Rainon Soja 26
*🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story*
26.
*Don Allah kar ki karanta wannan labarin indai baki biya kuɗin sa ba . Ga masu buƙatar payment na littafin Rainon soja ga yanda tsarin yake.... Regular group₦500 Vip group₦1000 SPC payment₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932*
Taƙaici ne ya kama Ma'eesha sai kawai ta cigaba da rera kukan ta don shi zaifi mata Daɗi a yanzu....Tun da babu mafita a tsakanin ta da Haidar abun da yaso ya kuma ga dama shine yake yi , idan yayi niyyar Abu babu wanda ya isa yasa shi ko ya hana shi . Hasbunallahu wani'imal wakeel . Shine kalmar data Furta a zuciyar ta . Jikin ta har ɓari yake yi na tsaban shiga tension . A Zuciyar ta cewa take “ Yanzu shikenan mafarki na ya wargaje kenan na zaman Nurse . Yanzu bani ba wani Aikin Asibiti sai aikin shiga Daji ? , Kai Uncle a cikin rayuwata matsala ne . Kallon sa tayi nan taga hankalin sa ƙwance hannun sa ɗaya na Driving ɗaya kuma na bisa Gyefen Kuncinsa yana Shafa Sajen fuskar sa da ya ƙwanta luffff .... Ji Ma'eesha take tamkar ta kame sajen ta fizga da ƙarfi don a yanzu tafi son taga ɓacin Ransa fiye da Annurin sa , tun da shima Baya son ganin farin cikin ta . Komawa tayi tana kwantar da kanta bisa Kujerar da take bisa kai , tare da kallon gyefen hanya tana lumshe sexy eyes ɗin ta . Tun daga nan babu wanda ya ƙara furta kalma ɗaya sai dai kowannen su da Abin da yake saƙawa a Zuciyar sa a haka har suka isa NDA . Inda a yanzu Da yawa Abokanan sa suke nan da Aiki don sun zama manya . Wasu kuma suna wasu garuruwan na daban . Don shima a gobe yake so su wuce Lagos .
**
Kaiwa da dawowa Hajiya Falmata ta keyi , tana cigaba da Bama ma'aikatan nata umarni . Wani irin Ɗauri tayi shi ya turo gaba ta wani kinkimashi irin na hamshaƙan Hajiyoyin nan marasa kirki Ɗaurin No Respect🤨.
“Oya kuyi maxa a fita dashi , a kwashe Kaman Buhu 100 haka Ina tunanin zasu isa ”. Ta furta zancen tana basu umarnin kwashe Buhuhunan Shinkafa ta Alhajin su . Sudai su Hajiya Turai da Hajiya Atika suna daga Sama suna Ƙallon ikon Allah, kowacce tana part ɗin ta ne , amma idanun su duka na kan inda Ake fitar da Buhunhunan shinkafan nan. Kowaccen su ji take a ranta inama ace itace ta samu irin wannan iko haka ?.
Wani irin tsaki Hajiya Atika tayi kana tace “ Rabi wai Anya kina ganin Aikin Bokan nan yana yi kuwa? Naga har yanzu banda iko irin na Hajiya Falmata ne a cikin gidan nan! Yo kina tsammanin idan da nice na fitar da Wannan Shinkafar zan kwana cikin gidan nan lafiya? Ai da sai dai na kwana a garin Kano ba dai nan ba .
Humm...Rabi ta sauke Numfashi na munafurci da ƙara famfo kana tace “ Ƙwarai kuwa Hajiya shi kuwa Aikin sa keyi tamkar yankar wuƙa , ta ƙare maganan tana fiƙi fiƙi da ido kamar na Ƙaramar kifi ”. A Zuciyar ta kuwa cewa take “ A'a ina ai ba zan yi sakacin da zaki daina aikana Wurin Aruguntsu ba . Saboda nima ina samun nawa ...yanda nake babu miji idan naje muna ɗan jefa zuciya nishadi , don ko aikin ki da yake yi sai ya neme Ni sannan , shi ba kudi yake so ba , Yaji daɗin mace kawai . Kudi kuma nike riƙewa.
To yanzu ya kike gani za'a yi ? Nifa SO nake a haɗa mawa Falmata Masifar da Ayau sai tayi kwanan gidan su ....Don wannan izzar nata da mulkin nata ya fara isa ta haka nan . A'a Ina magana kuma kinyi shiru ??. Hajiya Atika tayi maganan tana kallon Rabi cike da nuna damuwarta .
Allah yaƙarama Hajiya Lafiya tuba nake ”.
Hummm ....jan numfashi Atika tayi tana saukewa kana tace “ Me kika gani? Ya kuma za'a yi yanzu ?”. Ai yanzu Hajiya Zan gudu na isa gurin Aruguntsu amma kin san idan Aikin yanzu yanzu kike so sai an bashi masu kauri .
Wani irin dariyar jin daɗi Hajiya Atika tayi kana tace “ Ai wannan ba matsala bane indai za'a cika Aiki ....! Maza muje ki amsa sai ki wuce . To Hajiya Da girman kujeran ki . An buga Dole a bariki kece ta gaban Gaban Kowa indai a fadan Alhaji ne . Kan Hajiya Atika ne ya kara girma Wani irin cika wuya take yi cike da jin daɗi kana tace “ Kai Rabi wannan kirari haka ”. To ai gaskiya ne Hajiya kin san daga kuma ƙinta sai ɓata ”.
Muje yanzu a kai ma Aruguntsu bana son yau Falmata tayi kwanan sukuni .
**
Kaduna
11:00am.
Tun da suka isa direct Ɓangaren ƴan termer 1 ya nufi da ita . Wani babban fili Ma'eesha ta gani wanda duk abin ka babu karshen ta ,don idan kayi gudu gudu sai dai ka ganka a irin dajikan nan . A can bayan wurin kwanan Ɗaliban Sojan yake nan ne kuma wurin atisayen su.
Kallon Ɗaliban Sojan take yi maza dai sun fi yawa ,don mata bai fi biyu ta gani ba kuma ba Musulmai bane.
“Uncle What I'm I going to do here? , Kalli fa ka gani Wai Soja ka kawo Ni nayi ko girki kace zan rinƙa maka ? . Ta ƙare maganan tana narke masa tare da shirin saka masa kuka 😭 tana yi tare da kallon wani irin murɗaɗɗen Soja da yake ta Aikin Atisayen Motsa jiki da gudu .
Muryar Haidar ne ya katse ta cikin dakewa na ba wasa ya furta “Wanne kika yi choosing? ”. Da Sauri Ma'eesha ta furta “ Mai girkin ka zan zama ”.
Weldone Sir”. Muryar sojojin da sai a yanzu suka farga da isowan canonel Aliyu haidar suna darawa tare da ƙamewa. Gyaɗa masu kai yayi cike da bada umarni cikin ɗaga murya irin na Sojoji ya furta “ Su cigaba da Atisayen su , nan take kowa ya koma bakin aikin sa”.
Kallon Henry yayi kana ya kalli Ma'eesha yana furta “ maza jeki kuyi tseren gudu tare 🥺 Idanun Ma'eesha ne suka juya . Wanda sam ta kasa motsi don ita fa kalallaɓa ce , Wannan wacce irin rayuwa ce , Wallahi nasan ko da nake ƙarama ba ƙaramin wahalar Sa nasha ba .
Cewa nayi kiyi gudu dashi fa? Ya furta kalmar cikin doka Tsawa , wanda jiki na rawa Ma'eesha ta matsa ga Henry...........🤣🤣🤣tirƙashi Jama'a ya kuke ganin Ma'eesha da Wannan rangajejen halittar? Meye mahangarku bisa ga Abun da Haidar yake yi ma Ma'eesha , yana cikin So ne ko kuma ƙiyayya😌🥹. Meye ra'ayin ku bisa ga soyayyar Khalil da Ma'eesha .? Sannan waye ne asalin Alhajin Yes da No🤣 wato mijin su Hajiya Falmata?.
*Don Allah kar ki karanta mun wannan labarin indai baki biya ba . Regular group ₦500 Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan 08081202932#mamanteddy.*
Post a Comment for "Rainon Soja 26"