Rainon Soja 25
*🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story*
25.
Waro idanu waje Ma'eesha tayi tare da furta “ Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un na shiga uku wayyo Mami daddy.....Keeee!! Muryar Aliyu ya katseta cike da doka mata Wani irin gigitaccen Tsawa kana ya cigaba da cewa “ Wayyo Mami kike cewa? Yo sojan ne bakya so ko mene? . Cikin sauri ta katse shi tana gyaɗa kan ta sama Alamun eh ” kana tace “ Na tsani SOJA wallahi Uncle Haidar bana Son mace Soja, yanzu fa kaji Abinda Ya Khalil yace shima baya Son mace Soja. Ohhhh na fahimce ki”....ya furta yana kai hannun sa tare da sosa Gyefen saman cikakken gashin giran sa da Ya kusa haɗewa da Ɗan Uwan sa . Wato Saboda Khalil yace baya sha'awar mace Soja shine Kema bakya So kenan? . Hummm yanzu na fahimta , faɗa mun Son Khalil kike yi ne ko mene? Oya talk to me now . Faɗa mun yanzu!! Yayi maganan yana watsa mata Lulun idanun sa da suka saba rikitata , gashi a wannan lokacin magana yake kaman wanda zai kai mata hannu yasa duka”. Ma'eesha You keep silent? Hummm ya sauke yar taƙaitacciyar Numfashi kana ya cigaba da cewa “ Still you're a child , baki da hankali . To ki sani Bana ƙaunar wata alaƙa tsakanin ki da Khalil , ba Khalil kaɗai ba duka maza nake Miki magana babu alaƙa tsakanin ki da su . Sannan idan ma Soyayya kika fara to ki cire ma ranki do min kuwa karatu zaki yi na tsawon shekara 5 a SOJA kana ki zama cikakkiyar soja . Kin ga daga nan duk inda zani muna tare ....ya ƙare maganan yana kallon ta a kaikaice kana yace “ kar kiyi tunanin wani Abu na daban don na lura Ƙwaƙwalwar ki na juya Miki abun da ba dai dai ba .
Ni kawai kulawa dake nake yi , kuma Alƙawarin haka na Ɗauka , Sannan ina so ki Kaunaci soja a Zuciyar ki dama aikin duka , Saboda soja kaman ki zama , sannan kuma SOJA shine sanadin Rayuwar ki Ma'eesha , Don haka muna isa zan sa a fara baki atisayen motsa jiki . Daga nan kuyi na dambe .😱Uncle Dambe fa kace???? Ta katse shi tana waro idanun ta sai kuma hawaye shar-shar-shar . Wallahi Uncle Ni bana da ƙarfin dambe ban ma iyaba, sannan kuma wani irin Soja kake tunanin zan zama ? Wanne ciki ? Land Army kake nufi? . Yessss! Shi nake nufi . Ya furta a daƙile yana ƙara tattare giran sa . Land Army fa kace Uncle yau ya tabbata baka Sona, Sojojin da ake kaiwa daji a harbe kaman kiyashi kake so Nima na zama ɗaya daga cikin su .?
Wannan nayi niyyar ki zama , ko kina da Jah ko musu akai ne? . Daddy ma ai land Army yake mene kuma ya same shi , gashi har ya zama General a soja .
Kuka ta fashe dashi tana bubbuga ƙafarsa tare da cewa “ A'a wallahi Ni nurse nake so na zama , ba soja zan yi ba . Ai kaima Ba Land Army bane Sojan Airforce ne kai ni kuma nurse nake so na zama . A'a soyayya kika fara.............!
*Kuyi hakuri kwana biyu I'm busy shiyasa kuke ganin update din namu a haka 🙏🏻*
Post a Comment for "Rainon Soja 25"