Kurkukun Kaddara Book 2 Page 15
_~*BossLadiesWriters*~_
_*KURKUKUN ƘADDARA*_
_The Prisoners E15🔥💫_
*Daga alƙalamin Boss Bature*
~Middle step~
Lokacin da ta ɗago daga sujjadar fuskarta jaga jaga da hawayen, Tafin Hannayenta ta ɗaga sama ta soma ambaton sunan Allah tana Yi mashi kirari, Hakan Ba ƙaramin ruɗar da likitocin yai ba, shi dai Gabriel sai murmushi yake saki yana dubanta, Bayin Allah su kaɗai suka san Wahalar rayuwar da suka fuskanta Dole suji daɗin wannan Ranar, Ta jima tana addu'a,
Sam takasa miƙewa daga zaunan da take, Hawayen fuskarta tamkar zasu ƙare Sai sintiri suke yi saman kuncinta
"Angel pls stop shedding ur tears" Gabriel ne Yai mata maganar, Cikin shessheƙar kuka ta ɗago ta Kalle shi da rinannun idanuwanta waɗanda suka kada jawur da su
"Gabriel dole in yi kukan farin Ciki, kai ka sani irin wahalar da muka sha, munyi rayuwar kulle tamkar dabbobi har ƙwara ni akan sauran ƴan uwana tun suna jarirai, wannan ne karo na farko da zasu ɗanɗani rayuwar ƴanci acikin ƴan uwansu mutane, Iya cuta an cuci rayuwarsu mun tsira amma raunin dake acikin zukatanmu na har abada ne, saboda akwai abubuwan da muka rasa wanda nayi imanin baza su ta6a gogewa a tarihin rayuwarmu ba"
Hankalin likitocin ba ƙaramin tashi yai ba ganin yadda take kuka tana surutu gashi ba su fahimtar abunda take cewa, sai dai sun gane akwai abunda ke damun su wanda yai silar haifar masu da ciwon damuwa da baƙin ciki
Gabriel da ke a tsaye tuni shima ya fara zubar da hawaye.
Gabanta ne Ya ɗan faɗi Jin kukan Jemimah, Nan take shessheƙar kukan da ta ke yi ya dakata, Dr. Laura ce ta shigo Ɗakin hannunta ɗauke da Jemimah Tsabar jaraba ta runtse idanuwanta sun yi suntum saboda kuka, Sunan Genie kaɗai Take furtawa, jikin Angel na rawa Ta yunkura ta miƙe da sauri ta nufi dr. laura Hannu biyu tasa ta kar6eta sosai ta rungumeta a ƙirjinta, hannunta hada cannula da aka sanya mata.
"Angel" Muryar Batul ce ta ratsa kunnuwanta, da sauri ta É—ago tana kallonsu, A jere su ke shigo É—akin kowan nan su Yasha kuka Idanuwa sunyi luhu luhu, doguwar suman kawu nan su A hargitse kamar waÉ—anda aka koro daga gidan mahaukata.
Kowan nan su Na sanye da light blue uniform da aka sanya masu, hannayensu sanye da cannula na drip da aka sanya masu.
Batul ce ta farko, Bayanta Parveen ce da hannah, Sai mazan Javed da Naufal, da gudum gaske suka ƙarasa shiga ɗakin gaba ɗaya suka ƙanƙame Angel kamar zasu kada ita ƙasa.
Al'ajabi Ya hana Likitocin cewa komai, Sun saki baki galala suna kallon Ikon Allah, Aransu suna Mamakin ƙaunar da suke yi ma ƙaramar Yarinyar da su ke kira da Suna Angel.
Farin Ciki kamar zai kasheta, Daɗi take ji tarasa ina zata tsoma ranta, Sun lullu6eta suna yi mata kuka, ko numfashi daƙyar take Iya fitarwa
"Angel ina ne nan? Wanene Ya kawo mu? Wlh tsoro muke ji, munga wasu mutane da bamu saba gani ba, kada su cutar damu Angel, sai kallon mu suke yi kamar zasu lashe mu" Su parveen ne ke kora mata jawabi
"Ko dai mafarki muke Yi ne? Mu dake acikin Daji Ya akai muka tsinci kanmu a wannan wurin tare da wasu mutane masu fararen Kaya, Angel ko dai Aljannace da kike bamu labari? Idan mun mutu zamu shiga" Maganar Batul tayi matuƙar bata dariya, Daƙyar ta samu suka saketa, Ga jemimah ta ƙanƙameta Jikinta sai kerma Yake yi.
Azeeza tana maƙale da Gabriel Sarkin tsoro, Ta kasa ɗauke idanuwanta daga kan faces ɗin Likitocin dake a tsaitsaye cirko cirko suna kallonsu.
"Angel mun shiga ku, Sai kallon mu suke yi," Hanna ce ta yi maganar
Muryar dr. Laura ce ta katse masu Hanzarinsu cikin harshen turanci ta ke yin maganar
"Ku kwantar da hankalinku, babu wanda zai cutar daku, Anan inda kuke Asibiti ne, mu kuma da kuke gani likitoci ne da nurses haƙƙinmu ne kula da Lafiyarku, Za mu taimaka maku don ganin kun warware daga lalurar dake damunku, Muna so ku ɗauke mu tamkar Ƴan uwanku, idan ku ka yi hakan munyi maku alƙawarin zamu share maku hawayenku, Zamu gatanta ku mu baku kyakkyawan kulawa har izuwa lokacin da zamu miƙa ku ga Iyayen ku.
Tun da tafara Yi masu magana kowannansu Ya natsu yana sauraronta, da alama sun fara fahimtarta
Matsowa Kusa Dr Brown Yai daga gefenta Ya tsaya"duk wani abu da kuke buƙata zamu yi maku shi, ku ɗauka tamkar kuna a gidan Iyayenku ne, burin mu shine ku bamu haɗin kai, Ku daina Jin tsoron mu"
Muryar Dr Jack Ce Ta janyo hankulansu ga dubanshi
"Mun haɗa ku wuri ɗaya ne saboda mun fahimci ba za ku ta6a sakewa damu ba, idan har ba Kuna atare da Ƴar uwarku Angel ba, Muna fata Yanzu hankalinku zai kwanta, ga ku ga Mamanku Angel" Da zolaya yayi masu maganar, murmushi Angel ta saki tana kallonsu, daga gani suna da mutunci.
"Masoyiya Angel faɗa min me ki ke yi wa Yaran nan naki ne? Don na lura ba ƙaramin ƙaunar ki su ke Yi ba" Dr Brown ne yai magana haɗi da ɗaga mata gira ɗaya, Sunnar da kanta ƙasa Tayi dariya takeso tayi sai da takasa.
"Yaushe kika haife su ne? Sannan Ina Mijin naki"? Kunyace ta rufe Angel da sauri ta ɗaura Kanta saman sumar kan Jemimah dake ruƙe a hannunta.
Dariya Dr. laura ta saki"Wow Kunya take ji, To ko dai Matashin saurayin nan mai bacci ne mijinki? Wannan kyakkyawan don naji kamar kina ambaton sunanshi" gaba É—aya sun sanyata jin Kunya ji take kamar ta nutse ga farin Ciki da ya lullu6eta.
Da biyu likitocin suke zolayarta, Yana daga cikin aikinsu kwantar da hankalin Mara lafiya musamman su da suke son su saki jiki da su, Ta hakanne zasu samu bayanan da suke so daga gareta.
"Mun fahimci Masoyiya Angel bakinta ya mutu, saboda An sosa mata inda ke yi mata ƙaiƙayi, Yanzu faɗa min me kikeson Ci ke da Ƴan uwan naki mu kawo maku" Cikin kulawa Dr. laura ke yi mata magana.
Kallon sauran Ƴan uwan nata tayi
"Ko ba ku jin yunwa ne"? Shiru suka yi ba wanda Ya bata amsa, idonsu akan Angel, Dariya doctors É—in suka saki
"Oh Baku Iya magana sai da izninta, to ke masoyiya Angel Faɗa mana me kikeso akawo maki keda Ƴa'ƴan naki don bama son barinku da Yunwa"
Cikin Jin kunyarsu Angel ta furta"komai muka samu zamu ci" Jinjina kai Dr Laura Tayi kafin ta juya ta kalli Sister rebecca"A shirya masu lafiyayyan abinci da Kayan sha" amsa mata Tayi da toh da sauri ta juya ta fuce.
Dawo da dubanta tayi akan fuskokinsu
"Yanzu zamu tafi mu baku wuri Pls Idan an kawo maku abincin Ku tabbatar Kun cinye min shi duka kaf, zanji daÉ—in hakan,' dr Laura davis Na rufe Maki Dr Mark Yace"Zamu dawo Da Anjima, Kyawawan Æ´an mata, dole in za6i É—aya daga cikin ku, irin wannan Kyau haka"
Dr Bown Yace"ai ba kai kaÉ—ai ba mutumina, Ni ruwan ido ma ya hanani zabar É—aya, ta ko'ina Kyau nake gani musamman Masoyiya Angel ta tafi da ni" Dariya ce ta kubcewa Angel da Gabriel
Harara Dr Laura davis Ta watsa mashi"bazaiyiwu ba, Duk na riga ku, Nima nayiwa Æ´a'Æ´ana kamun matan aure a Cikin su' NishaÉ—i sosai suka sanya su.
"Zamu tafi Masoyiya Angel, Amma kafin nan Ki kula mana da Æ´a'Æ´anki, Ki lallashesu su daina mana kuka dake kanki bama so kuna zubda tsadaddun hawayenku" Cikin sanyin murya Angel ta amsa mata da toh, Sallama suka Yi masu atare suka fuce daga É—akin suna masu santin Kyawun Yaran acikin ransu.
Fitarsu keda Wuya Ange Ta fada saman Gadon rungume da jamimah tana tiƙar dariyar Farin Ciki tana faɗin"ALHAMDULILLAHI ALA KULLI HALIN"
"Kuyi Farin Ciki mana, Ina Tayamu murna Mun ku6uta daga Kurkukun ƙaddara, Mun zama masu ƴanci" Su Batul sunƙi sakin jiki har yanzu basu fahimci Ta ya ya akai suka tsinci kansu a wannan wurin ba.
Gabriel ne yai ƙoƙarin fahimtar da su abunda Ya faru zuwan Sojoji Dajin.
Wayyo Allah daɗi Wani irin annurin farin cikine Ya bayyana akan fuskokinsu, Bakunansu sun kasa rufuwa Fararen haƙoransu tamkar Gonar auduga
"Gabriel kana nufin Yanzu mun bar kurkuku da daji? Muna acikin Mutanan duniya" Fuskar Gabriel da murmushi Ya amsa masu"ƙwarai kuwa, Babu ku babu zubar da hawaye baƙin ciki da kunci sun ƙare" Tsabar Farin Ciki Suna kuka suna dariya, gaba ɗaya suka Haye saman Gadon Angel, suka kwanta a jere da ita sai daɗi suke ji saman ceilling ɗin ɗakin suka ƙurawa ido kowa Yana tariyo abubuwan da suka faru a rayuwarshi jin shessheƙar kukansu ta cika ɗakinne Yasa ta soma yi masu magana cikin lallashi
"Dan Allah ku daina, Yanzu lokacin farin ciki ne, Godiya yakamata Muyiwa Allah, a koda yaushe shi mahaƙurci mawadaci ne, yau gashi dai mun shaida hakan Allah ya kar6i kokenmu yaji ƙanmu ya raba mu da ƙangin rayuwar da muke aciki, A yau mu masu ƴan ci ne zamu shaƙi Iskar duniya son ranmu batare da wani yayi mana Iyaka da ita ba" Murmushine Ya bayyana akan fuskokinsu
Cikin shessheƙar Kuka Azeeza ta soma magana tana fadin"Ni ƴan uwanmu nake tunanawo waɗanda muka rasa acikinmu, tare da Salsabeel da ya taimaki rayuwar mu, nasan dole su kashe shi idan suka kama shi Yana acan kurkuku Suna azabtar dashi"
Naufal ya ɗaura da cewa"babu Deeja! Babu Mubeen Akan idonmu ya yanke jiki Ya faɗi, a lokacin muna aga6ar barin kurkuku....." Kasa ƙarasa maganar Yayi saboda kukan da ya ciyo shi.
Javed ya dasa daga Inda ya tsaya"Mun rasa tsohuwa tamira! Mun rasa Eve da Yasmin sannan mun rasa Hibba da Rubina, da Sarah! " tunkan Ya rufe Baki Angel ta ɗaura da cewa"Allah Sarki Unaiza Ƴar gidan daddy, da Majnoon Bayin Allah ban ta6a tunanin zamu tsira ba tare dasu, Muna ƙaunar ƴan uwanmu sosai, Sai dai mutuwa tayi mana Yankan ƙauna, Ta raba mu da su, In sha Allah zamu haɗu da su agidan Aljanna inda babu kurkukun ƙaddara babu duk wani mugu, Allah sarki tsohuwa tamira da Salsabeel waɗannan bayin Allahn Har duniya ta naɗe bazamu ta6a mantawa dasu ba, saboda Sun kafa tarihi acikin zukatanmu In sha Allah a koda yaushe zamu dinga binsu da addu'a, sannan zamu Cika masu burin su na ruguza tarihin KURUKUKUN ƘADDARA.
Abubuwa da dama suke tariyowa na rayuwarsu na baƙin Ciki da farin Ciki
"Angel Danish fa har yanzu bai farfaɗo ba, Haris kuma Bashi da ƙoshin lafiya nurse ta faɗa min abunda ke damun shi ni nasan silar deeja ne, Amma tace Ciwon nashi bazai jima ba, Zaiji sauki"
Jin wannan maganar yasa gabanta faɗuwa, A hanzarce ta miƙe zaune saman mattress ɗin, su Batul ma suka mimmiƙe suna kallonta, sun sha kuka fuskokinsu sunyi jawur dasu abunka ga farare, Ita dai Jemimah tunda ta lafe ma angel hankalinta kwance bata da sauran damuwa.
Ƙasa ƙasa da murya ta ambaci kalmar Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Gabriel Akwai matsala! Wai ni wace ƙasa ce wannan"? A matuƙar ruɗe ta jefa mashi Tambayar, duk budurin da akeyi bata lura da fararen fata bane sai da yayi mata zancen Danish.
"Ni kaina Angel bansani ba" Dafe kai tayi da hannu É—aya, Yayin da take bin ko'ina na room É—in da kallo, karaf idonta ya sauka akan wani hoto dake manne jikin bango, a jikin shi an rubuta
SAN ANTONIO TEXAS United states of America
zazzare idanuwanta waje tayi wuƙi wuƙi Muryarta Na kakarwa ta soma maimaita Sunan America, tun da take arayuwarta bata ta6a taka kafadarta a ƙasar waje ba, Iya Nigeria ne, Yau ƙaddara Ta jefo su America a maimakon Nigeria! Hankalinta idan yai dubu toh ya tashi, ta ya ya zasu Koma Nigeria har su samu damar ɗauko ruwan zamzam da zasu ba Danish? Don tana Ji aranta Baccin da yake yi bana lafiya bane zaiyi wuya ya farka batare da giant's heart ɗinsa ta motsa ba, Muryoyinsu Aruɗe su ke ambaci sunanta"Angel menene? Bamu tsira ba ko? Wani abu zai faru damu"? Girgiza masu kai tayi muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"Wlh ba Nigeria bace wannan ba ƙasa ta bace, America ce ƙasar turawa, taya akai haka ta faru!? Nauyayyar ajiyar zuciya suka sauke, don su basu san abunda take gujemawa ba, Lamarin ya girgizata har tafara tunanin dama kurkukun ƙaddarar ba A nigeria ya ke ba? Akwai gagarumar matsala dole su nemi mafita.
"Angel ae zamu Iya zuwa can ko"? Da sauri Gabriel ya amsa masu da cewa"Eh mana ba wani abu, kada ku damu kanku, Sojoji sunce idan muka basu haɗin kai zasu damƙa mu wurin Iyayenmu, Idan suka tambayemu sai mu faɗa masu cewa Mu ƴan nigeria ne"
Kafin wani Ya ƙara magana acikinsu, Nurse rebecca Ta turo ƙofar ɗakin Hannunta ruƙe da faffaɗan tray na kayan abinci da aka jera masu, A saman table ta ɗaura masu, kafin ta ɗago tana dubansu fuskarta ɗauke da murmushi tace"Idan kuna buƙatar wani abu zaku Iya kira awaya ku sanar dani" Ta yi maganar tana nuna masu wayar dake ajiye saman table, al'ajabi ne ya kama su wai yau sune ake tarairaya? har tambayarsu ake yi in suna buƙatar wani abu? Wannan wani irin abun farin ciki ne!
Har ta juya zata fuce, Muryar Angel ta dakatar da ita "Sister, which country are we in?" ? ta tambaye ta ne don ta ƙara tabbatarwa
Juyowa Nurse rebecce tayi fuskarta da fara'a ta furta"San antonio texas" idanuwan angel luhu luhu ta ce"Thank u"
Hankalin Angel Yaƙi kwanciya, sam bata lura Sun fara Cin abincin ba, gaba ɗayansu sun dawo bakin gadon, Su parveen banza ta samu, soyayyar kaza mai maiƙo ta damƙa tana turawa abaki atsiyace take cizgar Naman kazar, Jemimah ta sungumi tsiran nama ita da azeeza, Batul kuwa Soyayyan ƙwai ta ɗauka tana Ci har wani nannaɗe shi take yi kafin ta tura abaki, Hannah ko warmer ta ɗauka shaƙe da Chips tana ci, Ba baka sai kunne, Su naufal an dahi Chicken shawarma, Javed ko Kayan marmari ya damƙa yana sha, kamar kwancen Yunwa Sun zaƙe suna ci suna Korawa da lemu me sanyi kala kala aka kawo masu, basu san akwai cctv ba a ɗakin, Duk wani motsinsu ana kallonsu😂
Ita kanta Angel data dubesu saida gabanta ya faɗi, Ganin yadda suke cunkusa abinci abakunansu Kamar kuraye, Muryarta na rawa take faɗin'pls ku bi a hankali kada ku shaƙe" tamkar kurame babu wanda ya dubeta bama su san akan me take magana ba, a dole ta ƙyalesu ta zura hannu ta ɗauki burger tana ci...........
*BARI MU LEƘA GIDA NIGERIA*
*A DAULAR OBIE ESTATE*
A Zaune take dirshan acikin Katafaren Bedroom ɗin Obinna, wa'iya zubilla kai kace ɗakin matashin saurayine saboda tsabar haɗuwarshi, An kashe dukiya a furniture ɗin ɗakin komai na cikinsa launin Red and golden ne, Ko sarki Albarka, Tanƙamemen gadonsa Royal state bed irin gadon da ko mutun baijin bacci ya hau sai Ya runtsa, Ga wasu matassan kai launin red da golden jere a gaban headboard ɗin, Dogayen labulaye ne a kewaye da ɗakin, ga wasu bedside drawers masu ɗauke da lamp, daga saman ceilling ɗin ɗakin Haɗaɗɗen Chandeliar ne dake bada hasken ɗakin ga wata zungureriyar Sofa Bayan ita akwai arm chairs masu ɗan banzan kyau, Ga wani ƙayataccen table dake ɗauke da Kayan Ado na ɗaki. Daga jikin bangon ɗakin haɗaɗɗiyar wallpaper ce mai zanan flowers masu matuƙar ƙayatarwa da jan hakalin me kallonsu, floor ɗin ɗakin tamkar mirrored tiles ne Kana Iya ganin fuskarka a cikinsa tamkar madubi, ga wani Jigunannan Dressing mirror Tafkekan gaske Jerin tsadaddun turarurrukane ne asaman shi da sauran kayan gyaran jiki, idan nace zan cigaba da zayyana haɗuwar Ɗakin dattijon arziki tabbas zamu ƙare takun tsakiya wurin fasalta Kyawunshi.
Yana daga kishingiÉ—e saman lallausar mattress É—in gadon, Apple laptop ce agaban shi, Da alama Video call Ya ke yi da wani, É—abi'arsa ce yana magana yana shafa gemun shi wani sa'in har Jan shi ya ke yi.
Hajiya saratu tayi zaman cin tuwo saman lallausan carpet É—in gaban gadon shi, tana jiran Ya kammala Yin wayar, ta tsare shi da ido babu annuri akan fuskarta, Hankalin shi gaba É—aya yana akan fuskarta, Nazarin yanayinta ya ke yi, kamar daga sama ta tsinkayi muryar shi akanta
"Saratu kin wuni lafiya"? Ƙara tamke fuskarta tayi"lafiyalou baba, fatan na same ku lafiya" murmushin gefen fuska ya sakar mata"Alhamdulillah, in ce ko lafiya? Naga yanayin fuskarki da 6acin rai, Waye ya ta6amin autata ne yanzu in ɗaura ɗamarar yin yaƙi da shi" murmushin Yaƙe ta ƙaƙalo, har ta buɗe baki zatayi magana yai saurin tarar numfashinta"nasan kinzo gaishe da baban nakine kamar yadda kika saba, Naji daɗi sosai mamana, Bari na kira hajjaty A waya ta kawo mana dinner mu ci atare ni da autana" tur6une fuska Hajiya saratu tayi"ba yunwa nake ji ba, Zuwa nayi mu yi magana, kafin barina ɗaki sai da nayi magana da masu aiki nasan sun kai min a ɗakina"
"Ai nasan ba yunwa kike ji ba, Ni nake ra'ayin cin abinci tare da ke, idan mun kammala sai mu yi magana" aruɗe take kallonshi, ƙiri ƙiri Ya hana tayi magana.
Ba tare da ya jira amsarta ba, Ya É—auki waya dake saman bedside drawer, Ya kira landline na kitchen, bugu uku aka É—aga kiran, muryar sophia ce ta ratsa kunnansa cikin girmamawa ta gaishe da shi.
"Ina buƙatar Dinner ɗina a shigo min da shi ɗaki yanzu" amsa mashi tayi da toh kafin yai rejecting call ɗin, idanuwanshi akan saratu da ta haɗe rai, kasa jurewa tayi don baƙaramin takura tayi ba hakan yasa ta soma magana ba tare da ta jiran umarninsa ba.
"Baba ni gaskiya ba a kyautamin agidan nan, akan me za'a dinga kushe min ƴa'ƴana ana yabon na wasu, abun yana ƙona min rai bana jin daɗi, haba dan Allah wannan ba adalci bane, kuma ba girman Yaya Lateef bane da yaya mubarak su zauna suna faɗan maganganun marasa daɗi akan ƴa'ƴana, ni kaɗai ke ba'ason ya'ya na a family din nan ko dan saboda ban auri jinsin mu bane" Rai a6ace take yin maganar, tun da ta fara magana bai dakatar da ita ba, ya natsu yana sauraronta idonshi akan fuskarta, dama tun kafin ta fara yin maganar yasan meya kawo ta, Yana mamakin Halin saratu, ko irin alkunyar nan babu, idonta ya rufe akan ƴa'ƴa da miji, abu ɗayane take jin nauyin yi wato idan tana zazzaga masifa bata bari su haɗa ido dashi, murmushine akan tausasan la66ansa
"Kin gama maganar ko akwai saura" bata É—ago ta kalle shi ba idonta na akan carpet É—in da take a zaune dirshan
"Hateem Faɗa min menene sunan macan da take ɗaukar zigar miji"? ras taji gabanta yai mugun faɗuwa, A ruɗe ta ɗago da ido tana kallon fuskar obinna, ƙayataccen murmushine akan fuskarshi, Ji take tamkar ta yunƙura ta miƙe ta zuba da gudu don ta fahimci Video call yake yi da Yayanta hateem na ƙasar Canada, Hakan na nufin duk wata magana da ta ke faɗama babansu akan kunnanshi, Hankalinta ya tashi don ba ƙaramin jin shakkar shi ta ke Yi ba, duk acikin yayunta tafi fargabar sharafudden da hateem.
A hankali Obie Ya juya mata Lapton ɗin gabanshi don suyi magana da Yayanta, sunnar dakai ƙasa tayi sam ta kasa ɗagowa ta kalli screen ɗin laptop nasa
DaddaÉ—ar muryar prime minister Hateem ce ta ratsa kunnuwanta
"Ji ra kike in gaishe ki"? Girgiza kai tayi tamkar tana agabanshi, cikin girmamawa ta soma gaishe da shi
"Ina wuni Yayana, Ya aiki Ya iyali"
"Ki É—ago da ido ki kalle ni Saratu"! Da kakkausar Murya ya furta hakan, Yawu ta haÉ—iya kafin A hankali kamar maijin tsoro ta saci kallon screen É—in.
Tabarakallahu ahsanun khalikin!! Ni kaina da nake rubutawa sai da alƙalamina ya girgiza da ganin Kyakkyawar surar nan mai cikar kamala, gwarzon namiji jajirtacce, kallon ɗaya zaka Yiwa fuskarshi ka shaida Jinin Obinna ne, Yana ɗaya daga Cikin waɗanda su ke kama da babansu, basu baro komai nashi ba, Kyanshi, ɗabi'unsa da halayansa, Fatarshi kaɗai abun kallo ce, yadda kasan da ruwan madara ake mulketa saboda tsabar kyau, skin colour ɗinshi launin na mahafinshi ne, A zaune yake Cikin Katafaren Office ɗinsa dake a Presidential residence Na ƙasar Canada, tsayawa zayyana kyawun Office ɗin da dukiyar da aka kashe masa wurin zuba kayan cikinsa abune da hankali ba zai ɗauka ba, wata'ƙil zamu ƙare Takun tsakiyane wurin zayyana shi, wasu hadaddun tailored suit ne a jikinsa sunbi shape ɗin jikinsa, mutumin akwai ƙira.
"Bai kamata kiji kunyar haɗa ido dani ba Saratu, tunda har kika iya tako ƙafafuwanki kika zo ɗakin baba don kiyi mashi masifa, Ke ko kunya bakya ji? Ki zauna Miji Yana ziga ki Kan ƴan uwanki? Sara Ba haka nasanki ba, Ni ba haka ƙanwata take ba, jarumar macace mai hankali da tunani, why kike son bani Kunya"? Maganar Hateem tayi matuƙar sanyata jin kunya, duk sai ta ji haushin kanta ya kamata, tayi danasanin zuwa ɗakin obinna, saboda tana matuƙar jin nauyin Hateem, da ace tasan da shi suke yin video call da batayi gigin zuwa kawo ƙorafi ba.
"Kiyiwa kanki faɗa saratu, Ba girmanki bane, Ƴa'ƴanki ai namu ne, babu wani banbanci, nasan abunda Yaya mubarak da Yaya lafeef zasu faɗi bazai wuci akan Cigaban Ƴa'ƴanki bane, maisonka shike faɗa maka gaskiya duk min ɗacin ta, Maƙiyinka kuwa sai dai Ya 6oye maka yakamata Kiyi tunani ƙanwata" Cikin kwantar da murya yake yi mata nasiha, shi kanshi Obinna har lumshe ido yake yi saboda jin daɗin nasihar da Hateem Yake yiwa ƙanwarshi, kuma ga dukkan alamu jikinta yayi sanyi sosai
Muryarta tamkar zata fashe da kuka ta soma magana"In sha Allah yaya zan kiyaye, bazan ƙara biye mashi ba, zuciya ce ta ɗibe ni, Ni kaina nasani kuna son ƴa'ƴana shiyasa kuke yi masu faɗa don su gyara, duk wanda ya rasa faɗi a duniya yai asara, ina jin daɗin ƙoƙarinku akaina da ƴa'ƴana, Allah ne kaɗai zai Iya biyanku" idanuwanta har sun cicciko da ƙwalla
"Kada ki bari hawayen nan su zuba, Kinsan banaso ko"? ÆŠaga mashi kai tayi alamar eh"Okey yi min murmushin nan naki in gani" Dariyace ta kubce mata, da sauri ta É—aura kanta saman manyan laps É—inta
"Ya aikin naki? Fatan komai na tafiya lafiya" amsa mashi tayi da"lafiyalou"
Jinjina kai Hateem yai"Allah ya taimaka" sallama sukayi da ita Obie Ya juya laptop É—in, idon shi akan Hateem
"Shiyasa nake Ƙaunarku, Saboda ku ɗin na dabanne, ƴa'ƴana abun alfaharina, Allah Yabar munku, ubangiji Allah ya tsare mun ku Ya kare munku daga sharrin maƙiya da mahassada......"addu'o'i obinna yadinga jero mashi, Yana masa mashi da ameen ameen hada saratu wurin amsawa daga bisani Suka yi sallama dashi
Rufe laptop ɗin yai tare da miƙe ma saratu, Yunƙurawa tayi tare da matsawa gaban gadon ta kar6i laptop ɗin ta nufi saman desk ɗinta ta ɗaurata.
"Assalamu akaikum" muryar Hajjaty ce ta ratsa kunnuwan su, atare suka amsa mata da wa'alaikum salam shigo daga Ciki, Tura ƙofar tayi kamar kullum fararen Kayane a jikinta, Tasha uban ado kamar amarya, sam bata gaji da ca6a ado, Hannayenta sun sha ƙunshi na jan lalle.
Hajiya saratu dake a tsaye tana kallonta, Haushin Matar take ji, ta tsani taga ƴar aiki tana ɗaukar wanka kamar yar masu gida, zuciya da saƙe saƙe, sai ta dinga ganin kamar obinna bin jikinta yake yi da kallo, fargabanta kada wata rana dattijonsu ya ƙyasa, Ƙarasawa Hajjaty tayi cikin ɗakin Asaman Carpet ta ɗaura tray ɗin, sai faman sakar mashi murmushi take yi shima ɗin mayar mata da martanin murmushin yake yi, Hankalin Hajiya saratu yaƙi kwanciya Tana a tsaye ta ruke qugunta
"Yalla6ai fatan ka wuni lafiya, tun ɗazu nake jiran shigowarka gidan bansan kun dawo daga masallaci ba, ae da tuni na jima da kawo maka abinci" Yanayin yadda take magana muryarta tamkar ana busa sarewa, ƙamshin turarenta Ya addabi hancin hajiya saratu
Lumshe ido yai kafin ya amsa mata da"lafiyalou Alhamdulillah, nagode da kulawarki agareni, Kina ji da dattijon nan naki sosai nima na yaba da hakan"
Fuskar Hajiya saratu a ɗaure ta furta"ke! Tashi kibar ɗakin nan tunda kin kawo mashi abincin,ya gode sai anjima" miƙewa Hajjaty tayi tare da jiyawa ta kalleta"Ina wuni hajiya"
"Da ban wuni ba kin ganni, Ƴar rainin wayau sai yanzu kikasan dani aɗakin, dallah ni zo ki fuce waje" jikin Hajjaty yai sanyi duk sai ta ji ba daɗi
"Inaso zan zuba mashi abincin...." tunkan ta ƙarasa Hajiya saratu ta daka mata tsawa"Nace ki fita ko"? Matsawa tayi tare da fusgo hannun Hajjaty taja ta waje, Obinna dake a kishingiɗe saman gadon ƙayataccen murmushine akan fuskarshi, lamarin saratu sai addu'a ya fahimci kishin mahaifin nata takeyi.
Bayan fitarsu daga ɗakin, a bakin ƙofar suka tsaya da tafiya, Hajiya saratu na faman ciccije le6e ta furta"Ni ban yadda dake ba, akan me zaki dinga zuwa ɗakin Ubanmu, balallaga dake Ina laifin Ki turo matasan ƴan matan masu aikin su dinga yi mashi hidima"? Idanuwan hajjaty tuni sun cicciko tab da ƙwalla, ta tsani faɗan hajiya saratu, a shekaru kusan tsaran junane amma ta tasata gaba tanayi mata faɗa kamar wata ƙanwarta
"Ai shine ya za6eni bani nake kawo kaina ba, Yafi so ina yi mashi hidima, kuma ki tambaye shi zai fada maki hakan" Harara Hajiya saratu ta watsa mata"ae dole ya za6e ki, tun da kin riga kin asirce shi da wannan munafukin turaren naki, mace sai kace karuwa, Kin bi jiki duk kin feshe da turare Bakisan haramin bane mace ta fesa turare mai ƙarfi ba? Ina laifin wanda zaki ɗan matsa a hammata!" yawu hajjaty ta haɗiya batare da tace mata komai ba
"Idiot, daga yau karki kuskura In ƙara ganin Kin a ɗaki babanmu, tun fil azal ni baki kwanta min araina ba, Ina raga maki ne saboda mijina ba dan haka ba wlh da tuni na jima da korarki can ƙauyanku na can india, A tsawace takai ƙarshen maganar tare da ingiza hajjaty, tai taga taga zata faɗi daƙyar ta samu ta dafe bango, dogon tsoki Hajiya saratu ta buga kafin Ta juya ta koma ɗakin obinna.
Jiki asanyaye hajjaty ke tafiya yayin da hawaye ke bin fuskarta, Da mayafin hannunta take share ƙwallar dake sintiri saman kuncinta, Kalaman Hajiya saratu sun ƙona mata rai.
Tun fitar Hajiya saratu daga ɗakinta, Pravin Yana zaune gefen gadon shi, Shi da Tagwayensa zayn da zayn, suna zaune saman sofa, ransu ya 6aci matuƙa babu annuri akan fuskokinsu
"Yanzu me kuke so ayi"! ya jefa masu tambaya yana mai kallon fuskokinsu
"Ka sama mana hanyar da zamu bar ƙasar nan, saboda mun gaji da zaman gidan nan, a takure muke kowa baya son mu kusan kullum ne sai anyi mana Gori" murmushin gefen fuska Pravin ya ɗan saki Yana duban ya'yan nashi cikin so da ƙauna
"Kun bani Kunya wlh, Why maganar mutane zata dame ku? Har wani ya isa yasa kubar Danginku? Kenan wata rana zaku Iya kashe kanku saboda wani ya 6ata maku rai eye"! ɗaure mashi fuska suka yi don sun fahimci uban nasu babu zuciya a ƙirjinsa, shiyasa bai ganin illar abunda ake yi masu, yafi so su zama masu matattar zuciya irin shi
"Daddy pls, ka fahimce mu, bama jin daɗin zama gidan nan, america muke son komawa da zama" girgiza kai pravin yai"bazaiyiwu ba, ai baku keda kanku ba, Nima ina buƙatar ku atare dani, Ku faɗi wani abun na daban da kuke so zan iya yi maku shi" magiya suka dinga yi mashi akan ya amince masu su koma america,
"Daddy bafa da kuÉ—inka xaka É—auki É—awainiyarmu ba, munsan komai kakeso mommy zata yi maka taimakonmu kawai zakayi mu samu ta amince mana"
Ɗaure fuskarshi yai"saboda ni bani da arziƙin da zan Iya ɗaukar nauyinku"? Girgiza kai sukayi atare
Ta6e la66ansa yai"bansan me kuka ɗauke ni ba, Ita kanta mahaifiyar taku A yanzu bata kama ƙafata wurin arziƙi ba," kallon Juna su ka yi da mamaki akan fuskokinsu
Miƙewa yai daga gefen gadon Ya nufi gaban drawer chest, Ya buɗe ya zaro atm card, dawowa yai ya zauna yana fuskantarsu
"Banyi maku Iyaka da kuɗin dake acikin acct bank ɗina ba, don nasan har abada bazaku Iya ƙarar da su ba, a duk lokacin da kukeso zaku Iya cirar kuɗi ku biya buƙatunku, sannan kuje ƙasar da kuke so, Farin Cikinku shine nawa"
Kallon da suke yi mashi kamar basu yarda da maganarshi ba, saboda sun raina arziƙinsa,
Still murmushine akan fuskarshi yace"baku yadda da mahaifinku ba ko"? Shiru basu tanka mashi ba, Aransu suna ayyana may be babu ko sisi a atm É—in, idan ma akwai kudi to Na mommynsu ne tunda ita ke da kuÉ—i.
Miƙa hannu pravin yai tare da ruƙo wayarshi dake a gefenshi, kamar sakarkaru haka suka tsare shi da ido suna kallon shi, Daddana wayar yayi kafin Ya miƙa masu da sauri Zayn ya kar6i wayar Suka haɗa ido suna kallon screen ɗin wayar, Total balance ne na kudin dake a acct bank dinsa, tsabar firgita har saida suka ɗan zabura ganin millions of dollars, wanda a kuɗin nigeria Billions ne.
AruÉ—e suka haÉ—a baki wurin furta"Daddy Numbobi ne waÉ—annan ko kuwa kuÉ—in ne dagaske" dariya ya sakar masu
"Abunda idanuwanku suka nuna maku, Just ku É—auki atm É—in zan tura maku pin É—insa ta text message," lamarin yai mugun É—aure masu kai,
Girgiza kai Zayn yai"a'a daddy kuɗin sunyi mana yawa, ni tsorona ma kada ace Na mommy ne" Miƙa mashi wayar yai
"Idan har kuka bari na kar6i atm É—in nan kada ku ta6a tsammanin zan taimaka maku!" Kallon Juna sukayi zuciya na azalzalarsu akan su kar6i atm din suyi sharholiyarsu
"Zayn mu kar6a ko"? Girgiza kai zayn yai"A'a zaid kuÉ—in mommyne fa, idan muka ta6a zata gane ni dai ban goyi bayan hakan ba"
"Pls zayn tun da daddy ne ya bamu just mu kar6a kawai"
"No zaid, kuɗin sunyi yawa zasu sa mu shagala mu daina yin sallah ne" Pravin dake kallonsu ba ƙaramin dariya suka bashi ba.
"Har yanzu akwai ƙuruciya atattare daku, kuɗin kuke gudu? Ai nayi tunanin idan na baku jiki na rawa zaku kar6a, ban ta6a tunanin kuna da zuciyar Imani akan kuɗi ba, Sam baku da haɗama, Ga dama ta samu amma kuna ƙoƙarin yin watsi da ita"!
Muryar zayn na rawa ya furta"Daddy zamuyi shawara tsakaninmu, ka ajiye mana atm ɗin zamu kar6a" jiki na rawa ya ruƙo hannun Zaid suka fuce daga ɗakin.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa Ya maida atm ɗin inda ya ɗaukosa, komawa yai gefen gadon ya zauna yana cin abincin Da abla ta kawoma Hajiya saratu
*Dr.Jazz*
Tun zuwa shi gidan Mommynsa ta ke ta faman tarairayarsa tamkar ƙaramin yaro, Yana daga kishingiɗine saman doguwar sofa ya ɗaura kanshi saman laps ɗinsa, Sai zuba mata shagwa6a yake yi, yatsun Hannayenta na acikin sumar kanshi Tana yi mashi susa
Mahaifiyar Dr.Jazz Baturiyar ƙasar England ce, sunanta na asali Harriet, Silar zuwanta aikatau gidan ta musulunta suka canza mata suna zuwa khadija amma sunfi kiranta da Turai, Farace jawur tana da jiki bata da tsayi launin idonta green ne, sumar kanta launin blonde, A yanzu ba matsayin mai aiki take ba, Matace awurin Sir mubarak, Ya daɗe da auranta tun Bayan rasuwar matarshi Hajiya naja'at, Ƴa'ƴan shi biyu da uwar gidansa gaba ɗayansu ba mazauna Nigeria bane, Suna a ƙasar canada suna kula da Babban companynsu tare da sauran ƴan uwansu dake zaune agidan Hateem.
Turkish dress ne a jikinta, Riga da wando launin red colour, Ta É—aura satin scarve asaman wuyanta, ta zubo da gashin kanta har gadon baya, Allah yayita da ruwan kyau.
"Jazz sai nake ganin kamar baka yi kewata ba, Meyasa bakasan zuwa ganina? kullum Sai in ni na shiga gida nake samun damar ganinka idan naci sa'a baka tafi aiki ba.
Fararen idanuwanshi ya daura akan fuskarta,
"Mommy ba haka bane, Ni just banason haÉ—uwa da daddyne, ya cika faÉ—a, kuma sharri yake yi min yana cewa wai ni mata maza ne, Fisabilillah"
"Ya faÉ—i hakanne donka Gyara rayuwarka, ni kaina ina mamakin shagwa6arka sai kace wani yaron goye, komai naka irin na mata"
ÆŠaure mata fuska yai"mommy kina goyan bayansa kenan, yaci gaba da kira na mata maza"? Girgiza mashi kai tai"A'a, Ai nafi kowa jin haushin inji ya kiraka da hakan, Yana ta6a min zuciyana, donni nasan namiji na haifa ba maca ba" murmushi Jazz Ya saki"to kice mashi ya daina"
"Zan buga mashi warning, kada ka damuwa" maƙe mata kafadai yai"Allah mommy ni nasani wasa kikeyi, saboda ke kanki shakkarshi kike ji ba zaki Iya buɗe baki ki yi mashi magana akan ya daina ba"
Jan kumatunshi tayi da hannunta In jiwa ya faÉ—a maka! Ni bana jin tsoronshi awaja ne mutane ke jin shakkarshi, da zarar ya shigo nake juya shi son raina, Har girki yana yi min" Baki asake Jazz ke kallonta
"Uncle mubarak ɗin"! Jinjina masa kai ta yi"ƙwarai kuwa, ae dukkan Namiji bawan matane,
Har ya buɗe baki zai ƙara magana, Wayar Aljihun wandonshi ta soma ruri, miƙewa yai da sauri ya curo wayar, bayan ya duba sunan mai kiran nashi ya ɗago tare da kallon mommynsa, Wanene ya kira"?
Bai amsa mata ba sai dai ya sakar mata murmushi, da sauri Ya fito daga falon gidan, Kamar wani munafuki duk faɗin gidan bai isheshi ba sai da ya shiga garden tukunna ya dakata da yin tafiyar, Yai picking call ɗin jiki na rawa ya kara ta akan kunnansa, Kirari ya soma yiwa wanda ya kira shi wayar tamkar maroƙi,
"Yalla6ai Kajin nan suna nan cikin ƙoshin Lafiya, Suna samun kyakkyawar kulawa yadda ya dace," dakatawa ya ɗanyi da yin maganar, yana sauraron muryar mai magana,
"Ana basu hatsi yalla6ai mai rai da lafiya, Yanzu haka idan nagama magana da mama zan tafi gidan gona domin duba lafiyarsu," sai faman sakin murmushi yake yi, aladabce yake yin maganar
'kasan kajin turawa saida hatsi mai kyau, Gaskiya basu da matsala yalla6ai, biyu daga cikinsu ne kaÉ—ai suke neman gazawa, shi zakaran ciwon nashi Ya lafa, sauran Kajin muna nan muna basu kyakkyawar kulawa, in sha Allah zasu samu lafiya harma asamu nayin farfesun sallah"
Tuntsirewa dr Jazz yai da dariya hada dafe ciki.
duk wannan surutun da ya ke yi acikin waya baisan Sir Mubarak na tsaye abayanshi ba, daga shi sai gajeran wando, Da singlet fara, hannunshi ɗaya ruƙe da Cup na coffee
Mamaki ne ƙarara akan fuskarshi Jin dr jazz na Zancan kajin turawa awaya
"Okey toh, Zuwa anjima idan nashiga gidan Gonar zan Kiraka Awaya" Daga haka sukayi sallama, Juyawar da zaiyi karaf suka haɗa ido da sir mubarak, tuni yasha jinin jikinsa, Duƙar da kai ƙasa yai ido ya raina fata
"Jazz! Dawa kake magana a waya? Kajin menene naji ana magana akai? Ni dai A iya sanina likitan mutane ne kai bana dabbobi ba" sosa ƙeya jazz yai, mirya dabarbarce yake faɗin"am...umm..dama " Ya rasa ta ina zai taro zancen,
Kallon tuhuma Sir mubarak ke jafa mashi hakan yasashi yin saurin fauzewa
"daddy, Ni da abokina ne dr fawan muka buÉ—e gidan gona, kajin turawa ne muke kiwo, wasu ne babu lafiya shine ya kira muna tattaunawa game da yadda zamu shawo kan matsalar"
Ajiyar zuciya Sir Mubarak Ya sauke"Okey, mu shiga gidan" yai maganar tare da miƙa mashi Cup din hannunsa, da sauri jazz Ya kar6a Yana sha atare suka nufi gidan sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi.
*GIDAN ÆŠAN IYA*
Mahboob ne ke ta faman zuba sauri Yana tunkarar harabar ajiye motocin su, ya ɗauki wankan shadda, tunkan Ya ƙarasa idonshi ya sauka akan motar Uncle abdallah, ƙura ido yai yana kallon bayan motar sunanta Ya karanta, Aranshi Ya ayyana lallai mutanan nan ba ƙananun shaggu bane wannan mota haka mai tsada! saboda almubazzaranci da rashin sanin ciwon kuɗi, Ina laifin ko ƴar ƙaramar honda mutun ya saya ya wadatar, mutane sun ɗaurewa ƙaryar arziƙi wurin zama, Allah dai ya shirya mu, ae ni wlh ko nayi arziƙi ban Iya fidda kuɗina in sayi mota, na ƙwammace duk inda zanje in taka da ƙafata, idan ma da nisa ne ƙwara in biya kuɗi In hau motar Haya, Ita ma wannan motar da nake amfani da ita ba don babansu abokina ne ya bani kyautarta ba kuma ina ganin mutuncin shi saboda ya ji tausayina ya siyamin ganin ina hawa motar haya yasin da tuni na jima da siyar da ita' Shi kaɗai ya ke yin sambatunsa, Har ya ƙarasa gaban motarshi Ya buɗe front seat Ya shiga Ciki Yana ƴan dube dube, da alama wani abu yake nema, saƙo da lungu na motar yake ta bincikawa, har ƙarkashin seat, tuni ya haɗa uban gumi.
"Ina na ajiye zoben nan Jiya? Ko dai ban shigo da shi mota bane? fuskarshi a hautsine Ya jefawa kanshi tambayar, zurfin tunani ya shiga yi still bai tunano inda ya ajiye shi ba, A ƙarshe Ya soma tunanin kodai Ya shigar da shi ɗaki ne,
Fitowa yai daga cikin motar Ya datse murfin, Jiki na 6ari ya nufi cikin gidan.
Abie da Uncle É—an Iya ne zaune a saman sofas na palourn tare da Uncle abdallah, Sun nutsa suna tattaunawa dangane da 6acewarsu tajuddeen, Mahboob Ya faÉ—o falon Ko kallo basu ishe shi ba hankalin shi na akan zoben shi da bai gani ba.
"Wancan ba mahboob bane? Kamar naso na wayi fuskarshi" Uncle abdalla ne yai maganar,
Girgiza kai uncle ɗan Iya yayi Yayin da yake bin bayan mahboob dake ƙoƙarin karya kwana zai nufi sashen ɗakinsa
"Shine, halan bai gaishe ka ba"?
Murmushi É—auke akan fuskar Uncle Abdalla yace"Tun da muka zo ban yi tozali da shi ba, sai dai naji labarin shi awurin junaid"
Cikin nuna 6acin rai ÆŠan Iya yace"baida wayau ne ai ni bansan baizo ya gaishe ka ba, bari ya fito daga É—akin É—an rainin wayau, Zahra tafi shi hankali"
Abie yace"Ƙuruciyace ke damunshi, Zahra kuma ae tafi shi shekaru baza a haɗata da shi ba"
Ɗan Iya yace"babu wata ƙuruciya atare da shi, Sarai yasan me yake yi sai girman jiki ba wayau" da alama Ranshi ya 6aci da rashin gaishe da uncle abdallah da baiyi ba.
Kafin wani daga cikinsu ya ƙara yin magana Hajiya adama ta fito daga ɗaki hannunta ɗauke da baby junaid, tun da ya dawo daga school a wurinta ya wuni ya hanata sakat duk inda za ta je ƙafarta kafarshi toilet ne kaɗai yake bari ta shiga, Ta canza Kayan jikinta zuwa atampa riga da skirt, Ta yafa mayafi akanta, kafin ta ƙarasa shiga palourn Mamie ta fito daga ɗakin Ummi su biyu ganinta yasa suka nufi wurinta fuskokin kowannansu da fara'a suka soma gaisawa da junansu
Atare suka ƙarasa shiga palourn, Kowa ya samu wuri ya zauna, Kafin suka fara gaishe da Mazajensu, miƙa ma junaid hannu uncle abdallah yai"zonan kyakkyawan Jikana mu gaisa," da sauri Junaid ya sauko daga saman laps din Hajiya adama ya nufi sofa ɗin da uncle abdalla yake azaune Ya haye saman jikinshi yana faman sakar mashi murmushi, shafa fuskarshi yai da tafin hannunshi"Masha Allah mutumina, Ka tashi lafiya? Fadamin meyasa baka je school ba yau? Sannan baka bi mu zuwa masallacin Juma'a ba" Zaro ido Junaid yai haɗi da ɗan girgiza kanshi muryarshi da shagwa6e yace"nafa je, ae yau da wuri ake tada mu duk ranar juma'a, kuma ni ai ban isa zuwa masallaci ba inji mommy" maganarshi ba ƙaramin ƙayatar da su take yi ba, musamman In ya haɗa da shagwa6a,
"Junaid kaji tsoron Allah, Aneelerh ce ta faɗa maka haka? Faɗamin gaskiya ka dai san me ƙarya ɗan wuta ne" jin haka yasa shi saurin sanya tafukan hannayenshi biyu ya toshe fuskarshi Yana tiƙar dariya" muryarshi ƙasa ƙasa ya furta"ba ita bane, ae malaminmu ne yace mu ƙananu ne bamu isa ɗaukar zunubi ba" gaba ɗaya suka saki dariya, bayan sun tsagaita da yin dariyar ne, Uncle ɗan Iya yai masu gyaran murya hakan yasa suka dawo da dubansu gare shi.
"Dama yanzu nake shirin aikawa a kira mun ku, don mu haɗu duka muyi magana, Kafin mu shiga cikin zancen Ina ƙara yiwa baƙinmu barka da zuwa fatan kun wayi gari lafiya" da fara'a Hajiya adama ta amsa mashi a mutunce
Mami tace"tun ɗazu da safe take son yin magana mun fara sai nace ta bari idan kuka dawo daga masallacin juma'a zaifi mu haɗu mu duka mu tattauna tunda abune daya shafi kowannanmu da buƙatar aji shawara daga bakin kowa"
Jinjina kai Abie yai"hakane, Yanzu Ina aneelerhn take"?
"Tana a É—akin zahra, Bari na shiga na kirata" kafin ta mike muryar junaid ta katse mata hanzarinta.
"Ni zan Kirata" Bai jira amsarta ba, Ya sauko da gudu Ya nufi ÆŠakinsu, uncle abdallah ne ya É—an É—aga murya yana yi mashi faÉ—an ya daina gudu kada ya faÉ—i yaji ciwo, Jin haka yasa shi dakatawa da yin gudun ya soma yin tafiya a tsanake
A lokacin Aneelerh da Zahra suna zaune saman gado kowa ya dafi waya suna fira suna chatting, sun É—auki wankan dogayen riguna
"Ba zaki leƙa wurin surukar taki ba? Kin barta a ɗaki ita kaɗai" acewar zahra
"ÆŠazu da safe na shiga na gaishe ta, har ma na tarar da mami zaune suna tattaunawa shiyasa ban tsaya ba,"
"Gaskiya aneelerh ki godewa Allah, surukarki tana da mutunci ta iya magana ga faran faran da jama'a, Ni wlh ba ƙaramin burgeni take yi ba, Inasonta sosai, da ace tana da wani ɗan Bayan Yaya uzair Allah dana aure shi" har cikin zuciyarta take yin maganar,
Aneelerh na murmushi tace"Chief Owais din fa? Ko kin fasa"! farfari Zahra Tayi mata da ido
"shi wannan na dabanne, idan ana maganar ƙarauƙarau ba a maganar Zinari, My dream man inaji araina ma ya kusa dawowa ƙasar jiya har mafarkinsa nayi"
Murmushin gefen fuska Aneelerh ta saki
"Allah Ya cika maki burinki zahra, Ni na ƙosa inga fuskar Owais ɗin nan, har tambayarki nayi hotonsa kinƙi ki nuna min, bansani ba ko rowa kike yi min" dariya Zahra tayi"Ina jin fargabar zuciyarki ta buga silar ganin kyakkyawar fuskarshi, kuma kinga ke matar aure ce bana son ki kalli haramun" Sakin baki aneelerh tayi yayin da take kallonta, tama rasa bakin magana
"Fuskarshi tsadane da ita, idan har zaki Iya biyan farashi sai muyi ciniki in nuna maki" fashewa da dariya aneeleeh tayi jin wani zancen abakin zahra.
Faɗowa Ɗakin Junaid yai tun abakin ƙofa yake faman ƙwala mata kira"Mommy!mommy!" a hanzarce ta kai idonta ga ƙofar
"Babyn mommy lafiya kake ta ƙwalamun kira" tai maganar tare da sakowa daga saman gadon ta nufe shi, hannu biyi tasa ta ɗauke shi tana kallon fuskarshi
"Mommy ana kiranki, ki zo inji su abie"
"Sune sukace ka kira ni"? Ɗaga mta kai yai alamar eh ya ƙara da cewa"ke kaɗai banda Zahra"
Harara zahra Ta wurga mashi"aiko sai naje ɗan baƙin ciki, so kake kayi mun buƙulu wata'ƙil ƙudi ne za'a raba mana,
Saukowa tai daga saman gadon ta É—auko masu mayafi a closet ita da Aneelerh ta yafa mata akanta, atare suka fuce daga É—akin zuwa palour
Hankalin Mahboob Ba ƙaramin tashi yai ba, ganin babu zoben a ɗaki, duk yabi ya birkice ɗakin, ya tarwatsa komai, Hatta zanin gadon shi da fululluka duka yayi wurgar dasu saman tiles, ya zazzago da jerin ninkakkun kayansa na cikin wardrobe kaf dinsu Ya bazasu saman gadonshi, zufa ta ko'ina, Bawan Allah shine har ƙarkashin gado neman zobe, Cikin drawer chest, da laundry basket, kanshi harya fara yi mashi ciwo, ya tsani asara a rayuwarshi, a haukace ya tura ƙofar toilet dinsa ya shiga ciki Yana neman zoben, gaba ɗaya ya fara zaucewa, ganin babu zoben a toilet ɗin ya dawo ɗakin, yana haki zufa sai tsastsafo mashi take Yi, Idanuwanshi sunyi jawur dasu luhu luhu yakai maƙura tamkar zai rushe da kuka, jiri ne ya fara ɗibarshi a hanzarce ya koma gefen gadon shi ya zauna tare da sanya hannayenshi biyu ya tarbe kanshi Takaicin duniya ya ishe shi, bakomai yake tunawa ba face kuɗin da Aka sayi zoben, har zazza6i yai daya miƙa su dubu goma sha biyar. Ahakama kuɗin bada guminsa ya same su ba, Abokin shi ne ya siya mashi zoben saboda ya nuna yana so kuma baida kuɗi.
*Boss Bature✍️ Mu haÉ—u monday Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun Æ™addara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuÉ—in*
First bank
3196407426,
*Bature Hafsat Muhammad, za'a tura evidence of payment ta phone number É—ina 08169856268 Banda kira whatsapp kawai*
Post a Comment for "Kurkukun Kaddara Book 2 Page 15"