Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Rainon Soja 24

 *🕊️RAINON SOJA🕊️*

*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*


                    24.




Ya Khalil nifa Æ™aramar yarinyace kai ne fa naji kana yi ma Anti Jidder faÉ—a kan karta fara soyayya! “Yesss”Na sani Ma'eesha, amma tawa soyayyar ba shiririta bane irin nasu . I really......A'a Ya Khalil Anty Maryam fa? Kwanan fa Za'a yi baikon ku . Muryar Ma'eesha ya kuma katse ta wanda har kyarma jikin ta ke yi . Ma'eesha!!! Ya kira sunan ta cikin wani irin Murya wanda bata taÉ“a jin sa da irin ta ba . Hummmm .... Furzar da Huci yayi kana yace “ Ma'eesha Ni SOJA ne , duk Abinda zai saka Soja ya gurfanar da kan sa da Gwiwowin sa Æ™asa ba Æ™aramin abu bane ba , babba ne , wanda girmanta ya kai Akira wannan abun da rayuwar sa . Ma'eesha idan na rasaki numfashi na zai dakata da Aiki . Ina nufin zan zaÉ“i mutuwa da Rayuwa ta😭”. Dam-dam-dammmm Æ™irjin Ta ya buga da Æ™arfi ....cikin Muryar matsanancin kuka ta furta “ Sorry Ya Khalil ina Sonka”. Wani irin baya Aliyu yayi da yake jikin Æ™ofan yana zame hannun sa a hankali duhu duhu na gilma ma idanun sa . Ji yayi jikin sa yayi Wani irin mugun sanyi sam babu Æ™arfi a tare dashi bisa ga jin Furucin Ma'eesha na “ Ina Sonka!”. ZazzaÆ™ar Muryar ta ne ya kuma katse shi tana faÉ—in “ Kar kayi tunanin bana sonka Ya Khalil kome kace nayi maka a shirye nake zan maka shi ”. 


“ Cikin Sauri cike da jin DaÉ—i mara iyaka Khalil ya miÆ™e daga gurfanen da yake , Hannun sa biyu yasa yana tallabo kuncinta ta tare da saita idanun sa yana ÆŠaurawa bisa nata. “Thankyou Ma'eesha , na gode! 


Ya Khalil to Anty Maryam fa? Da.....shii ki manta da Wannan maganan zan Auri Maryam a wannan shekarar ke kuma zan cigaba da dakon soyayyar ki har ki girma ki kai lokacin da Daddy zai Aurar dake , A wannan lokacin zamuyi Aure mu gina Rayuwar mu cikin jin daÉ—i . Kece nake so ki haifa mun Æ´aÆ´a masu kama dake ....ya Æ™are maganan yana ÆŠaga mata gira tare da Sakin mata murmushi kana ya cigaba da cewa “ Zan Auri Maryam ,amma ba zata haihu ba . Kece zan jira ki zo ki haifa mun masu Albarka ”. 


Cike da Yarinta Ma'eesha ta gyaÉ—a masa kai tare da cewa “ Shikenan Ya Khalil zan yi barci yanzu ”.  Alright sweat dream...ya furta yana kama ta tare da nufar Bed É—in ta sai da ta kwanta sannan ya rufa mata bargo yana takawa tare da rage hasken fitilun Bedroom din yana nufar Ƙofar fita . 


Jin takon sa yasa Ali Haidar Saurin barin wurin yana nufa falo . 


A wannan dare a taÆ™aice sam Aliyu ya gaxa rintsawa , zuciyar sa na masa saÆ™a da Warwara . Inda ya kasa gasgata wani É“angare É—aya na Zuciyar sa . Sai dai kafewa da yayi akan cewa “ Khalil na son lalata Ma'eesha ne . Har ya fara tunanin É—aukar mataki da fushin Zuciyar sa ,sai kuma yace “ A'a ba haka zan yi ba , Ni yanzu da zan tafi tare da ita , ganin ta sai yayi masu duka wuya .bare har ya kawo wani zancen shashanci mtsww .  


**

7:35am. 

Mami na hango gaban dressing mirror tana gyara gashin kan Ma'eesha da yake fidda Sanyayyar Æ™amshi , ga tsawo da cika sunan ta kama mata shi ne wuri É—aya amma Tudunshi har yayi yawa gashi ya sauko har gadon baya . Ka rantse da Allah Jinin mami ce itama wato fulani . Riga da Wando ne ta jikin ta ,irin suit masu kyau na mata . Sai mami ta É—aura mata Hijab Æ´ar Æ™arama wanda bai Æ™are sauka kafaÉ—a ba ”. Turare take sa mata tana murmushi tare da cewa “ Yau sai na Lagos . Yessss Mami😄 Ma'eesha tayi maganan tana Wangale mata baki cike da fara'a kaman mai jin daÉ—in tafiyar ,nan kuwa dole ne yasa ta murmushin .  Gyara mata fuska tayi cikin simple make Up Babu Hayaniya. I love my daughter .....Ina sonki Nima Mami ”. Hannu Mami tasa tana rungume Ma'eesha tare da cewa “ ki kula sosai kinji Eaasha na?”............!


**

Dinning room

Tun da Aliyu da Khalil suka zauna babu abin da suke yi ma juna face auna ma juna kallon banza . Duk da shi Khalil na kai Zuciyar sa nesa . Sannan duk abin da suke yi babu wanda ya gane daga gare su . 


Keeee Da Allah kici a hankali ....kaman Ƴar matsiyata wanda suka fito da ga fari? . Muryar jidder ya katse su inda take doka mawa ma'eesha Tsawa cikin FaÉ—a da hantara . A hankali Ma'eesha ta janye Fork É—in da take cin Irish tana Ajewa a gyefe....inda cikin FaÉ—a Mami ta katse jidder da cewa “ Akan ki take ne? Masifaffiyar banza kawai  , Ai sauri take kada Ali ya fara Mata nashi sababin.....ku kiyaye ni duka ”. 



Gummm Jidder tayi tana cigaba da Kai Cuscus bakin ta , ranta a É“ace don bata son tayi ma Ma'eesha faÉ—a Mami ko Daddy su katse ta . 


Muryar General Saleh ne ta katse su inda yake furta “ Kici a hankali Ma'eesha ba zaki bishi ba sai kin Æ™oshi kinyi nakkkk sannan . 


GyaÉ—a masa kai tayi kana ya cigaba da cewa “ Kai kuma Ali ina so nan da 1 mount to 2 mount kafin bikin Khalil ka fidda wacce kake so ka Aura yanda muna gama nashi sai naka . Saboda dukan ku kun isa aje iyali kuna da Abunyi da Æ™arfin ku haka da ArziÆ™in ku ka fahimce ni?. 


Shiru Haidar yayi na yan sakanni don a yanzu shi babu lissafin aure a rayuwar sa , a cewar sa Abin da ake yi ma Auren yana Samun na bati a banza a waje . KuÉ—in sa nayi masa komai don haka baya sha'awar aure a yanzu . 


Aliyu da kai nake yi .....Muryar Daddy ya katse shi inda cikin sauri Aliyu ya furta “ Okay Daddy inshallah kamin lokacin ma , Abun da yasa har yanzu kuka ji shiru saboda Ni ina so na Auri SOJA ce . Ma'ana matar da zan Aura ta kasace SOJA kama na ” . 


SOJA...!!!! 


Duka suka haÉ—a baki wurin furta kalmar ciki har da Daddy da abun bai masa ba sam . Ita kuwa Mami buÉ—an bakin ta cewa tayi “ wow that's very good, Hakan yayi sosai Haidar Nima zan so ganin hakan . Ai hadin yayi ko Janar? . Ta Æ™are Maganan tana duban inda Daddy yake ya saki baki yana kallon ta . 


Kamin Daddy yayi magana ne Khalil ya amshe da cewa “ No Mami Sam baiyi ba . Ni fa babu Abin da na tsana irin naga mace wai SOJA abun ba burgewa sam . 



Hahahaha! 

Wani irin dariya Aliyu yasa wanda duka sai da suka tsaya suna binsa da kallo . Kana ya tsagaita yana kallon Khalil tare da cewa “ I found the solution, Ma'eesha taho mu wuce ”. 


Cikin Sauri Ma'eesha ta miÆ™e tana ma su Mami waving tare da furta “ Dad Byebye! Mami anti jidder sai na dawo ”. Banza jidder tayi mata a haka ita dai ta wuce Daddy suna biyo bayan su har farfajiyar gidan sai da suka fice daga gidan ne sannan suka koma ciki ” . 


Kaduna ya É—au hanyar nufa inda tun shigar ta tayi shiru ta koma kamar marainiya .


Aammm Ma'eesha me kike son ki karanta nan gaba? . 


Muryar Aliyu ya katse ta inda cikin sauri ta kalli inda yake , amma sam idanun sa baya ma akan ta . Cikin sakin fara'a irin nata ta furta “ I want to be a nurse ”. Ba tare da ya kalle ta ba idanun sa na kan hanya cikin bada umarni ya furta “ Ba zakiyi ba , SOJA zaki zama🙀 wannan tafiyar da zamuyi za'a fara baki horon atisayen zama soja........................!




*Don girman Allah kar ki karanta indai baki biya Ni ba . Gama su buÆ™atar wannan littafin regular group suna biyan ₦500 Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932.©Maman-teddy..... YouTube channel@MAMAN TEDDY.* *https://youtube.com/@mamanteddy4123?si=1cwxAAGsGEzYkelS*

Post a Comment for "Rainon Soja 24"