Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Kurkukun Kaddara Book 2 Page 17

_~*BossLadiesWriters*~_



           _*KURKUKUN ƘADDARA*_




~Middle step~

          


              _The Prisoners E17🔥💫_




*Daga alƙalamin Boss Bature*





 A Æ™alla sun shafe kusan 30 minutes a É—akin Danish, Ji suke kamar abarsu su kwanta a É—aki É—aya saboda haka su ka saba kwana a kurkuku, daga bisani Nurse tace dasu zasu tafi zuwa gobe zasu Iya zuwa su Æ™ara duba shi' jiki asanyaye suka miÆ™e suna tafiya suna waiwayon shi musamman Angel ji ta ke yi kamar ta koma ta rungume shi.


  Bayan fitar su daga É—akin, Nurse Ta raka kowan nan su room da aka kwantar da shi, ba su so aka raba su ba, har yanzu tsoron mutanan su ke ji, ba dan Angel ta lalla6a su ba da ko babu inda zasu je, a É—akinta zasu kwana, musamman Azeeza da jemimah É—aÆ™yar Angel ta lallashesu ta lalla6asu don ta fahimci dokar asibitin ce haka ba'a haÉ—a mutun fiye da É—aya a É—aki, wata'Æ™il sai idan ya kama dole, sauÆ™in ma kowan nan su akwai nurse É—aya da ke kula da É—akin shi, duk wani abu da zasu buÆ™ata zasu yi masu, hatta toilet suna raka mutun In ya buÆ™aci hakan musamman gasu da basu san yadda zasuyi amfani da wasu abubuwan ba.


A daren ranar sun yi kwanan farin ciki basu da wata damuwa.


*Daular Alhaji Musa wadata*


idan nace zan tsaya zayyana maku zunzurutun Kayan alatun da ke a gidan Alhaji musa daga ni har ku zamu koma Yin Mafarkinsa ne, wato Haɗaɗɗiyar Daular arziƙi ce, Katafaren Villa ne Wanda Idan ka zura ƙafarka acikinsa tamkar ka Bar Nigeria ka shiga Dubai ne, Aljannar duniyace ƴar ubansu, A ƙalla security din dake tsaron Kafcecen Gate ɗin shiga gidan sunkai su goma shabiyar, Wasu gabza gabzan Garada Masu Ƙirar sadaukan Yaƙi, Babu wasa akan fuskokin su, Bana tunanin ko aljani zai Iya gifta gate din gidan salin alin ba tare da sun cafke shi ba, Shantalelen titi ne zai sadaka da Cikin gidan kai tsaye daga bakin babban gate ɗin, yadda kasan da zallar goal aka ƙera ginin saboda ɗaukar idon gilassan Ƙofofin da Windows, ko gidan shugaban ƙasa albarka, Babu ce kaɗai ke babu agidan Alhaji musa, komai na gidanshi babu made in Nigeria, an zabga almubazzarancin dollar wurin ƙera ginin, don hatta sample dinsa da ƙwararrun da suka ginasa kaf aikin turawa ne.


Mamaki da al'ajabin dukiyar Uncle din nasa Ya hana shi Kwantar da hankalinsa, Tun Bayan da escords suka ɗauko su daga airport, Motocin suka shigo gidan gabanshi ke ta faɗuwa, saboda sabon gini ne baya a ƙasar Uncle ɗin nasa Ya mallake shi, shiyasa komai yake ɗaure masa kai, Kafin shigarsu gidan Saida shureim Ya dinga jero addu'o'i acikin zuciyarshi Yana neman tsari akan Allah ya kare shi daga shagalar duniya, Idan har zaman shi gidan ba alkhairi bane, Ya roƙi Allah da ya yi mashi silar barin shi cikin sauƙi ba tare daya sha Wahala ba.


Tun da suka shiga gidan Kamar wani baƙauye Haka ya dinga bin ko'ina da kallo, wasu matsiyatan Chandeliers saman ceilling Masu ƙyalƙyali tamkar zasu rubzowa mutun saman kanshi, Ga wasu Haɗaɗɗun twins stairs, masu ɗauke da Glass Elevator a gefensu. Idan ka shiga cikinta Kana iya hangen mutanan dake zarya a palourn Yayin da take Yin sama dakai ko take dawowa dakai ƙasa.



  A katafaren Palourn gidan kuwa Wasu Jigunannun Royal Sofas set ne Ƴan ubansu masu numfashi Ga Arm chairs kalar Na sarakuna, A gefe da gefen kujerun Sofa table ne, Tiles din palourn baida banbanci da Mirrored tiles Kana kallon Fuskarka acikinsa Idan kana Tafiya, zallar haÉ—uwa, An zuba komai na more rayuwa, Idan nace zan tsaya zayyana haÉ—uwar Komai dake acikin Gidan Tabbas zamu Æ™are middle step da last step acikin gidan Alhaji musa (🤣)


Babu wanda Yasan da zuwansu, Hatta Iyalinsa Ba su san da dawowar shi a yau ba, yana É—aya daga Cikin Halayan Alhaji musa, Idan zai yi tafiya babu wanda ke sani Matar shi ko Æ´a'Æ´anshi, Haka zalika Idan Zai dawo sai dai su ganshi, saboda zuwan ba zata Ya ke yi masu.


A Kwance take saman Prayer mat, Tasha Dogon Hijabi a jikinta duk ta ƙudundune kanta acikinsa, daga gaban dardumar Qur'anic Stand ne, ga dukkan alamu Bacci ne Yai awon gaba da ita a yayin da take Yin karatun al'ƙur ani mai girma.


  "Zeenat! Kiran Sunanta da akayi ne Yasa ta firgita a Hazarce Ta farka daga baccin ta É—ago da kanta tana faman zazzare dara daran Kyawawan idanuwanta farare Æ™al launin Ocean Blue, Masha Allah Kyakkyawar matashiyar budurwa Kamanninta sak Alhaji musa tamkar yayi kakinta, sai dai Daga gani Farar fatace Haskenta ya É—are na mahaifinta, Fara ce sol Jawur da ita, tana da yalwatacciyar sumar kai Launin blonde har saman fore head É—inta kwantaccen gashi ne, ga doguwar fuska, dogon hanci da Æ™aramin baki launin pink, Ba ta da Æ™iba ko misÆ™ala zarratin siririya ce, abu É—ayane ke da girma a jikinta, dukiyar fulaninta acike suke kamar an jera balon balon.

 

   "Zeenat! Bacci ki ke Yi"? Muryar Mahaifiyartace ta rasa kunnuwanta, da sauri ta zabura ta miÆ™e tare da wurga Æ™wayar idanuwanta kan Mai shigowa É—akin, babbar macace mai cikar kamala, Ta É—auki wankan Shadda ajikinta launin Ja, Tasha uban ado akan fuskarta, baturiyace Siririya bata da Æ™iba, daga ganin surarta a wurinta matashiyar budurwar ta gado hasken fata da launin ido, da kuma doguwar sumar kai, Hajiya Sarah Uwar gida kuma amarya awurin Alhaji musa, ta É—aure kanta da kallabi, hakan bai 6oye doguwar sumar kanta da ta sauko har gadon bayanta, Necklace É—in wuyanta da earrings É—inta na zallar diamond ne sai Æ™yalÆ™yali suke Yi da É—aukar ido.


  Muryarta Adisashe ta amsa mata"mommy karatun Æ™ur'ani nike Yi bacci ya É—auke ni bansani ba" ta yi maganar tana Yin miÆ™a haÉ—i da yin hamma


  "Ba ki ji dirar motoci ba ne"? Ras Taji gabanta Ya faÉ—i, Muryarta na rawa ta furta"dad... daddy is he back "?


 Ta6e baki Hajiya Sarah tayi"ya dawo tun É—azu, yanzu haka yana a É—akinsa, yace baya son takura, kinsan halinsa"


  Hankalin Zeenat Ba Æ™aramin tashi yai ba, ta rasa gane farin Ciki za ta yi ko baÆ™in Ciki, Tana son mahaifinta sosai, sai dai tana mugun jin shakkarshi saboda rashin sakar masu fuska da baya yi, duk da wani lokacin idan yaso yana nuna masu so da Æ™auna.


   Jin ta yi shiru zugudum tana faman zazzare ido Yasa Hajiya Sarah cewa"ya naga kamar baki farin Ciki da dawowarshi"? A hanzare ta girgiza kai" "I'm so happy he's back, na yi murna ai shi É—inne baya son takura" 


  Murmushi tasakar mata"Albishirinki"!

Da mamaki ta tsayar da eye balls É—inta kan face din momyn nata

  "Goro"! 

"Fari ko ja"

 "Fari" 

Matsawa Mommyn ta yi kusa da ita Cikin raɗa ta furta mata"Ba shi kaɗai ya dawo ba, Hada Yayanki Dr shureim yanzu haka Yana kwance a bedroom ɗin da aka ware masa" Tun kafin Hajiya sarah ta ƙarasa Maganar, Zeenat ta zube saman gwiwowinta tare da ɗaura goshinta saman tiles ta yi Sujjada tsabar farin cikin jin anzo mata da sahibinta


   "Ah lallai ashe Har yanzu Kina son Yayan naki, Hada Yin sujjada" É—agowa Zeenat Tayi, tare da miÆ™ewa tsaye Hijab É—in jikinta sai Ja da Æ™asa Yake yi.


  "Mommy bazan Iya jurewa ba, Zanje wurin Yayana inyi mashi barka da zuwa" tsantsar farin cikine akan fuskarta


  "No kada ki je Yanzu ki bari masu aiki su kammala Girka mashi abinci, In yaso sai ki je ki kai mashi a É—akinsa, Daddynki ne Ya bada Umarnin A girka mashi abinci hausawa"


  Zeenat da takasa rufe bakinta don Murna duk tabi ta Æ™agara don a kwaÉ—aice take da son ganinsa

  "Na faÉ—a maki zuwanshi ne Don ki kimtsa, Ki gyara kanki, Nasan Halinki da sanya dogon Hijabi salon kije mashi ahaka, Ki samu Ko É—an gyalene ki yafa a kafaÉ—a," turo baki zeenat tayi da Æ´ar shagwa6a tace"Mommy ae shima Yaya shureim É—in yafi son mace mai sanya dogon hijabi"


  "To ai bance bayaso ba, tun da acikin gidane ki samu gyale ki yafa" ta Æ™are maganar da zolaya ta furta"Muslimatun matar limam" Dariya Zeenat ta sanya tana kallon mommyn nata.


  "Zan koma kitchen, Ki tabbatar kin shirya da wuri" 


  Amasa mata tayi da toh


  Bayan fitarta, da sauri Zeenat ta cire hijab É—in jikinta, ta nufi toilet ta shige, cikin Ƴan mintuna ta fito Sanye da  bathrobe (rigar wanka) fara Ƙyal a jikinta, hannunta ruÆ™e da short towel tana tsane sumar kanta, Bayan ta kammala tsane gashin, a gaban tafkeken dressing mirror ta zauna saman chair tana Gyara Jikinta, Hair dryer ta kunna Ta busar da sumar kanta, Bayan ta gama ta soma shafa tsadaddun Mayukan shafawarta dake a jere gaban madubin.


Zeenatu muguwar sangartacciyace ta saba tun tana ƴar ƙarama duk In za ta yi make up ko zata sanya sutura masu aikin gidansu ne ke taimaka mata, saboda ba ta Iya komai na aikin wahala ba, hatta sanya ɗan kunne bata Iyaba wahala take sha, Yau saboda zumuɗin zuwan ya ya shureim bata bari wani ya taimaka mata wurin sanya sutura ba, tun tana agaban mirror mai aiki ta ƙwanƙwasa ƙofar ɗakinta ta nemi zinin shigowa, ta tambayeta Ko tana Buƙatar wani abu, tace mata a'a taje kawai za ta yi komai da kanta, ashe da rabon tasha wahala.


  Gaba É—aya saida ta faffasa kayan kwalliyar gaban mirror, bata da natsuwa ko misÆ™ila zarratin tana da rawar kai da zumuÉ—i, tun daga kan Hoda da ta É—auko zata shafa, Ta sil6e daga hannunta gaba É—aya ta tarwatse a saman tiles, garin hodar ya zube, Ta kuma janyo janbaki a tsiyace take murza ma la66anta nan take ya gutsire guntulan Ya faÉ—i Æ™asa ta jefar da shi, duk kwalbar turaren data É—auka sai ya sil6e Æ™asa Ya daki tiles kwalbar ta fashe ruwan Ciki Ya tsiyaye, hakan bai dame ta ba, don ta yi asararsu.


   Bayan Ta kammala Æ´an shafe shafenta, bata bi takan kayan da ta faffasa ba, tsallake su ta yi ta nufi tafkekiyar glass wardrobe É—inta, daga wajen glass É—in kana Iya ganin jerin suturar sanyawarta ashaÆ™e tamkar a company, Abayas, shadda atampa leshi, material, english wears, Pakistans, ga jerin Kayan baccinta, komai fa anzuba mata su, shalelen daddy musa


  Da hannu ta zuge glass wardrobe É—in, Ta Æ™ura ido tana tunanin suturar da zata sanya don ta burge Yayanta shureim, idanuwanta ne su ka sauka akan haÉ—aÉ—É—iyar atampa, yatsun hannunta na kerma ta cafko ta, tana kiciniyar ciro atamfar ai ko gaba É—ayan jerin Kayan da ke a gidan tsakiya suka zazzago saman tiles, ko ajikinta, saida ta 6arar da kayan wardrobe É—in wurin neman sutura É—aya kacal da zata sanya a jikinta, Ga abu a fili ta É—auka tasa shine bazata Iya ba, tafi so saita haukata komai na É—akin tukunna a Æ™arshe tabar masu aiki da wahalar gyara mata su.


Tamkar zata fashe da kuka, ruwan ido Ya hanata É—aukar Kayan da zata sanya don ta burge Yayanta.


   "Assalamu alaikum" Muryar É—aya daga Cikin masu aikin gidan ce babbar mace wadda suke Kira da Tani.


  Da sauri Zeenat ta juyo tana kallonta, 

 "Yawwa Tani, shigo ciki ki taimaka min narasa wasu Kaya zasu dace dani, Inaso ne na burge yaya shureim"


  Baki asake Tani take bin É—akin da kallo, Sam ba ta yi mamakin ganin yadda Zeenatu ta faffasa Kayan Kwalliyarta da turarurrukanta ba, Halinta ne yin 6arna kamar 6era.


  "Haba zeenat, Dubi yadda kika zazzago da ninkakkun Kayan Cikin wardrobe É—inki Æ™asa, sannan kinbi kayan kwalliyarki da kwalaban turare duk kin faffasa su why pls? Harfa larai na turo donta taimaka maki ki shirya a tsanake amma sai ki ka ce mata ta tafi za ki yi da kanki, yanzu kin kyauta abun da ki ka yi"? Cikin kwantar da murya take Yi mata magana.


 Zumbura mata Baki Zeenat tayi"Nifa bana son faÉ—a, Idan ma na faffasa su ai daddy zai canza min wasu, kuma ai bada gangan nayi ba ko"


  Girgiza kai Lami tayi haÉ—i da sakin murmushin takaici "Oh, Saboda kinsan daddynki zai siya maki wasu shiyasa kika faffasa su? Ke Baki damu da asarar dukiyar da za'ayi ba kenan"?


   Bubbuga Æ™afafuwa Zeenatu tayi fuskarta a tur6une tace"Ni ki daina Yi min faÉ—a, Nace maki ba laifina bane kuma in sha Allah zan gyara, pls ki taimaka min In gyara komai kada mommy tazo taga ban shirya ba"


  GyaÉ—a kai Tani tayi"ai dole kam in tayaki gyarawa, idan ba haka ba hada ni zata shafa"


  Ƙarasa shiga É—akin Tani tayi, cikin Æ™anÆ™anin Lokaci ta É—auko Parker ta tattara Kayan kwalliyar da zeenatu ta faffasa ta zubar a trash can na É—akin, Ta koma bakin wadrobe din ta soma ninke mata kayan da ta zubar a kasa ta jera mata su a cikin wardrobe, duk tana a tsaye ta ruÆ™e qugu tana kallon tani.


  Wani haÉ—aÉ—É—an Cord lace ta É—auko mata Red colour anyi mashi adon flower yellow.


  "Zeenat wannan zaiyi maki kyau sosai, Red and yellow, kalar farare ce sannan kuma kyawawa irinki"


 Washe fararen HaÆ™oranta tayi Jiki na rawa ta sanya hannu ta kar6i kayan da Tani ta miÆ™o mata, Sai da Tani ta taimaka mata wurin É—aura zani da É—aura É—an kwali don ba ta iya ba, masha Allah Lace É—in Yayi bala'en Yi mata kyau.


  "Bari na É—auko maki Takalman da zaki sanya" Tani ta yi maganar tare da nufar Shoe rack din É—akin, Inda jerin takalman Zeenatu suke na gayu masu tsini da flat, ta É—auko mata yellow kalar head É—inta.


 Ta dawo ta ajiye mata su agabanta, ta koma ta É—auko Jewelry box dinta, ta É—auko mata sarÆ™ar diamond da earrings, Bayan ta kammala sanya mata su, sai da ta gyara mata make up É—in fuskarta.


  Ita kanta Tani Kyawun Zeenatu ya tafi da imaninta, Inaga wanda Akayi adon domin shi.


   "Kinyi kyau sosai shalelen daddy musa, Muje kitchen É—in in shirya maki dinner dinsa ki kai mashi"


 Ta amsa mata da "Toh"


  DaÆ™yar take yin tafiya da high hills din Æ™afarta, Bawai don bata saba sanya takalmi mai tsini ba, sai don rashin natsuwarta.


  Bedroom É—inta a second floor Yake, Ƙa'ida ne idan zata sauko down stairs sai dai Ta hau elevator saboda a wurinta wahala ne taka bene.

 Atare da Tani suka Hau elevator É—in ta sauko dasu down, da kwarkwasa take yin tafiya tana taka tiles sautin na bada kwas kwas kwakwas.


 Kaitsaye kitchen suka nufa, tun daga Cikin Katafaren palourn gidan kana Iya hangen Masu aikin dake safa da marwa acikin kitchen, a tsakiyar falon ta dakata da yin tafiya.


 Tani tace "Bari na É—auko maki Kayan abincin" ta Æ™arasa maganar tare da juyawa ta nufi kitchen, badajimawa ta fito hannun ta ruÆ™e da wooden tray faffaÉ—an gaske, daga saman shi wasu haÉ—aÉ—É—un Warmers ne da flatware da sauran kayan abinci"


  "Anya kuwa zeenatu zaki Iya ruÆ™e tray din nan? Naji da nauyi, ko dai In raka Æ™i É—akin nashi"?


  Girgiza mata Kai tayi"a'a Zan Iya ki bani kawai" miÆ™a mata tray din tani tayi,

  Ta rurruÆ™e shi da hannu Biyu, tana tafiya tana rangwaÉ—a, Tani dake a tsaye ta Æ™urawa bayanta ido, ita tasan daÆ™yar zata Iya kai shi É—akin ba tare da ta 6arar dashi ba.

  


Ɗakin da aka warema Dr shureim a gidan baida banbanci dana sarki saboda luxury furniture dake a cikinsa, sam ta manta ba ta tambayi Tani a wani room ya sauka ba, sai faman wurwurga eye balls ɗinta take yi a ƙoƙarinta nata gano masaukinsa, Cikin sa'a ta hango ɗaya daga cikin ɗakunan dake a rufe ƙofar shi ta buɗe hakan na nufin anan aka saukar da shi.


A lokacin Yana a kwance saman katafaren gadon ɗakin, Ya cire Jallabiyar jikinsa, Iya short ne fari, ya zame arab turban din kansa, Kwantacciyar sumar kanshi baƙa wulik, ya sanya singlet tabi shape ɗin ƙirjinsa.


Bacci ne ya ɗauke shi gefen shi wayarshi ce ajiye yana cikin kallon hotunan abar ƙaunarsa bacci yai awon gaba da shi.


  "Yaya shureim É—ina" Muryar Zeenatu ce ke Æ™wala mashi kira, tun kafin ta Æ™arasa bedroom É—in.


  "Ya ya shureim am coming" kasancewar tana da zaÆ™in murya mai tsiwa har cikin kunnanshi yake jin muryarta.


  "Yaya shureim" firgigit! ya farka daga baccin haÉ—i da miÆ™ewa zaune la66ansa na ambaton sunan Allah, idanuwanshi har sun canza launi saboda bacci.


   É—akin Yabi da kallo a Æ™oÆ™arin shi na ya gano ta inda zata 6ullo, sautin takun tafiyarta ne Yaja hankalin shi ga kallon Æ™ofar É—akin.


  DaÆ™yar ta ke tafiya, sai faman zabga murmushi take yi akan fuskarta, tun da ta shigo É—aki ta tsayar da blue eyes É—inta akan fuskarshi, da Æ™arfi ta furta hubby na" kamar a mafarki shureim ke kallon zeenatu, kamar yau ya fara ganinta sam ya kasa motsawa daga zaunan da yake saman gadon.


    Ganin yadda take yin tafiya babu natsuwa yasa shi yin saurin furta"bari nazo na taimaka maki" maimakon ta dakata da yin tafiyar tun da yace zai taimaka mata, sai ma ta Æ™ara saurin tafiyar da take yi, a hanzarce dr shureim ya haura Æ™afafuwanshi ya sauko daga saman gadon sai dai kafin yai saurin zuwa gareta, Cikin rashin sa'a takalmin Æ™afarta ya karkace ai ko Gaba É—aya Ta saki tray É—in hannunta Ya kife saman tiles kayan abincin ciki duk suka tarwatse, Nan take zanin da aka É—aura mata Ya warware Ya zame Æ™asa, Daga Ita sai É—an pant É—inta.


  Runtse ido dr shureim yai, ba arziÆ™i ya dakata da yin tafiyar.


  Jikinta sai kerma yake yi, Kunya duk ta isheta muryarta na rawa ta soma magana"wayyo Allah na, Am sorry yaya shureim wlh duk zumuÉ—in ganinka ne bansan ya akai zanin ya warware ba, gashi na zubda maka kayan abincin" ta yi maganar tana faman yarfa hannayenta, Kunyar duniya ta ishe shi 


  "Yaya shureim bari na koma Tani ta gyara min É—aurin zanin, yanzu zan dawo maka da wani abincin tun da wannan Ya 6are" saboda tsabar ruÉ—u Anan tabar mashi zanin da kallabinta da ya warware, da takalmanta, da gudu ta juya ta fuce daga É—akin  


  A hankali dr shurem ya buÉ—e idanuwanshi Yana kallon 6arnar da Zeenatu tayi mashi, rashin natsuwar yarinyar ba Æ™aramin burge shi yake yi ba, Saboda yana samun nishaÉ—i sosai, tsabar shiririta ita da tace za taje a gyara mata zani ta tafi tabar zanan a Æ™asa.


  Yaushe rabon da ya yi dariya irinta yau harya manta, Hada dafe cikinsa tun da zeenatu tabar É—akin bata Æ™ara dawowa ba saboda Kunya gare ta, kamar ba jinsin turai ba, Tani ce tazo É—akin ta bashi hakuri game da 6arnar da zeenatu tayi mashi yace mata bakomai ai yarinyace yana yi mata uziri, Bayan tani ta kwashe kayan da ta 6arar mashi, Ta koma kitchen ta canzo mashi wani abincin ta dawo ta kawo mashi, kafin Tani tabar É—akin sai da ta tattara kayan zeenatu da ta bar masa zaninta da É—an kwalinta da takalman duka ta kwashe ta fuce da su, dr shureim yaso ta dawo suyi fira sai dai yasan abune mai wuya ta bari su Æ™ara haÉ—uwa yau sai dai zuwa gobe idan kunyar ta sake ta.


*PRISONERS MIDDLE STEP💋❤*


Ƙarfe 7 na safe agogan San antonio ta buga, adai dai lokacin Sojojin sun zo duba marasa lafiyansu daga headquater, mutun uku ne Commender, Major, tare da Captain sun zo cikin shigarsu ta kaki, A office ɗin dr. Laura davis suka fara zama domin tattaunawa.


    A6angare Angel tana Æ™udundune cikin bargo tasha baccinta, sai mutsu mutsu take yi duk ta yamutsa bedsheet É—in ga dukkan alamu mafarki take Yi, A firgice tafarka HaÉ—i da yakice bargon ta wurgar da shi gefe É—aya, hannayenta biyu saman fuskarta, cikin shaÆ™aƙƙar murya take ambaton sunan Danish, Mummuna mafarki tayi akanshi Ya farka Ya rikiÉ—a ya zama dodo Yana shan Jinin mutane, Hankalinta duk yabi ya tashi haiÆ™am gani take kamar mafarkinta zai iya zama gaskiya.


  Ta yi zurfi acikin tunaninta muryar Nurse ta Fargar da ita

   "Barka da safiya Masoyiya Angel, fatan kin wuni Lafiya" da sauri ta É—aura idonta kan fuskar nurse É—in


  In a cool voice ta amsa mata Lafiyalou


  "How are you feeling today? Are you experiencing any pain?" girgiza kai Angel tayi"A'a"

   "Okey, nasan zaki buÆ™aci shiga toilet, ki gyara fuskarki, akwai sojoji da suka zo suna son ganawa dake, Amma kafin nan Zan kawo maki breakfast É—inki ko kina da za6i na abunda kike son ci"?


  Girgiza kai Angel tayi"a'a"

  Okey daga haka Nurse É—in ta juya ta fuce, Saukowa tayi daga saman gadon abakin Æ™ofar shiga toilet ta zura slippers dake ajiye saman carpet, kafin ta tura door din ta shige ciki.


   A hankali take tafiya tana bin ko'ina na toilet É—in da kallo A tsaftace yake fari Æ™yal Kamar ba'a ta6a amfani da kayan Cikinsa ba.


  Agaban mirror Ta tsaya tana kallon Kyakkyawar fuskarta, batasan lokacin da murmushi Ya kubce mata ba, nan take dimples É—inta biyu suka lotsa, yatsun Hannayenta, ta tura cikin sumar kanta, a hankali ta soma barbaza gashin, aranta ta ayyana inama akai su saloon Agyara masu gashin kansu ba Æ™aramin kyau za su yi ba, fanfo ta kunna Ruwa Ya soma kwararowa cikin sink, ta shigo da niyar ta wanke fuskarta sai kuma ta tsinci kanta da sha'awar son Yin alwala, nan take ta canza ra'ayinta, Tsarki ta fara yi kafin ta soma Yin ta a tsanake, bata manta komai na daga yadda akeyin alwala ba, bayan ta kammala Yi, ta fito daga Cikin toilet É—in tana Tunanin tayaya zata Iya yin sallah bayan babu Hijabi? BuÉ—e Æ™ofar da akayine yasa ta É—ago tana kallon mai shigowa nurse ce ta shigo hannunta ruÆ™e da tray na kayan breakfast É—in Angel asaman table ta É—aura mata shi.


    ÆŠagowa tayi suka hada ido da juna"Is there anything you need?"


  Da sauri tace"Hijabi da abun sallah inaso zanyi" 

    Da murmushi akan fuskar nurse É—in tace"are u muslim"? ÆŠaga mata kai Angel ta yi alamar eh, nurse É—in tace"Okey, ki jira ni yanzu zan dawo"


  Fuce wa tayi daga É—akin, Angel ta sauke ajiyar zuciya, tana Æ™are ma É—akin kallo, shigowa nurse É—in tayi hannunta ruÆ™e da hijab da Prayer mat ta miÆ™a mata, Farin Ciki a wurin Allah bakinta yaÆ™i rufuwa.

  "Thank u so much" nurse É—in na murmushi tace da ita"never mind" ita kanta batasan Ina ne alÆ™ibla ba, sai da ta tambayi nurse É—in tayi amfani da wayar hannunta wurin yi mata bincike ta gano mata AlÆ™iblar da zata fuskanta tukunna ta shimfiÉ—a carpet É—in, a tsanake ta kabbara sallah, saman chair nurse din ta zauna tana jiranta, Raka'a Biyu Angel tayi kafin ta sallame sallar, wani irin daÉ—i take ji yau tayi sallah, bakinta yaÆ™i rufuwa, tafin hannayenta biyu ta É—aga sama tana karanto addu'o' kirari tafara yi ma Allah kafin tayi ma Æ´an uwanta da suka rasu addu'a, da su kansu a Æ™arshe ta roÆ™i Allah akan Ya haÉ—a ta da Æ´an uwanta ba tare da ta sha wahala ba, Allah yasa daddynta Yana araye, da auntynta Aneelerh. bayan ta kammala Yin addu'ar, Ta shafa a fuska, ta yunÆ™ura ta mike, ta nannaÉ—e prayer mat É—in da hijabin ta dubi nurse É—in


  "Kin gama" É—aga mata kai Angel tayi alamar eh, MiÆ™ewa tayi tare da zuwa gaban angel ta kar6i carpet din da hijabin juyawa tayi ta nufi closet É—in É—akin ta buÉ—e ta sanyasu aciki.


  "Aduk lokacin da kika buÆ™aci yin ibadarki zaki iya É—auka ki yi" godiya Angel tayi mata, daga bisani ta zauna zaman Cin breakfast, lafiyayyan kalaci aka haÉ—a mata, tana ci tana tunane tunane sam tamanta da sojojin dake jiranta.


  Sai da ta kamalla cin abincin ta Æ™oshi, Nurse É—in ta tattara komai ta fuce dashi, Zama tayi gefen gadon idonta akan ceilling ta Æ™urawa haÉ—aÉ—É—en kwan É—akin ido, Yayin da zuciyarta ke tariyo mata abubuwan da suka faru.


Ba zato ba tsammani ta tsinkayi muryoyinsu a yayin da suke shigowa ɗakin, A hanzarce ta miƙe tana faman zazzare gray eyes ɗinta akansu, sojojinne tare da likitocin, saman doguwar sofa ɗin ɗakin suka zauna a jere suna fuskarta, Dr Laura davis ta zauna gefenta, Kamar wata mara gaskiya duk ta kama kanta, Hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba.


  "Masoyiya Allah fatan Kin wayi gari lafiya? Ya jikin naki" muryarta adabarbarce tace"da sauÆ™i sosai" cikin kulawa suke Yi mata magana da harshen turanci


  Dr Mark jackson ne ya fara yi mata magana"mun nemi jin bayani daga bakin É—an uwanki Gabriel sai dai bai bamu haÉ—in kai ba, Yace duk abunda muke son sani ke ce zaki amsa mana.


 Jin wannan maganar yasa hankalinta Æ™ara É—ugunzuma.


  Fahimtar yanayin ta ne yasa dr mark cewa" Ki kwantar da hankalin ki, Bamu zo da niyar mu takura maki ba, Ƴan tambayoyi ne zamuyi maki da zarar kin amsa mana zamu tafi, munfiso ki natsu kiyi nazari kafin ki amsa mana" 


  "Kin shirya"? ÆŠaga mashi kai tayi alamar eh, duk tabi tasha jinin jikinta.

  "Da farko zamu so ki fada mana Ya akai kuka tsinci kanku A daji? Waye ya kai ku can? Sojojin kasar mu suna hasashen É—an Ta'addan daya gudu zuwa canne Yai garkuwa daku don ya kare kanshi daga farmaki da suka kai mashi, shin dagaske ne ko kuwa? Ƙura masu ido ta yi É—aya bayan É—aya take kallon fuskokinsu, tsabar fargaba Æ´an hanjin cikinta sai kaÉ—awa suke Yi, Tarasa Tayaya zata fara basu amsar tambayarsu? sam ba ta jin zata Iya faÉ—a masu ainihin Abunda Ya faru da rayuwarsu, ita aganinta kamar idan suka ji zasu guje su ne, musamman idan Danish Ya farka a matsayin giant ba Æ™aramar masifa zaija masu ba, Zaiyi wuya su yarda da abunda zata faÉ—a masu, saboda Labarin baÆ™ar izayar da suka sha a prison ba kowane zai gasgata kalamanta ba, zama su Iya tunanin Æ™arya take yi masu, bayan haka tana tsoron ta fada masu, su kuma su tara Ƴan jarida su sanar dasu a É—auki hotunansu ayi share da labarin prison tabbas yin hakan zai jaza masu babbar matsalar da zata Iya ja su rasa rayukansu don tasan dole Shuwagabannin kurkukun Æ™addara su bibiyi rayuwarsu ko dan saboda abu biyun nan na farko Garkuwar kurkukun da su ka gudu da shi, Na biyu don kada su tona masu asiri.


 duk da sanyin A.c dake ratsa fatar jikinta hakan bai hanata zubar da zufa ba, ta ko'ina take tsastsafo mata, Hakan ba Æ™aramin É—aure masu kai yai ba, farat É—aya suka fahimci akwai wani gagarumin al'amari atattare da yarinyar sai dai zaiyi wuya ta iya sanar da su gaskitar zance.


  Gyaran murya Commender yai mata, A hargitse ta wurga eye balls É—inta akan fuskarshi


  "Kin yi shiru baki ce komai ba meyasa"?


  Dafa kafaÉ—arta dr laura tayi da hannu É—aya"Ki kwantar da hankalin ki my daughter, Ki natsu ki bamu amsa, a shirye mu ke da mu taimaki yaruwarku, haÉ—in kanki kaÉ—ai muke buÆ™ata, kuma muna tabbacin zaki  Amsa mana tambayoyin mu"


 gaba É—aya ta ruÉ—e saboda saÆ™e saÆ™en da zuciyarta ke yi mata, wani sashe Yana jan kunnanta akan karta kuskura koda gigin wasa tace zata faÉ—a masu abunda ya faru a rayuwarsu, Yayin da wani sashe na zuciyarta ke Jan hankalinta akan ta faÉ—a masu wata'Æ™il su taimaka masu wurin kawo Æ™arshen Azzaluman kurkukun Æ™addara, Yanzu idan ta 6oye masu taÆ™i faÉ—a masu gaskiya kwatsam wani abin da ba'a fata ya zo ya same su har su rasa rayukansu shikenan tarihin kurkukun Æ™addara zai cigaba da wanzuwa ne.


  Sun tasata gaba kamar sun sami tv, duk sun Æ™agara da su ji amsarta, gashi taÆ™i buÉ—e baki tayi magana.


   "Idan har baki bamu amsar tambayoyinmu ba, zamu maida ku Dajin da muka É—auko ku"! Acewar Major


 Ras Taji gabanta ya faÉ—i, Lokaci É—aya ta fashe masu da matsanancin kuka mai ratsa zuciya Cikin shessheÆ™ar kuka take faÉ—in"Ni bansan komai ba, Bazan Iya tunawa ba, Namanta komai, É—an uwana danish shi ya sani"


  Ta Æ™ara rikita masu lissafi, Captain yace"kun haÉ—a baki ne? Mun tambayi É—an uwanki Gabriel ya faÉ—a mana cewa ke kaÉ—aice kika san komai, Yanzu kuma mun tambayeki kince kema bakisan komai ba A tambayi Danish! Why kuke son Yi mana yawo da hankali....? Da alama Ya Hasala ne dan muryarshi a kausashe yake mata magana.


  Da sauri dr laura ta katse shi"Sir, bata da Æ™oshin Lafiya, Ni a ganina bai kamata mu tsareta da tambayoyi ba a yanzu, Æ™aramar yarinya ce sai ana lalla6ata"


  Sassauta fushin fuskarshi Yai, Cikin kwantar da murya yaci gaba da cewa"Okey, Share hawayenki, ki daina yi mana kuka bama so" Muryarta Na rawa ta amsa mashi da toh.


  MiÆ™ewa Dr laura ta yi ta nufi fridge ta buÉ—e ta É—auko mata fanta me sanyi, ta haÉ—o mata da tissue, Ta dawo gefen gadon ta zauna tare da miÆ™e mata tissue É—in, Hannayenta na kerma ta kar6a ta soma goge Æ™wallarta da hancinta, Bayan ta gama share hawayen dr laura ta miÆ™a mata lemun kar6a tayi tare da yi mata godiya.


kamar tasan Mayyar fanta ce, Buɗe wa tayi agaban su ta kur6i ruwan lemun kusan sau uku tana sha, Sun tsareta da ido suna kallonta, hakan ba ƙaramin rikitar da ita yake yi ba.


  "Pls Masoyiya Angel, Ki taimake mu ki taimaki rayuwarki da ta sauran Æ´an uwanki, Ki faÉ—a mana gaskiyar abunda Ya faru a rayuwarku wanda yai silar haifar maku da ciwon damuwa, Idan har baso kikeyi mu maida ku daji ba" acewar Captain.


  "Abunda mukeson sani shine Ya akai kuka tsinci kanku a Æ™urmin dajin Evil forest? saboda É—an ta'addan Æ™asarmu da muke hasashen shine Ya kai ku can mun titsaye shi akan ya faÉ—a mana menene alaÆ™ar shi da ku, Ya faÉ—a mana cewa Baisan komai dangane da ku ba, Ya taimaki wasu daga Cikin Æ´an uwanku ne, Munyi dogon nazari akanku, da farko munyi tunani Æ´an Æ™asarmu ne ku, sai kuma muka ji kuna magana da wani harshe wanda bana nahiyarmu ba! Mun rasa gane daga wani Jinsi ku ke? sannan menene maÆ™asudin haddasa maku ciwon damuwa da baÆ™in ciki? lamarin ya É—aure mana kai da Æ™ananun shekarunku? hada me fama da ciwon zuciya! Wani abun al'ajabin É—aya daga cikin Ƴan uwanku yaÆ™i farkawa daga bacci mun rasa gane meke damun shi......" tun da major ya soma yi mata magana a tsanake ta tsare shi da ido tana kallon la66ansa har ya Æ™are maganarsa, tukunna ta fara magana

  "Gaskiya ne abunda É—an ta'addan ya faÉ—i, bashi ne yakaimu daji ba, Mun jima Acan kusan zance tun kafin mu mallaki Hankalin mu, bazan Iya tuna abunda Ya faru arayuwar mu ba, kome yakai mu Dajin, abunda na sani shine Munci baÆ™ar wahalar rayuwa dani da Æ´an uwana, wanda silar hakan yajaza mana depression...."

  Kallon Juna su ka yi, still sun fahimci bazata faÉ—a masu abunda suke son ji ba, sam bata son su sani babu alamun zata yarda da su.


  Murmushin gefen fuska Major ya sakar mata"Ni dama tunda naga idanuwanki da Æ™aramin bakin nan Naki raina ya bani kina da wayau sosai," duÆ™ar da idonta Æ™asa Ta yi zuciyarta na bugun uku uku.


  Dr. Laura sam ba ta so suka matsa mata da tambayoyi ba, tuntuni ta basu shawarar su bari Yaran su saba da su tukunna amma da yake Sojoji ne Yana É—aya daga cikin Halayansu, Idan suna son jin bayani daga bakin mutun ba wani uziri da suke Yi mashi dolenshi ya amsa masu.


  "Yaren da ku ke yin magana da shi na wace Æ™asa ne"? Captain ne Ya jefa mata tambayar.


 Muryarta na É—an rawa ta furta"Ni.. geria" Tsabar mamaki ne yasa su kallon Juna.


  "Kina nufin daga Nigeria ku ke? Tayaya hakan zai yiwu? Dama Nigeria suna da farar fata ne acikin su? a iya sanina baÆ™ar fatane mutanan Nigeria, Sannan matansu kuma basu da dogon gashi, kuma Launin idonki Kalar na mutanan Æ™asarmu ne"

  Dr. Mark jockson ne Yai maganar da alamun mamaki akan face É—insa

 Dr. Laura na murmushi ta dube sa"kada ka bani kunya mana, ko mu a Æ™asarmu ai akwai black americans, zai Iya yiwuwa suma suna da alaÆ™a da fararen fata ne ina nufin half cast"


     "Dagaske Ku É—in Ƴan Nigeria ne? Jinjina masa kai tayi"Eh, ai yaren da muke yin magana dashi hausa ne na nigeria, zaku Iya bincikawa"

     Ba Æ™aramin mamaki suka yi ba, Hatta turancin da yaran suke magana da shi sak Na america ne bana Nigeria ba.


   "Yanzu dai bazaki faÉ—a mana gaskiyar abunda ya faru da ku ba ko! To Shi É—an uwan naki da kika ce yasan komai tayaya zamu Iya farkar da shi daga bacci"! Anzo dai dai wurin da tafi so, marairaice masu fuska ta yi"maganinshi Yana a nigeria, dan Allah ku taimaka ku maida mu Æ™asarmu, idan ba haka ba É—an uwanmu zai Iya mutuwa" hada Æ™wallarta

  "Meke damun shi ne" Dr Brown ne yai mata tambayar, batare da ta yanke shawara da zuciyarta ba tace"nima bansani ba, Idan yafara bacci yana É—aukar tsawon lokaci bai farka ba, to akwai maganin shi kuma yana acan Æ™asar"

  Murmushi kowannansu ya saki, hakan yasa tasha jinin jikinta, Commender yace"Kin Iya acting, da farko kince bazaki Iya tuna komai daya faru a rayuwarku ba, amma ayanzu kin faÉ—i inda za'a samu maganin É—an uwanki hakan na nufin tunaninki yana nan baki manta komai ba ko"? É—aure mata fuska yai "Zaki faÉ—a mana gaskiya ne? Ko kuwa kunfi so mu je dake can headquater Ki amsa mana tambayoyinmu ta tsiya" tashin hankalin da ba'a sanya mashi date

  Maganar commender tayi matuÆ™ar tsoratar da ita Jikinta Ya hau yin kakarwa duk tabi ta rikice, A Æ™arshe data ga dagaske zasu titsayeta saita amsa masu tambayoyi ko su tafi da ita headquater, aiko da Æ™arfi tasa wata irin gigitacciyar Æ™ara data firgitar dasu, Hannayenta Biyu ta sanya ta daddafe kanta tana faÉ—in"Nace maku ni bansan komai ba! Dan Allah ku maidamu Æ™asarmu Nigeria, É—an uwana zai Iya rasa ranshi, Na roÆ™e ku idan har dagaske zaku taimaki rayuwarmu to ku maidamu Nigeria wurin danginmu," kamar mahaukaciya haka tadinga nanata masu akan su maidasu Nigeria.


  Hankalinsu Ba Æ™aramin tashi yai ba, ganin yadda Ƙwayar idanuwanta suka burkice Launin Ciki Ya 6ace sai zallar farin idon, Jijiyoyin wuyanta dana Gaban goshinta shatunsu ya fito ruÉ—u ruÉ—u, Jefar da robar fanta hannunta Æ™asa ta yi, a zafafe Ta miÆ™e saman gadon kamar Æ´ar daba, ta dunÆ™ule hannayenta, taci gaba da ambaton Ku rabu dani ku Æ™yaleni, Ku maida mu Æ™asar mu Nigeria nace ku kaimu Æ™asar mu, can muke son zuwa"


 Har suna haÉ—a baki wurin lallashinta"sorry ki kwantar da hankalin ki, zamu tafi yanzu, Ki daina kuka ki kwantar da hankali, Ki koma ki kwanta, babu wanda zai Ƙara tambayarki wani abu" sun firgita da ganin haukan Angel.


  Dr laura duk tabi ta ruÉ—e Sun rasa gane kanta.


 Kallon Sojojin ta yi"Pls, Ku Æ™yale yarinyar nan, Muje office muyi magana, idan ba haka ba za'a Iya samun matsala" gyÉ—a kai sukayi ba don sunso ba suka Juya tare da fucewa daga É—akin tare da Likitocin, Ya rage da ita sai Dr laura.


  "Pls My daughter kukan Ya isa haka, Ki koma ki zauna muyi magana kinji"? Lallashinta tashiga yi, DaÆ™yar Angel ke iya kallonta sumar kanta duk ta rufe mata fuska, dagangan ta Æ™irÆ™irarma kanta Ciwon hauka.


  Marairaice mata fuska Angel tayi"dan Allah ki taimaka mana, su maida mu Æ™asarmu, banaso mu rasa É—an uwanmu zai Iya mutuwa, maganinsa yana can, Nayi maki alÆ™awarin idan ya farfaÉ—o zan fada maku duk wani abu da ku ke son ji dangane da mu"


saukowa Angel tayi daga saman gadon, A sukwane ta zube saman gwiwowinta agaban Dr laura, Idanuwanta sun cicciko tab da hawaye take faɗin"Na roƙe ki Ki taimaka mana, kamar yarda Allah Ya taimake ki, Kice ma sojojin can sumaida mu Nigeria, Idan ba haka ba Ɗan uwana danish zai mutune, ba zaku Iya sarrafa shi ba, maganinsa yana acan, Ni na yarda ku sanya jami'an ku, su bimu can kasar don su shaida abunda na faɗa masu su sanya mana ido' Muryarta ashaƙe ta ƙarasa maganar.

  Tsananin tausayintane Ya kama dr. Laura har cikin ranta ta aminta da yarinyar, MiÆ™a mata hannu tayi"miÆ™e tsaye" da sauri Angel ta É—aura hannayenta asaman na dr laura, ta yunÆ™ura ta miÆ™e, ba zato ba tsammani taji ta rungumeta a kirjinta, Æ™amshin turarenta Ya daki hancin Angel sosai ta Æ™ankameta tana faman sauke ajiyar zuciya.


  Shafa sumar kanta dr laura tayi a hankali take yi mata magana

  "Ni tun farko banso suka tsareki da tambayoyinsu ba, sunyi gaggawar yin hakan, But Inaso ki kwantar da hankalin ki, Zanyi iyakar bakin Æ™oÆ™arina wurin ganin sun maida ku Æ™asar ku, idan har kikayi min alÆ™awarin zaku faÉ—a mana abunda ya faru da ku bayan É—an uwan naki ya farfaÉ—o kamar yadda kika ce"

  Cikin sanyin murya Angel tace"Nayi maki alÆ™awari shiyasa ma nace su sanya jami'an da zasu bibiyi rayuwarmu" ta Æ™are maganar tare da raba Jikinta daga na Dr laura

 Shafa fuskarta tayi"is ok, Zanje muyi magana da su yanzu ki koma ki kwanta ki huta"


 Amsa mata Angel tayi da toh, Bayan fitar dr laura, DaÉ—i kamar zai kasheta, don tana ji aranta zasu amince masu su koma Nigeria, juyawa tayi tana neman robar fantar data jefar a Æ™asan tiles can ta hangota gefen nightstand zuwa tai ta É—auko lemun ta koma gefen gadon Hankali kwance taci gaba da shan lemun fatanta Allah yasa su amince masu. 


Gaba É—ayansu sun Hallara a katafaren ofishin dr laura, Kowan nan su Ya samu wuri ya zauna saman haÉ—aÉ—É—un kujeru, table ne Ya ratsa tsakaninta da su,.


  "Shawarar da zan bada shine bai kamata mu takura masu da tambayoyi ba, duba da Yanayin yaran akwai ciwon damuwa atattare da su, tursasa masu zai Iya haddasa masu wata matsalar da bama fata" Dr laura ce ta kora jawabin idonta akan faces din sojojin

  Commender yace"Ya zamuyi kenan? Menene Mafita don muna buÆ™atar son Jin ainihin abunda ya faru da su a dajin nan"

  Numfasawa dr laura tayi"Munyi magana da yarinyar, tabbas bata manta komai ba, tasan abunda ya faru da rayuwarsu sai dai rashin yarda da tsoron fargabar abunda zai biyu baya idan ta faÉ—a mana sun Hana ta sanar damu, abun duba anan shine Babu yarda za'ae su saki jiki damu don ta yanzu, saboda basu sanmu ba bugu da Æ™ari kuma ba Æ´an kasar mu bane, donni na yarda da maganarta, Idan har munaso muci nasara akansu dole sai mun yi masu abunda su ke so, ta hakanne zasu saki jiki damu har su faÉ—a mana gaskiyar abunda mu ke son ji daga gare su, sannan suna buÆ™atar wadda zata Kula da rayuwarsu tamkar mahaifiyarsu, Ta hakanne zasu saki jiki da ita har su Iya faÉ—a mata damuwarsu, abu na biyu shine Muyi masu abunda suke so! Musamman ita Angel din ta roke ni akan mu maida su Æ™asarsu, Akan idonku kunga haukan da tayi mana tabbas akwai Æ™amshin gaskiya a maganarta, tace maganin É—an uwansu yana acan, kuma tace zamu Iya sanya jami'ae su bi su har can kasar sannan tayi alÆ™awarin idan harya farfaÉ—o zata faÉ—a mana duk abunda muke son ji.


 Shiru suka É—anyi na wani lokaci kowan nan su Yana nazarin maganar dr laura.


  Numfasawa Major yai kafin ya soma magana"Me zai hana mu damÆ™a Case É—insu ya koma hannun Hukumar Isod? (Intelligence Special Operations Division) Tun da shugabansu ÆŠan Æ™asar Nigeria, su kaÉ—aine zasu Iya bincikar Ainihin abunda Ke faruwa da yaran, saboda suna da Æ™warewa a 6angaren.


  Jinjina kai Commender yai da alama ya gamsu da jawabin Major


  "Hakane ka kawo shawara mai kyau, case É—in yafi dacewa dasu, Tunda Aikinsu ne Yin binciken sirri Harma da fafatawa idan ta kama kuma duk muna atare dasu banbancin kaÉ—an ne mu ba jami'an sirri bane su kuma duka sun HaÉ—a sunayin aiki a matsayin sojoji sannan kuma jami'an sirri" 


   Captain Yace"Nima na goyi bayan hakan, amma fa zaiyi wuya mu iya samun chief É—in nasu a waya, So the best way to contact him is through email, We need to start making our request for the case through their email, If they show interest in the case, we will turn everything over to them."


Commender yace"shugaban nasu ai  Yana a Washington (babban birnin america) kuma naji raÉ—e raÉ—en kamar cikin weekend da zamu shiga zai bar Æ™asar ya koma Nigeria, duk da bani da tabbaci kunsan aikin nasu na sirri ne babu mai sanin shiga da fucen su, Idan har muka samu ya nuna interest akan case É—insu komai zai zo mana da sauÆ™i, In yaso sai mu damÆ™a mashi Yaran ya tafi da su can, mu kuma zamu dinga bibiyarsu don jin ya ake ciki"


  Murmushi Dr laura tasaki, Har cikin ranta ba Æ™aramin daÉ—i taji ba, Fatanta Allah yasa Chief É—in Isod Ya amince da case É—in Yaran, ko dan saboda Yarinyar da ta roÆ™e ta akan amaida su Æ™asarsu"


   "Doctor, how long do you think it will take for the children to be discharged"? captain ne yai mata tambayar,


Dr. Laura ta bashi amsa da cewa "After the three-day injection course is completed, we will be able to discharge them, Shima Ɗayan Yaron mai fama da ciwon zuciya Zamu Iya sallamar shi idan har aka Kiyaye sharuɗɗan da zamu rubuta na bashi kulawa ta musamman, " ta ƙara da cewa"zasu Iya zama a asibitin namu har zuwa lokacin da shi chief ɗin zai Amsa mana buƙatar mu"


  Commender yace"dole ne mu sama masu wadda zata Iya kula da su tamkar Æ´a'Æ´anta kamar yarda kika bada shawara, wadda zata Iya tarairayarsu ta basu kulawar da zasu Saki Jiki sosai," Yai maganar yana kallon fuskar dr laura

    Major yace"why not bazamu damÆ™a amanar kula da yaran a hannun UMMIN AMERICA ba? Tun da itama Ƴar Asalin Æ™asar Nigeria ce, hatta yaren da naji Yaran suna magana da shi itama tana jin shi sosai" Jin Major Ya ambaci sunan Ummin america yasa Dr Mark da dr brown Kallon Juna ga dukkan alamu sun girgiza da jin an ambaci sunanta, Dr laura ta zaro ido tana faÉ—in" The Baddest mistress? There's no way we can leave the children in her care, She's a dangerous woman. How could she possibly know how to take care of them?" hankalinta bai kwanta da zancen miÆ™a yaran ga Ummin america ba saboda sanin wacece Ita.


Bayan ta ƙare magana Major yace"Ai ba yau tafara Yi mana aiki ba, tana taimaka mana sosai akan irin case ɗin nan, Ina da tabbacin zata Iya! Fiye da yadda baki tsammani"Kwa6e fuska Dr laura Tayi don ita har aranta Fargabar Ummin americe take ji, Kowa yasanta sananna ce a 6angare Iya karuwanci tantiriyar ƴar bariki ce, tayi ƙaurin suna america shiyasa su ke yi mata laƙabi da Ummin america, tsabar Iya shaiɗancinta har award ake bata akan Iya Karuwanci.


   "Mu zatayi ma aiki, bai shafi sana'arta ba, Kawai munaso Yaran su kace a hannunta amatsayin guardian É—insu, Kafin Mu damÆ™a mata su zamu yi yarjejeniya da ita idan har ta amince to lafiyalou ba zamu samu matsala da ita ba" ta6e baki dr Laura tayi"amma dai ba'a asibitin mu za'a gayyato mana ita ba, Don ina jin fargabar ta rikitar mana da ma'aikatan mu da surar jikinta"


 Gaba É—aya suka sanya dariya jin abunda tace, ta faÉ—i hakanne don tasan Ummin America kamar maganaÉ—isu take awurin Iya jan hankalin mutun da surar Jikinta, Dirine da ita na bala'e'

Sunjima suna tattaunawa a tsakaninsu kafin daga bisani Commender yace


   "Dr mun gode sosai da shawarar ki, Zamu koma bakin aiki Yanzu, Idan har Chief din isod Ya amince da buÆ™atar mu zamu tuntube ku" 


  Daga haka Sojojin sukayi Ma Dr laura sallama, Har bakin parking space na asibitin ta rakosu, Bayan tafiyar sojojin suka dawo Cikin asibitin. 



 *Boss Bature✍️ Mu haÉ—u gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun Æ™addara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuÉ—in*




First bank




3196407426, 




*Bature Hafsat Muhammad, za'a tura evidence of payment ta phone number É—ina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*

Post a Comment for "Kurkukun Kaddara Book 2 Page 17"