juyowa tai tana kallonsa da mamaki, kamar bazatai magana ba sai kuma tace, “A'a Abbas nagode wlhy kaje abinka, dana fita zan samu taxi”.

         Ganin zata cigaba da tafiya yay sauri cewa, “Ai boss ne yace a kaiki”.

     Tsaf ta gane wanda yake nufi, kuma tajishi sarai, amma saita share tai gaba abinta tamkar bata jiba.

      Abbas ya rasa yanda zaiyi, sai kawai ya zuba mata idanu harta fara nisa.


          

★★★★


     Cikin nutsuwa take tafiya tamkar yanda ta saba, wanda bai mata farin saniba saiya ɗauka yanga ce ko salon iya shege, amma sam ba haka baneba, tunma ba yanzu ba wannan shine asalin takun tafiyar Ummukulsoom tun tana a Ɗilau, tana tafiya tana kallon agogo, fatanta ta fita daga Barrack ɗin akan lokacin kawai.

         Cak ta tsaya ganin ansha gabanta, ta ɗago a fusace dan son ganin wane ɗan iskane? Dan ita ba sakarma mazan Barrack ɗinnan fuska takeba.

         Tsaye yake a ainahin sojansa, da alama daga motsa jiki yake, dan sanye yake da kayan training na Adidas farare tas, fuskarnan a ɗaure babu walwala kamar ko yaushe, duka hannayensa biyu zube a aljihun wando, sai earpiece daya maƙala a kunne wanda batasan mi yake jiba.

     Duk da taji wani iri sai ta janye idanunta itama tana kuma ɗaure fuska ta ratsa ta gefensa zata wuce.

      Hannunsa dake cikin wanda ya zaro tare da kamo nata ya maidota gabansa yana kuma haɗe fuska.

      Waige-waige Ummukulsoom ta fara, babu yawan mutane sosai, amma akwai ɗaiɗaikun sojoji irinsa masu fitowa motsa jiki da sanyin safiya, yanda baiyi magana ba itama sai bata tankaba, sai hannunta da take kici-kicin ƙwacewa wani haushi na kuma cikata, gashi yanata ɓata mata lokaci.

         “Banason abinda kakemin wlhy, ka sakarmin hannu malam”.

     Banza yay mata tamkar bai jiba, baikuma sake mata hannunba, sai da ya shaƙi iska ya fesar sannan ya watsa mata manyan idanun nan nasa masu matuƙar tasiri a gareta, itama hararsa tayi ta ɗauke kai.

       Murya ƙasa-ƙasa yace, “Ki koma ki canja waɗannan kayan, kokuma ki fasa zuwa makarantar, kuma daga yau Abbas zai kaiki ya ɗakkoki, ya rage naki kiyi yanda nace, kokuma kiyi naki tsarin”. ‘Ya ƙare maganar da sakin hannunta yay gaba abinsa ko wai-wayenta bai sake yiba’.

           Harara tabi bayansa dashi, itama ta juya taci gaba da tafiyarta batare da ta koma ɗinba.

          Tana tsaye a hanya danta samu taxi, mota tazo ta tsaya a gabanta, ƙin ɗaga kai tai ta kalli motar balle wanda ke a ciki.....

     Jitai kawai an fisgeta an tura a motar, tana niyyar yin ihu ya maida murfin ya rufe ya zagaya mazaunin driver ya zauna.

       yana shiga ta buɗe zata fita, fisgota yayi ya maida murfin ya rufe tare da saka luck.

    Duk yanda taso haɗiye kukanta ta kasa, saida hawaye suka silalo mata a kumatu, hankalin sa dake kan tuƙine ya hanashi ganin kuka take.

     Ita kuma taƙi kallonsa, takumaƙi magana dan zuciyarta a maƙoshi take.

     Har suka isa makarantar babu wanda ya tankama ɗan uwansa, kowa ya ɗauke kai ya haɗe fuska.

      Koda yay fakin sai bai cire luck ɗinba, hijjab ɗin dake bayan motar ya jawo ya ɗora mata akan cinya, cikin kakkausar murya yace, “Wlhy wannan yazama first and last da zan miki magana kiyi ignoring ɗina, dan zakisha wahalane wlhy. Fitarmin a mota”.

       Ko kallon inda yake bataiba ta buɗe ta fice abinta.

    Shikuma yaja motar tare da bula mata ƙura ya bar wajen.

     Tsaki Ummukulsoom taja tana harar hijjab ɗin, ta tsani mulkin mallaka a rayuwarta, wlhy badan furucin baba a kantaba da bazata sakaba sai taga yanda zaiyi.

    A fili tace “Sai shegen zuciya da faɗin rai kamar kuturu”.

     Hijjab ɗin ta warware ta saka kafin ta karasa class.



         Tun daga wannan ranar Abbas ya koma kaita maƙaranta, dan Attahir da kansa ya kirata yay mata faɗa akan hakan, yakuma ja kunnenta akan kayan da zata ringa fita dasu, dan ya kula ran Amaan yakai ƙolluwar ɓaci da abinda Ummukulsoom tai masa aranar, ba komai ya hasala shiba kuwa sai kishi mai tsanani da ya dade da karantar Ajiwa na dashi.

         Tabi dukkan shawarar Attahir kuwa, danshi matsayin uba yake a gareta, sai dai kuma bata sake ganin Amaan ba tun ranar, bata damuba, dan ba buƙatar ganinsa takeba, hankalinta ma gaba ɗaya yana kan exams ɗinta da yazo gangara.


      Tana saura kwana biyu ta kammala exams Attahir da Amaan sukayi tafiya.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


            Biki ya tashi lafiya su Suhailat dai basu kai ga komawa ba sai yau, taget nasu na gaba shine haɗuwar Zulfah da Basiru, dan haka suka sanya Abu duk yanda zaiyi yayi ya saka Basiru fitowa gida a yau.

     Kasancewar Suna tare da Meenal sai Abu bai wani sha wahala akan hakanba.

     Wajen wani hutawa na ƴaƴan manya sukaje, tunda suka shigo Zulfah na kallonsu, tana zaune a rukunin kujeru nacan gefe tana danna waya da shan Ice-creem.

     Kusan mintuna goma da shigowar su taga sun nufota, ɗauke kai tai tamkar bata gansu ba, Abu ne ya fara jan kujera ya zauna a wajrn yana faɗin “Assalamu alaikum, ƴammata ko zamu iya zama dan ALLAH”.

     Saida taja lokaci kafin ta amsa masa batare data kallesu ba.

      Basiru kam Uffan bai ceba, yama ɗauke kansa gaba ɗaya shima, shi adole mai aji mijin ƴar gwamna😝.

     Suna zama Zulfah ta miƙe tana tattara kayanta.

   Da sauri Abu yace, “Haba ƴammata ya zaki gudu? Komun takuraki ne?”.

    “Kusan haka”. Ta faɗa cike da yanga da salo.

    Hakanne ya saka Basiru ɗagowa yaga wace uwar iya ce.

     Cikin tsantsar mamaki yace, “k!”.

     Kallonsa tai itama tamkar yanzu ne ta gansa, ta ɗan fido ido, “Oh wai kune?”.

      Shima Abu saiya washe baki, “Lah ashema Friend ɗinmu ce? Ni ai bamma ganeki ba, Please zauna to”.

    Komawa Zulfah tai ta zauna tana wani shegen murmushi, musamman da taga basiru ya kafeta da ido.

      “Haba Friend daga ranar kuma saiki ɓata ɓat?”.

          Murmushi tayi batare da tace komaiba.

   Hakan yasa ta kuma birge basiru, amma saiya basar, cikin gadara yace, “Bani Accaunt Number naki na maida miki kuɗinki na ranar”.

      kallonsa tai tana wani narke murya, “Babie ai ni duk abinda na bada ya badu, bana taɓa jeka ka dawo, sai dai kaimin tukuyci da Number wayanka”. Ta faɗa tana zare wayarsa dake hannunsa.

    Sosai gabansa ya fadi, dan wayar da Number meenal ce kawai a ciki ta amsa.

     “Uhm kinga kawo na baki wannan” yay maganar da kai hannu zai karɓa wayar daga hannunta.

    Gocewa tayi tana wani munafikin murmushi da ita kaɗai tasan fassarar kayanta, “Saboda banida muhimmanci ko? Toni wannan itace tafi kwantamin arai”.

     Dama tanada Number, sai kawai ta saka tata tai save, takuma shiga inda bazai taɓa blocking nata ba, harda wasu tarkuna ta kafa masa, dan zulfah mayyace a wajen sanin sirrin waya.

    Wayar ta miƙa masa tana faɗin, “Thanks babie”.

    Bai iya cewa komaiba, dan shikam ko motsima ya kasa yi.

    Hirarsu suka cigaba dayi da Abu kusan awa ɗaya kafin tai musu sallama ta tafi. 

     

★★★★


    Washe gari suka koma gida, tun daga lokacin kuma suka tasa rayuwar basiru gaba ta waya, musamman a chart, duk wadda tai masa magana kuma a cikinsu saita nuna masa Meenal.

     Yasan halin Meenal da shegen siyan layikan waya kamar dangin ɓarayi ko kidinafa haka take. Sosai yake sakin jiki da kowaccensu suna hira har maganar banza ta shigo.

    Shiko daɗi yakeji Meenal ta dawo gareshi, tana zuba masa kalaman soyayya fiyema da na da.

     Zulfah kuwa idan tai masa magana ba sosai yake kulata ba.

 

     Sam Meenal batasan wainar da basiru ke toyawa ba, dan ba zaman gidan takeba, kullum abun natama ƙara gaba yakeyi, mantawa ma take da waji aure dake a kanta kwata-kwata.

       

           Gobe ta kasance valentine day, dan haka Meenal tazo gida ta kwana a tsarinta da shirinta gobe su fita yawon shakatawa itada Basiru, su more ƙuruciyarsu saboda muhimmancin wannan ranar a garesu (ƴan Boko zalla kenan🤣😝, da zaka tambayesu rana mai muhimmanci a musulunci bazasu faɗa maka ko ɗaya ba🤦🏻‍♀️, amma kowacce rana ta yahudawa sun santa, ALLAH ka rabamu da koyi da abinda zai halakar damu🙏🏻😢).

           Kafin ta iso gida sukai charting sosai da Suhailat da Lubna, duk kuma akan valentine day ɗin, shikuma duk ɗaukarsa Meenal ce, (ɗan daƙikiya kenan🤣😝).

      Haka itama zulfah ta turo masa massege, da yake yanzu yana ɗan kulata sai suka gaisa.

        Sai yamma Meenal tazo gidan, suka rungume juna itada basirun ta, tare da faɗawa wata sabuwar duniya, baiyi zaton samun yanda yake soba, amma a mamakinsa sai gashi ta basa kanta cikin sauƙi suka more.

     Ranar haka suka kasance cikin farin ciki a har wayewar gari. Da safe ma bayan sunyi sallar asuba a makare suka dawo falo suka baje suna hutawa da ɗanyin hira, daga nan aka fara canja salo, daɗi ya kama basiru ganin yanzunma dai Meenal ta saki jiki......

      Knocking ƙofa da akaine ya katse musu hanzari, Meenal dake a samansa ta sauka tana gyara igiyar rigarta, ta zata ko saƙon da ta bayan ai matane ya iso. Har Basiru zaice tabarsa ya buɗe sai kuma yay shiru..

     Koda ta buɗe sai taci karo da baba mai gadi riƙe da ƙatuwar rose flower and quisqualis da akaima shiri na musamman a cikin farar leda, sai ɗan kwali na alamar gift🎁.

       “Wannan fa?” tafaɗa a yatsine ba tare da ta amsa gaisuwarba.

     Cikin ɗan rawar jiki yace, “Hajiya watace ta kawo tace a bama Alhaji”.

       “Wata?!!!!!”

Ta faɗa cikin matuƙar hargagin da yajawo hankalin Basiru gareta.

   Karɓa tayi dan son tabbatarwa, ta juyo cikin falon sukaci karo da basiru daya taso, bangajeshi tayi ta zubar da flowers ɗin a falo ta fara ƙoƙarin buɗe🎁.....



🤼‍♀️🤼‍♀️🤼‍♀️🤼‍♀️🙊⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️masoyan basiru.😂😝



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


            Cikin nasara su Ummukulsoom suka kammala exams, farin cikin data tsinci kanta a ciki ɓata lokacine, a randa suka gama a ranar da daddare su Attahir suka dawo, sai dai idonta baiga Amaan ba.

    


*_WASHE GARI_*


       Sanin gidan babu kowa ya saka Ummu fitowa kanta tsaye, sanye take da kayan barci farin wando dogo da riga pink wadda ta lafe a jikinta mai gajeren hannu, sai hula, wata baƙar yunwa ta tashi da ita kasancewar jiya tayi barci da wuri bataci abinci ba, gashi har takai kusan 11 tana barci tunda tana fashin salla.

        Kicin ta nufa kanta tsaye da addu'ar samun abu mai sauƙi, ganin babu wani abinci ta dafe kanta, yau maman Ahmad tea kawai tasha ta fita aiki, dama inhar Attahir baya gida bata zaman haɗa breakfast, tana zaton kuma shima tunda safe ya fita, Bily ma ta fita wankin kai.

      Tukunya ta ɗaukko zata ɗora noodles, gabanta ya faɗin jin ƙamshin turarensa, gakuma alamar tsayuwar mutum da taji tabbas a ƙofar kicin ɗin, tamkar mai ciwon wuya haka ta juyo dan tabbatarwa.

      Tsaye yake a sojansa, ya harɗe hannayensa duka a ƙirji, fuskarnan tamau babu alamar fara'a, busashen yawun daya tsaya mata a maƙoshi ta haɗiye tareda ɗauke kanta tamkar bata ganshiba, tahau ɗauraye tukunya.

        Cigaba yay da kafeta da mayun idanunsa, a ransa yana ƙara wadatuwa da mamakinta, wai ƴar tatsitsiyar yarinyar nan da aka kawo masa legos ce a gabansa haka?, ya lumshe fararen idanunsa ya buɗe akanta, kafin ya taka a hankali zuwa inda take a gaban gas tana shirin kunnawa.

       Jinsa dab da ita yasata rimtse idonta zuciyarta na ƙara gudu, amma sam ta dake a fili taƙi nuna masa hakan, saima cigaba da hidimarta da take.

       Tattausan hannunsa taji a saman nata dake ƙokarin murɗa gas, numfashinta dake neman ƙwacewa tai azamar fisgowa tareda yun ƙurin barin wajen.

      ya sake matse mata hannu a cikin nashi tareda fisgota ta dawo ƙirjinsa, idanu ta rumtse kafin tafara tureshi, “Wai miyasa kakemin hakane? Nace maka banaso niba ƴar iska baceba”.

      Ko motsi baiyiba, har yanzu kuma fuskar na nan tamau, sai dai a ƙasan ransa dariya ƙarfin halinta ke bashi......

      “Sakemun hannu”. Ta faɗa cike da tsiwa.

       Banza yay mata, sai ma kuma mannata da jikin dirowa ɗin kicin ɗin da yay, yasa hannu ɗaya ya ɗago haɓarta, yayinda ɗayan kuma ke rike da duka hannayenta a baya, kallon ido cikin ido sukaima juna, wasu abubuwa yake zuba mata dake neman karya garkuwar jarumtarta, tai azamar lumshe idonta tana tura masa baki da ƙokarin ƙwace hannunta...........✍🏻


NO. 45


............Matso da fuskarsa yay daf da tata tamkar zai haɗe bakinsu, sai ya buso mata numfashinsa a kan fuska.

      Zuƙa tai ta haɗiye tana kuma tunzuro baki,  yasa yatsansa manuniya ya ɗalli bakin kaɗan, yana faɗin “fine girl nagani ai, amma ba zanyi ba, niba ɗan iska bane”. 

      Babu shiri Ummukulsoom ta waro idanu sosai a kansa, tare da azamar maida bakinta da sauri, saboda zafin da taji da kunyar furicin da yay.

      Shikam tuni ya ɗauke kansa tare da basarwa tamkar bashi ya faɗa ba.

     Dole ta sadda kanta ƙasa dan harga ALLAH bata taɓa jin kunyarsa ba irin yau, sosai furucinsa ya kunyata ta, ita sam bada manufar da yake nufi ta turo baki ba wlhy......

       Amaan daya kafeta da ido yana nazartar ta ya lumshesu ya sake buɗewa a kanta tareda sakin hannunta ya dafe dirowar yanda dai bazata gudu ba, “Karki zurfafa tunani, tunda kinaso zo nai miki matar Usman Ajiwa”. Yay maganar da matso da bakinsa kusa da nata.

    Babu shiri Ummukulsoom ta turashi tanason barin wajen, taga yau salon taɓara da bata kunya yakeji kawai.

        Saka ɗayan hannunsa yay a ɗayan gefen, ta ɗago ta kallesa fuska a ɗaure saiya ɗaga mata gira ɗaya cike da wani salo “K Haka zaki ringa tarbar naki mijin idan ya dawo daga tafiya?”. Yay maganar cikin wata ƴar shagwaɓa da narke murya.

     Janye idanunta tayi tana ƙara mamakinsa, fuskar dai a tamkenta take babu walwala, amma kuma sai iya shege yakema mutane tamkar ba shiba, ta ya mutse fuska cikin salon tura masa haushi tace, “Kanada matsala wlhy malam”. 

     Shiru yay bai amsata ba, ya dai kafeta da mayun idanunsa hannayensa harɗe a ƙirji.

     kallonsa tai Ƙasa-ƙasa ta janye idonta, mamakin yanda maƙogwaronsa daya fito sosai a wuyansa yake motsawa alamar akwai magana a ransa, take jinjinawa, a zuciyarta tace, “Miskilanci baiyiba wlhy”.....

        A fili kuwa saita marairaice masa, dan ta kula buyaginta bazai fiddata ba, ga yunwa na cinta.

       “ALLAH yunwa nakeji” ta faɗa cikin langaɓe kai idanunta na tara ƴan ƙwalla da suka ƙara musu ƙyalli da girma.

    Karon farko da ya sakar mata lallausan murmushi mai cike da ma'anoni masu yawa da tunda take bata taɓa ganinsa a kan kamilalliyar fuskarsa ba.

     “Ya salaam” ta faɗa a hankali saboda wani cikar haiba da kamala daya ƙara mata, sai taga kamar da gayya ma yay murmushin.

      Matsowa yay gabanta kaɗan yakuma ƙara kusanci a tsakaninsu har sunajin saukar numfashin juna. cikin raɗa yace, “Zan tabbatar miki nafi haka matsala ƴammata, amma sai nan gaba kaɗan”.

        Babu shiri Ummukulsoom ta lumshe idanunta saboda wani yarr da taji a jikinta.

    Shima ja yay da baya, yana nuna mata hanya alamar ta wuce.

    Cike da sassarfa tabar wajen tana ambatin Alhmdllh. Tukunyar ta ɗauka ta cigaba da hidimar ɗora noodles ɗinta.

    Shikuma ya jingina da bango tareda da harɗe hannayensa a ƙirji ya zuba mata idanu.

    Gaba ɗaya Ummu ta takura da zamansa, tare da kallon daya kafeta dashi babu wani risinawa ko basarwa kamar yanda yakeyi a da.

      Kasa jurewa tayi, dan aikin na neman gagarar ta gaba ɗaya, sai yin komai take a ɗan rikice.

    Guntun murmushi yayi yana janye idonsa cikin Basarwa, a ransa yace, “A shema Matsoraciya ce”.

     A fili kuwa saiya maida idanunsa kanta, cike da haushin wannan kallon ƙurulla ta ɗago nata manyan idanun ta kallesa, caraf suka haɗa ido, Ummu ta ɗan hararesa.

       luuu yay da nasa zai lumshe amma saiya buɗe batareda ya rufe ɗinba akanta, itama saita  janye nata ta maida ga girkinta tana ƙunkuni ƙasa-ƙasa yanda bazai jiba.

    Wani murmushin gefen baki yayi ganin yanda takeyi, ko wane motsinta sake tsundumasa a ƙaunarta yakeyi.

      Ummukulsoom data shareshi tana cigaba da aikinta takuma ji a jikinta ido na yawo a kanta, juyowa tai ta sake kallonsa, sai caraf suka sake haɗa idanu.

    Shine ya fara janye nasa, ita kuma ta ƙwaɓe fuska, “Nifa bana son kallo, dan ALLAH ka fita karma wani ya dawo ya ganka”.

     Yanzu kam sosai ya ɗago ido ya kalleta tare da lumshesu da buɗewa lokaci ɗaya, kamar bazai yi magana ba sai kuma ya gyara tsaiwarsa sosai yana mai fuskantarta gaba ɗaya, saɓanin da daya karkata kaɗan, “Idanma na kalleki ai sadakina na kalla ko madam?”.

     Kasa bashi amsa tayi ta ɗauke kanta gaba ɗaya, bata sake kallon inda yakeba harta kammala ta juye a filet, ta ɗakko ƙwai zata fasa. 

     Yace, “Hummm”.

 Juyowa tai ta kallesa amma sai ya basar kamar bada ita yakeba, itama ɗauke idanunta tai taci gaba da abinda takeyi.

      Kiransa da akai a wayane ya sashi fita yana amsawa, Ummukulsoom ta sauke ajiyar zuciya tana harar bayansa, a ranta faɗi take wannan irin takura har ina.


     Ƴar hayaniyar da tajiyo a falo ce tasata jin daɗi, dan kamar maganar Attahir, cike da ƙwarin gwiwa ta fito ɗauke da indomie ɗinta, ta sauke ajiyar zuya ganin Bily ma ta dawo, ga Yaa Attahir ma, Amaan na zaune har yanzu yana waya, ido suka haɗa tai saurin janye nata tana gaida Attahir da basu haɗu da safe ba.

     Ɗakinsu ta nufa dan tasan bily na can.

     Bata sake jin ɗuriyarsa ba dan ƙin fitowa tayi, shi kuma bai nemeta ba, dama akwai abinda ya kawosa gidan ya zauna zaman jiran Attahir ne.


    Kwanaki biyu da faruwar haka ya wuce kd, ita Ummukulsoom ma bata saniba, sai da daddare tana duba masseges a wayarta taga saƙonsa.

       _“Congratulations da gama exams my happiness, Naje KD, zankuma zauna har sai an bani matata sannan na dawo lagos, ki kula min da kanki dan ke ta Usman Mahmud Ajiwa ce shi kaɗai har a aljanna insha ALLAHU”_.

      Karan farko da tai murmushi akan saƙonsa tun bayan gane shine A-Waheed, ta lura indai a rubutu ne akwai zaro magana, ta bakine dai ya zame masa abu mafi wahala. ƙin masa reply tayi, ta cigaba da harkokinta hankali kwance.


★★★★★

         Sosai Maman Ahmad ta dage gyara su Ummu, dan dukkan kayan gyran jiki da kowanne fanni an dage musu, maganin sanyi kam tunda suka dawo dama suke shansa kala-kala, duk sunyi ƙyau da ƙara murjewa, kowa ya gansu yaga amare ƴan gata, su kansu sunaji a jikinsu sun canja.

    Biki ya matso gab dan kwanaki biyar kawai ya rage, dan haka washe garin da zai zama saura ƙwana huɗu su Ummukulsoom ke shirin wucewa kd, duk kuma sai jikinta ya fara yin sanyi, hakama Bily duk ta zama wata shiru-shiru, rawar kan nan duk yanzu babu shi, aiko Ummukulsoom saita samu damarta yanzu, haka zata zauna taita tsokanarta, tun Bily na iya maida murtani har ta bari, ashe haka akeji idan auren ya kusanto?.


  

⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


         Key ɗin motane ya faɗo mai matukar ƙyau da tsada, dan motar da ake yayice daga wane sai wane, sai ƴar takarda a tare da key ɗin.

      Meenal ta kalli Basiru dake tsaye yana kallonta hankaki kwance, danshi dai a saninsa bai aikata wani laifi ba.

       *_“Happy Valentine day my Handsome, i love you so much har ƙarshen rayuwa, wannan key ɗin motar tukuycin farin cikin da kabani ne jiya, danka shayar dani zumar danasan ko matar nan taka bata taɓa samuba, dolene kasamu tukuyci mafi tsada daga gareni. Ka duba wayarka na turo maka saƙo....”_*

       Kasa ƙarasa karantawa Meenal tayi, ta dage iya ƙarfinta ta zubama Basiru mari tana huci.

    Da sauri yasa hannu ya dafe kuncinsa baki buɗe, “Meenal ni zaki mara? Rainin har yakai ki ɗaga hannu ki mareni?”.

     “An mareka, kai wanene banda banza a banza, baƙin munafuki, to yau ALLAH ya tona asirinka”. Ta ƙare maganarda fisge wayarsa ta shiga bincike.

     Sosai jikinta ke wani irin tsuma da rawa, hawaye masu zafi suka wanke fuskarta, ta nunashi da ɗan yatsa tana ja baya, “Basiru yanzu nan har takai ka dinga ɗaukar jikinka kana turama karuwai? Dama haka kake daƙiƙi ban saniba.....”

     “K dalla banason hauka, ubanwa nake turama wa idan bakeba, naga kullum kece kike cewa na tura miki saboda kina kewat.....”

     Wani marin ta kuma sauke masa, kafin ya dawo hayyacinsa ta sake zuba masa wani,  sosai Basiru ya gigice, babu shiri ya kai mata duka itama, dan ankai bigiren da bazai iya jurewa ba.

       “Kutumelesi, lallai bakada hankali, harni zaka doka ɗan matsiyata” meenal tayi maganar tana ƙwala masa wani ɗan abun kwalliya dake sam center table ɗinsu.

     Kansa ya dafe yana layi, kafin ya fisgota cikin zafin nama shima ya hau jibgarta.

    Iyaka iyawa meenal ke zabga ihu itama tana kai masa duka, baba mai gadi daya iso da gudu saboda jin hayaniyarsu duk saiya ruɗe ya rasa ina zai nufa, fita yay da gudu neman mutane, hakan yay dai-dai da shigowar motar Su'ada yayar Meenal. a ƙofar gida ta faka motar ta fito hankali tashe saboda ganin yanda mai gadi ke tsaidata.

     “Kai lafiya kuwa?”.

 “Hajiya kiyi taimako Alhaji zai kashe hajiya wlhy.....”

    Bangajesa tai ta afka cikin gidan, saboda jiyo ihun meenal da takeyi sama-sama.

    Ɗane-ɗane ta iske Basiru saman Meenal yanata duka tamkar ya samu jakarsa.

    Sai da ta fara yin gajeren bidiyo sannan tasa iya ƙarfinta ta hankaɗashi gefe, lokacin meenal ta gama fita hayyacinta gaba ɗaya saboda shaƙar da Basiru yay mata a wuya. 

      Waya Su'ada tasa ta kira mahaifinsu kafin police, cikin mintuna da basu fi 20 ba saiga police tare da yayan meenal da yay aure kwanan nan.

     Duk yanda Basiru yaso musu bayani sunƙi fahimtarsa, tunma anan suka fara dukansa saboda gaddama da yaso musu, aka cukuykuyesa aka jefa a mota, ita kuma Meenal akai asibiti da ita....


   ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😞


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


            Tun isowarsu suka tabbatar da bikifa ya kankama, dan gida ya fara cika da dangi makusanta na nesa, inna laraba ma ta iso ta ɗilau da sauran dangin maman Ummukulsoom, hakama wasu daga dangin Ummi.

        Abokan wasa suka fara tasasu da tsokanar amare-amare, duk sai sukaji abun banbara kwai wai namiji da suna hajara.

     Isowarsu baifi da mintuna 40 ba saiga ƴan kawo lefe daga gidansu Amaan, ita Ummu ma abin ɗaure kanta yay sosai, lefe sai kace wani auren farko? Dan danan gida ya kacame da guɗe-guɗe, kasancewar zuwan ƴan kawo lefen Ummukulsoom babu jimawa sai ga lefen Bily itama, gidafa ya kuma kacamewa, komai sunyi abinsu akan tsari.

   Dole su Ummukulsoom suka fice gidan badan sun soba.


*_WASHE GARI_*.


     Da hantsi aka kai lefen yaya Zaid gidansu Aziza, wannan kam da Ummukulsoom akaje, taji daɗi sosai ganin ƴan uwansu na ɗilau ɓan garen babanta suma sun fara isowa.

    Sai surutu suke mata wai taji ƙyau da jiki, harda masu mata habaici a kaikaice wai shiyyasa ta guji ɗilau dan tafi ƙarfin mazajen can, (adai taƙaice suna mata shaguɓen sun san aurenta ya mutu), sarai ta fahimcesu kasan cewarta lauya, amma saita basar kamar bata fahimta ɗinba.

     Sai kuma akai sa'a Amaan ya kira wayarta dake hannun Bily a dai-dai wannan lokacin.

      Cike da tsokanar magana Bily da sam bata fahimci gugar zanarba tace, “Bestie ga mijinki na kira”.

     Duk kallon bily sukai su masu shaguɓen, Ummu kuma taɗan yatsine fuska kamar bazata amsaba sai kuma ta amsa saboda maida murtani.

   Sakin ranta tai cike da yanga tai sallama bayan ta saka wayar a hans free kowa naji.

      A hankali ya amsa tare da cewa “Inason ganin matata”.

    Murmushin ƙarfin hali Ummukulsoom tayi tana faɗin, “ba yau ba”.

    “Why?" ya faɗa a marairaice.

    Mikewa tai tabar wajen dan tasan wannan amsar kawai ta ishesu. Aiko duk sai jikinsu yay sanyi suka faɗa wasi wasin to kodai ƙarya akeyi dama aurenta bai mutuba?.

    Ita dai tuni ta koma gefe tana cigaba da wayarta da Amaan dake tambayarta kalar kayan da takeso suyi amfani dashi wajen mothers day ɗin da Momcy ta haɗa musu.

    Ita kuma ta dage akan bazata jeba gaskiya.

    Shiru yay mata bai sake tankawa ba, bai kuma yanke wayarba.

    Itama sai tai shirun tunda kuɗinsa akeci. Ƙitt ya yanke kiran ba tare da ya kuma cewa komaiba.

    Itama saita harari wayar ta koma cikin ƴan uwanta.


*WASHE GARI ALHAMIS* akai kamun amare har Ummukulsoom, da safe sukaje wankin kai da ƙunshi su duka ukun har Aziza, sai yamma lis suka dawo aka shiga taron kamu da akai a gidan Hajiya yaya.

    Babu wata hayaniya dan iya dangine na kusa suka zo kasan cewar auren duk tuwona maina ne.

      Abin ya kayatar sosai dan matane kawai a wajen, akaɗan sha kiɗan ƙwarya kowa ya kama gabansa zuwa magriba.

     JUMA'A bayan tasowa massalaci aka ɗaura auren Aziza da Zaid, sai Bilkisu da angonta Muhseen, a masallaci ɗaya aka haɗa dan kar a wahal da mutane, shiyyasa abun ya kayatar matuƙa,anguna sunsha ƙyau abin har ba'a magana.

     Hakama amare su Ummukulsoom dake a cikin gida. Zuwa yamma aka cigaba da shan karasun biki da Ummi ta shirya.

    Gaba ɗaya sai Ummukulsoom ta samu kanta da zubar hawaye, dan taji ana cewa yau ɗin za'a miƙa kowacce ɗakinta.

    Can bayan ɗakunan maman Ahmad sukaje ita da Bily suka haɗa kai sunata kuka ita da Bily, Peace da sukazo bikin da ƴan uwanta da Mom nasu tana zaune tana musu dariya, sai da ta fuskanci da gaske fa sukeyi saita koma lallashinsu, rayuwar hausawa na birgeta, inda sune amarya tata ɓarar da rashin kunya kenan da taɓara ita a dole ana bikinta, amma jiba su Ummukulsoom yanda suka shiga damuwa, sam babu wani rawar kai a tattare dasu kuma.


     Ana fitowa daga sallar magriba akace su shirya, duk sai suka rikice, sai da maman Ahmad taita lallashinsu sannan suka kimtsa, an miƙasu falon Abba inda baban Ummukulsoom da Dad da Hajiya yaya, gwaggo hinde, Inna laraba da yayyen Ummi ke zaune, daga Ummukulsoom har Bily fuskarsu a rufe take suna sharar ƙwalla.

     Bayan an fara saka musu albarka aka ɗora da faɗan bin miji da kiyaye dokonin ALLAH, aka koma kuma nasiha, kowa saida yay musu tashi a taƙaice kafin Abba ya dankama kowaccensu ƙyautar key ɗin mota yana haɗiye ƙwallarsa da ƙyar, bai taɓa aurar da mace ba sai yau, shiyyasa duk sai ya damu, ƙarfin hali kawai yakeyi. Ummi kam kasa dairewa tayi saida ta share hawaye.


      Ana idar da Sallar isha'i aka kwashi amare bayan an caɓa musu kwalliya, za'a fara zuwa wajen Mothers day ɗinne, daga nan kowanne ango ya ɗau amaryarsa.

    Sai dai fa su Ummukulsoom basu san da wannan shirin ba, ganin anmusu kwalliyar zuwa wajen taron sai suka ɗauka ko an fasa kaisu yau, dan haka daɗi ya kamasu sosai.........✍🏻


      

NO. 46


............Sun isa wajen Mothers event ɗin daya gama ƙawatuwa, duk wanda ya kamata ya hallara ya iso, dama amare kawai ake jira, hatta da anguna sun iso, Muhsin da Zaid ma na tsaye a jikin mota, suna baza idon isowar amare.

      Amaan kam yana cikin mota bai fitoba, lap-top akan cinyarsa da alama aiki yakeyi, dan Attahir ne a gefensa da takardu a hannu shima. Sai Abbas daya tuƙosa yana daga waje ya rufe musu ƙofar tare da kunna musu AC.

      Bayan an fito dasu Ummukulsoom daga mota kowacce na walwali da ƙyalƙyalin amarci Aunty Nurse ta ƙarasa ga motar su Amaan tai knocking glass ɗin motar.

     Attahir ne kawai ya kalli wajen, yasa hannu ya sauke glass ɗin.

     Aunty Nurse tai murmushi tana faɗin Yaya Attahir amarefa sun iso, Yaa Amaan ake jira”.

    Dukda yajisu bai ɗagoba, sai da Attahir ya zunguresa yana faɗin, “Wai Ajiwa bakaji bane? Amaryafa sun iso”.

    Numfashi ya sauke tare da ɗago manyan idanunsa farare tas ya kalli Attahir ɗin, baice komaiba ya ɗauke kansa kuma, lap-top ɗin ya ajiye gefe bayan ya kashe.

      Aunty Nurse ce dake riƙe da hannun Ummukulsoom ta zagaya gefensa ta buɗe masa.

      Fita Attahir yayi, shikuma ya ɗauki hularsa ya saka yana gyara zamanta da kallon kansa ta mirror ɗin gaban motar, sosai ta ƙara masa wani kwarjini na musamman da fitowarsa asalin bahaushe haihuwar arewa. ƙafarsa dake sanye da takalmi cyan color sau ciki ya fara zirowa a hankali, sai kuma ya fito gaba ɗayansa yana shaƙar iska mai haɗe da ƙamshin khumrar da aka zazzagama Ummukulsoom ajiki itada bily mai saka nutsuwa ga mai shaƙa, ya lumshe ido ya buɗe a kanta.

     “Oh god” ya faɗa akan laɓɓansa yana binta da wani kallo ƙasan ido. Itama ɗin a kaikaice take kallonsa, Shaddace gizna da taji ɗinkin babbar riga ta zamani, dan iyakarta gwuywarsa, komai na jikinsa cyan color ne, agogonsa ne kawai ya kasance na azurfa. Fuskar dai babu walwala sam, amma kuma bai ɗaureta tamau ɗinnan ba........

     Tattausan hannunsa daya zura cikin nata ne ya katse tunaninta, ya kuma damƙe hannun nata cikin nasa saboda wani santsi da laushi da yaji yanayi, gaba ɗaya ƙamshin turarenta ya saukar masa da wata irin kasala mai tsaida gudun jinin jiki, sai faman haɗiyar yawunsa daya tsinke yake da sauri-sauri.

      Saida Attahir yay musu maganar suje saboda sauran angunan sun shige da amarensu, kasantuwarsa babba garesu yasa sukai gaba, dan bai dace ya jera dasu ba.

      Ɗan juyowa yay ya kalli Ummukhoolsum da itama jikinta yay sanyi ƙalau, kanta a ƙasa bata kallon kowa, janyewa yay  yana sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya, da ƙyar ya iya cira ƙafarsa sukai gaba, taku suke a hankali tamkar masu tsoron taka ƙasar, masu wayoyi a hannu sai ɗaukarsu hoto suke har suka shiga cikin hall ɗin da mutane ke cike harda ƴan ɗilau.

      Sun burge kowa, kamar yanda sauran anguna da amarenma suka burge mutane, kujerar su guda ɗaya dake a tsakiyyarsu bily sukaje suka zauna. Ƙiri da muzu Amaan yaki sakin hannun Ummukulsoom, sai faman murzashi yakeyi a nasa a hankali, wanda hakan ba karamin kasala da tashin tsigar jiki yake sakama Ummukulsoom ba, ta gwada ƙwace hannunta yafi sau uku amma yaƙi saki, saima kuma damƙewa da yakeyi sosai.

    Yanzunma da zasu zauna taso janyewa ya kuma damƙe kayansa sosai.

    Babu yanda ta iya, dole ta ƙyalesa suka zauna akujerar, basu matsuba, amma spece ɗin dake a tsakaninsu bashida wani yawa, dan da waninsu zaiyi zaman da zai buɗe sosai dolene su gogi jikin juna. Yanzu kam kasa jurar salon da yake murza hannun tayi, ta ɗago manyan idanunta tana kallonsa da ƙunƙuni. Sarai ya jita, amma saiya basar kamar baisan tanayiba. sosai Ummu ta ƙulu da haushi, cikin salon muguntar da shi kansa baisan ta ƙwareba tasa ɗayan hannunta ta danƙara masa mintsini a gefen hannun.

     Juyowa yay ya kalleta tare da sakar mata hannu yana wani yamutse fuska alamar tabbacin yaji zafi sosai.

       “Ƙaramin gwalo Ummukulsoom tai masa tana ɗauke kanta”.

    Murmushine yaso suɓuce masa, amma kuma saiya haɗiye kayansa ya fuske yana ɗauke kansa. Tasan tabbas saiya rama, dan haka duk motsinsa sai yazaman a kan idontane.


      An fara buɗe taro da addu'a, kafin afara abinda ya tara mutane, Momcy tazo da kanta ta amshi Micrephone taima kowa godiya da halartar wannan taro, tareda fatan alkairin komawa gida lafiya, taja doguwar Addu'a ga amare da angwaye ta fatan kasancewa cikin aminci da zaman lafiya nahar abadan.

      Kowa ya amsa da amin, Ummi ma tayi bayani mai birgewa, amma mafi yawansa akan Amaan da Ummukulsoom ne saboda kara da dattako irin nata. Daga nan Attahir ma yazo yay nasa.

     Taro yaci gaba da gudana cikin aminci da kayatarwa.

    Gaba ɗaya Amaan a takure yake da hayaniyar, hakama Ummukulsoom dauriya kawai takeyi, ga haushin Amaan ya isheta da jan tsaki. Cike da takaici ta kallesa tana faɗin, “Kai jama'a, nikam gaskiya an isheni da tsaki”.

    Yasan dashi take, amma saiya share tamkarma baijita ba, saida yaja wasu mintuna ita harma ta manta ta takali faɗan, sannan ya juyo ya kalleta, baiyi magana ba, sai hannunsa daya saƙala ta bayan ƙugunta.....

    A matuƙar firgice Ummukulsoom ta kallesa, dukta rikice tana waige-waigen ko mutane na kallonsu, wannan rashin kunya har ina?.

     “Sake faɗa naji?” yay maganar a hankali cikin kunnenta.

   Hannu takai zata turo kansa ya riƙe ɗayan hannun, “Wlhy zakija na baki kunya gabansu Ummi babu ruwana ni”.

     Janye hannun tayi tana son muskutawa sai dai iyakar maƙurar kujerar kenan.

      “Kin ceci kanki” ya sake faɗa a hankali yana sakinta ya koma yanda yake ya sake zama.

     Numfashi Ummu ta sauke a hankali tana hamdala ga Ubangiji da girmama rashin ta ido irinna Amaan, ta tabbata komai yazo masa kai zai iya mata, shikuma ya basar abinsa............

     Kururuwan da mc yakeyi ta kiran Buhayyah da Zaid ce ta maidota hayyacinta. Buhayya da Zaid suka mike suna kallon juna da murmushi, dan sunsan misuka shirya.

      Suna fitowa cikin fili MC ya miƙama Zaid Micrephone yana faɗin, “Ango Zaid ya fito filine ba'a matsayin angoba yanzu, shida Buhayyah sun fitone zasu bamu nishaɗi domin farin cikin babban yaya *Lieutenant Colonel Usman Ajiwa da Amaryarsa Barrister Ummukulsoom*, dan haka muna buƙatar ganin babban yaya a filin nan tareda Amarya Brr.. Ummukulsoom”.

     Tafi gaba ɗaya Hall ɗin ya ɗauka.

      Amaan da duk yakeji kamar ya gudu ya kalli Ummukulsoom saboda alamar ya tashi da Momcy tai masa daga inda take zaune, hannunsa ya sake saƙalawa a nata suka miƙe tare. A hankali suka taku suka fito tskkiyar filin, Ummu ta zare hannunta a hankali dan bataso yacema zasu tsaya a haka, shima sai bai hanata ba ya saki hannun yana kallonta ƙasa-ƙasa, sosai Miss Green ɗin riga da zanin sukai mata ƙyau, ga mayen ƙamshinta da yay tasiri a kowanne fitar numfashinsa. 

       Da hannu Zaid yayma DJ magana alamar ya saki sauti.

    Dj yay masa jinjina yana sakin waƙar Umar m shariff ta *Burin so*


      A hankali Zaid ya fara taku yayinda sauti. yafara kaɗawa, kafin ya nuna Buhayyah yana bin Umar cikin ƙwarewa na fitar kowanne lafazi.

    *“Kin haɗu ƴammata, kinji manufata, soyayya nazo kibani ki maidani ɗan gata!  Kin haɗu ƴammata, kinji manufata, soyayya nazo kibani ki maidani ɗan gata”*

    

🎷🎷🎷🎸🎸🎸🎼🎼🎼

    Buhayyah dake wani yamutse fuska ta hau takawa a hankali tana zagayawa saitin Ummukulsoom Zaid na binta a baya da cigaba da rairo waƙarsa.


    _Baniyin ƙarya lokaci ɗayya sanki yaymini mamaya._


_kirani na shirya gani kan hanya gunki zanzo da soyayya._


_Saƙo na zuciya baniyin ɓuya zani nunawa duniya._


_Nasako kaya naci kwalliya na tahone mu gauraya_.


_Kenake kallo, hasken ki ya ɓillo, ya saka naita zillo ke zakimini gata._


*Kin haɗu ƴammata, kinji manufata, soyayya nazo kibani ki maidani ɗan gata! Kin haɗu ƴammata, kinji manufata, soyayya nazo kibani ki maidani ɗan gata*

🎷🎸🎼🎼🎼🎼

     Ya ƙare baitin da komawa bayan yaya Amaan ya maƙale a zuwan dai shine shi😂, ya ɗan tako zuwa gaban Ummukulsoom da Buhayyah yana zagayesu da cigaba da faɗin, 


 _Dana nufo gunki kin kauce, zuciya tawa kin sace, inda zaki soni kin dace, ruwan zuma ungo zaƙice, kina cikin raina, safiya dare rana, kona mace babu raina, da sonki zani ƙwanta._

  🎷🎷🎸🎷🎷🎼🎼

  Lumshe idanu Amaan yayi a hankali yanajin wani irin yanayi a ransa, shi idanma su Zaid da wasa sukai toshifa har cikin ƙasan ransa yakejin waƙar, baitin da Buhayyah ta karɓa cike da salon yanga tana bayan Ummukulsoom kamar yanda Zaid yake bayansa makale ne ya dawo dashi hayyacinsa yana kafe Ummukulsoom dake murmushi da ido.


_Ɗan matsa baya, kaji ɗan ƙarya na wucema a tarayya, bakajin kunya ka taho gaya ni kake cema soyayya, ka farama ɓuya ko a kan hanya baniso daina bibiya, na shige ƙurya kai kana baya karkasa nai ash......(Buhayyah ta dafe baki bata ƙarsa ba), ƙwarya tabi ƙwarya, gaye cire ƙarya, dai-dai da kai jeku shirya ni nayimaka rata._

  🎷🎷🎸🎼🎼🎷🎷🎷

    Atare suka ɗago ido wajen satar kallon juna sai caraf suka shige cijin na juna, gira ɗaya ya ɗaga mata alamar wai “Niɗin?” itama cikin salonta ta maida masa murtani wai “Eh”. Lallausan murmushin da bai shiryaba ya saki yana maida hankalinsa gasu Zaid dake zagayesu suna cigaba da rairo Baiti.


_Ohhh kin haɗu, ni nace kin haɗu, kin haɗu! Kin haɗu! Kin haɗu ƴammata._


_Kin haɗu ƴammata, ni dai kinji manufata, soyayya nazo ki bani ki maidani ɗan gatahhh._

🎷🎷🎷🎸🎷🎷🎸🎼🎼

     Nuna Ummu da Amaan yayi yay dai-dai da faɗin *_Ki mai dani ɗan gatahhhh_*.


Gaba ɗaya hall ɗin ya ɗauki ihu, Momcy ta fara tasowa tana zuba musu liƙi suda su yaya zaid, su Aziza da Muhsen da Bily ma suka taso aka saki sabuwar waƙar da Aunty Ummy yayar Amaan tasa akai musu.

      Cikin raɗa Momcy data matso kusa da yaya Amaan tace, “My dear Fodio adinga murmushi, yaufa ɗin ta musamman ce”.

       Murmushin ya sakar mata ba tare daya shiryaba, itama sai tayi tana rungumo Ummukulsoom jikinta.


      Haka taro ya gudana cikin farin ciki da birgewa, zuwa 11pm aka tashi.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


            Asibitin gidan gwamnati aka wuce da Meenal dake a sume, Basiru kuwa station.

     Cikin awa ɗaya ta dawo normal saboda taimakon gaggawa da aka bata, sambatun da take na zagin Basiru ya sakasu fahimtar bata cikin hayyacinta, allurar barci mai karfi sukai mata saboda fisge-fisge da takeyi tana riƙe wuya.

     Hakanne ya sake hasala mahaifinta, sam shi dama yaronnan bai masaba, dan kawai baya son ɓatama Meenal rai ne ya yarda ta auresa, ashe matsiyacine, to aiko zai gane kurensa, dan saiya gwammaci inama bai taɓa sanin meenal ɗinba har alaƙar aure ta shiga tsakaninsu.


     Sai dare Meenal ta farka, sai dai dukda ta farka a cikin hayyacinta hakan baisa zuciyar mahaifinta da ƴan uwanta ta sauka ba, kowa ji yake inama abashi basiru ya kawo ƙarshen numfashinsa.


★★★★★


     A station kam duka sukaima Basiru na fitar hankali, kafin su watsashi bayan kanta shi kaɗai su garƙame ɗan banza.

    Duk yanda ya jigata yake nishi da ƙyar babu wanda yaji tausayinsa, dama ya ishesu wani ɗan sanda cayay idan bai musu shiruba wlhy zaizo ya ƙara masa.


    Tsitt basiru yayi, ya koma nishin a hankali, dan yasan inhar sukace zasu sake dukansa wlhy mutuwa zaiyi, ƙyaƙykyawar fuskarnan tashi dukta fita hayyacinta da duka, tayi suɓu-suɓu wane ƙwaɓin filawar fanke🥴, ga ƙafarsa ta dama kamarma sun ji masa ciwo a cikin ƙashi, dan nishi yake da ƙyar.


   Kwana biyu da faruwar haka Meenal ta dawo dai-dai, basiru kuma dake station yana fama da ciwuka na jiki dana zuciya mahaifinta yay duk yanda zaiyi aka kwashi basiru zuwa prison, acewarsa bashi da lokacinsa yanzu sai randa ya shirya.

    Wannan shine dalilin ɓatan Basiru ɓat a duniyar mutane.


    Yayinda a gefe ɗaya su Suhailat ke cikin farin ciki, sun san dai sun kaishi ƙasa, aikinsu na gaba kuma yanzu suyita tunzura Meenal akan a kaishi court, ta wannan hanyarne haƙƙin iyayensu da yaci kuma zai fito da na ƴarsa ta wajen Lubna.


😳masoyan Basiru muna ruwa, xoxo a kawo ɗauki yayanki ya shiga jail🙊☹️😝😂⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


            Hankalin Ummukulsoom ya tashi ganin mota ɗaya zasu koma da Amaan yanzu, bama mota ɗayarne matsalarta ba, fatanta ALLAH yasa gidan Abba za'a koma.

     Amma fa sam taƙi nuna tana cikin ruɗanu akan fuskarta, a zuciyarta ne duk take a wannan yanayin.


Motocin su Bily ne suka fara fita tare da waɗanda zasu ɗan mata rakkiya da kuma dangin mijinta da sukazo wajen Mothers event ɗin.

      Sai nasu Aziza itada nata angon Zaid da gayyar ƴan ɗilau da wasu a cikin dangin Ummi.

     Motar su Ummukulsoom ce ƙarshen tashi, wadda saida Amaan yagama bankwana da abokansu sannan ya shigo aka maida aka rufe.

    Rumtse idanu Ummukulsoom tayi tana ɗauke kanta gefe tamkar batasan da zamansa ba. Sai da motar ta fito daga hotel ɗinne ya kalli tsakkiyarsu inda yabar lap-top ɗinsa. Idanu yaɗan fiddo a can ƙasan maƙoshi yana faɗin, “Ƴar lukutar Ummi system ɗitafa”.

    Kamar zata shareshi sai kuma taɗan juyo ta kalli sashensa, tabbas tana ɗan jin rabin jikinta akan abu mai tauri, amma sam bata lura mita hauba. Da gaske lap-top ce kuwa, yasa hannu yaja abarsa yana shafawa cikin narke fuska tamkar wani ƙaramin yaro.

    Baki ta taɓe tana kauda kai da faɗin “Taɓara”.

     Duk da yajita sai yay shiru, danshi sam baya abunda zai zubar da mutuncinsa gaban yaransa ko ƙannensa, saboda Abbas ne kuma bazata samu amsaba.

    Har suka iso gidan Dad babu wanda ya sake tankama ɗan uwansa a tsakaninsu, shi ya cigaba da aikinsa a lap-top ɗin ita kuma ta ɗauke kanta gaba ɗaya dagama sashensa.

      Iya waɗanda zasu kwana a gidan kawai motocinsu suka shiga, duk wanda zasu juya gidan Abba kuwa a waje suka tsayar da motocinsu, kowa ya fito ya shigo cikin gidan da ƙafa.

        Ƙanwar Ummi gwaggo Maryam da kanta ta fiddo Ummukulsoom a mota, Amaan kam saima ya sake gyara zama alamar bazai fitoba, yasan koya fito hayaniyace zata isheshi, wadda ya shawo a wajen fati din ma ta wadatar, dan yanzu haka kansa ciwo yake sai yasha magani.

    Ganin bai fita ba Abbas ya kalleshi kaɗan, cike da ladabi yace, “Sir mun ƙaraso?”.

      Kansa ya ɗago ya ɗan kalli Abbas ya ɗauke, cigaba yay da aikinsa a yana sauke ajiyar zuciya, da ƙyar yace, “Rufeni kaje a binka”.

     “Ok Sir, a bar AC n?”.    Kansa kawai ya ɗaga masa alamar eh, batare da ya buɗe baki ba.

     Abbas yay masa duk yanda ya buƙata, sannan ya fice ya barsa shi kaɗai a motar, dama Attahir tun acan suka rabu, dan Ahmad yay barci, mamansa kuma bata da lokacinsu, shine kuma ya maida su Hajiya Yaya gida.


★★★★★


        Sashen Yaa Amaan aka kai Ummukulsoom, komai an canjashi, dan kayan ɗakin da Abba yay musu kala bibbiyu itada Bily sai aka sakama Ummukulsoom ɗaya anan sashen Amaan na gidansu, ɗaya kuma aka wuce dasu legos tare da wanda Dad yay mata matsayin tasa gudunmawar.

     Kayane ƴan gaske da suka ƙawata falon, dan har fenti an canja, sai ƙamshin sabon fenti da sabon katako sashen keyi, har cikin bedroom ɗinsa da komai yay ɗas aka kaita aka zaunar, hawaye take a cikin gyalen na takaicin zartowa da akai da ita gidansa yau, itafa dukma zatonta gidan Abba za'a maidata itama, sai zasu koma legos a ɗakkota, ashe ƙullalliyar da akai musu kenan, gashi ko sallama batai da Bily ba. Hawayene masu zafi suka kuma silalo mata a kumatu saboda jin harta fara kewar ƴar uwarta.

      Ƴan rakkiya basufi mintuna goma sha biyarba kowa yay mata sallama ya fita akan sai sun dawo buɗar kai gobe idan ALLAH ya kaimu.

    Maman Ahmad taɗan duko ta gwargwaɗa mata wani abu a kunne tare da dora mata Handbag ɗinta a cinya ta fita.


    Cikin mintuna kalilan gidan yay tsit, waɗanda zasu kwana anan duk sun shige sashen Momcy, dama duk ƴan Ajiwa ne ma, sai ƙannen Momcy da ƴan uwanta ƙalilan.


        Aneesa ce kawai a sashen Ummukulsoom, itama tana ɗanyin Morping ɗin inda aka tattaka ya ɓaci ne, dan tasan mai sashen ya tsani ƙazanta, inma basu gyara ba kafin ya shigo to ko sunyi barcine saiya saka an tadosu sun gyara, kokuma ya kare akan Buhayyah. Sai da ta gyara komai fes ta saka turaren wuta saboda akwai wutar Gen.. Da aka kunna sannan ta fito tanama Ummukulsoom dake zaune har yanzu tana ƙwalla sai da safe.

        Tashi Ummukulsoom tai taje ta sakama ƙofar key tana hararta, dan bataso yace zai wani shigo mata, sai kace ƙofarce Amaan.

    Har aranta tasan bai daceba, amma fa ita bazata yarda yama ce zai zo su kwana ɗaki ɗaya ba, sai dai yaje sashen su Bassam ya kwana, dan bazata kwana ɗaki ɗaya da ƙaton gardi ba............✍🏻



Babu ruwana Ummukulsoom ce tace *ƙaton gardi*, karna sha suburbuɗa wajen ƴan Team ɗin Amaan 😝😂.



NO. 47


.............Aunty Ummy ce tai Knocking glass ɗin motar da Yaa Amaan ke ciki har yanzu yanata aikinsa hankali kwance, gefe ɗaya raɓar AC na ratsa sa.

       Saida yaja wasu seconds kafin ya ɗago manyan idanunsa yana kuma ɗan ɓata fuska ya sauke glass ɗin a hankali.

       Aunty Ummy dake tsaye ta ranƙwafo tana faɗin, “Angon nan kodai ɗaukarka zamuyi mu kaika?”.

     Guntun murmushi yayi kaɗan yana buɗe murfin da faɗin, “Uhm-Uhm Aunty, zanma kai kaina ne, dan nafiku zumuɗi, nabaku dama ku gama nakune”..

    Dariya sosai tayi ita da aunty Nurse dake bayanta, a ransu suna mamakin irin wannan dogon sharhi haka tamkar ba shiba.

    Shikam tuni ya basar kamar bashine yay maganarba, aunty Nurse ta karɓi kayan hannunsa daya tattaro a motar, bata yayi babu musu. Gaba yay suna binsa a baya, Aunty Nurse da aunty Ummy na tsokanarsa suna ƴar dariya.

    Uffan baicema kowannensu ba har suka isa ƙofar sashensa, juyowa yay ya amshi kayansa a hannun aunty Nurse yana musu alamar sai da safe da hannu.

    Basu ja zancenba suka juya shi kuma ya murɗa ƙofar ya shiga da sallama a ƙasan maƙoshi.

    Sosai ƙamshin turaren da aka saka ya tasiri a ransa, ya shaƙa ya lumshe idanunsa tare da takawa cikin falon sosai ya ajiye kayan hannunsa a kujerar farko.

     Babbar rigarsa ya zare, ya bar ƴar ciki kawai da wandon, dama hular a hannu ya shigo da kayansa, hannayensa duka yasa a ƙugu yana bin ko ina na falon da kallo, komai ya masa ƙyau tamkar shiya zaɓa, ya sauke idanunsa akan ƙofar bedroom ɗinsa yana ƙiyasta yanda zasu kwashe da ƙwailarsa (Ummu team bani na faɗaba Yaa Amaan ne kuma😂😝⛹🏻‍♀️).

             A hankali ya taka zuwa ga ƙofar, ya kama handle ɗin ya murɗa sai yaji gam a lamar a kulle take. Wani lallausan murmushi ya suɓuce masa yana girgiza kansa da kai hannu ya shafi girarsa. Hannunsa ya janye daga handle ɗin ya zubasu a aljihu gaba ɗaya, tsaye yay ya zubama ƙofar ido yana nazari. tsawon mintuna uku kafin ya sauke numfashi ya tako zuwa cikin falon.

        Zamansa yay cikin kujera kawai ya maida kansa ya jingina tare da lumshe idanusa ya faɗa duniyar tunani. Shi kansa bai san iya adadin lokacin daya ɗauka a haka ba, har aka kashe Gen... Saboda wuta da aka maido.


       Ummukulsoom kam tunda ta kulle ɗakin saita cire kayanta ta canja dana barci, dan a ganinta hankalinta kwance zatai barcinta ita kaɗai a ɗakin.

      Bayi ta shiga taɗanyi uzurinta, komai an kuma canjasa saɓanin sanda aka kawota da farko, bayan ta kammala ta fito.

    Gadon ta haye kewar bily na dawo mata sabuwa fil a zuciya, tsawon shekara shida basu taɓa rabuwa ba, duk inda ɗaya tasaka ƙafa ɗaya na tare da ita, sai gashi yau zasu kwana mabanbanta gidaje, bayan suna a cikin gari ɗaya. Ta share hawayen fuskarta tana gyara kwanciya, sama-sama tai addu'ar barci ta ɗora tunaninta daga inda ta tsaya.

          

        Amaan ya buɗe lumsassun idanunsa jin agogon dake falon ya buga ƙarfe ɗaya, iskar daya zuƙa ya turo ta bakinsa da hanci, kafin ya miƙe cike da takun dake nuna gajiya da kasala tattare dashi, harma da ƴar yunwa.

   Dani ya fara zuwa ya buɗe kwanikan dake wajen duka, gasashshen namane mai romo a kula, sai abinci da akaima dahuwa ta musamman, duk haɗuwar abincinnan bazai yuwu yacisa ba, dan dare yaja, ko yaci takura masa zaiyi. Maidawa yay ya rufe ya sakko daga ɗan tudun dani ɗin ya nufi ƴar durowar dake gaban tv, keys ya ɗakko aciki, da alama dai Ummukulsoom tayi bonono rufe ɗaki da ɓarawo🤣😝.

      Sai da ya ɗauki lap-top ɗinsa da babbar riga da hula a hannu sannan ya nufi ƙofar ɗakin ya zura key ɗin, cikin sa'a kuwa ya shiga alamun ta zare wanda ta kulle da shi. Ƙaramar ajiyar zuciya ya sauke tare da murɗewa....


      Da sauri Ummukulsoom da barci ya fara figarta ta buɗe ido jin ana taɓa ƙofa, tashinta zaune jiki na rawa yay dai-dai da shigowar Amaan cikin ɗakin, maida ƙofar yay ya  kulle kafin ya cigaba da takowa idonsa a kanta yana haɗiye murmushin dake neman kufce masa da ƙyar ganin yanda ta tsaya tamkar wata status tana kallonsa.

    Basarwa yay ya ajiye kayan hannunsa gaba ɗaya kan gadon ya zauna a bakin gadon shima. Takalminsa ya hau ƙoƙarin cirewa ba tareda ya ma nuna yasan da ita a ɗakinba, sai da ya gama tsaf sannan ya juyo ya kalleta gira a ɗage, sam fuskar babu walwala tamkar kullum, amma ƙasan ransa cike yake da farin cikin wannan ranar mai cike da tarihin da bazai mantaba.

      “Na miki ƙyau ne ƴammata?”

     Harara ta zuba masa tana ɗauke kai. Shima ya ɗauke nasan kan yana faɗin, “Bandama ƙarfin hali mai fada da masarautarsa har a nuna masa ƙofar da zai shiga?”.

      Sharesa tai ta fara yunƙurin sauka a gadon, baice mata uffanba, sai ma ya miƙe hankali kwance ya hau cire botirran gaban rigarsa ƴar ciki, tsaye Ummukulsoom tayi tana jiran ya matsa ta ɗauki key dake bedside drawer ɗin dake gefensa bayan ta ɗauki hijjab ta saka akan kayan barcin jikinta duk dama masu kaurine , kuma basu kama mata jikiba balle fidda mata tsiraici.

      Fahimtar hakan da yayne yasashi shareta ya cire rigarsa, ya zam daga shi sai dogon wandon da bes ɗinsa faɗa ƙal.

    Ƙin kallonsa tai, saima ƙunƙuni take a ranta wai wannan ai iskancine.

   Baisan tanayiba, ya kwashi key ɗin data ajiye da wanda shi ya shigo dasu ya nufi bathroom ɗin batare daya tanka mata dinba balle kallon inda take.

     “Nikam bazan kwana da ƙato ɗaki ɗaya ba, ka bani key na fita sashensu Momcy”.

     Saida ya kama Handle ɗin ƙofar toilet ɗin sannan ya juyo fuska a matuƙar ɗaure, da hannu ya nuna mata hanya alamar taje mana, yay shigewarsa.

    Takaici ya kume Ummukulsoom, ko motsawa a wajen kasa yi tayi, yaufa za'ayita kenan, dan koma mi zaiyi yayi ya gama bazata kwana a ɗaki ɗaya da shi ba.....

     Tana wajen tsaye tajiyo motsin ruwa alamar wankama yakeyi, ta harari bayin ta koma gaban mirror ɗinsa dake cike da turare da mayuka da kayan dai tsaftar jiki kala-kala, stool ɗin ta janyo ta zauna zaman jiran fitowarsa.

     Baifi mintuna ashirin ba ya fito.

    Ɗago kai Ummukulsoom tayi da hanzari ta kallesa, cikin azama ta janye idanunta saboda daga shi sai towel yellow ya fito, sai ƙarami a hannunsa yana goge kansa da bawani gashin kirki, dan askewa da yakeyi saboda yanayin aikinsa.

        Murmushin mugunta yayi, ya tako zuwa wajen mirror ɗin, gabanta ya tsaya yana kallonsu shi da ita ta cikin madubin tsawon seconds goma sha biyar kafin ya janye idanunsa ya matsa sosai gaban madubin ya ɗauki abinda zai ɗauka ya bar wajen.

     Sam batai zaton zai iya yunƙurin shiryawa a ɗakinba a gabanta, sai taga ya nufi drawer ɗinsa hankali kwance ya ciro kayan barci masu taushi farare tas.

     A saman gado ya ɗorasu, ya rufe durowar ya koma bakin gadon ya zauna ya ɗauki mai yana shafawa.

    Sosai kunya ta lulluɓe Ummu da mamakinsa, ga barci na fisgarta saboda hayaniyar biki ta kwana uku.

    Kanta ta ɗora saman madubin yanda bazata gansaba. ya kalleta kawai yana ɗaukar kayansa ya hau sakawa hankali kwance. Harya gama ya dawo gaban mirror ɗin ya ɗau turare ya fesa bata motsaba, gaba ɗaya ji take ta gama takura, yau kam taga ƙarshen rashin kunyar gayen nan.

     Wata kujera dake gefe ya jawo ya zauna kusa da ita, ya ɗora hannunsa a kan bayanta.

    Gabanta ne ya faɗi, dan haka ta ɗago ta kallesa da sauri, ganin yanda ya shige mata sosai ta ɓata fuska tare da yunƙurin miƙewa. Cikin sa'a ya jawota gaba ɗayanta ta zauna bisa cinyarsa, ram yay mata yanda bazata taɓa iya motsin kirki ba ma balle yunƙurin tashi.

     “Fushin da jan ajin ya isa hakanan mana matata”.

    Hararar da ta ruɗa dukkan kuzarinsa ta zuba masa, harga ALLAH inta hararesa yana tasiri a jikinsa fiye da zatonta. Lumshe idanunsa yayi ya buɗe a kanta yana jan numfashi da ƙyar da haɗiye busashshen yawun daya daskare masa a maƙoshi, dama tun jin jikinta da yay a jikinsa sosai jijiyoyin jikinsa suka saki......

       “Kariga da kayi saken da bazaka taɓa daina ganin wannan fushin a fuskar Ummukulsoom ba, Abubuwa uku idan sun tafi ba su dawowa: Magana da lokaci da mutunci. Mutane iri uku ne: Wasu kamar guba suke, gudunsu akeyi. Wasu kamar magani suke, akai akai ake nemansu. Wasu kamar abinci suke, a kullum dole ne a nemesu. Yi ƙoƙari ka zama wanda a kullum ake neman sa saboda amfaninsa”.

      A hankali ya kuma lumshe idanunsa tare da manneta da ƙirjinsa sosai, kalamanta na shiga kowanne kafa ta jinin jikinsa, yasan maganace ta faɗa masa cikin hikima, a hankali yakai bakinsa kan kunnenta yace, “Ba ka sanin daɗin lafiya sai idan ciwo ya sameka. Ba za ka san daɗin zaman lafiya ba sai ka gamu da tashin hankali. Ana sanin daɗin haɗuwa ne idan rabuwa ta zo Ummukulsoommm”.

      Yanda yaja sunan natane a cikin kunnenta ya tilastata sake cusa kanta ƙirjinsa, dan gaba ɗaya tsigar jikinta ta tashi, a tare suka sauke ajiyar zuciya, ya sassauta mata riƙon dayay mata alamar ya bata damar tashi.

    Da sauri ta yunƙura ta sauka, sosai maganganunsa suka bata mamaki, kenan yana nufin tun bayan rabuwarsu ya damu da ita komi?. Kallonsa ta ɗanyi taga shima ita yake kallo, tai azamar janye idanunta zuwa wani wajen.

     Kaɗan ya sauke numfashi yana tasowa shima, hannunta ya kama ya kaita saman gadon ya zaunar, kafin ya kama kafaɗunta gaba ɗaya ya kwantar da ita.

      Ita dai kallonsa take kawai ta kasan ido duk sai kuma jikinta yaɗanyi sanyi, bai sake cewa komaiba ya fara mata addu'ar barci, sai da ya kammala tsaf ya tofa mata tare da jan bargo yaɗan lulluɓa mata zuwa ƙirji, ya zame mata hijjabin jikinta. Duk yanda taso hanashi sai ta kasa hakan, dan wani kwarjini taga ya mata fiye da zatonta, shi kansa wani girma ta ƙara a idonsa da mutunci, baiyi zaton tanada sauƙin kai irin haka ba, dan harga ALLAH ya ɗauka yau bazama ta barsu su rintsa ba saboda tanadin rashin mutuncin datai masa. ya kuma yarda duk ɗan gaske baya yarda tarbiyyar gidansu da mutuntakar musulinci. Kansa ya duƙo ya bata sunba akan laɓɓanta daketa motsi alamar sonyin magana amma ta kasa, ya sumbaci goshinta sannan yayo ƙasa inda bata taɓa zatoba nanma ya sumbata. 

    Sosai ta waro idanu waje saboda matuƙar mamakinsa, ya sakar mata lallausan murmushin daya kusa sumar da ita a wajen. Ai babu shiri taja bargon ta rufe har fuskarta tana juya masa baya.

      Miƙewa yay yana cigaba da murmushinsa, ya zagaya ta can ɗayan gefen ya kwanta yana tunanin yanda zai iya kwanciya bashi kaɗaiba a ɗakin, ya riga da ya saba da kwanciyarsa shi kaɗai babu motsin kowa, harga ALLAH jinsa yake duk a takure, to amma ya zaiyi, yana buƙatar matarsa kusa dashi fiye da komai a halin yanzun.

     Harya kammala addu'arsa ya gyara kwanciya Ummu bata sake motsawa ba, addu'a dai take a ranta ALLAH yasa ba a ɗakin zai kwana ba, sai dai jin ya kwanta bayanta tasan addu'arta bata karɓu ba kenan.

     Abinda ya sata samun nutsuwa dashi sam bashi da wani rawar kai irinna angunan wannan zamanin da suke nuna kamar jikin macen ne mafi kwaɗaituwa a garesu, banda wannan sunbatar tata da yay a ƙirji yanzu bai taɓa kai hannunsa wani sashe na jikinta ba koda wasa, tasan kuma bawai dan baya buƙatar baneba, kawai dai shi komai nasa na nutsuwa ne da dattako.

     Tun tana fargabar ko zai far mata har taji ya fara sauke numfashi a hankali alamun barci yama fara tafiya da shi kenan.

    Itama dama barcin takeji, tsabar tsorone ya hanata yi, gashi dare yaja kusan 2:15am na dare, cikin ɗar-ɗar dai itama barcin yay gaba da ita.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡    


    Da asuba shine ya fara farkawa, ya buɗe idanunsa a hankali ya sauke akan fuskar Ummukulsoom data juyo tana fuskantarsa yanzu ba tare data saniba, sai dai tana a inda take alamun batada mirgine-mirgine wajen barci.

    Fuskarta tayi fayau tamkar tana murmushi, ƙyaƙykyawace mai yawan kwarjini da cikar haiba, komai nata yana da ɗaukar hankali musamman murjajjen jikinta da sam babu rama a tare da ita, luuu yay da idanu ya kuma buɗewa a kanta tare da kai hannunsa ya shafi laɓɓanta da babban ɗan yatsansa.

    Yanda ya keyinne ya saka Ummukulsoom kawo hannu cikin barci ta riƙe nasa tare da rungume hannun a ƙirjinta tana gyara kwanciya.

     Idanu ya tsura mata yanajin fitar murmushi a ƙasan zuciyarsa, sai dai sam babu akan fuskarsa, bai janye hannun nasa ba kamar yanda bai iya janye idanunsa da suka ƙara girma saboda barci daga kanta ba.

    Kuma motsawa tayi sai taji ƙamshin turarensa ya yawaita a hancinta, hakan ya tilasta ta buɗe idanunta dake cike da barci dan ta manta a inda take gaba ɗaya.

         Idanun Ummukulsoom kan bada wani yanayi na musamman a lokacin data tashi a barci, cikinsu yaɗanyi jaa su kumburo daga waje, ta buɗesu da ƙyar a kansa saita jasu suka koma tamkar zata lumshe ta sake buɗewa da azama ganin namiji a kusa da ita sabanin Bily da tasaba gani.

    Tuni Amaan yayi doguwar shiɗewa akan wannan salo na Ummu da sam ba yanga bace ko ɗaukar hankali.

    Saurin ture hannunsa tayi ta juya bayanta tana dafe ƙirjinta ta sauke numfashi.

     Shima ajiyar zuciya ya sauke ya yunƙura ya tashi da ƙyar dan jikinsa ya masa nauyi sosai alamun barcin bai ishesa ba. Bai ce da ita komaiba ya nufi bayi ɗaura alwala.

     Koda ya fito baiyi mata magana ba, dan yasan idonta biyu, ya ɗau jallabiya ya saka bayan ya zare kayan barcinsa sannan ya fice.

       Ummu tai ajiyar zuciya tana mamakin kanta, sai kace Amaan yazo mata da wani asiri, koda yake duk fa sonta da bashi laifi inhar zata tuna a zamansu na baya bai taɓa cutar da itaba, harkarta ce kawai baya shiga, sakin da yay mata da kausasan kalamansa ne kawai suka kasa barin ranta, *_ƙwaila mara zurfin ilimi...,_* wannan kalaman sune mafi ciwo da take ganin da wahala ta iya mantasu harta bama Amaan kanta da rayuwarta yanda kowacce mace kanyi a gidan mijinta......

   Jin an ƙwala kiran sallar shiga massalaci yasata tashi itama tai alwala domin gabatar da salla.


     Tana zaune bayan idar da salla ya shigo, sallama kawai yay ta amsa, daga haka babu wanda ya kuma tankama ɗan uwansa, ya ɗauki kayansa na trianing ya shiga bayi, mintuna kaɗan ya fito, a bakin gado ya zauna yana ƙoƙarin ɗaura igiyar takalmansa.

     “Ina kwana” Ummu ta faɗa cikin kauda kai gefe.

      Bai amsa ba ya cigaba da ɗaura takalman, tasan kuma sarai ya jita, juyowa tai ta kallesa cike da takaici, hakan yay dai-dai da miƙewarsa suka haɗa ido, fuskar dai tana a yanda ta santa a tamke, zuwa yanzu hakan baya damunta dan shi da Dad ta gama sallama muskilancinsu.......

     Wani ɗan tsigunnon da yay a gabanta na gayune ya dawo da ita hayyacinta, kuncinta ya sumbata cikin lumshe ido da buɗewa yana faɗin, “Amincin ALLAH ya tabbata ga zuciyar da bata fushi Matar Ajiwa”. Ya ƙare da busa mata iska a kan fuska wadda ta tilasta mata kallonsa.

    Ido ɗaya ya kashe mata yana mikewa ya fice abinsa ba tare daya damu da rashin amsawarta ba.

    Ta daɗe tana kallon ƙofar tamkar zata sake ganinsa a wajen, “Amaan” ta faɗa akan laɓɓanta ba tareda tasan dalilin ambaton sunan nasa ba. Har yanzu akwai barci a idonta, dan haka ta miƙe ta koma kan gadon ta kwanta zuciyarta na tunano mata Bilyn ta, ko yaya ta tashi itama? Oho.

    Babu jimawa barci ya kwasheta.


       Sai da gari yay haske sosai Amaan ya dawo gidan, a tsakar gida ya iske Dad zaune akan farar kujera yana duba wani littafi na addini, ga Coffee da aka haɗa masa ajiye a copy table ɗin da ke gabansa.

        Ƙarasowa Amaan yayi inda Dad yake, ya zauna kan ɗan dakalin da aka zagaye flowers ɗin gidan dashi yana faɗin “Barka da safiya Dad”.

    Kallonsa Dad yayi fuskarsa kadaran kada han yace, “Barka dai Fodio, yaya ɗiyata?”.

     Moso yaɗanyi kaɗan yana ƙara jinjina irin son da Dad kema Ummukulsoom, ya amsa da cewa, “Lafiya lau Dad”.

     “To Alhmdllh” Dad ya faɗa yana ɗaukar mug ɗin Coffee ɗinsa yakai baki.

    Buhayyah data ƙaraso ɗauke da gorar ruwa a kan karamin tire da kofi ta ajiye a table din tana gaida Amaan.

    Sau ɗaya ya amsa ya ɗauke kai, sai da yaga zata bar wajen yace, “K kawo min cup”.

     “To yaya” ta amsa da girmamawa.

    Babu bata lokaci ta dawo wajen, sanin Coffee zaisha ya sata ba tare da tama tambayesa ba ta duƙa ta haɗa masa.

    Amsa yay ita kuma ta bar wajen, yana sha suna ƴar maganar data shafesu shi da Dad, ya daɗe bai samu irin wannan damarba ga Dad tun bayan rabuwarsu da Ummukulsoom, shiyyasa sai yaji sam bayason tashi ya barsa. Shi kansa Dad zaman nasu yana sakashi shauƙi da nishaɗi, yanason Fodio, sai dai shi yana dannewa ne saɓanin Momcy data gaza.

       Anan Momcy ta fito ta samesu, gaisawa sukai da Amaan itama tana tambayar Ummukulsoom da gajiyar biki.

      Ya amsa yana maijin nauyin iyayen nasa.

    “Fodio tashi kaje ciki baka ganin lokaci yaja kabar min yarinya ita kaɗai”.

        Miƙewa yay tare da sakin guntun murmushi jin furucin Dad ɗin nasa.

       Momcy ma murmushi tayi.


        Falon tsaf alamun an gyarashi, duk zatonsa Ummukulsoom ce ma shi, bedroom ɗin ya nufa, ya murɗa ƙofar ahankali ya shiga, tana kwance abinta tana shan barci, ya taka zuwa gaban gadon, kallon kusan mintuna biyu yay mata ya bar wajen zuwa bayi, baya gajiya da kallon ko kaɗan.

     Harya fito daga wankan Ummukulsoom bata tashiba, shiryawa yay cikin ƙananun kaya marasa nauyi ya fito falo ba tare da ya tasheta ba, dan ya lura tanajin daɗin barcin sosai..........✍?


NO. 48



..........Ummukulsoom ta daɗe tana barci kafin ALLAH ya bata ikon tashi, ta sauke ajiyar zuciya ganin babu Amaan a ɗakin. Gadon ta fara gyarawa bayan ta sakko, kafin ta gyara ko ina na ɗakin ta fesa turaren ɗaki, batai gigin koda leƙa faloba, duk da zuciyarta na bata bayama sashen, dan batajin motsin komi.

    Bayi ta faɗa tayo wanka, hankalinta kwance ta ɗauro towel ɗinsa, bashi da wani tsawo, dan haka iyakar cinyarta ya tsaya.

    Ƙara sowa tai cikin ɗakin da ɗan hanzari saboda wayarta dake ring, ta share ruwan fuskarta tana murmushi da ɗaukar wayar, gudun karta saka a kunne ta jiƙe da ruwan dake bin fuskarta sai ta saka hans free. Cike da tsokana take faɗin, “Kaga ta gidan Muhseen amaryar ƙamshi”.

      Cikin sanyin murya daga can Bily tace, “Bestie ykk? I miss you so much wlhy”.

     “Nima haka Bily na, an mana wayo ko sallama bamuyiba jiya, amma yanaji muryarki haka ko baki da lafiyane?”.

        “Ummu bazaki ganeba, wlhy Muhseen mugune”.

    “Na shiga uku ni kulsoom, mugu kuma bily? Ya zaki danganta mijinki da wannan sunan miyay miki haka?”.

     Kuka Bily ta kuma sanya mata, da ƙyar ta lallasheta tai shiru. Bily tace “Ummu kofa tafiya bana iyayi wlhy saboda tsabar rashin tausayin da ya gwadamin”.

      Sai yanzune Ummu ta ranfo inda Bily ta dosa, ta sauke ajiyar zuciya, dan duk zatonta da wani mugun abu yayma Bilyn, yanda Bily ta kare maganar tana kuka saiya saka Ummukulsoom kwashewa da dariya, harga ALLAH bily ta bata matuƙar dariya da tausayi......

     “Yanzu nan bestie dariya ma zakimin ba zakiji tausayina ba? Wlhy serious nake miki maganar nan, yanzu hakama muna asibiti fa”.

    Tsayawa Ummu tai da dariyar babu shiri, “Wai dan ALLAH Bestie da gaske kike?”.

       “Hummm da kin ɗauka wasa nake ko? Shiyyasa naketa cewa ki faɗamin yaya abun yake? Tunda ke kinsan sirrin, amma kika kifeni Ummu, gaki nan hankalinki kwance k tunda kin wuce wannan siradin tun shekaru shida da suka shige.....”

      Murmushi kawai Ummu tayi tsoro na sake tsargata, Bily batasan itace ma wadda batasan komanba, ita a wancan zaman auren banda kiss da Amaan yay mata gaban Bukky batasan komai ba daya shafi rayuwar aure.....

    “Kinyi shiru bestie ”.

Ajiyar zuciya Ummu ta sauke idonta yay kwale-ƙwale da tsoro, “Toni bestie mi zance, kiyi haƙuri kawai kowa da haka ya fara, amma shima dai Muhsin yayi wauta wlhy, koda yake bamaga laifinsa ba tunda farin shigane, yanzu ya jikin?”.

     “Da sauƙi, gashi nan zamu koma gida, dama babu wanda yasan mun fito sai ke yanzu dana sanarmawa”.

       “Sorry bestie kinji, zan aiko a amsarmin sauran kazar amarcin”. Ummu ta kare maganar da tsokana.

    Ƙitt Bily ta kashe wayar tana mata ƙunkuni.

   Hakan sai ya saka Ummukulsoom ci gaba da dariyarta, ta yaye towel ɗin hankali kwance  zata shafa mai.

    Ganin kamar inuwar mutum ta cikin mirror ɗinne ya firgitata, tai saurin maida towel ɗin ta ɗaure tare da juyowa cikin zafin nama. Ba ƙaramar faɗuwa gabanta yayi ba ganin Amaan a tsaye jikin ƙofa ya harɗe hannayensa duka a ƙirji, hakama kafafunsa harɗe suke, ya jingina rabin jikinsa a bango. Harga ALLAH batasan adadin lokacin daya ɗauka a wajen tsayeba, babar damuwarta ma ace yaji wayar da sukayi da bily da kuma yaye towel ɗin da tayi yanzun, dan ta tabbata dolene ace ya ganta.

          Ƙasa tai da kanta tana haɗe fuska da matse ƙafafu alamar jin kunyar ganinta da yay da mazuran naɗe tabarmar kunya. Ya lumshe idanunsa daya janye daga kanta ya kuma buɗewa a kantan...

     “Amma haka bashi da ƙyau gaskiya, yakamata kafin ashigoma mutum a dinga neman izininsa mana” ta ƙare maganar cike da tsantsar takaicinsa da haushi.

     Murmushin gefen baki yayi yana warware hannunsa dake a ƙirji, hakama kafafunsa ya tsaya kyam a kansu tare da tura hannayen duka aljihun wandon jeans ɗinsa, Yanda yake kallonta ƙasa-ƙasa ne yasata jin ta sake takura, ya fara takowa a hankali cikin nutsuwa zuwa gareta.

     Bata iya motsawa ba, dan tanajin kunyar ta juya baya saboda towel ɗin jikinta, kasantuwarta mai ɗan jiki ya ɗaga daga baya sosai fiye da gaba. Rumtse idanunta tayi da ƙarfi saboda jin tsayuwarsa gabanta gab da ita sosai har tana iya jiyo saukar numfashinsa.

          Sunkai minti biyu a haka kowa ya kasa yin abinda ya dace, ita dai kunyace da takaici, shiko tsabar miskilancine da kasalar dake saukar masa a hankali.

      Ya turo numfashi kaɗan tare da zare hannayensa daga aljihu ya ɗora bisa kafaɗar Ummukulsoom.

   Ko motsi bataiba balle ta ɗago ta kallesa, sai dai salon bugun zuciyarta ya sake canjawa.

     Ganin haka sai ya nufi takalar magana, yakai hannu zai kwance towel ɗin.

   Babu shiri Ummukulsoom ta ɗago a harziƙe tare da riƙe hannunsa.

    Jaa yay kamar zai sunce saboda hannunsa na riƙe da tawul ɗin. Ganin bata da mafita sai kawai ta faɗa jikinsa ta ƙanƙamesa iyakar ƙarfinta.

        Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana wani munafikin moso tare da saka hannayensa biyu duka a bayanta ya zagayeta yana ƙara mannata sosai da jikinsa tare da lumshe idanunsa, duk illahirin tsigar jikinsa na tashi.

      Saida sukaja wasu mintuna a haka kafin ya iya buɗe baki da ƙyar yana faɗin, “Ke da baki fara ɗaukar karatunba, amma kike yima wanda yashiga makarantar dariya ko?”.

        Sosai gabanta ya faɗi, tai ƙoƙarin janye jikinta ya kuma matseta.

     “Ni sakeni, banason haka”.

    Babu musu ya saketa, tai saurin barin wajen tana harhaɗe hanya saboda kunya, shiko ya bita da kallo da mayun idanunsa harta ɗauki hijjab ta saka. Numfashi ya sauke a hankali ya zauna akan stool ɗin mirror ɗin.

      Bata kulashi ba, ta buɗe akwatinta guda ɗaya da aka kawo ta ɗauki kaya, bayi ta shiga.

    Baice komaiba sai kansa da ya dafe, yanason Ummukulsoom, amma yasan ita bata sonshi, amincewarma da tayi ta dawo garesa saboda mahaifin sane. Duk sanda ya tuna shifa kaɗai yake shirmensa a sonta jikinsa yakanyi sanyi ƙalau, haka zuciyarsa take, idan har ta tashi son abu bata ɗaukarsa da wasa, hakama idan ta tsanesa bata ma abun ƙin sauƙi. Iska yaɗan huro a bakinsa ya miƙe ya fice a ɗakin, dama ya shigone dan ya tadata tayi breakfast ganin rana tayi, saiya isketa tana waya da bily.


     Lokacin da Ummu ta fito Amaan ya fice, taja siririn tsoki tana zama tai ƴar kwalliya mara yawa, tare da ɗaura ɗankwalin daya zauna ɗas a kanta, ta birkiɗe jikinta da ƙamshi na musamman, daka ganta kaga amarya ta gaske, mayafi ta ɗauka a hannu da wayarta ta fito falon.

        Amaan na kwance cikin kujera idonsa a lumshe tamkar mai barci, sai dai idonsa biyu, ya tafi duniyar tunanine kawai a sashen aiki.

    Kallo ɗaya Ummukulsoom tai masa ta zauna cikin kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ta fara latsa waya.

       Ƙamshin mayen turarenta dake rikita lissafinsa ya mamye dukkan hancinsa da zuciyarsa, duk yanajin motsinta, sai dai yaƙi nuna hakan, kaɗan ya buɗe idanunsa a kanta yana ƙarema ƙwalliyar tata kallo, ta masa ƙyau sosai dan a asalin bahaushiyar tata take.

       Sai da ya gama ƙare mata kallo son ransa sannan ya buɗe idonsa sosai a kanta yana mata kallon kai tsaye.

   A jikinta taji ana kallonta, dan haka taɗago fararen idanunta tana kallon sa ba tare data ajiye wayarba.

    Gira ɗaya ya ɗaga mata. Ita kuma ta hararesa ta ɗauke idanunta.

        Janye nasa yayi shima ya maida ya lumshe, kusan seconds 10 ya sake buɗewa, wayarsa ya ɗauka ya shiga WhatsApp, kai tsaye inbox na Ummu ya shiga, ilai kuwa tana online, dama yayi zargin hakan ne, danya duba wayarta yaga ba kowanne chart takeba.

      Saƙo ya tura mata.

Tsabar mamakinsa saida ta ɗago ido ta kallesa, wato gata gashi zaune a waje ɗaya, tsabar bazai iya buɗe baki ba shine ya turo mata wai ta tashi suje su karya. Shareshi tayi.

   Ya sake tiro mata “Please mana Babie”.

      Leɓenta ta ciza na ƙasa, cikin son ƙureshi ta tura masa, “Indai bazaka faɗa da baki ba a barsa kawai”.

     Hannu ya kai saman kansa, dan wlhy ciwo yake masa saboda hayaniya, shi a ganinsa ba ƙaramin sake mata yakeba, yama kai maƙurar da yake ganin yazama mai surutu tsakanin jiya da yau.

   Wayar ya ajiye ya miƙe zuwa inda take, ya zare wayarta ya aje gefe, ɗago ido tayi ta zuba masa cike da tsiwa, sai dai yanda ya kafeta da nasa shima sai bakinta ya kasa furta komai. Ba tare da ya janye idanunsa ba ya ranƙwafo gaba ɗayanta ya ɗauka. Kallon kanta tayi ta kallesa da mamaki, ya lumshe mata idanu a hankali, dukda yaji tanada nauyi bai sauketa ba, sai takawa da ya farayi zuwa ga dani ɗin.

        Ya jawo kujera da ƙafa ya ɗorata akai yana ɗan sauke numfashi kaɗan alamar dai tanada nauyin.

        Ummu dai tsiwa ta koma ciki, sai kallon mamaki da take binsa dashi har shima ya zauna kujerar dake kallon tata, hannayensa duka ya saka cikin nata yana mai kafeta da idanu, duk yanda taso karsu haɗa ido hakan ya gagara, dan idanun nasa tamkar mayen ƙarfe haka suke, ba tare da tayi zato ko tsammani ba taji yace, “Ina ƙaunar ki Ummukulsoom, so irin wanda nake fatan mu kasance har a aljann...”

    Da sauri tai yunƙurin zare hannunta yay azamar sake damƙewa.

     Sosai ta kuma haɗe rai fiye da yanda tashi fuskar take shima, “Amaan karka yaudari kanka da wannan kalmar, domin Ummukulsoom ɗinnan ce dai ƙwaila mara ilimi daka sani, ba soyayya ta maidoni gidanka ba, na dawone danna rama *ALKAIRI DA HALLACI* ne kawai”.

     Tuni idanunsa sun fara canja launi, dan ya gama ƙosawa da yawan magana, daurewa kawai yakeyi saboda itace.

    Cikin halin ko in kula Ummukulsoom ta janye hannunta da idanunta ta hau buɗe abincin dake dani ɗin. Lafiyyen breakfast ne na musamman da Momcy ta shirya musu da hannunta, da kanta ta zuba masa ta tura gabansa, itama ta zuba nata.

      Sam taƙi yarda su kalli juna, abincinta takeci a nutse cikin kwanciyar hankali. Gani. taci kusan rabin nata shi baiko fara ciba sai ta kallesa, batare da tace Uffan ba ta janye idanunta tana taɓe baki.

    Tashi yay yabar wajen, ta bisa da kallo ƙasa-ƙasa harya shige bedroom.

     Baki ta taɓe taci gaba da cin abincinta hankali kwance. Tana kammalawa baƙi na shigowa, ashe ƴan buɗar kai har sunzo, saboda baki ƴan nesa da zasu wuce.

         Jitai gaba ɗaya damuwarta ta gudu ballema su murja ne dasu Nusaiba, duk sun fita a kamanninsu, idan ka gansu zuwa yanzu saika ɗauka sun kusa haihuwar kamar Ummukulsoom, dukda kasantuwarta mai jiki kuwa. Su kansu a duk lokacin da suke gabanta duk sai su raina kansu, sunsan Ummukulsoom tayi gaban da za'a daɗe ba'a cimmata ba, su Zeenat suna matukar yin takaici idan suka tuna sune suka cuci kansu da iyayensu, da yanzu suma suna tare da Ummukulsoom, amma gashinan ko ƴar secondary ɗinma basu kammala ba, dukda suna aure a birni babu wani cigaba a tattare dasu, tamkarma basuyi aji uku na makarantar ba.

        Tsokanarta suka shigayi sosai tana biye musu, dan sam Ummu bata da girman kai ko kyankyamin ƴan uwanta, ni'imar da ALLAH yay mata bata sakata bijirema gaskiya ba a mu'amulanta da kowanta.

      Wani abincin ta sake ɗibarma Amaan ta dora a babban tire, dan duk abinda ta tanadi masa bazata yarda ita ta cutar dashi ba, sauran abincin ta kawoma su murja, taje ta ɗauki nasa ta nufi bedroom ɗin.

    Hakanne ya saka su Hassatu fahimtar angon yana ciki kenan.

      

    Kwance ta iskeshi kan gado ya ɗora filo saman kansa ya rufe fuska, ta ɗanyi murmushi tana ajiye tiren a dirowar gefen gado. sannan ta zauna a gefen gadon kusa dashi kaɗan.

     Tunda ta shigo yana jinta, amma baiko motsa ba.

        “Karka ce zakayi fushi da abinci a kaina dan nikam babu ruwana, abinda kawai na sani shine bai cancanci zuciyarka a yanzu taso ƙwaila ba mai karancin ilimi a matsayin matar aure, dama matsayin yaya da ƙanwane zaifi dama-dama Alhaji, ga abincinan kaci, kokuma naje na sanarma Dad...”

    Ta ƙare maganar da miƙewa...

    Caraf ya riƙo hannunta, juyowa tai ta kallesa babu shiri, har yanzu kansa na cikin filon, zatai magana ya fisgota ta faɗo kansa gaba ɗayanta. Janye filon yay tare da ɗora ɗayan hannunsa saman bakinta jin zatai magana. Ya mirginata ta kwanta saman gadon sosai, yayinda shikuma ya maida rabin jikinsa a kanta yana zuba mata dukkan idanunsa cikin nata.

      Sosai tsoro ya shigeta, dan bata taɓa ganinsa a irin wannan yanayinba, idanunsa gaba ɗaya sun koma wani iri, hakama fuskarsa a matukar ɗaure take.

        Murya can ƙasan makoshi ya fara magana, “Duk abinda naso harna iya bayyanasa ga duniya koda a kan fuskata ce to lallai wannan abun mai matuƙar darajane a gareni” ya kama hannunta ya ɗora saman ƙinrjinsa “Saurara kiji yanda zuciyata ke nata gudun, ke lauyace, ko ban faɗaba ya dace ki fahimci mijinki a yanzu. ki kuma yafe masa laifinsa na baya, badan na wulaƙantaki na faɗa miki wancan maganarba, nayine domin ki zuciya wajen maida hankali a neman ilimi, wanda suke tunanin baki kaiba susan kinma wuce, ki tabbatarma da duniya babu wanda yafi wani ta hanyar dukiya ko ilimi sai wanda yakasance mai rinjayen tsoron ALLAH, sai dai ina roƙonki karki tambayeni dalili, dan sirrin wadda bazan iya tonawa asiri bane har ƙarshen numfashina, sai dai ki sani, ko wayar gari akai babu raina to *SON* kine sanadi Ummukulsoom”.

     Yana gama faɗa ya miƙe daga jikinta, baiko kalli abincinba ya fice daga ɗakin.


      Lumshe ido Ummukulsoom tayi a hankali maganganunsa na shiga kowanne sashe na jikinta, Amaan ɗane na ƙwarai da kowanne iyaye zasuyi burin samu, bai yarda ya zubdama mahaifiyarsa mutuncinta ba da ƴan uwansa a gaban matarsa, itama bayasan tozartata shiyyasa ya zaɓi shiga ƙuncin, maganar baba gaskiyace da yake sanar mata aduk yanayin data tsinci kanta ta kalli na ƙasa da ita bana sama da itaba, inhar bazata zama mai afuwa ba to itama baza a taɓa mata afuwa ba, kuma zuciyarta zata zama mai ƙishirwar samun salama a kowanne motsi na rayuwarta, da Amaan bason gaskiya yake mata ba bazai taɓa cigaba da bibiyar rayuwarta ba a ɓoye, da bazai kamu da ciwon hawan jini ba, dan kuwa Attahir ya bata result ɗin gwajin farko da akaima Amaan akasan yana da hawan jini, bayan ya saketa ne da wata ɗaya, damuwar da ya shiga ya sakashi kwanciya ciwo a syria, ga aiki da sukazoyi a gabansu, shine ya kaisa asibiti aka tabbatar masa yanada hawan jini, saida Attahir yayta ƙwalƙwalarsa da ƙyar ya sanar masa abinda ke damunsa akan rabuwasa da Ummukulsoom, amma sam sai yaki saurarensa a lokacin shima dan kawai ya horasa, har suka baro Syria Amaan hankalinsa baya tare da tunaninsa, ba komai ke kuma tada masa hankaliba sai ganin ya zalunceta, abinda yay mugun tsana fiye da komai kenan a rayuwarsa........

       Saƙon daya shigo a wayarta ne ya maidota hayyacinta, ta ɗauki wayar ta duba duk zatonta ko bily ce, amma sai taga Amaan ne, da mamaki ta buɗe saƙon.

     *_“Ba kowace zuciya bace zata fahimceni, ba kowane tunani bane zai fassara manufata, ba kowanne alƙali bane zai adalci a shari'ata, ni kaina nasan na cancanci Ummukulsoom ta tsaneni, dan babu mace data san darajar kanta da za'a jefeta da kalmar ƙwaila mara ilimi bata zafeta ba a rai da rayuwa, ni kaina dana faɗa a tsawon shekara shidda kalaman sunamin zafi balle ke dana faɗawa, kunyar furtasu ce yasa na ɓadda kama nazo miki matsayin Abdul-Waheed, bazan tilastaki ki soniba Ummukulsoom, sai dai ina roƙonki dan ALLAH ki yafemin ƙuntata miki danai da waɗannan kalaman, har abada bana sha'awar rayuwa ko mutuwa da haƙƙin wani a kaina koda da mummunan kallone....”_*  

        “Lokaci yayi da zaki manta komai ki karɓi Amaan Ummukulsoom”.

    Maganar Maman Ahmad ta doki dodon kunnenta, a firgice ta kalleta, saita ganta zaune kusa da ita alamar tare suka karanta saƙon.   “Aunty Hafsat yaushe kikazo?”.

     “Tun sanda kika fara karanta saƙonnan Ummu, dan kuwa nazo zan shigo naga Amaan ya haɗa kai da mota a harabar gidannan, hakanne yasa na fahimci akwai matsala, halan rashin kirki kika gwada masa a daren jiya?”.

     Jiki a sanyaye Ummu ta girgiza mata kai, “Wlhy banyi masa komaiba ni, kawai dai da safennan ya furta kalmar yana sona nikuma nace mizaiyi da ƙwaila mara ilimi”.

      “Banga laifinkiba da kika furta masa hakan, dan yanada ƙyau yakuma sanin darajarki, sai dai shawarar dazan baki Ummu ki ture komai a ranki ki zauna lafiya gidan aurenki, duk wani mutunci da kike tunanin kankaroma kanki ga Amaan mahaifinsa ya gama kankaro miki shi a gaba ɗaya ahalin Amaan ba Amaan kawai ba, ki kalli ƴan uwanki kawai kiga yanda kikai musu rata, Amaan mutumin kirkine, baya shaye-shaye ko neman mata, baya duk wani ashararanci da sunan wayewa, a zamanku bai taɓa cuta mikiba ko muzguna miki, rashin kulawa dake kuwa auren haɗi akai muku, ku duka babu wanda ke kula juna k da shi, iya jigata Amaan ya jigatu akanki, tun bayan rabuwarku bai sake sukuniba, dan ALLAH ki yafe masa dan nasan kema wlhy kina sonshi Ummukulsoom, kina dannewane kawai”.

      Shiru Ummukulsoom tayi tana haɗiye wani yawu mai kauri a maƙoshinta, duk abinda Maman Ahmad ta faɗa gaskiyane, dan irin haka Hajiya yaya da Gwaggo hinde suka faɗa mata, irinshi Inna laraba da Ummi da bily da Attahir suka faɗa mata, irinshi babanta da Abba suka faɗa mata, to mizaisa ta cigaba da kafewa akan abinda baikai ya kawoba, kowa yana kuskure ai a rayuwa ko, sam batai zaton yanada sauƙin halima irin hakaba, dan daga jiya zuwa yau da aka kawota gidan duk da rashin son maganarsa haka yaketa ƙoƙarin lallaɓata domin kawai ta fahimcesa......

     “Ummu karki ƙuntata ranki inhar bakison Amaan, tashi muje ke ake jira, dama kiranki nazoyi”.

     Ummu batace komaiba ta tashi, fuskarta ta gyara kamar yanda maman Ahmad ta umarceta suka fita.

     A mamakinta su murja duk sunbar falon, sai Amaan kwance cikin kujera Attahir na gefensa, da alama dai akwai matsala, dan yanda Attahir ya watsa mata harara kawai ya isheta amsa.

         Risinawa tai ta gaida Attahir, ƙin amsawa yay ya ɗauke kansa, Amaan na jinsu, sai kuma yaji babu daɗi da Attahir bai amsa mata gaisuwarba, amma baice komaiba.

       Jiki a sanyaye tabi bayan maman Ahmad suka fice.

     Saida Maman Ahmad ta fara rakata ta gaida dad da Momcy sannan aka maidota tsakar gida inda buɗar kai ya gudana, ba wani lokaci aka jaba, rabone kawai sai nasiha da aka ƙara mata, harda ƴan ƙwallanta da zasu tafi kuwa, sauƙintama anan aka bar maman Ahmad, sannan ba'a maidata sashen taba tana wajen Momcy daketa nan nan da ita kamar ƙwai ɗaya a miya.

      Suma wasu cikin ƴan Ajiwa aranar suka tafi, sai makusanta sosai aka bari, dayake zuwa yanzu Momcy karɓar mutunci take musu, dan sunga canji sosai a wannan bikin, waɗanda basusan abinda ya faruba sunata mamakin canjawarta............✍🏻



Babbar hasara a lahira shine ka samu ladanka a cikin littafin wani, ko ka samu zunibin wani a cikin littafinka. Kada ka zalunci mutane. Kada ka shiga cikin haƙƙinsu. Idan ka yi haka za su washe ladanka ko su lafta ma ka zunubinsu


NO. 49


 ............Koda maman Ahmad ta maido Ummukulsoom sashensu basu iske Amaan ba, ita takuma ɗan mata gyara kafin ta ƙara mata nasiha ta wuce akan sai sun haɗu a legas. 

       Tun Ummu na ɗari-ɗarin shigowar Amaan har ta saki jikinta, dan kuwa ko alamarsa babu har bayan sallar isha'i, kiran Bily tayi suka gaisa, tai mata yaya jiki?. Basu wani jimaba suka yanke wayar dan Muhsin na tare da ita, wayar Aziza ta kira, sai dai kuma a kashe, “A lallai amarcin naki mai lasisine Aziza” Ummukulsoom ta faɗa a fili, dan tun safe take neman Number Azizan amma a kashe, da su murja zasu wuce har saƙo ta basu akan su cema Azizar ta kirata, dan sunce can zasuje daga nan su kama hanyar gida.

         Buhayyah ce ta kawo musu abinci, bata wani zauna ba ta koma sashensu, dan tana shakkar Amaan yazo ya isketa a sashen.

     Tun dai Ummukulsoom na kawaicin rashin shigowar Amaan harta gaza ta fara kallon agogo, amma kamar almara har 10pm tama gota, jiki a sanyaye taje tai wanka ta fito, ko kallon abincin da Buhayyah ta kawo bataiba.

    Ganin fa wankin hula zai kaita dare sai ta fara lalubo Number ɗinsa daya bata a amatsayin Abdul-Waheed, sai dai tana kiran wayar sai taji ring ɗinta a ɗakin, waige-waige ta farayi tana kasa kunne wajen gane inda take, saman gado da take jiyota ta nufa, ta ɗaga filo sai taga wayar a wajen.

     *_Noorulain_*.

    Tsirama sunan ido tayi har kiran ya yanke, sai maimaitawa take a zuciyarta tamkar ta samu karatun salla.

      Amaan dake bayanta ya miƙo hannu ya zare wayarsa, a ɗan rikice ta waigo ta kallesa, tamau fuskarsa take babu alamar sassauci, ba tare da ta shiryaba idanunsu suka shige cikin na juna.

    Shine ya janye nasa cikin salon nasa na lumshe ido yana barin wajen, ta bisa da kallo ƙasa-ƙasa harya shige bathroom.

     Kaɗan ta sauke ajiyar zuciya, ta zauna bakin gadon tamkar wadda ƙwai ya fashema a ciki, ɗan sake matan da yayi daga jiya zuwa yau sai taji babu daɗi yanzu da fuskarsa ke a ɗaure matuƙa, ta ɗauki tsawon lokaci a wajen zaune, kamar yanda shima ya daɗe a bayin bai fitoba.

      Ɗaure da towel ya fito a ƙugunsa, yayinda hannunsa ke riƙe da ƙarami yana goge wuyansa zuwa ƙirji, kallo ɗaya yay mata ya lumshe idanu yana sauke numfashi da ɗan nauyi. Ko kaɗan bayason ganinta a yanayin damuwa, ya tako a hankali zuwa gareta, batare da Ummukulsoom tasan da zuwansa ba taji an janye hannun datai tagumi da shi.

    Kaɗan ta kallesa ta kauda ido saboda wata faɗuwar gaba da taji, ganinsa gabanta gingirin babu kaya ba ƙaramin harbawa zuciyarta tayiba dan tsoro, dama ga firarta da Bily ta ɗazun da safe ta kasa barin ranta, musamman ma furucinsa data yini dashi a arai tana tunani.

    Baice da ita komaiba yabar wajen zuwa gaban mirror, tamkar munafuka haka Ummukulsoom ta miƙe zata fita, harga ALLAH bazata iya zama yay shiri a gabanta ba, duk yana kallonta ta cikin madubin amma ya basar.

     Harta kama handle ɗin ƙofar zata murɗa yay magana da ƙyar, wadda Ummu ma sam bata jisaba.

      Kanta a ƙasa saboda batason kallonsa a yanayin da yake ta ɗan turo baki gaba tana faɗin, “Nifa banji mi kace ba ALLAH”.

      Juyowa yay ya kalleta sosai na wasu seconds, sai kuma ya ɗauke idonsa yana takawa gaban Wadrobe ba tare daya maimaita mataba.

   Takaici ya kama Ummukulsoom, ita kanta tasan zama da irinsu Amaan saika daure, dan takanji firar halin miskilamcinsa ga Attahir, duk da itama taɗan zauna dashi taga wani.

     Sai da ya ɗauko kayan barcinsa sannan ya koma gaban mirror inda ya ajiye wayarsa yay gajeren rubutu ya tura mata a waya.

    Wayarta tai ɗan motsi alamar shigowar saƙo,  Sam batai zaton shi baneba, dan haka ta kalli wayar zatonta ko Bily ce ko maman Ahmad.

     *_Coffee nakeso_*

Iya abinda ya rubuta kenan kawai, Kasa daurewa Ummu tayi, sai da ta ɗago ta kallesa, shima kallon nata yakeyi, dan haka ya ɗan langaɓe mata kai alamar “Please”.

     Batace komaiba ta girgiza kai kawai, dan wannan gayen addu'a kawai yake buƙata akan wannan halin nasa da babu mai rabashi dashi sai ALLAHN daya haliccesa da kayansa.

    Kusan Mintuna talatin ta dawo ɗauke da mug a saman ƙaramin tire da ruwa, da alama dai har sashen su Momcy taje ta haɗo masa, dan kayanta na nan babu abinda aka haɗa tunda ba zama zasuyiba, andai jibgesu a kicin ɗin ne kawai.

      Tashi yay daga kwanciyar da yayi a saman gadon, taɗan saci kallonsa saboda ya mata ƙyau cikin kayan barcin nasa marasa nauyi da suka lafe masa a jiki, ga wani ƙamshi na musamman yana fitarwa. Taja Copy table ɗin dake gefe ta ɗora tiren.

    Harta yunƙura zata bar wajen yay azamar cafko hannunta, rumtse idanu tayi ba tare da ta juyoba. “Mikake buƙata kuma?” ta faɗa a haka.

     Bai ce da ita komaiba ya jawota baya ta zauna saman gadon rabin jikinta a nasa. Gaba ɗayansu turaren junansu ne ya daki hancinansu, kowa ya shaƙa yana jin wani nishaɗi na musamman da saka ƙwanciyar hankali.

      Ganin bashi da niyyar magana bare sakinta sai ta ɗago ido ta kallesa, hakanne ya bashi damar janye hijjab ɗin jikinta, tai saurin riƙe hannunsa tana ɓata fuska, amma sam bai bata damar dakatar da shiba sai da ya cire shi. Ƙyawawan kayan barcinta pink suka bayyan, wandone iya gwiwa sai rigarsa itama dai bata da girma da hanunta siriri, sosai kayan suka zauna mata a jiki kasantuwarta mai cikar halitta da murjewar jiki. Babu shiri Amaan ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, yayinda ƙasan zuciyarsa shawarar Attahir ke dawo masa dalla-dalla.

    Ummukulsoom kam fuskarta ta ɗora saman damtsen hannunsa saboda harga ALLAH taji kunya ta kamata, zuciyarta ta shiga tsitstsinkewa jin ya saƙalo tattausan hannunsa ta bayan ƙugunta ya ɗorasa saman cikinta.

      Duk yanda taso ta fuske saita kasa, ta kama hannunsa zata janye ya kuma ƙanƙameta, murya na rawa tace, “Dan ALLAH ka bari, wlhy hakan bashi da ƙyau”.

    Taso bashi dariya, amma kasantuwarsa gwanin ɗaurewa saiya fuske yana ɗaukar coffee ɗinsa da ɗayan hannun ya hau shan kayansa a hankali yana wani lumshe ido.

     Ita kam ta gama sakankancewa da halin Amaan gaskiya, sai kace wani kurma...?

     Haka kawai yaji a ransa gulmarsa take da zuciya, dan haka yaɗan mintsini gefen cikinta.

     Babu shiri ta ƙankamesa tana sakin kukan shagwaɓa da kiran sunan Ummi, dan ta ɗanji zafi.

     Kofin ya ajiye ya maido dukkan hankalinsa gareta, “Kinci abinci?” ya faɗa a hankali kamar bayaso.

     “Ni na ƙoshi, ka sakeni barci nakeji wlhy”.

     Baice mata komaiba ya jawo ledar daya ajiye da hannu ɗaya, kallonta yay yana mata alama data buɗe ledar.

    Kamar zata sharesa sai kuma ta kasa, dan ta tuna nasihar Inna laraba ta ɗazun a gareta.

      Gasashshen kifine irin na musamman ɗinnan, ya haɗu iya haɗuwa, dan babu shiri yawun bakin Ummu ya shiga tsinkewa, a ranta kuwa rayawa take shi ango na zuwa da kazar amarci shi da kifi yazo, kai wannan bawa lamarinsa sai shi.......

       Tunaninta ne ya katse jin yatsansa saman laɓɓanta tare da kamshin kifin da yasha gashi, kauda kai taso yi zatai magana ya tura mata kifin a baki. Duk yanda Ummu taso zamewa kar taci kifinnan Amaan ya hanata kowacce damar kufcewa, dole ta haƙura ya bata da kansa iya yanda yaso.

    Shiko ko kaɗan bai ciba, ya kama hannunta zuwa bayi wai zai mata brush, yanzun kam ƙin yarda tayi sam, sai shima kawai ya barta yay alwala ya fito.

     Da harara ta raka bayansa, sannan itama tai alwalar kasancewar ta riga ta saba a duk dare idan zata kwanta sai tayi koda kuwa tana prioud ne.

       Zaune ta iskeshi bakin gado sanye da jallabiya saɓanin kayan barcin, ta ɗauke idonta zata nufu gado ya dakatar da ita da faɗin, “Tashi muyi salla”.

      Dakatawa tayi da yunƙurin kwanciyar ta zuba masa ido jin yanda yay mata magana murya a dake, sannan fuskarsa babu walwala. Wani kwarjini na musamman taga ya sake mata, ta sakko domin bin umarninsa tamkar yanda addini ya koyar da ita da tarbiyyar musulinci.

      Hakan yasaka Amaan jin daɗi da karajin kaunarta, ya kuma aminta da tarbiyyar Ummukulsoom hundred percent, ita ɗin ƴar ƙwarai ce mai bin umarnin iyayenta da aiki da ilimin islama ba wayewar boko ba dajin itama ta isa akan komai, musamman ma dashi ya kasance mai laifi a gareta, ashe dai ƙaryar mutane dakema mata kudin goro wajen faɗin dasun samu zurfin ilimi saisu zama bijirarru masu ra'ayin kansu saboda sunajin kansu dai-dai da kowa, wato abin ba'a bokon yakeba atarbiyya yake, tun farko daga yanda tarbiyyar mutum ya tashi to haka dukkan rayuwarsa ke wanzuwa koda shine yaga karshen biro kuwa.

    Sun gabatar da salla raka'a biyu, Amaan ya juyo ya dafa kan Ummukulsoom yana ambaton addu'ar nan da duk wanda yay sabon aure ya kamata yayita ga iyalansa.

    “اَللَّهُمَّ  إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا، وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا، وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ.

*_Allahumma innee as-aluka khayraha wakhayra ma jabaltaha 'alayh, wa-a'oothu bika min sharriha washarri ma jabaltaha 'alayh._*

       _Ya Allah ina rokon Ka laherinta da alhrin da Ka dabi'antar da ita a kansa, kuma ina neman sarinka daga sharrinta da shaarrin Da ka dabi'antar da ita a kansa._

        Kan Ummukulsoom a duƙe harya kammala ya janye hannunsa yana ɗaga hannunsa sama da cigaba da jero addu'a, sai dai kuma a ɓoye ba'a filiba.

      Itace ta fara miƙewa ganin sun kammala, gaba ɗayan jikinta a sanyaye yake, shi kansa ya gama lura da ita tsaf, amma sai ya basar kawai. 

    Can ƙarshen gado ta kwanta ta juya masa baya bayan ta cire hijjab da zanin jikinta, uffan baice mata ba, sai baima hau gadonba yaja wayarsa yana danne-danne tsawon lokaci har barci ɓarawo ya sace Ummukulsoom. Sai da ya tabbatar barcinta yay nisa sannan ya tashi ya kwanta shima.

     Tamkar yanda suka kwana jiya yauma hakane ta kasance, da asuba yau ta rigashi tashi, motsinta a bayine ma ya tashesa.

     Koda ta fito bata amince sun haɗa ido ba ta raɓa gefensa ta wuce inda abin salla yake. Shima alwalar yayi ya fice.


     Yau kam har gari ya fara haske bai shigoba, ga hadari daya ɗaure garin kasancewar damuna taɗan fara zama, sai zuwa can lokacinma Ummukulsoom ta gama gyaran ko'ina tasa turaren wuta ya shigo, har iskar hadari mai fidda ƙamshin ƙasa ta fara busawa a hankali.

     Shigar Ummu bayi kenan Amaan ya shigo, da alama dai motsa jiki ya zarce saboda ganin hadari, dan jikinsa sai zufa yake dukda iska mai sanyi da saka jiki kasala da akeyi kuwa, duk da yasan tana ciki saboda neman magana sai ya cire kayansa ya nufin bayin. Murɗawar farko ƙofar ta buɗe, Ummukulsoom dake zubama jikinta ruwan dumi wani daɗi na ratsata taji an buɗeta.

    Yanda ta ɗago kawai zai tabbatar maka tashiga ƙarshen firgita da ruɗani, musamman datai tozali da wanda bata taɓa zato ko tsammanin ganiba, ta dunƙule jikinta waje ɗaya bayan ta duƙe zata kwalla ƙara...

      Ko'a kwalar rigarsa shikam, amma ganin zatai ihu ne ya sashi isa gabanta cikin taku biyu kacal ya dora tafin hannunsa akan bakinta.

     “K lafiyarki kuwa?” yay maganar cikin kunnenta a hankali.

     Hannunsa ta fara turewa hawaye sun cika idonta taf, sai dai yaki bata damar cirewar, saima towel ɗin jikinsa daya saki ƙasa tare da sakar musu ruwan yana zuba a jikinsu.

        Yau kam Ummu takuma ƙara tabbatar da rashin ta idon Amaan, shi komai nasa kai tsaye yakeyinsa, babu ruwansa da dai-dainsa ga waninsa ko akasin haka, indai shi yay masa dai-dai to dole yazama dai-dai ga kowama da abin ya shafa.

        Da kansa yay mata wankan idonta arufe, hakama hannunta ta rufe ƙirjinta dashi ruf, duk dai yanda yaso ta saki jikinta ayi wankan ƙi tayi, dole ya wanke mata iya inda zai iya ya ɗaurayeta tare da ɗaukar bathrobe kalar ruwan toka ya saka mata, ko sashen da yake bata kallaba, tai azamar fitowa ta barsa a bayin saboda wani kuka da taji ya taho mata ba tare da tasan dalilin yinsa ba.

         Amaan ya lumshe idanu ya buɗe a hankali fuskarsa na fidda wani ɓoyayyan annurin murmushi.

     Koda ya fito saiya iske Ummukulsoom kwance a gado rufda ciki tana shashshekar kuka..

     Sosai ta bashi mamaki, to miye abin kuka anan? Sai kace wani abun ashsha suka aikata, Cike da nutsuwarsa yazo bakin gadon ya zauna yana ɗora hannunsa saman bayanta, ko motsi ƙinyi tayi duk da tanajinsa.

    Jikinta ya kwanto sosai ya sakar mata nauyinsa har numfashinta na fita da ƙyar.

      “Yanzu nan dan kin samu ladan yin wanka da mijinki shine abin kuka? Indai hakane to bara na kawo ƙarshen komai kawai ki kuma tabbatar da cewar Usman mijin kulsoooom ne”.

      A yanayin daya karasa sunanta da yanda yake mata raɗa a kunne sai gaba ɗaya tsigar jikinta ta tashi, ta haɗiye kukanta babu shiri jin yakuma sanyaya murya da narketa yana cigaba da faɗin, “Ki karɓa, ALLAH ya riga ya baki indai Amaan ne”.

    Haushi ya kama Ummukulsoom, an faɗa masa damuwa tai dashine, “Ai ni bana amsar abinda bai minba” ta faɗa cikin gatse.

      Birkitota yayi ta dawo rigingine, ya zuba idanunsa cikin nata dake zabga masa harara tana yunƙurin kwacewa, iya ƙarfinsa ya matseta tare da canjama kallon nasu sabon salo ta hanyar ɗora fuskarsa kan tata ya  haɗe b.....”

        A salon da yake binta duk jaruntarta kasa jurewa tayi sam, dan tariga da takai age ɗin da  jikinta yasan ma'anar saƙonsa, tun tana ɗaukar lamarin da wasa harya fara caja mata kai, dan tuni ya canja layi ma gaba ki ɗaya zuwa abinda sam bata kawo a ranta ba, musamman a yanda yay biris da ita a kawanki biyunnan, ko jiya daya nuna mata take-takensa daga ƙarshe ai basar da ita yayi.


★★★★★

       Sabon salo kenan, anguna na angwanci da daddare shi da safe yay nasa.

    Ummu kwance luf a jikinsa tana tsiyayar da hawaye masu ɗumi dake sauka a saman ƙirjinsa, shiko har cikin zuciyarsa yake jin saukarsu, sai dai sam yakasa buɗe baki ko sau ɗaya yay mata magana, sai faman shafar sumar kanta daya hargitsa yakeyi a hankali yana sauke tagwayen ajiyar zuciya shima.

       Wani so na haƙiƙa mai ratsa zuciya da ɓargon jiki yakeji akan Ummukulsoom, ji yake kaf duniya yafi kowa sa'ar mace ta gari, dama a ko yaushe cikin ƙyautata mata zato yake, sai gashi kuwa ya zama na farko a gonar da ALLAH yay masa ƙyauta ba tareda wayonsa ba ko dabararsa, kuma ƙanƙameta yayi a ƙirjinsa, yakai bakinsa saman goshinta ya sumbata sau biyu zuwa hancinta yana cigaba da sauke ajiyar zuciya tamkar shike kukan ba Ummukulsoom ba.

      A tare barcin wahala ya kwashesu, dai-dai sannan kuma ruwa ya kuma ɓallewa tamkar da bakin ƙwarya, yayinda garin ke kuma ɗaukar wani sanyi mai saka zuciya nutsuwa musamman idan kana tare da abin sonka.

  

     Barcinsu sosai sukasha, ita Momcy duk ta damu ba'a kawo musu breakfast ba, haka ta taso Bassam cikin ruwan ya kawo musu breakfast ɗin, tsit yaji falon, dan haka ya ajiye ya juya ya fita gudun aikata wani laifi.

         Kamar wasa barci yaja su Ummukulsoom har ƙarfe ɗaya na rana, kuma har lokacin ba'a daina ruwa ba .....


  Mutane masu son zuciya ma sunada rana a gareka, koba komai zasu tara maka ladansu ka karɓa a ranar da kowa ke fafutukar neman ƙari a littafin ayyukansa. Dan haka karkai baƙin ciki da zaluncin azzalumi, koda ɓatanci yay maka bisa son zuciya ribace a gareka, shi ko bai gane faɗuwace a garesa sai randa babu wata ƙofa ko damar da zai roƙi gafarar ka._*



NO. 50


........Amaan ne ya fara farkawa, buɗe idanunsa yay a hankali bisa fuskar Ummukulsoom dake barcin wahala, hawaye duksun bushe mata a fuska, ya tsira mata ido yana ƙare mata kallo irin wanda bai taɓa mataba.

     Komai nata abin birgewane, yanayin fuskarta irin na mutane ne masu karancin son hayaniya, sumbatar goshinta yayi yana sake cusata jikinsa, ji yake kamarma ya haɗiyeta shidai ya huta da zogin sonta dake ƙara faɗi kullum a zuciyarsa, shi kansa yasan ALLAH ya jarabcesa ne da son Ummu domin ya nuna masa iyakarsa shida mahaifiyarsa da ƴan uwansa, inda a labari akace akwai irin wannan soyayyar dake mamaye zuciya da jini da saiya ƙaryata, yama ce mai bada labarin mahaukaci ne, amma abin mamaki da al'ajab sai gashi shi ALLAH ya jarab cesa akan wadda yake ganin a baya bata kai ya sota ba.

       Kuka Ummukulsoom data farka ta sakar masa jin ya matseta a jikinsa ko numfashinta da ƙyar yake fita, sassauta mata riƙon yayi yana maida dukkan hankalinsa a gareta.

        Hawaye Ummu take wasu na korar wasu, dan ita kaɗai tasan irin azabar da takeji, har acikin barci a takure take. Amaan ya tashi zaune yana janye bargon da suke lulluɓe, bayi ya nufa ya haɗa mata ruwa mai ɗumi ya dawo. Har yanzu kukan take, bata taɓa sanin muguntar Amaan takai hakaba sai yau, da farkone ya bita a hankali, amma da labari yay nisa saiya manta da tausayin nata ya cigaba da binta da dukkan ƙarfinsa, a fili tace, “kai jama'a, ALLAH ya tsinema masu yin iskanci, banzaye duk wannan azabar da akesha haka suke kai kansu saboda ƙwaƙwalwar kifine dasu”.

    Amaan daya duƙo zai tadata maganarta karaf a kunnensa, harga ALLAH ta bashi dariya, kasa daurewa yay sai da ya murmusa kuwa, sannan ya ɗora bakinsa saitin kunnenta yana mata raɗa, “Gaskiyarki Babiena ALLAH dai ya shiryi masu iskanci”.

    Hannu tasa ta ture fuskarsa tana kuma sakin wasu hawayen masu ɗumi, gaba ɗaya haushinsa takeji wlhy.

       Duk yanda yaso ta tashi ƙi tayi saboda babu kaya a jikinta, da bargon take ƙudundune, rigar wankan data fito da ita ya shiga lalube, ya jawota yana ƙoƙarin saka mata ba tare da yayi magana ba, sai lokacin ta yarda ta tashi, sai dai taƙi kallon koda sashen da yake sam, ga hawaye har yanzu tanayi wanda shi yama rasa na miye hakan? Taku biyu tayi ta faɗa jikinsa tana fashewa da kuka mai ban tausayi, wanda ya nema rikita lissafin Amaan gaba ɗaya, dan ya lura akwai matsala gaskiya. Komar da ita yay bakin gadon ya zaunar fuskarsa cike da matuƙar tausayinta.

     “Miya farune?” ya faɗa a hankali.

     “Wlhy zafi, bazan iya tafiya ba, nashiga uku Ummi ya kasheni”.

     Tausayi ta bashi, duk jikinsa saiya kuma yin sanyi ƙalau, haka ya miƙe dukda ta masa nauyi ya ɗauketa zuwa bayi. Ummu taso tayi dauriya ganin yanda Amaan ya damu sosai, sai dai kuma ta kasa, dan ƙara mai ban tausayi ta saki lokacin daya sakata cikin ruwan ɗumin daya haɗa, ta ƙanƙamesa sosai tana sama da numfashi tamkar zata shiɗe.

     Lallai akwai matsala da gaske kenan, rasa miya kamata yayi yay, dole ya haɗa musu ruwan wanka sukai na tsarki kawai ya ɗakkota suka fito, dan lokacin salla ya gota.

     A daddafe Ummu tai salla, dama zazzaɓi mai zafine a jikinta, yanzu saiya ƙara turewa jikin yay ringis har haƙoranta na haɗuwa wajen rawar sanyi.

        Rasa abinda zaiyi yayi, sai zanin gadon kawai daya canja ya maidata kan gadon ya lulluɓe da bargo, yanata safa da marwa tsakanin falo da ɗaki, rashin mafita ta sashi kiran Attahir, bawai ya sanar masa abinda ke faruwa bane, yadai ce masa Ummu ce bata da lafiya.

      Sam Attahir bai kawo komai a ransa ba ya faɗama Ummi, dan suna zaune a falon Abba ne suna magana, aikin yamma ne da ita yau, ga ruwa kuma da aka tashi dashi, danma zuwa yanzu ya ɗauke sai yayyafi da akeyi kaɗan-kaɗan.

      Cokali Ummi ta ajiye tana faɗin, “tofa, ALLAH yasa ba Thypoid ɗin tace ta motsa ba, bara naje na fara dubata saina wuce asibiti”.

        Attahir yace, “Bara na kaiki to Ummi”.

     “A'a kayi zamanka ka huta, kunga ga baƙi a gida bazasuji daɗi dukmu fice mu barsu ba, nima zuwa 9pm insha ALLAH zan dawo gida Dr Sarah saita karɓeni da wuri”.

     Addu'ar dawowa lafiya sukai mata, sai dai kuma maman Ahmad tana zargin anya ba Amaan bane ya angwance? Badai ta furta ba tabar zancen a ƙasan zuciyarta ne kawai. 

         

     Momcy daketa kiran wayar Amaan ce yaƙi ɗagawa ta miƙe tana tunanin lafiya kuwa? Dan Dad ma ya kirasa bai ɗagaba, da farko tayi tunanin ko barci suke, amma ganin lokacin salla ya wuce tasan sun tashi sai itama ta kira,  dan Dad soyake ya fita zaije sokoto, Amaan ɗin kuma yace masa gobe zasu wuce, bai zama lallai ya dawo ya samu basu wuceba.

     Yana zaune a bakin gadon kan Ummukulsoom a saman cinyarsa yana shafawa, yayinda ya jingina jikinsa da gadon idanunsa a lumshe, zafin jikinta na ratsashi har cikin ƙashi. Sauraren isowar Attahir yake da yace zaizo da Doctor ta duba Ummukulsoom, shi sam bai kawo Ummi zatazo da kanta ba........

     Knocking ƙofa da yaji anayine ya sashi buɗe idanunsa ya tashi zaune sosai, a hankali ya zame kan Ummu a cinyarsa ya ɗora kan filo, barcin wuyane ya sake figar mutuniyar taku😂😝⛹🏻‍♀️.

        Yana buɗe ƙofar falon sai yaci karo da Momcy, sam baiyi zatoba, ta kallesa sama da ƙasa tana mamakin ganinsa a sanyaye.

       Matsa mata yay ta shigo ganin yayyafi na jiƙata, “Fodio baka da lafiya ne? Tun ɗazun muke kiran wayarka amma kaƙi ɗagawa?”.

       Da ƙyar ya iya cewa, “A'a Momcy”. Shi saima yanzu ya tuna da anan falo yabar wayar, gashi a silent take.

    Hannu ta ɗora a wuyansa sai taji jikinsa normal, ta sauke numfashi tana waige-waigen neman Ummukulsoom, “Ina yarinyata?” tai tambayar cikin kafesa da ido.

       Da hannu ya nuna mata bedroom.

    Zama tai a hannun kujera tana faɗin, “Jeka kiramin ita”.

    Shiru yay bai motsaba, sai da ya zuƙi iska ya fesar kafin yace, “bata da lafiya”.

    Bata gama saurarensa ba ta nufi ɗakin kai tsaye, binta yay shima, dan shikam bashida wata mafitar data wuce yabar Momcy ta taimaki Ummu, wlhy yarasa yaya zai mata, shi sam tunaninsa bai kawo ciwo tajiba ko wani abu, yafi ɗaukar abun matsayin bata saba ba daga shi har ita.

         

      Hannu Momcy ta saka akan goshin Ummukulsoom, zafi rau har huci yake, ta rumtse idonta tana faɗin “Ya salam, fodio tana cikin wannan halin amma kai shiru ko asibiti bakai yunƙurin kaita ba?”.

      “Bazata iya bane Mom, na kira Attahir zaizo da Doctor ”.

    Jitai kamar ta makesa, kai itakam indai wannan miskilancin Fodio zaima Ummu tana tausayinta, yanda itama take shan wahalar zama da Dad ɗinsu tasan Ummu zata fuskanci ma fiye da hakan, sai dai kuma akwaisu da tattalin mace idan sun keɓe, dan a hakama da suka manyanta a kullum Dad cikin faɗaɗa soyayyarsu yake, sai dai idan ta bata masa raine kuma babu ragi babu ragowa.

    “Kaga ɗauka key muje asibiti kawai” tai maganar tana yaye bargon da Ummu ke ciki, ALLAH ya sosa ya saka mata doguwar riga lokacin da zasuyi salla.

     Buɗe ido Ummu tayi tana yamutsa fuska zata saka masa kuka, duk zatonta Amaan ne ya buɗeta. Ganin Momcy sai tai yunƙurin tashi da hanzari, wata azaba ce ta ratsata, babu shiri ta koma ta kwanta tana sakin kuka.

    Runtse ido Amaan yayi saboda tausayinta, yarasa mike mata ciwo, gashi taƙi faɗa masa.

        Shiru Momcy tai tana kallon Amaan ranta a ɓace, dan zuwa yanzu kam tagama fahimtar inda matsalar take.

     Cike da basarwa ya janye idanunsa daga momcy yana tura dukkan hannayensa a aljihu, kafin ta samu damar masa magana akai knocking ƙofar falon. Dama hanyar kuɓuta yake nema daga tsatstsaresan da Momcy tayi da manyan idanun daya gada.

      Duk tunaninsa Attahir ne, yana buɗe ƙofar yaci karo da Ummi aunty nurse na biye da ita, da alama dai can sashen ta fara zuwa aunty Nurse ta rakota nan.

       Risinawa yay ya gaida Ummi kansa a sunkuye, dan harga ALLAH baisan tsiyar da Attahir ya shuka masaba kenan, kasa binsu yay ɗakin, ya kuma dakatar da aunty Nurse da ido alamar karta bita.

    Tasan halin kayanta, dan haka ta dakata a ƙofar tana cema Ummi ta shiga ciki.

     Momcy na zaune ta rungume Ummu jikinta tana lallashi, Ummi ta shigo.

       Hannu biyu da mutuntawa Momcy ta amshi Ummi, to dama ƙawayen junane, danma Ummi ce bata cika sakema Momcy ba saboda batason wasu halayyarta musamman ƙyankyamin talaka.

    “Tofa, kice tana nan tana miki shagwaɓa”.

    Dariya Momcy tayi kawai, dan itakam tausayin Ummu take har cikin ranta, duk da kuwa bataga ɓarnar da ɗan nata ya aikata ba.

     Fita Momcy tayi ta basu waje acewarta zata haɗoma Ummukulsoom abinda zataci, Ummi bata kawo komai a ranta ba takai hannu a wuyan Ummukulsoom tana kafeta da idanu dayin nazarinta, yanda idanun Ummu suka kumbura ne ya bata mamaki, da alama dai kuka tayi bana wasaba.

     “Autana mike faruwa? Dan wannan zazzaɓin kukane ya kawoshi?”.

     Langaɓewa Ummu tayi jikin Ummi tana kuma sakin kuka, “Nidai Ummi kije dani gida kawai”.

     Tsura mata ido Ummi tayi ba tare da tace komaiba, tana son tabbatar da abinda take zargi, dan haka ta janye Ummukulsoom a jikinta tana miƙewa tare da miƙar da ita, Ummu taso ta daure yanzun ma dan kar Ummi ta gane, sai daifa ta gaza hakan, dan hawaye har rige-rigen zuba suke.

       Ummi ta girgiza kai kawai danta gama fahimtar komai, maidata tayi ta zaunar zuciyarta na mamakin halin maza na yanzu, sam basama budurcin mace da sauƙi, a da idan aka kaima miji mata saiya haɗa wata yana lallaɓata kafin ma ya kai ga nemanta, sannan bazai taɓa zuwa mata a rana ɗaya ba, a hankali zaita binta harta buɗe, amma na yanzu tsabar mugunta da rawar kai zuwa ɗaya sukema yarinya, babu ruwansu da yanda zasu fatattaka ta balle ita yaya zataji, sun mata rai dai guda ɗayane, yanda za'a yankesu suji zafi haka itama macen kejin zafi koda a sannu aka bita tunda ba taɓa yi taiba. Koda yake wani lokacin harda laifin iyaye, maganin matannan da suke ɗurama yara ba ƙaramin jawo musu wahala sukeba, yarinyar ke dake a ɓame, batasan dawan garinba zaki bama maganin mata, tayaya kike tunanin namiji zai ɗaga mata ƙafa ya bita a hankali. Basu bama su Ummukulsoom komaiba sai tsumi, amma jiba yanda suka jigata, ita kanta Bily sai da akai mata ɗinki, toga Ummukulsoom ɗin nanma da alama sai anzo ga hakan, balle Amaan daba yaroba ma tsohon tuzuru........

       Da ƙyar Ummi ta yakice tunaninta ta maida hankalinta ga Ummukulsoom ranta duk a jagule, “Kin shiga ruwan zafine?” ta tambayeta.

     Kan Ummu a ƙasa ta girgiza alamar A'a.

    “Mi yasa?” cewar Ummi again.

     “Ummi da zafi, jinake kamar zan mutu wlhy”.

      Tasan ragwantakar Ummukulsoom batun yanzuba, har tunanin dama randa za'ace haihuwa tazo musu takeyi, cikin ɗan faɗa tace, “Wannan gangancine ai, dan ƙaniyarki ba dole kiji zafin da yafi na farkoba, dakinyi haƙuri kinɗan gasa wajen aida komai ya kuma zuwa da sauƙi, yanzu ko yariga ya tsuma ai”.

    Ita dai Ummu kanta a ƙasa tana hawaye, cire gyale Ummi tayi taje ta kulle ɗakin ta shiga bathroom, da kanta ta haɗa ruwa mai ɗan zafi tazo ta kama Ummu suka tafi, iyakar wahala da azaba Ummu ta shashi kafin su isa bayin, ta haɗa zufa sharkaf tamkar ba sanyi ake ba.

        Ummukulsoom na kuka da magiya Ummi bata saurareta ba saida ta dannata aruwan, tsawon minti goma sannan ta fiddota suka dawo ɗaki.

      “Ki nutsu na duba, matsayin likita nake a gabanki yanzu ba uwa ba, inba hakaba kuma zan ɓata miki raine”.

      Kai Ummu ta ɗagama Ummi, sai daifa har ga ALLAH tana matuƙar jin kunya, amma yaya zatayi, yanda Ummi taga wajen sosai tausayin Ummukhoolsum ya kamata. Dolene suje asibiti kam.

  

   ★★★★★

    Babu wanda ya sani a gidan aka fita da Ummukulsoom asibiti, shima Amaan ɗin yana wajen Dad suna magana,  Momcy ce kawai ta bisu tanata faɗa, sai Ummi ke bata haƙuri.

    Babu bata lokaci suna isa Ummi tai mata allurar kashe raɗaɗi data barci, ahaka tai mata ɗinkin. Dukda bata cikin hayyacinta saida taji zafin kaɗan-ƙaɗan cikin barci.

     Momcy kamar zata ari baki dan faɗa, ca take wannan rashin tausayine kawai, Ummi dai tanata lallashinta, tunda dai ta riga ta afku ai haƙuri shine magani kawai.

         Amaan tare sukazo asibitin shi da Dad, amma ba a sanarma Dad gaskiyar zancenba, ca akai masa kawai zazzaɓine Thypoid ɗin Ummukulsoom ce ta motsa mata, ya tausaya mata tare da jero mata addu'oi kafin ya wuce.

     Dad na fita Momcy ta hau kan Amaan da faɗa kamar zata mangaresa, shidai baice uffanba, tasan kuma bazaice ɗinba, kansa sunkuye a ƙasa yana kallon Ummukulsoom dake barci, shi sam baiyi zaton abin zaikai hakaba sam. 



A gurguje Please😞🥴


         Dole a asibitin Ummukulsoom ta kwana,  baba halima aka kawo ta kwana da ita, da Amaan ya kafe shi zai kwana, sai da Momcy tai masa wuju-wuju ne, Attahir yaja hannunsa yana dariya.

    “Kai wlhy ka haƙura da kwanannan, inba hakaba Momcy zaneka zatai a sibitinnan, ka kira ruwafa da yawa Ajiwa”.

     Idanunsa ya lumshe yana shafar girarsa, sai dai baicema Attahir komaiba, shi tausayin matarsa ma shine ya gallabi ransa, gashi taƙi yarda su haɗa ko ido, ko magana yay mata batason amsawa. Dole yabi Umarnin Momcy Attahir ya saukeshi a gida, ranar dai barcinsa ragaggene, ya kira wayarta kuma saiya ganta a ɗakin bata tafi da itaba a she, dole ya haƙura ya kwanta yanata juye-juye.


       Washe gari koda yaje ma ƙin yarda tayi ta kalli sashen da yake, ta dai gaishesa, ya tambayeta jiki taƙi amsawa, zama yay a kujerar ya kama hannayenta duka cikin nasa, dan baba halima ta fita su kaɗaine a ɗakin.

      “Bama za'a kalleni ba _Noorulain_?”.

    Kanta ta sake sunkuyarwa tana kumbura baki, a ranta faɗi take “anki a kallekan, mutum sai baƙar mugunta da miskilancin tsiya”.....

     Hannunsa yasa ya ɗago haɓarta duk dan su haɗa ido, sai kawai ta lumshe idanun.

     Guntun murmushin da bai niyyaba ya saki yana komawa bakin gadon kusa da ita, har yanzu hannunsa riƙe da haɓarta, bakinsa yakai gab da fuskarta ya ɗan sumbaci laɓanta.

    Da sauri ta ture hannunsa tana janye fusmarta, “Ni fa ka tashi ka fita karma wani yazo ya ganka anan”.

     “Aiba kwartanci nazoba ko?” yay maganar da fisgota ta dawo jikinsa. Haushinsa ya kuma kamata, ta dalla masa harar.

      “Indai kinamin wannan harar ALLAH zakita shan wahala, dan kamar kina cewa Amaan zo ka ƙara yi ne ehe”.

    Babu shiri Ummukulsoom ta waro idanu da mamakinsa.

   Ya ɗaga kafaɗa da taɓe baki kaɗan, “Nifa abin da ke raina na faɗa miki”.

        Shiru tai masa, dan itakam lamarin Amaan yafi ƙarfinta, dama gaskene da mutane ke faɗin mutum mai shiru-shiru sai addu'a, itakam ta yarda da wannan magana.

    Ƙin tashi yay daga jikinta har saida yasata taci abincin da baba halima ta zuba mata, ya bata magani tasha sannan ya tashi saboda shigowar Ummi.

  

     A dai taƙaice ranar da daddare aka sallameta, bayan Amaan yasha gargaɗi wajen Momcy, shi harma dariya ta bashi, kodai giyar wake yasha ai bayace zai jema Ummukulsoom ba dama.

    Gab da magriba suka shiga gidan, dan haka Amaan bai shiga cikiba ya juya tsaya suna gaisawa da Ameer,  maman Ahmad ta rako Ummukulsoom sashenta, Momcy kuma ta wuce nasu sashen itama.

      Maman Ahmad bata zauna ba ta fito dansu tafi, jirgin 8pm zasubi zuwa lagos yau, sallama taima Ummu dasake gargaɗarta akan abinda ya dace sannan ta fita.

      Da to kawai Ummu ta bita, dama basu iske su Amaan a sashen ba, duk sai taji babu daɗi da maman Ahmad ta wuce, tashi tai jiki duk a sanyaye ta shiga bayi, danyin wanka, tana shiga babu jimawa Amaan ya shigo ɗakin, motsin ruwa da yajine ya tabbatar masa da tana wanka, ya zare hannayensa a aljihu yana zama bakin gadon tare da zamewa ya kwanta rigingine, sai da ya jawo ƙaramin filo ya ɗora kansa sannan ya lumshe idanunsa a hankali.

     Kusan mintuna 30 da kwanciyarsa Ummukulsoom ta fito, dan saida tai gashi kamar yanda Ummi tace ta ringayi tsawon sati guda. 

       Ummu bata lura da shiba, sai dai taji ƙamshinsa, amma sai bata kawo a ranta yana ɗakinba.

     motsinta da yajine ya sakashi buɗe idanunsa kaɗan, ganin bata lura da shiba sai abin yaso bashi dariya, da yanzu an fara kumbura masa baki.

     “Mai makon a jirani nazo muyi wankan”. Ya faɗa ƙasa-ƙasa.

      A rikice Ummu ta juyo ta kallesa, jikinta har ƴar rawa yake wajen ƙoƙarin jan hijjab ta saka.

   Baki ya taɓe kaɗan yana miƙewa zaune, idanunsa ƙyam a kanta, itako sai faman kumbura fuska take da ƙunƙuni.

     Miƙewa yay ya taka zuwa inda take, sai ta matsa baya da faɗin, “Ana kiran salla kai kana nan ɗaukar magana”.

       Ta bashi dariya, amma saiya haɗiye kayansa tare da shafa girarsa ya zagayeta ya wuce bayi ba tare da ya tanka ba.

      Yana shigewa ta saki ajiyar zuciya tana lafewa a bango da rumtse ido, ALLAH da akwai yanda zatai jini yazo mata a yau da sai tayi, haka kawai take jin tsoron sake kwana dashi a ɗakin, dan ba ƙaramin wuju-wuju taji ba a shekaran jiya, Amaan jarumine, kuma gwarzo a zahirinsa da baɗini, inhar a haka za'a cigaba da tafiya lallai akwai sauran tsalle a gabanta harma da tsilge-tsilge.

    Harya fito tana wajen tsaye, da alama alwala kawai yayo, jitai kawai an bata sumba a kumatu.

    Tai saurin buɗe ido a kansa, ido yaɗan kanne mata ya wuce abinsa sam fuskar dai babu walwala.

      Yanzunma ajiyar zuciyar ta sauke, tare da kai hannu ta shafi kuncinta da ya sumbata..................✍🏻



Ba kowane ƙyawu yake zama ƙyaƙyƙyawa ba. Hakama ba kowane muni ke kasancewa Mummuna ba. Karda son zuciyarka ya ɗebeka ka kasance mummuna a zuciya ƙyaƙyƙyawa a kan fuska. Daure ka zama ƙyaƙyƙyawa a zuciya koda dukkan duniya zasu kalli fuskarka a matsayin mummuna._*


NO. 51


...........Ummukulsoom na zaune a inda tai sallar isha'i tana duba massege ɗin da Bily ta turo mata Amaan ya shogo.

      Kaɗan ta ɗago idanu ta kallesa ta maida ta sunkuyar, sosai take jin kunyar haɗa ido dashi tunda abin nan ya faru a tsakaninsu, shiko tuni ya harbo jirginta, amma da yake gwanine na basar da abu sai bai taɓa nuna ya fahimta ba.

      Ya zaune a bedside drawer da Ummu ke gab da ita zaune, dan har ƙafarsa na gogar jikinta, waya yake tunda ya shigo, amma inba ka saka kunne a wajenba bazaka taɓa jin abinda yake faɗaba.

    Idonsa na akan Ummu data tsirama waya ido tamkar gaske karatun take, sai dai a baɗini tuni ta bar karatun ta koma kallon ƙafarsa da sauraren wayarsa.

      Kusan mintuna biyar kafin ya yanke wayar yana sauke ajiyar zuciya, “Please ɗan bani ruwa”. Yay maganar idonsa akan wayarsa.

    Duk sai Ummu taji kunya, dan a ganinta baima dace ace saiya roƙa ba, wayarta ta ajiye ta miƙe, ya bita da kallo ƙasa-ƙasa, dan ash color hijjab ɗin ya mata ƙyau sosai, sai da yaga ta fice ya ɗauke idonsa yana miƙewa, kayan jikinsa ya hau zarewa dan wanka yakeson yi.

       Ummukulsoom data shigo da sallama kallo ɗaya tai masa ta janye idanunta zuciyarta na wata iriyar harbawa da ƙarfi, itakam dai batason wannan rashin kunyar tasa, banda rashin ta ido minene abin cire kaya ya zauna mata da ga shi sai boxer da best a ɗaki.

      Yanzunma waya yake dannawa, ta ajiye ƙaramin tiren data ɗoro ruwan gabansa ba tare da ta yarda ta kallesa ba,  gabansa ta durƙusa ta zuba masa a cup tare da miƙa masa idonta a ƙasa.   

          Tattausan hannunsa ya ɗora akan nata dake riƙe da kofin ruwan, jin yanda ya riƙe ɗinne ya tilasta ta ɗago fararen idanunta taɗan kallesa. Caraf idanunta suka shige cikin nasa daya kafeta dasu, saurin janyewa tayi tana shagwaɓe masa fuska.

      “Dama haka ake ba miji ruwa?” ya faɗa a hankali.

      Shiru bata iya amsawa ba, sannan ta kasa sake kallonsa, shima bai sake cewa komaiba ya janye kofin gudun kar sanyin ruwan ya cutar da ita, har zata miƙe tana hamdala a zuciyarta taji caraf ya riƙo hannunta. Kasa juyowa tayi, shikuma baice komaiba har sai da ya gama shanye ruwan data zuba masa. Kofin ya ajiye gefe yana ɗan girgiza hannun nata, dole ta juyo ta kallesa, kasancewar shima ita yake kallo suka sake haɗa ido.

     Lallausan murmushin daya narkar da zuciyarta ya sakar mata, mai tsadar da kafin yayisama aikine, ita kanta yaune ta fara ganinsa a fuskarsa, dan kuwa fararen haƙoransa saida suka bayyana. Kasa janye idanunta tayi daga garesa, sai ta tsinci kanta da kafesa da ido ba tare data shiryama hakanba. Kusan minti biyu suna a haka, ring ɗin wayar Ummu ne ya dawo dasu hankalinsu, kowanne ya sauke ɓoyayyar ajiyar juciya, Ummu ta zare hannunta a nasa ta ɗauki wayar dan duba wanene.

      Shima miƙewa yay ya nufi toilet zuciyarsa na wani irin harbawa, tabbas yau ya hango soyayyarsa a idanun Ummu sosai, sai dai baisan miyasa take ɓoye masa ba, kokuwa har yanzu bata huce bane oho?. da waɗannan tunane-tunanen ya fara wankan.

 

      Ummu kam ficewa tai falo tana amsa wayar Bily dake mata dariyar shaƙiyanci, dama tun a asibiti take mata idan ta kira jin yaya jikinta? Sai dai acan bata kulata, yau dai ta biye mata sunata kwasar rashin arziƙinsu da suka saba, daga ƙarshe suka shirya tare da faɗawa hirar yaushe gamo.

        Koda Amaan ya fito bai iske Ummukulsoom a ɗakinba, shirinsa yayi mai sauƙi cikin wandonsa dako gwiwa bai kaiba, sai riga mara hannu, yasa turarensa mai ratsa zuciyar mai shaƙa. lap-top ya ɗauka da wasu takardu ya fito falon shima, dan yasan dai nan Ummukulsoom ta gudo.

         Har yanzu Ummu waya take, tana kwance cikin doguwar kujera.

       Kujerar dake gefen inda kanta yake ya zauna, ya ɗora kayan hannunsa a table ɗin gabansu yana mai miƙa hannu ya zare wayar daga kunnenta.

     Da hanzari ta miƙe zaune zatai masifa sai taji ƙamshin turarensa, ALLAH ta zata ko cikin ƙannan sa ne, dan ba ƙamshin turarensa data saniba taji...

     Wayar ya saka a kunne bayan yaga bily ce, “K ina kika bar mijinki? Kika zo nan zaki ishemu”.

      Jikin Bily har ɓari yake daga can wajen fadin, “Afuwa yaya Amaan, sai da safe”. 

    Shi baima jira amsarta ba, dan tuni ya ajiye wayar yana zubama Ummu dake kumbura baki mayun idanunsa, gira ɗaya ya ɗage yana lumshe ido da buɗesu kan table ɗin daya ajiye lap-top ɗinsa.

          “Karki ce ban sanar mikiba, daga yau idan ina gida dukkan hankalinki nake bukata gareni, bana bukatar raba dai-dai ɗin lokacina da kowa”.

     Cike da mamakin ƙarfin hali irin nasa ta ɗago ido ta kallesa, lip ɗinsa na ƙasa yaɗan ciza alamar tabbatar da gargaɗinsa.

       Ummukulsoom ta janye idanunta kawai ta maida kan yatsun hannunta da take lanƙwasawa suna ƙara.

         Shiru babu wanda ya sake magana, shi yanata ƙokarin dai-daita system nashi, itako tana juya maganar dake son fitowa bakinta.. Ganin bata da mafita tace, “Abinci fa?”.

     Kallonta yayi ya janye idonsa, sai kuma ya maida lap-top ɗinsa sama table ya ajiye, “Zonan” yay maganar yana miƙa mata hannu.

       Kamar bazata motsa ba, sai kuma ta muskuta kaɗan alamar son tashin amma ta rasa abinda ya hanata yunƙurawa.

      Hannunsa ya miƙa sosai ya kamo natan cikin nasa, yay mata alamar ta miƙe da ɗayan hannunsa, koda ta miƙe ɗin jawota yay ta zauna a cinyarsa, yasa hannu ya zare hijjabin jikinta, duk yanda taso hanashi sai kuma ta kasa, ba komai bane ke taka mata birki ga aikata wani abun sai nasihar iyayenta da tsoron saɓama ALLAH.

       Yanda ya zubama ƙirjinta idone abin ya matukar bata kunya, sai dai shi ko a kwalar rigarsa, dan babu alamar wani jin kunya tare da shi.

       “Mrs Amaan wai har yanzu dai?”.

      “Har yanzu dai me?” ta faɗa tana kallonsa ido cikin ido ba tare da tasan ta yaya ta samu jarumtar hakanba.

     Shima haka ya kafeta da nasa, “Daga yanzu haka nakeson ki ringa min magana kai tsaye”.

       “Murmushi taɗanyi tana janye idanunta cikin nashi”.

    Shiru sukai su duka, shi dai ya fara ƙosawa da yawan maganar ne, a hakanma yasan yayi ƙololuwar ƙoƙari, dan so yake Ummu ta saki jiki dashi sosai. Daurewa yay  ya kuma cewa, “Yanzu baƙya tsoron ki bani abinci naci ki kasa ɗaukata Beauty?”.

     Sarai ta fahimci inda ya dosa, amma tsabar son ta manna masa shorme sai itama ta yatsina fuska da cewa “kamar ya?”.......

        Kafin ta rufe baki ya mannata da jikinsa sosai ya haɗe fuskarsu waje ɗaya, duk yanda taso ƙwatar kanta ta kasa, sai da ya sumbaceta iya yanda yake so sannan ya saketa da faɗin, “Kamar haka”.

     Cusa kanta tai cikin ƙirjinsa, lamarin Amaan sai addu'a, dolene ta ajiye komai ta rungumi mijinta dan yana bata farin ciki sosai, miskilancinsa ne kawai matsalarta gaskiya, wannan kam tasan sai dai haƙuri, dan bata isa canja abinda ALLAH ya gina ba.

         Hannunsa na saman kanta yana shafa gashinta dake fidda ƙamshi mai daɗi, harga ALLAH yana ƙaunar wannan halitta, harma baisan yanda zai musalta ba a fahimta, babban fatansa ALLAH yasa itama tai masa koda rabin son da shi yake matane.

    Da kanta ta tashi daga jikinsa, ba tare da ta yarda sun haɗa idoba ta nufi dani inda Buhayyah tazo ta ɗaura abinci.

         Da kallo kawai yaɗan bita yana janye idonsa, ya ɗauki biro da takarda yay ɗan rubutu.

     Ummu da taga abincin bamai nauyi bane saita zuba masa dai-dai misali ta dawo falon, lokacin harya ɗauki system ɗinsa ya ɗaura akan ƙafa ya fara aikinsa, zama tai a kujerar kusa dashi da take zaune da, kasancewar hannun kujerar ya haɗu waje daya sai ta ɗaura abincin saman hannun tana faɗin “Ga abincin”.

         Ba tare da ya kalleta ba ya nuna mata takardar daya ajiye saman table. Ɗauka Ummu tai tana dubawa.

     *_Gobe idan ALLAH ya kaimu zamu koma lagos, ana mini neman gaggawa a Office_*.

     Da mamaki a fuskarta ta kallesa, kamar zata share sai kuma ta tanka, “Gobe da wuri haka? Kofa gidan yaya Zaid da Bily banjeba, ga Inna harira ban mata barka da tashin baƙiba. Indai dan tanice kaje kawai ni daga baya saina taho k.......”

    Kallon daya zuba mata ne ya hanata ƙarasawa, ta haɗiye sauran maganar a hankali. Shima sai ya fasa maganar dake yawo a maƙoshinsa kawai yana ɗauke kansa. 

     Bata sake magana ba, saima wayarta data ɗauka ta shiga danne-danne.

    Shima Uffan bai sake tofawa ba ya cigaba da aikinsa, kusan mintuna Uku Ummu taga idan ta biye masa sai bakinta yay wari, duk da itama bamai yawan magana bace amma idan tana gaban Amaan zata iya zama Aku.

      “Wai nikam abincinfa kawu?”.

    Ta kare maganar cike da tsokana, dan goge laifinta.

     Kallonta yayi jin wai shinema Kawu?, hannu yakai saman kunnenta ya ja da murɗawa.

    Babu shiri Ummukulsoom ta riƙe hannunsa tana fadin, “Wayyo ALLAH yaya Attahir zai kashe muku ni”.

          Bai saki kunnenba, sai dai fuskarsa ta rage rashin walwala alamar maganarta ta bashi nishaɗi dai....

      “Dan ALLAH kayi hakuri, wlhy akwai zafi fa”.

        “Sake maimaitawa” yay maganar ciki-ciki da sake murɗe kunnen.

     “A'a na tuba aminin yaya Attahir ”.

    Yanzu kam dai kasa daurewa yay saida ya murmusa, Ummu ta rigada taga gadon barcinsa ai dama tuni, daga ita sai Attahir ne suke masa yanda sukaso ya ɗaga musu kafa, dan sunriga da sun zama wani sashe na rayuwarsa mai ƙarfin gaske bayan ahalinsa.

     “Hukuncin ki shine bani abincin nan a baki harna koshi”.

     Azabar da Ummukulsoom keji ce ta sata saurin amsa masa da eh zatayi, babban burinta dai ya saki kunnen.

        Saki kuwa yayi, ita kuma tahau kumbura baki da faɗin zata ramane, baice da ita uffanba ya kawo hannu zai sake damƙar kunnan ta tare tare da ɗaukar cokali ta ɗiba abincin, baki ya buɗe ta zuba masa yana kashe mata ido da ƙyafta idanu.

     Haka dole taita bashi abincin yanaci yana aikinsa, saida yaji ya ishesa ne ya ɗaga mata hannu alamar ya isa.

      Harta fara murna zata gudu taga ya tsareta da idanu yana mata alamar wai itama taci, kai ta girgiza masa, ya harare ta yana haɗe fuska tamau.

     Dole dai taci itama dai-dai misali. Sun jima a falon yana aiki itako tana danna waya har aka maido wuta, lokaci-lokaci Amaan kan amsa waya koshi ya kira da kansa ma. Sai da Ummukulsoom taji ta fara hamma ta miƙe ta barsa, dan ita tariga da ta saba barcin wuri.

     Bai hanata ba, ta shige abinta tai shirin barci tai kwanciyarta da addu'ar ALLAH yasa kar Amaan yace zaizo mata. Babu jimawa kuwa barci ya kwasheta saboda tana bukatarsa sosai.


       Wajen 12 Amaan ya miƙe, yasan dai Ummukulsoom ta jima da yin barci kam, ilai kuwa yana shiga ya isketa tayi barcinta. Bai tasheta ba shima yay shirin barcin ya haye gado, hadari nata cida alamar ko yaushe ruwa zai iya sakkowa.

      Jikinsa ya sanya Ummukulsoom yana gyara musu bargo, ko alama bai yunƙurin mata komaiba, yay Addu'a shima ya kwanta. Cikin barci yaji Ummu tana kuma lafewa a jikinsa alamar ɗumin jikin nasa ya mata daɗi sosai, dan har an fara ruwa.


*_Washe gari_*


         Su Ummukulsoom suka tashi da shirin komawa legas, duk yanda taso zuwa gidan Bily da Aziza Amaan ya kafa ya tsare, danma karta damesa sai ya miskile fuska, dolenta ta hakura tai musu sallama a waya ranta na ƙuna.

      Sabuwar nasiha Dad daya dawo daren jiya yay musu, tareda jera musu kalmomin addu'ar zaman lafiya da gargaɗin Amaan akan Ummukulsoom. Itama Momcy ta dora nata bayan ta nemi gafarar Ummu, hakama yaran gidan su Aneesa da zasu wuce gidajensu suma duk sai da sukazo suka roki gafar Ummukulsoom akan abinda sukai mata a baya da, Jud kam dama tunda ta tare gidan yake mata wani ladabi na musammam, dan a rayuwarsa yana matukar ganin girman Amaan a gidan, sam babu ruwansa ko taka haƙƙin wani da akan sani, sai dai idan da kuskure.

       

     ƙarfe huɗu suka baro gidan, Momcy harda ƴan hawayenta, dan taso Amaan yabar Ummukulsoom taɗanyi wata ɗaya anan su sake sabawa, taima Ummu gatan data gaza mata a baya, sai dai sam yaƙi yarda da hakan, ta juyashi dambu da takiya yace ai Ummukulsoom bata kammala abinda ya shafi karatun ta ba, ko yaushe za'a iya nemanta a makaranta. Babu yanda Momcy ta iya ta barsa da matarsa tare da binsu da addu'ar fatan alkairi.

     Sai da suka biya gidan Abba da gidan Hajiya yaya, sai dai duk basu jimaba suka fito. Ameer ne ya kaisu airport, bai taho ba kuma sai da yaga tashinsu.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


          Tsawon lokaci babu wanda ya sake jin ɗuriyar basiru, iyayensa tun suna kauda kai har abin ya fara damunsu, dan kuwa tun zuwan da yay so ɗaya bayan dawowarsu bai sake waiwayensu ba.

     Inna tun tana jin zata iya jurewa harta gaza, dama lokacin da suka tafi faransa haka taita ciwo a tsaye na damuwar rashin basirunta.

       Baba da kansa ya shiryo shida wani yaron innar basiru daya zauna a wajenta sannan yana karatu a zaria sukazo katsina kozasuji labarin basiru.

     Kai tsaye gidan gwamnati sukayo, sai dai fa wane mutum inji mutuwa, sam sun kasa samun damar koda ganin mai gadin gidan ballema mutanen ciki, tun suna zarya da marmari har suka fara jigata......


        Meenal kam duk da son da takema Basiru a baya zuwa yanzu sai taji ta gama tsanarsa, dan kuwa tanada tsananin kishi, sai da bayan an kama basiru ne ma taga ɓarnar kuɗi da yay mata ba tare data saniba, wasu maƙudan kudinta data ajiye agidan zatai amfani dasu akan wani muhimmin abu basiru yay sama da fadi dasu ashe.

     Hakan saiya sake bata takaici, ga ƴan iskan ƴanmatansa koda yaushe cikin kiransa da turo masa saƙo suke na rashin mutunci dake neman saka zuciyarta bindigewa, har sawa tai ai mata tracking numbers ɗinsu sai dai babu wani abinda aka samu daga garesu, da alama dai da shirinsu suma.

     Wannan abu sai ya nemi zarar da Meenal, ga su Suhailat data ɗauka aminanta yanzu suna kuma tunzurata a gefe da yake ta sanar musu komai, taso ƙona wayar basiru mom nata ta karɓe akan cewar wayarsa hujjace babba a garesu koda anan gaba wani abu ya taso, dan haka ta ɓoyeta ta hana Meenal ƙonawa.

     Maganar auren basiru dake a kanta kuwa babu wanda yabi ta kansa, ita kuma bata fasa dukkan abinda tai niyyaba balle tuna akwai wani aure a kanta.

      A haka aka shari tsawon lokaci Basiru na jail yana cin gabza, tsabar zalinci irinna manyan mu saima aka ɗaukesa aka saka cikin gagga-gaggan ɓarayi waɗanda aka yankema hukuncin kisa, basiru duk ya koɗe ya jeme cikin lokaci ƙankani, babu abinda ke tada hankalinsa da cin zuciyarsa a halin yanzu irin iyayensa da basusan halin da yake ciki ba, duk wanda yasan basiru ɗan gayu ɗan ƙwalisa, mai ɗaukar mata ya yada tamkar laidan ruwa, bayan ka shanye ruwan ciki ya gama maka amfani ka yarda ledan, to yanzukam ka gansa sam bazaka ganesa ba, wahala ya ke sha a cikin waɗanda aka sakashi, har dukansa sukeyi sosai. Kuka kullum babu fashi sai basiru yayisa, tun yanayi da hawaye harya koma da zuciya da ƙwanji.



   To dama masu iya magana kance *ɗan hakkin daka raina shike tsone idonka*. _wanda ya taka rawar wani kuma watan wata rana shi zai rasa filin taka tasa_. *Tsuntsun da yaja ruwa shine ruwa ke doka*. _Duk wanda yace tukunyar wani bazata tafasa ba tashi ko ɗumi ma baza tayiba_. *Duk abinda ya saka dariya wataran shine zai saka kuka*. _Yau dai ga matan da Basiru ya raina sun zame masa *WUTSIYAR RAƘUMI...*_😽😾



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


             Su Ummukulsoom sun isa lagos lafiya, inda Attahir da kansa yazo ya tarbesu, a fakaice Attahir keta tsokanar Amaan da idanu dan kar Ummukulsoom ta gani.

    Tun yana basar dashi harya kai masa duka. Gocewa Attahir yay yana dariya da faɗin “Kai malam nifa yayanka ne yanzu wlhy”.

     Amaan ya hararesa yana yin gaba ya barshi shi da Ummukulsoom dake musu dariya kasa-ƙasa, wannan abota  ta dade tana birgeta, dan cike take da ƙaunar juna da tsantsar amana.

      Cikin ɗaga murya kaɗan Attahir yace, “Badai kayi gaba ba, to sai kazo bikon ƙanwata gidan babban yaya”.

     Cak Amaan dake shirin shigewa falonsa ya tsaya.

      Attahir ya kalli Ummukulsoom yana faɗin, “ƙanwata shiga mota muje”.

     Cike da son ganin yanda za'a kwashe Ummukulsoom tai yunkurin komawa motar da attahir ya ɗakkosu...

    Ji kawai tai an ɗauketa cak, saita rikice sabo tsabar al'ajabinsa da mamaki, sam batai zaton zaiyi hakan gaban Attahir ba.

       Dariya Attahir ya shige mota yana yi, Ajiwa nashi kenan, mai abubuwan birgewa dana mamaki, harma da takaici.


      Duk da Amaan yanajin Ummun bata wasan yara bace wajen ɗan nauyi hakan baisa ya direta ba sai da ya shiga falonsa da komai ya canja. kai tsaye bedroom nashi ya nufa da ita, ya direta akan gadon shima yana kwanciya da sauke numfashi, sarai Ummukulsoom ta fahimci ya gaji ne, amma tsabar neman tsokala sai catai “Ya kamata na ƙara ƙiba kodan ka bar gigin min irin wannan ɗaukar amaryar a gaban yayana gaskiya”.

     Juyowa yay ya kalleta, sai ta basar tana maida kanta gefe dariya na tsunkulinta.

     Shima ɗauke idonsa yay daga kanta ya tashi zaune, tasan shirunsa na nufin ba yanzu zai maida murtani ba, sai ma ta gama mantawa da anyi sannan😹.........✍🏻



NO. 52



...........AMAAN da kansa ya nunama Ummukulsoom ɗakinta na da dai, dan anan aka zuba mata kayanta masu ƙyau fiye dana farko, amma a yanda ya nuna dai yafi bukatar su rayu a ɗaki ɗaya, bata musa masa ba, ta kwaso muhimman abubuwanta ta maido ɗakinsa.

     A ranar dai ta dagama Desmond ƙafa yay musu girki, sai dai a ƙasan ranta wannan karon da shirin canja komai tazo, dan kuwa matsayin *MATAR SO* tazo, ba *MACEN SHIGE* ba, shi kansa Amaan ɗin batace dashi komaiba akan hakan har sukai kwanciya barci, duk da atsorece take dashi matuƙa gaya.

     Sai kuma abinda tai tunanin zai farun bai faruba, dan kuwa wasanni kawai yaɗan mata suka shilla duniyar barci, shikam dai dama bada niyyar wani abu ya tsaya iya nanba, ya ɗau alƙawarin barinta ta warkene sosai, danshi dai a saninsa soyayya ta gaskiya itace tarayya akan samu ko rashi, tausayi da ƙyautatama juna, amana da gaskiya, adalci da tsantsar farin ciki koda bata hanyar kwanciya ba.

        Da asuba yana dawowa salla yay shirin motsa jiki ya fita kamar yanda ya saba, Ummu tana ganin ya fice ta nufi kicin inda takejin motsin desmond.

    Risinawa yay yana gaisheta bakinsa a washe, ta amsa fuskarta babu yabo babu fallasa, tareda ce masa yaje ya huta zatai komai.

    Cike da tsoro yace, “Please ma'am kar boss yay faɗan na barki da aiki".

     Karan farko da tai masa gutun murmushi, “No desmond karka damu bazaiyi faɗaba, jeka kawai”.

     Shidai a ɗar-ɗar ya fice badan hankalinsa ya kwanta ba, dan a halin Amaan sai dai ya bama wani labari badai shi a basa ba.

      Zagewa Ummukulsoom tayi ta shirya breakfast mai rai da lafiya, tareda tada kunnen duk wanda ya cisa, _a ganinta lokaci yayi da zatabi hudubar ƴan team dinta na wutsiyar rakumi, dan kullum cikin koya mata dabarun riƙe Amaan suke kodan ƴan team Amaan susan yanzu fa ba UMMUKULSOOM TA ƊILAU bace ba_😉.

      Dan danan gidan ya gauraye da ƙamshi, desmond kansa da yaje ya karanci wannan fanni duk yawunsa yabi ya tsinke da wannan ƙamshi.

      Lokacin da Amaan ya shigo gidan tunda ya shigo falon ƙamshin ya daki hancinsa, mamaki ya kamashi, yau kuma desmond da sabon salo ya zone? Da wannan tunanin ya karasa bedroom ɗinsa, tsaf ya gansa an gyara an saka turaren ƙamshi mai dadi, yaɗan murmusa kawai yana zame kayan jikinsa, shi duk zatonsa ko Ummu tana ɗakinta ne, sam bai kawo itace a kicin dinba.

     Koda ya shiga bayi sai ya iske ruwan wankansa a haɗe, jiyay wani girma da kimar Ummukulsoom sun daɗu a ransa, fara wankansa babu jimawa Ummu ta kammala da kicin, desmond ta barma ya gyara, ita kuma ta fiddo komai zuwa dani, falon baya bukatar wani gyara, amma duk da haka sai da taɗan karkaɗe kura abinka da lokacin damina, ta saka turaren wuta sannan ta nufi ɗankinta. Duk sai tajita a gajiye, ruwa mai ɗan ɗumi ta haɗa itama ta shiga wanka.

     Tana shiga Amaan na shigowa ɗakin ya biyo sawunta. Yasha mamakin jin motsinta tana wanka, shi duk zatonsa barci take ko kuma tayi wankan tuni bata dai ra'ayin fitowarne.

            Sanye yake cikin kakin soji ruwan ganye, sunyi masifar masa ƙyau, gaba ɗaya siffofinsa na jarumta da cikar haiba sun sake bayyana a garesa, ga wani kwarjinin angwanci da hasken musulunci na haska saman kamilalliyar fuskarsa.

        Wayarta dake saman drowar gefen gadon ya ɗauka yana dubawa, sam babu wani password a jiki, sai ƙyaƙykyawan hotonta itada bily sunyi ƙyau tamkar tagwaye, hatta da murmushinsu iri ɗaya ne, kowacce fararen haƙoranta sun fito masha ALLAH, haka kawai yaji sha'awar shiga ma'ajiyar hotunanta, da hotonsu na ranar Mothers event ya fara cin karo, sunyi masifar ƙyau, dan suna tsaye a filin rawane time ɗin dasu zaid ke raira musu wakar shakiyanci, duk da shi baiyi murmushi ba fuskarsa a sake take, itako taɗan sunkuy da kanta tana murmushi, yayinda shi ya kafeta da idanu..

        Ummukulsoom data fito daga wanka tai yunkurin komawa da sauri saboda ganinsa.

     “Garama ki dawo” ya faɗa cikin matukar sanyin murya.

    Kallonsa tayi, sai taga sam ba ita yake kalloba, har yanzu idonsa nakan waya da batai zaton tata baceba.

     Tamkar zata nutse dan kunya ta dawo, tasan dai tunda ya ambata ta dawo ɗin inhar ta koma ɗin akwai matsala, dan sai ya mata abinda saita gwammaci bin umarninsa tayi. A takure taja stool din mirror ɗinta ta zauna.

      Idanunsa masu haske da cikar gashi ya ɗago yana zubasu a bayanta daketa wani raɓar ruwan daya hade da gogaggiyar fatarta mai ɗauke da gashi kwantattu masha ALLAH. take tsigar jikin Amaan ta fara tashi, babu shiri ya janye idonsa ya maida kan wayar yana fisgo numfashi da kyar, bai sake gigin kallonta ba harta kammala abinda take a wajen ta mike zuwa Wadrobe.

         Kayanta ta ɗauka zata je bayi ta saka ya mike ya cafkota.

    Cikin marairaice face take rokonsa da ido alamar ya saketa. Yi yay tamkar baima fahimci komaiba, yasa hannunsa ya karɓe kayan tareda kwance towel din jikinta ya faɗi ƙasa. Babu shiri Ummukulsoom ta faɗa jikinsa tana rumtse ido, baice komaiba ya fara yunƙurin saka mata kayan a haka, ita dai bata hanashi ba, sannan bata buɗe idonta ba, duk yanda yaso haka yay da ita har aka gama, ya kama hannunta zuwa gaban mirror yana ru gumota ta baya da ɗora habarsa saman kafaɗarta yana magana cikin kunnenta a hankali. “Beauty na tafi kowacce mace ƙyau da iya ɗaukar gayu, wanda duk bai auri lukutar mace ba to lallai ya dage ya ƙosar da tashi a gida ta zama ƴar lukuta😝, dan lokacin ne zai fahimci wani ɓoyayyen sirriiii ko yaya ta wajenaaaa”. Yanda yaƙare maganar da wani salo sai ya nema hautsina tunanin Ummu, dama tunda ya fara magana tsigar jikinta ke tashi, sai ma ta rasa amsar daya dace ta bashi akan wannan magana, tai ƙasa da muryarta cike da nata salon tace, “Nidai babu ruwana, muje kaci abinci”.

         Murmushi ya ɗanyi yana gyara tsayuwa tare da ciro wayarsa a aljihu yay musu hoto a haka, ya saka hannu ya juyota suna kallon juna, nanma hoton ya kuma haskasu sannan ya maida wayar cikin aljihu yana kalonta “Faɗi gaskiya Noorulain, kodai kina tsoron siraran mata da mazansu suyi saƙwara dake?”.

    Babu shiri Ummukulsoom ta tuntsure da yar siririyar dariya tana fadawa ƙirjinsa, shima murmushi yayi har hakoransa na bayyana ya dora dukan hannayensa a bayanta ya zagayeta yana mai jin tarin kaunarta na kuma ratsashi.

      Daga karshe dai sai itace ta janye jikinta tare da kama hannunsa suka fita falo. Shiko babu musu yake binta. A dani ta diresa, ta ja masa kujera tana masa nuni da ya zauna, bai musa ba ya zauna tare da zuba mata ido, komai nata a nutse babu hayaniya ko rawar kai irinta wayayyun mata😝, duk abinda ya dace sai da ta haɗa masa sannan ta dago tana kallonsa cikin salon ɗaukar hankali da tasirantar da soyayyar da ba'a mantawa tace, “Yau bawan ALLAH zaici girkin matarsa”.

     Sosai Ummukulsoom ta narkar da Amaan, harma ya nema rasa a wace nahiya yake, idanunta suna cikin abu masu daraja dake matuƙar tasiri wajen narkar dashi a zahiri da baɗini, sai dai ita sam ya gama lura bata saniba, shiyyasa take masa salo iri-iri dasu, sassanyar ajiyar zuciya ya saki yana lumshe ido da budewa a kanta, ya ɗan muskuta yana shafar girarsa da ɗan yatsa..

     “Kulsoommmm, yanda kike daban haka komanki yake daban”. Iya abinda ya iya faɗa kenan yay mata nuni da ido akan ta bashi da kanta.

      Karan farko da tajita a sama matsayin kowacce matar aure da miji ke martabata da tsaftatacciyar soyayya bisa bigiren addinin islama ta gaskiya, umarninsa tabi ta fara ciyar dashi.

    Laumar farko Amaan ya kasa jurewa, ya lumshe manyan idanunsa tsawon wasu sakwanni har saida ya haɗiye sannan ya buɗe, hannun Ummu kawai ya damƙo ya bude tsakkiyar tafin ya sakar mata wata sumbata a ciki ta musamman, wadda sam babu wata ballagazar mace dake samun irinta, sai wadda ta rike kima da darajarta har gidan miji ba tare da ta rabama gayun titi ba ko mata shaiɗanu ƴan uwanta.

      Ummu ta ƙankame jikinta saboda harga ALLAH taji wannan saƙon har cikin kwakwalwar kanta babu algus.

      Sambatu dai ta shashi na santi iri-iri, duk da bada baki ya faɗaba a aikace yake nunawa, dan aɗan zaman nan da sukai ta gama lura dashi yafi bukatar yin komai a aikace fiye da yi da baki, sai da yay nak har yana ɗan nishi kafin itama ya bata da kansa, yanayi yana cakar da ita da salonsa, da ƙyar kowannen su yasha a hannun ɗan uwansa, badan jiransa ake a office ba da babu inda zaije saiya sha tagomashin amarci.

      Ummukulsoom tai masa rakkiya har harabar gidan, sai dai suna gama fitowa yaga su Osin ya dakatar da ita tare da kareta yay mata nuni da ta koma ciki, batai musuba taja baya tana fadin, *_“ALLAH ya tsare zuciyar da bata mance ambaton sa, ka bama gangar jikin da bata gajiyawa da bautarka dukkan kariya, ka bama ruhin dake ƙwaɗayin kusantarka da rahamar ƙarfin imanin kauda idonsa daga haramun da dukkan gangar jikinsa, kayi ƙyau irin wanda babu wani namiji da ya isa kamoka a zuciyar Ummukulsoom, ALLAH ka dawo min da mijina gida lafiya da tarin aminci”._*

     Gaba ɗaya Amaan ya kasa motsawa daga tsayuwar da yayi cak, banda kaikawo babu abinda zuciyarsa takeyi tamkar zata faɗo ƙasa, da kyar ya iya waigowa gareta, sai dai kuma ɓat, ta bar wajen ta shige, sai ƙasaitaccen ƙamshinta data bar ma hancinsa yana shaƙa a hankali yana lumshe ido, hancinsa na kaima ƙwakwalwarsa zuwa kowace magudana da jijiyoyinsa saƙo.

      Ya kai tsawon minti uku tsaye kafin ya cira ƙafarsa da ƙyar ya nufi motocin saboda ring da wayarsa keyi, yasan dai ogansu ne.

         Sai kuma zuciyarsa ta kasa zama waje ɗaya akan basirinta itada da desmond a gidan, ba wai dan yana zarginsu bane, sam wannan baizo kansa ba ma, kishine kawai irin na ma'abota imani da riƙo da sunnar MANZON tsira, waya ya zaro a aljihu yay kiran desmond, bugu biyu ya ɗaga.

    Bansan miya ce da shiba, naga dai desmond ya fito da wurwuri yazo inda motocin suke, Amaan ya sauke glass din sashensa yana kallon desmond cikin lumshe idanu, “Shiga mota mu saukeka duk inda kake buƙatar zuwa, idan na dawo kaima ka dawo zamuyi magana”.

      “Ok sir” desmond ya faɗa cike da girmamawa, lokacin har Amaan ya maida glass din sama.

    Ummukulsoom dake kallonsu ta Window falo tai murmushi, kenan shima zuciyarsa ta fara ƙyara masa zaman desmond a gidan a yanzu baida amfani kenan.

    Bedroom ɗinsa ta koma tai kwanciyarta tare da buɗe data danta gaisa da ƴan uwa da abokan arziki, musamman ƴan makarantarsu da sukai mata halaccin zuwa bikinsu, wasuma tun daga nan lagos ɗin suka tafi, wasu daga kano, bauci, adamawa, sokoto, aiko sun cancanci ta kara musu ALLAH ya huta gajiya ashe.


★★★★

       Kalaman Ummukulsoom sun zauna daram a zuciyar Amaan, koda ya isa office wajen ogansu  yaje, amma sam sai yazam baya fahimtar jawaban ogan, harya dawo Office itace ke masa kaikawo, ya kwanta cikin kujerar data kasance mazauninsa ya lumshe idanunsa yana juyawa a hankaki, duk yanda zai faɗama duniya matsayin Ummukulsoom a zuciyarsa bai zama lallai a fahimcesa ba, shiyyasa yabar wannan sirrin a zuciyarsa da gangar jikinsa kawai, dan sune kaɗai suka cancanci ajiye wannan sirrin. Kusan minti talatin yana a haka yakasa tsinana komai dukda tarin ayyukan saka hannu a takardu dake gabansa, ya sauke nannauyar ajiyar zuciya tareda buɗe lumsassun idanunsa ya ɗauki wayarsa ya fara tafa saƙo.


    Ummukulsoom ta shagala da chart a group ɗin da suka haɗa su hɗu, ita, maman Ahmad, Bily, Aziza, sai murmushi take saboda daɗin charting ɗin, dan gaba ɗayansu suna online shiyyasa firar ke tafiya dai-dai cikin birgewa.

   Saƙon daya shigo yanzu yaɗan ɗauki hankalinta, danta lura Number Amaan ce, fita tai a group ɗin koma free inda zata iya ganin inbox na kowa.

   Tabbas shine, dan haka ta buɗe saƙon, amma sai da ta kashe data yanda bazai fahimci da wuri ta buɗe ba.

          *_“Faffaɗar duniya mai cike da abubuwan ƙawa da birgewa, hakan kejan ra'ayin zukata da ƙwaɗaituwar kasantuwa a cikinta, Da ace zan rufe idanuna, na buɗesu a wata sabuwar duniya da ke da kamanceceniya da Aljannah, yazam dagani sai Ummukulsoom a cikinta, sai ƙyawawan furanni masu kamshi da ƙawa, sai tsuntsaye masu raira kukan dake saka nutsuwa, ga ni'imtacciyar iska mai busawa da ƙamshin ruwa, da nace nafi kowa sa'a a duniya, koda ban samu hakanba matata itace ajannata ta duniya, furannina, tsuntsuwata, sannan zuciyata gabaki ɗaya, ALLAH ya ni'imtar dake gareni har cikin aljanna, ya ni'imtar da rahamarsa gareki har ƙarshen numfashinki, ki zama sanadin zuwan iyayenki aljanna saboda nagartacciyar tarbiya da suka baki da kowanne iyaye ke fata ga ɗiyansu, ALLAH ya kara mallaka miki ni a zuciyata, karnaga hasken kowacce mace a idanuna da ruhina da sunan soyayya sai Ummukulsoom kaɗai”_*.

    Babu shiri Ummukulsoom taja filo ta ƙankame tana sauke numfashi gudu-gudu kamar wadda tayi gudu a cikin sahara. Amaan na dabanne kamar yanda komansa yake na dabban a gareta.😚


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


      Haka suka karasa wannan yini a daddafe cike da begen juna, kowanne tunanin ɗan uwansa ne ya zame masa abokin rayuwa, da yamma Ummukulsoom ta kuma dagewa ta haɗa lafiyyen abinci, har sannan Desmond bai dawoba, dan haka tai komanta cike da nutsuwa, gaba ɗaya gidan ya ɗauki haramar ƙamshin abinci dana turaren wuta zuwa na jiki da Ummukulsoom ta mulke kanta a ciki.

      A haka Amaan ya dawo gidan ya isketa, gaba ɗaya gaɓɓan jikinsa a kasalance suke, tun a ƙofar falon ya amshi kayansa dake hannun Abbas, dan baya buƙatar su sake shigar masa cikin gida, da da yanzu akwai banbanci.

     Motsin buɗe ƙofar ya saka Ummukulsoom dake jere abinci a dani ɗagowa ta kalli wajen, Amaan ya shigo yana baza idon inda zai hangota.

      Tai guntun murmushi tare da tsiyaya ruwa a kofi ta nufoshi cikin takunta na nutsuwa da birgewa, sanye take da rigar Material ruwan ganye mai haske, an masa ɗinkin bubu dayay masifar mata ƙyau, ta ɗaura ɗan kwali irin ɗaurin zara buhari da yay masifar fita da dogon hancinta zuwa idanunta. Ko motsi bai iya yiba, yana tsaye a inda yake ya zuba mata manyan idanunsa farare tas harta ƙaraso gareshi.

    Daf dashi ta tsaya, ta karɓa kayan hannunsa da hannunta ɗaya ta nufi falo ta ajiye tare da ruwan, shima ta dawo taja nasa hannun dariya na cinta, ganin yanda ya narke mata kamar wani ƙaramin yaro.

          Sai da ya zauna cikin kujera sannan itama ta zauna gefensa tana ɗora masa kofin ruwan a kan bakinsa. Dama ƙishi yakeji, hakan yasa ruwan ya kuma masa zaƙi da garɗi a baki, ga sanyi kaɗan da ruwan keda shi yanda bazai cutar da mai sha ba.

       “ALLAH shine abin godiya daya dawo min da kai lafiya cikin aminci da ƙarfin jiki dana zuciya, ALLAH ya albarkaci dukkan aikin daka gudanar yau, ya yafe maka kura-kuran da suka shiga cikinsa”.

      Lumshe idanunsa yayi ya buɗe akan fuskarta, akan laɓɓansa ya furta, “I love you so much Ummukulsoom”. 

        Yanda yay maganar cikin wani irin ƙaramin sauti saika ɗauka raɗa yakeyi, gashi ya kafeta da mayun idanunsa dake wani ƙyalli na musamman.

    Ƙasa Ummu tayi da kanta, itama ƙasa-ƙasa tace, “I love you too my Zunnurain”.

       Babu abinda ya iya banda jawota jikinsa ya rungume yana sauke wani irin numfashi, tsawon lokaci suna a haka kafin su miƙe zuwa ɗakinsa, kaya taɗan rage masa, sai dai bata bari ankai ga cikiba ta gudu, ya bita da kallo kawai yana jinjina kunyarta dake ƙara mata kima a idanunsa.

    Ruwa ta haɗa masa ta fito, dan karma ya haɗa sabgar wankansa da ita sai ta gudu da sauri waje ta barsa.

         Yasan mi takema gudun, baice komaiba ya shige.


★★★★★★


             A daren yau kam sam kasa daurewa Amaan yayi, duk yanda yaso yima Ummukulsoom kawaici saiya gaza.

     Sai dai ya bita a salon da bazata cutuba sosai, hakan kuma bai hana Ummu tai masa raki ba, dan ita dai a nata ganin banbancin kaɗanne dana farko, dukda kuwa yau sai da yay amfani da man zaitun.

     Tun a daren ya kimtsa kayarsa suka koma barci yana lallashinta da sanya mata albarka.

   Ita dai Ummu tana mamakin wannan lamari. wai duk azabarnan da ake sha ahaka wasu ke iskanci, to kosu basajin irin wannan azabarne shin?.

    Duk da murzar da tasha a hannun Amaan haka ta daure da safe ta haɗa musu breakfast, lokacin yana wajen motsa jiki, saboda mai sauƙi tayi sai ta kammala da wuri.


     Yau kam hatta da wanka shine yay mata da kansa, tunma tana zizzilewa harta barsa yay yanda yakeso, dan ta kula rashin tsayawar tata ɓata masa rai takeyi.

     A wajen cin abinci ma shine ya ciyar da ita suna zubama juna salon kallon soyayya mai kwantar da hankali.

    Da zai wuce wajen aikima haka ta zuba masa doguwar addu'a makamanciyar ta jiya, ya tafi maƙale da ita a ransa, duk motsinsa saita faɗo masa a rai, daga bisani ma saiya kasa jurewa ya kirata a waya, lokacin maman Ahmad na gidan taje mata.

     Duk da bawata maganar kirki yayiba taji daɗi sosai, koba komai taji muryarsa taji sanyi.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


       Haka rayuwar gidan taci gaba da tafiya cike da farin ciki, randa bai soba ya miskile mata, da yake tasan halin kayanta sam bata damuwa, rashin yawan maganarsa kuwa bai dameta ba, idan tanason suyi doguwar hira saita masa magana ta chart koda gata gashine, anan ne zai saki jiki suyi doguwar hira mai ban mamaki da birgewa.

    A haka suka kwashe sati huɗu da dawowa lagos, a kuma time ɗinne jarabawar su Ummu result ya fito.

   Sun tsinci kansu cikin tsantsar farin ciki ganin komanta ta sameshi yanda tai fata, aranar kam har ƙyauta ta musamman ta samu ga Amaan da Attahir, hakama Ummi da Abba suka kirata suna jera mata Addu'a, Dad ma saida ya kira, saiga Bily da yaya Zaid, duk sai Ummu ta rasa inda zata saka kanta dan daɗi, gani take tafi kowa zama ƴar gata a duniya, Baba kuwa ai dogon lokaci suka ɗauka suna shan hira, hardasu baba yalwa sai da ta gaisa...........✍🏻


NO. 53 & 54



............Rayuwa kenan, mai tafiya da farin ciki daddd ƙalubale, wataran a tashi haƙora washe da murmushi, wataran kuma saɓanin hakance ke faruwa. To suma su Ummukulsoom hakance take faruwa daga garesu, a kwana a tashi babu wahala wajen ubangiji, yau gasu da shekara ɗaya da watanni biyu da aure, zuwa lokacin cikin bily da Aziza duk sun tsufa sosai, dan suma ba daga zuwa suka samuba, sai dai Ummukulsoom shiru kakeji babu wani motsi.

     Abun naɗan cin ranta, sai dai bawai ya dameta sosai-sosai ba, dan Amaan ma ko a fuska bai taɓa nuna mata damuwa da rashin samun cikinta ba, lobewarsa yake hankali kwance.

      Zuwa yanzu dai Ummukulsoom ta zama lauya cikakkiya, sai dai muce ALLAH yayi jagora a dukkan lamura kuma.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


              Tunda ta tashi yau da ciwon kai ta tashi, gashi Amaan baya gida, dan tunda ya samu ƙarin girma ya zama *Colonel* ɗinan busy ɗinsa ya sake yawa, a daddafe ta gyara gidan ta haɗa tea tasha sannan tai wanka ta sake kwanciya.

    A wannan yanayin maman Ahmad tazo ta sameta, cikin riƙe haɓa tace, “wai kuwa Barrister anya bakiyi gamo ba kuwa? Wannan ciwo-ciwon naki fa yana bani mamaki, halan yauma bakije aikinba?”.

      Zaune Ummu ta tashi tana danne ciwon, cikin murmushi tace, “Kai aunty nikam ke da yaa Amaan bansan wayafi samin idoba, nifa banda komai, yau kuma bana gaya miki ina hutu ba”.

     “Oh aina manta, dama daga kd ne akace anata kiran wayarki kinƙi ɗagawa, shine nace bara naga ko lafiya? Dan Ummi ta damu matuƙa”.

     Da sauri Ummukulsoom ta dafe kanta tana laluben wayarta, ita sam tama manta da wayar na'a silent ne, tasan har Amaan kansa ya kira yama gaji kenan....

       Maman Ahmad ta katseta da faɗin “Al'bishirinki?”.

     “Goro” Ummu ta amsa tana cigaba da laluben wayar.

        “Bily ta haihu namiji, Aziza ma na asibiti”.

    Babu shiri Ummu ta saki wayarta data ɗakko ta daka tsalen murna ta rungume Maman Ahmad, ta rikice da farinci ainun maman Ahmad na mata dariya, kafin kace mi ta shiga bige-bigen waya.

    Maman Ahmad dai na zaune tana kallon ikon ALLAH. 

    Amaan kansa da ta kira ta sanarma ya tayasu murna, shima a ransa yana addu'ar ALLAH ya basu idan suna da rabo.

    Tuni ciwon kan Ummu taji ya watsakke, ga hotunan baby sun cika mata waya, sai mamaki take wai bily ce ta haifi ƙaton yaronnan?, zuwa ƙarfe huɗu na yamma itama Aziza ta sunkuto nata babyn namiji, saiko murna ta daɗu.

    Yau farin cikin da Ummu take ciki ko itace ta haihu iyaka kenan, ko da Amaan ya dawo bai samu kulawarta yanda ya kamata ba, rabin hirarta duk tana kan babys ɗinta, duk sai yaji ta bashi tausayi.


     Suna kwance da daddare ta sake ƙadandanesa saboda sanyin da takeji, jikinta ma da ɗumin zazzaɓi, murya can ƙasa tace, “Zunnur! Amma dan ALLAH gobe ne zamu tafi kd ko?”.

    Kansa ya girgiza mata ba tare da yace komaiba, ta narke masa da sakin kukan taɓara tana murje-murje a jikinsa, “Ni dai dan ALLAH ka barni na tafi, kagafa maman Ahmad ma gobe zata wuce”.

      Ƙafarta da take tutturzawa ya danne da tasa yana kuma lumshe idanu, ganin zata kuma haɗa masa zafi ya matseta a jikinsa, murya ƙasa-ƙasa cikin kunne yace, “Haba Beauty ki bari mana kinfa hanani barci, banda abunki ke da baki da lafiya inake ina tafiya wani waje.....”

    “Ni dai dan ALLAH na warke fa” tai maganar hawaye na tsiyayowa a idonta suka gangara ƙirjinsa.

     Numfashi ya sauke kaɗan ya miƙa hannu ya kunna fitilar ɗakin, haskene ya gauraye ko ina, ya ɗago fuskarta da ƙyar yana sauke manyan idanunsa kan hawayenta, shagwaɓarta tayi yawa kwanakinnan, abu kaɗan saita farama mutane kuka, haka shekaranjiya akan wata shari'a da takeyi, bamafa an kadata bane, daga dai taso a yanke hukunci sai alƙalin ya ɗaga shari'ar sai kawai Ummu tazo masa tana kuka, jiya ma da zaiyi tafiya harda kuka, shi yarasa wannan kuka kukan na miyene?

      Numfashi ya sauke a hankali yana maidata ƙirjinsa, murya a cinkushe yace, “Shikenan naji zakije, amma ba gobe ba, ki bari nanda kwana uku saimu tafi, nima aikin kusan sati uku zai kaini Abuja saimu dawo”.

     Dukda bataso hakaba taji daɗi, dan koba komai zata halarci bikin wasu ƙannensu a ɗilau su uku da za'ayi, dama tanata tunani ta ina zata lallaɓasa ya barta taje, to ga hanya mai sauƙi ta samu.

        Yanda ta ƙanƙamesan ya basa tabbacin ta amince, saiya dan murmusa tare da ɗago fuskarta ya haɗe bakinsu yana bata wata sumba mai kwantar da hankali da nuna tsantsar kulawa da soyayya a gareta.

     Sakin jiki tayi itama tana bashi haɗinkai da ƙyaƙykyawan saƙo mai zurma masoyan da zuciyoyinsu suka gama aminta da juna hundred percent. 

     

    (Da baya-baya nima na fito dan sunfi ƙarfina walle😬😑🤭).



★★★★★


     Kamar yanda Amaan ya alkawarta kwana uku suka shirya tafiya kd, Ummukulsoom na cike da tarin zumuɗi, bawai wannan ne farkon zuwanta ba bayan aurensu, a'a tajajje harma ɗilau kusan sau uku, biyu tare da Amaan ɗaya kuma biki sukaje har dasu bily ma da maman Ahmad.

      Gidan Dad suka sauka kamar yanda suka saba a sashensu, sun sami tarba ta ƴan gata tamkar yanda Momcy ta shagwaɓasu yanzu, duk yanda Amaan yaso Ummu ta bari sai washe gari ya kaita gidan Abba idan zai wuce Abuja sam taƙi, tabi ta addaba masa da shagwaɓa, daga karshe dai dole ya hakura ya kaita a ranar taje taga babys dayake duk suna wajen Ummi hatta da Bily ɗin. Farin cikin da Ummukulsoom ke a ciki ɓata lokacine, Ummi dai itama sai kallonta take da murmushi, dan ta hango itama dai Ummu ɗin ta kamu, musamman yanda ta ƙara buɗewa da cikar ƙirji, ga fatarta tayi wani luff tamkar bata ganin rana, sai yawan Complain kanta na ciwo, bata son ƙamshin turaren wane, batason na wane.

     Ummi taji daɗi sosai, fatanta ALLAH dai ya raba lafiya.

     A ranar dai bai barta ta kwana a gidanba, dole ta bisa suka koma gidan Dad badan ranta yasoba, washe gari kuma ya kafa ya tsare sai da yamma da zai wuce Abuja ya sauketa anan gidan Abba ya wuce nasa uzuri shima.

  

     Ranar kusan raba dare sukai hira ita da Aziza da Bily, maman Ahmad ma sai da Attahir ya kasa haƙuri ya biyota ya tasa ƙeyar kayarsa suka wuce, ita kanta Ummu da Amaan ya kirata yaji basuyi barciba faɗa ya kama mata, tayaya wai zata zauna surutun banza har tsawon wannan lokacin ita da bata da lafiya, ta inda yake shiga ba tanan yake fitaba, ita dai shiru tayi, daga ƙarshe ya maida kiran nasu bidiyo kol, saida yaga ta kwanta ta fara barci sannan ya yanke kiran.

        Zuwa ranar suna ai Ummukulsoom ta gama yin tiɓis da ciwo. amma tsabar kar Amaan ya hanata zuwa ɗilau taita daurewa da jurewa, koda yazo kd ranar juma'a da yamma bayan suna da kwana ɗaya kenan daurewa tai taƙi bari ya fahimta, aranar kuma ya tarkatota daga gidan Abba suka dawo gidan Dad.


★★★★★


       Haka taita dauriya har washe gari suka wuce ɗilau ita da shi. Osin ne ke jansu suna bayan mota, sai motoci biyu na yaransa, tun Ummukulsoom na dauriya harta gaza ta matso jikinsa ta lafe. Takardun hannunsa ya ajiye yana maida hankalinsa gareta, yanda ya tsira mata idanune ya tilasta ta lumshe nata tana kauda kai gefe.

        Hannunsa ya ɗora a goshinta, tai saurin riƙewa tana narke masa fuska, shima yanda zafin ya ratsa masa hannu saiya ɗan lumshe ido ya buɗe a kanta, da ƙyar ya iya buɗe baki yana faɗin, “Kinata wani danne ciwo saboda kar a hanaki zuwa yawo ko?”.

      “Nifa a'a” Ummu ta faɗa tana ɓata fuska.

    Bai sake cewa komaiba ya maida idonsa ya lumshe hannunsa bisa goshinta, a haka suka isa Ɗilau har barci ya fara kwasarta.

       Tunda motocin uku suka shigo yara ke binsu,  duk majalisar da suka gitta zakiji ana ga Umma nan tazo, daga nan saikiga an dasa hirarta ita da mijinta.

     A ƙofar gidansu motocin suka tsaya, Amaan ya tsirama fuskar Ummukulsoom idanu yana tunanin yanda zai tasheta, dan da alama barcin na mata daɗi, gashi matasan gidansu sun fito tarbarsa tamkar yanda suka saba, dan duk lokacin da yazo garin haka suke masa tamkar wani shugaban ƙasa.

     Abbas da yasan dokar bai buɗe ƙofarba, shidai ya fito ya tsaya daga waje, hakama sauran sojojin dake a sauran motocin. 

    Amaan ya ɗan kalli agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa yana turo numfashi kaɗan ta hancinsa, dolene ya tasheta badan ya soba, bakinsa ya kai dai-dai kunnenta ya hura a hankali.

    Buɗe ido tayi da ƙyar ta kallesa, harsun ƙara fitowa da canja launi,

    “Sorry Beauty mun iso” Amaan ya faɗa akan laɓɓa. Badan tana kallon bakinsa ba bazata taɓa fahimtar miyake faɗaba, yunƙurawa tayi a hankali ta tashi zaune, ta gyara mayafinta da fuskarta sannan ta kai hannu zata buɗe sashen da take, saurin riƙota yayi yana zuba mata mayun idanunsa masu haske da cikar gashi, “5pm zamu wuce”.

     Narke masa fuska tayi dayin rau-rau da idanu tamkar zatai kuka, “Wai yanzu da gaske bazaka barni na kwana ba Zunnur?”.

       Kamar bazai tanka ba sai kuma ya nisa yana murza hannunta da sake haɗe fuska, “Kinsan dai banason gardama, ke baƙya tausayin kankine, yau zamu wuce kiga Doctor”.

     “Ni dai lafiyata ƙalau, sai aita ɗoramin ciwo” ta ƙare maganar da cuno baki.

     Yatsansa yasa ya ɗalli bakin yanda zataji zafi, sauri saka hannu tayi tako dafe bakin idonta na cika da kwalla.

    Ɗauke kansa yayi daga  gareta ya fara ƙokarin fita, cikin yaransa wani yay azamar buɗe ƙofar ya fice abinsa ba tare da yabi takan Ummukulsoom ba data cika tayi fam da haushinsa.

     Ganin ya fita itama sai aka buɗe mata ƙofar, kunya sosai ta kamata ganin wajen cike da jama'a, sam batai tunanin hakaba, da tuni ta fito a motarnan, yanzu fa wani sai yamayi tunanin wani abun sukeyi....

       Ta ɗan kalli sashen da Amaan ke gaisuwa da mutane ta janye ido, shaddar jikinsa tai masa ƙyau sosai, a koda yaushe ya saka manyan kaya saisu kara masa cikar haiba da kamala tare da wani girma na musamman, tuni itama su murja sun fito tarbarta, kowa sai farin cikin ganinta yake, dan sun san koba komai zata jiƙasu da abinda ALLAH ya hore mata.

   A cikin gida mutane sai kallonta ake, kowa burinsa yay mata koda maganane ta kulasa, Ummukulsoom tariga da ta zama *Wutsiyar raƙumi* a cikin ƙauyen ɗilau da kewaye, yanzu haka shirye-shiryen kafa wata ƙungiya take a ƙauyen domin taimakon karatun ƙananan yara da matan aure. Abinda ke kara burge mutane da Ummu, sam bata da girman kai, gata da sakin fuska wa jama'a, bata nuna ƙyankyaminsu balle gudun abincin ƙauyen, idan tazo komai ci takeyi babu ruwanta.

     Yanzu haka tana ajiye gyale da handbag catai a bata tuwon dawa.

   Murja dake mata wani kallon sama da kasa suka kwashe da dariya ita da Hadiza da sa'ade.

    Hararsu tayi cikin wasa, “malamai lafiya?”.

    “A'a lafiya ƙalau, cika aikin soja muke kallo” cewar Azima da itama ke kwasar tata dariyar.

   Sam Ummu bata fahimcesu ba, ta ƙwalama mariya kira da taga ta gitta da tire an ɗora ruwa da kwanon shan ruwa sabo fil (itama yanzu yaranta biyu).

     Shigowa mariya tayi tana faɗin “Na'am aunty Umma, yi hakuri zanzo mu gaisa baba ne ya sani aiki”.

        “Keni ba wannan ba, tuwon dawa nakeso miyar kuka ko kuɓewa ɗanya, asamo yajin daddawa da manshanu”.

      “Naga ta kaina, Aunty Umma wannan lissafin fa? To bara nakaima yaya Amaan fura na dawo”.

         “To maza, idanma babu manshanun a aika gidan Inna laraba nasan baza'a rasaba”.

   Fita mariya tayi tana amsawa, yayinda su Hadiza suka dasa sabuwar dariya. 

    “Wai ɗan tuwon dawa muka samo kenan? Lallai soja baka da dama”.

      Sai yanzu Ummukulsoom ta fahimci iskancin da suke mata, cikinta ta shafa tana yatsine fuska, “Oh kufa baku da man kai, wai dama iskancin da kukemin kenan? To kuma saita kanku ni banida komai”.

      Nusaiba taimata gwalo tana faɗin, “Hakane kam baki da komai”.

   Ganin basu yardaba ta sharesu, aka koma tsokanar Hassatu dake fama da tsohon ciki, Ummu na faɗin ya kamata ta huta hakanan haihuwa bakwai, ai sai jininta ya gama ƙarewa.

     A haka Baba yalwa ta shigo ma Ummu da tuwon dawa sai tururi yake, “Umma ga tuwon, ga Ramatu can zata soya miki man shanun”.

    “Lah baba na sakaku aiki, maimakon kubar mariya ko bilki suyi”.

     Dariya Baba yalwa tayi tana faɗin, “Inani ina zama, nasani ko mijine, dan banason kishiya nima soja nakeso”.

    Murmushi kawai Ummu tayi kunya na kamata, shin kodai wai cikinne da ita, kowa sai jifanta da wannan kalma yake, hakama a wajen sunan su Bily. Koda aka kawo manshanu saita miƙe ƙafafu taci tai nak abinta, sunata hira da ƴan uwanta da suka cika ɗakin, cakakin suruntunsu yasa har aka shafa fatihar ɗaurin auren basuji bama, zafi ya ishi Ummu ta mike tana faɗin waje zata tasha iska, dama zamanta yasa duk suka taru, dan haka kowa ya fito, saida ta wanke hannu sannan suka sake kafa dandakin sabuwar hira, kowa sai kallon Ummukulsoom yake, komai nata birgesu yakeyi, kallonta suke tamkar wata sabuwar halitta daban a cikinsu.


      Shikam Amaan tunda aka ɗaura aure baba yasa aka kaisa can shagon dake soron wani maƙwafcinsu saboda sanin shi ba mutum bane mai son yawan hayaniya, wajen akwai sanyi kasancewar rufin kasane, kuma sabon gini sosai Amaan yaji daɗin hakan, yana ciki abinsa su Abbas na daga waje zagaye dashi, yara sai kallonsu suke daga nesa, hatta da manyan ma kwarjininsu ya cika idonsu, kowa dai yasan mu ƴan ƙauye da tsoron soja da ɗan-sanda😃🙊.

     Sai da za'ai salla ne ya fito yay alwala a ƙofar gida, mafi yawan mutane gani suke Ummukulsoom tariga da tayi nisan da sai dai a hangeta daga nesa, mijinta abin sha'a da birgewar kowa, itama haka komai nata a cike da birgewar.


         A cikin kananun maganganu na mata Ummukulsoom taji abinda ke faruwa na ɓatan Basiru daya janyowa iyayensa ciwo su duka saboda damuwar da suka tsinci kansu a ciki, da farko taso ta share zancen, amma kuma saita gaza hakan, saboda har gobe tana ƙaunar iyayen basiru, dan sam basuda laifi na komai a gareta, basu suka hana ɗansu ya aureta ba, hasalima suma sun shiga damuwa da rashin auren.

   Murja taja gefe tana tambayarta mike faruwa ne?.

      Murja ta sauke numfashi tana gyara tsaiwa, “Ai wlhy Umma abun babu daɗi, kinsan dai halin garinnan, idan abu yazo tun kanajin gaskiyar zance har kaji an canja labarin, kusan shekara biyu kenan babu basiru babu labarinsa, to da farko dai iyayen basu damuba sosai, dan kinsan ya taɓa irin wannan ɓatan kusan shekara biyar ba'asan inda yakeba, sai daga baya kuma yazo wai ashe yabi matarsane wai ko faransa oho dai, to tundai zuwan da yay yace sun dawo tunda ya tafi bai sake zuwaba, da yake ƴar gidan gwamnan katsina daya sauka yake aure, baba ado ɗin ance sunata zarya gidan an hanasu ganinsa, sai daga bayan nan ne labari yake fitowa wai wani ya kashe aka kaishi firizina, ammafa ashahadu a wuyan masu faɗa tunda nidai ba agabana akaina alkur'an”.

     Sosai Ummu ta girgiza da wannan batu, sai maimaita kalmar kisan take a ranta, harta cire zancen a ranta sai kuma ta kasa daurewa tai gajeren saƙo ta turama Amaan akan zataje wani gida ta duba mara lafiya.

    Kusan mintuna biyar yay mata reply akan saita dawo, amma ta jira ko Abbas kaɗaine yazo ya kaita.

      Sake tura masa saƙo tai akan basai Abbas ɗin yakaita ba, nan kusane.

    Ok

Kawai ya sake turo mata, ita da Murja suka zare jiki suka fita zuwa gidansu basiru.


      Hankalin Ummukulsoom yayi masifar tashi ganin yanda gidansu Basiru yay masifar lalacewa, bata sake ruɗewa ba saida suka shiga ciki sukaga halin da inna da baba ke ciki, sai talatu dake jiyyarsu su duka biyun, hawaye suka sulaloma Ummukulsoom, fitowa tayi ta kira Amaan, gaskiyar abinda ke faruwa ta zayyane masa, da farko faɗa ya kamayi saboda jin wani kishi da takaicinta, amma yanda take masa kuka da nuna masa ba abinda basiru ya aikata zai dubaba mutuncin iyayensa da tausayinsu.

    Yanke wayar yayi batare da yasake tanka mata ba, Ummu ta tsirama wayar ido ranta na suya, tana son Amaan, amma wani lokacin murɗaɗɗen halinsa na bata haushi, sam baka isa gane kansa ko yanke hukunci akan halinsa ba, idan yaso sauki yay maka, idan kuma ya murɗe ita kanta bata isa shawo kansa ba, sai ya gadama ya sauka dan kansa.

     Jitai kawai an rungumeta ta baya ana share mata hawaye, tai saurin juyowa ta kallesa dukda taji ƙamshin turarensa, sai dai batai zaton zaizoba, sai kawai ta faɗa ƙirjinsa ya rungumeta.

     Su murja wannan lamari ya birgesu, hakama yaya Auwalu da Hambali da suka masa rakkiya zuwa gidan, sai sojojinsa da suka tako masa baya dan aƙafa yazo saboda ance babu nisa, kuma yanason ganin gari shima.

    “To kukan ya isa shagwaɓaɓɓiya, kimin iso”.

     Hawayenta ta share tana murmushi, ta sumbaci gefen kumatunsa kafin ta shige saboda rashin kunyar da tayi gabansu yaya hambali da suka saki baki suna sake kallonsu.

     Amaan ko, ko a jikinsa, dan wajenma ya shafa yana sauke numfashi kaɗan, sai dai yaƙi kallon kowa dukda yasan bashi kaɗai bane a wajen.

     Mintuna kaɗan Ummukulsoom ta fito, nuni tai masa ya shigo. Tana gaba yana biye har cikin gidan, shi kansa jikinsa yayi sanyi da ganin halin da tsoffin suke ciki, yanda talatuwa ta sake masa bayani tana kuka sai zuciyarsa ta karye, a take yace talatuwa ta shirya su baba yanzunan zasu wuce dasu kd asibiti.

       A tare suka fito shida Ummukulsoom daga gidan, tafiya suke a jere da juna kowa fuska cike da damuwa, sai kallonsu ake, yayinda tuni har zance yafara fitowa, dan suna isowa ma su murja suka fara baza maganar cikin ƴan biki.

     Sai sakama su Ummukulsoom albarka akeyi, maimakon 5pm da suka shirya komawa sai ta cabja zani, a lokacin suka wuce dasu Inna da aka fitar ranga-ranga daga gida, talatuwa nata sharar ƙwalla.

      Sun taho jama'ar ɗilau na sake jinjina dattako da ƙyaƙykyawar zuciya irinta Ummukulsoom da mijinta, kafin kace mi gari yafara ɗaukar zance, harda masu cewa Amaan atake yayma gwamna waya wai asaki basiru (kai ƙauye akwai iya canja zance😂).


     ★★★★★


    Taimakon gaggawa aka shiga bama baba da inna, dukda Ummukulsoom bata da isashshiyar lafiyar itama haka ta daure, sai da Amaan yaga tayi laushi da yawa yaja hannunta sukabar asibitin, bayan ya bar yaransa biyu tare da talatuwa, akan duk abinda ake buƙata suyi.

      Ba gida suka wuceba, kiran Ummi Amaan yayi ya tabbatar tana asibiti, abin ya bama Ummu haushi, wai dannmi Amaan zai kira Ummi yace zaizo a dubata, koma kunyar Ummi bazaiji ba kenan. Shi dai bai tanka ba, dan wannan saurin fushin nata shikam zuwa yanzu ya fara mata uzuri a kansa.

       Gwajin farko da Ummi taima Ummukulsoom aka gano ciki ɗan wata biyu maƙale a mararta, kasa motsi Ummukulsoom tayi, dan itafa ko kaɗan batai tunanin cewar maganar mutane na batun cikin gaskiya baneba, catake surutune kawai, Ummi na fita fuskarta washe da murmushi Amaan ya jawo Ummukulsoom jikinsa ya hau kissing ɗinta, yama rasa yanda zai musalta farin cikinsa a yau, shima zai zama uba, ALLAH yay masa ƙyautar abinda babu mai bakashi a faɗun duniya, kuɗi ko mulki ballantana gata.


      Abu yayi daɗi, kafin kace mi zance ya baje dangi, musamman da suka koma gida Momcy sai nan nan take da Ummukulsoom, tamkar zata maidata ciki, shi kansa Dad yana cikin farin ciki matuƙa, ALLAH ya amsa addu'arsa kenan, dan kullum fatansa kenan da addu'arsa ALLAH ya bama su Fodion sa rabo suma, to gashi yazo lokacin da ba'ai zatoba.

         Tunda zancen cikinnan ya fito tattalin da Amaan kema Ummukulsoom saiya ninku, motsi kaɗan hannunsa nakan cikinta, ita harma sai ta fara fushi wai kowa harya fara daina sonta.

    Duk dauriyar Amaan akan kar yayi dariya saiya kasa, saida ya murmusa saboda ya fahimci itafa tsakaninta ga ALLAH take kukan akan anfi son ciki yanzu fiye da ita...

      “ALLAH idan bakimin shiruba murƙusheki zanyi, bar ganin baki da lafiya”.

    Muƙut ta haɗiye hawayenta saboda a ƴan kwanakinnan babu abinda tafi gudu irin Amaan yace zai kwanta da ita.Yay murmushi yana mikewa ya nufi bayi dama wanka zaiyi.

       Tun a daren Amaan ya fara bincike akan komai na Mahaifin Meenal, da ita kanta meenal ɗin, itama Ummukulsoom ta fara barci yafi karfinta, dole ta ajiye ta ɓingire barci, Amaan yay guntun murmushi yana ɗaukar lap-top ɗinta ya duba abinda ta samo itama, ya daɗe baiyi barciba, washe gari kuma tunda safe Ummukulsoom ta roƙesa akan ya barta ta fita wani waje, bai hanata ba, sai dai ya haɗata da Abbas.

        Saida suka fara biyawa asibiti taga yanayin jikin baba da inna sannan ta kuma sake ma talatuwa wasu tambayiyi kafin ta fice, ita ta amshi driving ɗin a hannun Abbas tana bin address ɗin da ta samu da taimakon ɗan gidan innar basiru na zariya, dan a waya ta kirasa sukayi magana, shima tace kome yake yazo kd a yau, dan tanason ta binciko komai da wuri, tunda tasan zata koma lagos da wuri saboda tarun ayyuka dake a kanta.

        Ummukulsoom ta ɗan sha wahala wajen abinda taje nema, har saida Amaan yama kirata yanata faɗa akan ta dawo gida hakanan, tunda yasan itama bawani lafiyane cikakkiya da itaba.

       So take ta lallaɓashi akan case ɗinnan, dan haka bata ja ba tasa Abbas ya tuƙota ya maidota gida, tana dawowa kuwa ta kwanta saboda zazzaɓin daya rufeta ruf, hakan ya sake ɗaga hankalin Amaan, gashi a yau yake son komawa Abuja, yasan kuma bazata yarda ta bisa ba a yanda dukkan hankalinta ya raja'a akan wannan zancen na basiru.


         Su inna suna samun kulawa ta musamman, dan haka a cikin sati ɗaya kacal suka murmure, sai dai damuwar rashin ɗansu, kuma yanda sukaga Ummukulsoom da Amaan harma da Dad da Abba da suka shiga cikin zancen suma sai suke kawaicin dannewa a gabansu.

     Har su Ummukulsoom suka cinye sati ukun da zasuyi babu wani labari game da basiru, dole suka tarkata suka koma dan tanada cases a gabanta da suke shari'a a kansu, ga laulayin ciki da dauriya kawai takeyi kasancewarta jaruma, da kuma son aikinta data kwallafa ma rai, dan duk wanda Ummukulsoom zakaga ta kare a gaban alƙali to katabbata shi aka zalinta, sannan kuma talakane mara karfi, shiyyasa abokan aikinta lauyoyi da yawa kejin haushinta, gashi kuma ALLAH ya bata ƙwazon aiki da jajircewa, sannan bata da tsoro sam, a ƙanƙanin lokacin data fara aiki har sunanta ya fara shiga bakunan lauyeyi da mutane, karanta ya fara kai tsaiko wajen karawa da manyan lauyoyin da ake shakkar haɗa shari'a dasu, ta fara ajiye tarihin nasarori.........✍🏻




............A gajiye ta shigo cikin Barrack ɗin, dan jan motar take tamkar wata ƴar koyo, tai horn ɗaya daga sojojin dake tsaron gidan nasu ya buɗe mata gate ta shiga, tunda tai fakin idonta ya sauka akan motocin Amaan, hakan ya tabbatar mata ya dawo gidan, dan kusan kwana uku kenan yana mai-duguri.

     Da hanzari ɗaya a cikin sojojin ya zo zai karɓar ƙatuwar rigarsu ta lauyoyi data fiddo a sit ɗin baya da handbag ɗinta, kanta ta girgiza masa tana ɗan dafeshi da hannu, dan kanta ke mata ciwo saboda fafatawar da sukai yau a kotu da wani shegen lauya mai masifar naci, amma dukda haka ta nuna masa *Mai laya kiyayi mai zamani* dan an yanke hukuncin kuma tayi nasarar kwatoma yarinyar da akaima fyaɗen haƙƙinta.

      Amaan dake jikin Window yana kallonta ya fito cikin takunsa na bajinta da lafiya, yanda take tafiya kamar mara ƙashine yasa harya fito bata ƙaraso ƙofar falonba, gabanta ya tsaya yana maijin tausayin jarumar matar tasa.

     A hanki ta ɗago idanunta da sukai mata nauyi, hannu ya buɗe mata ta shige jikinsa tana sauke ajiyar zuciya, shima nannauyan numfashi ya sauke yana sumbatar kanta, jikinta ringim da zazzaɓi kuwa.

    “Sannu da zuwa Sweet Fodio na, shine baka kirani ka sanarmin zaka dawo yau ba?” Ummukulsoom ta faɗa a hankali tana ɗagowa daga jikinsa.

    Baice komaiba ya janyeta a jikinsa yana amsar kayan hannunta, itama ya kama hannun nata suka shige ciki.

      Saida suka shiga bedroom ɗinsa da suke amfani dashi ya zaunar da ita sannan yay ɗan durƙuso a gabanta yana kafeta da mayun idanunsa, “Beauty ki ɗauki hutu haka mana”.

    Fusaka ta narke masa, “Dan ALLAH Yaa Amaan kayi haƙuri kaikace haka, idan na aikata haka cases ɗin mutane fa? Ni yanzu ciwon jikine kawai ke damuna, suko jikkunansu da zukatansu duk ke ciwo, karka kalli halin dani nake ciki dazai zama naɗan lokaci, ka kalli su yanda suka tsinci kayinsu”.

     Numfashi ya sauke yana mikewa, kusa da ita ya koma ya zauna ya jata jikinsa ya rungume, hawayen da take maƙalewa tuni sun fara gudu a fuskarta, bai hanata ba, baikuma ce mata komaiba, sai bayanta da yake ɗan bugawa kaɗan-kaɗan, saida tayi mai yawa sannan ya ɗagata ya cire mata kayan jikinta, da kansa yay mata wanka, ta ɗauro alwala suka fito.

     Tunda cikin ya bayyana bata iya girki, dan ko tayi bata iya ci, Amaan kuma ba zama sosai yake a gidaba, tafiye-tafiyansa yayi yawa, hakan yasa Maman Ahmad ta juri kawo musu a kowanne lokaci, yau ɗinma itace ta aiko ma Amaan abinci.

      Fita Ummukulsoom tai zuwa kicin ta haɗo musu fruit salad, dan tafi ƙaunar shansa fiye da komai, saiko tuwon Amala ko na dawa, a cikin firij ɗin dani ta saka ta wuce ɗaki danta gabatar da sallar la'asar, dan Amaan ma ya fita sallar.


★★★★


      Yanda take shan fruit salad ɗin hannu baka hannu ƙwaryane ya saka Amaan kallonta cike da tausayawa, ya amshi spoon ɗin yaci gaba da bata da kansa yana faɗin, “Beauty yunwa kikeji, amma bazakiji abinci ba sai baƙin tuwo, ni wannan Friendy n nawa bansan da wane salo tazo ko yazo ba” yay maganar hannunsa akan cikinta daya fara tasowa.

     Murmushi kawai tai masa ta zare cokalin tana cigaba da shan kayanta ganin yana ɓata mata lokaci.

        “Sweet Fodio kasan wane tunani nakeyi kuwa akan zancennan na basiru?”.

        Kallonta yay ba tare daya amsaba, amma hakan yana nufin hankalinsa na a kanta. Ta haɗiye abinda ke bakinta tana kuma dai-daita murya, “inaga ya kamata mu fidda maganarnan duniya ta sani, mutumin nan ɗan siyasa ne, bazaiso sunansa ya ɓaciba, da yaji zancen zai karaɗe duniya zai fara ƙokarin binne case ɗin, mukuma ta wanna hanyarne zamu kamashi dumu-dumu”.

      Kansa ya shiga jinjina mata idonsa kafe a kanta, tabbas ya aminta da zancenta, dan abubuwansu na kamanceceniya da juna musamman ta fannin bincike. Ganin ya fahimceta saita ƙara faɗaɗa masa bayani akan shirinta, a daren ranar kuwa suka saki bayanai ta hanyar wani abokin Amaan baban ɗan jarida dake da gidan tv nasa na kansa.

       A safiyar washe gari kuwa labari ya fara fita



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


         Hankali tashe Meenal da taci karo da zancen a social network ta samu mom nasu, dan matakin farko dasu Ummukulsoom suka fara bi kenan, sanin mafi yawan al'umma sun raja'a da social network yanzu, a take Momin su Meenal ta kira dadinsu dake can yana fafutukarsa ta ƴan siyasa, dan an kadashi ne a wannan zaɓen bayan ya kammala shekara huɗunsa, zuwa yanzu kuma soyake ayi hannun karɓa tsakaninsa da gwamnan daya kadashi bayan ya gama burin yin shekara takwas, daganan ya fito takarar shugaban ƙasa.

     Lamarin ya girgizashi, a take ya nema wani alƙali amininsa akan ayi duk yanda za'ayi case ɗin basiru ya canja salo zuwa wani abun daban, dan shifa har zuwa yanzu bai taɓajin zai yafema basiru ba saboda dukan da yayma meenal wanda ya barmata ƙaton tabo a fuska da duk sanda suka gani sai sun tuna da abinda yayi.

      Dama idonsu Ummukulsoom akansa suke, dan haka sukai amfani da wannan damar wajen yima baba mahaifin basiru jagora ya shigar da ƙara a wata babbar kotu dake nan kaduna da taimakon Abba da Dad.

       A daren ranar aka miƙama mahaifin Meenal sammaci daga kotu, sannan aka saka police binciko dukkan prison dake cikin katsina neman basiru.

          Har dai washe gari babu wani labari dangane da samun basiru, sai da akabi wasu manyan matakai kafin ai nasarar ganosa cikin gaggan ɓarayi, a yanda shirin mahaifin Meenal yakema saura kwana ɗaya kacal a kashe su basiru.

       A yanayin da aka ɗakko basiru daga jail abun babu daɗin gani, dan dolema aka zarce dashi asibiti daga nan, ashe dukan tsiya yaci hannun gayun da suke tare a daren jiya.

     Su Ummukulsoom suna lagos aka sanar musu da samunshi, dayake dukkan komai hannun Abba da Dad ya koma, dan hakama Abba yace Ummukulsoom tabar maganar shiga case ɗin a nemi kwararren lauya daya daɗe a aiki, amma sai Ummukulsoom taita roƙonsu akan zata iya.

     Ummi ce ta bada shawarar su barta kowa ya bita da addu'ar samun nasara, kar a sare mata gwiwa.

       Inna da baba sosai hankalinsu ya kara tashi ganin yanda ɗansu ya koma, ko mai fama da ciwon HIV iyakar lalacewar da zaiyi kenan, banda ƙwala-ƙwalan idanu babu abinda kake gani a jikin basiru, ya rame iyakar ramewa, fuskarsa kam tayi baƙi duk ya koje tayi tabbuna na raunikan duka saikace wani tsohon ɗan daba, ga wasu ƙuraje da duk suka bata masa jiki harma fuskar masu shegen wari dan ƙazanta, duk mai imani ya gansa saiya tausaya masa.

      Kwana biyu da samo basiru Ummukulsoom da Amaan da Attahir harma da a maman Ahmad suka dira kd da daddare, dan washe garine za'a fara shiga shari'ar su basiru.

      Kallo ɗaya Ummukulsoom ta iyama basiru dake barcin wahala ta fito abinta, jarumta sosai ta nuna wajen danne kukanta dan kar zuciyar Amaan ta sosu saboda kishinsa data gama fahimta akan lamarin, dukda da yarjewarsa take komai hakan bai hanashi yawan nuna ɓacin ransa ba idan ya ga ta cika yawan magana akan case ɗin, dan haka saita iya takunta, dan ita harga ALLAH bada wata manufa take hakanba, sam babu wata soyayyar basiru a ranta tun shekarun da suka shuɗe kafinma tasan kanta, tausayin iyayensa ne kawai ya jagoranci damuwarta akan lamarin.

           

★★★★★★


         Duk da ta tashi babu jin daɗin jiki haka ta nuna jarumtarta wajen dannewa aka shiga kotun, a wannan zaman maida kanta sakara tayi a kotun, lauyan da ke kare baban Meenal yanata murna akan ashema shashasha suka samo, danshi kam gaba ɗaya ya rainama Ummukulsoom wayau akan shari'ar, gashi dama a haife zai iya haifarta, danshi shirinma ritaya yakeyi nan kusa kaɗan.

      Jikin su Abba saiya fara sanyi akan yanda Ummu ta nuna sanya a kotu, shiko Amaan dama baima halarci shari'ar ba sam, sai Attahir ne kawai yaje.

          Ummukulsoom guduwa tayi, dan kar kowa yay mata maganar abinda tayi a kotu, dan ita tasan minene a ranta, batason kowa ya shigar mata aiki koda Amaan ne kuwa.

      Dad ne yake sanarma Amaan abinda ya faru a kotu yau, Amaan yay shiru yana nazari, har Dad ma yazata bazai samu amsa ba sai yaga ya nisa yana gyara zama, “Karku damu Dad, kubita a haka kawai, dan Ummukulsoom nada matuƙar wayo, karku ɗauka dan bata jima da fara aiki bane bata gama kwarewa ba, ni nasan tanada dalilin bama wancan lauyan damane, kuma zakace nina faɗa maka”.

      Kai Dad ya jinjina cike da gamsuwa da zancen ɗan nasa. Koda Amaan ya dawo sashensu baima Ummukulsoom maganarba, yama isketa har tayi barcin ta, shima kwanciya yay gefenta bayan yay shirin nasa barcin, ya daɗe yana kallonta tare da shafar cikinta kamar yanda ya saba a kowanne dare har barci ya ɗaukesa.


        Alƙali yabada damar jami'an tsaro su cigaba da tsare basiru, kuma Ummukulsoom ce ta bada wannan damar ta hanyar maida kanta sakara datai a kotu, lauyansu Meenal ya bada hujjoji masu karfi akan kisan kai Basiru ya aikata. Tayi hakanne saboda basiru ya samu tsaro, duk kuma abinda ya samesa a halin yanzu mahaifin Meenal za'a zarga kai tsaye. Shi kansa lauyan su Meenal saida aka fito ya harbo jirgin Ummukulsoom, dan haka hankalinsa ya tashi, wato wanan yarinyar shegen wayone da ita. Sam kasa barci yay a daren, yanata ƙulla dabaru na gaba ta yanda zai bada damar korar ƙarar ma.

     Itako Ummukulsoom da kowa ke ganin bazata iya komaiba bayan  Amaan da yay mata ƙyaƙyƙyawar fahimta barcinta ta kwasa hankali kwance harda munshari, (yo tasan ta gama fafe gorarta harda tanajin murfi, to mizai gagareta aranar tafiya? Idan ance ta fito🤷🏻‍♀️).

         Washe garima tunda safe ta fita a gidan, bata dawoba sai kusan 11, harma Momcy ta rufeta da faɗa saboda ko breakfast batayi ba ta fita, aiko itace da kanta ta zaunar da ita ta bata abinci, sai da taci ta ƙoshi sannan Momcy ta barta, shi dai Amaan yana zaune a falon yana jinsu da kallonsu amma uffan bai ceba, sai dai harga ALLAH sun birgesa, yanda kowa ke nuna kulawarsa ga matarsa yana tsintar kansa a farin ciki sosai.

       A ranar da daddare suka koma lagos, sai lokacin da aka ɗibarma shari'ar yayi zasu dawo.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


         Dad nidai da zakuji shawarata wlhy da kun janye batun kisannan da kuka ƙaƙabama basiru, gara ku fiddo gaskiyar maganar abinda ya faru ayi shari'ar nan a kansa, ina tsoron karfa shari'arnan ta canja salo muzo mu afka ciki........”

      “K dalla rufema mutane baki, ke mi kika sani ne? Duk ma abinda ya faru ba kece kika jama mutane ba, inda baki kawo ɗan matsiyatan nan ba a matsayin mijin aure har wannan abun ya farune?”.

     Baki Meenal ta zunɓura tana matsawa daga kusa da yayanta daya katseta a tsawace tamkar zai maketa.

     Shiru falon yayi, sai gungunin Meenal kawai, shima bawani fita yakeyiba.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


      Ɓangaren su Suhailat kam sunji komai daga bakin meenal, sai dai suma fa ba haka sukaso lamarin ya kasanceba dan basuso Abban Meenal ya juya zancen zuwa wai kisankai Basiru yayiba, a ganinsu gamma ai shari'a akan abinda ya akata musu a zahiri bawai a sakko wani zance daban ba da sam babushi a tafiyar, hakan tamkar zalintar basirunne kuma. Amma abinda suka sani koma dai miza'ayi gaskiyar zance zai fita suma har a nemosu.



*_BAYAN SATI HUƊU_*

  

             Bayan sati huɗu aka sake zama shari'ar basiru, sai dai fa a wannan karon salon Ummukulsoom ya bama kowa tsoro, musamman data kawo zancen auren Meenal da basiru, dan saida ta gama bincike tsaf akan dukkan aure-auren da basiru yayi hatta da abokansa su Najeeb.

     Ta nemi alfarmar alƙali na ganin Meenal, hakan yasa Meenal tasowa ta tsaya inda ake tsayawa. Wasu irin tambayoyi masu ruɗa tunani Ummukulsoom takema Meenal, har lauyansu yay magana, amma kasancewar tambayoyin Ummukulsoom nakan tsari sai alƙali bai karɓi ƙorafinsa ba aka bama Ummukulsoom damar cigaba da yima Meenal tambayoyi.

       Meenal fa ganin za'a ƙureta saita zurma bisa ga ƙafa da Ummukulsoom ta bata nayin talala a tambayar data jefa mata ta ƙarshe.

      Gyan-gyan gyan gyan, zancen Meenal fa ya tabbata, dan shari'a ta canja salo, cikin hikima da dabaru na Ummukulsoom ta dawo da shari'ar ainahin kan hanya na batun dukanta da basiru yayi, bawai batun kisan kai da akace yayi a farko ba.


★★★★★★


      A can ɗilau kuwa labari nata yawo cewar Ummukulsoom tazama alƙaliya🤭🤣, wai itace kema basiru shari'a bayan mijinta ya ƙwatoshi hannun ƴan shan jini, shima basirun ashe ɗan shan jini ya zama shiyyasa yay kuɗi yaketa auren ƴaƴan masu kuɗi (sharaton kenan sunan wata ƙarya🥴😬😹⛹🏻‍♀️)


          A wannan zamanma ba'a yanke hukunci ba, dan alƙali ya buƙaci ganin matayen da duk basiru ya aura a tsawon rayuwarsa.

      Wannan zance ya hargitsa hankalin Meenal, dan abinda bata taɓa saniba kenan koda a mafarkinta, ashe kafin ita Basiru yama zauna da wasu matan a matsayin rayuwar aure?.

 

      Ɓangaren Ummukulsoom kam kamar yanda ta gana da Suhailat tai mata jagoran ganinsu Lubna a wancan karon, wannan karonma Suhailat ɗin ta kuma nema, dukda kuwa tayi nauyi da cikinta tsoho haihuwa yau ko gobe, lubna kuwa harta juyo, hakama Fannah dake da biyu.

   

      Randa aka halarci zaman kotun da Ummukulsoom take fata da addu'ar ya zama na ƙarshe da ƙyar ta kawo kanta saboda rashin jin daɗin jiki, dama saida Dad ya saka baki Amaan ya bari ta baro lagos, shi bama ya ƙasar kusan sati biyu kenan, amma yaso hanata saboda yasan batajin daɗin jikinta.

      Sai da Dad yay masa magana sannan ya haƙura, amma ita kanta tasan badan yaso hakan bane, dan haka kafin su shiga kotun ta kirasa tace yamata addu'ar nasara karta shiga bada son ransa ba komai ya lalace.

    Guntun murmushi yay daga can wanda har tana jiyo sautinsa, waɗannan halayyar na Ummukulsoom ne ke ƙara masa ƙaunarta a zuciya, komanta yanada tsarinsa bisa ga bin dokokin addininta na islama, sam bata da ra'ayin jeka nayika irin na wasu matan yanzu dake jinsu kafaɗarsu dai-dai data miji, takan kalli mi addini yazo dashi bawai ra'ayin kaiba ko ƴanci.

     Cikin sanyin murya yace, “ALLAH ya bada nasara Mrs Ajiwa, in har kika samo na sara a wannan shari'ar zan miki ƙyauta mai tsoka insha ALLAHU”.

      Wani farin ciki taji ya kamata, ta lumshe ido tana sakarma wayar sumbar data saka jikin Amaan dukya saki daga can, Bily ta riƙe haɓa tana kallon ikon ALLAH, soyayyar Ummukulsoom da yaya Amaan abar birgewace da tarin sha'awa ga kowacce ƴa mace dake gidan miji, a duk lokacin da ɗaya ya ɗau zafi a cijinsu saikiga ɗayan ya kwantar dakai, basu taɓa yarda su ɗau zafi a lokaci ɗaya, wannan ne ya ƙara girmama zaman lafiya a tsakaninsu, koda saɓanin yazo saikiga yazo da sauƙi.

       Tsokalema bily ido Ummukulsoom tayi tana faɗin “Kallonfa madam?”.

      Bily da taji zafi taima Ummu dundu mara zafi a baya, “Wlhy yau badan babyna dake cikinki ba dasai na rama, muguwa kawai, duk salon muguntar yaya Amaan kin gama kwasheta.

      Dariya Ummukulsoom tayi tana ɗaukar ƙatuwar rigarta ta lauyiyi ta ɗora saman rigar abayarta oxblood, ta ɗora hular saman baby hijjab ɗin dake wuyanta, tayi ƙyau sosai, dan saida Bily tai musu hoto, suna shirin shigewa dan angama shari'ar da bayan ita za'ai tasu sukaci karo da A'i tana kuka.

     Sam A'i bata gane Ummukulsoom ba, sai ita Ummukulsoom ce ta gane A'i ɗin.

     “Wanake gani nikam kamar A'i?”.

     A'i dake share hawaye da bakin zani ta fyace bajina ta goge da gefen zaninta tana kallon wannan haɗaɗɗiyar mace dake gabanta tana mata magana, jikinta har karkarwa yake wajen ƙarema Ummukulsoom kallon tsaf.

     Murmushi Ummukulsoom tayi tana gyara tsayuwa, “A'i nayi mamaki da baki ganeniba, Ummukulsoom ce fa matar Amaan da kuka zauna a lagos tare cikin dodan Barrack”.

    A matuƙar razane A'i tayi baya, sai kuma ta zube ƙasa jiki na ɓari tana zare ido tamakar ɓarawon gwamnati a gaban efcc (naga idi kar ai farfesuna🤭😝😹⛹🏻‍♀️😂).

          “Dan ALLAH hajiya da gaske kece?”.

     Bily dake zubama A'i harara tace, “Inba ita bace zata baki wannan dogon bayanin da kikajine? Halan salon annamimancin nakine ya kawoki kotu?”.

      Kuka A'i ta fashe dashi mai ban tausayi, cikin sarƙewar halshe zata fara bayani Ummukulsoom ta kalli agogonta, “kinga A'i yimin afuwa na fito shari'arnan inhar ban takuraki ba, dan saurana minti goma kacal”.

     Mamaki ya kuma kashe A'i, anya kuwa wannan yarinyarce ƴar ƙauye da ko magana batasonyi a gabanta?, cikin rawar baki tace, “A babu komai hajiya, ai wlhy ko ca kikai nanda wata ɗaya na jiraki zan jiraki, a fito lafiya”.

    Gaba Ummukulsoom tai tana murmushi, da mamakin yanda A'i dukta lalace ta tsofe tamkar ba'itaba.


★★★★★


      Kasancewqr yau kowa ke fatan kawo ƙarshen shari'ar su basiru kotun ta cika maƙil ga duk wanda ke ƙwaɗayin ganin ƙarshenta, hatta da A'i bata bari an barta a baya ba saida ta shigo burinta kawai taga micece Ummukulsoom a wajen.

      A mamakinta saiga Ummukulsoom Buhari ɗilau na gabatar da kanta matsayin lauya mai kare wanda yay ƙara, wato Basiru.

        Tunda aka fara zaman shari'ar shi kansa Basiru sai yaune za'a kawosa kotun, saboda Alhmdllh jikinsa yayi ƙyau, zuwa yanzu yana fahimtar mi akeyi saɓanin da daya zama kamar wani dolo-dole sha giri girbau.

        Sunansa Ummukulsoom ta fara ambata a matsayin wanda zataima tambayoyi, dan haka kotu ta buƙaci ganin basiru wanda aka turo ciki wheelchair👨🏻‍🦽 ƙafarsa ɗaya a yanke saboda riɓewar datayi yana prison, dan dukan da ƴan sanda sukai masa a wancan lokacin yata cinsa, rashin gata kuma ya hana ya samu kulawa harta zama ciwo wadda ke fidda ruwa mai wari, wannan dalilinne yasa aka tsanesa a cikin jail, kowa ke ƙyankyaminsa da hantararsa, to fiddosan nan da akai likitoci sukace dole a yanketa saboda cutar ciwon suga dake a jikinsa ba'a saniba, gashi hartaci ƙarfinsa sosai. 

       Amaan ne ya biya kuɗin aikin, aka kuma gudanar cikin nasara.

    Tunda Aka shigo da basiru cikin kotun akan Ummukulsoom ya fara sauke idanunsa, koyaya Ummukulsoom ta koma fuskarta bazata taɓa ɓoye masaba, dan tunda ya barta tunaninta bai taɓa barinsaba, yana turetane kawai da ƙarfin tsiya saboda huɗubar shaiɗan limamin zuciyarsa da yayta jagorancin munanan ayyukan daya tafka.

     Yanda ya kafeta da idanu yana sharar hawaye ya saka Ummukulsoom sake haɗe fuska ta manna eyeglasess ɗinta saman ido sosai, saɓanin da data ɗan jawosa ƙarshen hanci.

    Hakan na nufin babu wasa a tattare da ita, dan haka shima saiya kama kansa ya koma kukan zuci, tunda take zuwa asibiti dubashi bata taɓa zuwa idonsa biyuba, sai bayan ya tashi a barcine talatuwa ko inna ke sanar masa Ummukulsoom tazo dubashi ta wuce, a duk sanda aka faɗa masa hakan sai yayi kuka, sai gashi a yau ya ganta a inda baiyi tunaniba, tana a matsayin mai kuɓutar dashi itada ya wulaƙanta, itace ta ceto iyayensa daga wahalar ciwo da suke ɗanɗana ta hanyar kaisu ga maganin da ubangiji ya basu waraka, Ummukulsoom da yake ganin yafi ƙarfinta saboda ɗan karatun digiri da yayi yau itace a gabansa matsayin lauya mai zamani, ta zame masa RAINA KAMA, dama masu iya magana kance CIKI DA GASKIYA wuƙa bata hudashi, shi gashi rashin gaskiyar yasa yaja wukar tai fata-fata da nashi cikin, da yanzu suna tare da ƴan yaransu abin sha'awa, jiba yanda ɗan matashin cikinta yay mata ɗas, Ummukulsoom ta zame masa *WUTSIYAR RAƘUMI* a lokacin da komai yafi ƙarfinsa hatta da ƙafafu da ƙyawun da yake takama da tinƙahon dasu.............

      A ɗan tsawace Ummukulsoom taima basiru data ga baya tare da duniyarsa magana, ya kawo numfashi a zabure yana kallonta jiki na ɓari, sassauta ɗaurewarta tayi gudun karta ruɗar dashi ta sake jeho masa tambaya da faɗin “Kasan wannan ai malam basiru?” ta ƙare maganar da nuna Suhailat............✍🏻


[3/11, 10:54 AM] ❣️Noor-ur-Rahman❣️: *_NO. 55 & 46_*



............A gajiye ta shigo cikin Barrack ɗin, dan jan motar take tamkar wata ƴar koyo, tai horn ɗaya daga sojojin dake tsaron gidan nasu ya buɗe mata gate ta shiga, tunda tai fakin idonta ya sauka akan motocin Amaan, hakan ya tabbatar mata ya dawo gidan, dan kusan kwana uku kenan yana mai-duguri.

     Da hanzari ɗaya a cikin sojojin ya zo zai karɓar ƙatuwar rigarsu ta lauyoyi data fiddo a sit ɗin baya da handbag ɗinta, kanta ta girgiza masa tana ɗan dafeshi da hannu, dan kanta ke mata ciwo saboda fafatawar da sukai yau a kotu da wani shegen lauya mai masifar naci, amma dukda haka ta nuna masa *Mai laya kiyayi mai zamani* dan an yanke hukuncin kuma tayi nasarar kwatoma yarinyar da akaima fyaɗen haƙƙinta.

      Amaan dake jikin Window yana kallonta ya fito cikin takunsa na bajinta da lafiya, yanda take tafiya kamar mara ƙashine yasa harya fito bata ƙaraso ƙofar falonba, gabanta ya tsaya yana maijin tausayin jarumar matar tasa.

     A hanki ta ɗago idanunta da sukai mata nauyi, hannu ya buɗe mata ta shige jikinsa tana sauke ajiyar zuciya, shima nannauyan numfashi ya sauke yana sumbatar kanta, jikinta ringim da zazzaɓi kuwa.

    “Sannu da zuwa Sweet Fodio na, shine baka kirani ka sanarmin zaka dawo yau ba?” Ummukulsoom ta faɗa a hankali tana ɗagowa daga jikinsa.

    Baice komaiba ya janyeta a jikinsa yana amsar kayan hannunta, itama ya kama hannun nata suka shige ciki.

      Saida suka shiga bedroom ɗinsa da suke amfani dashi ya zaunar da ita sannan yay ɗan durƙuso a gabanta yana kafeta da mayun idanunsa, “Beauty ki ɗauki hutu haka mana”.

    Fusaka ta narke masa, “Dan ALLAH Yaa Amaan kayi haƙuri kaikace haka, idan na aikata haka cases ɗin mutane fa? Ni yanzu ciwon jikine kawai ke damuna, suko jikkunansu da zukatansu duk ke ciwo, karka kalli halin dani nake ciki dazai zama naɗan lokaci, ka kalli su yanda suka tsinci kayinsu”.

     Numfashi ya sauke yana mikewa, kusa da ita ya koma ya zauna ya jata jikinsa ya rungume, hawayen da take maƙalewa tuni sun fara gudu a fuskarta, bai hanata ba, baikuma ce mata komaiba, sai bayanta da yake ɗan bugawa kaɗan-kaɗan, saida tayi mai yawa sannan ya ɗagata ya cire mata kayan jikinta, da kansa yay mata wanka, ta ɗauro alwala suka fito.

     Tunda cikin ya bayyana bata iya girki, dan ko tayi bata iya ci, Amaan kuma ba zama sosai yake a gidaba, tafiye-tafiyansa yayi yawa, hakan yasa Maman Ahmad ta juri kawo musu a kowanne lokaci, yau ɗinma itace ta aiko ma Amaan abinci.

      Fita Ummukulsoom tai zuwa kicin ta haɗo musu fruit salad, dan tafi ƙaunar shansa fiye da komai, saiko tuwon Amala ko na dawa, a cikin firij ɗin dani ta saka ta wuce ɗaki danta gabatar da sallar la'asar, dan Amaan ma ya fita sallar.


★★★★


      Yanda take shan fruit salad ɗin hannu baka hannu ƙwaryane ya saka Amaan kallonta cike da tausayawa, ya amshi spoon ɗin yaci gaba da bata da kansa yana faɗin, “Beauty yunwa kikeji, amma bazakiji abinci ba sai baƙin tuwo, ni wannan Friendy n nawa bansan da wane salo tazo ko yazo ba” yay maganar hannunsa akan cikinta daya fara tasowa.

     Murmushi kawai tai masa ta zare cokalin tana cigaba da shan kayanta ganin yana ɓata mata lokaci.

        “Sweet Fodio kasan wane tunani nakeyi kuwa akan zancennan na basiru?”.

        Kallonta yay ba tare daya amsaba, amma hakan yana nufin hankalinsa na a kanta. Ta haɗiye abinda ke bakinta tana kuma dai-daita murya, “inaga ya kamata mu fidda maganarnan duniya ta sani, mutumin nan ɗan siyasa ne, bazaiso sunansa ya ɓaciba, da yaji zancen zai karaɗe duniya zai fara ƙokarin binne case ɗin, mukuma ta wanna hanyarne zamu kamashi dumu-dumu”.

      Kansa ya shiga jinjina mata idonsa kafe a kanta, tabbas ya aminta da zancenta, dan abubuwansu na kamanceceniya da juna musamman ta fannin bincike. Ganin ya fahimceta saita ƙara faɗaɗa masa bayani akan shirinta, a daren ranar kuwa suka saki bayanai ta hanyar wani abokin Amaan baban ɗan jarida dake da gidan tv nasa na kansa.

       A safiyar washe gari kuwa labari ya fara fita



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


         Hankali tashe Meenal da taci karo da zancen a social network ta samu mom nasu, dan matakin farko dasu Ummukulsoom suka fara bi kenan, sanin mafi yawan al'umma sun raja'a da social network yanzu, a take Momin su Meenal ta kira dadinsu dake can yana fafutukarsa ta ƴan siyasa, dan an kadashi ne a wannan zaɓen bayan ya kammala shekara huɗunsa, zuwa yanzu kuma soyake ayi hannun karɓa tsakaninsa da gwamnan daya kadashi bayan ya gama burin yin shekara takwas, daganan ya fito takarar shugaban ƙasa.

     Lamarin ya girgizashi, a take ya nema wani alƙali amininsa akan ayi duk yanda za'ayi case ɗin basiru ya canja salo zuwa wani abun daban, dan shifa har zuwa yanzu bai taɓajin zai yafema basiru ba saboda dukan da yayma meenal wanda ya barmata ƙaton tabo a fuska da duk sanda suka gani sai sun tuna da abinda yayi.

      Dama idonsu Ummukulsoom akansa suke, dan haka sukai amfani da wannan damar wajen yima baba mahaifin basiru jagora ya shigar da ƙara a wata babbar kotu dake nan kaduna da taimakon Abba da Dad.

       A daren ranar aka miƙama mahaifin Meenal sammaci daga kotu, sannan aka saka police binciko dukkan prison dake cikin katsina neman basiru.

          Har dai washe gari babu wani labari dangane da samun basiru, sai da akabi wasu manyan matakai kafin ai nasarar ganosa cikin gaggan ɓarayi, a yanda shirin mahaifin Meenal yakema saura kwana ɗaya kacal a kashe su basiru.

       A yanayin da aka ɗakko basiru daga jail abun babu daɗin gani, dan dolema aka zarce dashi asibiti daga nan, ashe dukan tsiya yaci hannun gayun da suke tare a daren jiya.

     Su Ummukulsoom suna lagos aka sanar musu da samunshi, dayake dukkan komai hannun Abba da Dad ya koma, dan hakama Abba yace Ummukulsoom tabar maganar shiga case ɗin a nemi kwararren lauya daya daɗe a aiki, amma sai Ummukulsoom taita roƙonsu akan zata iya.

     Ummi ce ta bada shawarar su barta kowa ya bita da addu'ar samun nasara, kar a sare mata gwiwa.

       Inna da baba sosai hankalinsu ya kara tashi ganin yanda ɗansu ya koma, ko mai fama da ciwon HIV iyakar lalacewar da zaiyi kenan, banda ƙwala-ƙwalan idanu babu abinda kake gani a jikin basiru, ya rame iyakar ramewa, fuskarsa kam tayi baƙi duk ya koje tayi tabbuna na raunikan duka saikace wani tsohon ɗan daba, ga wasu ƙuraje da duk suka bata masa jiki harma fuskar masu shegen wari dan ƙazanta, duk mai imani ya gansa saiya tausaya masa.

      Kwana biyu da samo basiru Ummukulsoom da Amaan da Attahir harma da a maman Ahmad suka dira kd da daddare, dan washe garine za'a fara shiga shari'ar su basiru.

      Kallo ɗaya Ummukulsoom ta iyama basiru dake barcin wahala ta fito abinta, jarumta sosai ta nuna wajen danne kukanta dan kar zuciyar Amaan ta sosu saboda kishinsa data gama fahimta akan lamarin, dukda da yarjewarsa take komai hakan bai hanashi yawan nuna ɓacin ransa ba idan ya ga ta cika yawan magana akan case ɗin, dan haka saita iya takunta, dan ita harga ALLAH bada wata manufa take hakanba, sam babu wata soyayyar basiru a ranta tun shekarun da suka shuɗe kafinma tasan kanta, tausayin iyayensa ne kawai ya jagoranci damuwarta akan lamarin.

           

★★★★★★


         Duk da ta tashi babu jin daɗin jiki haka ta nuna jarumtarta wajen dannewa aka shiga kotun, a wannan zaman maida kanta sakara tayi a kotun, lauyan da ke kare baban Meenal yanata murna akan ashema shashasha suka samo, danshi kam gaba ɗaya ya rainama Ummukulsoom wayau akan shari'ar, gashi dama a haife zai iya haifarta, danshi shirinma ritaya yakeyi nan kusa kaɗan.

      Jikin su Abba saiya fara sanyi akan yanda Ummu ta nuna sanya a kotu, shiko Amaan dama baima halarci shari'ar ba sam, sai Attahir ne kawai yaje.

          Ummukulsoom guduwa tayi, dan kar kowa yay mata maganar abinda tayi a kotu, dan ita tasan minene a ranta, batason kowa ya shigar mata aiki koda Amaan ne kuwa.

      Dad ne yake sanarma Amaan abinda ya faru a kotu yau, Amaan yay shiru yana nazari, har Dad ma yazata bazai samu amsa ba sai yaga ya nisa yana gyara zama, “Karku damu Dad, kubita a haka kawai, dan Ummukulsoom nada matuƙar wayo, karku ɗauka dan bata jima da fara aiki bane bata gama kwarewa ba, ni nasan tanada dalilin bama wancan lauyan damane, kuma zakace nina faɗa maka”.

      Kai Dad ya jinjina cike da gamsuwa da zancen ɗan nasa. Koda Amaan ya dawo sashensu baima Ummukulsoom maganarba, yama isketa har tayi barcin ta, shima kwanciya yay gefenta bayan yay shirin nasa barcin, ya daɗe yana kallonta tare da shafar cikinta kamar yanda ya saba a kowanne dare har barci ya ɗaukesa.


        Alƙali yabada damar jami'an tsaro su cigaba da tsare basiru, kuma Ummukulsoom ce ta bada wannan damar ta hanyar maida kanta sakara datai a kotu, lauyansu Meenal ya bada hujjoji masu karfi akan kisan kai Basiru ya aikata. Tayi hakanne saboda basiru ya samu tsaro, duk kuma abinda ya samesa a halin yanzu mahaifin Meenal za'a zarga kai tsaye. Shi kansa lauyan su Meenal saida aka fito ya harbo jirgin Ummukulsoom, dan haka hankalinsa ya tashi, wato wanan yarinyar shegen wayone da ita. Sam kasa barci yay a daren, yanata ƙulla dabaru na gaba ta yanda zai bada damar korar ƙarar ma.

     Itako Ummukulsoom da kowa ke ganin bazata iya komaiba bayan  Amaan da yay mata ƙyaƙyƙyawar fahimta barcinta ta kwasa hankali kwance harda munshari, (yo tasan ta gama fafe gorarta harda tanajin murfi, to mizai gagareta aranar tafiya? Idan ance ta fito🤷🏻‍♀️).

         Washe garima tunda safe ta fita a gidan, bata dawoba sai kusan 11, harma Momcy ta rufeta da faɗa saboda ko breakfast batayi ba ta fita, aiko itace da kanta ta zaunar da ita ta bata abinci, sai da taci ta ƙoshi sannan Momcy ta barta, shi dai Amaan yana zaune a falon yana jinsu da kallonsu amma uffan bai ceba, sai dai harga ALLAH sun birgesa, yanda kowa ke nuna kulawarsa ga matarsa yana tsintar kansa a farin ciki sosai.

       A ranar da daddare suka koma lagos, sai lokacin da aka ɗibarma shari'ar yayi zasu dawo.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


         Dad nidai da zakuji shawarata wlhy da kun janye batun kisannan da kuka ƙaƙabama basiru, gara ku fiddo gaskiyar maganar abinda ya faru ayi shari'ar nan a kansa, ina tsoron karfa shari'arnan ta canja salo muzo mu afka ciki........”

      “K dalla rufema mutane baki, ke mi kika sani ne? Duk ma abinda ya faru ba kece kika jama mutane ba, inda baki kawo ɗan matsiyatan nan ba a matsayin mijin aure har wannan abun ya farune?”.

     Baki Meenal ta zunɓura tana matsawa daga kusa da yayanta daya katseta a tsawace tamkar zai maketa.

     Shiru falon yayi, sai gungunin Meenal kawai, shima bawani fita yakeyiba.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


      Ɓangaren su Suhailat kam sunji komai daga bakin meenal, sai dai suma fa ba haka sukaso lamarin ya kasanceba dan basuso Abban Meenal ya juya zancen zuwa wai kisankai Basiru yayiba, a ganinsu gamma ai shari'a akan abinda ya akata musu a zahiri bawai a sakko wani zance daban ba da sam babushi a tafiyar, hakan tamkar zalintar basirunne kuma. Amma abinda suka sani koma dai miza'ayi gaskiyar zance zai fita suma har a nemosu.



*_BAYAN SATI HUƊU_*

  

             Bayan sati huɗu aka sake zama shari'ar basiru, sai dai fa a wannan karon salon Ummukulsoom ya bama kowa tsoro, musamman data kawo zancen auren Meenal da basiru, dan saida ta gama bincike tsaf akan dukkan aure-auren da basiru yayi hatta da abokansa su Najeeb.

     Ta nemi alfarmar alƙali na ganin Meenal, hakan yasa Meenal tasowa ta tsaya inda ake tsayawa. Wasu irin tambayoyi masu ruɗa tunani Ummukulsoom takema Meenal, har lauyansu yay magana, amma kasancewar tambayoyin Ummukulsoom nakan tsari sai alƙali bai karɓi ƙorafinsa ba aka bama Ummukulsoom damar cigaba da yima Meenal tambayoyi.

       Meenal fa ganin za'a ƙureta saita zurma bisa ga ƙafa da Ummukulsoom ta bata nayin talala a tambayar data jefa mata ta ƙarshe.

      Gyan-gyan gyan gyan, zancen Meenal fa ya tabbata, dan shari'a ta canja salo, cikin hikima da dabaru na Ummukulsoom ta dawo da shari'ar ainahin kan hanya na batun dukanta da basiru yayi, bawai batun kisan kai da akace yayi a farko ba.


★★★★★★


      A can ɗilau kuwa labari nata yawo cewar Ummukulsoom tazama alƙaliya🤭🤣, wai itace kema basiru shari'a bayan mijinta ya ƙwatoshi hannun ƴan shan jini, shima basirun ashe ɗan shan jini ya zama shiyyasa yay kuɗi yaketa auren ƴaƴan masu kuɗi (sharaton kenan sunan wata ƙarya🥴😬😹⛹🏻‍♀️)


          A wannan zamanma ba'a yanke hukunci ba, dan alƙali ya buƙaci ganin matayen da duk basiru ya aura a tsawon rayuwarsa.

      Wannan zance ya hargitsa hankalin Meenal, dan abinda bata taɓa saniba kenan koda a mafarkinta, ashe kafin ita Basiru yama zauna da wasu matan a matsayin rayuwar aure?.

 

      Ɓangaren Ummukulsoom kam kamar yanda ta gana da Suhailat tai mata jagoran ganinsu Lubna a wancan karon, wannan karonma Suhailat ɗin ta kuma nema, dukda kuwa tayi nauyi da cikinta tsoho haihuwa yau ko gobe, lubna kuwa harta juyo, hakama Fannah dake da biyu.

   

      Randa aka halarci zaman kotun da Ummukulsoom take fata da addu'ar ya zama na ƙarshe da ƙyar ta kawo kanta saboda rashin jin daɗin jiki, dama saida Dad ya saka baki Amaan ya bari ta baro lagos, shi bama ya ƙasar kusan sati biyu kenan, amma yaso hanata saboda yasan batajin daɗin jikinta.

      Sai da Dad yay masa magana sannan ya haƙura, amma ita kanta tasan badan yaso hakan bane, dan haka kafin su shiga kotun ta kirasa tace yamata addu'ar nasara karta shiga bada son ransa ba komai ya lalace.

    Guntun murmushi yay daga can wanda har tana jiyo sautinsa, waɗannan halayyar na Ummukulsoom ne ke ƙara masa ƙaunarta a zuciya, komanta yanada tsarinsa bisa ga bin dokokin addininta na islama, sam bata da ra'ayin jeka nayika irin na wasu matan yanzu dake jinsu kafaɗarsu dai-dai data miji, takan kalli mi addini yazo dashi bawai ra'ayin kaiba ko ƴanci.

     Cikin sanyin murya yace, “ALLAH ya bada nasara Mrs Ajiwa, in har kika samo na sara a wannan shari'ar zan miki ƙyauta mai tsoka insha ALLAHU”.

      Wani farin ciki taji ya kamata, ta lumshe ido tana sakarma wayar sumbar data saka jikin Amaan dukya saki daga can, Bily ta riƙe haɓa tana kallon ikon ALLAH, soyayyar Ummukulsoom da yaya Amaan abar birgewace da tarin sha'awa ga kowacce ƴa mace dake gidan miji, a duk lokacin da ɗaya ya ɗau zafi a cijinsu saikiga ɗayan ya kwantar dakai, basu taɓa yarda su ɗau zafi a lokaci ɗaya, wannan ne ya ƙara girmama zaman lafiya a tsakaninsu, koda saɓanin yazo saikiga yazo da sauƙi.

       Tsokalema bily ido Ummukulsoom tayi tana faɗin “Kallonfa madam?”.

      Bily da taji zafi taima Ummu dundu mara zafi a baya, “Wlhy yau badan babyna dake cikinki ba dasai na rama, muguwa kawai, duk salon muguntar yaya Amaan kin gama kwasheta.

      Dariya Ummukulsoom tayi tana ɗaukar ƙatuwar rigarta ta lauyiyi ta ɗora saman rigar abayarta oxblood, ta ɗora hular saman baby hijjab ɗin dake wuyanta, tayi ƙyau sosai, dan saida Bily tai musu hoto, suna shirin shigewa dan angama shari'ar da bayan ita za'ai tasu sukaci karo da A'i tana kuka.

     Sam A'i bata gane Ummukulsoom ba, sai ita Ummukulsoom ce ta gane A'i ɗin.

     “Wanake gani nikam kamar A'i?”.

     A'i dake share hawaye da bakin zani ta fyace bajina ta goge da gefen zaninta tana kallon wannan haɗaɗɗiyar mace dake gabanta tana mata magana, jikinta har karkarwa yake wajen ƙarema Ummukulsoom kallon tsaf.

     Murmushi Ummukulsoom tayi tana gyara tsayuwa, “A'i nayi mamaki da baki ganeniba, Ummukulsoom ce fa matar Amaan da kuka zauna a lagos tare cikin dodan Barrack”.

    A matuƙar razane A'i tayi baya, sai kuma ta zube ƙasa jiki na ɓari tana zare ido tamakar ɓarawon gwamnati a gaban efcc (naga idi kar ai farfesuna🤭😝😹⛹🏻‍♀️😂).

          “Dan ALLAH hajiya da gaske kece?”.

     Bily dake zubama A'i harara tace, “Inba ita bace zata baki wannan dogon bayanin da kikajine? Halan salon annamimancin nakine ya kawoki kotu?”.

      Kuka A'i ta fashe dashi mai ban tausayi, cikin sarƙewar halshe zata fara bayani Ummukulsoom ta kalli agogonta, “kinga A'i yimin afuwa na fito shari'arnan inhar ban takuraki ba, dan saurana minti goma kacal”.

     Mamaki ya kuma kashe A'i, anya kuwa wannan yarinyarce ƴar ƙauye da ko magana batasonyi a gabanta?, cikin rawar baki tace, “A babu komai hajiya, ai wlhy ko ca kikai nanda wata ɗaya na jiraki zan jiraki, a fito lafiya”.

    Gaba Ummukulsoom tai tana murmushi, da mamakin yanda A'i dukta lalace ta tsofe tamkar ba'itaba.


★★★★★


      Kasancewqr yau kowa ke fatan kawo ƙarshen shari'ar su basiru kotun ta cika maƙil ga duk wanda ke ƙwaɗayin ganin ƙarshenta, hatta da A'i bata bari an barta a baya ba saida ta shigo burinta kawai taga micece Ummukulsoom a wajen.

      A mamakinta saiga Ummukulsoom Buhari ɗilau na gabatar da kanta matsayin lauya mai kare wanda yay ƙara, wato Basiru.

        Tunda aka fara zaman shari'ar shi kansa Basiru sai yaune za'a kawosa kotun, saboda Alhmdllh jikinsa yayi ƙyau, zuwa yanzu yana fahimtar mi akeyi saɓanin da daya zama kamar wani dolo-dole sha giri girbau.

        Sunansa Ummukulsoom ta fara ambata a matsayin wanda zataima tambayoyi, dan haka kotu ta buƙaci ganin basiru wanda aka turo ciki wheelchair👨🏻‍🦽 ƙafarsa ɗaya a yanke saboda riɓewar datayi yana prison, dan dukan da ƴan sanda sukai masa a wancan lokacin yata cinsa, rashin gata kuma ya hana ya samu kulawa harta zama ciwo wadda ke fidda ruwa mai wari, wannan dalilinne yasa aka tsanesa a cikin jail, kowa ke ƙyankyaminsa da hantararsa, to fiddosan nan da akai likitoci sukace dole a yanketa saboda cutar ciwon suga dake a jikinsa ba'a saniba, gashi hartaci ƙarfinsa sosai. 

       Amaan ne ya biya kuɗin aikin, aka kuma gudanar cikin nasara.

    Tunda Aka shigo da basiru cikin kotun akan Ummukulsoom ya fara sauke idanunsa, koyaya Ummukulsoom ta koma fuskarta bazata taɓa ɓoye masaba, dan tunda ya barta tunaninta bai taɓa barinsaba, yana turetane kawai da ƙarfin tsiya saboda huɗubar shaiɗan limamin zuciyarsa da yayta jagorancin munanan ayyukan daya tafka.

     Yanda ya kafeta da idanu yana sharar hawaye ya saka Ummukulsoom sake haɗe fuska ta manna eyeglasess ɗinta saman ido sosai, saɓanin da data ɗan jawosa ƙarshen hanci.

    Hakan na nufin babu wasa a tattare da ita, dan haka shima saiya kama kansa ya koma kukan zuci, tunda take zuwa asibiti dubashi bata taɓa zuwa idonsa biyuba, sai bayan ya tashi a barcine talatuwa ko inna ke sanar masa Ummukulsoom tazo dubashi ta wuce, a duk sanda aka faɗa masa hakan sai yayi kuka, sai gashi a yau ya ganta a inda baiyi tunaniba, tana a matsayin mai kuɓutar dashi itada ya wulaƙanta, itace ta ceto iyayensa daga wahalar ciwo da suke ɗanɗana ta hanyar kaisu ga maganin da ubangiji ya basu waraka, Ummukulsoom da yake ganin yafi ƙarfinta saboda ɗan karatun digiri da yayi yau itace a gabansa matsayin lauya mai zamani, ta zame masa RAINA KAMA, dama masu iya magana kance CIKI DA GASKIYA wuƙa bata hudashi, shi gashi rashin gaskiyar yasa yaja wukar tai fata-fata da nashi cikin, da yanzu suna tare da ƴan yaransu abin sha'awa, jiba yanda ɗan matashin cikinta yay mata ɗas, Ummukulsoom ta zame masa *WUTSIYAR RAƘUMI* a lokacin da komai yafi ƙarfinsa hatta da ƙafafu da ƙyawun da yake takama da tinƙahon dasu.............

      A ɗan tsawace Ummukulsoom taima basiru data ga baya tare da duniyarsa magana, ya kawo numfashi a zabure yana kallonta jiki na ɓari, sassauta ɗaurewarta tayi gudun karta ruɗar dashi ta sake jeho masa tambaya da faɗin “Kasan wannan ai malam basiru?” ta ƙare maganar da nuna Suhailat............✍🏻

[3/11, 10:54 AM] ❣️Noor-ur-Rahman❣️: *_NO. 57 & 58_*



...........Kai basiru ya ɗaga  zuciyarsa na hantsilawa saboda ganin Suhailat dake tsaye a ɗayan a kwatin tamkar an kara mata ƙyau duk da tsohon cikin dake jikinta.

      “Magana zakai da bakinka malam basiru, dan hakanne zai fiddaka daga zargin kisan kai da ake maka” Ummukulsoom ta faɗa tana bashi dukkan ƙwarin gwiwa.

    Hakanne yasaka lauyan su meenal yay ƙorafi akai, “Ya mai shari'a lauyan mai ƙara kamar tana faɗa masa yanda zaiyine ba tambaya take masa ba”.

    Alƙali yayma Ummukulsoom gargaɗi akan ta gyara salon yanda takema Basiru tambaya.

    Amsawa tayi cikin risinawa ta sake maida hankalinta gareshi.

     Cikin rawar baki basiru yace, “Eh na santa, itace matar dana fara aure, daga baya kuma sai muka rabu”.

       “ALLAH sarki, to malam basiru bayan ita Suhailat ka ƙara wani auren kafin Meenal ne?”.

      Shiru Basiru ya kasa amsawa, sai hawaye dake zirara a kumatunsa, wani irin kunyar Ummu yakeji da nauyinta....

     Ummukulsoom ta sake mai-maita masa tambayar yayinda take taku a hankali cikin kotun. 

     “Malam basiru kai muke saurare fa”.

    Sake daurewa basiru yayi ya shiga zayyano bayanin aurensa da Lubna, harma da Fannah kafin ya rabu dasu ya auri meenal. Kotu tayi tsit kowa na saurarensa, al'ajabi ya cika iyayensa da talatuwa, su dai duk basusan yayi wannan aure-auren ba, lallai lamarin basiru sai addu'a kawai.

     Bayan yakai aya ne har inda faɗa ya haɗasa da Meenal aka kaisa jail ya kuma sharce hawaye.

        Ummukulsoom ma numfashi ta sauke tana jinjina kai da kallon alƙali, “Yamai girma mai shari'a wannan shine gaskiya lamari daya faru har basiru ya tsinci kansa a prison, dan inada shaidu kwarara akan hakan da tabbatar da gaskiyar maganarsa, kaf matan da basiru ya aura suna nan, kuma sun tabbatar min da sune suka ɗanama basiru tarko tsakaninsa da meenal, badan komaiba sai dan su rama abinda yay musu”.

    Alƙali dake kallon Ummukulsoom yana wasa da pen akan hancinsa yaja numfashi, tare da sunkuy da kansa yay ɗan rubutu ya ɗago yana bada umarnin bayyanar matan basirun duka.

       Suhailat dama ta fito, dan haka itama lubna ta fito itada Fannah, mamaki al'ajab ya gama kashe Meenal, sam bata taɓa kawo hakan a ranta ba koda da wasa akan su Lubna.

      Tambayoyi aka shiga musu suna bada amsa tamkar yanda basiru ya faɗa, suka kuma tabbatarma kotu sune suka kafama Basiru tarko ya afka, badan komaiba sai dan gujema Meenal shiga irin halin da suma suka shiga ta dalilinsa da matan da zai iya yaudara a bayanta, idanun basiru sunyi tsiru-tsiru, sai hawaye da yake malalarwa yana kallon ɗiyarsa ta wajen Lubna. alƙali ya gamsu da dukkan bayanan da suka gudana, ya kuma wanke basiru daga zargin kisan kai da ake masa, wahalar da yasha na zaman jail kusan shekara uku ba tare da an yanke masa hukunciba ne yasa ya samu sassauci daga kotu, zaije gida ya cigaba da jiyya, sai tara da zai biya su Suhailat, tare da maida dukiyar maharfin Suhailat da yaci, da kuma biyan dukkan kuɗaɗen da aka lura da ƴarsa tun daga goyonta har kawo yanzu data zama ƴar babba kusan shekara takwas.

          Kuɗin dake accaunt ɗin basiru aka kwaso, basukai adadin abinda ake buƙata ba, dan haka Abba da Dad suka cika, sai dai Lubna tace ta yafe na rainon Amal, amma har abada babu ruwansa da Amal, yasa a ransa bai taɓa haihuwa ba, kuka mai cin zuciya basiru ya saki, wanda ya sanyaya jikin mutane da dama a wajen, son zuciya dama ai ɓacin zuciyane.

     Basu bar kotunba sai da aka bama kowa haƙƙinsa, ya saki meenal daketa tsine masa da jifansa da kalmar ALLAH ya isa, yayyen Suhailat kansu badan sunga ruwa ya ƙarema basiru ba da saisun wajiga rayuwarsa, amma yanzu a cewarsu sun barsa da sakamakon daya samu daga ALLAH.

     Haka suka wuce ɗilau inna da baba da talatuwa sunata sharar ƙwalla, Zaid ne ya kaisu har gida. Ummukulsoom kam gida suka wuce da A'i data maƙale musu, da Bily harta hana aje da ita sai da Ummukulsoom ta lallaɓeta.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡

     

        A'i kuka take sosai da shartar hawaye tana gurfane gaban Ummukulsoom da duk tausayinta ya kamata, dan azahirin gaskiya A'i ta kuma tsufa da fita hayyacinta, saikace ba itaba.

     “Ki gafarta mini uwar ɗakina, na kasance azzaluma wadda ta jagoranci mutuwar aurenki, wlhy sam mijinki bashi da laifin komai akan sakinki, dan kuwa dai harda asiri a lamarin, saboda mahaifiyarsa tayi-tayi ya sakeki yanata mata yawo da hankali saboda baison saɓama mahaifinsa, ni ce na bata shawara akan ta bishi ta ƙasa kawai, dan maganar da take masa bata da amfani, munyi haka da kwana biyu saiga yarinyarnan data taɓa zuwa gidan harya doketa  tazo (Bukky) kuɗi ta bani naira dubu ɗari akan na saka wani abu a gadonki, wannan abun kuma irin mugun asirin nan nasu ne na yarabawa, wanda idan har sukai maka ikon ALLAH ne kawai zaisa ka dawo dai-dai. niko na amince mata zan saka saboda ganin waɗannan maƙudan kuɗi, a yanda taimin bayanin asirin dama sai yallaɓai ya fara sakinki sannan, daga nan asirin zai fara tasiri, dan ance inhar kina gidansa ko wani daya shafesa to bazai aikin komai a jikinki ba. Kina wanka na lallaɓa na saka miki wannan abu a ƙasan gado kamar yanda ta umarceni, sannan na saka wanda shi maigidanki zai taka, bisa tsautsayi kuwa ina gama sakawa ya shigo gidan, daga nan kuma ne na kira mahaifiyarsa na sake tunzurata itama ta kirashi ta tunzurasa da barazanar koya sakeki kota tsine masa. Munso kafin ya sakeki yaci mutuncinki sosai, sai dai hakan bai kasanceba, magana kaɗan ya faɗa miki wadda ni a wajena bata gamsu ta zafi ba, nifa dukkan wannan abu da nakeyi burina shine ɗiyata Aina'u ta shigo gida ta auri yallaɓai bayan k kin fita, sai kuma hakan bata faruba, dan asirin da akai miki ALLAH ya taƙaita miki wahala kika zauna wajen babban Aminin mijinki Attahir, asirin jikin yallaɓai sai baiyi wani tasiriba yabar jikinsa cikin kwanaki uku kacal da rabuwarku, shinefa ya biyo sawunmu nan kaduna, kai tsaye niya tunkara, ya titsiyeni saina faɗa masa gaskiya, niko na dage babu komai, aiko aranar ya saceni daga gidansu aka koma dani lagos, Wlhy Uwar ɗakina nasha wahala hannun mijinnan naki, saida nayi dana sanin zuwana duniya, a take na zayyane masa komai harda amincewar mahaifiyarsa, itama Bukku take ko wa? Aranar aka kawota inda nake, tare yayta hajijiya da rayuwarmu saida mukai tiɓis ya maidata gidansu tare da gargaɗin da mahaifinta ya tabbatar idan yallaɓai yay wani motsi komai nasa ya rushe, shinefa yasa basu ɗau matakin komaiba, nima ya maidoni gida can ƙauyenmu, yajamin dogon gargaɗi akan inhar ya sake ganin kafata a kaduna nasan sauran, wannan yasa ban sake zuwa ba sai wannan ganin da kikaimin, shima ƴata Aina'u ce kishiyarta ta ƙonata da ruwan zafi shine ake shari'a, anma yankema kishiyar hukunci. Naga rayuwa uwarɗakina, wadda nasan ko alhakinki ya isa hanani zaman lafiya, dan ALLAH ki gafarceni, a kullum dake nake kwana nake tashi, dan duk muguntar da nai miki saita dinga dawowa kan Aina'u........”

     “Ai hakan shine dai-dai tsohuwar banza kawai”. Aziza ta faɗa tana harar A'i.

      A'i ta kuma fashewa da kuka tana sake sabon gurfane a gaban Ummukulsoom dasu Aziza. Da sauri Ummukulsoom ta dakatar da ita tana faɗin, “Nikam baba na yafe miki, ALLAH ya yafe mana baki ɗaya, idanma ban yafe mikiba ashe ban godema ALLAH tarin ni'imomin da yayminba kenan, tunda gashi sanadin rabamun naga dangin mahaifiyata, na koma makaranta nasamu ilimin da yake amfanar al'umma, daga ƙarshe na koma gidan mijina, iyayensa da ƴan uwansa suna sona, nazama *Wutsiyar raƙumi* ga wanda yay min butulci da ahalina dama ƙauyenmu gaba ɗaya, A'i bake ba dukkan wanda yay min wani abu a yau ni Ummukulsoom buhari na yafe masa, nima ALLAH ya yafe mini nawa kura-kuran”.

      “Ameen ya rabbi” su Bily suka haɗa baki wajen faɗa har Ummi dasu hajiya yaya, yayinda itama A'i taketa zuba godiya tana share hawaye da bakin zani.


      Koda A'i taci ta ƙoshi sai su Ummukulsoom suka bita asibiti inda Aina'u ke jiyya, dukda tama fara warkewa abin babu ƙyan gani, su Ummukulsoom duk saida sukai hawayen tausayi, sunma A'i alkairi suka tafi, Ummukulsoom ta bata Number ta akan konan gaba wani abu ya taso ta nemeta zata taimaketa da ita abinda ALLAH ya ni'imtata dashi itama.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


       Basiru ya zama abin kallo da kwatance a ƙauyen ɗilau da kewaye, har niƙo gari ake zuwa kallonsa daga maƙwaftan ƙauyikan ɗilau, yayinda ƴammata suka haɗa masa waƙa a dandali, wadda tuni ta shige bakunan yara da samari, wani lokacinma da biyu ake zuwa jikin dannin gidansu ana rairawa, kokiji mata nayi cikin liguden daka.

    Ƙiri-ƙiri fitowa koda ƙofar gida a ƴar wheelchair ɗinsa ta gagaresa, wasiƙar da Ummukulsoom tai masa randa za'a wuce da ita gidan Amaan itace ta zame masa abar karantawa safe da yamma yana kuka, yanzunma yana daga jikin bishiyar dalbejiyar dake tsakar gidansu saboda zafin da akeyi, zaune yake akan tabarma da ƙafarsa ɗaya da rabi, ya jingina da bishiyar yana karanta takardar, murmushi da hawaye na fita daga garesa a lokaci ɗaya.


      *_Assalamu alaika_*

  _Nasan a lokacin da wannan takardar zata iso gareka babu komai a ranka sai ƙarin tsanata Basiru, banga laifinka ba, dan kuɗi sunsha juya zukatan al'ummar duniya, sun kawo saɓani a tsakanin abokai, sun kawo saɓani a tsakanin ma'aurata, sun kawo tsakanin iyaye da ƴaƴa, sun kawo tsakanin masoya tamkar yanda suka zama sanadi a tsakanina da kai, koban faɗaba a yanzu nasan akwai ranar dana sani daga gareka, dan kayi kuskuren yarda duniya ta aureka iyayenka na fushi dakai, wannan shine kawai babbar damuwata, dan ALLAH basiru kafin ka auri wadda kakeso yanzu, ina roƙonka ka sasanta kanka da iyayenka, wannan kaɗaine zai zame maka hasken cin duniya hankali kwance, na manta dakai har abada, koda kuwa sonka zai zama ajalina, sai dai kai inason karka manta dani har ƙarshen rayuwarka, wannan halaccin kawai kaimin ya wadatar dani._


        Talatuwa ta zare takardar tausayin ɗan uwanta na sake ratsata, wannan takarda ta Ummukulsoom ta zame masa tamkar wani karatun salla, tanada tabbacin harya gama haddaceta ma. Zama tai tana lallashinsa da bashi baki akan yakamata ya saki ransa zuwa yanzu, ya fiskanci yau ɗinsa, dan kuwa jiyansa ta wuce bisa rubutaccen alƙalamin ƙaddara da babu hannun dake gogewa, a yau ɗinsa yake, wadda tazo masa da sakamakon bashi damar duƙufa neman gafarar ALLAH da iyayensu domin yaga ƙyaƙykyawan sakamako a gobensa a duniyarsa da lahirarsa.


⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


           Kamar yanda Amaan ya alƙawarta yana dawowa ya biyo kd suka wuce da Ummukulsoom, ya dankara mata kyauta mai tsoka irin ta masoya, dan taci nasara kamar yanda yay fata, iyayensu nata sanya mata albarka, sannan ta kara daraja da kima a idon mutane.

     Haka rayuwar taci gaba da shurawa Ummukulsoom na jan cikinta da cigaba da aiki, yayinda busy yaketa ƙaruwa ga Amaan, lokacin da cikinta ya tsufa dole ta koma gidan Attahir da zama kusa da maman Ahmad, idan kaga taje gidanta to Amaan yana a gari. 

        Yana tafiya kuma zata koma can, dukkan wani tattali dai tana samunsa daga maman Ahmad, sai da cikinta ya ƙara tsufane Momcy tazo har lagos da kanta ta ɗauki abarta suka koma kd, dan tagaji da yawo da hankakin da Amaan ke mata.

     Kowa tausayin Ummukulsoom yake a gidan da tattalinta, hatta da Ameer da ayanzu ya maidata abokiyar shawararsa, kuma Aunty sama aunty ƙasa, ita dasu Aneesa kuwa ai bama ajin kansu, kowane motsinsu aunty Ummukulsoom, idan suna son abu a hannun Amaan ta hannunta sukebi, idanma taga babu yawa saita musu ba tare da takai masa kukanba, sai dai yaji suna masa godiya ba tare da yasan akanmi ba, daga bayane yake fahimtar abinda Ummukulsoom takeyine da sunansa ashe. Rasa mima zai mata ya nuna jin daɗinsa yayi, dan aganinsa magana da fatar baki bazatayi ba saidai yayta mata addu'ar gamawa da rayuwa lafiya har ƙarshen numfashinsa.

        Kwanan Ummukulsoom huɗu a gidan ta tashi da nakuda a safiyar alhamis, babu bata lokaci sukai asibiti da ita, tasha wahala kafin ALLAH ya sauketa lafiya ta sunkuto ƴarta mace mai kama da ita tamkar tayi kaki ta tofar.

      Faɗa muku farin cikin da wannan ahali suka tsinci kansu ɓata lokacine, tun a wannan ranar zancen haihuwar ya isa ɗilau.

    Kasancewar baby da maijego lafiya aka tarkatosu zuwa gida, dan Momcy ta kafa ta tsare Ummukulsoom na kusa da ita.

       A ranar da yamma shima Amaan ya isa garin, daga Cameroon yake, duk rashin fara'arsa ranar saida jama'a da yawa suka gane yana tare da farin ciki na musamman.

         

★★★★★★


       Yana zaune gefen Ummukulsoom dake kwance a kan gadon Momcy ya rungume ƴarsa a ƙirji idanunsa lumshe, shi kaɗai yasan abinda yakeji a ransa, yau shine da ƴa matsayin mallakinsa har abadan, duk inda ta shiga za'ace jininsa ce.

       A hankali ya buɗe idanun tare da kai bakinsa ya sumbaci goshin yarinyar yanajin wata irin tarin ƙaunarta na shiga har cikin ɓargonsa, baki Ummukulsoom ta taɓe tana juya masa baya, ita adole kishi takeyi, dan tunda ya shigo baibi takanta ba ta ƴarsa yakeyi.

      Ajiye Babyn yay yana murmushi, ya kwanto jikin Ummukulsoom yana mata raɗa a kunne. Ture kansa tai tana sake turo baki gaba da faɗin, “Anki ɗin, kuma karka sake kulani wlhy”.

     “Tab, akwai matsala kenan ai Beauty, kece Amaan fa, daga sanda kika bar kula Usman fodio ai babushi sai hotonsa, ALLAH yay miki albarka, ya baki ladan rainon ciki dana naƙuda, tare da bamu ƙwarin gwiwar tarbiyarta bisa ka'ida da dokokin addinin islama”.

     “Amin ya rabbi” Ummukulsoom ta faɗa tana rungumesa itama, bakinsa yakai kan nata ya sumbata, yakuma maidawa zai ƙara Momcy ta shigo.

   Sallallami ta fara da rike haɓa, daga karshe ta kora Amaan yabar ɗakin da masa gargaɗin karta sake ganin ƙeyarsa.

    Murmushi kawai yayi ya fita yana shafar keya, itako Ummukulsoom kunya ta hanata yarda su haɗa ido da Momcy dake mata faɗa itama akan ta kiyayi biyema Amaan danshi bashida matsala, ita zai ta ɗurama ciki ya bari da aiki shi yana gefe yana barcinsa harda nashari.

     Ita dai Ummukulsoom batace ƙalaba, Amaan ma tun daga ranar sai ya kiyayi shigowa saboda ma kullum su Bily anan suke yini, zaizo dai da safe su gaisa hakama da yamma, idan magana yake bukatar suyi saiya kirata a waya taje sashensa kosu haɗu a harabar gidan, dan sashen nasuma sau ɗaya yace taje akan wani muhimmin magana da sukayi, shima kuma Momcy tasan da zancen.

     A haka akaci kwanaki bakwai na zaman bakwai, inda Dad da Momcy suka nuna bajinta a kayan barka, hakama ƴan uwan Amaan suma alkairin da yake musu tun suna ƙananunsu da wanda Ummukulsoom ɗin take musu duk basu mantaba, dan sunyi hidima da jikinsu da aljihunsu.

    Hakama baba daga ɗilau yayo tasa bajinta shi da su baba yalwa dasu murja, ananma su Attahir sunyi tasu, hakan yasaka Ummukulsoom da kara tabbatar da itafa ƴar gatace ta gaske a wajen ƴan uwanta, kowa burin share mata hawayen maraicin rashin uwa yake wanda ta fuskanta tana karama. An raɗa suna bayan sallar asuba inda baby taci sunan Jamila (anma Momcy takwara kenan) kuma Dad ne yayi, dan shi Amaan ya bama zaɓi, shi kuma sunan iya marigayiya mahaifiyar Dad yaso a saka, amma hakanma baiyi baƙin cikiba, dan yasan Dad yanada dalilinsa. Aiko sai gashi Momcy harda hawayenta tayi. 

     Za'a dinga ma baby alkunya da suna *_Noor-ur-Rahman_*.

       A ranar dai kam ba'a cewa komai, dan an raƙashe an kwalle, inda maijego da baby suketa shan gayu, zuwa yamma mata sukasha shagalinsu a cikin gida, Suhailat, Lubna, Fannah harda Meenal saida sukazo wajen suna, dan yanzu sun ɗinke sun zama ƙawaye suda Ummukulsoom, sudai sunce birgesu take, komai nata na masu ajine da nutsuwa, gashi bata da girman kai.

     Hayaniya tayi yawa a gidan, inda dole Amaan yabar gidan, dan bazai iya da wannan hayaniyarba, bai dawo gidanba sai kusan 12, lokacinma harsu Ummukulsoom sun jima dayin barci, sai zuwa safiya ya gansu.

    Kwanaki biyu dayin suna ya koma lagos ya barsu wankan jego. Haka Ummukulsoom taci gaba da shayar da Noor-ur-rahman cikin amin ALLAH, gefe kuma tana wankanta na jego Momcy na gyarata gyara na musamman irin na ƴan gata, itama Ummi nayin nata, hakama su hajiya yaya da gwaggo hinde tsoffin kwarai, kamar yanda suka gyara su bily haka itama Ummukulsoom akai mata.

     A haka su Ummukulsoom sukai arba'in, taje ɗilau tai kwankinta huɗu da taho, wannan gani ma da basiru yay mata har kuka yayi, musamman daya ɗauki Noor-ur-rahman, yarinya kyakykyawar abin son kowa, daka ganta kasan Ummukulsoom ce ta haifeta saboda tsabar kamannin da take da ita. Ganin zaman banzan da basiru yake Ummukulsoom ta bashi shawaran ko zai dinga sai da kayan miya anan ƙofar gidansu.

     Jiki na rawa ya amince yanata zuba mata godiya da sake neman gafararta, itadai tace yabar mata wannan godiya haka komai ya wuce a gareta, bata baro ɗilau ba saida taba wani yayanta Surajo kuɗi yaje ya saroma Basiru kayan miya a zaria, aka kafa masa tebir a ƙofar gida yanda zai dinga samun taro da kwabo na taimakon kansa da iyayensa. Haka Ummukulsoom ta barosu suna kuka da saka mata albarka shidasu Inna, Noor-ur-rahman kanta tasha du'ai kala-kala. basiru jiyake kamar yace kar Ummukulsoom ta tafi, tamkar ta zauna ace matarsa ce da ƴarsa, ko bayan tafiyarta yasha kuka, yau gashi wadda yake tunanin yafi karfi itace gatansa, tanata masa hihima batare da ta duba abinda yah mataba.


★★★★★


      Washe garin da Ummukulsoom ta dawo kd Amaan ya iso shima, a daddafe ya barta ta sake kwana huɗu taɗan yawata gidajen dangi ya tarkata matarsa da ƴar babinsa suka koma lagos.



⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡⚡


       “Wai wannan kallonfa malam?” Ummukulsoom ta faɗa tana kallon Amaan da shima ya kafeta da ido.

      Kwantar da Noor-ur-rahman yay a ɗan gadonta, ya nufo Ummukulsoom data matsa gaban mirror tana shafama jikinta turare, cak ya ɗauketa batare da yace uffanba.

     Duk yanda Ummukulsoom ke masa magiyar ya sauketa bai saurareta ba, bargo yaja ya lullubesu bayan ya matseta a jikinsa.


Nidai ƴar ɗakko rahoto sai naji luff, dole naja roba-robar ƙafafuna nayo waje ina kunkunanin da yake kaima dai kanada wanda zaku shiga bargon😽😑🙊⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️..............✍🏻

[3/11, 10:54 AM] ❣️Noor-ur-Rahman❣️: *_Typing📲_*



     



    *_🩸WUTSIYAR RAƘUMI!!......🩸_*

                 _(Tai nesa da ƙasa)_



                *_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



         _Duk yanda rayuwa takai ga tsawo wataran sai ɗan adam ya fahimci taƙaitacciyace daga garesa, bazaki/bazaka tabbatar da hakanba saika buɗi ido kaga tawagar mala'iku a kanka sunzo amsar ruhinka, kafin wani lokaci ka jika a wannan gidan na wucin gadi (kabari) kafin randa kowanne bawa zai tabbatar da gidansa na gaskiya, wutace ko aljanna😭? ALLAH ne kawai masanin wannan sirrin😭😭😭_



*_NO. 59 & 60_*


  ..............Rayuwa taci gaba da tafiya, soyayya tsakanin Ummukulsoom da Amaan ba'a cewa komai, ga ƴar babynsu Noor-ur-Rahman ƴar gatan Affahn ta, yayinda a ɓangaren aiki su dukansu suketa sake samun ɗaukaka da ƙarin girmansu saboda ƙyawawan zukatansu, tuni Ummukulsoom ta kafa ƙungiya a ƙauyen ɗilau, wadda taketama mata hidima wajen basu jari da buɗe musu wani ɗan lokaci na fahimtar dasu ilimin addini dana zamani, tun maza na noƙewa har suka fara sakin jiki da makarantar saboda canji da suke gani ga matansu.

    Ga iyaye sun dage wajen barin yaransu mata su cigaba da karatu mai zurfi, dan Ummukulsoom tazama madubin dake haska ɗilau da kewayenta, ita ba ahalinta kawaine ke amfana da alkairinta ba, ta kowace kamar yanda kowa yake nata a birni da karkara. 



*_BAYAN WASU SHEKARU_*


          Ƙyaƙykyawar budurwa ce tsaye ƴar kululluɓa haka takema wani ɗan matashin saurayi da bazai gaza shekaru ashin da biyu ba magana, amma ya miskile fuska yaƙi ya kulata sai faman danna waya yakeyi, cikin fushi ta tallare masa ƙeya tana juyawa cikin falon gidan ranta a ɓace harda hawaye.

       Dattijon da bazai gaza shekaru 60 ba yana zaune cikin kujera yana duba littafin Fiqhu ya ɗago manyan idanusa farare tas yana kallonta, “Noorin Affah miya faru kuma?”.

      Zama tai kusa dashi tana sake matso hawaye, “Affah kaga Noorul-Ayn ko, na masa magana yazo na aikesa ya amso min abu wajen yaya Ahmad amma ya shareni yanata game a waya bai kulani ba”.

      Yanda take hawaye sai tausayinta ya kama Amaan, yarinyar tanada haƙuri, musamman akan shegen miskilancin ɗan uwanta Mahmud da suke kira (Noorul Ayn) danshi nasa kalar miskilancin ma da banne shida  Amatul-kareem.

     “To ya isa haka share hawayenki, banace kidaina masa kuka ba shi ƙaninki ne? Jeki kiramin shi”.

     Tashi Nuoor-ur-rahman tayi ta fita tana goge kwallarta, a inda tabar Noorul-Ayn anan ta iskeshi zaune ko motsi baiyiba, ta dalla masa harara tana faɗin, “Kazo Affah na kira, miskilin banza kawai”.

     Nanma bai tanka mataba, miƙewa kawai yay ya nufo falon.

       Noorul-Ayn ya zauna a ƙasa saitin ƙafar Amaan da tunda ya shigo yake kallonsa, su kansu da suka haifi Noorul-Ayn bazasu iya tuna yaushe sukaga hakoransa a waje ba yana dariya, haka yake kullu yaumin fuska a cinkushe, kuma babu abinda akai masa, magana kuwa sai yaji bala'in Ammi (Ummukulsoom) yake yinta a gidan, dan ita batai masa da sauki, ca take bazata iya da wannan banzar halayyarba, taci wahalar ubansa taci tashi.

       “Noorul-Ayn mina gaya maka ranar akan Noor-ur-Rahman?”.

     Shiru yay bai tanka ba, kuma ga maganar a maƙoshinsa amma bakinsa ya kasa furtawa, Ummukulsoom data shigo falon a gajiye batare dasun lura da itaba ta dakama Noorul-Ayn tsawa, “Wai kai dan uwarka ba magana ake dakaiba ne?”.

      Duk kallonta sukai, yayinda Noorul-Ayn ya janye idonsa a kanta yana fisgo magana da ƙyar yace, “Affah kayi haƙuri, itace ta isheni da hayaniya aka, ai tasan dai zanje ɗin”.

        Zama Ummukulsoom tai kusa da Amaan tana harar Noorul-Ayn dake magana a hankali kamar mai ciwon baki, yayin da Noor-ur-rahman taje ta kawo mata ruwa mai sanyi.

       Amaan ya jinjina kai kawai, lamarin Noorul-Ayn sai dai addu'a kawai, “Amma data maka maganar idan bakaso ta dameka basai ka tashi ka tafi ba, banason raina na gaba, ka shiga hankalinka a gidannan, inba hakaba wlhy gidan Uncle Bassam zaka wuce gobennan, danshi ba ɗaukar wannan iskancin naka zaiyiba, mutum saikace wani kurma ko gunki......”

      “Ya isa haka ayi hakuri Ammi” Amaan ya faɗa a hankali yana riƙe hannunta, dan yitake kamar zata make Noorul-Ayn. Itama Noor-ur-rahman duk sai tausayin ƙanin nata ya kamata, ta kama hannunsa suka fita kuma tana lallaɓasa, dama haka suke, kullum babu fashi saisunyi faɗa, dan ita hakurine da ita, batason kuma shariyar da Noorul-Ayn ke mata sam, ko hirarnan da zakaga anayi da kane ita bata samu suyi, sai dai ita da Amatul-islam, itakuma yarinyace, sune ƴan biyun da Ummukulsoom ta haifa bayan haihuwar Noorul-Ayn ɗin da kusan shekara goma sha ɗaya, harma sun fidda rai da haihuwa saikuma ga cikin su, ta haifosu tagwaye sukaci sunan Ummi da na Maman Ummukulsoom wato Hassana, amma sai ake musu alkunya da *Amatul-islam & Amatul-kareem*, to itama Amatul-kareem ɗin haka take miskila ta bugawa a jarida, duk sun kwaso Amaan ɗin.


       Su Noor-ur-Rahman na fita Amaan ya kalli Ummukulsoom yana murmushi, “Beauty kinga kin gama faɗan sunkuma haɗe kansu, kodai wanine ya kunnomin ke wajen aiki zaki huce haushin kan yarona?”.

      Murmushi tayi tana kwantowa gefen hannunsa, “Aini wannan hali naku sai ku wlhy Zunnur, gashi nan Noorul-Ayn yazo ya takaku ya shanye, ALLAH miskilancin yaronnan yana bani takaici shida Amatul-kareem, da ana cirewa dana biya ko nawane an rabasu dashi nikam”.

       Lumshe idanunsa yay ya buɗe yana murmushi, tare da sumbatarta a goshi, “Sai dai aita haƙuri damu Noorulain ɗina, muma ba'a san rammu baneba”.

       “Uyimmm, amma kuka iya share mutane, haƙuri nake kawai nima wlhy Sweet fodio” tai maganar tana jan hancinsa.

     Gaba ɗayanta ya sanya a jiki yana murmushi, ihun Amatul-Islam ya saka Amaan saurin sakin Ummukulsoom, autoci sun dawo daga School.

     Jikinsa ta faɗa tana murnar ganin iyayen nata, yayinda itama Amatul-kareem dake biye da ita fuska babu fara'a ta faɗa jikinsa ya haɗasu ya rungume.

    Barin jikinsa sukai suka koma wajen Ummukulsoom itama tai musu oyoyo, saiga Noorul-Ayn da Noir-ur-Rahman sun dawo suma, Noir-ur-Rahman ta jasu ɗakinsu danta cire musu Uniform, shikuma Noorul-Ayn ya wuce kicin zuboma Ummukulsoom abinci data sakashi.


      Haka rayuwar gidan take, babu ruwan Ummukulsoom da ƴar aiki tunda yaranta sukai wayo, dukda kasancewar Noorul-Ayn namiji haka take sakashi duk aikin da zata iya saka Noir-ur-Rahman, dan haka yaran suka tashi a hore, babu sangarta ko san jiki, kosu Amatul-Islam dake da shekara 10½ a duniya Ummukulsoom sakasu aiki take.

     Ta kuma zama babbar mace, tayi ƙiba sosai, yanda ta ƙara girman jiki haka ta kara girman daraja a idon duniya, tazama abar alfahari a kauyenta da ahalinta dama mata, dan tuni ƙungiyar data kafa tagama tsiro da yaɗo, wanda manyan mata ke cikinta suna hidimtawa matan karkara da yara, musamman yaran da ake bautarwa ta hanyoyi daban-daban, tariga ta zama tauraruwa ta mata da yankinta na arewa, sunanta yakai tsqiko a ƙungiyar lauyoyi da har takai ana shakkar karawa da ita akan shari'a, hatta da alƙalan shakkarta suke, dan ita duk yanda gaskiya take saita kwalƙwalota.

      Rayuwar gidansu abin sha'awa itada mijinta Usman Mahmud Usman Ajiwa, da ayanzu haka ya zama babban mutum shima, mai riƙe da muƙamin Lieutenant general na soji, duk inda matarsa ta sanya kafa hannunsa na ciki da addu'arsa, yana taimakonta da karfin aljihu dana shawarwari da dabaru, yayinda suke zuba soyayyarsu da bata tsufa sam, sai daifa halin na nan daram bai canjaba ga Amaan, ga karin Amatul-Kareem da Noorul-Ayn da suka sake samu, a yanzu haka auren Ahmad da Noir-ur-Rahman watanni kaɗan ya rage.

    Abotarsu da Attahir kam  ai saima abinda yay gaba, dan suna nan gam-gam.

     Hakama tsakanin Ummukulsoom da Bily da Aziza, harma dasu Suhailat da suka dunƙule yanzu, ko ƙungiyarnanma atare suke jagorancinta.

   

Ɓangaren Basiru kam zuwa yanzu Alhmdllh, dukda yazama gurgu dai ALLAH ya sama jarin kayan miyar da Ummukulsoom ta bashi albarka, harma ya auri wata yarinya dagacan wani ƙauye, itama dai tanada lalurar shanyewar ƙafa, dan karya zauna haka babansa ya nema masa aurenta, annan cikin gidan aka gina musu ɗaki ɗaya suke zaune, yanzu haka yaransu biyu, Amal ma yarinyarsa ta wajen Lubna tana zuwa lokaci-lokaci kamar yanda Ummukulsoom ta roƙa.

 

     Rayuwa gasu Ummukulsoom sai dai ace Alhmdllh, dama tuni sun dawo Abuja da zama, shiyyasa ko yaushe ƙafarsu na kd da ɗilau, ita da yara dama uban gayyar Amaan, aduk ƙarshen watan duniya a kd suke yinsa ko ɗilau ko Ajiwa, da anyi hutu kuwa yara na gidan Momcy kosu tafi ƙauye, dan Ummukulsoom tace ƙauye shine gatan kowa, rayuwa a cikinsa babbar makarantace da mutum baya iya mantawa, dan haka take son a koyaushe yaranta su rayu a ciki koda bata tare dasu.✍🏻😢🙏🏻😅🚶🏻‍♀️🧳👜🌂⛹🏻‍♀️.



*_ALHAMDULLAHI ALA KULLI HALIN_*


     Godiya ta tabbata ga ubangijin al'arshi daya jagoranci hannayena da ƙwakwalwata wajen kawo muku wannan gajeren labari, Abinda na faɗa dai-dai ALLAH ya taramu a ladan, wanda nai kuskure ya rabbi ka gafarceni😭🙏🏻


*Gai suwa tare da fatan alkairi da jinjina ta kai gareku masoyan ƙwarai, lallai kun nuna mana halacci irin wanda zuciya bazata taɓa mantawa dashiba, dan mun tabbatar akwai tarin masoya tare damu waɗanda idan zamu ƙare rayuwarmu wajen rubuta free novels wlhy bamuyi asara ba, ALLAH ya saka da alkairi yabar zuminci na har abadan*



_Duk wanda na ɓatama rai a lokacin rubuta wannan buk ya yafemin, nima na yafema kowa, wlhy har waɗanda suka zagemu ba tare da mun aikata musu komaiba ni dai Bilyn Abdull na yafe musu, koda ace sun aikata mummunar magana mafi munine a gareni, nima ina fatan ALLAH ya yafemin nawa kurakuran sanadin yafe musun danayi, dan ALLAH wanda duk na ɓatamawa ya yafemin, dan zata iya yuwuwa wannan shine novel ɗin Bilyn Abdull na ƙarshe a rayuwa, bani da tabbacin ganin wayewar gari balle dogon buri, ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗaya😭🙏🏻_



*_Ka ƙyautatama wanda ya munana maka koda shi ALLAH bai basa fahimtar gane ƙyautatawar kai masa ba, murmushi sadaƙa ne, hakama ƙyaƙykyawan kalami sadaƙa ne, ƙautata zato sadaƙa ne, riƙe harshenka daga aibanta waninka ma sadaƙa ne, yafiya ga al'umma koda sun shekara dubu suna munana maka sadaƙa ne, ALLAH ka bamu damar yin sadaƙa koda bata kuɗi bace muyi da ayyukanmu🙏🏻😁_*






*_I LOVE YOU IRIN TRILLIONS ƊINNAN MY GUYS, ALL ZAFAFA NA CEWA I LOVE YOU WUJIGA-WUJIGA, MAZGA-MAZGA, MARASA IYAKA😉🥰🥰🥰🥰😍😍😍😘😘😘😘😘😘😘🥰🥰🥰🥰🥰🥺._*






*_I miss you😢🤗⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😁._*



*_Writer_*


1-Rashin sani.

2-Auren ƙaddara ko biyayya?.

3-Ƙanwar uwace ko kishiyar uwa?.

4-Ban saketa ba!!.

5-Nawaff!!.

6-Ni da aminiyata!!

7-Kukan kurciya....!!.

8-Sabon Al-amaree!!.

9-Karayar arziƙi!!.

10-Abdul-maleek bobo!!.

11-Siyasa ko ƙabilanci?!!.

12-Ciki da gaskiya....!!.

13-Sanadin bikin salla!!.

14-Raina kama.....!!.

15-Mutum da duniyarsa!!.

16-Wutsiyar raƙumi....!!.





*_Bilyn Abdull ce🤙🏻😉_*

Post a Comment for "Wutsiyar Rakumi Complete Hausa Novel "