Mai Daki Complete Hausa Novel
SADAUKARWA
Sadaukarwar littafin ta Iyayena ce,
Alhaji Chindo Muhammad Sodangi da
Hajiya Fatima Musa Sodangi, Ubangiji
ya saka muku da alheri ya kuma kara
muku lafiya amin.
TUKUICI
Tukuicin littafin naki ne;
Khadija Chindo Sodangi (Mrs Nasiru
Idiris)
JINJINA
Jinjinar littafin taki ce Amarya ba kya
laifi (Maman Umar) Zuhuriyya Ibrahim
(Mrs Lawal Chindo Sodangi), Ubangiji
ya raya Umar da Imani
FATAN ALHERI GARE KU
Fatima Abdulkadir Kazaure
Hafsat Iliyasu Unguwar Rimi
3
Khadija Usman Nasarawa
Nafisatu Ibrahim Muhammad
Fatima Ahmad Shehu Kaduna
Maryam Muhammad Gusau, Zamfara
Umaima Abubakar Umar
Maijidda Uba Magaji
Na gode, Ubangiji ya saka da alheri
amin.
KUNA RAINA
Hajiya Maryam (Mami) Dan Hassan
Hajiya Jamila Ibrahim Na-Bature
Hajiya A'isha Balarabe (Jazan)
Ubangiji ya bar zumunci amin.
4
Littattafan SODANGI:
Uwar Mijii
Naga Ta Kaina
Rabon Kwado..
Cikar Alkawari
Wayyo Duniya
Yi wa Wani..
Abu Naka...
Mata Ma su Duniya
Nufin Allah
Kifi Na Ganinka...
Daga Kin Gaskiya...
Da Kamar Wuya..
Mai Uwa...
Duk Daya..
Mata Da Kicin Dinsu
Wacece Ni?
Wata Fuskar...
Mijin Ta ce
Garin Banza..
Ga ni Gare ka
5
Biyan Bukatar Rai
Shamaki
Hattara
Mata Masu Duniya
Kyautata
Ayi Dai Mu Gani...
Tabbataccen Alamari
In Kunne Yaji..
Halin Rayuwa
Mai Daki.
Littattafan ba sa nufin yi da wani ko
habaici ga kowa sai dai an rubuta su ne
don fadakarwa da nishadantarwa, ana
neman afuwa ga duk wanda yaga wani abu
yayi kamar abinda ya shafe shi, ba da shi
ake ba dace ne kawai.
6
MAI DAKI.3
Bin ta da kallo suka yi cikin
mamakin irin yadda ta dangwarar
da kula, wannan kuma wacece?
Ina dan murmushin da ban san na meye ba
na ce, yarshi ce.
Fu Suka hada baki Yarshi? Na ce, Eh, ita
ce ta biyun tana da wa yana Makaranta
Dankaci ke ki ce akwai babbar magana
haka suke sakaka babu tarbiyya.
Ban sake cemusu komai ba mikewa
nayi na shiga kicin na debo plates da
cokala na dawo sai ga Larai ta shigo dauke
da wata kular da kato kular ruwa mai
famfo alamar abin sha ne a ciki.
Ta gaisa da su Baba Ladi sannan ta juya
ta tafi. Na bude kular miya da taji naman
kaji ta ukun kuwa kunun aya ne mai kauri.
Na zuba musu na mika musu sannan
nima na zuba naci sosai saboda yunwar da
ke damuna.
7
Sai da muka gama cin abincin ne Baba
Iya ta ce "To kai mu wurin uwar mijin taki
mu gaisa ko 'yannan."
Na mike suka bi ni. A bakin kofar
dakin muka yi sallama ban shiga ba sai da
ta ce a shiga.
Karba sosai tayi musu sannan suka fara
tattaunawa a kan al'amuran aure da
halayya na ya'yan zamani na rashin
kunya da fitsara har suka kawo kan danta
tana basu labarin rasuwar da mahaifinshi
yayi ya bar mata su tun bata fi shekaru
talatin ba a duniya.
Ya barta da Ahmad da Yayarshi Kausar
da a yanzu take aure a Kano wurin dangin
Babanta, da aure-auren da ya yi guda hudu
mata biyu suka haifan mishi 'ya'yanshi
Zaidu da Zainaba.
Sai kuma wata ta haifi Ziradat da
Zinatu, sai wasu biyu da ba su haihu ba.
8
A raina na ce, "Dankari! To me yasa
bai taba gaya mun cewa ni ce matarshi ta
biyar ba?"
Na kawar da wannan tunanin daga
cikin raina, ko bai gaya mun yawan matan
da ya aura ba ai ya gaya mun yana da
'ya'ya hudu.
Shi kenan magana ta kare.
Hira sosai suka y1 sannan suka taso
muka dawo sashena. Hajiya ce tasa aka
mayar da su Baba Ladi gida bayan nayi
musu kyaututtuka daga cikin kayan
aurena.
Kwalliya sosai na sake tsalawa da
yamma shadda danya da aka yi wa wani
irin dinki na Senegal ruwan kofi na saka,
na saka dan kunne fashion ruwan zaren
jikin shadar.
Na feshe jikina da turaruka sannan na
kunna bumer na saka na daki yabi gidan gaba
daya. Karfe shida daidai naji tsayuwar mota a
Wurina.
9
Na leka, Ahmad ne. Na dawo na zauna ina
jiran naga shigowarshi ban ji ba, har aka yi
magriba aka yi Isha'i sannan ya shigo dakin.
Yana kallona ya ce "Wow! Allah na gode
maka da kayi mun baiwa da samun Hauwa' u
a matsayin mata ka bani zaman lafiya da ita
ka albarkace mu da albarka da ka ke yi wa
Ma'aurata.
Murmushi na rinka yi har ya iso in da
nake ya jani zuwa jikinshi ya rungume
ni yana rada mun a kunnena ke baki iya
yiwa mijinki oyoyo ba ne?
Rike hannuna yayi ya jani zuwa wani
wuri da ban kula da shi ba a gidan. Kofa
ce ya budeta muka shiga.
Babban wuri ne, don falon yafi nawa.
Duk wani abu da ke falon faci ne tas tun
daga kujeru har zuwa labule.
Falon ya matukar kawatuwa ba
kadan ba, bai bar ni a nan ba cikin
dakinshi ya wuce da ni.
Wanka za ki taya ni nayi."
10
Na gwalo ido ina kallonshi, ya ce
"Ko ba za ki iya ba?
Nayi shiru, murmushi yayi ya soma
cire kayan jikinshi na kawar da kaina
zuwa kallon wani wawakeken hoton da
ke manne jikin bangon gadon shi na
wani irin ruwa da ke zubowa daga wani
tsauni zuwa wani dan koramai masu
tsuntsaye.
Kafin na juyo har ya shiga bayan
gidan dakin. Mintuna kadan ya sake
fitowa da tawul daure a kugunshi yana
goge jikinshi da wani.
Dauko mun kaya a cikin wardrop
din gabanki. Na bude ina dubawa.
An kakkasa kayan kashi-kashi, under
wears, kayan barci, jallabiya da tract
suit alama na babu kayan fita a wurin na
ce wacce zan dauko maka?
Ya zubo hannayenshi ta kwibina tare
da dora kanshi a kan kafadata har ina
11
shakan kamshin man wankan da yayi
amfani da shi da ke jikinshi.
Ya ce, "Kamshin turarenki mai dadi
Hauwa'u. Ban iya ce mishi komai ba
don ban saba irin wannan mu'amallar
ba.
"Idan ba ki san wacce za ki ba ni ba,
to bar shi haka mana kawai ba shi kenan
ba, dama ai ba fita zan sake yi ba."
Na jawo wata rigar barci da ke can
sama saboda ya sassauta rikon da yayi
mun, na ce "To ga wannan. Ya ce, "To
juyo ki saka mun.
"To ai saika sake ni tukuna
zan iya saka makan.". Na juyo ina saka
mishi rigar tun daga hannu har na daure
mishi belt dinta.
Yayi murmushi ya ce, "Hauwana
kenan." A falon shi muka zauna yana
kallonlabarai yana yi mun yan
12
hirarraki ya ce, "So nake na dan takura
miki kadan."
Na ce,"Wacce irin takura kuma?" Ya
ce, To ban sani ba ko ba za ki ji dadin
ta ba, so nake daga gobe na fara cin
abinciki. Idan ki ka yi mun haka zan ji
dadi."
Nayi murmushi "Nima hakan yafi
mun ai, kamar na gaya mishi haka sai
na fasa. Ya ce, "Ba ki ce komai ba."
Na ce,Yadda duk ka ke so haka zan
yi." Ya ce, "To na gode."
Washegari daga fitan shi sai ga
cefane rigigif babu abinda babu, kaji,
kifi, nama, tumatir, komai dai na
bukatar gida.
Wayata na dauka na kira shi na ce,
"Za a yi na rana ne da za a kawò
maka?'
13
Ya ce, "A'a Hauwa'u wannan Haj1ya
tana sawa a kawo na dare kawai za ki
yi."
Na ce, "To me za ka ci da daddaren?
Yayi shiru zuwa can ya ce, Na baki
zabin yau dai kam ko meye ki ka yi zan
ci."
Tsayuwa nayi ina kallon cefanen da
aka yi, na rasa yadda zan yi na fara
tamfar wacce bata taba girki ba.
Karaf na tuno da littafin Momin
Hindu, shi na dauko na bude ina
dubawa amma na kasa zaben abinda zan
yi.
Da kyar na iya zaben wani da na
gani ina dubawa meat 'tagine' sunan
ne ya yi mun dadi, har nake dubawa
ganshi ba mai wahala sosai ba.
14
Sannan akwai kayan hadin gaba
daya, yanayin yadda naga girkin a
hoto.
Na fara hada kayan amfanin nama,
mangyada, yaji, tattasai, attarugu,
albasa, tafarnuwa, gishiri, maggi,
karas, citta, bawon lemon tsami,
tumatirin gongoni da ruwa.
Nan da nan na hada abubuwan na
rangada miyata mai wani irin kyau da
sha'awa. Na daukó ledar cous-cous
na dafa saboda ganin da nayi da shi
zai dace.
Na kira Momin Hindu ina bata
labarin abincin da nayi. Tayi
murmushi ta ce, "To saura abin sha."
Na ce, To ai ban san me zan yi na
sha ba. A gajarce ta gaya mun.
Ina gamawa na shiga bayan gida
nayi wanka.
15
Yau ma kwalliya nayi ta materia
ya kuma yi mun kyau sosai. Na yane
jikina da babban gyale na dauki
babban food flask din da na zubawa
Hajiya abinci a ciki na dauka nayi
sallama a bakin dakin na shiga, bayan
an ba ni 1zinin shiga.
Na ajiye abincin a gefe na zauna.
Ta kalli food flask din ta ce "Ai ba sai
kin rinka sako abinci ba don ba ci
suke yi ba, sannan ga Larai nan idan
muna bukatar abu zata rinka girkawa,
mijinki kawai ban da mu."
Na kai kamar mintina goma na
tashi na dawo wajena, na kalli agogo
har yanzu karfe shida bata yi ba.
Na gyara kwanciyata a kan
doguwar kujera na kunna TV ina
kallon CCTV Documentry da ake yi
akan wani kabarin tsohon Sarkin
16
Kasar Sin da ya mutu shekaru dari
biyar da suka wuce.
Yau ma Ahmad bai shigo ba sai
bayan sallar Isha'i. A dakin shi na
ajiye mishi abincin saboda wankan da
yake yi.
Ya fito yana goge jikinshi da tawul,
ya samu na ciro mishi riga da wando
na hutawa masu sauki.
Ya dan yi murmushi yana kallona
tare da amsa gaisuwar da nake yi
mishi.
Yasa hannu ya dauki kayan da na
ajiye ishi akan gadon yana sakawa, ya
gama ya riko hannuna.
"Muje ki bani abinci." A kasa ya
zauna a kan kafet yana duba wani
sako da ya shigo wayarshi, ni kuma
ina zuba mishi abinci a plate.
17
Na gama na tsiyaya mishi coconut
juice din da nayi mishi na fara mika
mishi.
Ya karba ya dan yi murmushi ya
ce, "Bismillah zan fara cin abincin
amarya. Nayi murmushin jin abin da
ya ce. Ya kai juice din bakinshi ya
kwankwade ya ajiye kofin a kasa.
Ya kalle ni na dauka madara ce, na
ce a'a ba madara ba ce, ya ce To
menene'? Na ce Juice din kwakwa
ne."
Ya sa cokali ya fara cin abincin
gaba daya muka yi shiru sai da ya
cinye abincin tas sannan ya ce, "To
masallah Allahu, na gode Hauwa u.
Allah ya yi miki albarka, ya kuma
ba mu zaman lafiyamai dorewa.
Abinci yayi kyau."
18
Nasa hannu na kwashe kwanukan
na fitar na kai kicin, sannan na dawo
na zauna. Ya fara magana, "Tunda ki
ka zo ban samu wani lokaci na zaunar
da ke don nayi miki magana dangane
da al'amuran gidana ba.
Amma duk da hakan dai nasan kin
ga abinda ki ka gani na zahiri. Akwai
mahaifiyata wacce idan kin lura za ki
gane ba ni da wanda nake girmamawa
nake kuma so fiye da ita.
A rayuwata ita kadai ce na mallaka
ina nufin mallakar da ban taba wayar
gari na gane na rasata ba.
Ina yi mata soyayyar da bana yiwa
kowa shi a duniya Hauwa'u, don
kuwa nasan itama tana yi mun fiye daa
hakan.
Babana ya rasu ne ya bar ni ban fi
shckaru biyar ba a duniya, amma
19
kuruciyarta bai sa ta barni zuwa wani
mijin ba.
Sai ta zauna da ni da Yata don ta
tarbiyyantar da mu, ta ilimantar da mu
ta hakura ta sadaukar da jin dadin
rayuwarta.
Don haka duk wani abu da ki ka ga
nayi a yau ko na zama a yau din nan
to da bazarta ne. Ina rokonki daki
taimake ni ki zauna lafiya da ita.
Zan iya yin hakuri idan ki ka saba
mun, amma ina da gajen hakuri ta
fannin sabawa mahaifiyata.
Sai abu na biyu, nasan kin ga yara
to ina so ki san ko ni da nake ubansuu
Hajiya bata yardar mun ta bani
yancin shiga harkarsu ba.
ldan kin ga wani abu da suka yi
miki da bai yi miki dadi ba, to na
roke ki da kiyi hakuri, idan kuma kin
20
ga ba za ki iya ba to ki jira ni na dawo
ko menene a lokacin sai ki fada mun.
Ina yi miki wannan maganar ne
saboda ni nasan kan gidana, na kuma
san matsalar da ke cikin shi. Ina so ki
taimake ni na samu nutsuwar da nake
bukata a cikin gidana."
Na yarda da duk abubuwan da
mijina ya gaya mun da kanshi ya
kuma roke ni a kai ina kuma iyakacin
kokarina wajen ganin na biya mishi
bukatunshi.
Gara nake shirya mishi kullum mai
dadi, daga cikin littafin girkina a
kullum kuma bai gajiya wajen yaba
mun.
Haka nan baya gajiya da yabon
kwalliyata, don kuwa kullum a cikinta
nake safe da yamma, matukar yana
gidan.
21
lna son mijina ina kuma son zama
da shi. Zama nake yi na yanci da
walwala. A yanzu ne kuma na gane
me ake nufi da zaman aure.
Zama na hakika ba mai cike da
kunci ba. Zama na sanin hakki da
yancin dan Adam.
A yanzu ne nasan so nasan abinda
kalmar take nufi don abinda nake ji a
game da Ahmad.
Shima burinshi a kullum bai wuce
na ganin ya faranta mun ba. Da
matukar wuya ya dawo gida ba tare
da ya riko mun wani abu ba, wanda
zan yi amfani da shi don kaina ba don
shi ko wani ba.
Iyayena kuwa yana mutunta su
tamfar nashi. To abinda nake so
kenan na kuma samu, zan kuma
jurewa zama da ya' yanshi da
22
mahaifiyarshi kamar yadda ya ce, don
na tabbatar mishi matsayin shi a
wurina.
Watana biyu cif, Ahmad ya ce na
shirya a kai ni gida wuni. Cikin doki
ranar na kama shiri. Tsaraba sosai
yayi mun wanda zan tafi dashi tamfar
wacce take nesa.
Nayi sallama a kofar dakin Hajiya
na shiga a gefe na durkusa na gaya
mata zuwana gida.
Ta ce, Eh mijin naki yazo ya gaya
mun. Allah ya kiyaye hanya, ki gaida
manyan naki. Na fito na shiga mota.
Bala direba ya tuka muka tafi.
Babu wanda bai yi murna da ganina
ba.
Umma ta ce, "Haka fa Allah ke
lamarinsa, ki duba ki gani wannan
auren naki nutsuwarshi ma daban. "
23
Wajen karfe uku Ahmad ya kira ni
a waya. Na dauka "Yaushe ki ke
shirin zuwa gida ne?
Na ce, "Ina ce wai ko za ka bari ne
na yi sallar Magriba tukuna daidai
lokacin dawowarka kenan."
Ya ce, "To abincina fa? Ko zan
zauna da yunwa ne yau tunda nayi
karambanin yi miki gwaninta?
Nayi maza na ce, "A'a yallabai
mu tafi." Ban iya tsayawa jiran
Babana ba na kama shiri.
Tasi'u ne yake ta magana yana
cewa, Zai bini yaje yaga gidana,
Umma ta ce, Aa a wane dalili ka
bari dai a kai ku wani lokacin." Ba
tare da wata fargaba ba na ce a hada
musukayansu shi da Sabi'u.
Wurin Hajiya muka fara shiga, na
gaisheta. Su Tasi'u ma haka, na mike
24
zan fito ta ce mun, "Zo mana. Na
dawo na sake tsugunnawa ta ce, Su
waye wadannan?
Tana nuna su da baki, na ce
Kannena ne. ziradat ta leko daga cikin
dakinsu ta kalli su Tasi'u ta ce, Wai!
Sannan ta kwashe da dariya.
Ta ce, Lallai kuwa. Na tashi bayan
ta bani umarnin tafiya, na dawo
sashena amma ina jin wani abu a
raina maras dadi.
Muka shigo falona sannan na kara
bin yaran da kallo wadanda tuni suka
bi lafiyar kujera suka zauna. Ni nasan
mu ba masu kudi ba ne.
Amma daidai gwargwado Umma
tana iyakacin tawajen ganin ta
tsaftace danta babu kazanta a tare da
shi.
25
Tsarguwar da nayi ita ce tasa na
leka na kira Bala direba na ba shi
kudi na ce ya sayo mun kaya daidai
nasu Tasi'u set bibbiyu wadanda zan
yi musu amfani da shi.
Aikina na fara yi gadan-gadan
saboda kada na makara. Abinci mai
kyau sosai nayi mishi. Sai da na gama
sannan nayi wa su Tasi'u wanka na
saka musu sababbin kayansu nima
nayi wankan nayi alwala, sannan nayi
kwalliyata.
Ka'idar Ahmad shi ne, yana
dawowa zai shiga wurin
Mahaifiyarshi, idan aka yi sallar
Magriba ya dawo zai shiga suyi hira.
Daga sallar Isha'i ne zai shigo
wajena, don haka yau ma hakan ya yi.
Yana ganin su Tasi'u ya sai
murmushi.
26
"A'a'a, ke ki ce yau muna da
manyan baki a gidan nan, amma ba ki
sanar dani ba, ai da na shigo da kayan
tsaraba. To yanzu me ki ka ba su na
saukan baki?"
Na bude baki zan yi magana ya ce,
"A'a bar su kawai su bani amsa.
Suka fara lissafa mishi abubuwan da
suka ci tun da suka zo.
Sai da suka gama ya ce, "Ba ta ba
ku sweet ba, ba ta ba ku Ice Cream ba
kenan kun ga bata iya karbar baki
ba."
Ya jawo wayarshi daga aljihu ya
kira Bala direba ya ba shi kudi ya ce
yaje ya siyo mishi Ice Cream da
candy.
Sannan ya kalleni, "To baiwar
Allah ya ya ki ka samu gida? Nayi
murmushi har cikin zuciyata na ce
27
"Lafiya lau yallabai, kowa yana
gaisheka tare da godiya mai yawa, sai
dai ban ga Baba ba saboda gudun
kadana makara."
Ya mike ya nufi hanyar sashen shi
ina bin shi har muka shiga. Ya tsaya a
bedroom din shi yana tube kayanshi,
ni kuma na wuce bayangida ina hada
mishi ruwan wanka a kwarmi.
Ya ce, Ki koma wurinki kawai
saboda yaran nan na ce to. Ban dawo
ba sai da na ajiye mishi dukkan abin
da zai bukata idan ya fito daga
wankan.
Na dawo dakin inda na bar su
Tasi'u suna nan inda suke, kallon
cartoon din da na saka musuna
Kiddies world suke yi har yanzu.
28
Ban dade da dawowa ba Bala ya
shigo da aiken da aka yi mishi babbar
leda cike da kayan kwalama.
Ya ajiye ya juya na kira shi na debi
mai yawa na ba shi saboda sanin da
nayi yana da yaya suna kuma zaune
ne a boys Quarters din gidan.
Godiya sosai yayi ya juya. Na bai
wa su Tasi'u wanda za su iya ci na kai
saura fridge na ajiye saboda Ice
Cream din kada ya narke.
Ganin da nayi hankalinsu ya yi nisa
yasa na koma wurin Ahmad ya gama
shirinshi har ya fito falon yana
kokarin fitowa na ce, "Ai abincinka
nazo na baka ya ce mu koma wurinki
na ci a can, na ce to."
A falona yaci abincin shi muka ci
gaba da hirar mu, su Tasi'u ma suna
harkokinsu har suka yi barci. Na
29
dauke su naje daya dakin nawa na
kwantar da su na dawo in da Ahmad
yake.
Ya jawo ni jikinshi ya kwantar da
ni a kan kafafunshi yana shafa gashin
kaina.
"Tun da ki ka zo gidan nan ina
kallon ki ba ki taba yin kitso ba." Na
ce, Ai ban san inda za a yi mun
kitson ba ne a unguwar nan."
Ya ce, "Eh mai yi ma su Zainab
tazo tayi miki gobe. Na ce, "To."
A dakinamuka kwana ya ce
saboda su Tasi'u kada a bar su su
kadai. Sammako sOsai yanzun nake yi
saboda karyawar Ahmad tunda na
lura ba son shayi da biredi yake yi ba.
Pizza na mishi na hada mishi da
ruwan lipton saboda complain din da
30
yake yi akan tebar shi da take kara
habaka.
Duk da na gaya mishi ni bana
ganinta. Sai da na sallame shi ya tafi
sannan na dawo na shirya su Tasi'u
cikin sababbin kayansu muka karya
muna 'yar hirarmu cikin raha da ban
dariya suna bani labarai.
Su na tambaya abinda zan girka
musu suka fadaa na shiga nayi musu
muka ci tare sannan na dauko Ice
Cream din su na jiya na ba su suka
sha suka ce mun za su je wasa a waje.
Kamar na hana su sai dai naga kada
na takura su tunda yara ne.
Tashi nayi na nuna musu wurin da
yara suke wasa sannan na dawo
dakina na hau gado na kwanta.
Ban dadc sosai da kwanciya ba sai
ga dan aika daga kasuwa Ahmad ya
31
aiko shi da sakon su Tasi'u. Na karba
ina dubawa.
Kaya ne masu asalin kyau yan
kanti set uku-uku, sai takalma sandals
na asali.
Na ajiye kayan na leka don na kira
su daga nesa na hango su a kan lilo,
don haka na dawo na bar su suka ci
gaba da wasan su.
Ni kuma na shiga kicin don fara
shirin abincin dare. Ihun da nake
jiyowa ne yasa ni saurin fitowa, don
kuwa ya yi mun kama da na Tasi'u.
Sai dai kafin na fita waje har sun
shigo dakin cikin tsananin rudewa na
kwallara kara tare da fadin "Inna
lillahi wa inna ilaihi raj1'una."
Jini ne kawai har ya rine rigarshi
gaba daya. Waje nayi da gudu saboda
rudewa.
32
Daga nesa Bala direba ya hango ni
ya taho cikin sauri "Lafiya, lafiya? 99
Na ce, Zo ka gani. Na taho dakin
har ya zauna a kasa cikin saurin shi
ya sunkunci Tasi'u nima na bishi a
mota ya saka shi zuwa asibiti.
Ban jira dawowansu ba bin su nayi.
Ba karamin jin ciwo Tasi'u ya yi
ba, don kuwa sai da aka yi mishi
dinki a keyarshi a ka yi dressing din
wurin aka yi mishi allurai sannan
muka dawo gida wajen karfe shida da
rabi na yamma.
Har dakina Bala direba ya kawo shi
kan kujera ya ajiye shi. Muryar shi
har ta dishe saboda kuka. Na tsaya a
kanshi ina kallon shi saboda tausayin
da ya bani.
Na koma bandakina na dauko
sandar goge-goge na goge duk jinin
33
da ya mannu a tayels din na saka
dettol na sake gogewa sannan na
shiga kicin cikin sauri don na dan yi
wa Ahmad abincin da zai ci.
Sai dai ko dorawa ban yi ba sai ga
motarshi ta shigo gidan, duk da haka
ban fasa ba saboda nasan ba wurina
zai wuto ba.
Cikin kankanin lokaci na yi mishi
fried rice da coleslaw salad, sannan na
dawona dauki Tasi'u da barci ya riga
ya dauke.
Naje nayi mishi wanka da ruwa
mai zafi saboda ya ji dadin jikinshi,
na hada mishi tea na ba shi sannan na
ba shi magungunan da Likita ya ba
shi.
Naje na kwantar da su ban wani bar
su suka tsaya kallo ba.
34
Ahmad ya shigo lokacin ne nake
wanka amma kafin na fito ya tafi
dakinshi, don haka sai kawai na bi shi
can.
Shi ma wankan na samu yake yi
don kuwa dabi'arshi ce vin wanka, da
zarar ya idar da sallar Isha'i yana cin
abincin shi yana dan kallona.
Zuwa can dai ya kasa yin shiru ya
ce, "Menene ya faru ne amarya?
Na ce "Me ka gani? Ya ce, "Ba
haka na saba ganinki ba. Kamar nayi
shiru don kuwa abin da zuciyata take
ta gaya mun kenan sai dai na kasa.
Abin kawai da na sani shi ne,
Sabi'u ba zai yi mun karya ba, don
kuwa yana wurin da abin ya faru ya
kuma tabbatar mun da Ziradat ce ta
wurgar da Tasi'u akan liie ya ji
wannan ciwon.
35
Na share hawayena da na gama yi
mishi bayani, ya ce "Yanzu yana
ina? Na ce, Ya yi barci. Mikewa
yayi ya taho dakin da nake kwantar
da su har yanzu wata irin ajiyar
zuciya yake yi.
Duk da nisan da barcin shi ya yi ya
zuba mishi ido yana kallon lafcecen
bandejin da aka toshe ciwon da shi,
ya juya ya fita.
Shiru naji bai dawo ba, na mike
zan fita sai na hango shi yana tahowa
daga sashen Hajiya, duk da ban san
me ya faru ba gabana ne ya fadi da na
kalli fuskarshi.
Na kauce na ba shi hanya ya shige
daki ya kwanta, ni ma kwanciyar nayi
ban ce mishi komai ba, tunda shi ma
bai ce mun ba.
36
Washegari sai da ya gama shiri zai
fita ne ya kalle ni.
"Kiyi hakuri Hauwa'u, zan so ki
dauke shi a matsayin tsautsayi duk da
dai nasan ganganci ne kawai irin na
yara."
Na ce, "Babu komai." Ya fita, Na
shirya kamar kullum na shiga sashen
Hajiya don na gaisheta.
Kallon kawai da ta yi mun ne ya y1
matukar sanyaya mun jikina.
Na gaisheta ta amsa sannan ta ce,
Ko da wasa kada ki kuskura ki kara
kai karar yaran nan wurin Babansu na
gaya miki kada ki kara.
Ba a yi mun haka, kada ki shiga
gonata saboda bana son abinda zai sa
na saba miki. Tashi ki bani wuri."
37
Dawowa dakina nayi, nayi
sumukwi nayi tsit saboda sanyin da
jikina ya yi.
Ban yarda na mayar da su Tasi'u
gida ba kamar yadda naso nayi sai da
ya ji sauki sosai har aka cire mishi
bandejin.
Ahmad kuwa siyayya ya yi musu
mai ban sha'awa har da Kekuna ya ba
su, sannan yasa Bala ya mayar da su
gida.
Na riga na saba duk ranar Litinin
da Alhamis Hajiya tana Azumin
nafila, tunda nazo kuma duk da cewar
da tayi na daina saka mata abinci idan
nayi bai sa na fasa yi mata girkin
abincin buda baki a wadannan
ranakun ba.
Tun tana hanawa har tayi shiru,
kasancewar yau Alhamis sai na shirya
38
mata farfesun danyen kifi mai hadi
sannan nayi mata lafiyayyen alcle na
ganye da kunun gyada na danyar
shinkafa.
Na hada wuri daya ina nufin dauka
na kai sai ga wayar Ahmad ya aiko
dan aike na ba shi takardar da ya bari
a kan bed side din shi da ke cikin
dakinshin.
Hakan ne yasa nayi waya sashen su
don Larai tazo ta dauki abincin, sai
aka ce bata nan, don haka na ce
Zainab tazo ta dauka.
Na shiga na dauko wa dan aiken
sakon shi na ba shi, sannan na dawo
na ci gaba da harkokin abincina.
Sai da na kammala komai nayi
wanka nayi kwalliya tare da sallar
Magriba sannan na fito wurin Hajiya
don nayi mata sannu da shan ruwa.
39
Ina shiga Ahmad yana fita saboda
sallamar da aka yi da shi a waje.
Na durkusa gefe na gaisheta tana
amsawa kamar kullum yanayinta ta
kuma yi mun sannu. Na mike zan fito
sai naji an kira sunana.
Na waiwayo da sauri don ganin
mai maganar. Tun da nazo gidan yau
ne naji Zainab tayi magana da ni.
Tana rike da kofar dakinsu da
hannu daya yayin da dayan kuma
take nuno ni da shi.
"Kada ki kuskura ki sake yin waya
ki ce a turo ni ki aike ni kin ji na gaya
miki. Ba na daukan raini idan kin lura
za ki gane tunda ki ka zo gidan nan
ban taba shiga harkarki ba.
Idan me aika ki ke so, to gayawa
wanda ya ajiye ki ya nemo miki." Ta
juya ta koma dakin da ta fito.
40
Ina tsaye a bakin kofar dakin ko
ina a jikina sai tsatsafo da gumi yake
yi.
Murmushi Hajiya tayi ta ce "Kai
Zainab kenan, ina dai yi miki addu'a
Allah ya shirye ki. Je ki abin ki
Hauwa'u rabu da ita."
Na juyo na dawo daki raina a
cushe. Har lokacin da Ahmad ya
shigo na rasa yadda zan yi na saki
raina.
Duk wani abinda na saba yi mishi
na mishi sai dai da muka kwanta
Juyawata nayi na rabu da shi, don
kuwa abin har yanzu yana cina.
Yayi tambayar har ya gaji wai na
gaya mishi abinda ke damuna na ce
babu komai. Ya ce, haka kawai ki ke
mun irin wannan abin.
41
Nayi shiru naga zai ja mun wata
matsala na ce mishi ba ni da lafiya, ya
ce Idan ba ki da lafiya ba za ki yi
magana ba sai kawai ki juya mun
keya?
Juyowa nayi na ba shi hakuri,
sannan aka zauna lafiya.
Duk wani kokari da nake yi na gani
ban shiga sabga r 'ya'yan Ahmad ba
nayi shi, amma hakan bai sa sun bar
ni ba tare da su suna shiga tawa
harkar ba.
Babu ma dai shaidaniya irin
Ziradat, haka kawai yarinyar bata
kwanta mun ba. Gara Zainab bata
kallon inda nake bata yi mun magana
amma ita ko baki nayi to sai tasan
yadda tayi ta yi musu abinda ransu ya
6aci.
42
Duk wanda tayi wa rashin
mutuncinta hakuri nake ba shi tunda
ko a gaban Hajiya ne hakurin zataa
bayar sai ko bin su da take yi da
addu'ar shiriya.
Ba ni da wata matsala daga wurin
mijina, muhimmmin abu kenan a
wajena.
Wata irin iska mai karfin gaske aka
yi da daddare, wacce ta bugo satelite
dish din sashen su ya fado kasa.
A lokacin nan Ahmad baya nan,
don haka ba a gyara ba. Tun da abin
nan ya lalace sai suka dawo kallon su
Wurina.
Ziradat da Zinatu safe, rana da dare
a dakina suke wuni, ba na sawa ba na
hanawa.
Sannan ga su da ciye-ciye duk
abinda suka ci kuma to a wurin za su
43
yar da bawon shi ko kuma su bar
kwanon a wurin ko da wacce irin
shara ko gyara na yi wa gun.
Ban taba daga ido na kalli abin da
suke yi ko na gaji nayi musu magana
ba.
Abin dai da na sani shi ne, ya kusa
wucewa tunda maigidan ya dawo a
jiya da daddare bayan tafiyar da yayi
ta wajen sati biyu.
Na gama aikina tas da yamma na
gyara dakina da na Ahmad na duba
babu wani abin da zan yi.
Don haka nayi wanka na gyara
kaina, nayi kwalliya ta burgewa
sannan na dawo falona da yake ta
kanshi na zauna ina kallon
programme din (Ask Huda) da ake yi
a Huda TV.
44
Kan wata tambaya dangane da jinin
Haila da ake amsa ta wacce ta dade
tana daure mun kai.
Sai kawai Zinatu ta shigo dakin
nan da sauri ta dauki remote ta canza
zuwa kidsco wai zata ga cartoon.
Wani gululun takaici ya taso min,
ban san yadda aka yi na daka mata
tsawa ba.
Na ce, "Meye haka? Dalla can
mayar mun inda ki ka same shi."
Iyakacin abinda na ce kenan yarinyar
nan ta tayi jifa da remote dinnan ya
daki bango ya wargaje.
Sannan ta falla a guje tana kurma
wani irin ihu, sai ka ce wacce ya
yanke wa wata gaba a jikinta.
Wani sabon takaicin ya sake kama
ni, ganin remote din ya ki aiki na
tattara shi na aj1ye.
45
Na shiga dakina na bi lafiyar gado
ina 'yan sake-sakena.
Larai ce tayi sallama ta shigo, wai
in je Hajiya tana kirana. Na fito bayan
na lullube jikina da gyale.
"Me ya hada ki da Zinatu ki ka
bugeta?" Na kalli yarinyar yadda ta
takure a jikin kujera har yanzu kuka
take yi.
Na ce, "Hajiya ban bugeta ba." Na
fara kokarin yi mata bayanin abin da
ya faru.
Ta ce, "Dakata! Kin ga yadda muka
fara zama cikin fahimtar juna? To ba
na so wani abu ya shigo daga baya,
don idan nayi niyyar daukan mataki
akan mutum abin ba ya yi mishi kyau.
Kada na sake jin an ce ko kallon
banza kin yi wa wani da a cikin gidan
46
nan, ballantana har ta kai ga kin saka
hannu a jikinsu.
Ki zauna a matsayinki su zauna a
matsayinsu. Ni bana dukan yarana
tunda ubansu ma a haka na
tarbiyantar da abina.
Duk wanda ya ce ba zai yi hakuri
da su a haka har kafin su fahimci kan
al'amarin duniya ba, to sai yasan
nayi.
Ba na so, kada kuma na sake jin
don sun je wurinki sai kiyi mata haka
har tana sulewa saboda razana? Ai
nan gidan ubanta ne tana da ikon
shiga duk inda take so ta wala."
Na dawo dakina nayi alwala nayi
sallar magriba har aka yi Isha'i ban
tashi daga wurin ba.
Don haka na mike nayi sallar Isha'i
tare da shafa'i da wutiri. Motsin
47
Ahmad naji a wurin shi ne na dauki
abincin shi na kai mishi.
Ina ajiyewa ya ce, "Me ya hada ki
da Zinatu ki ka yi mata irin wannan
dukan? Wato kin gane ko? Ni da ki ke
gani ina matukar tsoron tashin
hankali.
A waje ban huta ba, babu abin da
nake bukata irin na shigo gida dan
hutun da zan yi da iyalina na yishi
cikin kwanciyar hankali da farin ciki
ba.
Menene haka? Tun farko na gaya
miki kiyi kokarin zama ba tare da
wani abu ya hada ki da wani yaro ba,
saboda nima hakuri nake yi da su.
Hajiya kuma ina matukar kokarin
ganin bacin rai, bai same ta ba
ballantana a ce sanadina ne,"
48
Naga fadan nashi zai yi yawa
saboda wani abu bai taba hada ni da
shi makamancin haka ba, a tsawon
zaman da nayi a gidan na watanni
shida.
Na ce, Ban fa bugeta ba." Ya
watso mun ido "Ba ki bugeta ba? Na
ce "Na rantse maka ban bugeta ba."
"Me ki ke nufi kenan? Kina so ki
ce mun Mahaifiyata tayi miki karya?"
Nan da nan na fara kuka saboda jin
inda ya mayar da abin.
Nan take kuma fadan yafi na dah
wai na karyata mishi uwa. Ga gaskiya
nan kiri-kiri jikin yarinya ya rure har
zazzabi ya rufeta amma kina karyata
mahaifiyata.
Mara kunyar yarinya, tashi ki ba ni
wuri."
49
Na tashi na dawo dakina nayi kuka
har na gaji, idanuna suka yi luhu-luhu
saboda rashin barcin da ban yi ba.
Na gama abin karyawa kamar ba
zan shiga sashen nashi ba, tunda
korata ya yi jiya sai naga kada na
karawa kaina matsala.
Na dauka na kai mishi na ajiye na
juyo abina, tunda a da wannan damar
tayin gaba da wani ina dai bin doka
ne kawai. To da haka wanna ya wuce.
Ba karamin taka tsantsan nake yi
da yaran Ahmad da mahaifiyarshi ba,
saboda ina son aurena.
Gashi kuma cikin kankanin lokaci
sai na mallaki abubuwan kadara irin
Su,gold da zinari saboda yawan
tafiyar da yake yi.
Kuma shi mai sakin hannu ne.
matsalata a kullum ba daga shi ba ne
50
sannan babu fashi sai dai idan bai yi
tafiya ya dawo ba sai an ce nayi kaza
nayi kaza.
Ita kuma Hajiya ta ce aja mun
kunne, to garin aja kunnen sai ya
zama tashin hankali, ina batawa
mahaifiyarshi rai.
Sannan babu damar nayi musun
ban yi ba sai laifin nawa yayi yawa,
na karyata mahaifiyarshi, don haka
kullum a haka muke.
A daidai wannan lokacin ne ta
bayyana ina dauke da juna biyu har
na shiga wà ta na uku.
Hakan ne ya matukar takura ni naa
kasa yin Azumin watan Ramadana,
saboda tsananin laulayin da nake yi.
Ba Ahmad ba ma har Hajiya a
wannan lokacin ta sassauta mun, don
51
haka babbar matsala a yanzu
laulayina ne da kuma yaran.
Tunda yanzu ba barina suka yi da
karata wurin Babansu duk da laulayin
da nake yi bai hana ni kiba na murje
ba.
Shirin sallah sosai ake yi don kuwa
gidan ma a cike yake da mutane 'yan
uwan su da suka zo daga kauye da
kuma babban dan Ahmad Zubair.
Wanda yanzu ne muka san juna da,
shi.
Shi kam babu laifi yana da hankali
don Aunty ma yake kirana. Haka nan
nima duk da sanin da nayi suna buda
baki a wurin Hajiya hada mishi nake
yi da Babanshi.
Sannan ganin shi yasa hatta Zainab
ta saurara da wasu abubuwan
ballantana su Ziradat.
52
Zama yazo yayi yana gaya mun
abubuwan da yake so nayi mishi, na
sallah saboda bakin abokanshi da za
su kawo mishi ziyara.
Na ce, To ka bari mana idan nayi
na Babanku sai na diban maka a ciki.
Yayi godiya sosai, take kuma farin
cikinshi ya bayyana, ya tashi ya tafi.
Bai dade da fita ba na fita don
zuwa sashen Hajiya kai mata farfesun
kodar da Ahmad ya aiko ya ce nayi
mata da hannuna.
Na isa bakin kofar tun kafin nayi
sallama naji Ziradat tana cewa, "Ai
munafuka ce tunda gashi har Hajiya
ma yanzu ba ta yarda idan mun ce
mata tayı mana wani abu.
Ni a matan da Babanmu ya aura
duk ita nafi tsana. Hajiya ta ce,
53
"Um'um Ziradat na fa kwabe ki da
irin wannan maganganun."
Shi kuma Zubair cewa ya yi "Ni
banä son irin wadannan maganganun
ban san abinda yasa Baba yake biye
muku ba.
Menene laifin wannan matar? Ko
harkar mutum bata shiga ba za ku
taba barin Baba ya zauna lafiya da
mata ba. Shi kuma ku ke sakawa a
matsala."
Sallama nayi na ajiye mata na fito
na dawo wurina, a raina na ce kwaji
da shi, ni kam nawa auren daram in
Allah ya yarda.
Shiri sosai nayi na sallah mutanen
gidan kaf na basu abinci da abinsha
da su kek din da nayi ba tare da nayi
la'akari da Hajiya tayi ba.
54
Makwabta baki daya sai da na
zagaya su da abinci. Ahmad ne kuma
ya taso keyar su Zainab suka kai mun
rabon.
Gidanmu ma duk da ya aike musu
da nama cikin babban baho saboda
yankan da yayi da kuma shinkafa da
tumatur kwando.
Bai hana ni kai musu abincin sallah
ba wannan kuwa Bala direba na aika.
Da yamma ne baki abokan harkar
Ahmad suka zo gidan hakan ne yasa
sashenshi ya cika dankam ba kadan
ba.
Nima gagarumar liyafa na shirya
musu sinasir da farfesun kafar saniya
sai dambun nama da kek da manyan
donghnut na asali mai ridi.
Sai kwalayen juice wanda na hada
musu duka a cikin wani madaidaicin
55
kwando na Rafia da nayi rafin
dinshi da wata 'yar leda da aka rubuta
iyalan gidan Alhaji Ahmad Rufa'i
suna muku barka da Edil Fitr.
Kuma gaba dayansu ya wadace su.
Shima abin yayi mishi dadi ba kadan
ba.
Ya shigo dakina lokacin da nake
shirin shiga wanka har yanzu
fuskarshi a washe take ya sa hannu ya
dauke ni yana cewa bari nima na taya
ki wankan irin wannan gajiya da ki ka
yi haka.
Duk da dai ni da yunwa ki ka bar ni
na ce, "Haba yallabai na dauka ai
yau ba za ka ji yunwa ba."
Dariya yayi ya fita bayan ya gaya
mun yana jirana idan na gama shiri.
Doguwar riga na saka mai gyale na
dauko abincin a babban tire na nufi
56
falon shi na waje don a nan na jiyo shi
alamar ya sake yin wasu bakin.
Ni kuma ba zan iya jiran tafiyar su
ba tunda na gane yana 1in yunwa.
Wani irin santsi ne ya debe ni gaba
daya na zame na kife a kasa tire yayi
nesa ya kife abubuwan ciki suka
tarwatse.
Karar fashewar abu da salatin da
nayi ne yasa Ahmad tahowa wurin
cikin sauri har ya karaso inda nake.
Ba iya motsawa ba sa hannu yayi
ya dauke ni zuwa cikin dakinshi
tunda daga inda nake nan dinne ya fa
kusa.
"Sannu Hauwa'u."
Sai dai ko amsawa na kasa yi
saboda wani irin gigitaccen ciwo da
nake jiwowa daga gadon bayana yana
hadowa har gabana zuwa marata.
57
Ya juya yana kiran Larai don tazo
ta kwashe barin da aka yi yana kumna
gayawa Hajiya.
Durkusawa nayi saboda murdawan
da yake yi mun da irin azabar da na
ke sha.
Ahmad yana shigowa tare da
Hajiya daidai lokacin dá naji kamar
fitsari yana zubo mun.
Hajiya ce ta fara salati tana karawa,
wannan wane irin mummunan
faduwa ki ka yi 'yannan. Ai jini nake
gani."
*Jini Hajiya?" Ahmad ya fadi
daidai ya kara matsowa inda nake
cikin sauri ya dauke ni zuwa mota
muka tafi asibiti.
Jinin da ya zuban ya yi yawa, don
haka cikin ya lalace wankin ciki aka
yi mun aka sallamo ni da magunguna
58
muka dawo gida wajen karfe sha
biyun dare saboda cewar da Ahmad
yayi a sallamo ni mu dawo gida.
Cikin dan kankanin lokacin da abin
ya faru nayi wani irin ramewa saboda
bakar azabar da na sha.
A daren Hajiya tazo duba ni ta
kuma hado mun da abincin da ta girka
mun, tuwo miyar kuka ta ce na ci na
sha maganina.
Ba karamin jjjaga Ahmad ya yi da
barin da nayi ba, don kuwa shi mutum
ne mai son haihuwa.
A yanzu kuma Zinatu ita ce
karamar 'yarshi, wacce a bana ya ce
mun shekarunta takwas.
Hakanne yasa ni daurewa nayi
niyyar wartsakewa duk kuwa da abin
da ke damuna a zuciyata.
59
Da safe ma Hajiya ta shigo ta
gaishe ni, haka Larai da Bala direba
de matarshi sai Zubairu.
Wajen karfe tara ne Ahmad ya sake
shigowa ya kalle ni, ganin ina zaune a
kan gadon "Har kina iya tashi?
Na dan yi murmushi na ce, "Ai naji
sauki. Ya zuba mun ido tare da
kamo hannayena duka biyu ya rike a
nashi hannuwan yana dan matsawa.
Yace, Kin dai daure Hauwa'u ba
kin ji sauki ba, ki taya ni addu'a
Ubangiji ya ba mu. wasu masu
albarka." Na ce, "To amin."
Yayi shiru zuwa wani lokaci ya ce
"Ina son zama da ke Hauwa'u. Ina
rokonki ki kara hakuri da duk wata
matsala da ki ke fuskanta a tare da ni
ko wai nawa."
60
Ban fahimci inda maganar tashi ta
dosa ba, amma sai na dan yi
murmushi kawai.
Duk kokarina bai wuce na ganin na
nunawa Ahmad cewa naji sauki ba.
Na dan daure na yi kwalliya na sanya
doguwar riga na fito ina lallabawa
zan shiga dakin, shi ne naji maganar
Zubair.
Kamewa nayi na kasa shiga.
"Na rantse Baba naga lokacin da
Ziradat ta saka ai ba zan yi maka
karya ba, amma ina gaya maka ne
don kada wata rana suyi abinda yafi
haka."
Ahmad ya ce "To kai Zubairu me
yasa da ka ganta ba ka ce komai ba?"
Ya ce, "Ai ni ban san da wata
manufa tayi ba. Na juyo. na dawo
dakina saboda na fahimci wani
61
muhimmin abu ne duk da dai ban san
ko menene ba.
Wajen La'asar na rinka jiwo ihun
yaran, sai dai n1 kam ban je ba, don
ban san abinda yake faruwa ba kumna
babu ruwana ko ma menene.
A dakina yau ma na kwana sai dai
tare da Ahmad.
Washegari matar Bala direba ta
dawo gaishe ni tana zaune a kan
kujera muna yar hira saboda
mutuntani da matar take yi da kuma
kokarin shiga sabgata yasa nake dan
hira da ita.
Don ba za ta wuce sa'ata ba.
"Oh ni 'yasu, wadannan yara kuma
ashe sune."
Na ce, Su ne kamar ya ya?
Wadanne yara? " Nayi mata
tambayoyin a tare kuma lokaci daya.
62
"Au, jiya ba ki jiyo ihunsu ba? Ai
Baban ne ya yi musu duka ba na wasa
ba, don wansu yaje ya gaya mishi
cewa ita wannan shu'umar ita ce ta
saka miki abu ki ka fadi."
Nayi shiru ina kallonta saboda jin
abin da take fada, abin dai ya yi
matukar bani mamaki, sai dai duk da
haka ban tanka ba don tsoron halin
mutane.
Shiru nayi a kwance ina tunani me
nayi wa wadannan mutane haka?
Ahmad ya shigo ya nemi wuri kusa da
ni ya zauna.
"Ya ya Amarya me ke faruwa ne?"
Ban ce mishi komai ba sai zuba
mishi ido da nayi. Ya jawo ni jikinshi
yana cewa.
63
"Kin san fa tunda wannan ya fita to
aiki ya koma baya, sabon zubi kumna
zamu yi yanzu."
Daurewa nayi na ce mishi "To,
amma dai ai ba yanzu ba ko?" Ya ce,
"Eh to, ko gobe tunda Likita ya ce
bari ba a wuce kwana uku, ko ba haka
ba?"
Wartsakewa nayi saboda
farantawa maigidan rai na nuna mishi
naji sauki don hankalinshi ya kwanta.
Haka nan kuma abubuwa sun
matukar yi mun sauki ba kadan ba,
tunda dai yanzu zan iya ganin Ziradat
a hanya ba tare da ta ja mun tsaki ba.
Abin har mamaki nake yi, wai 'yar
karamar yarinya mai shekaru goma
sha uku ce ta ke irin wannan abin.
64
Lokacin komawan Zubair
Makaranta ya yi, don dama hutun
nasu ba mai yawa ba ne.
Tambayar shi nayi abinda yake so
nayi mishi na tafiya. Ya yi shiru yana
'yan tunane-tunane.
Ya ce, Ai ba na so ne Baba ya ji
zai ce na cika fitina, tun da ana siya
mun komai."
Na ce, "To fada mun ba zan bari ya
ji ba." Ya ce, "To ina son kek irin
wanda ki ka yi da sallah."
Na ce, "Sai me?" Ya ce, "Ko shi
kadai aka yi mun Aunty na gode. Na
ce, "To shi kenan.
Cefane sosai nasa aka yi na kira
Larai muka yi aikin tare. Cincin nayi
mishi mai yawa, nayi mishi kek na
sassaka su a leda daidai saboda kada
su bushe tunda Makaranta ce.
65
Sai dambun naman da nayi mishi
cikin babbar roba fara.
Ana gobe zai tafi na ba shi tsalle ya
rinka yi kamarzai yi ya ya don murna.
Sallamaa muka yi mai dadi ya kumaa
roke ni idan Babanshi zai je mishi
visiting na raka shi muje tare, na ce
to.
Da yamma ne Ahmad ya shigoo
bayan ya kai shi Makaranta ya dawo
na kawo mishi ruwa mai sanyi yasha
sannan ya yi hamdala ya ce "Zubairu
ya ce na sake yi miki godiya."
Ban saurare shi ba kicin na koma
na hado mishi fruit salad na kawvo
mishi, ya karba yana sha ya ce "To ni
ina nawa dambun naman?"
Na kalle shi na gane da gaske yake
yi na ce "Ban ajiye maka ba saboda
ya ce ba ya so ka sani."
66
Ya dan yi murmushi ya ce, "Haka
ya gaya mun, to amma kuma sai ya
kasa yin shirun ya fada mun da
kanshi.
Kin san alheri komai kankantarshi
yawa ne da shi, to ballantana irin
wannan."
Na ce, "Kai dai don Allah bari zuga
ni, ai ba da kudina nayi ba a cikin
cefanen gida na saka."
Ya ce, "Ko ma dai ya ya ne ai
cefanen gida idan wata ce ba za ta yi
ba, ina so kuma na gaya miki cewa ba
Zubairu ki ka yi ma ba ni ki ka yi ma,
zan kuma tabbatar. ban mance
alherinki ba."
Komawar Zubairu Makaranta sai
abubuwwa suka sake rincabewa. Ashe
dama sun bari ne don sun gane yana
kai kararsu wurin Babansu.
67
To yanzu ba ya nan sun ci gaba
daga inda suka tsaya. Sai dai Ziradat
ta riga ta tsorata saboda dukan da
Baban ya yi mata a kaina.
Zainab ce take nuna mun salo iri-iri
na rashin kunya da kuma nuna 1sa,
amma na danne zuciyata ko kallon
iya-shegenta bana yi.
A daidai nan ne kuma wani sabon
laulayin ya kama ni, watanni uku
bayan barin da nayi.
Amma a hakan na tsaya tsayin daka
wajen ganin na gamsar da mijina duk
wata lalura tashi.
Kullum nayi mishi maganar zuwa
gida sai ya yi mirsisi ya hana ni, ya ce
ba na yi mishi adalci da yana gari
amma sai na tsallake hidimominshi na
tafi gidanmu.
68
Na ce, To ai kai da rana kana
kasuwa, da daddare ne ka ke dawowa
gida ka bar ni mana naje da rana na
dawo kafin lokacin dawowarka gida?
Sai ya ce, Wai a'a yafi son idan ya
tuna ni a lokacin da yake kasuwa ya
rinka tuna ni a cikin gidan shi ina
harkokina.
Kallon Ahmad kawai nayi nayi
murmushin takaici, amma a raina
tunda ba ni da abin yi a kai, ba na
musu dashi koda kuwa hukuncin da
ya yanke bai yi mun dadi ba.
Hakanne yasa da yazo tafiya Kano
gaida kanin Babanshi da ya yi rashin
lafiya, tafiyar kwana daya sai na tuna
mishi da zuwana gida.
Ya ce, Ba ki fa da lafiya Hauwa'u.
Na dakatar da hada mishi kayan da
69
nake y1, na ce "Haba yallabai, ba
haka muka yi da kai ba fa."
Ya ce, "Eh na sani, amma ai
wannan karon tafiyar tawa ba mai
jimawa ba ce, kwana daya zan yi."
Na ce, To ni ai tawa tafiyar wuni
ce. Shiru yayi sai da ya fita wurin
Hajiya ya dawo sannan ya ce naje
gidan yau Bala zai kai ni."
Nayi tsalle don murna ya ce, "To
kin gani ba. Nayi-nayi da ke ki rinka
kula da irin wadannan abubuwan kin
ki kanmar kin mance da abinda ya
same ki wancan karon."
Ahmad yana tafiya nayi shirina tsaf
na rufe sashena na fito na shiga wurin
Hajiya don nayi mata sallama.
Sannan na fito harabar gidan na
samu Bala har ya yi warming din
mota ni yake jira.
70
Sai kawai ga Zainab da Ziradat sun
fito su ma za su je unguwa. Kai tsaye
suka nufi motar za su shiga.
Bala ya ce, "A'a Zainab kada ki
shiga motar nan, Hajiya zan kai
unguwa a ciki."
Tayi mishi wani wawan kallo.
Akwai wata HHajiya nc a gidan nan
baya ga wacce dama can na sani? Ina
tsaye a gefe ina kallonsu ban tanka
ba.
Ita dai Ziradat ta dan nutsu duk da
dai nasan ba wani hankali ta kara ba.
Zainab ce da Bala dircba suke ta
jayayya ya shiga mota ya tuka ya ki,
ita kuma ta fita a motar ta ki.
Ziradat fita kije ki kira mun
Hajiya. Ba a wani jima ba sai ga
Hajiya ta iso wurin cikin hijabinta.
71
"Lafiya?" Ta kalli Bala dircba. Nan
da nan ya fara yi mata bayanin abinda
ke faruwa.
Hajiya ta kalli Zainab ta ce, "To ke
Zainaba ku shiga mana idan aka
sauke ta a gidansu sai a kai ku taku
unguwar ba shi kenan ba."
Nan take ta fashe da kuka ita
gaskiya ba za ta shiga mota da ni ba,
bayan ba sonsu nake yi ba.
Na kalli Bala na ce, "Bala idan ka
kai su ka dawo kayi mun magana.
Ya ce,"To Hajiya. Na dawo na shiga
dakina na zauna.
Ban san yadda zan yi da yarannan
ba, abinda na sani shi ne bana kin su.
Na zauna kato-kato ina jiran Bala ya
dawo da su Zainab mu tafi bai dawo
gidan ba sai wajen karfe hudu da rabi.
72
Har sashena ya iso yayi sallama, na
ce "Kun dawo Bala? Ya ce, "Eh
Hajiya kiyi hakuri zai fara yi mun
bayani na ce a'a Bala babu komai je
ka kawai."
Ya tsaya zai ci gaba da ba ni
hakuri, na ce ba fushi nayi ba Bala,
amma kaga gidanmu zan je yanzu
kuma yamma ta riga tayı, ya ce to
Hajiya na gode.
Washegari ba ni da halin fita tunda
Ahmad zai dawo gida a ranar, don
haka tashi nayi don nayi mishi shiri.
Da aikin wurinshi na fara. Na
wanke bayan-gida, nayi shara ko ina
fes sannan na canza labilayen dakin
gaba daya na zuba wasu na kira mai
wanki na ba shi.
Na sake shimfida ko ina ya yi kal,
sai kamshi kawai. Na dawo sashena
73
na shirya mishi abinci na yi mishi
fruit salad sannan na shiga bandaki
nayi wanka nayi kintsi na sosai.
Nayi kwalliya mai kyau ta riga da
siket, ina gamawa ko sai ga isowar
motarshi cikin gidan.
Sai da ya shiga wurin Hajiya kamar
yadda ka'idar shi yake, sannan ya
shigo wurina da gudu na isa inda yake
na rungume shi ina mishi oyoyo.
Yana dariya ya ce, Anya Hauwa'u
ce kuwa ba canje aka yi mun ba da ba
na nan?
Na ce, Canje kuma 'Yallabai? Ya
ce, Eh mana naga ne sai wani
danyacewa ki ke yi kina dawowa 'yar
karamar yarinya.
Sashen shi muka shiga don ya yi
wanka, yana ganin irin gyaran da na
yi wa wurin ya ce, "Wow! Ke da
74
waye ku ka yi wannan aikin
Hauwa'u?
Na ce, "Da waye ka ke tsammanin
zan yi?" Ya dan yi shiru zuwa can ya
dan kada kai ya ce, "Ke kadai ko?"
Na ce, Yauwa ashe ka gane kenan?
Ya ce, To Allah yayi miki albarka. Na
wuce shi na shiga bandakin shi ina
hada mishi ruwa da turarukan wanka.
Ya shiga ni kuma na fito na ciro
mishi jallabiya ruwan kasa saboda
sanin da nayi zai fita zuwa Masallaci
idan anyi magriba.
Yana cin abinci ina zuba mishi
yana ba ni labarin garinsu da mutanen
garin.
Ya ce, "Sai kin haihu zamu je su
ganki suga abin da muka samu. Ya ce
kin ga ma na manta jiya da muka yi
waya ban tambaye ki su Umma ba.
75
Na ce, Ai ma ban je ba. Ya kalle ni
ya ce, Ba ki je ba kuma? Na ce, Eh. to
saboda me? Nayi shiru ban ce mishi
komai ba.
Ya ce, Ke dinnan fitanarki yawa ne
da ita, da ban bar ki ba da har yanzu
kina yi mun mitar na hana ki zuwa
gida.
Ya fita sallar Magriba ya wuce
wurin Hajiya, bai dawo ba sai da aka
yi sallar Isha'i sannan ya shigo.
Tashi ki shirya muje gidan tare.
Sannan ya wuce sashenshi. Ya dawo
sanye da jamfa da wando na yadin
material din maza yana rike da
mukulln mota a hannunshi.
Ni ma yadin material na saka mai
hadari ya kuma yi mun kyau sosai.
Muka fito tare muka shiga wurin
Hajiya don yi mata sallama.
76
Ta ce, lna zuwa haka a daren nan?
Ya ce, "Yar wata unguwa zata raka
ni. Ta ce, To a dawo lafiya. Muka
fito.
A wani babban shago ya tsaya ya yii
siyayya mai yawa, sannan muka wuce
gida.
Hira muke yi sosai da Umma shi
kuwa yana wurin Babana ba mu dawo
ba sai wajen karfe goma na dare.
Tashi nayi naga jini kadan-kadan
yana fitar mun, sai dai ban kula na
gani ba sai bayan da Ahmad ya tafi
kasuwa.
Bana son daga mishi hankali, don
haka nayi nufin bari sai ya dawo naayi
mishi bayani.
Nayi ta aikace-aikacena ba tare da
wani abu a raina ba, tunanina dai bai
wuce laulayi irin na ciki ba.
77
Sai da na gama ayyukana na shiga
bayan gida da nufin yin wanka, sai
kawai na ganni kace-kace cikin jini.
Sauri nayi na fito na dauki waya na
sanarwa Ahmad cewa ina son Zuwa
asibiti, ya ce lafiya? Na ce ch, ba na
dai jin dadi ne kawai, ya ce to Allah
ya sauwake.
Bala ya kai ni asibiti sai dai tun
kafin nan a takure nake cikin sauri
aka kai ni dakin Likita sai dai gwajin
farko ya tabbatar mana cikin ya
lalace, ya fita daga mahaifa dole a
cire.
Duk da halin da nake ciki a haka na
daure na kira Ahmad.
Cikin kankanin lokaci ya iso
asibitin, sai dai duk da saurin da ya yi
har an shigar da ni don wanke mun
mahaifa.
78
Duk da kokarin da nayi tayi na
hana kaina kuka kasa daurewa nayi da
Ahmad ya iso kaina.
Wannan karon ma bari nayi na ciki
wata hudu har da sati biyu, kamar dai
wancan kenan.
Kwana nayi a asibitin kowa kuma
yazo duba ni har daga gidanmu.
Likita ya shigo saboda sallama ta da
za a yi Ahmad yana yi mishi wasu
yan tambayoyi.
Ya ce, To dai a fayil dinta na ga ta
samu matsala makamanciyar wannan
shima a watanni hudu, don haka
tunda ga abinda ka fada zamu sake yi
mata scarming don mu gani ko da
matsala.
Likitan ya jawo wata 'yar takarda
yayi rubutu ya bamu. Ahmad ne da
kanshi ya kai ni wurin scarning din
79
muka dawo Likita ya duba ya ce, "To
a gaskiya ta samu matsala ne a
mahaifa saboda jijigar farat-daya da
mahaifarta tayi a wancan karon.
Saboda irin faduwar da tayi, hakan
ne yasa mahaifarta ba za ta iya rikke
wani ciki da zai yi fiye da watanni
hudu a mahaifarta ba.
Saboda bakin mahaifarta da ya riga
ya bude. Kuma shawarar da zan ba ku
a yanzu shi ne, kafin a san matakin da
za a dauka a kan matsalar, ta dan yi
hutu.
Don kuwa idan tayi wani cikin ma
a yanzu abinda zai faru kenan.
Dawowa gida muka yi jikinmu a
sanyaye, ni kam Ciwo ne ya rufe ni
jinya sosai Ahmad kwata-kwata ranar
bai fita kasuwa ba.
80
Bai kuma fadawa kowa abinda
Likita ya ce ba. Kwana biyu ko
abincin da zan ci daga wurin Hajiya
ake kawo mun.
Kullum kuma Ahmad zai ba ni
hakuri saboda lurar da yayi na dan
saka damuwa a raina.
Duk kokarin da nayi kada ya
fahimci wani abu kasawa nayi. Yau
ma yana zama zai fara mun magana
kuka na kama yi.
Sai da nayi ya ishe ni sannan na
share hawayena, babu abinda ke tsaya
mun a rai naji zuciyata ta baci irin na
tuna 'ya' yan Ahmad ne suka yi mun
wannan sanadin.
To tambayar ita ce, shin idan da ni
ce nayi wa wani a cikin su haka anya
zan zauna lafiya kuwa?
81
Amma gashi nan ni sun yi mun sun
zauna lafiya, sun ma mancc in ban da
shi Ahmad da yake ba ni hakuri.
Duk da warkewan da nayi a duk
lokacin da na tuna ina jin wani iri na
kuma kasa sakewa nayi harkokina
kamar da.
Ko shi Ahmad din ya lura ya gane
hakan, don yau ma muna zaune a
falonshi muna kallon labarai ya Juyo
yana kallona.
Hauwa'u magana nake so nayi
miki. Na lura duk tsawon lokacin nan
har yanzu ba ki saki jikinki ba.
Na kuma tambaycki shekaran iya
ko wani abu na damunki ne kin ce
a'a, lafiyarki kalau.
Ina so ki san wannan abun ba ke
kadai ya samu ba har da ni, amma
82
kuma kin takura ni na rasa walwalar
da a da nake farin cikin samu.
Idan ni ne nayi miki wani abu ki
gaya mun na gyara, idan kuma a kan
matsalar nan ne ina so kiyi hakuri.
Ina kokarin a wannan watan da zai
kama idan zan yi tafiya mu tafi tare
saboda wannan matsalar, sai ki ga
Likita a Dubai."
Ban ce mishi komai ba, amma nayi
kokari wajen ganin na rage takura ko
don saboda Ahmad.
Sai dai har karshen wata yazo ya
wuce Ahmad bai yi tafiyar ba, bai
kuma ce mun komai ba.
Muna kwance a dakinshi da
daddare a daren da ya dawo daga
Legos dauko wasu kayan shi da suka
shigo.
83
Nayi mishi maganar tafiyar da ya
ce zamu yi don ganin Likita. Ya ce,
"Kiyi hakuri Hauwa'u, ina nan ina
wasu shirye-shirye ne kawai."
Sai dai ba a wani jima ba ya shirya
ya tafi Dubai ya dawo ba tare da ya ce
mun komai ba.
Na shiga dakinshi na same shi
zaune ya baje takardu, lissafi yake yi.
Na zauna a gefe ina jiranshi ya gama
shiru bai gama ba har na gaji' na mike
na kwanta nayi barci.
Washegari tun da Asuba yayi shirin
shi gaba daya alamar daga wurin
Hajiya zai wuce.
Haka ina ji ina ganin babu yadda
zan yi ya fita. Da daddare kuwa da ya
dawo sai da na gama mishi komai
sannan na kwashe kwanukan.
84
Wai kafin naje na dawo nayi mishi
maganar da ke Cina a zuciyata nan ma
dawowa nayi na samu wai Hajiya ta
ira shi.
Zama nayi daram a kan kujera ina
jiran shigowarshi, bai shigo ba sai
wajen karfe goma da kwata.
Har yanzu ba ki yi bacci ba?" Na
ce, "Eh kai nake jira." Ya ce, "Akwai
magana kenan? Na ce, "Eh."
Ya gyara ya kwanta ya ce, "To ki
barta gobe kafin na fita kasuwa sai
muyi."
Na ce, Idan kuma a wurina tana da
muhimmanci fa? Ya ce, "Komai
muhimmancinta ki barta sai gobe, don
a yanzu na gaji."
Wani irin gululun bakin ciki ne ya
tokare mun makogorona. Da kyar
nake iya numfashi.
85
Tashi nayi na dawo dakina na hau
gadona na kwanta. Sai dai ban iya yin
barcin ba.
Ji nake yi kamar na koma na samu
Ahmad muyi duk wacce zamu yi da
shi daren nan amma ba zan iya ba.
Ko wani sauraron shi ban yi ba da
safe haka nan shi ma bai bukaci ya ji
maganar da nake son yi da shi ba.
Da dai ya gama shirinshi ne zai fita
ya leko dakin.
"Hauwa'u ina son burabusko da
miyar bindi". Na ce, To babu tsakin
shinkafa." Ya ce, "Ki karba a wurin
su Hajiya." Ya tafi.
Babu abinda na tsana yanzu a
rayuwata irin zuwa wajen su Hajiya.
Tun da dai gaisheta ya zama mun
dole, to kullum da safe ina zuwa
86
amma baya ga haka bana komawa sai
wata safiyar.
Sai da aka yi sallar Azahar sannan
na dauki roba na shiga wurin Hajiyan
na gaya mata ina son tsakin shinkafa.
Ta kalli Zainab ta ce, "Zainaba
tashi ki debowa Mamanku tsakin
shinkafa."
Ta dago ido ta kalle ni, sannan ta
ce, "Maman wasu dai Hajiya, ammna
ban da mu."
Ta ce, "To naji bana dai son rashin
kunya, karbi ki debo mata. Kin dai
kusa tafiya Makaranta a huta."
Ta ce, "Ai idan na ganc tafiyata zai
sa wasu murna ma sai na cc na fasa."
Ta dawo da tsakin a hannunta ta
dangwarar a kasa.
Ban tsaya sauråronta ba, dauka
nayi na yi tafiyata.
87
Zainab a yanzu ta rubuta
jarrabawarta na gama makaranta
sceondary, Jami'a ake neman mata
har ma an samu.
Dawowa wajena nayi na shiga
kokarin ganin na kammala cikin
lokaci, kuma nayi sa'a yayi kyau ya
yi dadi.
Ga kamshi ko ina a cikin gidan. Ina
gamawa na shiga bandaki nayi wanka
na fito kenan naj1 motsi a falona.
Don haka na fito falon bayan na
sanya zulumbun hijabina don ganin
ko waye.
Zainab ce rike da tircn abincin
Babansu, gabaki dayan shi zata fita.
Sa hannu nayi na rike na ce "Yau
kam a'a, abin ya ishe ni haka ba zai
yiwu ba.
88
A duk ranar da ki ka ga kina da
bukatar cin abincina to rinka gaya
mun sai na rinka saka sanwa da ke.
Ba haka kawai idan na gama girki
ki saka hannu ki sunkuci na mijina
kiyi gaba ki bar ni da dora sabo ba."
Ta zuba mun ido tana kallona, nimna
ita nake kallo, don na lura su gaba ki
dayansu ba su san zuru ba.
Kuma a gaban kowa sai Zainab ta
caccaba mun magana ba za a ce
komai ba.
Ba tun yau ba lokuta da dama sai
na gama abinci sai tazo ta sunkuta
gaba daya ta tafi da shi wurinsu ta ci
1ya cinta ta rabar da saura.
Wani lokacin ma ko rabi ba a ci sai
ta bar shi haka ya lalace, sannan ba za
ta dauko kwanukan ta dawo da shi ba
sai dai ni nabi bayan su.
89
Sau daya Hajiya bata taba yin
magana a kan hakan da take yi ba,
duk da tasan abincin danta Zainab
take dauka.
Kallon da take yi mun ne ya ishe ni
nayi nufin karbe tiren, sai kawai
yarinyar nan ta kabar da tiren gaba
daya abubuwan ciki suka watse.
Abincin ya zube a kasa, sannan tayi
murmushi ta raba ta gefena ta wuce.
Zubawa abincin da ya tarwatse din
ido nayi ba na ko kyaftawa.
Ban taba ganin danyen rashin
mutunci irin wannan ba.
Cikin dakina na koma na sanya
doguwar riga na futo zuwa wurin
Hajiya don na gaya mata abinda ke
faruwa.
Na shigo na zauna a kasa zan fara
magana sai ta ce "Dakata! Yau kuma
90
abin naki har ya kai ma ki hana
Zainaba abinci?
Ta dauko kuma kin biyo ta kin
kifar. Me ki ke nufi da abinda ki ka
yin?
Kin taba siyo abinci kin shigo da
shi gidan nan ne da ki ka samu damar
hana wani?"
Na ce, "Hajiya..". "Bana son jin
komai daga bakinki, nasha gaya miki
ba sau daya ba ba sau biyu ba cewa
duk abinda za ki yi a gidan nan to ya
tsaya tsakaninki da wasu amma kada
ki tsallako hurumina, don ba za ki ji
da dadi ba.
Ya ya za ki hanata cin abincin da
ubanta ya kawo ya ajiye takamar kina
matarshi?"
91
Tun ina daurewa bacin raina har
ban san sanda na fara zazzago
maganganu ba.
"Ai tun farko da nazo gidannan na
fara kawo abinci sashen nan aka ce na
daina don kuwa akwai mai girki.
Me yasa tunda haka ne idan tana
son abincina ba za ta fada mun tun da
wuri ba sai na girka da ita, sai ta bari
na gama tazo ta dauke gaba daya
haka ake yi?
Duk hakurin da nake yi da yarann
nan bai isa ba kullum kokarinsu bai
wuce na ganin sun kure ni ba.
Menene na yi musu?
Tunda na fara magana har na gama
Hajiya bata sake cewa komai ba, sai
kallona kawai da take yi.
Zuwa can ta ce, Lallai kin isa, ni
ki ke gayawa irin wadannan
92
maganganun? Dama ai biri ya yi
kama da mutumn.
Tun kwanakin baya na gane ya ba
ki isasshen damar da ta wadace ki. To
amma ba laifinki ba ne.
Tashi ki ba ni wuri, bari yazo ya
same ni mu san wacce muke ciki da
nida shi."
Mikewa nayi na dawo dakina na
kara tsallake abincin a wurin na shiga
uwar dakina na zauna.
Ni kaina na gane nayi kuskure
amsawa Hajiya da nayi, to amma ya
ya zan yi da raina?
Rashin 'yancin yayi yawa, ace wai
har a kan budurwar yarinya mai
shekara goma sha shidda kamar
Zainab za a zaunar da ni a titsiye ni
wai nayi laifi!
93
Kawai takamar ina auren ubanta
bayan da za a bi Silsilar abin za a iya
fahimtar ba ni ba ce mai laifin.
To amma saboda daurin gindi da
Son kai sai ya zama komai suka yi
daidai ne.
A madadin abubuwa su gyaru
kullum kara cabewa suke yi?
Kamar yadda ya saba dawowa haka
ya dawo yau ma. Ko inda yake ban je
ba ballantana na ba shi wani abu.
Don kuwa babu, na kuma san an
gaya mishi komai da ya faru.
Karfe tara har ta wuce ina zaune a
kan sallayata da nayi sallar Isha'i a
kai ban tashi ba.
Jiran kawai abinda zai biyo baya
nake yi. Bai shigo dakin ba sai wajen
karfe goma na dare.
94
Yadda nayi zaton zai shigo ba haka
ya shigo mun ba. Ya karewa abincin
da har yanzu yake shimfide a kasan
falon da food flask din da kuma
fasassun plates din kallo.
Ya sunkuya ya kwashe plates din
da kofunan da suka faffashe ya zubar
a abin zuba shara na nan kicin.
Sannan ya fito ya dawo da abin
kwashe shara da tsintsiya yasa ya
kwashe ya gyara wurin tsaf, sannan
ya wanke hannunshi ya zo ya zauna a
inda nake muna fuskantar juna.
"Ba kya jin maganata Hauwa'u, ko
nayi miki magana ba kya ji. me ya
hada ki da Zainab?"
Nan take na fahse da kuka saboda
karayar da nayi. Nayi kukana sai da
na gaji nayi shiru, sannan nayi mishi
bayanin komai.
95
Tun daga lokacin da Zainab ta tsiro
da abubuwanta har zuwa yau abinda
ya faru.
Ya yi shiru zuwa can ya ce, "Me
yasa ba ki taba gaya mun ba? Na
kalle shi.
"Na gaya maka fa ka ce? Idan na
gaya maka me za ka yi? Na taba gaya
maka wani abu da aka yi mun ka
dauki mataki?
Sannan ko karata aka kawo
wurinka ko ni ce da gaskiya ko ba ni
ba ce ba ka taba saurarona ka ji ta
bangarena ba.
Ni dai a kullum ni ce maras
gaskiya, 'ya'yanka kuma masu
gaskiya. A ina ne aka ce a yi haka don
daidaita zaman lafiya?
96
Ni kenan kullum ina da matsala da
'ya'yan miji, to menenhe aibuna? Me
nayi musu?"
"Za ki iya zama a Kano?"
Tambayar ta yi mun kwatsam! Na bar
kukan da nake yi a take na kalle shi.
"Ina da gida a Kano, idan kin yarda
za ki zauna a can sai na mayar da ke
can tunda ina shirye-shiryen bude
wata harkar a Kano kwanannan.
Ina son zama da ke Hauwa'u. Ni
kaina nasan ina da matsala a cikin
gidan nan. Kiyi hakuri a yanzu ko
meye Zainab zata yi miki ki daure ki
jure saboda ni da ke mu samu biyan
bukatarmu."
Hankalina ya dan kwanta, ya ce
"Ina neman alfarma idan ba zan
takura miki ba?"
97
Na ce, "Ta meye?" Ya ce, "Abinci
nake so ki samar mun wanda zan ci,
yunwa ta dame ni."
Tashi nayi a daren nayi wa Ahmad
dan girki mai sauri yaci sannan muka
kwanta.
Tun daga nan na samu sassaucin
damuwa, sai dai Hajiya ta daina amsa
gaisuwata, duk da haka kuma ban
daina zuwa gaisheta ba.
Zan zauna na kai mintina goma
bata saurare ni ba. Shi ma na lura
yana da 'yar matsala amma tunda dai
bai bude bakinshi ya fada mun ba sai
ban tambayar shi ba.
Na dai tsaya tsayin daka wajen
ganin bai kuntata da yawa ba, don
nasan matsalar ba ta wuce ta Hajiya
ba.
98
Ba a fi wata daya zuwa kwanaki
arba'in ba sai shirin Ahmad ya
kammala na bude babbar harkarshi ta
kasuwanci a Kano.
Har yaje ya yi sati daya a can don
ya tabbatar komai ya daidaita, sannan
ya dawo.
Muna kwance a dakinshi yana bani
labarin yadda abin yazo cikin
gagarumar nasara, ni kuma dokina sai
karuwa yake yi zai bar zama da su
Hajiya da 'yan fitinannun jikokinta,
zan koma Kano tare da mijina.
Ina ta ayyano irin tattalinshi da zaan
kara yi da irin abubuwan da zan yi na
ci gaba don kaina.
Don kuwa nima yanayin
kasuwancin Ahmad yana ba ni
sha'awa, har nima na kan yi tunanin a
99
matsayina na mace idan zan gwada
babu mamaki nayi nasara.
Na ce, Kaga idan muka koma ni ma
sai na gwada kasuwancin mata na
cikin gida.
Kallona ya yi cikin mamaki.
"Kasuwanci kuma Hauwa'u?
Na ce, "Eh mana, na zannuwa da
gwala-gwalai irin naku ba."
Shiru yayi yana kallona, ya ce
"Ashe kina sha'awar kasuwanci?"
Na ce, "Eh, zama da kai ne yasa
hakan, da can ba na yi."
Ya ce, To bari kayan da nayi oda
wannan watan su zo sai na diban miki
a ciki ki gwada muga irin taki nasarar.
Kin san mata da yawa suna karban
kaya a hannuna kuma suna samun
riba ba kadan ba.
100
Amma abin da na lura da shi shi ne,
sai wacce ta iya rikici saboda siyan
kayan gida yawanci bashi ne.
Ke kuma ban ga wannan a tare da
ke ba."
Ba mu yi bacci ba sai karfe daya
saboda 'yan hirarrakin da muke yi.
Washegari bai kintsa da wuri ba
saboda bakin da yayi abokan
kasuwancinsa.
Sai kusan sha daya na rana. Ya
shigo dakina rike da mukullin
motarshi yana ba ni sakon da zan bai
wa Bala direba idan yazo, saboda
haihuwar da matarshi tayi.
Sannan ya shiga wurin Hajiya.
Kwanciya nayi don na dan yi barci
kafin Azahar tayi. Sai dai ban ko yi
nisa ba naji sallamar Larai.
101
Daga cikin dakin na daga murya
ina tambayarta ko lafiya? Ta ce,
Lafiya kalau Hajiye ce take kiranki.
Gabana ne ya fadi, to menene
kuma? Ba dai naje na gaisheta ba.
Nayi sallama a kofar dakin na shiga.
Har yanzu Ahmad yana nan bai fita
ba, yana zaune can gefe a asa,
kanshi kamar zai dunguri kasa saboda
irin sunkuyon da ya yi.
Jikina a sanyaye na zauna a gefe
nesa da inda yake.
"Ina ce dai ita ce wannan?"
Hajiya ta fara magana.
"Yarinyar da ko darajar sauran
matanka bata kai ba. A kanta ne kuma
nake baka umurni ka ke kin bi.
Abinda ban taba zaton zaka iya yi
ba shi ne take umurnina. Na kyale ku
102
na zuba muku ido amma gaba
dayanku ba ku fahimci hakan ba.
Nan wurin nan kazo mun da
maganar za ka kaita Hajji a bana na
ce a'a banyarda ba, don ina ta binka
ka biya wa Lado dan kanina har
yanzu ba ka biya ba kana daga
tafiyar.
Sai ka dawo min da maganaar
zuwan ku Dubai wanda wannan ma
duk wani salo ne na kin bin umurnin
da na bayar din.
Ka dai nuna mun a yanzu kai ma ka
girma. Ba a wani dauki lokaci mai
tsawo ba yarinyar nan ta zo har dakin
nan ta zage ni.
Na gaya maka ban ji ka dauki
matakin komai a kai ba. A jiya kuma
abinda ka zo da shi shi ne za ka daukec
ta ku koma Kano da zama ko Amadu?
103
To bari ka ji wata magana, idan ba
mantawa nay1 ba, ko a ranar da na
haife ka, nayi nakudar ka ne ni kadai
a dakina na haife ka na yanke maka
cibi da kaina.
Sannan ne nayi maka wanka kafin
wasu ma daga gidan suka san na
haihu, kenan ka gani babu wanda ya
taya ni.
Don haka ba zan haifi da nayi
tarbiyyarshi da irin abubuwan dadi da
wahala da dawainiyar da nasha wata
tazo ta kwace mun shi rana tsaka ina
kallo ba, babu ita.
Zagina da tayi ba ka ce komai ba
saboda ka daina gudun bacin raina sai
nata, to na yafe maka amma ko don
na yi wa tufka hanci ya zama hakan
bai sake faruwa ba.
104
Ga takarda da biro nan na baka
rubuta takardar sakin aurenta
yanzunnan ka bata, auren nata ya ishe
ni haka."
"Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un."
A bayyane na furta saboda firgitan da
nayi. Saki kuma? Wannan wacce irin
musiba ce?
Na kalli Ahmad wanda har yanzu
yake a yadda na same shi, sannan na
kalli Hajiya.
Kamar kullum tana zaune ne a kan
dardumarta ta sallah, sanye da
zurmemen hijabinta.
Zan iya cewa a tsawon zaman da
nayi a gidan na watanni ashirin ban
taba ganin ranar da na ganta babu
hijabinta ba.
Sai nayi sha'awar ace ita din mata
ce mai sassauci da rangwame a kan
105
al'amuranta, tunda kowa ya shaideta
mace ce mai yawan Ibada.
To me yasa ita din halinta ya zama
haka. Danta da yake matukar
kokarinsa wajen ganin yayi mata
biyayya ya kaucewa bacin ranta ya
batawa wanda ya bata mata.
Danta da a kullum yake fadin irin
alherinta da dawainiyar da tayi da shi
wajen ganin bai yi maraicin uba ba.
Danta da a kullum yake fadin cewa
ita ce abinda ya fi so da girmamawa a
duniya shi ta ke yi wa irin wannan
kuntatawar da kuma rashin sassauci?
Lallai halinta sai ita.
Take na fara kokarin rarrashin
zuciyata don ta samu sassaucin
tsananin da zata fuskanta a gaba.
106
Na rinka tunanin abubuwan da zan
yi wadanda za su taimaka mun a
rayuwata da zan shiga nan ba da
dadewa ba.
Tunda nasan babu makawa Ahmad
zai aikata abinda Hajiya ta umurce shi
tunda da bakinshi ya tabbatar mun
cewa ita din bata taba bashi wani
umurni da ya ketare ba, face ya
aiwatar da shi komai tsananin shi.
** ** **
Ina kwance a kan shimfidaddiyar
katifata da ta sha lallausan shimfidan
zanin gado na yadin (American bed
sheet) dan asali da bargonshi.
Na kai hannu na shafa yadin zanin
gadon tare da tuna ranar da na fara
shimfida shi a kan gadona, lokacin da
107
nake ganiyar cin amarcina a gidan
Ahmad.
Na runtse idanuwana da karfi
saboda wasu tunane-tunane da suke ta
kawowa zuciyata ziyara.
Tunanin abubuwan da suka zo suka
kuma wuce tamfar a mafarki tamfar
dai ace wani barci kawai nayi mai
dadi na kuma farka.
A da can, ban taba tunanin haka
al'amurana za su kasance ba. A
matsayin shekaruna a yanzu ashirin
da uku kacal a duniya.
Amma har an fara kirga mun
aurena. Yanmata da yawa sa'o'ina ba
su ma yi auren ba, ballantana har ace
ya kare.
Take kuma nayi hanzarin yin
Istigfari da na tuna akwai wasu mata
kuma da suke zuwa duniya su gama
108
rayuwarsu a cikinta su koma ga
mahaliccinsu ba tare da sun yi auren
ba.
Don haka ba zai yiwu nayi wa
Ubangijina butulci ba, a kullum zan
kasance mai yawan godiya a gare shi
bisa irin yawa-yawan n imomin da
ya yi mun a rayuwata.
Ban kuma dauka wannan
mummunan jarrabawa ba ce sai na
dauka cewa ni kuma tawa kaddarar
kenan ba kuma zai yiwu na tsallake
wata kaddara tawa ba face kawai na
roki Ubangijina da kowacce ta tashi
zuwa mun, to ta zamto mai sauki.
Ya kuma ba ni ikon dauka don
Imanina ya zamto cikakke tun da aan
gaya mana cewa Imaninmu ba zai
cika ba sai mun yarda da kaddararmu
ta alkairi ko wanin alkairi.
109
Bai kuma jarraba ni da ciwo ba ko
wanina ko kuma ya jarrabe ni da rashi
na wata gaba a jikina ba.
Sannan da aurena ya mutu a farko
sai ya bani wanda ya fi mun na
farkon, to ina rokon shi a yanzu ma
ya bani wanda ya fi mun na biyun.
Sai dai tunanina yana kawowa
daidai nan sai naji gabana ya yanke ya
fadi ras!
Kenan na rabu da Ahmad ba zan
sake komawa gidanshi ba? Ina son
mijina shima kuma yana sona.
Mahaifiyarshi ce matsalarmu, don
kuwa idan ba don shigarta cikin
lamarin ba to don ta ya'yanshi zan
iya zama da su a yadda suke, tunda
ina son ubansu.
Sabanin matsalata da Ishak wanda
a lokacin da aka yi aurena da shi
110
shekaruna goma sha bakwai ne a
duniya.
Ba komai yasa a ka yi auren ba
face rashi da mahaifina yake ciki ga
kuma kwadayinshi a kaina na ganin
ni din nayi karatu.
Ya dauke ni ya ba shi ni ba tare da
wani dogon nema ko bincike ba,
saboda jin irin alkawuran da yayi a
kaina.
Alkawuran da suka zamo shi ne
sanadin faruwar auren da kuma
rugujewarshi.
Idan kuma da ace zaman da yayi da
ni akwai adalci a ciki ko kuma
sassauci ko tausayawa wadanda
wadannan abubuwa sune suka hadu
suka zamo soyayya da kauna to duk
da da sauki.
111
Idan har akwai abinda nake tunawa
da Ishak da ke sake sani kin shi to bai
wuce dukan rashin tausayi da yake yi
mun ba.
To sai na auri Ahmad, mutumin da
ya an yanci na walwala. Nayi
rayuwar aure irin wacce ban taba
mafarkin ana yin irinta ba a gidan
aure.
Saboda irin sona da tattalina da
mijina yake yi. Ya nuna mun cewa ni
din ina da matukar muhimmanci a
wurinshi.
Ya kuma so ni so na hakika, ya
mutunta iyayena da yan uwana, ya
guje mun bacin raina, ya tattali farin
cikina.
Amma sai gashi 'ya'yanshi da
mahaifiyarshi sun ki yarda su bar ni
112
na zauna da shi duk da hakuri da
halinsu da nake yi.
Idan har ina da laifi ko kuma wani
ganganci da na aikata a lokacin da
aurena na fari ya mutu, to a wannan
karon kam nasan ba ni da wani laifi.
Sai dai na kasa hakura, fatana bai
wuce da ni da shi mu samu maslaha
kan al'amarin aurenmu ba.
Tunda dai an yi sa'a saki daya ne a
tsakaninmu.
An kwaso kayana tas daga gidan
Ahmad, ba wai don na hakura da
zama da shi ba.
Sai dai kawai don jiran shawarar da
shi da kanshi zai zartar a kan maganr.
Sakon da ya turo mun kenan a waya
daren da na dawo gida.
113
Cewa na saurare shi kan shawarar
da zai yanke na neman mana mafita
nan da kwanaki uku.
Sai kuma kudi da suka shigo
account dina masu auki.
Ta bangaren Babana dai abin ba a
cewa komai, don kuwa bakin cikinshi
ba ya' misaltuwa.
Umma kam har a wannan karon ba
ta ce komai ba, harkokinta take yi.
Nayi matukar kokarin ganin ban
takura kaina da tunane-tunane ba, ta
hanyar shiga duk wani hidima na gida
da ake yi.
Har girki na karba ni nake yi da
sassafe kan bakwai zuwa bakwai da
rabi na kammala abin karyawa.
Idan na gama kumana zauna taya
Umma saye da sayarwanta, muna
kulla na kullawa.
114
Babbar matsalata ba ta wuce na
rashin barciba. Sai nayi matukar sa'a
ne kwarai nake samu na dan runtsa.
Al'amurana ne kawai za su yi ta
dawo mun rayuwar da nayi da Ahmad
mu'amallarshi da kuma yadda yake
harkokinshi a cikin gidanshi.
Daga manya zuwa yara da kuma
masu yi mishi hidima bisa sassauci da
ganin mutuncin kowa.
Ranar shi da farin cikinshi dakuma
fushin shi da kuma wasu abubuwa
masu dama.
Me yasa mutane ba su da tausayi
ne, babu sassauci a cikin al'amura
amma kuma mu sai muce muna
neman sassauci a wurin Ubangijinmu.
Bayan mun san shi ne ya yi umurni
da mu yi wa na kasa damu sassauci da
adalci.
115
Duk da abin da Hajiya tasa danta
ya yi mun zama dashi bai fita a kaina
ba, har yanzu kuma jiran shi nake yi
naji abinda zai ce.
Satina uku cif a gida Ahmad yazo
sai da ya gaisa da Babana da Umma
sannan na same shi a zauren gidanmu,
bayan Babana ya aiko Tasi'u cewa
naje na same shi.
Cikin kyakkyawar shiga na dogon
hijabi da na dora akan kayan dake
jikina dinkin atamfa riga da zani na
same shi.
Nayi matukar kokarin daurewa ta
ganin bai fahimci wani abu game da
halin da na shiga ba.
Kaina na sunkuye na gaishe shi
bayan na zauna akan shimfidar
tabarmar da aka yi mishi.
116
Ya amsa cikin yanayin shi kadaran
kadahan. Ban kalle shi ba na ce, "Ya
su Hajiya?"
Ya dan yi jim bai amsa ba kafin ya
ce, "Suna nan kalau." Abinda a sani
kuma shi ne kallona yake yi duk da
kin yarda mu hada ido da nayi ta
hanyar kallon 'yan yatsun hannuna da
na yi wa lalle a safiyar yau.
"Nayi tafiya ne Hauwa'u, shi ne
abinda yasa ba ki ganni ba, tafiyar ta
dauke ni tsawon kwanaki goma sha
takwas, sai a daren jiya na dawo. Don
haka kiyi hakuri."
Shi dai mai yawan bada hakuri ne,
abinda zuciyata ta ke fada mun kenan.
To amma hakurin da ya bani a yanzu
menene ma'anarshi?
117
Nayi hakuri ne a kan sakin da ya ya
mun, ba zai iya sake zama da ni ba ko
kuwa nayi hakuri ne na koma dakina?
A yanzu ne nasan na daga kaina na
kalle shi muka hada ido alamar ya
dade yana kallona hakan bai sa na
daina kallon shi ba babu abinda ya
canza a tare da shi.
Komai nashi yadda yake illa
idanunshi da launin su ya dan surka.
"Kiyi hakuri Hauwa'u." Abinda ya
sake fada kenan a lokacin da na
sunkuyar da kaina na hadiye wani abu
mai tsanani da ya rike mun wuya.
"Ina so ki san kowa da irin
jarrabawarshi a rayuwa ni tawa
jarrabawar kenan.
A tafiyar da nayi nasa mutane
daban-daban sun je don su taushi
zuciyarta har sau úku.
118
A tunanina idan na dawo zan samu
wani dan sauyi daga gareta a game da
maganarmu wanda har da hakan ne
yasa na kara jan kwanakina na
dawowa.
Amma da na iso gida sai ban ga
hakan ba, don haka ne nayi
sammakon zuwa Kano a yau na gana
da kanin Mahaifina da a gobe nake sa
ran zai zo don ya samu Hajiyan."
Wani irin tunani ne ya yi gaggawan
shiga zuciyata da kwakwalwata, duk
da irin kwabata da zuciyata take yi sai
da bakina ya furta na ce.
"Idan a kaina ne ka ke tura mutane
wajen Hajiya to na roke ka ka daina
saboda kai da kanka ka gaya mun
cewa baka taba saba mata ba.
119
Kenan kana so ka tilastata ta
hakura ta barka ka zauna da ni ba bisa
son ranta ba.
Wanda hakan ba zai sa ta yi
sassauci a kan kiyayyar da take yi
mun ba."
"Ba a kanki nake turawa ba, a
kaina ne saboda halin da na shiga,
barin ki gidan da kuma dawowan da
nayi ba kya cikin shi.
Gaskiya ki ka fada, ban taba yin
makamancin hakan ba sai a yanzu
wanda nasan ko ta sassauto ta hakura
to akwai wani tsanani da za ki iya
fuskanta.
Amma ina so nayi miki alkawarin
ba zai yiwu na barki haka ba.
Har a yanzu ina da niyyar dauke ki
a gidan zuwa Kano. A karo na biyu na
120
dago kai na kalli Ahmad da har yanzu
yake kallona.
"Ba zan jagoranci batawarka da
Mahaifiyarka ba. Burina bai wuce
naga mun daidaita matsalolinmu sun
kare mun maida aurenmu ba.
Amma sai dai dama matsalar ba
tamu ba ce a inda matsalar take kuma
banga alamar wani sauki ba.
Ina rokonka kada ka tilasta
Mahaifiyarka zama da ni, don Allah.
Yadda a yanzu zuciyata ta hakura
ina rokonka kaima ka sakawa taka
Zuciyar sassauci.
Ina kaiwa nan na mike na shiga
gida, na fada kan katifata, kuka nake
yi irin wanda na dade ban yi ba.
Duk yadda na kai da son zama da
Ahmad abin ba zai yiwu ba.
121
Ya zama dole na taushi zuciyata na
danganaa na fawwalawa Ubangiji
lamarinshi, don ya isar mun ya bani
abin yi.
Kwana nayi cikin wani yanayi da
ba zan iya kwatantawa ba, don saukin
abin ma nayi alwala nayi ta nafilfili
ina rokon Ubangiji sauki, da
kyakkyawan zabi.
A cikin satin ne aka kai sadakin
Yaya Auwalu abin da muka dauka shi
ne za su saka ranar auren da nisa.
Sai kawai muka ji sun saka sati
hudu kacal.
Muna zaune da Umma a tsakar
gida muna kullin kukar da Baba Ladi
ta aikowa Umma na siyarwa.
Na ce, "Amma Umma gaskiya
auren nan da suka saka ya yi kusa da
yawa."
122
Ta ce, ""To ai na Allah ne, sannan
shi Babanku jiya ya same shi yayi
mishi bayanin komai.
Ya ce, Babu damuwa, don yana da
dan abin da ya dade yana tanadawa
don shirin auren.
Na ce "To ai shi kenan."
Umma ta ce, "To sannan kin san
shi hidima irin wannan ba ka shirya
mata nemi taimako kawai a wurin
Ubangiji idan tazo maka."
Na ce Haka ne, Allah yasa mu
gani lafiya." Ta ce, To amin.
Ke kuma Ubangiji ya baki mafita
kan wannan matsala da ta same ki na
mutuwar aure, ya ba ki miji nagari da
zai zauna da ke bisa adalci da
kyautatawa.
Ya kuma zaunar da ke a dakinki ba
tare da kin sake fitowa ba."
123
Ban iya amsawa Umma ba, don
kuwa babu abin da nake so naji irina
ce Allah ya sassauta zuciyar Hajiya ta
bar ni na koma dakina.
Gidan Alhaji Ahmad Rufa'i, don
kuwa har a yanzu dinnan burina
kenan ko zuciyata tayi kamar ta
hakura sai kuma ta kara harzukowva.
Idan na tuna da irin rayuwar da
nayi tare da shi, daurewa kawai nake
yi nake rokon zabin alkairi a wurin
Ubangiji a lokacin da nayi sallah.
Amma idan da da hali to da rokon
komawa kawai na rinka yi ko da
hakan yana nufin batawar Ahmad da
Mahaifiyarshi.
To amma abinda na sani shi ne,
idan nayi haka ban yi mishi adalci ba,
don kuwa da kanshi ya gaya mun
124
cewar ta sadaukar da farin cikin
rayuwarta domin shi.
Da kuma Yarshi da har a yau din
nan ban ma santa ba.
Sannan shi din ko ba don haka ba
mahaifiyarshi ce da Aljannarshi take
karkashinta.
Hakan da na sani shi ne yasa na
danne zuciyata na kara ba shi
shawarar cewa mu hakura har a jiya
da ya kira ni.
Don na tabbatar da ban zalunce shi
ba. Idan yaso ni kuma Allah sai yayi
mun kyakkyawan sakamako.
Shiri sosai muke yina shirin bukin
Yaya Auwalu. Ya hada lefenshi rigijif
gwanin sha'awa.
Samun Umma nayi na ce mata ina
so na kwashe kayan dakinta na zuba
mata nawa na gidan Ahmad.
125
Ta kalle ni ta ce, To a wane dalili?
Ki zuba mun kayanki ke kuma idan ki
ka tashi yin wani auren ko kuma ki ka
koma dakinki fa?
Tunda ai ba gama iddah ki ka yi
ba. Na dan yi murmushi na ce,
"Umma ai komawata gidan Ahmad
abu ne mai wuya.
Tunda ba matsala ce a tsakanina da
shi ba, matsalar Mahaifiyarshi ce ba
ta kuma da niyyar yin sassauci a kai."
Ta ce, "Eh dai duk da haka ki bar
Umma ba sai kiyi mun addu'a ba
su ba ni da bukata." Na ce, "To ba
kawai idan na tashi yin wani auren
Allah ya bani wadanda suka fi
wadannan ba."
Ta ce, "To amin, amma dai duk da
haka ba zan saka kayan dakinki a
126
nawa dakin ba, haba abin ma ai bai yi
tsari ba."
Da safe na shirya na gama aikina
da wurwuri na samu Babana na roke
shi ya bani izinin fita don ina da
uzuri.
Yayi shiru zuwa can ya ce, "To kin
dai san mutane ba a iya musu, ni fa
ina gudun magana.
Amma idan kin ga a matse ki ke shi
kenan kije amma kada ki dade."
Babban shagon da muka yi
siyayyan kayan aurena naje, mutumin
kuma ya gane ni.
Nayi mishi bayanin bukatata na son
canza kayan tare da neman sanin
cikon da zan yi mishi.
Cikin sauki da mutunci muka
daidaita na zabi wasu masukyau nayi
127
mishi ciko na dawo gida da motar
kaya.
Su kuma suka saka nawa da damna
suke jingine a dakin su Tasi'u suka
tafi da su.
Sai da nasa a ka yi wa Umma
fentin dakinta tsaf sannan a ka zuba
mata sabbin kayanta a ciki.
Abin sai wanda ya gani, duk da irin
fadan da Babana yayi mun wanda bil
hakki abin ya ba shi haushi.
Ni a raina dadi naji don kuwa
nasan shima Babana idan ya hau
gadon zai huce.
Tun ana saura kwanakki ake ta
isowa yan biki kowa da shirin shi,
yan uwan Umma daga Gamawa da
na Babanmu daga birnin Kudu.
Su Inna Hadiza suka tasa ni a gaba
kowa da abinda yake fada.
128
Ba ni da abinda zan ce musu don
na riga na gaji da bayani.
Da daddare Baba Ladi ta kira ni
dakin da aka sauketa da yake na Yaya
Auwalu ne tana yi mun magana ne ita
ma kamar kowa a kan rabuwata da
Ahmad.
Ban ce matakomai ba ta yi ta
maganganunta ina jinta. Ta ce, "Wato
ina miki magana kin yi shiru ko?
Na dan yi murmushi daidai wayata
tayi kara na dauka Ahmad ne.
Gabana ya fadi kamar kowanne
lokaci idan ya kira abinda ban san
dalilin faruwar hakan ba.
Nayi mishi sallama ya amsa.
"Ya ya shirin biki?
Na ce, "Mun gode Allah."
Ya ce, Wato sai a yanzu nasan
rashin kirkinki."
129
Na ce, Da na yi me kuma
'Yallabai?"
Ya dan yi murmushin da na jiyo
sautinshi har a cikin wayar. Ya ce, "Ba
kya kirana Hauwa'u, ba ki damu da ni
ba a yanzu.
Yau kwana goma sha hudu ban kira
ki mun gaisa ba, hakan bai sa kin yi
tunanin ke ki neme ni ba.
Sannan sai aka saka auren Yaya
Auwalu ba ki saka ni cikin wadanda za
ki gayyata ba."
Na ce, "To kayi hakuri.
Ya ce, "An ya zan iya kuwa? Ina dai
so a duk lokacin da ki ka tunani ki rinka
yi mun adalci."
Na ce, "To."
Ban san adalcin me Ahmad yake
sonayi mishi ba. Sannan a tsakaninmu
wanene ya kamata ya yi wa wani
adalci?
130
Ni ce zan yi mishi adalci ko shi ne zai
yi mun'? Wayar da na tsirawa ido ita ce
ta sa Baba Ladi fara sabuwar magana ta
bar wacce da take yi.
"Kina yi mishi irin wannan so me ya
fito da ke? A hankali na kalleta na ce
mata, "Mahaifiyarshi."
Da yamma kawai sai mota ta tsaya
aka fara sauke kaya, buhun shinkafa
biyar, sugar, filawa, wake, gero,
mangyada, manja, maggi, tumatir da su
albasa kwando-kwando.
Sai cinyoyin bayana Saniya guda
biyu, sakon Ahmad ne. sai yadin
material 'yan asalin Dubai guda biyu,
boyil biyu.
Sai atamfa Erclusive guda biyu duka
a dinke. Takalma set kafa biyu da za su
iya shiga da kayan.
131
Sai gyale biyu, kayan duk a dinke
suke. Na zuba musu ido ina kallo. Wani
sanyi ya rinka kwarara a cikin zuciyata.
Shi ma har a yanzu da alama bai
fidda rai ba. Text nayi mishi na godiya,
duk da korafin da ya yi na ba na
kiranshi.
Don kuwa ban ga dalilin yin hakan
ba. Text din yana shiga sai ya kira, na
ce "Mun ga sako mun gode."
To fa! Lallai kam da gaske Ahmad
yake ba zai iya hakura da Hauwa'u ba.
To idan kuma Ishak ya ji labarin
abinda ya faru shi ma zai dawo?
Bari in dan huta a nan kafin na dora
daga baya, don haka sai mu tara a littafi
na (4) kuma na karshe insha Allahu.
Taku;
Haj. Hafsat C. Sodangi
(Mrs Yunus Abdullahi Dabai)
08025078968, 07035586299
132
Post a Comment for "Mai Daki Complete Hausa Novel"