Tantiriya a Gidan Yari Book 1 Paga 81-85
🏫 TANTIRIYA 🏫
A GIDAN YARI
BOOK 1
81-85
Official
By
AsmaBaffa
SADAUKARWA NE GA
AIDA MAMAN TASNIM
PAGE NAKU NE
Ummin Saddiq
Aunty Nurse Zaria
Uwar Batoola
*👭GARKUWAR MATA👭*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
08089965176
07084653262
Ashraf Ahmad Maleek, kakansu wato Maleek Dan asalin kasar Somalia ne,Matarsa Zeenatu Yar asalin Nigeria ce Katsina state,Maleek hamshakin me kudi ne tun a zamanin da,Zeenatu matarsa tun tana karama ta fara bin Maza,Wanda gidansu suna da rufin asiri baza ace babu ce ta kaita ba.
Daga haka ta fara guduwa Bariki sai a nemeta a rasa, sai sanda taga dama take dawowa gida,idan ta dawo zata zo da surutu masu tsada da kudi in tayi kwanaki kadan ta koma,su biyu iyayenta suka Haifa yayarta ita ta gari ce Bata Dade da aure ba Allah ya mata Rasuwa a ka bar Zeenatu wacce Bata Jin magana ko kadan,sai yawon karuwanci ta sa a gaba,iyayenta sunyi kuka sun gaji sun mata addua sosai,a yawon karuwancinta ta hadu da Maleek shima ya leka Bariki ya Maidata dadiron sa har Soyayya ta kullum tsakanin su, suka tuba daga Bariki suka dawo gida aka daura musu aure.
Bayan ya aureta ya dauketa zuwa kasar su can Somalia acan Kuma Allah ya bata ciki ta haifo Danta namiji Uzairu, daga shi Bata sake haifar namiji ba sai mata,ta Haifo yarta ta biyu Salamatu,Khudrah,Yusra,Lateefa,sai Allah yayi mijinta Maleek ya saki Zeenatu.
Bayan ya saketa sai ya auri wata matar a can kasar sa ta haifar masa Surayya,Rafeeqah,daga Nan sai matar tasa ta mutu, ya dawo Nigeria Abuja suka daidaita aurensu,Zeenatu tace ita baza ta koma kasar Somalia ba,sabo da Yana sonta ya tattaro yaransa suka dawo Nigeria gaba daya,sai da yaransu suka girma kaf suka aurar dasu bayan kowanne da karatusa da sana'ar yinsa,duk yaransu sabo da kyawawa ne babu wacce ta auri talaka a ciki ko wacce me kudi ta aura a garin Abuja.
Salamatu wacce aka fi sani da Mima itace ta fara aure,ta Auri matashin Soja me ji da kudi Ahmad,Allah ya Bata haihuwa,haihuwarta ta farko Khalid ta Haifa wanda shima Soja ne babba a yanzu a Lagos yafi zama tare da matarsa da yaransa hudu.
Na biyu ta haifo Nazeer lokacin anyiwa sauran Yan uwanta aure amma a cikinsu mutum hudu basa haihuwa,taso ta haifi yara mata sabo da ta basu su kyauta su rike amma Maza take Haifa,gajiya tayi ta hakura tana sake haifar Ashraf wato Spark kyakyawan gaske ne na karshe, ita kanta tana sonsa amma haka ta hakura ganin Yar uwarta Surayya ta damu da shi,kullum Ina Danta sabo da Spark kullum sai tazo gidan,kullum tana siyo Masa abubuwa,Mima tana yaye shi ta kaiwa Surayya har gida tace gashi nan ta bar mata tsakani da Allah har abada ya zama nata,babu ruwanta Kuma ko shiga safgarsu baza tayi ba.
Surayya sai murna amma Sam mijinta Alhaji Aliyu baya son rike Dan wani shi,kawai sai ya tsani Spark,tun Yana yaro har Spark yayi hankali yasan Mijin Mummy baya kaunarsa,gashi Mummy ta shagwaba shi sabo da haka ma Yana gama secondary ta dinga koya Masa business iri iri Kuma Allah ya taimake shi din,Makarantar Soja ta sashi sai da yayi nisa yace bazai iya ba shi,a haka tana lallaba shi ya daure har ya gama ya fito a Soja sak,ana turashi yaki wata kasar yayi resining dama ba so yake ba ya bar aiki,dama shi ya gaji Yana so ya dinga tara sumarsa da shanawa duk babu kullum aiki aiki duk yayi duhu zai lalace yace bazai iya ba,baza a canja Masa halitta ba haka kawai akan fatararsa ta lalace gwara ya zauna da talauci.
Yo Mummy ta gama shagwaba shi baya Jin magana,gashi da mugun ra'ayi idan ya kafe a Abu sai dai a kyale shi,ba a Masa dole shi,ya taso ba abinda yake nema ya rasa, Alhaji Aliyu Kuma baya sonsa tun asali,zagi hantara duk Yana Masa har ma ya daina jin haushi, Mummy kasar waje ta turashi yayi masters akan business,dama tun Yana secondary take biya Masa kasar waje tana kaishi, Yana zuwa hutu can ya shakata har ya girma kullum a tafiye tafiye yake kasa kasa baya rayuwa sosai a kasa Nigeria.
Gashi da Nasibi a rayuwa,tunda suka taso su ba musu fada duk abinda kayi daidai ne,su kansu su Mummy iyayensu sunyi duniyanci kadan, daga baya suka tuba,basu basu wata tarbiyyar kirki ba bare su bawa wani.
Spark kullum kudinsa na bunkasa ganin mijin Mummy ya tsane shi sai ya Gina gidansa katafaren kawai ya koma can,Alhaji Aliyu da kansa yace Spark ya daina kulashi sabo da bakin ciki yaga yaro ya girma a gabansa yazo ya fishi kudi.
Mummy suna yawan zuwa asibiti akan rashin haihuwa amma sai ace kalau suke mijinta ne da matsala,sannan baya iya biya mata bukatarta,a haka ta hakura take zaune da shi,ya Sha gwada nemo aure Mummy ce take ruwa da tsaki ta Hana auren ta hanyar masifa da tijara .
Tunda taji ance ita kalau take kullum suna yin fada da Aliyu zata Masa gorin haihuwa tace hakuri take alfarma take Masa,ga shegen son kudi duk family din su Mummy haka suke su da sunga me arziki to shine nasu,sannan duk kusan kangararru ne basu da kyawawan halaye na iyaye mata,shi yasa tunda mijinta Taga lallai aure zai kara da gaske Taga ita bata haihu ba,ta ya za a kawo wata idan ta haihu ita shike nan baza ta samu gado ba,akan gado taga gwara ta kasheshi.
Tana tunanin ya zatayi idan ta kashe shi ta tsira kar a gane itace sai katsam Jamilu yazo me magani dabara ta fado mata ta aikata.
Bayan Mima ta bada Spark sai ta sake haifo namiji Misam ta dauke shi data yaye shi sai ta bawa Dan uwanta Namiji Uzairu lokacin Dansa Daya a duniya tal wato Kamal, ya dade da aure Kuma ,sai ta Kara Masa da Misam,bayan an bashi Misam sai Kuma ya Kara aure duka matansa suka dinga haihuwa sai da suka haifar Masa yara takwas Kamal shine babba shine Kuma mate din Spark,abokin Spark ne tare sukayi school,amma a kasar waje Kamal shi Engineering ya karanta ya dawo Yana aikinsa Yana samun kudi,ya Gina gidansa shima sannan Yana da budurwa har an kusa biki ma.
Misam shi matar Uzairu ce bata kaunarsa,idan mijinta baya gidan sai ta dinga dukan sa tana zagin sa,idan mijinta na gidan ba Wanda take so kamar Misam a gaban miji,Yaranta sune yara su take wa fada da tarbiyya,Misam ko me zaiyi baza ta yi Masa fada ba, har ya taso ya girma ya fara yawon dare amma bata taba yi Masa fada,tana kallo Uzairu Bai sani ba Idan ma taga zai gane sai ta boye ta kare zancen kar ma ayi Masa fada ya shiryu,har Misam yayi nisa a neman mata sannan Kuma Kamal ya gaji ya fadawa Abbansa Uzairu,Uzair hankalinsa ya tashi an bashi Amana.
Yaransa kaf gasu Nan a shirye amma na wata an bashi ya lalace a hannunsa sabo da rashin kula,ya dawo lallai sai Misam ya shiryu Misam yace kayi sake Baba da baka bibiyar Amanar ka, ka manta matarka azzaluma ce kawai ka barni a hannunta ba ruwanka da bincika me ake min Ina ta nuna Maka ka gane kaki sai da na lalace, yanzu bazan daina ba nasan mata nayi nisa,kullum ana bata min rai ba dole na tafi Inda zanji dadi ba,Ba irin nasihar da bai yiwa Misam ba yaki ji,sai addua ya koma a dalilin haka ya saki uwar gidansa gaba daya Kuma yaki dawo sa ita har gobe.
Kawaici irin na Mima Bata taba zancen ba tasan Kuma me Misam keyi, tana yi Masa nasiha ma amma bata taba zancen ba a wajen wasu, ko da kuwa ace danginta ne, tunda ta bayar ta Bada tsakani da Allah, babu bincike ya zama Danka duk da tana Jin ciwo tasan ana zaluntar Misam a gidan amma ta hakura.
Bayan Misam duk sauran Yan uwan suna haihuwa su har su Babar Wahida,mace daya ce Bata haihuwa itama, ita Kuma uba daya suka hada da su Mima, Yan ubanci yasa ta hanata Dan ita,Ahmad Mijinta shine ya dauki Rafeeq da hannunsa ya bawa Yusra itama yace ai babu dadi kin bawa Wanda kuke uwa daya uba daya kin Hana waccen Dan Kuna yan Uba,Mima tace ni wlh banyi niyyar Bada Rafeeq ba duk yarana kyawawan ciki duk na bayar dasu,yace kika Bada Spark ma wato ita waccen Dake Yar uwarki ce uwa daya uba daya,me yasa yanzu zumunci ba ayi Dan Allah? ba kara ba komai, kowa Keke da Keke wlh ni na bata Rafeeq ya dauke Rafeeq ana yaye shi ya bata kyauta.
Duk Wanda suke uwa daya uba daya da Mima sai da suka ji haushi.
Shike nan Mima ta tsaneta sosai sannan tayi mugun sawa Rafeeq Ido,ta takura Masa har ya girma idan yaje gidan sai ta dinga tambayar shi me da me ake Maka? Kana cin abinci? Bata dukanka? sabo da haka Rafeeq ya daina zuwa gidan ya tsane su gaba daya har su Khalid ba ruwansa da kudinsu da kayansu,shi yafi son wacce ta raine shi, akan a zageta gwara a zage shi,ba Wanda ya isa ya taba Masa wacce ta Raine shi,ita Kuma Yusra mijinta akwai kudi amma ba wani sonta yake ba,aurenta yayi sabo da sha'awa tana Masa biyayya iyakar iyawar ta amma baya Gani,ya tsaneta ma sai auri saki ya iya, Dake shine baya haihuwar, gashi da mugun son kudi Yana da kudi amma baya ciyar da iyali,kullum gidansa garau garau ake ci a haka ma da taimakon Rafeeq,Yusra tana Shan wulakancin da namiji tayi tayi ya saketa yaki Kuma Bai fasa wulakantata ba,duk abinda tayi Dan ta birge shi to fa bata birge shi, shi tsabar mugunta ma baya so wani ya taimaka Masa a gidansa amma shi zaici me dadi a waje zai sa suturar da yake so sannan zai hau motar da ya ga dama amma banda iyalinsa,Rafeeq ganin haka ya fita shirginsa,Spark ne ya dauki nauyin karatun Rafeeq da komai nasa,da kasar waje zai kaishi yace a'a ya barshi a Nan Nigeria sabo da Mama babu Mai taimakon ta sai shi, Spark yace ya Fadi sana'ar da zai iya ya bashi jari,yace ai shi joint za a bude Masa,anci dariya aka bude Masa Kato me kyau da ma'aikata da komai shike nan ya zama Baban shawarma joint,ga school dinsa Yana zuwa private da hostel dinsu sabo da tsakanin su da gida akwai nisa shi yasa.
Mummy Kuma tunda Taga Yana samun kudi Yana taimakon Yusrah mamansa wacce ta Raine shi sai haushi ta sawa kudin Rafeeq Ido,sai ya tara kudinsa a accnt sai tace lallai sai yazo ya bata kudi,ta dinga ta karbe kudin ta hanashi gaba ta hanashi baya,ko yaushe a Dora jari Spark yake watarana Kuma Misam Yana bashi,Khalid ya siya Masa mota amma ya siyar ya Dora jarinsa shike nan suka yi fada da Yan uwa Dan me zai siyar da mota ya Dora jarin Shawarma,Sai ya daina kulasu du sai yaga dama, ya fita harkar kayan su, ko an bashi baya karba tunda ana Masa gori a dinga sashi Yana yin abinda baiga dama ba.
Mima kanta sai Kara ta kaiwa Spark ta Rafeeq ya daina kula su gashi gashi,ya same shi ya Masa fada shine ya Dan sakko,amma idan ba Spark ba da Misam ba ruwansa da sauran,shima tarbiyyar tasa da gyara sai dai bai Kai sauran lalacewar ba.
Bayan an bayar da Rafeeq Mima tace ta gama Bada yara a duniya, sai ta haifo mace Kuma,a da matan taso ta raba sunfi dadin raino da tankwarawa,idan macece Bata da matsalar Maza sai yanzu Kuma ta haifi Bisma wacce itama tayi aure da yaranta biyu tana zaune a Uk,sai Badia itama tayi aure da yarta Daya a garin Bauchi,su ma basu da wata tarbiyyar kowa harkar gabansa yake babu me yiwa wani fada,Wanda kake shiri da shi to da shi kawai zaka yi zumunci.
Daga Nan Mima ta haifo Waleed,Atif,Arham duk makarantar sojoji sukeyi matasa dasu,sai Kuma ta haifi mata biyu Anam,Zainab suma duk sun zama Yan mata haka marasa tarbiyya ne,ga kudi ga sakaki na iyaye sai abinda suka ga dama,karatu Kuma da wuri ake saka su shi yasa zaka gansu yara amma sunyi Nisa a karatu,Ina kaje boko Ina zasu boko,Islamiyya a gidan ake musu sai sunga dama suke zuwa ma dake Islamiyya ce amma boko ko basa so sai sunje.
Mace komai kankantar ta matukar me kudi ya fito to dole aure zasu mata karatu tayi a gidan mijinta shi yasa su Badia ko secondary basu gama ba aka musu aure a hannun mazajensu suka yi karatu.
Idan talakane Kuma sai suce yarsu karatu zata yi sabo da baza su bashi ba.
Duk sun lalata family dinsu sun tarwatsa kansu.
Ci gaban labari
Ana Kai Invitation prison Azima me kwana ba wando ta cika Umarni ta raba na Beauty a gidan tace kowacce tayi addua da fatan Alkhairi tunda ba a samu zuwa ba, suna ta tayata murna,Zagawa tayi ta katangar bangaren Maza wata a ciki ta dagata sama ta watsa musu Iv ta ko wacce kusurwa ta bangaren mazan.
Dan Indo ya dawo daga cikin ball yaga IV da yawa ya dauka ya fara karantawa sabo da IV din gidan yarin daban suka bayar da kudi aka buga musu ba irin na normal mutane da aka raba bane,ya karanta yaga an saka
Iyalan General Ahmad Maleek
Na farin cikin gayyatar ku
Zuwa wajen daurin auren
Yayansu, Wanda an riga an daura shi tun 12Jul
Naila Hashim (Jamilu)
Da Angonta
Ashraf Ahmad Maleek(Spark)
Ku da baku samu damar halatta ba a tayamu da addua,yanzu haka an Kai Amarya dakin mijinta idan da rabo ma an samu tuni.
Sabo da takaici Dan Indo ta hannunsa ya yayyaga,ya kurma ihu tare da furta Kai Yan matan gidan yariiiiii.......kuzo nayi muku cikiiiii.....kun San yanda ake cikiiiii .....Kafin kace me gidan yari bangaren Maza ya dauka Jamilu yayi aure,kowa yazo Dan Indo yake nema.
Jamilu da yayi aure ba a kawo mana shi gidan yari ba mun more,Dan Indo yace ba labari gashi wannan Spark din ubansa ma Soja ne duk iskancina ai bazan kawo matar wani ba.
Scoler ne ya saki shewa ahayyeeee chass wa ya fada muku barno gabas take? Ai na fada muku Terror yayi gabas kunyi Yamma wlh na gaba yayi gaba na baya sai labari billahillazi,Jamilu tana can tana tsotsar madarar Nido,washer yace har milky me bukunboti ma yanzu ta zuki abarta da tsinken zuka straw .
Malam Sharu kuwa suna Gani suka fara Alhmdllh Alhmdllh wato aihin Allah ya karbi adduar mu ya shirya Jamilu da Spark,Allah ya Kara dankon kauna da soyayya har mutuwa,Malam Garzali yace Astagafrillah wato sai naji darshin hassada a raina, hassada ta darso a kirjina,naji Ina yiwa wannan yaro Spark Hassada da samun Jamilu Tantiriya naji wannan ni'ima dama kaina ta fada,Allah ya shiryeka Dan uwa cewar Malam Jilani.
Su Naila suna hanya Spark sai waya yake wa driver Wanda ya dakko Amarya da kawayenta kayi fa tuki a hankali karka cuceni Mubarak,Wlh ka kashe min Amarya sai ka mutu kaima, Mubarak Dan gidan yayan su Mima ne Uzairu,sauran biyu Kuma yayyen Wahida ne,dukkansu cousins din spark ne ba yanda suka iya haka ya tattaro su dakko Amarya.
Naila kuwa hirarsu kawai suke da su Rayya sai fulatanci suke,Chika kuwa Misam ta dinga nemowa a social media ta ganshi kuwa a Instagram tayi following dinsa,tana duba pics dinsa da videos dinsa gasu Nan latest,sai dai tana yawan ganinsa da Yan mata,ana shigowa garin Abuja Naila ta fara murmushi harda rawa da kafadu anzo.. anzo... Mubarak yace Spark ya samu daidai shi wlh,Naila tace ai dama nace bazan bacci ba idona kirrrrr sai anzo,Mubarak Yana dariya ya kira Spark a waya yace Ango munzo muna Abuja amma gidan Mummy zamu fara kaita sun ce,Spark yace to kuje Gani nan, Mubarak yace Kai Spark harka ta mata me zaka yi Kuma,Yace baka da hankali Mubarak ance ma Amarya wasa ce ya ja tsaki ya kashe wayar.
Naila ya kira a waya yace Amaryata? Naila ta kama dariya tace nazo ai no more damuwa,yace yeah mun daina fada ai Kuma,wani wuri suka yi parking,Dattijai mutan kauye basu San haka ba a rayuwarsu sai yau,Motocin Spark ne guda hudu masu tsadar gaske sababbi gal suka karaso wajen da su Amarya suke,Mota Daya Kamal ne da Rafeeq sai wani Abokin Spark shima farook,Daya motar Kuma sojoji ne mutum uku Helux baka me rufaffen baya tana Shining,Ango Yana cikin farar mota Yar ubansu an mata wata uwar kwalliyar flowers kana gani kasan ta Amarya ce.
Gaba driver ne shima Soja ne ke tuka shi,kofa driver ya bude Masa ya fito,Ya Sha wata Gezna kalar adon leshin Naila milk,yau ya sa hula a Saman tarin sumarsa wacce ta Sha gyara,Sajensa da dan gemu yasha gyara sai sheki yake,Naila tace ga nawan nan,Chika tace uhmm muna kallon sabon salo yau duk akan Amarya Allah ya bamu itaku Naila,Rayya tace aradu dama ance duk Wanda yaje gidan yari Bada hakkinsa ba sai ya daukaka.
Chika tace nima nan na hango tawa Daukakar Rayya,dole sai na auri kanin mijin yarinyar nan Naila,baza ta sabu ba,ai ko Misam ya shirya ko Rafeeq cikinsu dole wani ya Kara rage mugun iri idan ba haka ba na tambade,Dije tace ni kuwa Ja'e ma da zai dawo to ni wlh da na gama tawa Daukakar aradu na Saba da Hallaren Ja'e,duk kudin mutum,duk kyawun Da namiji ke ko da Larabawa za a tara min a jefa Ja'e cikinsu to Ja'e zan zaba,Rayya tace yo me za ayi da mutum ba saniya sai motoci.
Spark ne ya tako cikin takunsa na Yan gayu ya bude bayan mota yaga Dije ce ya Maida ya rufe yace shi yasa naga motar ta min duhu,dayan side din ya zaga ya bude yace lantarki haba yanzu naga haske,dariya Naila tayi a hankali tace bari nayi kunya tunda Amarya ce,Mayafinta ta lulluba a kanta fuskarta duk ta rufe sai ta mayafin kawai take kallon mutum,Hand bag dinta ta dauka sannan ya riko hannunta ta fito a hankali, Spark Yana tsotsar alawa a bakinsa Naila tace San min abinda kake ci,ya ma manta shi Yana Shan abu,cirowa yayi da hannu ya sa mata a baki yace haba in kayi aure shike nan baza a barka kayi kiba ba, komai Kaci sai matar ta ci,mata ku dai zuciyar ku a mace take kullum a baku,Naila tace Dan Allah karka sa Amarya ta dinga dariya ana ganinta,Su Goggo ana mota suna ta salati.
Goggo tace yau ni Ramatu naga abinda ya isheni ni 'yasu,rashin kunya kiri kiri,wallahi Kin Gani Tani hannu ya rike mata,Tani tace yau ni Ina zan iya kallon wannan fitsara,dole Kakan Naila yaji zancen nan cewar Goggo,Tani ta rafka salati ganin Spark ya rungume Amarya suna dariya a Jikin mota,mayafinta ya daga ya shigar da kansa shima,Goggo tace haka duniya ta koma? Shike nan duniya tazo karshe an kusa tashin kiyama,ke Kinga Dan Allah mun bani Ramatu,ai muna kauye ta nan yajuju da majiju zasu fara bullowa,Goggo tace na fadawa Naila idan ta fara ganinsu ta bugo mana waya mu kimtsa,Me tuki dai yana ta dariyar su Goggo,bangaren su Dije ma sai salati suke suna Jin kunya,Chika kuwa ficewa tayi da su Kamal suna ta daukan Amarya da Ango pics da video iri iri,sai da suka gama sannan Spark ya sa Amarya a motarsa ya shiga gefenta suka tafi gidan Mummy.
Mummy ya ta iya Danta ne ya fada mata zasu zo haka ta kira kawaye da wasu Yan uwan suka je gidanta za a kawo musu Amarya,Mima kuwa duk dangin kusan suna gidanta itama suna jiran Amarya,suna cewa wannan bikin arna kawai aka yi Amarya ya gama kwashewa da ita sabo da iskanci yanzu ace za a kawo musu ita,Mima tace mu da muka gansu akan gado ai magana ta kare Kuma,ni wlh tunda ake haihuwa ban taba ganin yaro irin Spark ba, kace zaka Masa Baki yace zai afka Maka.
Maman Rafeeq tana ta dariya tace kar ki Masa baki wlh hukuncin Allah ne,Kuma Dan kin gansu akan gado sai kice yayi wani Abu ba fa lallai bane zafi ya rage maybe,Mima tace ai kune Yan zamani Kuma ba wasu manya bane Kun San ya matasan yanzu suke,Maman Rafeeq tace sai addua wlh yaran yanzu,Lateefa tace ai Ubansa ne ya daure Masa gindi shi yasa ko me yace sai ya hau ya zauna,duk yaran da basa gabansa yafi kaunar su,da wuri yake musu Abu,ko Rafeeq Dan yaki karba ne amma ya damu,baya son sana'ar Nan tasa wai Shawarma Joint kiji iskanci,wlh duk kudi ne yasa su yin haka,basu da matsala ne shi yasa suke wannan iskancin cewar Kawar Mima.
Mima tace yanzu haka Amaryar da dan cikinta a gaba irin dai ta Christian,gata tsagera idonta kar ni dai na shiga uku banyi dacen suruka ba cewar Mima tana zuba tagumi.
Har gidan Mummy suka shiga tare da parking,Chikar gayu ita ta shiga motar kayan Naila sun wuce gidan Amarya ita da me Jan motar.
Spark fitowa yayi ya budewa Naila tare da riketa ya fito da ita,Mummy suna leke ta window Baki ta tabe tace kuzo kuga duk Yan kauye ne suka kawota amma dai sunga kawayen Umma duk su Yan birni ne basu da mukusa,Oh ni na shiga uku ya kwaso min matsafa yaran talauci,dama wata yar film ce Yar gidan masu kudi, Ni tunda tayi yankan Kaunar ma wlh ban sake Ganinta ba,ita a Yan film din ma ba wata popular bace domin tunda naji ita ya aura na shiga bincike Ina tambayar kawayena ko sun San wata Nasiba Yankan kauna ba Wanda ya ganeta,wata tace maybe irin sababbin Nan ne Yan giggiwa ba Wanda ya sansu sai karya,idan kin kure su baifi a Waka suke fitowa ba,ai kyau ya bi da wanka,indai wanka ne basu da na biyu,Mummy tace ku gyara gasu Nan dangin tsiya anzo za aci arziki.
Zama suka yi suka nutsu, Spark cikin mota ya koma ya zauna,Goggo tace tafi a hankali Naila,cikin kawayen Umma daya sun rike hannunta sai zuba guda suke ayiririri,Spark yaji guda har kunnensa yace yanzu nasan Amarya ta iso harda Kara sauke glass yace bari naji da kyau.
Kida gaba daya motocin suka saki gaba daya iri daya wakar yan Nija,Rafeeq Yana mota harda rawa a zaune,Yana cewa layi yazo kanmu,Mummy su kansu dariya suke tace wannan yara namu anyi Yan iska, yanzu dan Amarya shine aka sa mana uban kida haka duk sun hanamu Jin kunne, Dangin Amarya suka shiga da sallama ga katon carpet, a nan suka zaunar da Amarya tana zuba kamshi,duk sauran mutanen dakin sun yaba da Amarya amma Banda Mummy ta dai danne ne kawai sabo da Spark kar yazo ya mata tijara,amma da sai ta jefar da magana,amma duk da haka sai da tace ai da baku batawa kanku lokaci ba ma ya dauki abarsa ai mun ganta a gidan nasa tuni tasan har gadon kwanansa.
Goggo tace yo ko ba komai ai tazo ta gaida iyayen Angon nata, ta ganku ku ganta ai wata girmamawa ce daga wajen Iyayen Amarya Hajiya,Badan yace muzo ba ma baza mu zo ba, sai mu wuce dakin mijinta kawai,idan badan zamani ba ma waye yake wani Yan biye biye da Amarya har wajen uwar rainon Ango,wai bama uwar da ta haifi Dan ba,sai zamani yanzu a fara wani biye biye da Amarya ana samu gantali a hanya,Mummy mukus suka yi sunji Goggo ta Maida martani,Mummy taji ciwon maganar Goggo wai uwar raino wato sabo da bata Haifa ba ake mata gori.
Kawar Mummy malamar makaranta ce itama tare suke koyarwa a primary school,tace please arziki ya kawo mu ba wani abu ba,Amarya ce gata nan yarku ce dai,ba wani abu ba, a bude taro da Addua,aka yi addua aka shafa Banda Mummy dake danna waya tana chat da Basiru Kusan ta, wata ce a dangin Ango babbar mace tayiwa Amarya nasiha sosai,tace Allah ya kade fitina kinji.
Naila ta fara kukan karya tana shesheka,su Goggo duk sun zaci da gaske kukan take,harda cewa yi hakuri yar nan kowa da haka ta Saba,Tani tace 'ya mace ai 'yar gidan wani ce, duk haka aka yi mana Naila aure sai hakuri,Goggo tana cewa rabuwa da iyaye ba wasa ba,Allah sarki sabo da gidane da iyaye,ko Kaka 'yar Nan ta tuna ai tayi kuka,Mummy ita dariya ma suka bata yarinyar da suka samu kwance a kirjin mijinta wai yanzu itace take kuka, Mummy tace ai fa Amarya sai da kuka ai,Rayya ce ta taba Naila tana girgiza kafadarta tace ki daina kuka kinji nima zaki sani kuka shike nan mun rabu an raba mu,ta rungume Naila ta fara kukan gaske ita,Naila ta kankame Rayya tana kukan karya,Goggo tace dole kuyi 'ya'yan nan,saurin kuka ne dani karku sani nima Dan Allah.
Mummy baki ta saki tana mamaki tace a ranta amma yarinyar nan anyi Karuwa kaga yar iskar yarinya,yau naga Bariki,lallai bariki iyawa ne wlh,Bariki ba sai an nemi Mazan banza ba,a fili tace to Alhmdllh mun gode Allah ya bada zaman lafiya,sai a kaita can gidan Mima din,suka yi godiya suka mike tuni matan dangin Ango suka rako su da Abinci anyi wrapping dinsa a wasu paper masu kyalli na musamman,ruwan roba da lemuka carton sunfi biyar, Mummy komai sai anyi karya,a bayan mota aka zuba,Amarya kafin tazo Ango ya bude mata ta shugo, yana cikin mota bai fito ba kidansu suke Sha kamar zasu tsaga gidan,Rayya ce ta rufewa Amarya murfin tana share hawayenta na gaske ta shiga mota suka fita sai gidan Mima.
Kidan suka rage sai kadan kadan kowa suke ji a motocinsu,Naila mayafinta ta janye kadan tace na Sha kukan karya kowa ya daka ta Tantiriya zai kashe kansa watarana,Spark yace au Kuka kika yi? Naila tace na karya ba sai bani hakuri akeyi,Rayya mahaukaciya wai kaji ta fara na gaske,Spark yayi dariya yace kin birgeni keep it up,Naila taji dadi ya yaba a ranta tace ka shiga uku idan muka je gida tunda kace naci gaba ai yau kwana zanyi Ina kuka sai na Kara birgeka.
Spark yace saura su Mima Kinga kunkan karya yasa kinyi zufa,driver karo AC,driver ya karo AC yace to shafa wata powder kar aga Amarya da gumi kamar na wani kwalbe,Naila powder ta sake shafawa sama sama ta gyara sosai harda gyara pink jambakinta tace yayi? lekawa yayi yace yawwa,Mayafin ya gyara mata yace badan kayan Nan suna da kyau ba da tuni sun yi dukun dukun a tafiyar motar nan,Naila tace na gaji ma wlh baka ji kafata ba,Yace wannan karki damu da gajiya Hallare zata sauke miki ita tsab,Naila tace sai kace wani magani da ake cewa Daga,tafi Daga ai.
Gidan Mima a cike yake da Yan uwa kaf Maza da mata sabo duk ba a San Amaryar ba,kowa ya baza Ido zaiga Amaryar Spark,za dai muga karyar Spark a Ina ya kare,Badia kanwarsu wacce itama tun daga Bauchi tazo har Abuja da yaranta kawai Dan taga matar Spark wacece,dama idan mutum yayi fice a iya shege da tsirfa to kowa zuba Masa Ido ake aga zabinsa.
Anam tace munzo bikin amma tsabar haushi Bai auri Wahida ba yasa duk muka koma, ko gidansa bamu je ba bare mu ganta, Munji dai ance Yar aikinsa ce,Yar kauye ce ma,tab yanzu haka ma mummuna ce,mazan Nan suna ta dariya suna jira su sha kallon Amaryar Spark,taron na Mata ne amma duk sunki tafiya kamar mayu.
Harda sake kunna fitilun palon,duk ranar da take gari,wani Arham yace tunda naga ko status Spark baiyi da ita ba nasan bata hadu ba, ai gudu yake kar ayi Masa dariya,Dan Allah Mima kuce ta yini a Nan mu ganta sosai zuwa yamma sai a kaita gidansa.
Mima tace ai dama yace anan zasu yini sai yamma za a kaita can,wai ko uban me ake saka Masa a bed masu aiki basu gama hada gidan ba,Badia tace lallai Yaya duk tsadar kayan gidansa? Mima tace ke kuwa zai kawo 'yar gold ya bazai canja komai ba,ai gidan ya koma sabo wlh ya canja komai na gidan,Kuma in Kinga kayan da ya canja sai kin rantse 'yar shugaban kasa ce zata tare a gidan.
Har kofofi duk an canja ke har su globes bai bari ba,ai naje gidan na Sha kallo, nan kusa baza ki samu gida me kyau da aka kashewa kudi haka ba,ni mamaki ya bani ma,mutumin da watarana budurwarsa ta Ghana ta yaudare shi, karshe ya gane kudinsa ta ci kawai, yazo nan gabana yana cewa Mima I swear na gama love har abada bazan Kara son wata ba, tana gwada yanda Spark ke magana,wai budurwarsa ta karshe Lilly?Anam ta tambaya, Mima tace ita fa.
Spark ya Sha wahalar soyayya mata hudu ne suka yaudare shi, Kuma duk da haka gaskiya Banga wacce yake so irin wannan da ya aura ba,cewar Mima,Yana sonta sosai,idan ta kirashi jikinsa har rawa yake,amma waccen kuwa wlh ko sun kira sai yaga dama yake dagawa,kiji Yana musu tsawa,sannan suna yaudararsa idan ya gane zaki ga ya rabu dasu ba wahala Kuma zai ci gaba da rayuwarsa normal kamar komai bai faru ba.
Wannan Naila kuwa akanta zai iya haukacewa na tsorata da Spark akan yarinyar nan,sai yanda tayi da shi,mu da a gabanmu ya fada mana ni da uwarsa Mummy yace ya zama Sallamamme,sai abinda tace,mu ja girman mu idan ba haka ba ko me tayi mana bazai iya magana ba,shi yasa ba ruwana da gidansa,badan ma yace muje muga gyaran gidan ba bazan je ba.
Badia tace to ko dai asiri suka masa kin San 'yan Fulani fa.
Karar motoci suka ji da Uban kida suna zuwa gidan suka saki sautinsu,Mima tace ai Spark ne yayi aure sai abinda kuka gani Kuma,kannen Spark gaba daya kasa hakuri suka yi suka fice Compound kallo,Spark yasan sa Ido suka fito yi,dariya yayi kawai yace wai Dan uwanka ma a zamanin nan bayanka yake so ya Gani,nafi karfin ku yara bazan fado kasa ba always Spark On top ne,Driver ne ya bude masa kofa ya fito ya zaga ya budewa Amarya,Su Badia suna ta kallo tace Uhmmm kofar ma sai ya bude mata sai kace Yar me kudi,Kansa ya zura cikin motar Yana yiwa Naila rada yace,behave well nasan ke Oga ce,Naila kafa daya ta zuro,Kannen Spark harda leke suka hango farar kafa ta Sha lalle me kyau,Anam tace to ai ba fara ce me kyau ba,bakake ma akwai kyawawa wlh sunfi ma fararen kyau wasu,mu a fada mana haske duk danginmu ba baki,Hannunta Spark ya riko ta fito,Kanta a lullube ,Arham yace ai dole dai a bude mana fuskar, Spark Goggo ya mikawa Naila yace Amana,zuwa yamma za a dauke ta,Make shi Goggo tayi tace to fitsararre mu Kuma ayi ya damu? Yana murmushi yace kwana zakuyi mana kuga Abuja gobe a maidaku a jirgi,Goggo tace Dan nan ni bana son na shiga jirgi matukar ba Makkah zanje ba,kawai Dan fitina da asarar kudi a iya Nigeria zamu hau jirgi aradu baza muyi asara ba baza muyi Maka asarar kudi ba,Rayya tace Goggo wlh sai dai ke a Maida ke a mota sai cutar mu kuke yi da tuni a jirgi zamu zo mu koma,Yaya Spark a biya mana zamu hau mu,Spark ya tsaya a cikinsu sai surutunsu suke suna dariya da nishadi.
Yan uwansa duk mamaki ya kamasu mutumin da baya dagawa kowa kafa wai shine tare da Yan kauye suna wani hira da dariya,Badia tace su Spark an fado,Arham yace ni wlh ya birgeni na koma fan din Amarya ma,irin wannan nake nema Ido rufe,Kuma ma ai a kauye akwai Yan birni a birni ma akwai Yan kauye,idan Kuma kunce talakawa ne duk ba da arziki aka haifi kowa ba sannan babu me mutuwa a binne shi da dukiya,Kuma yanzu ta tashi daga Yar gidan talaka ta zama matar me kudi.
Ai kai Arham Dabba ne wa yake ta Kai cewar Badia,su Googo Naila ta rike tace muje ciki,suka tafi ciki a hankali tare da Amarya suna ta guda har cikin palon,Mubarak ne yace sai ka bamu kyautar mu da ka mana alkawari, Spark yace ai dai Kwa bari na shiga dakin Amarya gobe na baku cikin nishadi,Suka ce ba damuwa barshi sai goben maybe ma zaka fi bamu da yawa,yace wai nawa kuka ce ne? 50k muka ce,yace gobe Kuma ai sai 100k sabo da Ina Ango na sak,suka ce a barshi sai goben,suka juya da mota suka tafi har Spark din,Rafeeq kuwa Misam yake wa magana yace
Shi yasa na tsani Yan gidanmu wlh Sam basu da hankali,ji wannan sa Ido haka,Misam yace Kai kake saurarar su ma,wannan Badiar tafi kowa Munafunci sai kace ba yan uwa ba,Kai Ana dabbancin a gidan Nan wlh yanzu zasu saka baiwar Allah a gaba.
Rafeeq ya furta ai wannan daidai take dasu bana jinta Allah yasa idan suka fada musu bakar magana su rama.
Suna shiga tafkeken palon sai kamshi da Sanyi kawai ke tashi,kullum gidan da kida kamar yaran Arna,Palon ma kida suke ji a manyan Speakers sai da suka shiga sannan aka rage kidan sosai amma yana tashi kasa kasa,Goggo tace bayin Allah a kashe mana kida addua zamu yi,sai lokacin Anam ta kashe suka zauna da Amarya a Saman Carpet.
Naila Amarya anci gaba da kukan karya kasa kasa ta wani langabar da Kai anyi kasa da shi tana wasa da zoben hannunta me tsada da Spark ya saka mata a mota,Mima ma Jin Amarya tana kuka tace a ranta amma yarinyar nan muguwar criminal ce,Addua aka yi sosai sannan Maman Rafeeq da tafi dama dama a ciki itace ta yiwa Amarya nasiha,harda cewa Kinga dai shi dan dangi ne ato ki girmama masa yan uwa sannan kema su girmama ki,ayi hakuri da juna, tunda kika ce kinji kin gani kina so dole sai ayi hakuri,Mima tace ya zama dole kuwa,Goggo tace shine dai yaji ya gani yace Yana so Kuma,yo mace ke auren namiji ko namiji ne ke auren mace? Sadaki ya biya wuri na gugan wuri million guda sadaki sannan aka bashi,Yar masu shanu ce fa Wanda suka gaji arzikin dabbobi,Mima kirji ta dafe tace what? Serious fa? Million Daya? Goggo tace ai harda mota sabuwa gal tana can wajen Ubanta yayanta yana boris da ita a cikin gari, yo a dauki wannan zizar a sadaka ne,kallon wannan kawai yayi ai sai ya samu nutsuwa.
Kalleta fa baki ga kalarta bane?ai ba matar yara bace,ku godewa Allah ma da muka baku da wuri ba sai da muka bari ya kwanta a gadon asibiti ba kawo ruwa kawo ciyawa ana so ya farfado.
Dukkansu kallon kallo suka fara Goggo daga magana daya sai fadar magana take musu iri iri,Tani tace Kunga mu ku bamu waje sallah zamu yi,Mima tace Anam nuna musu yanda ake amfani da toilet din basu sani ba na sani,Goggo tace Kalli hakoran mu dukkan mu hakoran Makkah ne a bakunan mu har Yan matan nan su Rayya duk munje Makkah kasa me tsarki,har akwai wata toolet da bamu gani ba,ki tambaya kiji ko da kike zuwa Makkah bakya haduwa da Yan Fulani duk mune ko Ina,wlh babu wani abinda zaku yi bamu iya siya ba,a Daji kawai muke ne, ba rayuwa muka sa a gaba ba.
Mima tace da Haram ba,Goggo tace wlh yarinya ki kiyayeni ba a wasa da Fulani ba a kawo mana raini sai na sa a batar dake duk kudinki,mukus suka yi ba wacce ta sake ko tari sunji tsoro ko su Goggo suna daga cikin criminal basu sani ba,basu San Goggo barazana tayi musu ba kawai.
Tani tace a kawo muku kayan arziki irin wannan iyayenta su yarda da danku suna son Yar su amma suka dauka suka bashi ita Amana,mutum me daraja,yaro ya samu yarinya duniya guda zai samu ya moreta, yayi mata ciki, ta haifa Masa yara amma ku zauna Kuna fada mana magana,Baku da tsari Kai dan Allah ku canja tsarinku, ku canja hali, Sam halin ku baiyi ba,baku yi ba,Kun sire min wlh,nononta kadai aka bashi ya isheshi rayuwa bare a Kai ga lu'u lu'un,duk Yan dakin kunya suka ji Yan matan da samari suka shiga boye dariyarsu,Maman Rafeeq tace Dan Allah kuyi hakuri haka,Tani tace Allah to a dinga zaginmu a fakaice, yarinyar nan fa ba nonon jaka gareta ba bana saniya bane na mutum ne,yau na tabbata bazai bari ta sake ba,Kuma kawai an baku ita kwasha kwasha shine ake zagin mu,jarababben Dan naku ma da naci, in banda kwarzaba me zaiyi yarinya Kun jawo mana asarar kudi sai mun dinga kawo mata magani kar ya lalata ta,Lateefa tace to kuyi hakuri ku taso muje kuyi Alwala.
Maman Rafeeq Hannun Amarya ta rike taji Laushi tace a ranta ba abin kayi magana ba ayi Maka cari,bari na fada a raina laushin nan kamar bata aikin wahala.
Toilet Lateefa ta kaisu cikin wani bedroom hadadde ta shimfida musu Sallaya manya da yawa sannan ta fito suka bar musu dakin suka koma Palo suka fara gulmar rashin mutuncin dangin Amarya,Mima tace Kinga Goggo nan kamar zata dake ni.
Anam tace Kuma da sai kuyi shuru, baku kyauta ba wlh ai ko ba komai suci darajar Spark yanzu sai sunyi ta gulmar a can,Mima tace who cares? suna ta gulma,Arham su mazan jira kawai suke a bude musu Amarya su ganta,Mima tace wannan naci da yawa yake wai gidan Spark din ne Baku sani ba,ba sai kuje ku ganta ba a can,wannan fa taron mata ne,Kun samu a gaba,amma sabo da basa Jin maganar iyayensu kin tashi suka yi,funfurus suka yi a wajen sun zauna a kujeru wasu kuma a kasa.
Su Goggo Sallah suka kasaru ta azahar,Naila ma tayi harda wanke fuska da sabulu tana idar da Sallah ta fara shafa powder tana gyarawa,tayi Yar make up dinta sama sama tayi kyau sosai ta sake shafa turaruka har Jikin kayanta da mayafin sannan Goggo tace ni wai ya naga idon ba alamar anyi kuka ne? Naila tace na rantse kuka na dinga yi na gaske fa,Abbana na tuna ta sake kebe baki,Goggo tace to ya isa kinyi kukanki,tace yanzu karki sake rufe fuska kyale shegu su ganki ai ba mummuna bace,kawar Umma tace yawwa ta Dora mayafin a kanta ta bar fuskar a waje, suna zaune sai ga Anam ta shugo musu da abinci ta ajiye,ta fice da sauri tace na ganta wallahi ta hadu,Badia tace tayi dariya Kinga hakoranta? Anam tace a'a,to rufe mana baki yanzu haka karyayyen hakori gareta,Badia ma ta dauki wani abincin ta shigar musu da shi Dan ta ga Amarya,taci sa'a Naila na magana ta ganta taga hakora masu kyau reras,sai ta fito tace na tabbatar ba karya.
Mima tace ahh Dan fa kyakyawa fa kyakyawa ce gaskiya, magana ta Allah tana da kyau wlh ko ita zata yi kanta baza ta yi haka ba amma fa ba kyan hali bata da kunya,Anam tace bari na sake Kai ruwan nan na ganta again,ta dauka kenan Arham ya kwace wai shi zai Kai,Mima tace je kice su fito Palo zasu fi sakewa,amma ni kar su bata mana dakin yara su fito ato.
Amma kin San masifarsu kice su fito zasu fi sake wa.
Anam ta shiga tace Amaryar mu ku fito Palo wai zaku fi sakewa,suka mike,kawar Umma a ciki tace wlh su Goggo Kun kwato mana yanci sosai,gashi sai lallaba mu akeyi ana Jin tsoron mu,Goggo tace ai ba a bari yanzu Kai ya kulle, ke kyaleni nan zuwa na Makkah sau takwas, a waye nake karrr ba me daga min Kai,wacce shinkafa ce banci a Makkah ba,wanne tayal (tiles)ne ban gani ba,su Tani wlh duk sun je yafi sau uku,haka su Rayya duk an biya musu sun je,shi kanshi Hashimu Baban Naila tun Yana saurayi mahaifinsa ya biya Masa yaje har sau biyu,Umman Naila kanta zuwanta biyu Makkah.
Kawai mutum idan talaka ne sai a manta da yaje Makkah, Alhajin ma baza a dinga fada Masa ba ko Hajiya,me kudi kuwa ko bai je Makkah ba kila ma Amurka yake tafiya duk Shekara,ana tafiya Makkah Ibada shi idan ya hau jirgin Amurka zai ware amma sai kiji ana Alhaji ya dawo ne,Anam tana jinsu tana dariya,Tani tace ai talaka shi kullum sai an nuna Masa bakin ciki a rayuwa, Alhajin ma ko Hajiya bakin ciki ake Masa sabo da bai iya Jin kida ba,bai iya saka damammen kaya ba Yana fitsara yana badala,bai waye ba ake ganin talaka,me kudi ko jahili ne to wayayye ne ai ya waye.
Palo suka dawo Goggo ta Kalli su Arham tace Kai Ina abincin mu na uwar rainon Ango? ni na shige su Maza sun tarar mana a Kai,duk Dan nono na da yayi saura sun kalle min shi,dariya suka yi ba shiri har matan,ke Naila Dan ubanki ki dinga saka hijab Kinga kallon da suke miki ko Ango Bai miki irinsa ba,ni dai Ina ganin bala'i da masifa a gidan nan,zasu cinye Amaryar da Ido,kannen miji ne ku ba kyau wlh,kallon ya fita daga na musulunci,wlh duk sai kunci ubanku idan baku bar palon nan ba,Mikewa suka yi sabo da masifar Goggo badan sun gaji da kallon Amarya ba suka fice, Arham ne ya kawo musu abincinsu na gidan Mummy saura kadan ya taka Goggo bai kula ba,Goggo ta durma masa dundu,ya sunkuya Yana ajiye kayan,tace dan ubanka karya ni zaka yi,tunda muka zo dama naga kana daga min gira Karuwa ce ni? da aure na da komai,Arham Kara ya saki Yana Sosa bayansa ya fice Yana hararar Goggo.
Goggo tace wai a cikin ku wace uwar Angon ne? aka nuna mata Mima,tace shi yasa take ta uban takama,Naila kuwa su Goggo suka yi suka yi taci abinci taki ci,sun rasa dalili,Badia tace idan kunya kike ji ki koma bedroom kici,Naila kamar doluwa wai ita a dole amarya me kunya, tace a'a yace kar naci sai an kaini can gidan,Goggo ta tsaya da cin abincin tace Dan ubanki kashe kanki zakiyi? tun safe Baki ci komai ba sai kinje gidansa,Naila a hankali ta furta ai munyi alkawari da shi ne, ni bazan karya ba,Duk na dakin dariya suka yi,Anam tace tab lallai namiji zaki biyewa? ai kuwa zai kaiki ya baro,wlh wayo zai miki kije ki danni kaza yayi maganinki,Naila taki ci Kuma da gaske Spark shi yace ko zata ci taci kadan karta cika cinkinta ya tanadar musu better.
Goggo ce ta sata gaba tace Dan ubanki muje daki mu zaki wa iskanci,ta kora Naila dakin da suka yi sallah harda rufewa ta mika mata plate din fried rice da hadin salat,ta kawo mata fruits,da ruwa da lemo,tace wlh idan baki ci ba sai naci ubanki a dakin nan.
Naila tace ni za a sa na dinga bijirewa mijina tun yanzu,haka tana ci kamar zata yi kuka sai da taci ta koshi dama yunwa take ji, Goggo ce ta bude Jakarta da wani tsumi a roba tace shanye ragowar,Naila ta shanye tas tace karki sake ya ga wani magin mata a wajenki,Naila tace ai na sani Goggo ai kawai ko me yaji daga Allah ne natural ba Kari, Goggo tace yawwa yar gari,idan Kun Saba ma zaki ga Yana baki kudin kina siya,wasu mazan Kuma da iyayi sai suce ni bana son shaye shayen Nan,ni kawai ki zauna yanda Allah yayi ki,kina zama Kuma wangalewa zakiyi shike nan Kun dinga fada kenan,karshe ko ya fara neman aure ko neman mata,sai an dage da gyara yanzu.
Banda Kuma na hauka ko me aka baki ki Sha ko a dinga baki abubuwa kina matsi dasu ko wanne hauka karki karba zaki kashe kanki,Naila tace to an gama.
Kwanciyarta tayi a Saman gadon tace bacci nake ji,Goggo tace kiyi abinki domin da dare baza kiyi ba 'yar nan.
Naila ta kwanta sai bacci kamar gidansu, Spark ne ya kira wayarta Goggo na dakin ta dauki wayar tace kasa kasa bacci take,Spark yace okay,kar a tashe da wuri gwara tayi abinta yanzu,Goggo tace ubanka Kai fitsararre,wayar ya kashe yana dariya shi masifar Goggo dariya take bashi,gata a waye ba ruwanta.
Spark Chika ya sake kira yace an gama hada bed din? tace ae tun dazu ma har Yan aiki sun gyara ko Ina yanzu kayanta nake shirya mata,yace yawwa Yar Albarka Allah ya baki yayana ko ta biyu ya Kara Dake,Chika tace amma baka kaunata wlh,ni kaninka nake so,Yace to Allah yasa,tace Ameen,yace kin bude kayan Lefen Nan? tace ae yace a kwai Nighty din Nan zaki ganta wata gantalalliya pink,kin ganeta? Chika tace ban gane ta ba,yace wata tsirarar riga haka,wata zaki ganta tafi ko wacce watsewa da tambadewa? Chika tana ta dariya tace na ganta yace to ki ajiyeta a Saman bed ba ruwanki da ita.
Chika ta ninke ta tare da ajiyeta a Saman bed daga Dan kasan pillow kadan ta fada Masa Inda ta ajiye, har su towel duk sababbi aka saka guda biyu biyu komai sabo aka canja,Spark Yana ta waya da Chika yana sata tana shirya kayan da suka dace ba sai an nema ba,Yini tayi tana aikin,abinci sai dai taga an kawo mata take away lafiyayyen da kayan Sha.
Tana gamawa ta dawo aikin Naila itama wannan ba sai sunyi waya ba ta san komai,tana gamawa yamma tayi likis, sallah kawai ke tsaida ta da cin abinci,sai da gidan Nan ya koma neat ko Ina an gyara shi Kal Kal,ta hau turare gidan da kayan kamshi, ko Ina lungu da sako,har makwafta sai da aka raba musu kamshin.
Naila tana ta bacci lokacin dangi ma duk sun tafi sai Yan gida sunce ai a hankali zasu je gidan Amarya ganin gida.
Goggo ce ta tashi Naila tace taje tayi wanka,Naila tace nayi a can ni a kaini haka na gaji muje can ni yayi min wankan da kansa,Goggo Baki bude take kallon Naila tace zaki tashi ko kuwa,Ga kayan da zaki sa kin San komai da kanki kika zaba ma wai ni wacce irin fitsara ce ne wannan? Kya fada min wanka da miji.
Naila tashi tayi taje tayi wanka,suka sake wani hada mata na turare tayi ta fito ta shirya,Cikin Material Dan kasar India tayi kyau dinkin riga da Skert ne,sosai tayi kyau,Kawayen Umma ne Suka tayata shiryawa sannan suka fito kaita suma duk sunyi wanka sun canja kaya,Maman Rafeeq,Lateefa,sai Badia sune suka rakasu domin Ango shi baya African time har ya turo motoci aka kwashe su zuwa gidan.
Chika tayi wanka itama ta canja kaya tana jiransu,suna zuwa duk wata addua sai da suka tsaya aka yi sannan suka shiga ciki a Palo sai da suka yi suna ta kallon gida suna guda,ko Masu kudi suka Kalli gidan sai sun Kara bare talakawa da mutan kauye,za a saka Naila a dakinta tace can ne Goggo waccen ne dakinsa.
Dan Allah ku dinga sharhi
Idan ba a sharhi bama iya typing..
Masu Sharhi Ina matukar godiya.
AsmaBaffa
Post a Comment for "Tantiriya a Gidan Yari Book 1 Paga 81-85"