Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Babban Goro Complete Hausa Novel

 [9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BISMILLAHI RAHAMIN RAHIM 


Wannan littafin sadaukarwa ne ga Aunty na Anty Maijidda musa 




BABBAN GORO...! 

       

          NA 


KHADEEJA CANDY



1___Tsaye yake gaban wani k'aton dressing mirror, sanye da black suit yana gyara necktie, 

 _Give me freedom give me fire give me reason take me higher see the champions take the field now you define us make us feel proud_

A hankali yake bin sautin wak'ar suna rerewa tare, wani _pear watch_ naga ya ɗauko yasa bayan ya feshe jikin shi da turare _the real man_ tsaye yayi yana kallon kanshi a mirror, nan nima na tsaya ina k'are mashi kallo.

Dogone kuma fari fes mai dogon hanci gashi da manyan ido a gefen bakinshi an manna mashi dimples. 

Murmushi yayi ganin yadda suit ɗin ya zauna jikanshi yayi mashi kyau sosai kamar dan shi akayi shi, sai da ya ɗauki wani _blue oil_ ya shafa a kanshi sannan ya nufo wani ɓangaren na ɗakin, 

Babu komai a gurin sai sai jerin talkama na gani na faɗa, wasu _half cover shoes_  ya ɗauko yasa, 

   Sai da ya sake duba kanshi a madubin sannan ya nufi part ɗin maihaifiyarshi. 


*****


Da sallama ya shigo Safiya ta amsa mishi, zaunawa yayi yana faɗin 

“Ina Momi.?” 

“Tana ɗaki wanka take” 

“ok” 

Hannu ya kai ya ɗauki wani littafi dake saman Center table _The broken heart_


“Man ka karanta news kuwa.?” 

Nasir ne ya shigo yana maganar rik'e da jarida a hannunshi, kai Saif ya girgiza 

“A'a miya faru ne.?”

Jaridar ya mik'a mishi yana faɗin 

“Wai wata yar minister ce tayi k'ok'arin kashe kanka”

“Wow a ina.?” 

Saif ya tambaya bayan ya k'arɓi jaridar,

“A Nigeria”

 Nasir ya bashi amsa 

“Toh mi akayi mata.?” 

Zaunawa yayi yana bashi amsa

“Nima abinda nake son sani kenan nida yan'jarida” 

Sai da Saif ya ɗan karanta jarifar sannan yace 

“Yar minister man fetur ce Dr. Salamatu Abubuwa Yola kuma ita kaɗai ta haifa” 

Safiya ta rik'e baki

 “Amman dai ta mutu ko?” 

“A'a bata mutu ba tana dai cikin mawuyacin hali” 

Saif ya faɗa still yana duba jaridar, 

Safiya ta cige baki 

“Amman wallahi naso ta mutu dan ina jin daɗi ne yayi mata yawa” 

Murmushi Nasir yayi 

“Haba dai kiji ance ita kaɗai mahaifiyarta ta haifa kiyi mata wannan fatan yanzu haka fa mahaifiyarta tana cikin kiɗima” 

“Toh ai gani nake iskanci ne yayi mata yawa idan ba shi ba miye na kashe kai?”

Nasir yace 

“Baki san dalilinta ba” 

“A'a Ya Nasir babu wani dalili ina jin dai kawai ta gaji da duniyar ne ko kuma bata da hankali” Faɗar Safiya, 

Tashi Saif yayi “Allah ya kyauta ni bari na lek'a part ɗin Dad idan Momi ta fito kice mata na fita” 

Kai Safiya ta ɗaga mishi yasa hannunshi aljihu ya fice, 


_LABARAN DUNIYA,_

_Mai Karantawa  Fareeda Muhammad Yabo. Da Farko Ga Kanunsu Bom Ya Fashe A Wata Mashaya Dake Amerika, Isra'ila Ta Shiga Teburin  Tattauna Da Falasdin, Wata Kotu A K'asar Masar Ta Yan Kewa Wasu Matasa Hukuncin Shekaru Goma Gidan Kaso , Shugaban K'asar Turkiyya Zai Kaiwa Takwaransa  Na K'asar Faransa Ziyara, A Najeriya Kuma Wata Yar ' Minister Tayi Unkurun Hallaka Kanta.._


Alhaji Bashir Bature ne kishingiɗe cikin makeken ɗakinshi da aka k'awata da kayan alatu yana sauraren radio dake gefen shi yana aiki,

Salamar da Saif yayi ne yasa shi ɗago kai tare da amsawa 

“Wa' alaikassalam” 

Guri ya samu kusa dashi ya zauna

 “Barkada Safiya Dad” 

Hannu Dad ya kai ya kashe radio sannan ya amsa mishi

“Barka dai Ka tashi lafiya.?” 

“Lafiya kalau Alhamdulillahi” 

Tashi Dad yayi zaune ya kalli Saifa yace “Ya maganar Matarka?” 

Kawarda Fuska yayi yana ɗan sosa kai, 

Dad yace “Saifullahi Hak'uri fa ake da mata, duk wani mai iyali da kake gani hak'uri yake muma da ba muyi hak'urin ba da bamu kai yanzu ba nan gaba kaɗan fa Uba zaka zama idan babu hak'uri yaya kenan? Kaga itama kanta tayi nadama tunda har kaga iyayenta sunyi magana”

Wani guntu numfashi yaja “Dad ni Wallahi halinta ne bana so kuma nayi nayi da ita tak'i ta chanja” 

“Ka daiyi hak'uri ka dawo da ita muga abinda Allah zaiyi” 

“Shi kenan Dad zan maida ta In Sha Allah” 

“Toh Allah yayi maka albarka ya baku hak'urin zama da juna” 

“Amin Dad thank you” 

Tea cup ɗin dake gabanshi ya ɗauka ya kurɓa sannan ya sake kallon Saif 

“Saifullahi” 

A natse na amsa

 “Na'am Dad” 

“Ina son yanzu idan ka fita kaje gidan Dr. Salamatu Abubakar Yola ka bincika min lafiyar yarta dan faɗa min tayi unk'urin hallaka kanta kuma yanzu ma naji a labarai” 

“Ok Dad zanje yanzu dana fita amman Dad an faɗi dalilin yin hakan da tayi?” 

Gyaran murya Dad yayi 

“Har yanzu ni dai banji wani dalili ba ina dai son kaje ka bincika” 

“Yanzu ma dana fita daga nan can zanje” 

“Yayi Kyau karfa ka manta da zancen Matar ka” 

Tashi yayi yana murmushi “Toh Dad bazan manta ba” Sai da yayi mishi Sallama sannan ya fice.

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO...! 


           NA 


KHADEEJA CANDY 



Episode___2


Saif na fita parking space ya nufa, yana shiga motarshi yayi mata key yayi horn aka buɗe mashi gate, 

Hanyar da zata kai shi gidan Dr. Salamatu ya bita yana gudu kamar zai tashi sama daman haka al'adarshi take gudu a mota, 

Yana isa yayi horn maigadi na lekowa yaga Saif jiki na rawa ya bude mashi yana ɗaga mashi hannu, 

Yana yin parking ya fito ya cikin gidan, duk inda yabi gaishe shi ake cikin girmamawa da rawar jiki,

 tun kamin ya k'arasa parlor wata tsohuwa ta tareshi bayan sun gaisa tace 

“Hajiya fa bata nan tana asibiti dan gidan ba lafiya” 

“Eh naji ai shi ne abunda ya kawo ni wace asibitin aka kai ta?” 

“Kings Hospital aka kaita”

Bai tsaya jiran ta k'ara cewa wani abun ba ya ya juya tunda yaji abinda yake son ji. 

     Cikin minti biyar ya isa asibitin yana yin parking ya nufi Emergency,

 Reception ya tafi aka faɗa mishi ɗakin da suke, a hankali yake tafiya har ya isa gurin. 

Tsaye ya tararda Dr. Salamatu, wasu mata na tsaye kusa da ita duk kansu sun rakfa uban tagumi especially ita sai ruwan hawaye take, 

Da sanyin jiki ya k'arasa kusa dasu 

“Dr. Salamatu” 

Da sauri ta kalleshi kamin tayi magana ya rigata 

“Mr President yace nazo na duba jikin yarki ko tayi rai?” 

Cikin muryar kuka tace 

“Eh sunce tana da rai sai dai ban tabbatar da lafiyarta ba dan tun jiya basu barni na shiga ba yanzu ma suna ciki suna duba ta” 

“Okey” 

Kawai yace ya juya da nufin tafiya hakan nan kuma sai ya samu kanshi da kasa tafiyar, juyowa yayi ya zauna a kujerar dake gurin yana kallon kofar ɗakin, 



2 hours later... 

Likitoci uku suka fito daga cikin ɗakin, da sauri Dr. Salamatu ta nufe su tare da matan har Saif, ɗaga daga cikin likitocin ne ya tsaya yana yi mata bayani kamin ya bata izinin shiga, 

    Da sauri Dr. Salamatu ta nufi ďakin su kuma matan dake tare da ita suka samu guri suka zauna. 


                           *******


Zaune take sanye da k'ananan kaya idanunta sunyi wani fari fatar k'aramin bakinta ta bushe sai faman sauke ajiyar zuciya take,

Babu abinda take ji sai tsanar kanta, 

         A hankali ta kai hannunta a baki ta shiga cizon akaifarta, jin an taɓa kofa yasa ta juyo tana kallon kofar,

      Dr. Salamatu ce ta shigo rungume da hannayenta fuskantar shakaf da hawaye, cijin sayyayiyar murya ta kalleta tace

 “Minal My child...” 

Juyarda fuska Minal tayi  “Dan Allah Mummy ki fita i don’t want to see you anymore” 

Sauke hannayenta tayi ta nufota tana faɗin “Minal ina son ki-” 

Hannu ta ɗaga mata tun kamin ta k'araso kuda da ita 

“No Mummy i don't want to understand i hate you karki zo kusa dani” 

  Cikin tsawa take maganar tana k'ok'arin saukowa saman gadon, 

Da sauri tayi baya tana matsar kukan dake son fito mata, 

Dai-dai lokacin Saif ya shigo ɗakin yanayin yadda yaga Dr. Salamatu yasan ba lafiya ba, sai da ya kalli Minal sannan ya sake kallonta yace 

“Yaya jikin nata?”

Ba tare data kalleshi ba ta bashi amsa, 

“Better” 

Kai ya gyaɗa ya ɗan kalli Minal da itama shi take kallo.... 

    Cikin tsoro Dr. Salamatu tace “Minal zaki sha tea.?” 

Tsawa ta katsa mata kamar mai faɗa da yarta “Bana so bana son ganin ki ever again miyasa kika kawo ni asibiti miyasa? miyasa kika ceci raina baki barni na mutu ba?” 

Cikin kuka da sanyin murya Dr. Salamatu tace “Because I'm your mother bazan iya kyale ki ki mutu ba” 

Kai Minal ta girgiza tana hawaye

 “No you are not my mother ke ba uwata bace stay a way from me” 

“I'm your mother Minal no matter what I'm still your own mother nice na haife ki Minal” 

Dr. Salamatu ce take maganar tana nuna kanta hawaye na mata zuba, 

 Tunda Minal ta soma maganar ya lumshe ido yana ɗan cizon baki, sosai yake jin kalaman sunyi mashi girma, 

       Ya tsinar fuska Minal ta shigayi tana haɗiye yawu da karfi kamar mai shan maɗaci, ta tsire baki ta kalli Dr. Salamatu tace “Ke ba uwata bace ke... -” 

  Tasss Saif ya wanke mata fuska da mari tun kamin ta k'arasa maganar da sauri ta dafe kunci tana kallonshi,

   Baki Dr.Salamatu ta rik'e tana kallon Saif da k'arfin hali irin nashi.

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO...! 


          NA 


KHADEEJA CANDY 



Episode___3


Cikin wani irin ɓacin rai Minal ta zaburo masa 

“Who do you fucking think you are da zaka saka kazamin hannunka ka mare ni?” 

 Saif kamar jira yayi cikinta da matsifa 

“Quiet silly little stupid girl taya zaki rik'a fadawa Mahaifiyarki waɗannnan kalaman bakisan darajar iyaye ba ko or maybe baki da hankali” 

Da karfi tace 

“Nayi ni ba mahaukaciya bace nayi saboda ina da damar yin haka get the hell out of here here” 

Zai sake magana Dr. Salamatu ta rik'e mashi hannu 

“Ka barta tayi duk abinda take so tana da damar yin duk abinda take so” 

Cike da mamaki Saif ya kalleta 

“Kinsan abinda kike faɗa kuwa yarki ce fa ke kika haifeta ba ita ta haife ki ba ko dai kin manta ne?” 

“Please Saif let her b thanks for the Concern” 

Taɓe baki yayi ya janye hannunshi daga rik'on da tayi mishi ya juya ya fice, 

    Yana fita Dr. Salamatu ta nufo Minal tana bata hak'uri

 “I am so sorry dear i.. -” 

Hannun Minal ta ɗaga mata hakan yasa ta kasa k'arasa maganar... 

“You too Mom please just go” 

Yatsanta ta shiga murzawa “Please Minal ki fahimceni mana banyi hakan dan na cutar da rayuwar ki ba nima bada son raina hakan ya faru ba inason ki kwantar da hankalinki nayi miki bayanin komai”

Hannu Minal ta kai ta danna wata yar karamar ɗanja ja dake gefen gadonta, nan take ɗakin ya ɗauki k'ara cikin mintunan da basu fi 3 ba likitoci suka shigo tare da nurses, 

Dafe kai Minal tayi tana kallonsu 

“Dan Allah ku fitar dani daga nan bana son ganinta” 

 Da sauri wata daga cikin likitocin wadda nake zaton bahaushiya ce ta kalli Dr. Salamatu,

“Dan Allah Hajiya ki ɗan bata guri for now tana muna bukatar natsuwar ta” 

Kai kawai Dr. Salamatu ta ɗaga ta juya ta fice tana hawaye, 

   Tana fitowa wata daga cikin matan dake tare da ita ta dafata tana tambayar lafiyar Minal, 

Kasa magana tayi saboda kukan da ya ci karfinta, nan suka shiga tambayarta ko lafiya duk hankalinsu ya tashi, 

sai da tayi mai isarta sannan ta share hawaye ta ta ɗauki Jakarta tana faɗin

 “Babu komai Minal kuma taji sauki” 

Tana kaiwa nan ta nufi hanyar fita su kuma suka rufa mata baya, 


         A k'ofar Emergency suka tararda Saif tsaye kamar mai jiran fitowarsu, Tsayawa Dr. Salamatu tayi dai-daishi sannan ta kalli matan dake tare da ita tace “Kuje gurin mota”

 Ba musu suka nufi gurin motar 

Sai da suka fice sannan ta kalli Saif zatayi magana ya rigata 

“I'm sorry to ask you miyasa yarki ta tsaneki kuma tayi kokarin kashe kanta?” 

Wani dogon numfashi taja tare haɗiye wasu yawu da karfi 

“Kace wai Mr President na gode sosai da kulawarshi kuma kace taji sauki ina mika mashi gaisuwar ban girma” 

Bata tsaya jiran abunda zai sake cewa ba tayi tafiyar ta 

   Ajiyar zuciya ya sauke ya ɗaga kafaɗunshi,

_Toh wai miye na damuwa da sanin dalilin koma minene ai can su suka sani nidai nayi abinda ya kawo ni_

A zuci yayi wannan maganar yasa hannayenshi aljihu ya fice. 



                         MINAL.... 

Sai da suka tabbatar da hankalinta ya kwanta sannan suka fice suka bar mata wata nurse guda ɗaya, tana haɗa mata tea, 

   “Please brought borrow me your phone” 

Ta tambaya tana matsar gurin da akayi mata karin ruwa, 

Juyowa nurse ɗin tayi ta kalleta tana murmushi tace “OK but you should drink this tea first” 

 Ta k'arasa maganar tare da mika mata tea ɗin, ba musu ta karɓa ta kai baki, sai da ta shanye shi kaf sannan ta dire kofin tana shafe bakinta,

     Hannu naga nurse ɗin tasa ciki aljihu ta ciro wayar ta mika mata, da sauri ta karɓa tana mata godiya "Thank you” 

Murmushi Nurse ɗin tayi “Your welcome” 

Sannan ta juya ta fice, 

  Wasu numbers Minal tasa guda goma sha ɗaya sannan ta danna calling.

Ringing tayi har ta katse ba'a ɗauka ba nan ta sake bugawa, 

“Com-on pink the call pink the call” 

Abinda take faɗa Kenan tana yarfar da hannu, 

Sai da ta kusa katsewa sannan aka ɗauka cikin rawar murya ta soma magana 

“Hello Deen ina asibiti yanzu haka” 

Shiru tayi can kuma tace 

“I need to see you Deen urgent” 

Banji mi aka ce mata ba na dai ji tace 

“Ok” 

Ta kashe wayar, 

Ido ta tsurawa tana shafa gashin kanta,


27 MINUTES LATER.... 

Aka turo kofar ɗakin aka shigo

 “Deen” 

Abinda wadda ya shigo kenan ya faɗa yana kokarin maida kofar, 

 Ganin tana unkurin saukowa yasa shi yin saurin k'arasa kusa da ita ya zauna saman godon suka rike hannayen juna, 

       Nan da nan idonta suka kawo ruwa nan ya ware hannunshi na dama ya shafa gefen fuskarta 

“Kinyi unkurin kashe kanki Deen why kinsan da kin mutun kin mutu kafira kenan kuma ba zaki sake ganin kowa ba.?”

   Hawaye ne suka zubo mata “Bansa abinda zanyi ba na tsani rayuwata ne...”

Fashewa tayi da kuka mai karfi har lips ďinta na rawa, 

    Rumgume ta yayi yana faɗin

 “I love you Deen faɗa min mi yasa kikayi unkurin kashe kanki?” 

“Not now Deen bana son maganar a yanzu zan faɗa maka wani lokacin” 

  Kanta ya shafa “Kenan as you wish” 

Shiru ne ya biyo baya babu wadda ya sake cewa wani abu har na tsayon lokaci, 

    Can ta ɗago kai ta kalleshi “Deen bana son zama Kasar nan duk jin nake ta ishe ni zan iya aikata komai idan ina ciki bana son kusanci da Mummy” 

“Kina son barin kasar ne?”

“Yes kuma yau yau ɗin nan Please kuma bana son kowa ya sani” 

  “Ok but not today dan kinga yanzu ko fitarki cikin asibitin nan aiki ne dole sai na samu abokina yayi min hanya kuma yanzu ba lalle bane a samu jirgi ba, but i promise you da safe zaki bar kasar nan” 

Kai ta ɗaga mishi “Ok in the early kuma bana son Mummy ta sani just between us please”

Fuskarta ya rik'a da hannayensa biyu,

“Anything for our friendship do you want me to a company you?”

  “No me along”

Ta bashi amsa tana kokarin kwantar da kanta saman jikinta,

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO...! 


           NA 


KHADEEJA CANDY 



_Kin nuna min so kuma kina kan nuna min Ummeenat Abdulhameed i really appreciate your love and support_


Episode___4


8:37PM.......

Saif ya shigo gida, part ɗinshi ya fara wuce wa,

 Sai da ya watsa ruwa ya ɗan huta sannan ya nufi part ɗin Momi, 

     Da sallama ya shiga sanye da jallabiya, babu kowa parlor sai tv dake da aikin shi, kai tsaye ya nufi upstairs ɗakin Momi. 

       Zaune ya tararda ita sanye da glasse a idonta tana duba wasu takardu, sallamar da yayi ne yasa ta ɗago kai ta kalleshi tare da amsawa, 

“Wa'alaikumussalam Saif” 

“Na'am Momi ya gidan?” 

“Gida lafiya kalau daman ina nemanka” 

Zaunawa yayi yana faɗin “Toh gani Momi Allah dai yasa lafiya” 

Glasse ɗin ta cire ta aje sannan ta fuskanceshi

 “Akan maganar matarka ne Saif shi fa Aure ɗan hak'uri ne kaji ka k'i ji ka gani ka k'i gani ita mace dole sai anyi hak'uri za aji daɗin zama da ita ballantana yarinya kai kace kana sonta Auren soyayya kuka yi bai kamata a ce har saki ya shiga tsakani ku da ita ba” 

Nisawa Saif yayi,

 “Shaidan ne amman kuma ai na maida Aure na” 

“Naji ka maida Auren ka amman miyasa ka hana matarka ta dawo ɗakinta?” 

“Momi ni halinta ne bana so duk na tuna sai naji nafi sha'awar zama ni kaɗai ba tare da ita ba” 

Ajiyar zuciya Momi ta sauke

 “Kana yabo Huddallah da mugun hali wadda ni ban taɓa ganinta da shi ba, kuma idan ma tana da wani halin ai yanxu zata daina tunda saki ya shiga tsakanin ku,

 Amman ace abi yak'i ci ya k'i cinyewa har iyayen ta su kai ga magana” 

Shiru yayi kanshi a kasa wadda hakan ya bawa Momi damar cigaba, 

“Ina son dan Allah ka mayar da matar ka ɗakinta ba zai yiyu ka dawo nan ka tare ba dan ka saki matarka kaje ɗan Allah ka ɗauki matarka ku kuma gidanku hankalin mu ya kwanta nata ya kwanta na iyayenta ma ya kwanta” 

Gefen fuskar shi ya shafa “Shi kenan Momi insha Allah yau zanje na ɗauko ta ko Dad yayi min magana indai shine matsalanku daga yau ya wuce” 

“Haka nake so Allah yayi maka albarka ya baku hak'urin zama ya kawar da fitina.

 Amman a'ce dan ka saki matarka sai ka dawo gida ka tare sai kace mace” 

Da dariya Momi ta k'arasa maganar, 

Shi ma tashi yayi yana dariyar yayi mata sallama ya fice, 

        Yana fitowa ya nufi dining area,

 Zaunawa yayi ya zuba ma kanshi abinci, sai da yaci yayi nas sannan ya dawo saman kujera ya zauna sai tunane tunane yake. 

Sai kusan goman dare sannan ya tashi ya nufi part ɗinshi, ruwa ya sake watsawa ya shirya cikin shadda blue color da bakar hula bayan ya ďauki car keys ďinshi ya nufi parking space, 

Yana tada motar ya ɗauki hanyar da yasan zata kai shi gidansu Huda, 

A hanyarshi ta isa can ne ya kira wayar Dad yana labarta mishi yadda sukayi da Dr. Salamatu, 


  Murna Alhaji Aminu Ibrahim. Yayi sosai ganin Saif yazo ya tafi da matarshi,

  Huda kan sai da nuna halinmu na mata wai ita ko a jikinta alhalin a zuciyarta farinciki ne falau,

 Har taso tak'i zuwa sai kuma wata zuciyar ta hana ta dan tasan halin Saif duk tayi kuskuren k'in binshi ba zai sake dawowa ba sai dai ta kai kanta, 

           Nasiha sosai Mahaifiyar Huda tayi musu Hajiya Ramatu sannan ya ɗauki matarshi suka nufi gida,


   

        WASHE GARI..........

Ziwww (vibration) kake ji wayar Saif dake saman bedside drawer tana yi, 

Daker ya mika hannu ya ɗauki wayar saboda nauyin bachi da yake ji,

Huda na kwance saman kirginshi, ba tare daya duba mai kiran ba yayi picking ya kara a kunne, 

Bansan mi akace mishi ba na dai ya buɗe ido da sauri ya zabura wadda har yayi sanadiyar tashin Huda “What?” 

Abinda ya furta kenan yana kokarin saukowa saman gadon, 

Tashi yayi tsaye yana faɗin “Ok gani nan zuwa” 

Nan ya kashe wayar ya ɗora ta saman mirror, 

Kallon Huda yayi dake mika ya sakar mata murmushi. 

   Bathroom ya nufa, a gaggauce ya watsa ruwa ya fito

Wardrope ya nufa ya shirya cikin kanana kaya Black Jean and white t-shirt anyi mata zane blue, 

Huda dai sai kallonshi take ganin yana kokarin saka takalma yasa ta tashi zaune tare da jan bargo ta rufe jikinta,

“Dear wai lafiya dai?” 

Dagowa yayi ya kalleta

 “Wani ɗan aiki ne ya taso” 

Fuskar mamaki tayi,

“Yanzu da safe nan dear yau fa weekend kuma ko breakfast bakayi ba”

Rika ta yayi ya kwantar saman gadon 

“Cigaba da bachi ki i will be right back ok?” 

Kiss ya manna mata saman goshi ya shafa fuskarta ya fice,

     Cikin yan mintuna ya isa gidan, a parlor ya tararda Dr. Salamatu tare da wata budurwa da bazata wuce sa'ar Minal ba.

   Dr. Salamatu na ganinshi ta tashi tsaye da sauri hawaye na bin fuskarta, 

    Gurin ya samu ya zauna zaiyi magana ta riga shi

 “Saif bani da wadda zan kira ya taimaka min sama da kai Saif yata zata iya shiga cikin wani hali bani da kowa sai ita, ita kaɗai na haifa Saif ka taimaka min karna rasa ta dan Allah” 

Cikin kuka ta k'arasa maganar har muryarta na rawa, 

Kanshi ya shafa ya sauke ajiyar zuciya,

 Sam bai jidaďin yadda ya tararda Dr.Salamatu tana kuka ba ko kađan baya son kuka ko na yaro balle babbar mace,

 jin kukan nata yayi yawa yasa ya ɗago kai ya kalleta “Yanzu ya kike so nayi?” 

Da sauri buduwar ta kalleshi tace 

“Koma minene kayi mana ka taimaka mana” 

“Tana ina yanzu?” 

“Tana Airport munje bamu samu ganinta ba ance Kasar zata bari kuma kaga zata iya shiga ko wane irin hali tunda zuciyar ta a rufe take” 

Wannan karon Dr. Salamatu ce take maganar cikin kuka, 

Shiru yayi ya tsurawa carpet ɗin ido har na tsawon lokaci...

 Can wani tunanin yazo mashi da sauri ya tashi ya fice ba tare da yace dasu komai ba.

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO...! 


          NA 


KHADEEJA CANDY 


_Vote me on wattpad @khadeeja _candy_



BABI NA SHIDA___6


Cikin yan mintuna suka isa, 

Sara na yin parking ta kalli Munal Minal suka tuntsire da dariya, da gudu suka fita motar suna a rigaggan shiga cikin gidan. 

   Minal ce ta riga kaiwa tsakiyar parlor, tsayawa tayi tana juyi da dariya, 

    “I really don't know how much I miss this place” 

Kai Sarah ta girgiza daidai lokacin da k'arasa kusa da ita, 

“Maybe a million”

“Nope” Minal ta faɗa tana juya ido, 

“Thousands” 

“Nope” 

Sarah ta zauna saman kujera tana faɗin

 “Oops you really don't missed it at all” 

Faɗawa Minal tayi saman kujerar tana dariya,


BAYAN AWA UKU... 

 Minal ce jingine jikin windon kitchen tana kallon flowers,

Wani iska ne maidaɗi yake kaɗawa sai faman sauke ajiyar zuciya take tana. 

   Sarah na jingine jikin kofa, tana kallonta ba tare da ta sani ba, 

“Mil Deen ya faɗa min kinyi kokarin kashe kanki kuma kin gudu kin zo nan ba tare da sanin kowa ba miyasa?” 

Kamar daga sama Minal taji maganar, da sauri ta juyo ta kalleta, 

Can kuma ta ɗauke kai ta ratsa gefenta ta fice daga kitchen ɗin

   Rufa mata baya Sarah tayi tana faɗin, 

“Nima baki son faɗa min ko.?” 

Tsayawa Minal tayi cak. Ganin hakan yasa ita ma Sarah ta tsaya bata k'araso kusa da ita ba, 

“Deen ya faɗa miki komai Sarah” 

Ba tare data juyo ba take maganar, 

Sarah ta ɗaga mata kai

 “Eh ya faɗa min baki son maganar”

Juyowa Minal tayi idonta cike da hawaye, da yaren faransanci tace, 

“Wadda zan Aura ya guje ni, kuma matar da nake zama tare da ita take kulani tana yi min gata ashe ba ita bace Mahaifiyar data haife ni ahalin da nake yanzu ban san waye Mahaifina ba basan a ina iyalina suke ba bani da kowa ni kaɗai nake”

Sanyi jikin Sarah yayi ganin yadda hawaye ke zuba a idon Minal, 

K'arasowa tayi kusa da ita ta rungume ta. 

“Shhhhh ki daina cewa baki da kowa bai kamata ki damu ba har yanzu ba ke kaɗai kike ba muna nan tare a koda yaushe ni ina nan a tare dake Deen ma yana tare dake kuma ba zamu taɓa rabuwa ba” 

Maganar take tana buga bayan Minal alamar lallashi,

Sun daɗe a haka kamin Minal ta sake ta, ta wuce bedroom. 

Fridge Sarah ta nufa bayan ta buɗe ta ɗauki wata farar kwalba ta nufi ɗakin da Minal ta shiga,

  Zaune ta tararda ita tsakiyar godo idanunta a rufe ta dafe kai tana girgiza shi. 

Kwalbar Sarah ta mika mata “U need a fresh brain Mil” 

D'agowa ta fara yi tana kallon kwalbar kamin ta mika hannu ta karɓa, 

“Thank you” 

Ta faɗa tana lumshe idanunta da sukayi ja saboda kuka. 

Murmushi tayi mata “Your welcome” 

Ta kai hannu ta ɗauki car keys dake saman drawer, ta nufi kofa tana faɗin, 

“I'm out” 

Kai Minal ta ɗaga mata, 

“Ok take care” 

“I will” Ta faɗa tana kokarin rufe kofar.

Minal sai da taji tashin motar sannan ta buɗe kwalbar ta dagata sama ta kafa a baki, 

Bata dire ba sai da taji babu gurin iska a cikinta sannan ta sauke kwalbar tana haki, 

  Nan da nan wasu ruwa suka tarar mata idanu, 

Kai ta girgiza jin jirin da ya soma ɗi banta, tafi minti biyar a haka sannan ta sake kai kwalbar a baki ta shanye ragowar. 

D'aga kwalbar tayi sama tana kakkaɓewa daga bisani ta jefar da ita,  

“Oh i need more” 

Cikin magagi tayi maganar kamar mai jin bachi, tana kokarin mikewa tsaye,

   Sai da ta kai tsayen jiri ya ɗubeta ta faɗi kwance saman gadon, 

wani irin numfashi ta rik'a ja tana juya ido har bachi yayi gaba da ita.



21:42GMT......

Saif ya sauka masaukinsa sai da ya huta sannan ya shiga bedroom ya sakarma kanshi shower yayi alwala ya fito,

Wani farin yaɗi ya saka marar nauyi, ya shinfiɗa carpet ya kabbarta sallah,


SOME MOMENT LATER.... 

Kwance take saman gado bayan ya kare cin abinci, sai faman gyasa yake yana shafa ciki, 

Babu wadda ya faɗo mashi a rai sai Huda da sauri ya tashi ya ɗauko wayarshi daman tun cikin jirgi ya chaja sim. 

Nan ya shiga saka number Huda, ringing tayi ta yi sai da ta kusa hankewa sannan aka ɗauka, 

“Hello dear” 

Shiru tayi har sai da ya ɗauka ta katse, sannan tace

“Kaga yarinyar da kaje nema?” 

Cige bakinshi yayi, 

“Wace yarinya kuma? Mi kike nufi ne?” 

ciki da mamaki yayi maganar,

“Oho ni ina na sani Dad dai yana son magana da kai” 

Tashi yayi daga kwance da yake zuwa zaune, 

“Ina Dad ya ganki?” 

“Gidan naje ɗazu bayan fitarka” 

A takaice ta amsa mishi, faɗa ya shiga mata 

“Wa kika tambaya da zaki je? Ba zaki zubar da halinki ba ko? Kuma kinsan... -” 

Shiru yayi jin ta katse wayar, yayi murmushi jin haushi, 

“Lallai yarinyar nan yayi miki kyau” 

Ya daɗe tsaye yana girgiza kai kamin ya shiga danna ma number Dad calling. 

    Cike da fargaba yayi sallama, bayan Dad yayi picking, bai amsa Sallamar ba ya haushi da faɗa, 

“Me kaje yi a new york? Kayi yimin karya kayi ma matarka karya kace nine na aike ka sai ka faɗa min sakon da na aikeka karɓowa” 

Shiru Saif yayi ya rasa abinda zai ce, 

“Baka ji nane kayi min shiru mi kake son maida kanka?”

Nan ma shiru yayi yana jin faɗan har cikin ranshi, 

    faɗa sosai Dad yayi mishi sannan ya bashi umarnin barin kasar gobe da safe, 

Jiki na kwari Saif yayi mishi Sallama, ya faɗa saman kujera yana busar da iskar bakinshi, 

“Ni mi ma yasa na kiraki?” 

Tsaki yaja, 

“Wallahi ba ki da kirki ko kaɗan” 

Nadama yake sosai na kiran Huda da yayi, ya daɗe  zaune gurin yana tunane tunane daga bisani ya tashi yayi shirin bachi.

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO...! 


          NA 


KHADEEJA CANDY 



_Sadaukarwar ta Anty Maijidda ce_



_VOTE ME ON WATTPAD @KHADEEJA _CANDY_



BABI NA BIYAR___5



Direct Asokoro villa ya nufa, yana yin parking ya nufi part ɗin Dad, 

Tsaye yayi lokacin daya isa bakin kofar ɗakin ya shiga kwankwasawa da sallama cike da adabi, 

“Waye ne?” 

Daga can ciki aka amsa mishi, 

   Jin muryar Momi yasa ya tura kofar ya shiga a hankali

“Nine Momi” 

Fuskar mamaki Momi tayi “Lafiya kayi mana sammako haka?” 

Kusa da ita ya zauna ,

“Lafiya kalau wata alfarma nazo nema gareku” 

Dad dake shan tea ya kalle shi 

“Alfarma kuma wace irin Alfarma kake nema?” 

Sai da ya nisa sannan yace

 “Dad So nake ka bada umarni tsayarda duk wani jirgi da zai tashi daga yanzu zuwa nan da karfe goma sha biyu” 

Daga Momi har Dad kasa fahimtar shi sukayi 

Momi tace

 “Miya faru Matsalar tsaron ne ko me?” 

“Babu ko ɗaya Momi yanzu Dr. Salamatu ta kirani tana kuka tace na taimaka mata karta rasa rayuwar yarta tana son guduwa ne tabar kasar. 

Shine nake son ka hana tashi da jiraje idan na kwace passport ɗinta sai komai ya cigaba” 

Kai Dad ya girgiza

 “Bazan maka haka ba Saboda ya ɗaya tilo a hana dubun mutane yin abinda suke so” 

Rokon shi Saif ya shigayi,

 “Dan Allah Dad ka taimaka min ba dan kowa zakayi ba sai dan ni, Dad zata iya shiga ko wane irin hali idan ba'a hanata tafiyar ba, yanzu Dad idan Safiya ce ya zaka ji?” 

Dafashi Momi tayi 

“Saifullah Safiya ba zata yi abinda wannan yarinyar tayi ba wannan ina tunanin bata da hankali ko kuma tana share share-” 

Tarar numfashinta yayi 

“No Momi ba haka bane akwai abunda mahaifiyar ta tayi mata ne”

 Juyowa yayi gurin Dad yana mishi magiya

“Dad Please do this favor for me na riga na faɗi haka zansa ayi dan Allah karkasa naji kunya ka bada umarnin”

Dad yace 

“Kai ke da ikon kasar ne da zaka ce haka za'ayi?”

Tasowa Momi tayi ta dawo kusa da Dad ta zauna cikin lafazi mai alamar tausa ta soma lalla6ashi,

   “Ka taimaka mishi karya ji kunya tunda har ya faɗa, yana nufin yana da matsayi a gurinka” 

Shiru Dad yayi na tsawon lokaci, kamin ya janyo waya ya bada umurni yin hakan, 

  Godiya sosai Saif yayi mishi sannan ya tashi ya fice suka bishi da kallo, 


  Gudu ya rik'ayi kamar zai tashi sama cikin yan mintuna ya isa Airport ɗin, 

Kai tsaye gurin da ake tantance fasinjoji ya nufa, tun kamin ya k'arasa ya rik'ajin sanarwa an hana tashi da jirage na wani ɗan lokaci, 

 Yana isa gurin duk suka tashi tsaye suka sha jinin jikinsu, hannu suka bashi bayan sun gaisa ya kalli babban su,

“List ɗin passenger da zasu tashi nake so” 

“Ok Sir” 

Nan ya kalli na gefensa

 “A kawo mishi list” 

Da sauri mutumin ya juya ya nufi wani ďan tebur dake kusa da su 

 Cikin yan mintuna ya kawo mishi files kusan guda goma sha biyu, 

  Wayarsa ya ciro cikin aljihu ya danna kira ana daukar yace

 “Minene full name ɗin da take anfani dashi”

 Can naji yace ok ya kashe wayar, 

Wadda ke rike da files ɗin ya kallah 

“Duba min Amina Alhassan Minal” 

Jiki na rawa yace,

“Ok Sir bari musa a computer yafi sauki” 

Kai kawai ya ɗaga mishi yaja kujera ya zauna, 

   Ana saka sunan nan take computer ta nuna har da ɗan karamin pic ɗinta, 

Juyowa yayi ya kalli Saif

 “Sir gata amman tana cikin fasinjoji da suka tashi” 

da dauri ya yashi tsaye

Da karfi Saif ya furta

“What bayan an faɗa muku karku bar jirgi ko ɗaya ya tashi.? Mi kuka aikata kenan a baku umarni ku tsaɓa me kuka dauki kanku sai kunyi nadamar abunda kuka aikata” 

B'ari jikinsu ya shigayi ko wanne cikinshi ya ɗori ruwa, ɗaya daga cikinsu ne yayi kokarin yin magana 

“Yan laɓai ayi hak'uri koda aka bada umarnin hana tashi da jirgi jirginsu yayi minti talatin a sama kuma kasan idan jirgi ya riga ya tashi babu yadda za'ayi a tsayar da shi” 

Shiru yayi ya jingina da gurin, can ya kalleshi 

“Ina jirgin ya nufa?”

Cikin sauri ya bashi amsa

“New York” 

“Akwai jirgin da zaije can yanzu?”

 Saif ya Tambaya

“Babu shi yanzu Sir sai dai anjima da maraice karfe hudu abinda yayi kasa” 

Kai ya ɗaga musu ya tashi ya fice. 


    Driving yake yana danna calling ana yin parking yace “Dr. Salamatu jirgin su Minal ya riga ya tashi nasa an tsayarda tashin jiraje amman already nasu ya tashi”

 Shiru ya ɗanyi sannan yace

 “New York ta nufa eh i will try my best nan da 6 hours zan isa can zanyi wani abu akai insha Allah” 

Yana kashe kiran ya sake danna wani kiran

 “Hello Hashin ina son kujera ɗaya daga cikin kujerun da zasu je New York anjima, no yanzu akwai inda zanje karka yarda nayi missed flight” 

Yana kaiwa nan ya danna red bottom ya karama motarshi jiya.



   3:11PM...... 

Ya shigo gida da gudu Huda ta tareshi,

“Dear tun safe sai yanzu?” 

Kiss ya manna mata a gefen kumatu 

“Am so sorry dear wani ɗan aikin ne ya rik'e ni” 

“Dear wai wane irin aikine yau fa Weekend” 

Zaunarda ita yayi saman kujera

 “Meeting mukayi da wasu Indian yanzu ma new york zanje” 

“Wasa dai kake ko?” 

Tashi yayi yana faɗin 

“Allah da gaske wani aikin ne ya taso” 

Bedroom ɗinshi ya nufa nan itama ta tashi ta rufa mishi baya, 

Koda ta shiga ta tararda shi yana cire rigarshi, ido ta bishi dashi har ya ɗaura tawul ya shiga bathroom, 

Gefen gado ta samu ta zauna ta zubawa bathroom ɗin idon har ya gama wankan ya fito, 

Wardrobe ya nufa, ganin yadda ake kallon shi yasa ya sakar mata murmushi

 “Wai wannan kallon na lafiya ne?” 

Bata ce mishi komai ba har ya goge jikin shi ya shafa mai yana kokarin saka tufafi tace

 “Wai da gaske tafiya zakayi?” 

“Gashi kina gani karfa ki ɗaga hankalinki ba dadewa zanyi ba” 

Ya k'arasa maganar tare da ɗaukar turare yana fesawa a jikinshi.

Juyowa yayi ya kalleta yadda ta wani haɗe rai sai yasa shi yin murmushi ya fesa mata turaren a gefen wuya ya zauna kusa da ita

 “Wai minene na wannan fushin my heart?” 

Kamar ta fasa kuka “Toh dear kaje new york ɗin dani mana ko kuma ka bari har wani sati” 

Dariya yayi 

“Ai ba zai yiyu ba idan ma yawo kike so toh ki bari har na dawo sai muje duk inda kike so” 

A gogon hanninshi ya duba da sauri ya tashi tsaye 

“Kai kinga har 3:40 tayi kuma 4 zamu tashi” 

Bedside drawer ya buɗe ya ɗauki wasu abubuwan da yasan zai bukata ya saka a wata yar karamar jaka

Hannunshi ta riko cikin yanayin damuwa 

“Dear ko dai baka hak'ura bane?” 

Hannun nata ya manna ma kiss 

“Na hak'ura mana ai da bazan barki ki dawo ba Dad ne ya aikeni ai kinga ai bazan ce masa bazani ba ko?” 

Jikar ya ɗauka tare da riko hannunta suka nufo parlor, har bakin mota ta rakashi, nan ya ɗanyi huge ɗinta

 “Ki min addu'a kinji?” 

Kanshi ta shafa

 “Allah ya dawo min da kai lafiya” 

  “Amin thank you ki kula min da kanki” 

Kai kawai ta ɗaga mishi tana kallon shi har ya tada motar ya fice, 

Sai da ya biya Maitama ministers hill ya karɓi pictures ɗin Minal da information sannan ya wuce, 


NEW YORK..... 

14:44GMT jirgin su Minal ya sauka, kai tsaye ta nufi hanyar fita Airport ɗin, sanye da wani blue jean yayi tight ɗinta sosai, sai yar fashion t-shirt pink color, 

Babu komai a hannunta daga ATM sai Passport, haka ta fito tana janye gashin kanta da iska ke kaɗawa, 

Jin am dafata yasa tayi saurin waigowa, 

“Sarah”

 Abinda Minal ta faɗa kenan tana kallon budurwar farar fata, 

Hannayenta Minal  ta kama tana dariya

 “Mil Barka da zuwa birnin mu birni mai yanci da walwala” 

Mamaki ne ya bayyana a fuskar Minal 

“Sarah ya a kayi kika san nazo?” 

Sama Sarah tayi da glasse ɗin idonta

 “Deen ne ya faɗa min tun jiya kuma shi ne ya faɗa min lokacin da jirginku zai taso da kuma lokacin da zai sauka shiyasa na tare ki nayi marmarinki sosai Mil”

Da dariya ta k'arasa maganar tana jan kumatun Minal, 

Da sauri Minal ta rungume ta idonta cike da hawaye

 “Nima nayi marmarinki Sarah  ina sonki sosai” 

“Nima ina sonki Mil” 

Duk da yaren faransanci suke wannan maganar,

     Nan Sarah ta rika hannunta suka nufi gurin da aka tana da dan aje motoci,

  Wata red sport-car suka shiga Sarah ce a driver seat, Minal na zaune a front seat, a hankali ta tashi motor suka hay t-t.

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO...! 


         NA 


KHADEEJA CANDY 



_DEDICATED THIS PAGE TO MIEMIEBEE Thank you DEEN🤞🏻._



BABI NA TAKWAS___8


Kallon shi kawai ta bishi da shi har ya zauna a kujerar dake facing ɗinta, 

Shiru yayi yana kallonta sannan yace, 

“Miyasa kika tsani Dr Salamu bayan ita ce ta haife ki?” 

Shiru tayi kamar baza amsa mishi ba can kuma ta soma magana, 

“Mummy ba ita ce ta haife ni ba bansan waye mahifina ba bani da kowa ban kuma san haka ba sai da wadda muka kulla maganar aure dashi yace min iyayenshi sunce ba zai aure ni ba dan bani da uba kuma Mummy ba ita ce ta haife ni ba, 

Ni kuma ban musa masa ba saboda na sha tambayar Mummy waye Mahaifina taki ta faɗa min sai ma cewa take na daina mata maganar na daina damuwa zata yi min duk abinda nake bukata, 

Kuma lokacin dana same ta da maganar sai tace min lallai ni ba da aure aka haife ni ba ni kuma da naji haka sai nayi unkurin hallaka kaina” 

Tana maganar hawaye na mata zuba, 

   Tunda take maganar Saif ya natsu yana saurarenta har ta kai aya, tausayinta ne ya kama shi idan har abunda ta faɗa gaskiya ne ta chanchanci a tausaya mata dan rashin uba ko gurin namiji akwai ciyo barre ya mace, 

Tashi yayi ya koma kusa da ita ya zauna yaja kanta ya dora saman kafaɗar shi, 

Cak.! Kuka ya tsaya mata wata rahama ta ratsa mata jiki, lumshe ido tayi ta kusa kanta cikin jikinshi tana shakar daɗadden kanshin dake fita daga jikinshi. 

    Sunyi minti goma sha biyar a haka, sai can ya ɗago kanta yasa handkerchief mai ɗauke da sunanshi sai kanshi turare yake ya share mata hawaye, sannan ya tashi tsaye, 

   Kallo ta bishi dashi har yakai bakin kofa sannan ya juyo ya kalleta, 

“Ki kwantar da hankalinki Deen ɗinki zai dawo yanzu” 

Kai ta ɗaga mishi “Atm ɗina fa? ” 

Bai bata amsa ba sai kawai ya juya zai fice, ganin hakan yasa tace “Please karka faɗawa Mummy ina nan” 

Nan ma baice da ita komai ba ya fice, 

A hankali ta kwantar da kanta hannun kujera tana kallon handkerchief ɗin shi da bari gefen kujerar, wani sabon kuka ya taso mata.



Driving yake yana shan karatun Sheik Shuraim, har ya isa Maitama Ministers hill tunanin Minal yake, gaskiya duk wadda yake cikin gata irin na Minal ya wayi gari akace bashi da uba xaiyi bakin ciki sosai, 

Yana yin parking Dr. Salamatu ta fito da sauri ta nufoshi, 

“Anyi nasara kuwa?” 

Kai ya ɗaga mata ya mika mata abubuwan daya karɓa hannun Minal, 

“Anyi nasara ki rike wannan nasa a kasa mata takunkumi bata iya zuwa ko ina a yanzu koda tana da waɗannnan abubuwan” 

Da sauri tace “Ina take Saif?” 

“Wannan ne kawai bazan faɗa miki ba dan ta rik'i haka a gareni kuma kinsan ke kika saka ta cikim halin da take ciki yanzu” 

Yana kaiwa nan ya juya ya shiga motarshi, jiki a sanyaye ta k'arasa kusa dashi “Kaima kana zargi na kamar ita?” 

“Toh misaya ba zaki faɗa mata wacece ita ba? A yanzu ta riga tasan ba kece kika haifeta ba idan ma har shine kike jima tsoro karta gujeki ko? da kin faɗa mata gaskiya tun farko da bata shiga halin da take ciki yanzu ba” 

Tana kokarin maida hawayenta tace “A shirye nake na faɗa mata komai Saif nayi nadamar yin hakan da nayi” 

Kafaɗunshi ya ɗaga “Idan bukarta hakan ta taso ita da kanta zata neme ki” 

 Bai tsaya jiran abinda zata ce ba yayi ma motarshi key, itama bata kara cewa wani abun ba har ya bar gidan.




                  ********




“Dear wai mi yake damunka ne naga cin abincin kawai kake amman hankalin ka baya gurin?” 

Drink ɗin dake gabashi ya ɗauka sha yana murmushi, 

“Wai yanzu Huda idan kika wayi gari Hajiyar ki tace ba ita ta haife ki ba kuma Abbah yace ba shi ne mahaifinki ba kuma duk family da kika gani ba naki bane ya zaki ji?” 

Kallon mamaki tayi mishi “Wannan wace irin magana ce wannan Saif?” 

“Please just answer me” 

Kai ta jinjina “Gaskiya zanji ba daɗi zan kuma yi bakin ciki wata kila har na gudu saboda takaici kuma zanso sani suwaye iyayena ya kuma akayi na zo hannun waɗanda ba iyayena ba” 

A hankali ya kaɗa kai alamar gamsuwa yace “Kuma ace akan haka har na rabu dake ya zaki ji?” 

6ata fuska tayi "Haba dai dear miye na wannan maganar kuma gaskiya idan ka rabu dani kashe kaina zanyi ko kuma na haukace gaskiya ka daina bana so” 

Hannayenshi ya ɗaga “Na daina Dear” 

Cigaba yayi da cin abinci yana tunane tunane, 

“Wai miyasa kayi min wannan tambayar?” 

Kallonta yay da murmushi “Saboda kina kaunar Saif” 

Dariya tayi ta tashi tsaye, 

“Toh angon Huda nidai na koshi over” 

Tashi shima yayi tsaye “Nima ai na koshi daman ke nake daku” 

Hannunta ya rik'a suka nufi bedroom bayan ya kashe wutar parlor.



VOTE! 

COMMENT!! 

SHARE!!!

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO...! 


         NA 


KHADEEJA CANDY 


_Vote me on wattpad @khadeeja _candy_



BABI NA BAKWAI___7



SAIF..... 

Yana yin Sallah Asuba ya shirya y nufi Airport, dan yasan halin Dad ɗinshi matukar ya tsallake abunda umarni daya bashi komai zai iya faruwa, 

      Karfe 10pm a gogon ya iso yana sauka Airport yayi ma direba shi waya, cikin kankanen lokaci ya iso suka nufi gida. 

   A parlor a tararda Huda, tana ganin shi ta taso fuska a washe ta tareshi, 

“Sannu da zuwa dear” 

Bai amsa mata ba ya ɗauke kai ya nufi ɗakin shi, yana shiga ya cire kayan jijinshi ya shiga bathroom ya ɗan watsa ruwa, bayan ya fito yayi sallah. ya nufi dining 

    Tana ganin ya fito ta bishi tana mishi magana, nan ma banza yayi da ita har ya kare cin abinci ya koma ɗakinshi, 

Nan ta bishi tana kiranshi tana shiga taci gaban shi tana mishi magana. 

Sai a lokacin ya kalleta, 

“Wai  minene Huda mi kike so nayi miki ne?” 

Cikin ɗaga murya yayi mata tambayar,

  Kamar ta fasa kuka, “Tunda ka dawo kak'i kayi min magana sai fushi kake dani” 

“Ai dole nayi fushi dake halin nan naki bana sonshi kuma bazaki chanja ba, 

Miyasa kika je kika faɗawa Dad maganar tafiyar nan bayan ga yadda mukayi da ke wama kika tambaya da zakije.?” 

Hawaye ta somayi

“Saif saboda ka daina sona kake min haka ko? Shiyasa ka sakeni bayan kuma ka mayar da ni kaki yarda na dawo gidan ka, washe garin dana dawo ka taka jirgi kabar kasar nan dan kuma na faɗawa Dad yayi sanadiyar dawowarka shine zaka hauni da matsifa, saboda ka ga ina sonka Saif ko shiyasa kake son karkata zuciyarka zuwa ga wata ko?, 

Mi yasa kake son wulakanta ni Saif yanzu one year da yin Auren mu amman ace har saki ya shiga tsakanin mu, What is next kuma?” 

Kuka ta saka mashi marar sauti, shikan ido kawai ya sakar mata dan gaskiya ma tayi mishi yawa, 

Kamar da wasa sai gata har kasan carpet tana kuka mai karfi. 

   Sai da tayi mai isarta sannan ya duka ya rikota suka zauna saman gado, fuskarta ya rik'a, 

“Dubi yadda kika bata fuskarki da kuka kamar karamar yarinya, wane Mak'aryacin ne yace na daina sonki?” 

“Haka ne mana Saif” 

“A'a ba haka bane Huda har gobe ina sonki sakin da nayi miki sheɗan neda kuma halin nan naki dan ki chanja, kuma babu wata yarinyar da nake so banda huda” 

Ya k'arasa maganar yana jan hancinta, 

Sai a lokacin ta tsagaita kukan “Toh mi kaje yi new york?” 

“Mamanta ce tace na taimaka mata kar ta rasa yarta” 

“Ni dai na daina bana so” 

Murmushi yayi “Toh shi kenan na daina” 

Da sauri ta kalleshi “Da gaske?” 

“Eh mana tunda uwargida na bata so ai dole na daina abun har da su kuka ba zan sake ba tunda Huda ta bata so”

Murmushi tayi ta shigar da kanta cikin jikinshi, shi kuma ya shiga aika mata da sakwanni yana zolayarta.



MINAL..... 

Haske ne ya doki fuskanta sakamakon buɗe labulen ɗakin da Sarah tayi, 

Hakan yasa ta farka ta ja bedsheet tana lulluɓewa, 

“Ohhh Sarah I'm not done yet” 

Baki Sarah ta buɗe “You don't done what? Please wake-up baby you already done”

Har ta juya sai kuma ta juyo tana shafa gashin kanta “And before I forget Deen is on the phone” 

Da gudu Minal ta sauka saman gadon har tana kokarin ture Sarah, 

“Oh my Deen” Kamar wata karamar yarinya ta k'arasa gaban wayar ta dauka ta kara a kunne, 

“Hello Deen” 

Daga can cikin wayar aka amsa mata, 

“Ya kike Deen ya enjoyment?” 

“Komai Kalau kaifa?” 

“Nima kalau Sarah tace min kina jindaɗi haka ne?” 

“Eh haka ne ba nida wata damuwa a nan” 

Shiru ya ɗanyi sannan yace “Baki tambayi Mummy ba” 

B'ata fuska tayi kamar yana ganinta “Oh Deen please don't kasan banason maganar ta” 

“Na sani Deen amman fa ta damu sosai kuma kinsan tana sonki” 

Shiru tayi bata ce komai ba jin hakan yasa ya ɗauko mata wata firar, 

Sun daɗe suna waya daga bisani sukayi sallama.



K'arfe 8am Saif ya shigo part ɗin Dad, faɗa sosai Dad yayi mashi sai da yaji ba daɗi daker ya samu Dad ya saurara mishi, 

Hak'uri Saif ya bashi sannan ya tashi ya nufi part ɗin Momi, itama sai da tayi mishi nata faɗan kamin daga bisani ya jata da fita, 

 Sai uku da wani abu ya bar gidan bayan ya gama cin abinci, 

Kai tsaye gidansu Minal ya nufa, da tunane tunane ya isa gida, har ya zauna parlor pictures ɗin Minal dake hannunshi yake kallo, 

   Bai daɗe da zama ba Dr. Salamatu ta fito yadda Saif ya ganta sai duk ta bashi tausayi, duk tabi ta rame kamar ba ita ba, 

    Jiki a sanyaye ta zauna ganin dawowarshi da pictures ɗin Minal a hannu haka ya tabbatar mata da baiga Minal ba, 

Tasowa yayi ya karaso kusa da ita ya mika mata pictures ɗin 

“Ban samu ganinta ba” 

Karɓa tayi tana faɗin, 

“Babu komai Saif kayi kokari Allah ya saka da alheri” 

Hannayenshi yasa aljihu, 

“Babu komai yima kaine ki yi ta mata addu'a shine kawai mafita” 

Kai ta gyaɗa mishi ta share hawayen da suka zubo mata.

“Ba'a sameta ba ko?” 

Budurwar ce ta fito tana tambaya, 

“Eh ba 'a sameta ba Kairat” 

K'araso tayi kusa da ita ta zauna tana faɗin

 “Daman nasan ba za' a taɓa samun Sister ta sai ta hanya ɗaya” 

Daga Saif har Dr. Salamatu kallonta suka, 

“Ta hanyar Deen!” 

“Wanene Deen?” Saif ya Tambaya, 

“A bokinta ne ko kuma nace Amininta duk wani abu nata mai muhimmanci yana hannunshi ta yarda da shi sosai bata kaunar bacin ranshi ko kaɗan ina ganin ma shi ne ya shirya mata yadda tabar kasar nan” 

Dr. Salamatu ta amsa mishi, 

Ido ya tsurawa Kairat ɗin kamar mai karantar abu a fuskarta, can ya ɗauke kai yace

“Yanzu ya za'ayi na same shi?” 

Da sauri Kairat ta tashi ta nufi ɗaki “Ina zuwa” 


Bata daɗe ba ta fito rike da wani ɗan karamin kati ta mika mishi, “Wannan shine address ɗin shi” 

Jimmm ya ɗanyi kamin ya mika hamnu ya karɓa, ya dade yana kallon card ɗin sannan ya tashi ya fice.



NEW YORK..... 

Babu abinda suke sai ciye ciye sun cika ɗaki da waka suna ihu kamar wasu sabbin mahaukata, 

Sam basu lura da Telephone ɗin dake ringing ba, sai da suka je chanja waka, 

Da sauri Sarah ta nufi gurin wayar, 

Tana ɗauka ta kwalawa Minal kira da gudu ta k'araso jin ance Deen ne ya kira, 

Tana kara wayar a kunne kamin tayi mishi magana yayi mata cikin wata irin murya tana karkarwa, 

“Minal kiyi min wani taimako karna rasa raina Please” 

“Miya faru Deen?” 

“Ina son ki bar New York yau yau ki dawo Nijeriya idan ba haka ba zan iya rasa raina” 

“Miyasa Deen mi yake faruwa?” 

“Kawai kizo idan baki son na rasa raina kinji?” 

“Ok gani nan zuwa” 

Nan ta aje wayar ta nufi bedroom, Sarah ta rufa mata baya tana tambayar ba'asi, 

   Cikin yan mintuna ta ɗauki Passport dinta da Atm ta fito, sosai Sarah taso ta hanata zuwan amman sam taki yarda, ganin haka yasa dole tayi Driving ɗinta Airport, 



6:24AM...... 

Ta iso Nijeriya ta tari taxi, bata ajeta ko ina ba sai Gidan Deen, 

Fita tayi tana faɗin “Ina zuwa kaji?” 

Kai kawai ya ɗaga mata ta nufi cikin gidan, 

Ko ina sai da ta duba cikin gidan amman bata ga Deen ba balle alamunshi, 

Tsoro ta soma ji , da sauri ta nufi gurin da tasan ya saba aje wayoyin shi, ɗaya gada cikin wayoyin ta sauka ta danna mushi kira, 

Ringing ɗaya aka dauka amman ba'ayi magana ba, 

“Deen gani gidanka kana ina?” 

Ya ɗan daɗe kamin ya amsa mata “Ok gani nan zuwa” 

“Ok” 

Na  aka katse wayar, ido ta tsurawa wayar, ta zauna saman kujera dan sam ta manta da mai taxi dake waje, 

Bayan wasu tan mintuna taji parking ɗin mota, tashi tayi ta nufi kofar fita, 

Kamin ta k'arasa Saif ya shigo tsaye tayi tana kallon shi har ya k'araso kusa da ita sannan ta shiga leka bayan shi, 

  Ganin ba Deen yasa ta tsara gefenshi da niyar fucewa, 

 Fisgota yayi da karfi ya dawo da ita, 

“Ina zaki.?” 

Yana tambayarta ta tambayeshi, 

“Ina Deen” 

Fuskar Saif a haɗe yace, 

“An salami mai Taxi” 

“Bashi na Tambayeka ba ina Deen?”

Baki ya taɓe yasa hannunshi aljihu ya ciro wayarshi ya danna kira, nan da nan akayi picking, Hands-free yasa ya mika mata wayar, 

   Deen ne cikin rawar murya yake magana, 

“Please Deen duk abinda yasa ki kiyi rayuwata na cikin haɗari” 

Jikinta a sanyaye tace “Ok Saif mi ya faru da kai?” 

Kamin yayi magana Saif ya fisge wayar ya kashe, 

Nan ta kalleshi 

“Mi kayi mishi?” 

“Banyi mishi komai ba yanzu dai zanyi mishi idan baki yi yadda nake so ba” 

Ido ta tsura mishi wani irin tsanar shi take ji amman babu yadda zata yi dashi sai ido, 

  Badan taso ba tace “Na amince zanyi yadda kake so amman Please kada ka cutar dashi”

“Bani Atm ɗinki da passport” Da sauri ta girgiza kai “A'a bazan maka haka ba ask something else” 

Kujera ya nuna mata alamar ta zauna, tana juyawa ya fisgota yasa hannunshi aljihunta ya ciro Atm da passport har da wasu yan kananan takardu, ya jefar da ita saman kujerar.

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO...! 


         NA 


KHADEEJA CANDY 



_Ina godiya gareku sosai masoya na da makaranta da kuma marubuta yan'uwana Na samu sauki ALHAMDULILLAH_




BABI NA GOMA___10



Cike da nauyin baki Mummy ta soma magana, 

_“Asalina ni yar garin Kwara ce ni ibira ce shine yare na kuma yaren iyayena da yan'uwa na, Alhaji Abubakar shine mahaifina ma aikacin banki ne Mahaifiyata kuma Hajiya Amina malamar makaranta ce nice first born a gurin iyayena Kanne na huɗu uku maza mace ɗaya dukan mu iyayemu suna bamu kyakkyawar kulawa da tarbiya baya wasa da karatun mu musamman na addini._

_Daga garin Neja akayi ma Mahaifina Transfer zuwa Yola, nan muka dawo da zama gaba ɗayan mu, koda muka dawo Yola na gama Secondary school, sai mahaifina yasa nati jam cikin sa'ah naci sai ya nema min admission a university,_

_Kamar wasa na fara karatun sai gashi na kusa kammalawa da yake mace ce ni mai maida hankali ga abunda na sawa gaba hakan yasa ban taɓa faɗuwa a jarrabawa ba hakan kuma yasa na samu masoya saosai sai dai bana kula kowa har na kammala karatu na._

  _Bayan results ɗina ya fito na sami mahaifina da zancen zan koma makaranta nayi mastas shi kuma ya sauya min tunani da zancen Aure_

_Banyi mashi musu ba na amince dan kawai na faranta musu rai,”_



Shiru ta ɗanyi sannan ta cigaba,

_“A haka Abbana ya bani damar zaɓen duk mijin da nake so, ni kuma duk tarin samarin da suke zuwa kawo min harin banga wadda nake so ba hakan yasa na bawa iyayena zabi duk wadda sukaga ya dace dani. Sun ji daɗe sosai yadda nayi musu sukayi farinciki_

_Bayan kwana biyu dayin maganar mahaifina ya kawo min wani saurayi son kowa kin wadda ya rasa wato mahaifinki kyakkyawa ne sosai fari fes yadda kika ganki babu abunda kika rage a kamaninshi, naji daɗin zaɓin da iyayena sukayi min saboda duk a samarina banga irinsa ba a ɓangaren kyau da iya wanka_

_Wata biyar Abbana yasa na Aurena, duk wani abu da ake bukata na Aure Abbana ya rik'a siya yana aje min_. 

 _Soyayyah ce ta shiga tsakanin mu sosai idan yazo fira kamar kar muyi sallama, idan abu ya same shi kamar ni ya sama, Wata rana rashin lafiya ta kama shi har aka kwantar da shi asibiti mukayi ta yawon zuwa ganinshi har Allah ya bashi sauki aka sallameshi, bayan ya dawo sai ya dinga fushi dani wai banje gida na duba shi ba, Duk Wani far'ar shi da nake gani sai ya daina na rasa gane kanshi gashi kullum cemin yake ciyon shi karuwa yake,_

_Hakan yasa na yanke shawarar kai mishi ziyarar, duk da nasan Addinina na ya hana banyi tunanin wani abun ba kuma ni a tunanina kamar ba komai bane mace ta kaiwa namiji ziyara tunda naga a makaranta ma friends ɗina suna kaiwa samarin su ziyara_

_Nayi Mamakin yadda na same shi dan ya banbanta da yadda kullum yake faɗa min sam babu alamun ciyo a jikinshi, da kanshi ya buɗe firij ya ɗauko lemu ya zuba min sannan ya dawo kusa dani ya zauna muna fira muna shan lemun, daga nn ban sake sanin inda nake ba”_

   

   Lumshe ido tayi wasu hawaye masu zafi suka zubo mata, bayan kamar minti biyar ta buɗe ta cigaba da maganar,

_“Koda na farka ya aikata alfasha dani! Nayi ta kuka yana bani hak'uri, nayi bakin ciki sosai a hkan na lallaɓo na nufo gida”_

(Daya daga cikin illolin ziyarar ɗakin saurayi ke nan shiyasa duk abunda musulunci ya hanemu dashi toh barinshi shi yafi Allah ya tsare mu da zuri'armu AMIN)

   _“Sam ban bari mahaifana sun gane halin da nake ciki ba har na tsayon sati biyu, tun lokacin da abun ya faru Alhasan ya dinga jigilar zuwa gidan mu yana bani hak'uri, ni kuma na juya masa baya naki kulashi hakan yasa sai shi kuma ya daina zuwa, haka sai yasa na kara tsanar shi sai na ɗinga tunanin ko auren shi nayi wulakanci kawai zai biyo baya kuma wata kila ya rik'a neman matan banza maybe ma halinshi ne akan wannan dalilin yasa nace wa mahaifina bana son shi sai mahaifina ya taramu a parlor yana tambayar ko wani abun ne ya shiga tsakanin mu nan nace mashi babu komai shi kuma yace shi dai idan bana son shi zai iya janyewa dan yaga yaga take take na kuma daman mutanen unguwa sunce bana da mutunci bansan girma ba. Bakin cikin furucinshi yasa na tashi tsaye gaban mahaifina na nuna shi da yatsa nace, Eh bana son ka duk abinda kasan ka kawo ka faɗa a biya ka,_

 _Baki da da kunya baki da tarbiya a fasa ɗin idan an fasa waye a matsala abun ya fito bakinshi kenan yana rawar kai, a nan ni kuma nace mishi ina da tarbiya alhasan kaine dai baka da ita kuma baka haɗa hanya da ita ba wulakantacce dan karin girma_

_Nan take mhaifina ya watsa min mari yana faɗin taya zamu tsaya gaban idon shi muna faɗin waɗannnan kalamai idan bama son junan mu ai sai mu faɗa ba sai an kai ga haka ba, sai da yayi mana tas daga ni har shi sannan yace idan baya sona ya aiko a karɓar mishi kayanshi, haka ko akayi kamar mai jira sai ga iyayen shi ya aiko wai shi ya fasa Auren kuma duk abinda ya kawo ya yafe Allah ya haɗa kowa da rabon shi, nima ban damu ba dn banyi tunani ina ɗauke da cikin ki ba,_

_Da wani Cousin ɗina Abbah ya haɗa mu, ya saka lokacin Auren mu Wata biyar kamar yadda yasa ni da Alhasan, Wata biyu da faruwar hakan rashin lafiya ta sameni mai tsanani har ta kai bana iya tashi nan mahaifina ya sani a mota da mahaifiyata muka je Asibiti, a nan aka tabbatar min da ina ɗauke da cikin ki_

 Nan kuka ya yaci Karfin ta ta kasa k'arasawa, Wani irin sanyi jikin Minal yayi nan itama ta fara zubar da hawaye.

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO...! 


         NA 


KHADEEJA CANDY 




BABI NA TARA___9



             BAYAN KWANA UKU....... 

Zaune take a parlor tana shan wakar Rahama _(you can in the emergency room)_

Sai ruwan hawaye take tana shafa gashin kanta, 

Bugun kofar da taji anayi ne yasa ta  share hawayenta ta tashi ta nufi kofar, ta buɗe. Ganin Saif yasa tayi juya zata rufe kofar, 

   Cikin wani irin zafin nama ya tura kofar ya fisgota abun ka da marar jiki haka ta tafo suww ta faɗo saman faffaɗan kirshinji, 

Da sauri ta ɗago tana kallon shi gabanta sai bugawa yake da karfi, cikin ɗaga murya tace, 

“Mi ya kawo ka nan bayan duk abunda kake so ka samu ko ko kazo kaje da raina ne?”

Glasse ɗin idonsa ya cire suna haɗa ido tsigar jikinta ta tashi, da sauri ta kawar da nata idon tana haki,

Cikin sanyayyiyar murya ya soma magana, 

“Minal banyi duk abunda nayi dan na cutar dake  ba nayi ne dan kawai na taimake ki da kuma mahaifiyarki, 

Minal tun lokacin da kuka faɗa min dalilinki na yin haka sai tausayinki ya kamani na kasa samun sukuni, ban laifin abinda kika aikata ba dan nima kaina idan haka ta same ni kwatankwacin abinda zan aika ta kenan” 

D'ago kai tayi ta kalle shi idonta cike. Da kwallah, 

Handkerchief ya ciro ya mika mata yana faɗin, 

“Am ready to help you ki gane ko kuwaye iyayen ki Minal nayi miki alkawari zan shige miki gaba har sai kinsan suwaye iyayenki” 

Yanayin kalaman shi yasa ta kalli kwayar idonshi, duk da kwarjinin da idon nashi suke mata bai hana ta ganin tsantsa gaskiya dake shinfiɗa cikin idon ba, 

Babu alamar wasa ko yaudara a idon shi balle a kalaman shi shima ɗin baiyi kama da masu irin wannan halin ba, 

Hakan yasa ta karɓi handkerchief ɗin ta share hawayenta tace, 

“Thank you Saif amman am sorry bazan iya ganin Mummy a yanzu ba” 

“I know Minal kawai ina son ki je ki tambaye ta yadda akayi kika zo hannunta, kiyi tunani Minal har ba wadda zaki aura ya guje ki saboda haka miyasa ba zaki so sanin wacece ke ba! Ya akayi kika zauna hannun Dr. Salamatu miyasa iyayen ki suka barki wace ce Dr. Salamatu a wajenki duk baki son waɗannnan amso shin Minal?” 

Da sauri tace “Ina so Saif ina son sani wacece” 

Ajiyar zuciya ya sauke, 

“Fine jeki chanja dress ɗinki muje gurin Dr. Salamatu” 

Kallon jikin nata tayi wata t-shirt ce jikinta yellow ta rufe mata jiki sai dai bata da dogon hannu, sai saket ɗin atamfa wadda ya kai mata har kasa, 

Juyawa tayi ta koma ciki, a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya jingina jikin kofar, 

Bata daɗe ba ta fito sanye da gown ɗin atamfa sosai tayi mata kyau sai dai kanta ba ɗankwali, tsaye tayi bakin kofar tana kallon shi kamar mai tunani hakan ya tabbatar mishi da kwankwanto take, 

Hannunshi ya mika mata, 

“I can trust me Minal” 

Sai da ta haɗi muyau sannan tace “Ina bukatar nayi shawara da Deen” 

Kai Saif ya girgiza mata, “Baki bukatar kowa a yanzu kina tare da Saif just trust me” 

Shiru tayi tana kallon hannun nashi kamin ta mika mashi tana hannun,

Sai da yasa a front seat sannan ya saki hannunta ya zagayo ya shiga driver seat, 

Hannu ya kai ya kunna wakar TAYLOR SWIFT _(the story of us)_, ya fara driving.




A hankali take satar kallonshi a zuciyarta tana mamakin abunda yasa yake son yi mata wannan taimako ko kuma sanya kanshi cikin sha'aninta, 

  Wannan duk plan ɗin Mummy ne dan gata na dawo a gareta, haka wata zuciyar tace mata,

Can kuma ta jefama kanta wata tambayar, amman taya Saif zai bar Mummy tayi using dashi? Bayan mutum ne mai akida ɗaya kuma babu wadda ya isa ya sa shi abinda bai tashi ba babu kuɗin da Mummy zata nuna mishi har yaja ra'ayinshi ya mata wannan aikin Saif mutum ne mai zaman kanshi da kanshi how.... 

“Minal tun lokacin dana barki nan kika kwana?” 

Tambayar daya jefa mata ne ya katse mata tunani, 

Sai da ta shafa wuyanta sannan tace “Eh a nan nake” 

“Kuma shima Deen ɗin a nan yake kwana?” 

“A'a baya kwana a nan sai dai yana tayani fira sai dare ya raba sannan yaje ɗayan gidanshi ya kwana wani lokacin kuma ya kan kwana nan” 

Shiru yayi wani abu ya tsaya mishi a wuya duk sai yaji ba daɗi, ko babu komai yar uwarshi ce musulma yana kishin yadda take sakin jikinta tana mu'amala da maza yana bakin cikin yaga mace musulma a irin wannan halin, 

    Kallonshi tayi “Miyasa ka tambaya?” 

Shima kallonta yayi ya ɗan sakar mata murmushin gefen fuska “Babu komai” 

Daga nn bai sake cewa komai ba ita bata sake cewa ba har suka isa. 

    Yana yin parking gabanta yayi dakan uku-uku, bai ce mata komai ba ya buɗe motar ya fita, 

Bayan kamar minti biyar ya fito ya nufo motar, koda ya buɗe motar baiga kowa ba, nan ya rufe motar ya nufi wajen gidan, sai da ya fita harabar gidan gaba ɗaya sannan ya hango ta jinkine da bangon gidan tana kallonshi. 

K'arasa yayi kusa da ita “Mi yasa kika fito? Baki yarda dani bane?” 

“Na yarda da kai kawai dai am not ready to meet her” 

Ajiyar zuciya ya sauke, 

“Minal karki manta badan taji daɗi zakije ki ganta ba no saboda kina bukatar wasu amsoshi ne right?, 

Ko bayan haka matar nan bata chanchanci haka daga gareki ba she's take good care of you for more than twenty years duk wani jindaɗi ta baki babu wata ya mace da zata nuna miki gata kina ganin idan kika mata haka kin kyauta kenan after that baki san uzurinta ba”

Kasa tayi da kanta, tana lumshe ido,

“Wannan dama ce a gareki Minal karki bari ta wuce ki”

Hannu ta mika mishi tana ɗaga kai, 

Badan yaso ba ya mika mata nashi hannun ta rik'e gam sannan suka nufi cikin gidan,



Rike take da hannunshi har suka isa cikin parlor, 

    Dr. Salamatu na ganinta ta tashi tsaye da sauri, 

“Minal my child” 

Bayan Saif Minal tayi ta taɓe kamar wata karamar yarinya da taga abun tsoro, 

Hakan yasa Dr. Salamatu ta tsaya bata k'arasa kusa da ita ba ta rungume hannayenta, 

Saif ya kalleta “Da kin zauna da yafi” 

Ba musu ta koma ta zauna tana kallon Minal, shima Saif a kujerar dake kusa dashi ya zauna, ganin hakan yasa ita ma Minal ta zauna a kujerar daya zauna jikinta na gogar nashi, da yake kujerar zaman mutum biyu cikin dabara ya matsa aka samu space tsakanin su, 

Mummy ce ta fara magana “Na sani Minal i hurt....” 

Da sauri Minal ta tari numfashinta “Mummy I'm not here to tell me love me or hurt me I'm here to tell me who I really am who is my father and who is my real mother?” 

 A takaice Dr. Salamatu ta bata amsa “I'm your real mother Minal nina haifeki” 

Ido Minal ta sakar mata alamar bata gamsu ba, 

A hankali hawaye suke saukowa a fuskar Dr. Salamatu cikin rawar murya tace “Minal zan faɗa miki ko wacece ke a yau zan tona asirin dana shekara ashirin da uku ina boyewa” 

Shiru tayi ta noce kai, ganin haka yasa Saif ya tashi tsaye da niyar fita, dan a tunaninshi bai dace yaji sirrin su ba,

Nan itama Minal ta rik'e mashi hannu ta tashi tsaye, Mummy kamar tasan abunda yake ranshi sai ta kalleshi, 

“Zauna Saif duk abunda zan faɗa ma Minal zan iya faɗa maka” 

Kai ya girgiza zaiyi magana Minal tace “Please Saif for me” 

Kasa magana yayi sai ya koma ya zauna ita ta zauna, Sit parlor yayi kamar babu mutane har na kusan minti biyar, sannan Mummy ta ɗago ta kallesu ta fara magana........... 




VOTE! 

COMMENT!! 

SHARE!!!

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO...! 


          NA 


KHADEEJA CANDY 



_Gun zance ka iyawa halshenka wani guri kuma karda ka kai kanka sannan ka zamo mai kare mutunci ka_👌🏿

            _NURA M INUWA_



BABI NA GOMA SHA D'AYA___11


Kuka Mommy tayi sosai kamin ta cigaba, 

_“Bakin cikin kan iyayena sun yi shi sukace sai na faɗa musu wadda yayi min cikin nace Alhasan ne, nan take suka je suka same shi da batun nan ya karya tani yace shikan ko hannu na bai taɓa rikawa ba kazafi nayi mashi har da cewa sai yayi karata daker iyayena suka samu ya hak'ura Abbah na ya sani gaba sai na faɗa mishi cikin waye na rantse mishi yaki ya yarda ni_

_Tun daga lokacin na soma fuskantar wulakanci ɗaki ɗaya aka ware min kullum ciki nake rayuwa bana zuwa ko ina har cikin ki ya kai sata tara, Ranar wata Laraba naqudarki ta taso min da taimakon mahaifiya na haife ki”_

    Dagowa tayi ta kalli Minal idonta na zubar da hawaye tace “Tun da na haife Tausayinki ya kamani na rayuwar da zaki shiga da kuma zuwan wannan ranar da zaki tambaye ni waye ke” 

   

Wata irin ajiyar zuciya Minal ta sauke ta jinginar da kanta jikin Saif. Tana kallon Mummy da ya cigaba da zancen, 

_“Duk wace ta haihu tana bukatar kulawa amman ni ban samu ba sai ma lokacin na gane bana da gata abinci yara ake bani ruwan nono na ya soma kafewa a haka na wata biyu ni da ke muka koma kamar masu ciyon kanjamau saboda rama ban taɓa tausayin kaina ba kullum ke nake tausayi, wata rana Abbah na ya fitar dani cikin ɗakin da nake Mamana na kuka ya sani a mota mukayi ta tafiya mai nisa sai da ya kai hanyar dake tsakanin Abuja da Kaduna ya sauke ni ya kuma yi min gargaɗin karna kuskura waiwaiya su da duk dangin su dan na riga na ja musu abun faɗi_

_A gurin ya barni naci kuka sosai na saɓaki a baya ina tafiya idan na gaji sai na tsaya na huta haka na rik'ayi har na kai wani kauye dake kusa da gurin, mutanen kauyen saun tarɓeni sosai ni kuma nayi musu karya nace yan fashi suka tare ni nayi gudu har na kawo kauyen nace musu mijina yana cikin garin Abuja, sun nuna min so sosai suka haɗa min kuɗin mota da rakiyar wasunsu aka kaini tashar garin na hau mota Abuja,_

_Dana shiga cikin Abuja sai na shiga gidajen masu kuɗi bara idan dare yayi sai naje wani tsohon shago na kwana, Wata rana ina halin baran na faɗa gidan Alhaji Mamman, yanayin halin da nake ciki ya bashi tausayi gani da kuruciyata hakan yasa ya sani gaba yana yi min tambaya dalilin baran nawa, ban ɓoye mushi komai ba na faɗa mushi labarina sosai ya tausaya min shi da iyalinshi_

_Daga lokacin ya maidani gidanshi ya rik'e ni yana nuna min gata ni dake cikin yan kwanaki mukayi bulbul bayan na yayeki yace zai maidani makaranta sosai naji daɗi kuma na Amince dan daman abunda nake jira kenan, a matarshi ya sani tare da Matarshi da yar shi Kairat muka je har yola gurin Abbah na ɗauko takarduna nan sosai ya so ya shirya ni da Abbah amman sam yak'i yarda sai ma cewa da yayi wai karuwanci zanje yi da gaggan nayi wannan cikin,_

_Ban damu da duk wani furuci nasu ba tunda ba albarka suka cire min ba kuma daman ni ke nake yima tanadi, yana dawowa ya nema min admission na shiga yin mastas ke kuma ya samo mai rainonki, ina gama mastas ya sake nema min admission na koma University nayi  degree a ɓangaren Economics, ke kuma ya saki a Primary school,_

_Bayan na kare karatun ya nema min aiki a kanfanin da yaki aiki, da sannu sannu har aka bani karamar manajan kanfanin, Kina kare Secondary School, na name miki Chartere By act of Congress The American University, Maza da dama sun yita neman Aurena amman naki yarda nayi Auren dan kawai nayi miki tanadi_

_A lokacin Alhaji Mamman ya soma sani a harkokin Siyasa ni kuma na shiga gadan gadan har na samu karamar Minister man fetur, ban tsaya nan ba na shiga siyen hannayen jari ba ɗaya ba duk dan ki samu jindaɗi yadda kowa yake ji,_

_Daf da zaki gama Secondary school na koma gurin dangina ba dan komai ba sai dan nasan duk kika girma sai kinso ganin family ki, sunyi na'am dani a lokacin sai dai kece suka ce ba zasu karɓa ba dansu a dangin su babu shegen dan haka karna na kuskura nuna masu ke_

_Nayi mamakin yadda dangina suke da riko wata kila ko dan suna yare ba hausawa ba, ni kuma tun daga lokacin na yanke shawarar kin haɗa ki dasu dan karsu wulakanta ki,_

_Kina gama Secondary School kika dawo Nijeriya, ni kuma lokacin na sauka daga muka mina sanadiyar chanjin gobnati da aka samu nan ne ke kuma kikace kina son na nema miki makaranta a faransa_

_Bayan tafiyarki karatun ne wannan gobnati ta hau akamin babbar ministen man fetur_

    Ajiyar zuciya ta sauke tace, 

_Da kika dawo sai kika kika fitar da wannan saurayin naki wadda ya chanja miki tunani har kika rik'a k'ina a kanshi_. 

  K'asa Minal tayi da kanta tana haɗiyar yawu, idonta cike da hawaye, 

Tashi Mummy tayi ta shiga bedroom, bayan kamar minti goma ta fito rike da wani littafi mai kamada Diary daga gani tsohuwar ajiya ce dan duk tayi kura, ta mika ma Minal tana faɗin, 

“Wannan littafin na aje shi ne danki duk gurin da wani family members naku yake address ɗin shi yana nan ciki wannan shine tarihin ki Minal ina fatar zaki sami natsuwa” 

Hannu Minal tasa ta karɓa  tana kallon fuskar Mummy dake kokarin maida kukan dake son fito mata, 

Juyawa tayi ta koma ɗakin hawaye na mata zuba, Hannu Minal ta mika zata rik'o hannun Mummy, da sauri Saif ya rik'e mata hannun tana kallonshi ya girgiza mata kai, alamar a'a. 

   Nan itama ta fashe da wani irin matsanai cin kuka ta chusa kanta cikin kirginshi, rumtse idon yayi da suka yi mishi jawur kamar wadda yayi kuka, 


Kukan tayi sosai sai da ya tabbatar da ta samu sukuni sannan ya ciro handkerchief ɗinshi ya share mata hawaye ya rik'a hannunta suka fice, 

Gurin da yayi parking ɗin motarshi ya nufa sai ya saka ta sannan ya shiga ya fara Driving, 

Har suka isa babu wadda yace da wani uffan ita dai sai kuka take yi, shi kuma ya kasa bata hak'uri. 

  “Minal miye haka kuma tun ɗazu kuka kike kodai baki yarda da abunda Mummy tace miki bane?”

Bayan ya kashe motar yayi mata maganar yana ɗan buga sitarin motar, 

“Na yarda Saif ina dai jin ban kyautawa Mummy ba ina ma ban aikata abunda na aikata ba miyasa idona suka rufe na kasa fahimtar Mummy mi yasa banyi mata uzuri ba? Ji nake yi ba daɗi bansan miye abun yi ba”

Kallonta yayi, 

“Minal in dai har kinyi nadama to kije ki bata hak'uri ki nuna mata kinyi nadama kuma ki roki gafarar ta kinji?” 

Kai ta ɗaga mishi tana share hawaye, sannan ta buɗe motar da niyar fita, sai kuma ta juyo ta kalleshi. 

  Murmushi ya sakar mata wadda ya faɗar mata da gaba ya wani lumshe sleeping eyes ɗinshi ya buɗe still yana murmushi, 

Ta daɗe tana kallonshi kamar ba zata ɗauke idon ba, sai kuma ta k'arasa fitar ta rufe mishi motar.

Bai bar gurin ba sai da yaga ta shige cikin gidan sannan ya sauke ajiyar zuciya ya sama motar shi key, 

  

Kai tsaye gidanshi ya nufa yana yin parking ya dubi a gogon hannunshi, 10:41pm ya gani kai ya ɗan girgiza ya buɗe motar ya fita, 

 Da sallama ya shiga yana kallon gurin da Huda ta saba zama, cikin sa'a kuwa ya hangota zaune ta tsaɓa ado tana kallon tv kamar bata san da shigowar shi ba, duk da yasan taji sallamar maybe tayi hakan ne dan yayi dare, 

Kusa da ita ya k'arasa ya ɗan lek'i fuskarta

“Dear kina jina kika ki amsa sallama ko?”

K'ara ɓata fuska tayi, 

“Sai da nace maka karka daɗe zamuyi zaɓen cake amman kaje ka zauna har yanzu” 

Sai a lokacin ya tuna da maganar Birthday ɗinta, da sauri ya zauna kusa da ita, 

“Ayyah Wallahi kwata-kwata na manta.. -” 

Ganin yadda ta kalleshi yasa ya chanja maganar, 

“I mean wani abun nayi important ba wai mantawa nayi ba” 

Taɓe baki tayi “Ba wani nan daman dai baka ɗauki abun da muhimmanci bane har akwai wani abun important da yafi nawa?” 

Bayan ta ya shafa cikin daɗadɗiyar murya da yasan zata kashe mata jiki ya soma bata hak'uri kamar mai raɗa, 

“Am so sorry Dear tuba nake muje yanzu mu zaɓa” 

Kallon shi tayi kamar ta musa masa sai kuma taji ba zata iya ba, ganin hakan yasa ya rik'a hannunta suka nufi bedroom.

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO...!


         NA 


KHADEEJA CANDY 



_There are 4 things you can never recover, The stone..after the throw. The word..after it’s said. The occasion..after it’s missed. The time..after it’s gone._

                    


BABI NA GOMA SHA BIYU___12



MINAL.............. 

Juyi take tayi saman gado tana tunanin  Mummy, sai damn shafa Diary take wasu zafafan hawaye na mata zuba, 

  A hankali taja filo ta rungume, wani irin tsanar kanta ta karaji,

 Tun jiya bata samu ta rumtsa ba gashi yau ɗin ma bachin yaki d'aukarta dan sam idanunta babu alamun bachi ciki, 

Tashi tayi zaune tana cizon bakinta, ta janyo wayarta ta danna ma Deen kira, bugu ɗaya ya ɗauka, 

  “Hello Deen”

“Ma'am Deen kana kusa ne.? Ina son magana da kai” 

Daga can cikin wayar ya amsa mata, 

“A'a bana kusa Deen amman dana kare abunda nake zanzo ok” 

Kasa kasa ta amsa mishi 

“Ok”

 ta kashe wayar, ta tsura ma Screen ɗin ido, 

Motsin da taji yasa ta tashi ta nufi parlor, Kairat ta gani tsaye tana wasa da keys ɗin dake hannunta, da gudu taje ta rungume ta

“Ke lafiyar ki?”

 Kairat ta tambayeta tana kokarin boye murmushin dake fuskarta, 

Sakinta tayi ta kama hannayenta, 

“Thank you for coming daman ina bukatar wadda zamu tattauna” 

Zaunawa Kairat tayi tana faɗin “Saif ne yace min nazo” 

Ajiyar zuciya ta sauke 

“Kairat Mummy ta faɗa min komai ta faɗa min ko wacece ni Kairat Mummy ta wahala sosai kamin nakai matsayin da nake yanzu”

Nan Kairat ta tari numfashinta, “Kuma lokaci ɗaya kika juya mata baya idonki ya rufe kika kasa fahimtar komai kunnen ki a daɓe kika ki saurara mata” 

Idonta cike da hawaye

 “Nayi nadama sosai nayi dana sanin yin hakan da nayi kuma ina bakin cikin dana saka Mummy cikin bakin ciki” 

“Toh idan dai har haka ne Minal kije ki bata hak'uri yanxu baki san halin da take ciki ba saboda ke Minal kuma nasan duk ta ganki zataji daɗi zata kuma yafe miki abunda kika mata kinsan Mummy bata da wani farinciki sai naki” 

Shiru ta ɗanyi 

“Sis kina ganin Mummy zata saurare ni kuwa zata yafe min nan take ta fahimci ne?” 

“Sosai ma ai tasan ke a rashin sani kuka yi kuma kin gane kinyo ba daidai ba yanzu kika zo neman gafara zata yafe miki kinsan tana sonki sosai ai”

Haka Kairat tayi ta mata har ta karfafa mata gwuiwa. 



                     ******


Kuka sosai Dr. Salamatu tayi har sai da ta godewa Allah kukan data shekara ashirin da wani abu batayi irinshi ba, rayuwarta, ta baya dawo mata a rai wani kololo ya tsaya mata a rai. 

   Ajiyar zuciya take ta faman saukewa, sakamakon wano kololo da yayi ya tsaya mata tana dafa zuciyarta wai ko zata zamu sassauci amman sai kara jin abun take yi Har yaya kokarin taushe mata numfashi, 

Hakan yasa ta tashi ta nufi downstairs, 

tana sauka ta buɗe firig ta ɗauki gorar Swan, saman firig ɗin ta ɗauki cup ta zuba ruwan. 

   Sai da tasha kopi biyu sannan taji abun ya ɗan kwanta mata, dawowa tayi saman kujera ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, jin bata samu sukuni ba yasa ta tashi ta nufi babban parlor gurin da tsohuwa da Talatu suke zaune suna kallo.

   Har ta kusa isa sai kuma ta juya ta nufi upstairs, ɗakinta ta koma ta kwanta sakamakon ciyon kan da taji yana son taso mata, idonta ta rufe kamar mai bachi tana haɗiyar yawu, 

   

“Mummy.........” 

Kamar daga sama taji kiran da muryar Minal hakan yasa tayi saurin buɗe idon ta kalli kofa, 

  Gurfane take kasan gwuyoyinta fuskarta shakaf da hawaye, 

“Mummy ki yafe min na tuba nayi nadama nayi hakan ne dan kawai nasan ko wacece ni Mummy I'm so sorry” 

Da sauri Mummy ta sauka saman gadon ta nufi kofar ta tada ita tsaye ta shigo ta ita cikin ɗakin, 

   Sake zubewa kasa Minal tayi ta rik'e kafafaun Mummy tana kuka kuka na gaske mai nuna tayi nadama har a cikin ranta, 

“Mummy ban kai Ya ba ban miki halanci ba ban kyauta miki ba ban kuma kyauta ma kai na ba nayi babban kuskure dana yi miki mummunan zato ki yafe min kar kiyi fushi dani” 

Dafata Mummy tayi tana hawaye 

“Ki daina kuka Minal banga laifinki ba daman nasan sai wannan ranar tazo dole ne wata rana zaki bukaci sanin ko wacece ke, ni ban taɓa fushi dake ba, na kuma yafe miki duk abinda kika yi min” 

Tashi Minal tayi tsaye ta rungume ta tana kuka, 

   Murmushi Kairat dake tsaye bakin kofa tayi ta kunno kai cikin ɗakin,

 “Daman ai na faɗa miki Mummy zata yafe miki kinsan tana sonki sosai ai” 

Sakin Mummy tayi ta share hawayenta ta kalli Kairat, “Thank you Sister” 

Kumatunta Kairat taja 

“You most welcome” 

 “Allah yayi muku albarka”

Mummy ta faɗa tana kallonsu cike da jidaďi, 

  Haɗa baki sukayi gurin amsawa, 

“Amin Mummy”

Snap suka zube Kazan carpet Mummy Tana Kara labarta ma Minal halin rayuwar ta,

     Daren ranar ɗaki ɗaya suka kwanta da Mummy ko wane zuciyar shi cike da fariciki. 



WASHE GARI............ 

 Dummm! Kake ji wani wawan dudu Kairat ta kai mata a baya, a firgice ta farka ta tashi zaune, 

   “Mi akayi?” 

Baki Kairat ta saki 

“Huh tambaya ta ma kike dubi time ko gani karfe nawa yanzu wane irim bachi ne haka?” 

Sai da ta murza ido sannan ta dubi a gogon, 

“Eleven pass ten” 

Kairat ta bugar mata kai

 “Kika kai har 11 kina bachi dan kawai jindaɗi” 

Kan ta dafe

 “Oh Sis kan nan ma fa ciyo yake min” 

“Yau toh ni ina ruwana ya fashe mana dan Allah wake up” 

Tashi tayi dan tasan ba yadda ta iya dan idan tace zata koma Kairat ba zata barta ba, bedroom ta nufa tana mika, 

  Bata daɗe ba fito tana faɗin “Ina Mummy Sis?” 

“Ta tafi aiki tun ɗazu tana da meeting ɗin da bazata iya canceling ba kuma bata son a tashe ki ta dai ce na kula dake” 

Taɓe baki Minal tayi tana rike da kofar toilet,

 “Haba Dear yama za'ayi Mummy tace ki kula dani how old are you ma da zaki iya kula dani definitely Mummy ba za tace haka ba” 

Tashi Kairat tayi tana dariya, 

“Of course i can little girl come let me show you something” 

Da gudu ta fisgi hannun Minal suka nufi downstairs, bata sake ba sai da suka kai Dinning room, 

“WOW” 

Minal. Ta faɗa tana kallon kalolin abincin da aka jere, saman dining ɗin, 

“Kairat duk wa yayi wannan?” 

“Nice mana duk wazai miki wannan idan ba ni ba” 

Plantain Minal ta ɗauka ta kai baki,

 “Please Sis faɗa min gaskiya” 

Sai da ta ɗan tsakure ta sannan tace 

“Mummy ce ta haɗa miki kinsan tana sonki ai” 

Wani irin daɗi ne ya ziyarci zuciyar Minal, hannu tasa a baki tana murmushi, 

“I know and I love her too” 

Murmushi Kairat tayi ta mika hannu a ɗayar kujerar ta ɗauko wani ɗan karamin kwali mai zagaye da fulawowi,kamar gift ta mika mata 

“And this one is from Saif” 

Da sauri Minal ta karɓa taja kujera ta zauna ta shiga buɗewa, 

Wani ɗan karamin Cake ne da wata yar karamar paper fara mai haske gefen cake ɗin, sai da ta gutsuri cake ɗin taci sannan ta shigo karanta takardar, 


  ```      HELLO MINAL.... 


How are you? How particularly is Dr. Salamatu weather treating you? Ina fatar komai ya zama daidai yanzu! Na hango ki kina ta rawa cikin bachi na,```


Murmushi ne ya suɓuce mata ta lumshe ido tana tsutsar baki, har na kusan mintuna sannan ta buɗe su kan takardar, 


```Ah ha! That is it i just want to see your smile and say good morning to you have some breakfast and have a nice day.```


                         *~Sign~*

                                    *Mr. S B_B*



A bayan takardar aka rubuta, 

   

*Your Brother From Another Mother*



Da murmushi ta rungume takardar tana kallon Kairat data sakar mata ido, 

“Waya aiko ko shine ya kawo da kanshi?” 

Hannayenta ta ware alamar ban sani ba,

 “Nikan karki tambaye ni nima gani nayi a aje miya rubuce a ciki?” 

Da sauri ta mayarda takardar bayanta 

“Ba ruwanki please ni dai bani number shi idan akwai”

Baki da murguɗa mata

 “Nima bana da ita kije can ki nema” 

“Kince Mummy tace ki kula dani fa haka ake kula sa mutun ba'a bashi abunda yake so?” 

“Ai kince karya nake yi right? Bazan iya kula dake ba” 

“A'a na daina zaki iya Allah” 

Dariya Kairat tayi ta nufi Stairs, 

“Toh kici abinci saina baki yar Mummy” 

Murmushi Minal tayi ta shiga cin abincin cike da shauki.





Wattpad @khadeeja_candy 


Candynovels.wordpress.com 


#Share

#Vote

#Comment

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO....! 


          NA 


KHADEEJA CANDY 



_Never ignore a person who loves and cares for you, because one day you may realize that you’ve lost the moon while counting the stars._



BABI NA GOMA SHA UKU___13



“Wai kina nufin bachi zakiyi.?”

Idonta a lumshe ta ďaga mishi kai alamar eh, 

“Toh karma ki fara kwana biyu fa haka kike min kina barina online gurin za6a miki Cake har biyu na dare kina sharar bachinki kuma yanzu kice bachi zakiyi ai nine n chanchanci haka”

Maganar yake yana wani shafa bayanta ita Kuma tana kwance saman cinyarshi, ďaga kai tayi ta kalleshi

“Anjima kuma zaka za6a min rigar da zan saka da takalmi”

Murmushi yayi,

“Lallai yarinya daďi yayi miki yawa kiji daďin sake yin bachi ki barni ko?”

Zatayi magana wayarta dake kan flat table tayi ringing, da sauri ya ďaga ta daga jikinshi ya nufi gurin da wayar take, juyowa yayi bayan ya duba wayar yace

“Number ba suna”t

Tana jin haka tayi saurin tasowa kamin ta karaso ya danna picking ya kara a kunne, 

Yanayin fuskarshi naga ya chanja alamar mamaki,

“Wanene.?” 

Da sauri naga ya kalli wayar ya kalleta 

“Muryar naji wai hello Dear nace wanene ya kashe wayar” 

Faɗuwa gabanta yayi da sauri ta karɓi wayar ta shiga dubawa, 

“Ni ban ma san mai number ba ina jin wrong number ne” 

Kafaɗunshi ya ɗaga ya rik'a fuskarta ya sakar mata kiss a goshi, 

“Bari naje shirin aiki karna zama doja akai karata gurin Dad ok?” 

Kai ta ɗaga mishi yayi mata murmushi ya nufi ɗakinshi,

       Da kallo ta bishi sai da ya shige sannan ta dafe kirjinta ta sauke ajiyar zuciya ta nufi kicin tana dannar wayar, 

Yana shiga ya cire kayanshi ya shiga bathroom yayi wanka ya fito ya shiga shirya kanshi, 

  _DiLLL_ wayarshi tayi kara alamar sako, kallon wayar kawai yayi ya ɗauke kai sai da ya gama shirinshi tsaf sannan ya ɗauki wayar ya duba, 


           ```   HELLO Mr. S. B_B 


Minal Alhasan ce bansan kallaman da zanyi amfani dasu wajen gode maka ba na sani cikin farin cikin da ban taɓa mafarkin shiga ba na gusar min da duk wani bacin rai na, ka sami nida Mahaifiyata cikin farin ciki mun koma kamar yadda muke a da na gode sosai Saif Allah ya saka maka da Alheri bazan taɓa mantawa da kai ba. 


                  FROM MINAL!```



Murmushi yayi yasa wayar aljihu ya fice, 



“Wai mi kike ma murmushi ne?”

Kairat ta tambaya, 

Murmushin ta sake yi ta mika mata wayar, 

“Duba da kanki” 

Ba musu ta karɓa tana dubawa, 

“Oh Sis yanzu ki rasa irin text ɗin da zaki tura Mishi sai irin wannan ?” 

Fuskar mamaki tayi “Mi kike nufi?” 

“Toh yanzu dan Allah miye abun burgewa cikin wannan massage ɗin sai kace wata yar kauye” 

Tsaki taja ta fisge wayarta ta tashi da nufin barin ɗakin, 

 “Aikin banza daman ai ni ban taɓa yin abu kika yaba min ba kullum ni ban iya komai ba”

“Matsalar ki kenan ba ada ikon faɗa miki gaskiya sai ki hau tsakanin da Allah ni banga abun burgewa cikin wannan message ɗin ba abu kamar ba wace tayi karatu a waje ba” 

Tsakin ta sake ja a karo na biyu ta watsa mata harara ta fice tare da jan kofar ɗakin da karfi, 

Dariya kawai Kairat tayi ta cigaba da dannar wayarta. 



                      *******************



Bashi ya dawo gidan ba sai 9:30pm a gajiye ya shigo, kai tsaye ɗakinshi ya nufa ya shiga bathroom ya watsa ruwa ya fito jallabiya ya ɗauka ya saka tare da ɗan short jean sannan ya fito ya nufi ɗakin Huda,

  Zaune ya tararda da ita laptop na gabanta tana faman duba wasu riguna, ko sallamar da yayi bata amsa mishi ba, 

Kusa da ita ya zauna bayan ya sakar mata kiss a kunci yace 

“Dear mi kike yo haka baki masan na shigo ba?” 

“Wallahi ina ɗan duba wasu riguna ne da zan saka ya aikin?”

“Alhamdulillahi aje wannan aikin muje muci abinci yunwa nake ji”

“Nima fa yunwar nake ji daman kai nake jira ka dawo” 

Hannunta ya rik'a 

“Toh na dawo tashi muje downstairs” 

  Kallonshi tayi “Take away fa nake nufin kayi mana dan tun abincin rana ne da Larai ta dafa kuma faten doya kasan kuma baka sonta ni kuma ban samu na dafa komai ba” 

“A'a wasa dai kike ko?” 

“Wallahi da gaske nake ba kaga abunda nake ba tun ɗazu nake Online ban samu kayan da suka yi min ba”

      Sam bai yarda ba tashi yayi ya nufi downstairs, 

Sai da ya duba ta tabbatar da gaske take sannan ya sake nufo ɗakinta rai a bace, bakin kofa ya tsaya fuskar shi a ɗaure, 

“Huda wannan wane irin wulakanci ne ace ni da gidana amman bana da halin jindaďi kamar sauran maza wannan wace irin rayuwa ce?”

B'ata fuska tayi “Haba dear wai miyasa baka ganin tausayi nane wai aikin gidan nan kace baka son kowa yayi sai ni tun safe fa nake ta kai da kawo cikin gidan nan ga wannan aikin dake gaba na shin dame kake son naji dan Allah kuma wannan faďan ma kasha yinshi kaga bazan iya wani abun ba tunda gidan mu bamu saba da aiki ba akalla yanzu nayi shekara biyu gidan nan kullum abu ďaya ya kamata ka ďaga min kafa mana”

Wani murmishin jin haushi yayi ya kađa kai kawai ya fice,

   D'akinshi ya dawo ya faďa kwance saman gadon yana ta tunanin magagganun da Huda tayi mishi da kuma hali irin nata ,lokaci lokaci yakan ya tsaki yana gwaďa kai hannunshi na hagu na saman cikin shi,

   Jin yunwar ba zata barshi ba yasa ya tashi ya ďauki keys ďinshi ya fice.



ROYAL KING HOTEL............ 

    Minal ce a tsaye kusa da reception, sanye da doguwar riga ta farin material mai kyali da yar hula sai kalle kalle take kamar bakuwar gurin,

  Juyowar da zatayi ta hango tafe, tun kamin ya karaso ta rika sakar mishi murmushi, shi kan baia san tana yi ba dan hankalinshi kwata kwata baya jikinshi,

Ganin zai wuce ta yasa ta kira sunanshi,

“Saif...”

Juyowa yayi yana neman mai kiran sai a lokacin ya lura da ita, murmushi ya sakar mata

“Minal mi kike yi a nan?”

“Ai kaine ya kamata nayi ma wannan tambayar”

“Ni ai kinga Namiji ne Take away nazo yi ke da wa kika zo nan?”

Hannu sata a baki kamar wata karamar yarinya

“Ni da Mummy tana gurin biyan kuďi”

Hangen Mummy tafe yasa ta karaso kusa dashi tana nuna ta 

“Gama ta nan zuwa” 

Kallo đaya yayi ma Minal ya ɗauke kai ya kalli Dr. Salamatu da ta k'arasa kusa dasu, 

“Good evening Dr. Salamatu” 

Fuskarta a sake ta amsa mishi

“Evening Saif ya kake?” 

“Lafiya kalau ya hak'uri ya abubuwan?” 

“Da godiya na gode sosai Saif Allah ya saka maka da Alheri” 

Da sauri ya tari numfashi ta 

“Oh ai babu komai Allah ya tsare gaba” 

Minal ce ta amsa da 'Amin' ta rik'a hannun Mummy suka nufi kofar fita shi kuma ya kunna kai cikin Hotel ɗin,




WASHE GARI.......... 

Tunda Minal tayi sallah asuba bata koma bachi ba sai kawai ta nufi kicin, abubuwan duk da tasan Mummy naso  gurin breakfast su ta shiga haɗa wa cikin taimakon Allah kuwa ta kammala komai in time, 

  D'akinta da dawo ta cire kayan bachin dake jikinta ɗaura tawul ta shiga bathroom, bayan tayi wanka ta fito bata tsaya shafa komai ba tana tsane jikinta ta nufi wardrobe ta saka dogon wando jean da riga T shirt green color ta ɗauki wani guntun ribon ta ɗauke gashin ta sannan ta nufo ɗakin Mummy,

    Bata tararda kowa ɗakin ba, motsin ruwan da taji ya tabbatar mata da tana bathroom guri ta samu ta zauna tana kallon kofar banɗakin har ta Mummy ta fito, 

“Mummy good morning” 

Da murmushi Mummy ta amsa 

“Morning Minal how are you har kin tashi?” 

“Eh tun ɗazu ai nima na haɗa breakfast” 

Zaunawa Mummy tayi kusa da ita tana shafa kanta

“Allah yayi miki albarka Minal ya kara miki lafiya ya shirya min ke” 

Hannunta Minal ta rik'a “Amin Mummy tashi muje kici abincin”

Ba musu Mummy tashi suka fice, 

  Downstairs suka nufo, kamin su k'arasa saukowa Minal ta hango Kairat zaune tana breakfast, aiko ba shiri ta saki hannun Mummy ta nufo Dining area da gudu, Kairat na ganinta ta tashi da sauri ta zagaya ta baya tana dariya, 

“Minal am so sorry inajin yunwa ne kuma tsohuwa tace min ke kika girka  da kanki shine naci naji idan yayi daɗi” 

Dariya Mummy tayi ta kalli Kairat 

“Nan kika kwana ne?” 

“A'a Mummy yanzu na zo ina kwana” 

“Lafiya kalau ya gidan?” 

Kujera Minal ta jama Mummy 

“Mummy zauna  a nan kici lokacin zuwa aikin ki yayi” 

Nan ta juyo gurin Kairat

 “Ke kuma ki wuce ɗakinki ko ki koma gida” 

Mummy ta zauna tana faɗin,

“Babu inda zataje kin taɓa ganin mutun ya bar gidan su yaje wani gurin?” 

Fuskar shagwaɓa Minal tayi 

“Toh Mummy taje ta haɗa ma kanta breakfast ɗin dan ni ba zata ci min abunci b katuwa da ita” 

Mummy zatayi magana tsohuwa dake kokarin shigowa ta rigata, 

“Yau ku ji min Minal ke da nake dafa miki kina ci fa” 

Juyowa Minal tayi “Ke tsohuwa mi ya kawo ki nan, kuma ni ai ba wani girma ne dani sosai ba balle kice ita fa tayi uku ɗina haka kawai zan dafa mata abinci” 

Tsohuwa tace "Ai ba ita kika dafa ma Hajiya kika dafa ma Hajiya kuma uwarta ce dan haka dole ta ci” 

Dariya Kairat tayi “Yauwa tsohuwa faɗa mata dai cin abinci kan har na gama dai dai kiyi hak'uri” 

Mummy dake cin abinci ta kalli Kairat “Zauna kici tun bai huce ba yar mamarta” 

Kujera Kairat taja ta zauna tana yima Minal gwalo, ɓata fuska Minal tayi kamar ta fasa kuka 

“Har da ke ko Mummy” 

Mummy ta kalleta “Yau toh ya zanyi Minal ya tace fa” 

Rumgume hannayenta tayi “Toh duk ku tashi ma na fasa baku abincin” 

Tsohuwa ta rik'e baki “Har da Hajiya?” 

“Eh har da ita kuma kema ba zaki ki ci shi ba” 

“Yau ni tsohuwa dani mi zanyi da kwai da plantain ni tun da safe na karya da  koko da kosai kuma kuma na ci ɗumame dan haka ki rike abinki indan ni” 

Fuskar shanu Minal tayi ta koma saman kujerar parlor ta zauna, dariya tsohuwa tasa mata ta nufi kicin tana gyara tsintsiyar da ta shigo da ita, Mummy da Kairat ma dariya suka rik'a yi mata Kairat har da wani rawar kai 


Sai da Mummy ta gama cin abinci ta sannan ta tashi yana hamdala tace “Minal Allah yayi miki albarka abincin nan yayi daɗi kin iya girki” 

Kawar da fuska tayi “Nidai Mummy kyale ni bazan sake dafa miki ba” 

Murmushi Mummy tayi nufi upstairs tana faďin “Na kyale ki kinga ma tafiya ta amman dai ayi hakuri a sake dafa min yayi daďi kin iya girki”

Wink Kairat tayi mata da ido tace “Mummy so fa take ta nuna miki ta iya girki ayi mata Aure”

Filon kujera Minal ta ďauka ta jefe ta dashi “Tashi ki bar gidan nan busa kawai kibar biredi”

Fashewa Kairat tayi da dariya “Ai ni bana da Wata muguwar kiba dan kina kamar ki kare ne kike ganin kiba ta amman ni daidai nake yanzu ma maza son fi son masu ďan jiki ba irinki ba masu kamar su kare”

Minal tace “Wallahi karya ne anfi son irin mu na gaban mota”

Kai Kairat ta girgiza,

“Ki yarda kawai Allah anfi son irin mu yanzu idan muka auri miji ďaya sai yafi sona dake”

Sai a lokacin minal tayi dariya

“Lallai Yarinya waya faďa miki miji ďaya zamu aura har ya fi sonki dani? Ai ni bazan aure mijin wata ba wata kuma ba zata auri miji na ba”

“Toh wanene mijinki wanene kuma mijin wata?” Kairat ta tambaya,

“Idan na auri mai mata toh mijin wata ne ni na aurar mata miji dan zaki ji ance mijin wance ta aura, idan kuma wata ta auri mijina  ita ce ta aurar min miji dan haka bazan auri mijin wata ba saurayi zan aura ba kuma zan bari wata ta aurar min miji ba”

Tasowa Kairat tayi ta dawo kusa da ita tana zolayar ta,

“Koma minene kara ki chanja da gaskiya miji ďaya zamu aura”

“Lol Ke kama kanki ba zaki iya kishi dani ba dan ni bana son kishiya”

“Yau ai nima ba kanwar lasa bace kinga tun nan mun saba da munje can cigaba kawai za muyi”

Da dariya tsohuwa ta fito kicin tana zolayar Minal, daďi Kairat taji ta samu mai kama mata suka rika caccakar Minal tun tana ramawa har ta gaji ta samu su ido,

Suna haka Mummy ta fito da shirinta na zuwa office, tana sauko downstairs Kairat ta tare ta “Mummy dan Allah a aura mana miji ďaya da Minal”

Watseta Mummy tayi “Ke dan Allah rufe min baki tun ďazu ina jinku kun tarar mata har da tsohuwa kuna takura mata yar baiwar Allah”

Daďi Minal taji, “Ai dama kin aura mana miji ďaya ďin da ita wallahi da kin sha wahala”

Minal ta karasa maganar tana hararar Kairat, kallonta mummy tayi “A haka Minal da wannan jiki” 

B'ata fuska Minal tayi “Oh Mummy har da ke ko?”

Da fata Mummy tayi “A a ina nufin kina da kiba”

 Ture hannun Mummy tayi ta nufi upstairs, Kairat da tsohuwa suka sa mta dariya har Mummy sai da tayi mata dariya sannan ta fice Kairat nayi mata Allah ya kiyaye,


      Haka suka cigaba da rayuwarsu cikin farinciki da kwanciyar hankali da kuma jindaďI, 

 Mummy tafi kowa farin ciki da daman haka take son ganin farincikin Minal shine kwanciyar hankalinta, yadda suke rayuwa yanzu har yafi na da kamar ba uwa da ya ba sai ka dauka kawaye ne ko kuma abokanin wasa tsakanint da Mummy har ma Kairat.




*I'm still on wattpad @khadeeja_candy*

_Don't forget to vote and comment_

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO...! 


        NA 


KHADEEJA CANDY 



BABI NA GOMA SHA HUDU___14



Wattpad @khadeeja_candy 



BAYAN WATANI UKU............ 

    A firgice Saif ya farka sakamakon ringing ɗin da wayarshi take, sai da ya ɗan murza ido sannan ya ɗauki wayar ya duba ganin bakuwar number yasa ya maida wayar mazauni ta ya juya ya cigaba da bachin shi, 

 yaji kiran yayi yawa sannan ya mika hannu ya ɗauki wayar ya danna picking ya kara a kunne, cikin murya bachi ya ce


“Hello” 


“Hello Saif how are you?” 


“I'm fine who is on the line.?” 


“Minal ce” 


Daga kwance da yake ya shafi kanshi, 


“Oh ya kike?” 


“Lafiya kalau” 


Sai da ya nisa sannan yace 


“Kina bukatar wani abun ne.?” 

 

Shiru ta ɗanyi, 


“Eh ina bukatar ganin ka idan kana free” 


Tashi yayi zaune


“Ok amman sai jibi nake free zan shigo idan na kare abun da nake” 


Cike da jindaɗi tace


 “Ok ba matsala @.?”


Sai da ya kalli a gogon ɗakin sannan yace 


“@9pm”


“Ok see you” 


“Alright bye” 


Ya kashe wayar yana sauke ajiyar zuciya, sai a lokacin yaji sarar da kanshi yake na farkawar da yayi a firgice. Ya ɗan daɗe zaune sannan ya sauko saman gadon ya nufi bathroom,


 kamin ya kai wayarshi ta sake yin ringing, da tsaki ya juyo dan a zatonsa Minal ce ta sake kiran, yana dubawa yaga PA ɗinshi nan yayi wurgi da wayar saman. Gado ya shiga bathroom ɗin, 


Bayan ya fito ya shirya cikin farar shadda da bakar hula da takalmi suma bakake, yayi kyau sosai haka ya fito kamar wani karamin saurayi, 


Keys ɗinsa ya ɗauka tare da waya ya saka aljihu ya fice,

  Hanyar downstairs ya nufa, kuskuskus ɗin da kunnuwa shi suka jiyo yana tashi ɗakin Huda ne yasa shi da wowa da baya ya tsaya daidai kofar yana sauraren su, 


   “Kawata kiyi amfani da wannan ance shi baya saka komai, kuma yana kariya sosai ba kamar wacan ba” 


“Yauwa ta waje na haka nake so na gode sosai wallahi, kinga wannan ai ya fiye min allura da magungunan gargajiyar nan dan ni ba yarda nake dasu ba sai naga ma kamar basa yi”


“Ai ki gwada wannan kawai yar gari, nima dashi nake amfani kuma har yanzu ban taɓa samun wata matsalar ba shiyasa ma nace bari kema na kawo miki” 


“Ai kuwa Wallahi kin kyauta na gode sosai Allah ya bar Zumunci” 


“Amin kinga bari na tashi kar mijinki ya dawo ya same ni yace kullum cikin yawon zuwa gidan ki nake” 


“Hahaha Saratu sarkin tsoro ai mijina bashi da wata matsala kiyi zaman ki mu sheki ayar mu” 

“A a kara dai na tashi, gidan su Hauwa nake son biya wa itama akwai nata sakon” 



Jin alaman fitowar ta yasa shi saurin komawa ɗakin shi, magana ɗaya da biyu da shiga masa yawo a kunne, _Ta fiye mata alura, ita bata son mai matsala_ me hakan yake nufi kenan?, Huda na shan maganin hana haihuwa ne ko kuma me? Wai shin mema wannan Qawar ta ta take yawan zuwa yi a gidan ne tun da gashi har ita da bakinta ta faɗa wai kar yace tana yawan zuwa gaskiya ya kamata ya bincika dan ga dukan alamu akwai wani abu a kasa, 


Hular shi ya cire ya dora saman mirror, sai kai da kawo yake cikin ɗakin saman gadonsa ya kwanta yana nazari da tunano wasu maganganun da kunnenshi suka jiyo masa, 

      

Bayan kamar mintuna arba'in ya tashi ya fito daga cikin ɗakin, daga bakin kofar ɗakin sa ya hango Huda zaune a parlor tana aikin data saba na kallo, 

 Hakan ya bashi damar wuce wa ɗakinta kai tsaye dan tabbatar da abunda yake zargi.


Bincike ya shiga mata kamar wadda ya bata ajiya, ya buɗa can ya buɗe can har jakar yan kullenta sai da ya zazzage, amman bai ga komai ba, 

  Har ya juya da nufin barin ɗakin sai kuma yaji a zuciyar sa da akwai wani abun, Wardrobe ɗinta ya nufa ya buɗe duk sai da ya zubar mata da tufafi kasa gurin bincike nan ma ba komai, 

  Kamar wadda aka tsakura sai kawai ya leka karkashin gadonta, akwati ya hango ɗan karama, da sauri yasa hannu ya janyo shi ya hau saman gadon ya zauna yana kokarin balle kwaɗo da aka rufe shi dashi, 


Yayi iya yinsa wajen ganin ya ɓalle kwaɗon amman abun yaci tura, hakan yasa ya buɗe wata yar durowa da yasan tana aje keys ɗinta,  gaba ɗaya ya kwaso so ya shiga gadawa, cikin sa'a kowa ya samu mai daidai da kwaɗon, jiki na rawa ya lakkama ya buɗe akwatin, 


Magunguna ya gani kala kala wadda cikin zan iya cewa har da na mata, ya mutsa ya shigayi kamar mai ɗatu, wani table naga ya ɗauko mai kananan ɗiya yana dubawa gaba da baya, 


Kai naga ya girgiza, ya tashi a fusace ya fice tare da maganin, 

Downstairs ya nufo tun kamin ya karaso ya kwala mata kira, 


“Huda minene wannan.?” 


Yanayin kiran yasa gabanta ya faɗi, ɗago kai tayi tana kallon shi har ya sauko, maganin ya watsa mata a jiki yana mata wani mugun kallo, 


Tana ganin maganin gabanta ya faɗi, sai a lokacin ta tuna da baya gidan toh yaushe ya shigo bata sani ba miya kai shi ɗauko wannan maganin bincike yayi mata kenan? Ko dai yaji abunda suka tattauna ne? Ba mamaki ma a fili na aje shi har ya gani, Wani rabon ido take tana mamakin lokacin daya shigo da kuma ganin maganin da yayi, cikin taku tace 


“Wai wannan kake magana? Jiya da qawata tazo ta manta dashi” 


“Ke karki raina min hankali wace Qawar ce zata shigo cikin gidan nan har tasa miki shi a akwati” 


Tashi tayi tsaye ganin yadda yake tada jijiyoyin wuya, ga fuskar sa ba rahama, 


“Saif Wallahi.. -” 


Kasa k'arasa maganar tayi sakamakon hannun daya ɗaga mata, 


“Bana son rantsuwa Huda kinyi matukar kaiwa karshe halinki ya isheni wannan wace irin rayuwa ce? Kinfi kowa sanin yadda nake son haihuwa amman kika ɗauki maganin hana haihuwa kika sha, for what.? Ance miki bana iya kula da yaran ne ko nace miki sunyi min yawa ne.? Ko kuma baki da lafiyar da zaki haihu ne?” 


Kasa bashi amsa tayi, zufa sai karyo mata take, abunka da marar gaskiya lokaci ɗaya ta zube kasan gwuiwoyinta  ta fashe da kuka, 


“Dan Allah Saif ka yafe min kayi hak'uri Wallahi kuskure ne” 


Hannayensa ya rungume ya ɗaga kansa sama, 


“Ban san mi yasa na fara son mace irinki ba Huda har ya kai ni ga Aurenki, bansan wace irin kalar mace bace ke komai naki ya banbanta dana sauran mata duk wata rayuwa da macen Aure take a gidan mijin ta ke baki yi, 

  Damuwar mijinki bata dame ki ba damuwar ki kawai kika sawa gaba komai sai kinga dama kike yi a gidan nan amman duk wannan bai ishe ki ba sai kin sha maganin hana haihuwa, wadda ke kanki kinsan zai iya haifar miki da matsala wai haihuwar ce baki so ko me?” 


Kuka take sosai tana tushe baki, 

“Indai har haihuwar ne baki so ba sai kin kara shan maganin ba ni zan ɗauki mata ki” 


Da sauri ta kalleshi, tana ganin juya ta rik'o kafarshi, 


“Dan Allah Saif ka yafe min karka aikata abunda zaisa mu shiga wani halin kafi kowa sanin halin dana shiga a baya bazan iya rayuwa ba kai ba Saif karka min abunda kasan zai iya zama ajalina Saif ina sonka” 


“Yes, kina sona Huda shine kawai abinda kika sani kuma kika iya dana taɓa ki kice kina sona sai yawan nuna kishi a kai na, amman duk abinda zai faranta min rai ruwanki dashi damuwa ta bata dame ki ba, 

Na gaji huda kalaman nan su nake ta maimaita miki kuma da bakinki kince bazaki iya chanja wa ba na ɗaga miki kafa dan haka zan ɗaga miki kafar daga yau” 


Yana kai wa nan ya fisge kafarsa ya nufi ɗakinshi, toshe bakin ta tayi yana matsar kukan daya zo mata, sai wani abu takr tana numfashi da karfi, da gudu ta tashi ta nufi ɗakinta.

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO...!


     NA


KHADEEJA CANDY



_I dedicated this page to my special good friend of mine, Sweetheart you can do it no wrong, my happiness is all yours._

      _More grace to your shining star's ROSE OKAFOR Rosy Lurv_


                  WATTPAD @khadeeja_candy 



BABI NA GOMA SHA BIYAR__15


Tana shiga ta faɗa saman gado tana kuka,ta tsora ta sosai da yadda taga Saif irin wannan ranar take gudu, daman hausawa suncd rana dubu ta ɓarawo,ɗaya ta mai kaya.

Wayarta dake saman kujera ta baɗo mata a rai,cikin rawar jiki taje ta ɗauka, ta shiga neman number Mummy. Sai da tayi mata kira biyu sannan ta ɗauka,


“Dan Allah Momi kizo gidan nan yanzu ki ceci raina”


Cikin kuka take maganar tana gurfane a kasa kamar mai rokon gafara. banji mi akace mata ba na dai ga tana girgiza kai


“Eh Momi Saki zaiyi dan Allah kizo yanzu”


Nan ta kashe wayar, ta faɗi kasan carpet gana kukan dake zuwa mata har cikin ranta, ko kaɗan Huda bata son taga Saif yayi fushi da ita, musaman yanzu da take fushin nashi har a fuska, Saif mutun ne mai hakuri duk abunda take masa yakan shanye ya kyale ta idan har taga fushinsa a fili toh lallai ranshi ya ɓace sosai.


Cikin mintuna Ashiri da wani abu Momi ta iso gidan,Huda najin tsayawar Motar ta ta fito da gudu daga ɗakin ta nufo downstairs, Saukowarta yayi dai-dai da shigowar Momi falo, faɗawa Huda tayi jikin Momi tana kuka


“Faɗa min mi kikayi masa miya haɗa ku?”


Momi sai Tambayar take abunda ya faru,ita kuma ta kasa magana sai kuka take, duk hankalin Momi ya tashi,


“Saif ɗin yana nan ne?”


Daker ta iya ɗagawa Momi kai sai wani kara narkewa take kamar wadda akayi mutuwa


“Saifullah! Saifullah!!”


Kira Momi take kwala mishi kamar zata tada gidan, 

Yana daga kwance ya soma jin kiran bai amsa ba dan bai ɗauka Momi bace duk da yaji kamar muryar ta, Sai da yaji kiran ya tsanan ta sannan ya tashi a kasale ranshi kuma aɓace ya nufi kofar fita,

  Tsaye Yayi bakin Stairs ɗin yana kallon Momi da ke lallasar Huda tana harararsa, haka ya nufo downstairs yana mamakin abunda ya kawo Momi yanzu a gidan dan ba kasafai take zuwan gidan ba. Wata zuciyar tace masa Huda ce ta ta kira ta, Baki ya ɗan tsosa a ransa yana zata iya tunda ba kunya ne da ita ba,


Har ya Karaso Momi bata daina Harararsa ba, cikin girmamawa ya gaisheta


“Momi ina wuni”


Bata amsa masa ba sai kawai ta haushi da masifa,


“Mi Huda tayi maka da zaka sake ta?”


Zaunawa yayi saman kujera yana maida numfashi, ganin hakan yasa Momi ta katsa masa tsawa kamar wani karamin yaro


“Ba da kai nake magana ba kayi min shiru ko nima shashancin zaka yi min?”


D'agowa yayi ya kalleta,


“Momi..-”


Sai kuma yayi shiru, Kallonsa Huda tayi da jajayen idanunta kamar munafuka wani ɓangare na zuciyarta tsoron abunda zai fito bakinsa take dan tasan Momi ma bazata raga mata ba sai tayi mata nata faɗan,

Ido cikin ido ya kalleta yana magana da Momi


“Momi matsalar mu ce da kika sani ta baya Huda ba zata taɓa chanajawa ba sam,nayi faɗa har na gaji bata ji ni kuma na gaji gaskiya da halinta kuma nasha faɗa miki tun baya yau ba”


Zaunar da Huda Momi tayi saman kujera sannan itama ta zauna tana kallonshi


“Saboda ba kasan Miye Aure ba ko? Shiyasa kake son saki a rayuwar ka nayi bakin cikin jin haka daga gareka Saifullah ban taɓa sanin cewa bakan mutucin Aure ba sai a yau,

Duk abunda zaisa Namiji ya saki matarshi Babban abun ne, Amman kai ka ɗauke shi ba komai ba miyasa kake son maida kanka wani irin kalar mutun ne?”


Gashin kansa ya shafa daman yasan indai faɗa ne sai Momi tayi masa musamman yanzu da take ganin Huda bata daɗe da dawo ba. ɓangaren Huda kuma daɗi takeyi tana hamdala da Saif bai faɗi dalilin faɗan nasu ba, ita kanta tasan tayi sa'ar miji dan ba kowa ne Namiji ne zai iya ɓoye sirrin matarsa ba, duk da a koda yaushe Iyaye sukan faɗa mana idan faɗa ya shiga tsakanin ka da Iyalinka toh ka barshi tsakanin ku, dan idan kuka faɗa ma Iyaya koda ku kun shirya kanku ko an shirya ku zaku iya manta abun ammman Iyaye basu manta ba.


A hanlaki ya furta,


“Momi bafa sakin ta zanyi ba kawai ina bata tsoro ne wasa nake mata”


Nan Momi ta saki baki


“Wasa kuma au shi sakin har wasa ake dashi? kasan mi kake faɗa?”


Salon faɗan da take masa sai ya chanja, Shi dai kanshi na kasa har tayi ta gama sannan ya shiga bata hakuri


“Naji duk abunda kika faɗa Momi kuma hakan ba zai sake faruwa ba In'sha Allah Allah ya huci zuciyar ki”


Tashi tayi tana faɗin,


“Kowa dai yayi na gari dan kansa kuma duk abunda kayi wa yar wani sai anyi ma taka, ya dai kamata kayi ma kanka faɗa kasan ciyon kanka ka rika Y'ar mutane da mutunci ba ka wulakanta ta ba”


Juyowa tayi gurin Huda,


“Ke kuma duk abunda kika san yana kawo miki matsala da mijin ki ki daina ki guji ɓacin ransa idan zaki iya kunga tafiya ta”


Bata tsaya jiran mi zasu ce ba tayi tafiyar ta suna mata a sauka lafiya,

Bayan Fitar Momi Huda ta nufo Saif da nufin masa magana ,sai kawai taga ya tashi tsaye yasa hannayensa aljihu ya nufi upstairs,

A hankali ta jingina da kujera tana kallonsa har ya shiga bedroom ɗinsa.


Yana shiga sai yaji duk wani haushi na Huda da yake ji ya karu, ba damar ya sake mata faɗa yasan kiran Momi zatayi ta faɗa mata shi kuma sam baya son Momi taga kamar bai ji maganar ta ba. Can guraren Azahar ya shirya cikin manyan Kaya ya ɗauki makulin motarsa ya bar gidan.




                    *****    *****    *****

Bai shigo ba sai dare. a falo yaci karo da ita kwance saman doguwar kujera sanye da wata rigar bachi mai ɗaukar hankali, baibi ta kanta ba duk da tayi masa sannu da zuwa, haka ya nufi ɗakinsa ba tare daya amsa ba.



WASHE GARI.................

Tun takwas da rabi ya bar gidan dan kwata-kwata baya son huda ta sashi a ido danshi fushi yake da ita bilhakki.

Huda kan bata ma san fitarsa ba dan bata tashi ba sai goma na safe, tana tashi ta nufi kicin ta haɗa masa karrin kummalo dan a zaton ta yana nan tunda bai saba fita da wuri ba. Bayan ta kare ta nufo ɗakinta tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga ta feshe jikinta da turare, sannan ta nufo ɗakinsa,

 Haka ta fito sululu kamar hawainiya ta koma ɗakinta idon cike da ruwan hawaye, Tana shiga ta faɗa saman kujera tana share hawaye, wunin ranar wuni tayi cikin ɗaki, Sai kusan La'asar ta fito koshi dan yuwar da taji tana matsa mata lamba ta nufi dinning,ruwan tea ɗazun ta zuba tasha ta sake koma wa ɗakinta.



                        ***********

Saif bai shigo gidan ba sai da ya tabbatar da ta isa yin bachi, rashin ganinta a falo ya tabbatar masa da hakan. wutar falo ya kashe ya wuce ɗakinsa,

      Washe gari ma haka yayi mata koda ta tashi ya ficewarsa duk da yake ta tashi da wuri yau, abunka da wadda bai saba ba sai duk tabi ta shiga damuwa, sam baya son Saif ya fita safgarta dan ya riga ya saye mata jiki da zama tare dashi,daga iya zuwa yau duk ta wani chanja ta koma wata kala har da yar ramar rashin cin abincin da take dan iya karta ruwan tea, 

Tunani take tayi yadda zata filloma lamarin, Dan tasan haka ɗin da Saif yake mata ba karamin fushi yake da ita ba, kuma shawo kansa sai ta shirya, bayabda saurin fushi kan amman kuma idan yayi yayi kenan sai kuma wani ikon Allah.




                          *****  *****  ***** 


                                MINAL............


K'is! k'is!! k'is!! kake ji taunar cingan ɗin da Minal take tana danne-dannen wayar dake hannunta, Kairat na zaune kusa da ita tana rubuce-rubuce jin abun yayi yawa yasa taja tsaki,


“Haba Minal dan Allah ki jefar da cingan ɗin nan tun ɗazu kin damu mutane da taunar cingan kamar wata tsohuwar karuwa”


Harara Minal ta watsa mata,


“Wadda ya raina tsayuwar wata a hawa yake ya gyar idan zai iya ko idan kuma bazai iya ba sai ya zuba ido”

Kairat zatayi magana Talatu ta shigo Gardem ɗin tana faɗin 


“Minal ga abokin ki can harabar gida yace a kira ki”


Da sauri ta tashi tana faɗin,


“Toh nama bar miki wajen ci tsinci abinda zaki tsinta”



Tsaye ta tararda shi jikin Mota yana dannar waya, Rumgume shi tayi kamar yadda ta saba,


“I miss Deen?”


Lumshe ido yayi naɗan mintuna ya buɗe ya shafa kanta,


“I miss you too Deen you look so pretty”


Murmushi tayi ta sake shi,


“Thank you ina ka fito?”


“Gida nayi miss ɗin fita dake ne kwana biyu bamu fita ba”


“Oh Deen shekaranjiya fa muna tare”


“Eh but a gida ba waje ba yawo fa nake nufi”


Hannayenta ta ɗaga sama 


“Fine indai wannan ne karya dame ka shiga mota muje indai yawo ne”


Murmushi yayi ya buɗe Motar ya shiga, ita kuma ta zagaya mazaunin gaba ta shiga ya kunna motar suka kama hanya.




#Oneheart

_SHOW ME WHAT I WANNA SEE  YOUR VOTE AND COMMENT AND DON'T FORGET TO SHARE_

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO...! 


          NA 


KHADEEJA CANDY 



_Another one for you ROSY LURV my shinkafa jallof_


               WATTPAD @khadeeja_candy 



BABI NA GOMA SHA SHIDA__16



Basu dawo gidan ba sai bayan Isha'i, da sauri ta fito Motar ta tana masa sallama ta shiga gida.

 Yanayin yadda ta shigo yasa Kairat da tsohuwa dake zaune falo suka tsora ta, Kairat ta dafe,

 

“Oh Sister miye haka dan Allah zaki shigo ba ko sallama ji duk yadda kika tsorata mu”


“Mtwsss, toh idan kun tsorata sai what ni banda lokacin ku”


Bata tsaya jiran abunda Kairat zata ce ba ta nufi Upstairs da gudu, Tana shiga ta cire kayan dake jikinta ta ɗaura tawul ta shiga banɗaki, cikin yan mintuna tayi wanka tare da alwala ta fito.

 Wani ɗan karamin tawul ta janyo ta shiga goge jikinta, a gaggauce ta nufi gaban madubi ta shafa mai, bayan ta kare ta ɗauki wani zane tare da Hijab ta saka ta shiga Sallar magariba da Insha'i,

    Tana karewa ta nufi wadurof ta ɗauki wata Night gown ta saka black colour, ta dawo gaban madubi ta shiga gyara gashin kanta, gafe ɗaya tayi da gashinta ta kala masa wani ɗan farin abu tare da ribon, sannan ta ɗauki hoda ta shafa bayan nan bata shafa komai ba sai man baki.


Black Tom's ta ɗauko tasa bayan tasa awani kyakkyawan agogon hannu,

shikan turare bansan iya adadin da ta saka ba, ta daɗe tana kallon kanta a madubi sannan nufo downstairs. Talatu ce ta fara yi mata magana


“Masha Allah Minal kinyi kyau”


Murmushi Minal tayi tayi mata godiya, Tsohuwa ma ta kalleta gana murmushi bata ce komai ba,


“Koma baki ce nayi kyau ba nasan nayi”


Minal ta faɗa tana kallon Tsohowa, dariya Kairat tayi


“Wallahi kuwa Minal kin kyau sosai”


“Thank you sister karku cinye ni”


Dariya sukayi har ita,nan ta zauna suka dasa fira cike da nishaɗi duk da zuciyar ta ta tana can wani guri,




                               SAIF.................

Kwance yake rairai saman gado, idonsa a lumshe kamar mai bachi ya rumgume hannayensa a kirji yana sauke a jiyar zuciya,

Can kuma ya buɗe ido ya tashi zauna yana duba a gogon hannunsa goma da rabi ya gani, tsaki ya ɗan ja ya tashi tsaye yana mika ya fice.



Zaune take cikin ɗakinta tana rera kuka a hankali kamar karamar yarinya, can kuma taga abun bayayi ta share hawayen ta, ta tashi ta ɗauki makulin Motar ta nufo downstairs, takun tafiyar talkaminta yasa Kairat ta lekowa daga ɗakinta, kamin ta karasa sauka Kairat tace,


“Bai zo ba ko?”


Tsayawa tayi Cak ba tare data juyo ba tace


“Eh kuma kinsan babu abunda na tsana irin Disappointed”


Busar da iskar bakinta Kairat tayi,


“Toh yanxu ina zaki?”


“Clup”


A takaice ta bada amsa still bata juyo ba, Kairat batayi unkurin hana ta duk da bata jidaɗin zuwan da zatayi ba, Sai ma rakata da tayi. bakin kofar falo ta tsaya yana kallonta har ta tada motar ta fice.


Dawowa Kairat tayi cikin falon ta zauna, ta ɗauki rimot ta danna Zeeword. bata daɗe da zaman ba taji ana buga kofa, banza tayi sai da taji an sake bugawa sannan ta tashi ta buɗe, Saif ta gani tsaye jikin kofar hannayensa sanye cikin vaki ya gumɗe baki, kofar tsaki tana kallonsa


“Sannu da zuwa”


Kai ya ɗaga mata,


“Ina Minal.?”


Bai bata amsa ba ya sake yi mata tambayar


“Ina Minal?”


“Ta gaji da jiranka yanzu ta fita”


“Ta fita? Ina taje?”


Ya tambaya yana mamakin fitar ta yanzu cikin dare tana mace,


“Club”


Kairat ta bashi amsa,


“Club”



“Daman tana zuwa Club ne?”


“Eh can ne gurin zuwanta musamman idan tana cikin bacin rai”


Ya mutsa fuska yayi,


“Wane Club.?”


“Club ďin take haďe da hotel ďin City People”


Bai Sake cewa komai ba ya buďe Motarshi ya shiga. Kairat na tsaye tana kallonshi har ya bar harabar gidan.



                        ***********************


Tana isa ta nufi gurin kar6ar tiket kamar yadda ta saba, bayan ta kar6a ta kunna kai cikin Club ďin. Guri ta samu ta tsaya tana kallon mutanen dake kai da kawo cikin Club ďin, bata jin shiga can ciki yau hakan yasa ta jingina da jikin ginin gurin tana wasa da makulan dake hannunta,


Ta daďe a haka sai da taji wakar Rihanna ta tashi _We Find a Love_ Sannan ta ďago da niyar shiga cikin hall ďin sai kawai taji an fisgota da wani irin karfi har sai da bangaji wani akayi waje da ita, Sai a lokacin ta kalli fuskarshi cike da mamaki tace 


“Omg kardai kace min kai ma kana zuwa nan”


Hannunta kawai yaja, bai tsaya ko ina da ita ba sai gurin da yayi farkin ďin Motarsa, bayan ya sake mata hannu ya haďe fuskarsa,


“Miya kawo ki Club Minal.?” 


“Just to have some fun”


“Fun?”


Ya faďa yana mamakin abunda ta furta,


“Did you hear yourself.? a nan zaki samu Fun Minal kina musulma ďiyar musulma.

 idan har wani abun ne yake damunki ai sai ki ďauki Qur'ane ki karanta amman miye Amfanin zuwa Club kina mace musulma kuma cikin dare.?”


Busar da iskar bakinta tayi tana soshe-soshe, yana son kawar da maganar


“You know what yunwa nake ji sosai bari naje gida”


Tana juyawa ya katsa mata tsawa,


“Shiga Mota zamu yi magana”


kallonsa tayi 


“Nace maka ina jin yunwa ina son naci wani abu” 


Ido ya zaro mata,


“Do as i say”


Da sauri ta nufi Gaban motar ta shiga, dan tsorata da yadda ya ďan zare mata idon da yayi. sai da ta shiga ta zauna sannan shima ya shiga, ba tare daya kalleta ba yace


“Mi yasa kike son ganina?”


Kallonsa tayi,


“Nace maka ina jin yunwa”


“Mi yasa kike son gani na bani amsa”


Jim tayi kamar ba zatayi magana ba, can kuma ta murza hannunta


“I just miss you and..-”


Sai kuma tayi shiru, kallonta yayi


“And what.?”


“Ba komai amman daga zuwan ka sai min tsawa kana min faďa bayan ni babu wadda yakr min haka”


Ido yatsa mata yana kallon fuskarta, ta wani mararaice tana son maida kwallar data zubo mata, murmushi yayi yana mamakin yadda Minal take ďaukar kanta karamar yarinya, gatane yayi mata hawa ko tsabar iskanci ne? tambayar da yayi ma kansa kenan still yana kallon fuskar ta, ta wani turo baki tana sharar kwallah kamar karamar yarinya, murmushi ya sake yi a karo na biyu ya rufe motarsa ya tada,


Fita yayi daga harabar Club ďin gaba ďaya ya nufi wani ristoran dake kusa da gurin, yana yin fakin ya buďe Motar yana faďin


“Fita muje”


Banza tayi masa har ya fita daga motar, sai da taga sai da taga ya buďe ganbun ristoran ďin sannan ta fita ta rufa mishi baya,

Koda ta shiga har ya kama gurin zama, dube-dube take har ta hangoshi, gurin ta nufa,

zaman ta yayi daidai isowar mai wani ma'aikacin gurin,

A hankali Saif ya kalleshi 


“Cope only”


Juyowa yayi gurin Minal


“And you Mrs?”


Kallon Saif tayi suka haďa ido, ko wane fuskarsa ba yabo ba fallasa, ďauke idon ta tayi ganin shi yaki ďauke nashi idon tace da mutunen,


“No need”


Kai ya gyaďa mata, Bayan ya wuce Saif ya kalleta,


“Amman kinsan saboda ke nazo nan ko? ke kika ce yunwa kike ji”


“Yes ina jin yunwa amman ba zan iya cin abinci a nan ba”


“Why?”


“Because I'm human”


Kallon mutane dake gurin yayi,


“Su kuma waďan nan mutanen fa?”


“Ba mutane bane”


“And me?”


A nan ta ďanyi murmushi,


“You are human too”


Fuskarsa ya shafa har zuwa saman kansa ya ta6e baki,


“Maybe i m not dan banga banbancina da mutanen da suke wannan gurin ba”


Murmushi tayi mai sauti,


“If not toh miye kai?”


Kafaďunsa ya ďaga


“Ban sani ba nima what i'm?”


Yanayin yadda ya mayar mata da tambayar yasa ta dariya, dariyarta yasa duk mutanen da suke gurin hankalinsu ya dawo gare ta, da sauri ta rufe baki tana matse dariyar,


“What is funny.?”


Saif ya tambaya,Cikin dariyar tace


“You are such an angle Saif”

Lumshe ido yayi ya buďe


“Angle Minal kinsan abunda Angle yake nufi kowa?”


Dai-dai lokacin mutunen ya iso, tashi Saif yayi tsaye ya ciro kuďinsa ya ďora saman tebur ďin ,


“We all done here”


Ganin hakan yasa Minal tashi tana wani abu da baki, 


“Minal...”


Daidai lokacin da suka kai bakin kofar fita akayi mata kiran, tare suka juyo, suna kallon wadda yayi mata kiran, yana karasowa kusa dasu sai kawai ya mika mata hannu,


“Hi Minal”


Da far'ah tace


“Isma'il”


Zata mikasa hannu Saif ya rike ya mika masa nashi, Kallon Saif mutunen yayi kamin ya sake kallon Minal yace 


“You look so cute”


Kamin ta amsa Saif ya tigata,


“Thank you”


Ya fisgi hannunta suka fice daga gurin, Bayan sun shiga Mota ya kalleta yace


“Wanene wannan Minal?”


“Yayan wata friend ďita ce”


Ya kunan motae yana faďin 


“Na ďauka shima abokin ki ne kamar Deen”


“Deen is my best friend ever”


“Tell me something about Deen”

Murmushi tayi,


“Deen mutun ne mai kyau hali yana da amana gashi da hakuri ga kawaici”


“Ya akayi kika haďu dashi”


“Why you ask me?”


“Nothing just”


“Naje karatun faransanci a faransa a lokacin muka haďu dashi class ďin mu ďaya dashi kuma gurin zaman mu ma ďaya  gashi kuma kasar mu ma ďaya hakan yasa muka shaku dashi yana so na sosai yana nunamin kulawa, sai kuma wata kawar tawa Sarah ita kan bafaranshi yace yar faransa mu uku ne kawayen juna,

  bayan mun kare makaranta muka zama AMINAN JUNA har ďayan mu baya iya siyen abu bai saya ma đayan ba a haka muka mua haďa kuďi muka siye gida a New York lokaci lokaci mukan je hutu a can, da muka dawo na nageriya sai shakuwar mu da Deen ta karu”


Tana kaiwa nan ya sauke ajiyar zuciya, yace


“Wace Hotal kike son ki ci abinci?”


“Hotal mafi tsada”


Shiru ya ďanyi kamar mai tunani sannan ya kara gudun motarsa,


Sha biyu saura kwata yayi fakin gidansu Minal. cike da jindaďi ta fita motar ta shiga cikin gidan, shi kuma ya kama hanyar gidansa,

   Koda ya Isa sha biyu da shirin, yana fita motar ya nufi cikin gidan, tunane-tunane, Yana tura kofar Falon Huda ta tashi tsaye Fuskarta shakaf da hawaye, tsayawa tayi tana kallonta. ita kuma ta nufo tana kuka ta kamma hannunshi ta rike,

  Wani kallo yake mata wadda ba zan iya cewa ga fassarar sa ba, can yace 


“Baki bachi ba?”


Kai ta ďaga masa dan bazata iya magana ba, janta yayi ya rumgume nan ta kara fashewa da kuka,

 Sunyo minti biyar a haka sannan ya ya zauna saman kujera rike da ita, sai da ta tsagaita kukan sannan ya dago kanta yace


“Baki yi bachi ba?”


“Ya za'ayi na iya bachi bayan ka fita tun wuri baka dawo ba sai yanzu kuma nasan duk saboda ni ce kake haka Dan Allah Saif ka yafe min zan iya jure komai amman banda rashinka karka min horon da zai cutar dani ko Allah mukayi ma laifi yana yafe mana dan Allah kayi hakuri Saif”


Kanta ya shafa, yana sauke ajiyar zuciya


“Na yafe miki Huda amman karki kara”


“Da gaske?”


Hancinta ya lakata,


“Na saba yi miki karya ne?”


Murmushi tayi ta girgiza kai da jajayen idanunta ta koma kirginsa ya rumgume ta.




        WASHE GARI.....................

Tare suka haďa kayan kari, cikin farinciki da jindaďi ,musamman Huda dan nata baya misaltuwa daman haka take so, shi Kuma Saif ya sake jiki kamar babu abund ya ta6a shiga tsakaninsu. bayan sun karya ya shiga ďakinsa  yayi shirin ofis.har gurin mota ta rakashi, ya fice tana ďaga masa hannu.



Uku da yan mintuna ya tashi daga ofis ďin, bai zame ko'ina ba sai gidansu Minal, Dr. Salamatu tayi mamakin ganinsa tana tunanin abunda zai kawo shi gidan yanzu,

    Da far'ah ta tar6e tasa aka kawo masa drink, Kaďan ya kur6a ya kalleta


“Wata magana nake son muyi dake idan ba damuwa”


Kai ta ďaga masa,


“Babu komai Saif ina sauraren ka”


“Mi yasa kike kyale Minal tana taka rawar da taga dama?”


Bugun zuciyar ta ne ya karu, daman can jikin yana bata akwai wani abinda ya kawo shi gidan,


“Saif ina tunanin Minal ko abunda ya shafe ta yana tsakanin ni da ita ne”


Yi yayi kamar bai jita ba ya sake jefa mata wata tambayar,


“Baki tunanin abunda ya faru da ke zai iya faruwa da ita? ace tana y’a mace amman taje wani gurin ta kwana, tayi shigar da duk tga dama har Club take zuwa kuma duk a tana musulma ďiyar musulma ? yanzu kina ganin gatane kike nuna mata ace ta bar kuma ba zata dwo ba sai taga dama wace amsa zaki bawa Allah idan ya tambaye akan tarbiyar ta?”


Kawar da fuska tayi, cike da sanyin jiki


“Saif bani da yadda zanyi ne duk lokacin data fita hankalina a tashe yake har sai naga ta dawo”


“Kuma ba zaki iya hana ta ba ko?”


“Ba zan iya hana ta ba Saif  bana son abunda zai 6ata mata rai”


Kai ya jinjina,


“Lallai Annabi yayi gaskiya daman yace karshen duniya kuyanga zata haifi uwar gijiyar ta”


Jin motsin ta6a kofa yasa tayi saurin share hawayenta. Minal ve ta shigo Falon sanye da dogon wando da wata yar t-shart fara marar hannu sai wata riga mai kamar ta sanyi data ďaura a kugu, tayi fakin ďin gashin kanta guri ďaya hannunta rike da magazin.

     Tana ganin Saif ta karasa gurin tana murmushi, kusa dashi ta zauna 


“Sannu Saif yanxu kazo?”


“Eh yanzu na zo”


Ya bata amsa yana ďan kirkiro murmushi, juyowa tayi ta kalli Mummy tare da mikaata magazin ďin, da murmushi ta kar6a ta shig dubawa, kamin ta ďago kai ta kalleta


“Oxford University Minal?”


“Yes Mummy ita nake son junawa makarantar tana da kyau sosai  ki shiga online ki gani”


Cike da damuwa Mummy tace,


“Minal ba zaki tsayar da karatun nan haka nan ba?”


Dariya tayi,


“Mummy idan banyi karatun nan ba mi xanyi?”


“Aure mana” faďar Saif dake gefenta, Mummy ta ďaga kai 


“Haka ne Minal kiyi aure zaifi karatun nan kinga hankalina xai fi kwanciya”


Tashi tayi ta koma kusa da Mummy ta zauna,


“First i want you to know that a m old enough to know what I want or is good enough for me to Mummy karatun nan shi nake so kuma shine abunda tafi dacewa dani kuma mummy karki manta kema karatun nan kikayi har ika kawo inda kike yanxu har kike yi min gata and Mummy everyone has got the right to decide his own destiny”


Shiru Mummy tayi, Saif zaiyi magana ta tari numfashinsa,


“She is right Saif she old enough to decide her future”


“A wace aya ko hadisi.?”


Duk kallonshi sukayi ganin yadda ya jefo musu tambayar, Minal tace


“Saif muna maganar rayuwa ne”


“Rayuwa babu ska addini a ciki ? mi kik ďauki kanki ne sak tufafin da zasu fitar miki da tsiraici da zuwa club ko kwana wajen gida shine rayuwa? duk wani abunda Allah yace baki yinsa kin đauki rayuwar turawa kin makkalawa kanki abun kunya abun bakin ciki kina yar musulma”


Wani irin baci ran minal yayi, na take ta zaburo masa,


“Haka nake so kuma bazan chanja ra'ayi naba dan bazan bi ra'ayin kowa ba”


Tashi yayi tsaye yana nuna ta da hannu,


“Tirrrr dake Minal Tirrr da mai hali irin naki kin kaskanta kanki tunda kike koyi da kafirai ina son kisani duk abunda kake so tare dashi zaka tashi ranar alkiyama kuma duk abunda ka mutu kana aikatawa akanshi zaka tashi ranar lafira”


Hawaye ne suka wanke ma Minal fuska, lallai BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE idan ba Saif ba waya isa ya tsaya gaban Minal ya faďa mata waďannan kalaman? wani kallo take masa ta rasa abunda zata ce masa dan ya riga ya gama da ita,

   Ganin haka yasa Dr.Salamatu ta kalli Saif,


“Saif wannan ba..-”


Hannu na ďaga mata,


“Excuse me Dr. Salamatu dole ne ki faďa mata gaskiya dolene ki faďa mata abunda musulunci ya shar'anta mata dan musulmace ita ma ba ki kyale ta tabi son ranta ba, idan kuma ba zaki iya ba toh ki barni ni na faďa mata”


Da gudu Minal ta nufi Upstairs tana kuka, ta shige ďakinta, Saif ya kalli Dr.Salamatu,


“Ban san abunda yasa kika nuna ma Minal gatan da babu wadda ya isa ya tsayafaďa mata gaskiya ba”


Komawa tayi ta zauna saman kujera tana sauke ajiyar zuciya,


“Saif ban ta6a faďa maka wani abu game da Minal ba, Saif Minal ba ba ďaya take da sauran mutane ba”


Kallon rashin fahimta yayi mata,


“Kamar Ya.?”




_GHOST READER'S PLEASE_ 

    _VOTE! VOTE!! VOTE!!!_

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO...!


      NA


KHADEEJA CANDY



WATTPAD @khadeeja_candy



BABI NA GOMA SHA BAKWAI___17


Shiru Mummy ta ďanyi, sannan tace “Saif Minal tana da cutar sikila da ita aka haife ta  shiyasa kullum cikin rashin lafiya take, idan ka lura haka jikinta yake bata kiba kuma abu kaďan ya isa yasa ciwon ta ya tashi.

Saif duk mai cutar Sikila in har sun rayu sun girma basa wuce shekara 25, Shekarun Minal 23 a duniya, Saif bansan ta rai ba amman Minal tausayi take bani gashi ita kaďai na haifa bani da kowa sai ita idan ban barta tayi yadda take so ba sai naga kamar na cutar da ita .zuwa zuwa nasan wata rana za'a wayi gari ba ita....- ”


Kuka ne ya ci karfinta ta kasa karasawa, Lumshe ido Saif yayi cike da tsumayi, can kasa kasa ya sinkayo muyar Dr.Salamatu tana cewa,


“Ba a nan kawai a abun ya tsaya ba Minal tana da blood cancer Kuma kasan blood cancer bazai ta6a fita ba har sai an chanja jini, gurin chanjin jini kuma mutun zai iya rasa ransa dan babu tabbas ko zai rayu.Saif bazanbiya hana minal abunda take so ba koda raina take so ba zan iya hana ta ba matukar yana sata farinciki ina fatar ka fahimce ni”


Bai ce da Mummy komai ba dan baya jin akwai abunda zai iya furta mata a yanzu, tshi yayi tsaye tare da saka hannayensa aljihu, ya nufi kofar fita,

  Jinginawa Mummy tayi jikin kujera tana kallon Saif har ya fice, sannan ta sauke ajiyar zuciya ta share hawayen da suka zubo mata,



                       **********

Har ya isa gida tunanin maganar da Mummy ta faďa masa ta Minal yake, Tabbas Minal abar tausayi ce amman wannan ba zai zama dalilin da xai sa mummy ta rika kyaleta tana yadda take so ba.

   

“Sannu da zuwa Dear”


Cike da fa'ah ta tar6eshi dai-dai lokacin daya kawo baki qafar falo. Da murmushi ya amsa,


“Yauwa sannu wannan kwaliyar fa?”


Fari tayi da ido, ta kar6i makulin motar dake hannunshi


“Kai akayi ma. Muje kayi wanka muci abinci”


Ba musu suka nufi Upstairs tare, har ďakinsa ta rakashi ta taya shi cire kayan jikinsa ya ďaura tawul ya shiga wanka,

   Ita kuma ta buďe waduraf ďinsa ta ďauko masa janabiya da guntun wando ta ďora masa saman gado sannan ta fice ta nufi dining tana shirya kwanukan abincin.



                           ****** ****** *****



    Zaune suke falo, tana kwance saman jikinsa yana wasa da yatsun hannunta. Kallo ɗaya zakayi mashi kasan hankalinshi baya gurin, dan idonsa ma ba akan tv suke ba.

   Bugun kofar da akayi ne, ya ďago hankalinsa zuwa gurin kofar. Huda kan yin tayi kamar ba taji ba daman can haka halinta yake indai akan bugun kofa ne. Sai tayi banza da mutun sai yayi ya gaji sannan ta buɗe. irin matan nan ne masu wulakanci da kyaluwa, (Iri Mrs J Mood 😜).


   Yunkurin tashi yayi da nufin zuwa gurin kofar, da sauri ta rike masa hannu


“Ina zaka.?”


“Ba kiji ana buga kofa ba?”


“Naji mana ka kyale ko wanene har sai munga damar tashi mana”


“A'a idan ba zaki ba ni bari na duba”


“Zauna bari na duba ďin”


Tashi tayi ba dan taso ba, ta nufi kofar. A fusace ta buďe da nufin yima ko wanene masifa, sai kawai taga Budurwa tsaye cikin doguwar rigar atamfa da gyale.


“Sannu”


Kairat tace da ita. 

Wani kallo Huda ta watsa mata tun daga saman ta har kasa, bata ga alamun talauci ko makamancin hka a tattare da ita ba,  tun daga kan tufafinta Juwa halittar jikinta hakan yasa batayi gaggancin faďa mata wata banzar magana ba. Tun da  batasan ko wacece ba sai kawai ta ďauke kai tace.


“Wa kike nema.?”


“Saif. yana ciki?”


“Wacece ke.?”


“Sunana Kairat Ibrahim Ahlam”


_Ibrahim Ahlam_ a zuciyarta ta maimaita sunan. tasan waye Ubanta koda bata san wacece ita ba. fitattacen mai kuďi kuma sanannen ďan siyasa mai faďa a ji cikin najeriya,


“Saif nake nema nace yana ciki.?”


Ganin yadda ta tsaya kallonta yasa Kairat, maimaita mata tambayar. Juyowa Huda tayi gurin Saif,


“Dear. kasan Kairat.?”


“Kairat.?”


Da karfi ya zaburo, jin ta ambaci Kairat, ya nufi kofar. 

Mamaki ne ya kamata ganin yadda ya kar6a sunan ya kuma nufo kofar jiki na rawa.

    Yana isa, ya kara buďe kofar yana faďin,


“Kairat shigo mana”


Sai a lokacin ta ďanyi murmushi, ta tako kafarta ta shigo cikin falon, wani 6angare na falon ya nufa da ita, ya nuna mata kujera


“Zauna ina zuwa”


Zaunawa tayi tana karewa hotunan su dake manne kallo. Wani gurin yana rik'e da Huda wani gurin kuma suna manne da juna, har ma da inda yayi mata kiss. 

Haka nan sai taji wani irin, duk bata jidaďin ganin hotunnan nasu ba. _Ko miye dalili oho!_

   

     Da kansa ya ďauko mata abun sha da cup, ya dire mata, sannan ya zauna a kujerar dake fuskantar, ta ya sakar mata manyan  idanunsa dake kwance da wasu ruwa saboda fari.

    

   Tsif falon yayi Huda na can daga zaune can gefen tana satar kallonsu. Kairat kuma tun lokacin data zuba drins ďin ta maida kanta kasa,  

Saif kuma jiran yake ta fara masa magana dan yasan bazai wuce abunda ya faru tsakanin su da Minal ba daman hankalinsa ya kasa kwanciya tun lokacin da ya baro gidan, ganin ya saka Minal da mahaifiyarta kuka.


  Kairat. Sai da tasha lemun sannan ta kalleshi cike da nauyin ido,


“Saif. Naje gidanku akace nazo nan, na tararda kai tare da iyalanka kayi hakuri da takurawar da nayi maku”


Murmusawa ya ďanyi ya shafi dogon hancinsa,


“Ba komai what is important now you are here”


“Saif. I want to talk to you about what you say to Minal earlier”


Gyara zamansa yayi, ya tattara hankalinsa ya mika mata, yana kallonta cike da natsuwa.


“All my ears Pretty Kaiyrat”


Har cikin jijiyar jinin zuciyar ta taji kiran sunan nata da yayi, wata rahama ce ta rufe mata jiki sai taji kamar babu wadda ya iya kiran sunan nata daďi irinshi.





```Don't forget to Vote Comment and share.



#KhadijaAbubakarAlkali

#OneheartOnelove```

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO. 


       NA


KHADEEJA CANDY 


Candynovels.wordpress.com 


WATTPAD @khadeeja_candy 



_Masu cewa idan ba zan karasa ba na faďa da masu cewa sai an manta page nake typing da masu cewa yanga nake kuma bana yi da yawa duk kuyi hakuri dani bana da time ne sosai shiyasa, LOVE YOU ALL._



BABI NA ASHIRIN__20


Sai ya tabbatar da hankalinta ya kwanta sannan ya ďago ta yana faďin,


“Kar fa kiyi bachi nasan halinki Yar baby”


Dariya tayi ta kallesa,


“thanks for your caring”


Murmushi yayi mata,


“It's my pleasure”


Ya sake ďaga kai ya kalli windo sannan ya juya yana faďin,


“Tunda kin hakura bari naje gida ki gaida min da Dr.Salamatu”


“Ai da ka shiga ka gaishe ta”


“A a wannan zuwana naki ne bana kowa ba sai dai wani lokacin Ki gaida min da Kairat”


Dariya ta sake yi cike da jindaďi ta mika hannu ta riko hannunsa,

Bai yi unkurin hana ta ba har ya kai gurin da ya faka motarsa. Sai da taga zai shiga sannan ta sakeshi fuskarta shimfiďe da murmushi.


Tsaye tayi tana kallonsa har ya fice sannan ta juyo ta shiga falo cike da nishaďi,

    Kai tsaye upstairs, ta nufa hannunta a baki kamar irin yarinya, 


“Kairat”


Ta kira sunan ta tana kokarin buďe kofar ďakin.

 Da sauri Kairat ta share hawayen dake idonta ta kalleta tana murmushi,


“Na'am sister”


Kusa da ita ta zauna, tana murza ďan hannunta.


“Yanzu ya tafi ya bani hakuri kuma yace na gaishe ki”


Murmushi tayi ta rika fuskar Minal,


“Yanxu kin hakura ko komai ya wuce?”


“Eh man tunda ya bani hakuri ai na hakura”


“Uhmmm amman ni da Mummy babu yadda ba muyi dake ba kika ki hakura”


“Ai toh ai shine ya 6ata min rai kuma yaban hakuri kinsan shi na daban ne”


Kairat ta haďe yawun dake bakinta, ta sake mata hannaye


“Toh yanxu hankali ya kwanta”


“Yes Sis”


A nan ta tashi tana murmushi ta nufi hanyar ďakinta.

  Ajiyar zuciya Kairat ta sauke ta kwantar da kanta saman filo ta lumshe ido, tana numfashi a hankali.


Minal tana shiga ďakinta ta faďi zaune saman kujera tana murmushin da ta kasa dainawa tun ďazu, 

  Kalma ďaya zuwa biyu ta hana mata sukuni.  _Ina kinshinki ina bacin ciki wani namiji wadda ba muharraminki ba ya kalli surar jikinki_ me yake nufi ne.? Miyasa yake kishi na ? Mi yasa ya damu dani sosai.? Dubu yadda yazo yake bani hakuri kamar bashi ya 6ata min rai ba,

  Dora kafafunta tayi saman hannun kujerar tana lumshe ido.



                          ****************


K'ARFE TAKWAS DA RABI......

              8:30pm.

 Juye juye take tayi saman carpet ranta a jagule jikinta kuma a mace, kamar marar lafiya.

   Tashi tayi ta ďauki wayarta ta kunna wakar Rihanna _work work work_ ta saka iyafis ta faďa kife saman gadon ta rumtse ido. Bata samu yadda take so ba, sauran ďan sukunin daya rage mata sai ya kara fita ba shiri ta tashi zaune ta cire iyafes ďin ta kunna kira'ar Shuraim, ta kai bolon đin karshe.

   Ahankali take bin suratul Baqara ďin suna karantawa tare. Can ta janyo Laptop, ďinta ta shiga facebook. Notifications ta fara dubawa kamin ta kai gurin massages, sama-sama tayi reply ďin wasu massages wasu kuma ta kyale su, ta koma newsfeed. Posts ta ďinga dubawa wadda ya dace ta dabnawa like ta danna. Daf da zata sauka online ta duba friendsrequest.

    Saif Bashir Bature ta gani, first friendsrequest. Da sauri ta duba profile ďinshi, information ďin data gani about him ya tabbatar mata da shi ďinne na gaske, ga kuma pictures ďinsa dake kai, da wasu family members. 

  Dawowa tayi baya ta danna accept sannan ta cigaba da duba profile ďinsa, 


 Tana Haka massage ya shigo mata,


 ``` Thanks for accepting my request Kaiyrat``` 


Yanayin yadda ya rubuta sunanta nata ya kara tabbatar mata da lallai shi ďinne.


```Your welcome```


Ta rubuta masa as reply, tana taunar hakoranta,

Nan take taga Video call. Ya kirata. Tsayawa tayi tana tunani miyasa ya danno mata videocall.? Oh maybe yana son ya tabbatar da idan ita ďince, hakan yasa ta amsa masa kiran.


Dimm! gabanta ya faďi saboda kwarjinin, murmushinsa da kuma yadda kyakkayawar fuskarsa ta cika mata screen ďin computer.

   

“Kece ko gumkinki.?”


Ganin yadda ta ke kallonsa ba ko motsi. A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta ďan saki murmushi,


“Nice mana kai ma kai ne ko gunkin ka.?”


Dariya yayi,


“Rama wa kikayi.? Ykike ya gida?”


“Lafiya kalau na gode da zuwan da kayi ka bawa Minal hakuri”


Tsoke fuska yayi ya ďan turo hanci gwanin sha'awa,


“Oh never mind Dear it's my pleasure”


“Thanks too”


Ta faďa tana murmushi. Da tunanin abunda zata ce,dan duk ya ďaure mata jiki da sarka da bazan iya cewa ga kalar ta ba!



Shima idon ya tsura mata yana kallon beautifull face nata, da kuma yadda take kunnar kallonsa, duk sai yaji ta kara burgeshi. Wani zillo zuciyarsa take akansa duk da har yanzu bai gama tabbatar da sonta yake ba,

     Saidai kuma jinta yake duk ta make ko ina na ilahirin zuciyarsa, dan ta tara komai da yake so a mace. Suturce jiki, tunani, sanin ya kamata ga kuma uwa uba kunya. 


“Hy are you still there!”


Ido ya kara sakar mata da murmushin da ke kayar mata da gaba,


“Yes pretty anything for me.?”


Dariya abun ya bata daga ita har shi, basu da wani abun cewa sai magana suke kamar wayanďa aka saka dole,


“Laugh huh? What is funny.?”


“Nothing naga kawai kaki kashe laptop ďin bayan baka da wani abun cewa”


“So glad to know that you’re having fun, especially With me”


“Lol Saif I...-”


Bata karasa maganar ba ta rufe loptop ďin da sauri. Tana kallon Minal data shigo yanzu, tana kallon laptop ďin.

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO...!


          NA


KHADEEJA CANDY 


Candynovels.wordpress.com


WATTPAD @khadeeja_candy 



BABI NA GOMA SHA TAKWAS___18



A hankali ta ɗo ta kalli kwayar idonshi, suna haɗa ido gashin jikinta ya tashi, a hankali ta kawarda nata idon tace,


“Saif mi yasa kayi ma Minal haka? Mummy ta faďa min komai ita ma Minal ďin ta faďa min”


Yawu dake bakinsa ya haďe. ita kuma tayi masa kallon jiran amsa.


“Kaiyrat abunda Minal take yayi yawa abun ne ya dame ni shiyasa har nayi unkurin yi mata magana, abunda take ya tsa6a ma addini bata da wta rayuwa sai ta turawa ni kum sam bana jindaďin hakan”


“Saif ba kai kaďai ya dama ba dukan mu ya dame mu badan muna jindaďin abunda take muka saka mata ido ba,sai dan idan akan mata magana ko kuma kayi unkurin chanja mata rayuwa da karfin tuwo zai iya haifar mata da matsala, Saif da ba kai bane babu wadda ya isa ya tsaya gaban Mummy ya faďa ma Minal bakar magana. kai kaďai ka kai ka faďa ma Minal maganar da zata saka ta kuka ta kyale ka”


“Amman kinsan haramun ne a zuba mata ido tana yadda take so ko? kenan koda Sallah tace ba zatayi ba babu wadda zai iya yi mata magana ko?”


“Tana Sallah Saif Minal bata ta6a fashin sallah ba sai dai wani lokacin bata yinta a cikin lokaci duk wani aikin na ibada baya wuce Minal matsalar ta ďaya share share da kuma tufafin da take sakawa sai kuma rayuwar turawa da ta ďauka ta makalawa kanta kuma hkan ba zai rasa nasaba da zaman da tayi can kasashen turawan ba.

 Saif idan kana son ka chanja Minal dole ne ka fara nuna mata son duk abunda takeyi kamin ka nuna mata kin shi kai tsaye dole na ka jta jikinka ka nuna mata muhimmanci abunda kake so tayi kamin ka nuna mata illar wadda take yi a yanzu ki tsaye,

 zaka iya janta jikinka da kalamai masu daďi da kuma kulawa”


Wani murmushi yayi wadda ya fitar masa da beaut point.


“Taya kike ganin zan iya hawo kan Minal har ta daina abunda take bayan ke da kike da dangantaka da ita baki iya jan hankalinta ta daina?”


“Zata daina Saif just trust me and try zata iya canjawa a kanka bata bata canja a kaina ba saboda ni da kai a kwai babbanci kai Namiji ne ni kuma Mace ce zata iya daina akanka bata daina akaina ba”


“Ban fahimta ba toh miye banbanci n dake a gurinta.?”


“Zaka fahimta nan gaba. na gode da lokacinka da ka bani na barka lafiya”


Tana kaiwai nan ta tashi ta gyara yafin mafinta ta nufi kofa. Shima tashi yayi ya rufa mata baya suka fice tare. a bakin kofa ya tsaya yana kallonta har ta buďe motarta tana kokarin shiga ya kira ta,


“Kaiyrat”


A hankalin ta juyo ta kalleshi. Wani kyakkyawan Murmushi ya sakar mata,


“Thank you”


Itama murmushin ta mayar masa tana kaďa kai,


“Welcom.”


ido ya tsura mata har ta zauna cikin motar, ta saka mata key tayi ribas tabar gidan. sai da mai gadi ya rufe gate ďin sannan ya juyo ya dawo cikin falon.

   Huda na ganinsa ta tashi ta nufi Upstairs, shikan bai ma kula da da kishi  take ko wani abun ba dan hankalinshi baya gurinta. Kairat yake tunani da kalamanta, shi kan ta burge shi.

  _Gaskiya tana da hankali da tunani tunda har ta iya yin wannan maganar da wannan tunanin ai ita ma yar mai kuďin ce amman bata hali irin na minal kuma tayi karatun a waje itama, amman bata ďauki halinsu ba da yake tana da hankali kalli ko shigarta shigar musulmai koda yaushe zaka ganta cikin kamala gata black beauty_ 

 

Yana kokarin Zama yake wannan tunanin. (Ni kan nace Saif kodai an kamu🤔)


Huda kan tunda ta shiga ďaki ta kasa zaune ta kasa tsaye, sam hankalinta yake ya kwanta da ganin Kairat ďin da tayi. _toh miye tsakaninsu ? ina yasanta? miyasa yaje da sauri ya tarbeta ? miyasa ya koma can gefe suna magana ? ta lura da irin kallon da yake mata da kuma wadda ita ďin take masa kardai ace sonshi take! shin mima suka tattauna? _

Goshinta take bugu da karfi tana safa da marwa. daker ta samu ta zauna gefen gado still tana tunani.

  Kardai ace Saif sonta yake! kai bazai ta6a yiyuwa ba sai dai idan ita ďince take son jan hankalinsa dan ita bata yarda a kwai mace da mijinta zai iya so ba. toh mima ta rasa da har mijinta xai iya hango wata ? amman da yake mata yan iska ne aun iya jan ra'ayin mutun zasu iya bin ko wace hanya ganin sunja hankalin mijin ko dan mulki da kuďi da yake tattare dashi uwa uba kuma ga kyau. kai dole na ta gano abunda yake tsakaninsu dan daga ganin idon wannan Kairat ďin irin gogaggin karuwan nan ne na turai kai zama ba gannin ba dole ne nayi musu tsakani. tun kar tafiya tayi girma.


   Tashi tayi zuciyar ta na bugawa da karfi ta nufi hanyar falo.

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO. 


       NA


KHADEEJA CANDY 


Candynovels.wordpress.com 


WATTPAD @khadeeja_candy 



BABI NA GOMA SHA TARA___19


Zaune ta tararda shi jingine da kujerar, ga duk kan alama tunani yake dan baiji saukowar taba, 

   Sai kawai ganinta yayi tsaye akan sa tana wani kumburi. Murmushi ya sakar mata ya Hannunta ya rik'a da niyar zaunar da ita, sai kawai ta fisge hannun ta kara haɗe fuska


“Saif wacece wannan.? Mi tazo yi?” 


Ya ɗan daɗe yana kallonta kamin ya bata amsa


“Wacece ita ina ganin ita ya kamata kiyi ma wannan tambayar. Mi tazo yi kuma, tazo ne akan maganar Minal” 


“Minal”


Gabanta ya faɗi, 


“Kamar ya maganar Minal nifa ban gane ba”


“Naje nayi mata magana ne akan yanayin shigar ta da kuma rayuwar turawa da take” 


Zama tayi kusa dashi, 


“Saif har yanzu baka daina zancen Minal ɗin nan ba ina kace min ba zaka sake kula ta ba?

Mi kuma ya kaika gurinta yanzu Saif yarinya ance ba yarinyar kwarai bace ba shaye-shaye take yi kuma ance bata da Uba kai baka ma jin kunya a ganka da mace irinta.?” 


Dariya, “Huddallah kenan toh ai ni sonta nake ba, kuma dan an ganni da ita ai ba wani abun bane tunda mutunci yar uwata kuma musulma. 

   Faɗa min waya ce miki bata da Uba kuma tana shaye-shaye.?”


“Ina zama na aka zo aka faďa min ai kasan abun duniya baya 6oya”


“Toh duk wadda ya faďa miki karya yake yi bata da Uba aka haifeta! Shaye shaye kuma a da ne tayi yanxu ta daina”


“Kare ta dai kake son yi Saif amman nasan wadda ya faďa min ba xai min karya ba, kuma ni banga abunda ta fini dashi ba da har zai ďauki hankalinka gurinka”



Hannu ya kai ya shafa fuskarta,


“Kina wahalar da kanki Huda, na faďa miki ba son Minal nake ba ni kwata kwata bata cikin tsarin rayuwa ta”


“Amman mi yasa kake kula ta?”


Duk yadda zai mata ba yarda zatayi ba dan yasan halin Huda da naci indai akan kishi ne, amman shi kan har cikin zuciyarsa Minal bata cikin tsarin rayuwarsa, Hancinta ya lakata ya tashi ya Upstairs.


Yana shiga ďaki ya cire kayan dake jikinsa ya ďaura  dan karamin tawul ya shiga badroom,


Koda ya fito jikinsa da sanyi da alama wanka yayi, a gaggauce ya shirya cikin kananan kaya black jean da farar T-shirt, ya feshe jikinsa da turare, sannan ya ďauki Atm ďinsa da makullin mota ya fice.

 

Har lokacin Hud na zaune inda ya barta tana tunane-tunane, sam zuciyarta taki yarda da Saif ba son Minal yake ba, indai har da gaske ba sonta yake ba toh ina ruwansa da duk wata rayuwa da zata shiga.

   Tana wannan tunanin ya sauko downstairs, kallo ďaya yayi mata ya ďauke kai yana murmushi, yasan har yanzu abun ne take tunani ganin yadda tayi nikin nikin da fuska babu Annuri. Baice da ita komai ba ya nufi kofar fita, itama bata ce dashi ba dan haushin sa ne ya karu ganin yadda ya ďauki wanka zai fita, har ya fice kallonsa take zuciyarta na raya mata can zaije.


    Sai da taji tashin motarsa sannan ta nufi harabar gidan tana kwalama masu gadi kira, jiki na rawa suka iso suna mata gaisuwar girmamawa,

Bata amsa musu ba ta hau su da masifa.


“Wai miye aikin ku a gidan nn ba gadi ba kuna me wannan yar iskar yarinyar ta shigo min har cikin gida?”


“Hajiya tace ita yar Ibrahim Ahlam ce shiyasa muka barta ta shigo” 


D'aya daga cikinsu ne ya bata amsa,


“Ina ruwana da waye ubanta nan gidana ne ba nata ba karku sake bari wata mace ta shigo min cikin gida ba tare da izinina ba duk kuka sake haka wallahi ba kin aikin ku”


Hakuri suka rika bata, ita kuma sai wani kumburi take bata sake ce musu wani abun ba ta juya ta koma cike da gadara.


                   ****   ****    **** 

 A hankali taji ana buga kofar falon, tashi tayi ta nufi kofar tana tambayar waye, Ba a bata amsa ba har ta buďe kofar.

  Murmushi ya sakar mata


“Kaiyrat”


“Na'am Saif”


Ita ta mayar masa da murmushin tana kara wangale kofar. 


“Shigo mana Saif a gidan ba bakinka bane”

Bai shigo ba sai kawai yasa hannayensa aljihu ya sakar mata ido har sai da idanuwansu sukayi taraiya, da sauri ta sauke nata idon cike da kunya ta ɗanja baya.

Hakan da tayi sai ta burgeshi dan shikan yana son mace da kunya da kuma kamun kai, Murmushin dake fuskarsa ne ya faɗaɗa.


“A'a bazan shigo ba har sai Qawarki tayi min izini”


“Yar'uwarta zaka ce ba qawata ba tana can Garden zaune”


Ta karasa maganar tana nuna masa hanyar Garɗen ɗin, Girarsa ya haɗe akamar tambaya,


“So.?”


“Sai kaje ka bata hakuri”


Kai ya kaɗa, ya ɗga daga jikin kofar ya nufi hanyar Garɗen.Tsaye tayi tana kare masa kallo, ita kan raywarsa tana bugerta bai ɗauki kansa wani ba, kuɗi dake tare dashi basu rufe masa ido ya wulakanta kowa ba, rayuwarsa so simple gashi kyakkyawa. Ya iya zama da kowa,

 Sai da ta daina hango shi sannan ta rufe kofar falon tana sauke ajiyar zuciya.



Zaune take saman doguwar kujera tana rubuce-rubuce da biro kamar wata karamar yarinya sai yage takarda take tana zubarwa,

  Dariyar da taji anyi yasa ta ɗago kai ta kalli gurin da Saif yake tsaye, Kara haɗe fuska tayi ta mayarda kanta gurin rubutun da take, wai ita ala dole tana fushi,

 Karawo yayi kusa da ita da fuskar zolaya,


“Har yanxu baki hakura ba kenan yanxu daga faɗar gaskiya shi kenan na zama mai laifi.?”


Bata ce dashi komai ba sai rubutunta take kamar ma bata san dashi a gurin ba, ganin hakan yasa ya fisge biron dake hannunta ya jefar,


“Zuwan nan da nayi dan ki kawai nayi shi Minal nasan na ɓata miki rai but am sorry bazan sake ba”


Tashi tayi tsaye ba tare data kalleshi ba tace,


“Na hakura”


Sai ta juya da nufin tafiya,Da sauri ya riko ta ya juyo da ita.


“Wanna hakurin ai na dole ne”


Sai a lokacin ta ɗan kallesa ta ɗauke ido,


“Toh mi kake son nace maka?


“Ba wani abun nake son kice min ba kawai hakuri nake son gani a fuskarki, Minalina son ki fahimci wani abu. duk abunda nayi miki nayi ne dan ina kishinki Minal ina bakin cikin yadda kike sakin surar jikinki ga mazan da ba muharramanki na suna kallonki, Minal bana son yadda kike kwaikwayar rayuwar turawa fan abanga abun burgewa a rayuwarsu ba Kishinki ne kai ni ga furta miki kalmomin da suka ɓata miki rai, ina fatar zaki min uzuri ki fahimce ni yanzu”


Shiru tayi kamar mai nazari, Ganin hakan yasa ya riko hannayenta yana kallon fuskarta dan ta tabbatar da gaskiyar maganar sa.

  Har cikin birnin zuciyarta taji sanyin tafukan hannayensa, Nan take kanshin turarensa ya shiga kai ma hancinta hari. Bata an karaba taji faɗuwar gaba sakamakon haɗa ido da tayi dashi. Cikin taku ta kawarda nata idon, da murya mai kamar kuka kamar shagwaɓa tace,


“Amman Saif miyasa kace tirrrr dani? wanna kalamar ita tafi min zafi kuma na kasa gane dalilin furta min ita da kayi Miyasa ba zaka fahimci halin da nake ciki ba?”

Idonta cike da ruwan hawaye ta karasa maganar, fuskarta na kallon gefe. Bakimsa ya cika ma iska, dan yasan duk yadda yake son ta fahimta ba fahimta zatayi ba. Hannu ya kai ya shafa gashin kanta, yaja zuwa kirjinsa ya rugumta. 


“Kiyi hakuri Minal nayi miki alkawarin bazan sake ba”


Kara kamkamesa tayi ta lumshe ido tana shakar daɗadɗen kanshin dake tashi daga jikinsa, Ta hakan ya gane ta hakura daman yasan idan ba hakan yayi mata ba, baxata hakura ba.

     Jikinsa ne ya bashi ana kallonsa. hakan yasa ya ɗago kai ya kalli windon dake fuskantarsu, Kairat ce tsaye jikin windo tana kallonsu fuskarta ɗauke da murmushi.

 Daga inda yake tsaye ya aika mata da sakon lafiyayyen murmushi wadda zan iya cewa har cikin zuyarsa yake. 

   Ita kuma ta ɗago masa babban yatsanta alamar well done tana murmushi, sannan taja windon ta rufe zuciyarta a rike. Jinginawa tayi jikin windo  gumɗe da baki.

  Can kuma naga ta rumtse ido ta sulale kasa zaune, tana girgiza kai kamar mai magana da wani.

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO. 


      NA


KHADEEJA CANDY 


Candynovels.wordpress.com 


WATTPAD @khadeeja_candy 



BABI NA GOMA ASHIRIN DA D'AYA__21



“Miyasa kika rufe laptop ɗin.?”


“Ba komai na gama abinda zanyi ne ya akayi.?”


“Ba komai Mummy tace na tambaye ki ina kika je min Sarka.?”


Kairat ta tashi tsaye,


“A'a ba wani sarkanki ni tace ta siyo ma”


“A'a-a'a tace ni ta siyo ma ke sai ta sake zuwa”


“Dan can ji kanta aje a tambayi mummy ďin”


“Ae aje ďin”


Da gudu Minal ta fice tana arigaggan zuwa gurin mummy, Ta riga Kairat isa ďakin sai ta rika yima mummy wink da ido.


“Mummy bani kika siyo ma wannan Sarkar ba.?”


Murmuahi Mummy tayi dai-dai lokacin da Kairat ta shigo ďakin tace,


“A a Kairat na siya ma ke nace sai wani satin”


Dariya Kairat tayi mata tana mata gwalo,


“Allah na gode maka yarinya kinji kunya”


Kukan shagwa6a Minal tasa,


“Gaskiya ni mummy kina gwada min banbanci Ni barin gidan ma zanyi”


“Sai kin dawo Allah ya kiyaye Hanya”


Mummy ta faďa da fuskar zolaya tana murmushi,


Tashi tayi ta bar d'akin tana hararar Kairat, Nan Kairat ta rufa mata baya tana zolayarta,



BAYAN AWA D'AYA....... 


Duk zaune suke falo suna fira suna cin Tofin da Talatu tayi musu, Kairat sai santi take wai ya ake yinsa. Duk dariya suka sama, har Mummy Minal tace


“Da madara ake yinshi”


“Dan can ji kanta kena tambaya ne sai kace iyawa tayi”


“Wallahi Mummy ta daina ce min aji kaina kona mata ďan banzan duka”


Tashi mummy tayi,


“Idan ba gurin na bar muku ba ba zaku barni na huta ba kullum faďa kuke kamar kananan yara”


“Ai itace ta fara jana”


Minal ta faďa tana hararta, Kairat taja tsaki


“Ji kanta dana jaki saina kaiki ina?”


“Kinji ko mummy baza ta daina ba”


Mummy dai bata sake ce musu komai ba da nufi ďakinta, Haushin hakan yasa Minal ta ďauki Filo ta jefe Kairat dashi, Nan Kairat ta sake ce mata


“Dan Allah can ji kanta an faďa ance ji kanta”


Banza tayi da ita ta cigaba da matsar rimot tana cin tofin, 


“Idan kinji ma na sake miki magana kice min ba Minal ba”


Dariya Kairat tayi zatayi magana, Jafar ya turo kofar falon ya shigo da sallama,


“Amin wa alaikassalam” 


Talatu ta amsa masa, sai da ya gaidasu sannan yace


“Wai Saif yace a kira masa Kairat”


Dimmm gaban Minal da Kairat ya faďi, suka haďa ido kamin daga bisani Minal.ta janye nata,


“Kodai Minal yace.?”


Kairat ta tambaya,


“A'a kedai yace a kira masa yana nan waje”


Rasa tayi abunda zata ce dashi, idan tace baxata ba Minal zatayi tunanin wani abun ne idan kuma taje Minal zatayi tunani wani abun ne kuma, toh ya zatayi.?

    Minal ce ta katse mata hanzari, da faďar


“Jeki kace gata nan zuwa”


“Toh”


Da sauri ya tashi ya fice. Kairat ta kalleta


“Haba Minal nace miki zani ne?”


“Amman kinsan Saif yafi karfin wulakanci ko.?”


“Lallai kan Kuma baki san abunda yake tafe dashi cikin daren nan ba”


Talatu ta faďa tana kokarin tashi. Tashi itama Kairat tayi ta nufi hanyar ďakinta, Ta daďe tsaye kamin ta saka hijabinta ta fito.


Tsaye ta hangosa jikin mota sanye da bakar jallabiya ya rumgume hannayesa yana kallon sama kamar mai kidayar taurari,

  da sanyin jiki ta karasa kusa dashi, cikin sallama. a hankali ya sauke idanunsa akanta ya kamar mata murmushi.

  Bata jira ya amsa tambayar ba ta aika masa da tambayoyi,


“Me kazo yi yanxu da dare nan Saif.? Minyasa kace akira maka ni ? mi zanyi maka.?”


Ido ya kura mata,

“Wace Tambayr zan fara amsa miki”


“Mi kazo yi da dare haka.?”


“Daga gurin Abbah nake wasu file na kai msa shine nace bari na biyo kinsan kusa ne”


Kai ta ďaga masa tana kallon windon falo kamar mai jin tsoro,


“Miyasa kace a kirani Bayan ga Minal.?”


“Ke naga damar kira”


Cikin kakkausar murya ya bata amsa, Nan ta kallesa,


“Abunda kake bai kamata ba Saif”


“Ke kina yin abunda ya dace ne.?”


“Ba haka bane yanzu Minal zatayi tunanin ko wani abun ne”


“Toh sai me dan tayi tunanin kina tsoronta ne?”


“Bana tsoronta”


“Miyasa kike gudun 6acin ranta.?”


“Saboda ina son farin cikinta”


Kai tsaye yake mata tambayoyin tana bashi amsa. A hankali ya gyara tsayuwarsa fuskarsa ba yabo ba fallasa yace,


“Bari na faďa miki wani abu da baki sani ba a kaina Kaiyrat, Bana yin abu a tambaye ni dalili, bana tambaya a maida min tambaya, bana cewa A ace min B ba mai kallon tsakar idona ya faďa min bakar magana, Bana kira a kashe idan bani na kashe ba. Duk abubuwan nan dana faďa kin aikata su na kyale ki ne dan kawai ina mutunta ki and i have something behind your heart, so don't try me again”


Nan ya jefa mata gift ďin dake hannunsa,


“Bana kyauta a mayar min idan kinga dama ki ďauka ko ki jefar”


Bai jira cewarta ba ya buďe motarsa ya shiga, da wani karfi ya fisgeta ya fice gidan kamar kyaftawar walkiya.

   Sai a lokacin ta iya yin tsotsin kirki, dan tunda ya fara maganar tayi saranda tana saurarensa.  Dukawata tayi ta ďauki gif ďin da aka naďe cikin jar fefa mai zanen heart, ta nufi kofar falo, jikinta sayyaye.

   Tana turo kofar falon Minal ta kalleta, Murmushi Kairat ta sakar mata tabkaraso da sauri kusa da ita kamar ba ita ba,


“Minal kinsan meye.?”


Kai ta girgiza mata, Kusa da ita ta zauna tana mika mata Gif đin


“Wai kiran da yayi min danki ne fa kinga abunda ya siyo miki wai tsoron baki yake ji karki watsa masa kasa a ido.”


Da sauri Minal ta mika hannu ta kar6a zuciyarta cike da farinciki,


“Tsorona sai kace wata dodo miye a ciki.?”


“Ai bai yarda na buďe ba wai sai na kawo miki kuma yace na gaishe ki”


Da karfi Minal ta fixge fefar. Kairat gabanta sai faďuwa yake kar Minal.tqga wani abun da zai sa tayi tunanin yana sonta Allah allah take idan bai rubuta sunan ta ba ko wani abu daya danganceta, Da farko batayi niyar bata ba sai kuma tayi tunani idan bata bata ba toh me xata ce mata Saif yazo yi a gida kuma gurinta.


Cake ne cikin kwali mai ganen heart guda shida guri ďaya, ďaya ta ďauka tabkai bakinta ta lumshe idon tana murmushi. Can kuma ta buďe idon ta rumgume Kairat, Dariya Kairat tayi wadda zan iya cewa bata kai ciki ba, tace


“Minal kin jidaďi ko.?”


“Sosai ma”


“Minal kina son Saif ko.?!”


D'agowa tayi daga jikinta tayi kasa da kanta,


“Amman ina jin tsoron kar shima ya juya min baya Bana sin daga baya wata matsalar ta fito yace ba zai zauna dani ba”


Hannu Kairat ta kai ta rika fuskarta, tana murmushi


“Zai soki Minal ba zai barki ba Saif ya banbanta da sauran maza Ba zaki sake bakin ciki ba Minal no more sad, no more tears wadda kikayi a baya is enough idan mutun bai faranta miki ba Minal toh bazai bakanta miki ba”


Sake rumgume ta Minal tayi ta rumtse ido tana sauke ajiyar zuciya,


“Na gode sosai Kairat”


“Don't mention you deserve more”


Kairat ta faďa tana lumshe ido,


“Kuma shima kamar yana sona ko Kairat.?”


Kai ta ďaga mata tana share hawayen da suka zubo mata,


“Sosai ma Minal yana sonki sosai”


Kara rumgumeta tayi cike da jindaďi.

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO. 


       NA


KHADEEJA CANDY 

 


Candynovels.wordpress.com 


WATTPAD @khadeeja_candy 



BABI NA ASHIRIN DA BIYU___22


Cike da ɓacin rai ya isa gida. Mamakin kansa yake wai Namiji kamar shi Kairat zata tsaya tana yimai yadda taga dama, wani gurin kuma laifin kansa yake gani tunda shi ya sake mata fuska har taga damarsa.

   Da wannan tunanin ya shiga ɗakinsa, Kwance ya hango Huda ta baje saman gadon tana sharar bachi, matsawa yayi kusa da ita ya kura mata ido hannayensa zube cikin aljihu. Zuwa can ya ɗauke kai ya nufi wadurof ya canja kayan jikinsa zuwa na bachi, bayan ya gama shirinsa na bachi ya kashe wutar ɗakin yazo bayan Huda ya kwanta.


                                 *     *     *


“Mtwssss” 


Yaja tsaki, Nasir ya kallesa,


“Wai dan na yi maka sammako kake wannan tsaki.? idan mitin ɗin ne baka son zuwa sai ka na koma na sauke ka”


“No ba haka bane mitin ai ko baka zo ba dole ne naje, kawai wani abun ne yake ɓata min rai”


“Name.? ko san yan jarida sun yaɗaka”


Kallon rashin fahimta Saif yayi masa,


“Sun yaɗani kamar ya wani abun na aikata ne.?”


“Kar dai kace min baka san komai ba!”


“Allah ban sani ba, meke faruwa ne?”


“Aiko kusan jarida nawa ta buga wai kana soyayyah da ya Dr. Salamatu”


Hannu yasa ya dafe kansa, yada soma sara masa yanzu,


“Kai wai yan jaridar nan basu da hankali ne! Su abu kaɗan ya zama na labari Mtwss”


“Wai kana nufin bada gaske bane.?”


“Babu abunda ke tsakanin mu, ni ba sonta nake ba beside ni Qawarta nake so kuma ita ma ta fara bani haushi”


“Baka sonta amman kake kula ta.? Haba Saif nifa ba mutun bane da zaka ɓoye ma sirrinka”


“Allah da gaske nake ni babu abunda ke tsakanin mu, ina kula ta ne kawai dan tana bani tausayi saboda kazantacciyar rayuwar da take, amman ni ba sonta nake”


Murmushi Nasir yayi ya bugu sitarin motarsa,


“Karka ce min baka sonta Saif, baka sonta kake kokarin ɗorata a hanya? Wannan ai kai ba zai ɗauka ba”

 

Saif ya ɗan fusata,


“Ai sai kayi tayi tunda baza yarda ba”


“Ka yarda kana sonta Saif Tausayi silar so da baka sonta da bazaka iya zama da ita ba koda na minti ɗaya ne, and Saif abunda kake kokarin yi ba xai taɓa yiyu ba Kairat bazata taɓa sonka ba koda tana son ka bazata nuna maka ba, 

 Saboda taraiyarsu da Minal ta zamo kamar yan'uwa, toh faɗa mi taya Kairat zata so abunda Minal take so?”


Saif ya kalleshi,


“Ce maka akayi tana sona?”


“Tana sonka Saif kuma kaine ka ɗasa mata son a zuciyata, da bata sonka bazaka mata abu ta kyale ka ba, An faɗa min babu wadda ya isa yasa Minal tayi abunda bata tashi ba amman kai kana sata kuma ta daina,

   Kai da bakinka kake faɗa min minal tana shaye-shaye tana zuwa club tana mu'a mala da maza yadda kai hakan baya yi maka daɗi, kasan abunda yasa baka jindaɗi! saboda kana sonta, Kairat ta fita hankali da hali mai kyau hakan yasa taja hankalinka har ka fara sonta, Bari na faɗa maka wani abu da har yanzu ka kasa ganewa Saif, Minal ce kake so ba Kairat ba Kairat halinta kake so Minal kuma zatinta kake so da ace Minal zata canja hali, Halinta ya dawo kamar na Kairat, da bazaka sota ba, Toh kaga Minal ce ainihin mace da kake so”


Shiru yayi, ya tattara girar kasa da sama yana nazarin maganganun Nasir. Ganin hakan yasa Nasir ya faka gefen ti-ti, ya kalleshi kana ya cigaba,


“Saif Minal matar aure idan kayi mata kallon tsafta, Zaka iya maidata yadda kake so tunda kana rike da zuciyarta, Idan ka ɗorata a tubar sai ta Kairat natsuwa da cikar kamala, kuma zata rika ganinka da kima ta mutunta mahaifiyarta ma nasan zata jidaɗi zaka buga baban tarihi a rayuwarta, Yanzu isan kaso Kairat idan Kairat ta canja halinta tsanarta zakayi, amman Minal kaga yadda halinta yake kuma kana tare da ita a haka,

    Saif idan baka so Minal ba ka zalunce ta, dan kai ne ka nuna mata kulawar da har ta ɗasa mata sonka a zuciyarta, Minal abun tausayi ce Saif, Ta rabu da saurayinta akan bata da uba, yanzu kaima idan ka rabu da ita zatayi tunanin sabod haka ne, kuma zaka ɓata taraiyarsu da Kairat.”


Ajiyar zuciya ya sauke ya lumshe manya idanunsa, ta lumtse labbansa. Nasir ya cigaba,


“Idan ka auri Minal zaka fi samun kwanciyar hankali saboda bata da ishenshen wayo sosai kamar Kairat, amman kaga ita bom ne zaka haɗa tsakaninta da Huda babu wadda zai kyale wani kaga anyi ba ayi ba kenan”


A hakali ya buɗe idonsa ya kalli tsadadden agogon hannunsa yace


“Ja Mota muje kar muyi latti”



                       ***       ***      ***




Kukanta daya jiyo.ya haddasa masa faɗuwar gaba tun kamin ya karaso cikin falon, Da hanzari ya karaso kusa da ita ya zauna jikinsa na gogar nata,


“Lafiya kike kuka waya mutu.?”


Da jajayen ido ta kalleshi,


“Ni kan da mutuwa ce.da ta fimin sauki sama da abunda naji kuma na gani”


Bayanta ya shafa, alamar rarrashi


“Toh faɗa min minene”


“Saif mi kaga a jikin Minal da ni bana dashi har ya ɗauki hankalinka kake sonta ? a da na ɗauka zance mutane sai yanzu na tabbatar tunda har a jarida an faɗa wai ynzu kana daf da aurenta, saboda ta ɓata da saurayinta saboda kai Saif miye bana maka?”


Bushewa yayi da dariya, hakan yasa ta kara fusata, daker ya iya saita kansa ya kalleta


“Wallahi kina burgeni Huda kin iya kishi kamar a shirin fil ko kuma littafin marubuta, Toh miye na zama kina zubar da hawayenki a banza wai zanyi aure, nifa Mijin mace huɗu ne ni banga abun kuka a ciki ba duk kinbi kin haɗa wannan zufar”


Tashi tayi tsaye tana masa kallon tsana,


“Da gaske ne kennan.? aiko Saif da kayi min butulci”


“Butulcin mi Huda na taɓa miki alkawarin bazan yi maki kishiya bane”


Harara ta watsa masa ta shige ɗakinta. Shi kan ko ajikinsa dan baiga anfanin kukan ba, shi dai yasan bazai mata alkawarin kin aure na tunda yana niyar yinsa ko da ba yanzu ba. 

   Ruri wayrsa tayi alamar kira, Number Minalya gani, sai da tayi ringing kamar zata katse sannan ya ɗauka, Zazzakar muryarta ta daki dodon kunnensa,


“Assalamu Alaika”


Sallamar da tayi tasa yaji kuzarin amsa mata,


“Wa'alaikissalam”


“Saif ina son magana da kai, oh sorry ya Gida?”


“Gida lafiya kalau faɗi maganar ki”


“A'a ba a waya zan yi ba ina son kazo gida yanzu”


Shiru yayi, kamar ba zaiyi magana ba, jin haka yasa ta marairaice masa murya kamar mai shirin yin kuka,


“Saif dan Allah wata magana zamuyi”


“Ok gani zuwa”


“Thank you sai kazo”


Kashe wayar yayi ya tashi ya nufi gurin cin abinci, sai da yaci ya koshi sannan ya nufi ɗakin Huda. Zaune ya tararda ita manne da waya a kunneta, tana ganinsa tayi sauke sauke wayar tana kallonshi.

Daga bakin kofa ya tsaya yana murmushi, 


“Kin daina kukan.?”


Banzanta tayi masa, ta juyarda kanta, bai sake ce mata wani abunba ya juya ya nufi ɗakinsa.

    Wanka yayi ya shirya cikin kananan kaya masu kyau da ɗaukar hankali, sun karɓe shi sosai sun kama jikinsa, sai kanshin turare yake kamar kanfanin pure cure. cikin takun girma ya dauko kasa ya nufi harabar gidan.



                        ***       ***      ***


Ido ya sakar mata, hannayensa zube cikin aljihu yana kallon yadda ta nufoshi da gudu, kanta ba ɗankwali, gashin kanta yasha gyara ya sauko har gadon bayanta, tana sanye da doguwar riga baka har kasa sosai tayi kyau kamar wata matashiyar ba indiya, yadda take gudun ma abun sha'awa da gashin kanta sai kaɗawa yake iskar na ɗibarsa.

       Numfashinta kamar zai ɗauke ta karaso kusa dashi, ta mika masa jaridar dake hannunta,


“Saif kaga abunda suka rubuta a jarida game da mu?”


Ko motsi bai yi ba balle yayi mata magana,har lokacin kallonta yake da yadda ɗan karamin bakinta ke motsi, 

  

“Saif ya kamata kayi wani abu kasan halin yan jarida ko ɗazu sai da wani ya kira ni yana tambaya na wai da gaske ne!”


Sai a lokacin ya haɗe yawun dake bakinsa, Ya gyara tsayuwarsa


“Baki iya gaiauwa bane!”


Da sauri ta gyara gashin kanta, ta ɗan natsu 


“Sorry Ina wuni.?”


Bai amsa ba, sai kawai ya mika ɗayan hannunsa ya karɓi jaridar dake hannunta yana dubawa. Zuwa can ya ɗago kai ya kalleta,


“Toh miye a ciki karya suka faɗa ne.?”


Sororo tayi tana kallonsa jin irin tambayar da yayi mata, ta daɗi ita dashi suna kallon juna kamin ta iya saita muryarta,


“Karya kan suka faɗa”


Jaridar dake hannunsa ya aje saman mota ya kai hannunsa ya rika gefen fuskarta, a hankali ya furta


“Ba karya suke ba Minal I LOVE YOU AND I ONLY WANT YOU TO LOVE ME!”


Wani bugu zuciyarta tayi wadda bata taɓa jin irinsa ba a rayuwarta. Kallon kallo suka rikayi ita dashi. Idonshi sun karantar da ita gaskiyar abunda ya furta mata, sai da bata da tabbacin hakan tunawa da maganar da kanwarsa tazo tana faɗa mata jiya.

    Da sauri ta janye fuskarta, idonta taf da hawaye tace


“Saif baza taɓa son mace irina ba, bana cikin tsarin matan da kake son ka aura, kanwarka ta faɗa min kana yaudarata ne kawai dan ka cin ma burinka, Saif tace min bana da tarbiya, 

  Kuma ni karuwace sannan kuma yar zina!. Nasani baza so ni ba saboda bana da Uba kuma ga ciyon dake tare dani and i know i m not your type”


Hawaye ne suka zubo mata, dai-dai lokacin data kai aya a maganarta

  Wani irin kalar tausayinta yaji ya kamashi. A gefe ɗaya kuma yana mamakin wace kanwar tasa ce tazo tayi masa wannan lalatar,

 A hankali ya matso kusa da ita ya kama hannayenta


“Minal ai kinsan ban neman mata ko?”


Kai ta ɗaga mashi,


“Toh taya zanyi amfani dake na cinma burina miyasa baki yi wannan tunanin ba,?

 Minal rashin mahaifinki bai dame ni dan nima da Allah yaso da haka zai yi min, duk kuma mutu min da zai kyamace ki dan ciyon dake jikinki wawane,

 Minal weather you believe me or noti I LOVE and I really mean it ai kinsan babu Wanda ya isa ya sani abunda ban tashi ba ko?”


Nan ma kai ta ďaga masa,


“So just trust me I'm for what ever”


Yawu dake bakinta ta haɗiye, tace


“But...-”


Da sauri ta ɗora yatsansa saman leɓenta,


“Shiiii no but kawai ki bar zuciyarki taso wadda take so zan tsaya miki naci alwashin kasancewa dake har abada”


D'agowa tayi ta kalli cikin kwayar idonsa, shi kuma ya sakar mata murmushi ya rumgumeta.



      A hankali Kairat dake tsaye bakin kofar Garden tana kallonsu ta share hawayen dake idonta, ta nufi wata bishiyar mangoro, ta jingina da ita, ta ɗaga kanta sama wasu hawaye masu zafi suka rika zuɓo mata.

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO. 


       NA


KHADEEJA CANDY 


Candynovels.wordpress.com 


WATTPAD @khadeeja_candy


 

Kainuwa Writers Association 



*23*


Ido a rufe ya isa Asokoro villa, dan yau so yake yaji wace munafurka qanwarsa ce tayi masa wannan wawancin,

   Sallama ma dan ta zamo masa dole ne kawai yayi ta. 

   Kallo ɗaya Momi tayi masa ta gane yana cikin ɓacin rai, 

    

“Momi ina wuni.” 


Ya gaisheta ne yana kokarin zaunawa saman kujerar dake fuskantar ta ta,


“Lafiya kalau Saifullah ya gidan?”


“Lafiya kalau Momi ina su Safiya.?” 


“Suna ciki lafiya dai.?” 


Bai ɓoye ma Momi komai ba, akan Minal da kuma abunda tace Kanwar tasa tazo tace mata, 

     Kai  Mummy ta girgiza, 


“Amman basuyi tarbiya ba, ina ruwansu da ita Safiya Rukaiya Lubna” 


Momi ta kwala musu kira, ba ɓata lokaci suka fito suka zauna suna gaida Saif, 


Bai amsa ba sai kawai yace,


 “Cikin ku wacece taje gidan su Minal?” 


Kallon kallo suka rik'ayi da junanasu zuwa can Safiya tace, 


“Nidai ba ni bace” 


“Toh wacece.?” 


Ya tambaya a tsawa ce, nan kuma kowa yayi shiru, Momi ta kalleshi, 


“Ita bata faɗa maka ko wacece cikin su ba.?” 


“Ae ita ai bata sansu ba tace wadda ta faɗa mata dai fara ce kuma tace ita kanwata ce” 

“Wannan ba hujja bace tunda dukansu fararene” 


Faɗar Momi tana kallonsu, Saif ya fusata sosai


“Wallahi ko wacece ta faɗi kanta kamin na gano ta dan wahala kawai zata sha”



“Nice Yaya”


Tana faɗa ta koma gefen momi, tana kallonsa 


“Toh uban waya aikeki”


Ta ɗan ɓata fuska,


“Amman Yaya ya za'ace wannan yarinyar kake so fisabillillahi yarnya nan fa bata da Uba kuma shaye shaye take kuma ance yar iska ce”


Kamin yayi magana Momi ta rigashi,


“amman Safiya baki da hankali toh ina ruwanki da ita ba shi ya ganta a haka yace yana so ba”


“Amman Momi jifa harda yan jarida sai buga labarin suke ai ana son idan mutun zaiyi aure ya auro yar mutunci yarinyar nan fa yar iska ce kuma bata da uba”


Momi ta fusata,


“Idan yar iska ce sai me! da ake ɗauko karuwa fa a gidan karuwai a sata bara'ah a aureta balle wannan da take karkashin iyayenta, Kuma ke kika maganar bata da uba shin ita ta halinci kanta ne ko kuma iyayen nata sun shawarce ce ne da zasu aikata ni mutane auna bani mamaki sai a rinka cewa yarinya shegiya shin ita tayi kanta ne ke zaki aureta ne ko ke zaki zauna da ita ne?”


Kuka ta shiga rerawa irin na marasa gaskiya, Saif dai baice komai ba dan Momi ta biyashi, daman yasan bada saninta taje gidan ba.

  jin tana kokarin maida kukan na gaske yasa shi katsa mata tsawa,



“Wallahi zan dake ke duk ba ki bar nan gurin ba”


Da gudu ta tashi ta nufi hanyar ɗakinsu, Rukaiya da Lubna suka rufa mata baya.

  Momi ta kalleshi cike da natsuwa tace


“Kana ba wani matsala a wajen huda.?”


“Matsalan me Momi nifa ba mijin mace ɗaya bane kuma daman ni ina da niyar karin aure dan kinsan matsalolin da muke fuskanta tsakanin mu”


Ajiyar zuciya Momi ta sauke,


“Toh Allah ya zaɓa mana abinda yafi zama alheri”


“Amin momi haka nake son kice”


                          ******     ******    ******


“Hello Dr.Khadija yau ana tuna damu”


“Hmm ai kullun kuna cikin rai ya kike ya gidan”


“Lafiya kalau ya aikin naku”


“Aiki da godiya, wai wata magana naji agame da mai gidanki ko gaskiya ne.?”


Dariya Huda tayi a ɗayan ɓangaren sannan tace,


“A jarida kika gani ko”


“Eh wai mijinki zai kara aure zai auri yar Dr.Salamatu Abubakar Yola”


“Zainab kenan ke yanzu ko ance miki mijina zai kara aure zaki yarda, ai Saif mijin Huda da Huda da Huda ne ita kaɗai”


“Wai ke yar yanzu baki daina wannan aikin kishin ba, Huda yaushe zaki san kin girma ya kamata ace izuwa yanzu kinsan ciyon kanki”


Huda ta tashi zaune, tana buɗar hanta,


“Zainab indai barin kishine ne.sanin kishin kai toh wallahi yanzu na fara indai akan Saif da uban kowa zan iya ɓatawa kuma wallahi wallahi matukar ina raye Saif bai isa ya kara aure ba nidai ce zama dani ko ba daɗi”


“Huda kiji tsoron Allah taya zaki ce ki hana mijinki aure bayan kinsan yana da dalilin yinsa, Huda ke ba haihuwa kike ba ya kamata ace kin tausaya masa kin barshi ya kara aure ko dan haka, 

   sannan bawan Allah nan kina zalumtarsa iya zalumta kina tare da abokinsa sannan ahi kansa bakya kyatata masa kuma yanzu kice zaki hana sa aure bakya tsoron hakkin Allah ne idan kika mutu me zaki faɗawa Allah”



Dariya tayi kamar wadda akayi ma albishi,


“Allah sarki Qawata Zainab aikwai ki fa da nasiha a koda yaushe, amman bakya yinta a inda ya dace, yau ni kaɗai nake aikata zunubi ne ko ni kadaice nake zaman aure da zina kowa fa yana nasa saɓon amman sai a zo a samu mutun ɗaya a sha masa kai ina ruwanki ne mijina ne ko mijinki, ni bana son wani wa'azi ki aje abunki wata rana zai yi miki amfani amman ba yanzu”


Bata tsaya jiran abunda Zainab ɗin zata ce ba ta kashe wayar tana jan tsaki,


“Ke kin cika matsala wallahi sai mutun na cikin farinciki ki ɓata masa rai, ki barni naji da abunda zanji mana nace miki ina so wata nasiha ne sai kace wata yarinya mtsss stupid”


Haka tayi da matsifarta tana jin haushin ɗaukar kiran da tayi,




MINAL...................

Sanye ta fito da gown ɗin atamfa tayi rolling ɗin kanta da jan ɗankwali, Fuskarta babu Kwaliya sai dai ta kawatata da murmushi na zumuɗin ganin abokin nata,


“Deen...”


Ta faɗa daidai lokacin data karaso kusa dashi. Ya ɗan daɗe kamin ya ɗago kai ya kalleta da fushi a fuskarshi, nan take murmushin dake fuskarta ya ɓace,


“Sad face Deen mi nayi maka ko dan ban faɗa maka da wuri ba?”


“So.da gaske aure zakiyi kenan?”


Da kakkausar Murya ya tambaya,


“Ae mana Deen aka wasa da maganar aure ne, baka yarda ba dana faɗa maka a phone”


“You betray me Minal kin nuna min true color ki”


Mamaki ne ya cika mata fuska, mamako na taya ta farin ciki sai yace ta ci amanarshi me yake nufi ne,


“Ban fahimce abinda kake nufi ba Deen”


Wani murmushi yayi,


“Kin tsallake ni ki auri wani bayan kinsan duk zaman da mukayi ke nake jira”


Ido ta kura masa kamar bata gane abunda yake faďa ba, 


“What you are staring at me common tell me I don't know nasan haka zaki ce”


Kai ta girgiza tana haďiyar yawu


“Deen ban fahimta ba”


“Yes ai bazaki fahimta ba amman bari kiji na faďa maki wani abun da baki sani ba, nima sai naci taki ki rubuta ki aje”


Yana kai wa nan ya juya, da sauri ta riko shi,


“Ni bana fatar cin amanar kowa Deen ni ban ta6a maka kallon matsoyi ba dan haka ban karanta sona a idonka ba kai kuma baka faďa min ba”


“Karya kike Minal karke kice bakinsan ina sonki ba babu wadda zai kalli zamantakewar mu da ke yace babu soyayyah a tsakanin mu kawai dai kin nuna duniya irin cin amanar da kika min ne kin bawa makiya na damar yi min dariya”


Kai ta girgaza idonta taf ta hawaye tace


“Wallahi ban sa kana sona ba Deen kallon aboki nake maka kuma ďan'uwa kada ka rubuta ni a matsayin mai cin amana ba zan iya cin amanarka ba Deen”


Idonta ya kallah,


“Zan yarda da hakan idan kika janye maganar auren ki da Saif kika aure ni”


Sakin baki tayi,


“Deen Saif ya riga yayi maganar aure na kuma na bashi da amincewa taya yanzu zan dawo nace na fasa Deen...-”


“Ba sai kin karasa ba Minal kin nuna min ni wanene a gareki Thank you”


Rigarsa ya ka6e ya juya a fusace ya shiga motarsa. ita dai tsaye kawai tayi yana kallonsa har ya fice.

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO


      NA


KHADEEJA CANDY 


Candynovels.wordpress.com 


WATTPAD @khadeeja_candy 



Kainuwa Writers Association 



*25*


Numbar Momi ta kira, Bugu biyu aka ɗauka. jikina na rawa tace


“Hello Momi ina wuni”


“Ba momi bace Safiya ce momi tana part ďin Dad lafiya naji muyarki haka.?”


“Ba lafiya ba Safiyya wai kina da labarin Saif aure zaiyi.?”


“Allah sarki kardai kice min sai yanzu kika sani bayan saura sati ďaya a ďaura musu aure”


“Naji amman ban tabbatar ba sai yanzu dan ni a tunani na bada gaske bane sai yanzu da ya kawo min kayan faďar lefe wai saura sati biyu a ďaura masa aure” 


“Toh ya rage miki ne saboda kiga kishiya ba zata wallahi anty da ba Yayana bane da nace azzalumin ace duk zaman da kukayi ya rasa da me zai saka miki sai kishiya, kishiya kuma irin wannan yar shaye shaye karuwa kuma shegiya hmmm namiji kenan”


Fashewa Huda tayi da kuka,


“Wallahi Safiya da ace a mafarki ne aka ce min Saif zaiyi aure bazan yarda ba amman yanzu wai har shi da kansa yake faďa min”


“Kuma kinsan wani abun haushi su Momi da Dad suka goya masa baya sam ni hakan bai min daďi ba dan ni tun lokacin da aka ce yarinyar nan tayi unkurin hallaka kanta naji na tsaneta, shiyasa naje har gidansu nayi mata wankin babban bargo data faďa masa yazo gida dukanane kawai baiyi ba amman sai kinga yadda yake tada jijiyar wuya akanta ita kuma Momi ta goya masa baya”


Cikin muryar kuka Huda tace,


“Wallahi Safiya ban yi zaton Momi zata goya masa baya ba ya aureta mace haka”


“Hmm ai duk goya masa baya sukayi nice kawai nayi masa magana ina nuna masa illolinta sai yace min wai shima tausayinta yake gani kuma idan bai aureta ba hankalinsa bazai kwanta ba wai yaci amanar ta jifa ke har Nasir goya masa baya yayi gurin aurenta wannan yarinyar ta tsafe kowa nice kawai bata samu sa'ah kuma nafi karfinta”


Kasa magana Huda tayi sai kuka take, tana murje murje kasan karfin, hankalinta ne ya kara tashin jin ance kowa ya goya masa bayan yayi wannan auren,


“Oh ji min Anty Huda wai kuka kike ne! Allah sarki ni ina ganin laifin mata masu kuka akan kishiya name a a wallahi bazan wahalar da rayuwa taba”


Daker ta iya furta,


“Safiya hankalin Saif ya riga ya gama tafiya gurin yarinyar nan kwata kwata yanzu baya kulani gashi sai zagin iyayena yake yana cimin mutunci shiyasa ma na kira na faďawa Momi ina cikin matsala Safiyyah”


“Ke ďan Allah ki daina zubarda hawayenki akan wata yar iska, ai akan wannan yarinyar komai sai iya yi miki dan ta riga tayi masa magani amman kinsan wani abun ba ai idan tasan wata bata san wata ba indai magani ne tayi ni kuma zanyi mata makirci wadda yafi magani”


Tashi Huda tayi zaune, tasa hannu tana share hawayenta


“Me kike nufi Safiyyah zaki taimake ni ne?”


“Ae taimako kan zanyi miki zan yima kaina da duk family mu dan wannan da kika gani da kowa zata iya raba shi kuma tunda nace bana sonta bana sonta sai na hana auren ta da Yaya”


Wani sanyi sanyi Huda ta fara ji, cikin zuciyarta wadda bai gama hawa saman fuskarta taba,


“Mi zakiyi Safiyyah.? wallahi da kin taimaka min daman nasan duk cikin family ku babu mai sona irinki”


“Yanzu ne zan nuna miki so Huda sai na hana ta zama gidan Yaya kota halin yaya keda yaya kuma mutu kan raba, ai daman ance mai laya kiyayi mai zamani kuma BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE,in dai ita takamarta magani ni kuma zan nuna mata zamani da boko da kuma kalar barinki da bata sanshi ba”


Wannan karon Dariya Huda tayi,


“Amman wallahi da kin faranta min rai kin cire min damuwata”


“Hmmm kawai kisa ido kiyi kallo, ke dai daga yanzu ki daina nuna masa kishi da haukar nan ta mata ki bishi kar kuma ki sake kiran Momi da sunan yi mata sheidair wani wani sau da kafa sauran bayani sai gobe idan nazo.”


Tana kaiwa nan ta katse kiran, da sauri Huda ta kalli wayar tana buďar baki da fuskar mamaki,


“Ikon Allah daman ance duniya mai faďi abunda ka sani shi ka sani wadda baka sani ba baka sanshi ba ashe Safiyya mace ce”


Abunda ta faďa kenan tana kokarin tashi tsaye,da nufin komawa saman gado ta zauna.




                    ******        ******       ****


MINAL.................

  Safa da marwa kawai take cikin falon, tana busar da iskar baki. Tun kairat na kallonta har ta gaji tayi mata magana,


“Wai lafiyarki Sis kike wannan yawon haka.?”


Da sauri tazo kusa da ita ta zauna, fuskarta cike da tsananin damuwa tace


“Sis Deen ne nayi da kiran wayrsa bai ďauka ba daga karshe ma sai kashewa yayi har yanzu fushi yake dani ya kasa fahimta ta”


Wani dogon tsaki Kairat taja,


“Deen! Deen!! Deen!!! haba Minal miyasa ba zaki aje shi a inda ya aje ki ba har yashe zaki fita harkar sa ne aure fa zakiyi kuma ke da kanki kike faďa min Saif yace kiyi masa alkawarin ba zaki kara kula sa ba  yanxu Deen ďin nan ya fita harkar ki ai kodan haka yaci ace kema kin kyale shi”


Tashi tayi tsaye a fusace, ta nufi hanyar Upstairs tana faďin,


“Ai daman nasan ke ba fahimta zakiyi ba, shekarar mu nawa tare yanzu yana fushi dani ace bazan bashi hakuri ba, ko an faďa miki abota karya ce shashasha kawai”



Da ido kawai Kairat ta bita tana kaďa kai,


“She kenan kije yi ta yin abunda kike ganin yafi miki wadda bai ji bari ba yaji hoho” 





                     **********************



“Amincin Allah ya tabbata a gareka ya kai wannan natsattsen matashi”


A hankali ya ďago kai ya kalleta. a nan ta cire katon bakin gilashin dake makalle idonta cikin tattausan lafazi tace,


“Sarki ya tabbata ga Ubangijin wannan halittar,

Hakika kana da kyau, da kwagiji kana da cikar kamala da sanya zuciyar yan mata faďuwa, babu wata mace zaka ce kana sonta ta kika sai idan tana da wata manufar ne da daban, 

   Mutum ne kai mai rikon amana wadda har hakan yasa Minal ta aminta da kai kai kuma ka bata kanka ka zamo mata raqumi tana jan akalar daga karshe tace amanar ka, wadda ko kwankwanto babau nasan zaman da kayi a wannan gurin ita kake tunani”


Kallon natsuwa yayi mata, shidai bai ta6a ganinta ba sai dai fuskarta tayi masa kamada fuskar wadda da yasani,


“Wacece ke.?”


Ya tambaya yana mata wani kallo, idonsa a jawur kamar wadda yayi shaye-shaye, murmushi ta sakar mashi sannan tace,


“Sunana SAFIYYAH BASHIR BATURE kanwa gurin SAIF BASHIR BATURE zan iya zama.?”


_Safiyyah Bashir Bature_  cikin zuciyarsa ya maimaita sunanan yana kallon mutanen dake zaune gurin shakatarwa kamar mai neman wani.

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO. 


       NA


KHADEEJA CANDY 


Candynovels.wordpress.com 


WATTPAD @khadeeja_candy



*24*



“Saif tun ɗazu ne yazo i was so sad...” 


Hannu ya ɗaga mata, fuskarsa a haɗe


“Minal kin dame ni da labarin Deen bana da alaka dashi so please ki daina min a maganar sa” 


ta ɗan gyara zamanta, ta fuskance shi


“Am sorry but ni yanzu yana ganin naci amanarsa fa” 


Banza tayi mata kamar bai jita ba, zuwa can ya kalleta yace, 


“Minal kinsan abunda nake so dake” 


“A'a” 


“So nake kiyi min alkawari ba zaki sake kula wani namijin ba ba zaki sake saka tufafin da zasu fitar miki da tsiraici ba, ba zaki sake kula Deen ba da duk abinda ya shafe shi” 



“Saif Deen abokina ne fa” 


“Ni kuma mijinki ne just promise me Baby”


Baza iya masa alkawin rabuwa da Deen ba ko kuma kin kula shi dan haka yasa ta tashi da nufin shiga cikin gidan, 


“Ok i wll thing about it”


Da sauri ya riko ta yana dariya, daman yasan abune mai wahala tayi ta rabu da Deen yanzu,


“Common Minal karkice min kinfi son Deen da ni”


Dawowa tayi ta zauna,


“Saif kana da muhimmanci a gareni kana babban gurbi a zuciya matsayinka daban matsayin Deen daban bana son kana haďa matsayin sa da naka,

 Saif yanzu Deen yana kallo na a matsayin mace da taci amanar ya kamata na goge wannan shatin da idonsa sukayi mani” 


“Fine”


Kawai yace ya tashi, ya nufi kofar da zata fitarshi daga Garden ďin,

  Da hanzari ta cigabansa, 


“Haba Saif daga magana sai kayi fushi”


“Dole nayi fushi Minal nifa wadda zaki aura taya kike ganin zan iya jure kina magana da wani me kike son mutane suce ta kike son a kalleni.?”


Shiru tayi yana nazari, wani gurin yana da gaskiya sai dai ita kan bata iya rabuwa da Deen yanxu,


“Ok i wll i promise amman Saif Deen ba yanzu ba i want to talk ko him”


Kafaďunta ya dafa,


“Fine amman ba just at onces”


Kai ta ďaga masa, azuciyarta kuma ba daďi.

   Hannunta yaja ta rakashi har gurin Motarsa.




                      ******     ******     *****


“Ku ajesu a nan”


Yace da yaran da suke ďauke da akwatuna, yana nuna musu gurin da zasu aza,


Sai da suka gama jearasu tsaf sannan suka fice. Shi kuma ya xauna saman kujera yana kwalama uwar gidan kira


Da Sauri ta sauko downstairs, ďaure da tawul, jikinta kuma da sanyin ruwa, da alama wanka ta fito.

  Murmushi yayi mata,


“Oh wanka kika fito ne”


“Ae dear waďannan kayan fa.?”

 

Ya kishingiďa da kujeara yana sauke ajiyar zuciya,


“Gasu nan dai duba ki gani”


Ba musu ta shiga buďe akwatu nan zuciyarta cike da fargaba,

  Kayane na gani na faďa masu kyau da tsaďa babu abunda babu cikin tun daga kan kayan kwaliya zuwa na shafe shafe su tufafi ba a maganarsu, 


Bayan ta gama dubawa ta ďago da raunanin, idanu ta kalleshi,


“Na gani Saif kayan waye.?”


“Naki ne ko baki so.?”


“Nawa fa kace?”


“Ae Momi tace na siya na kawo miki abunda babu sai ki faďa min kuma duk abinda kike so ki faďa min”


“Momi fa kace Saif ka fito kayi min magana ban gane inda ka dosa ba”


Ya ďan daďe kamin yayi mata magana dan yasan maganar ba zata mata daďi ba, ita kuma ta sakar masa ido tana mai kallon jiran amsa,


“Kayan faďan kishiya ne nan da sati biyu zanyi aure insha Allah”


Bushewa tayi da dariya, duk falon ya cika da amonta, ta nuna shi da tsaya


“Haba dai Saif bana son irin wannan wasan fa ni kasan babu abunda na tsana irin ayi min wasa lokacin da nake gaske”


Kallon, kur yayi mata,


“Ba wasa bame sweetheart wallahi da gaske nake”


Tashi tayi tsayi, fuskarta babu annuri,


“Au ashe da gaske da ake faďar kara aure zakayi ina karya tawa yau har ya rage sauran sati biyu a ďaura maka auren, kai ko kunya baka ji ka buďe baki ka faďa min har ka ďebo wannan hegun kayan ka kawo min nayi me dasu tsirara ka ganni ne amman ban ta6a sanin kai azzalumi bane sai yau Saif”


Kalamanta sun fusata shi dan shi ba irin mazan nan bane masu tsaya mata na faďa musu magana son ransu ba,


“Ke kimshin haukarki ya tsaya kanki karki kuskura faďowa kaina wallahi zaki raina kanki duk abunda zakiyi sai dai kiyi amman bazan fasa aure nan ba tunda iayayena basu hanani ba babu wadda ya isa ya hanani”


Bai jira cewarta ba ya nufi hanyar ďakinsa. Ita kuma ta shiga ďiban kayan  tana zubarwa tana kuka,


“azzalumi wallahi ba za'ayi wannan auren ba mugu ni zaka ďasawa bakin ciki wallahi sai ka raina kanka”


daga nan ta zuba da gudu ďakinta, tana ihu kamar mahaukaciya.Kasan carpet ta faďi tana murje murje da kiran ta shiga uku, ta daďi a haka can wani tunani yazo mata da sauri ta nufi gurin wayarta.

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO


       NA


KHADEEJA CANDY 


Candynovels.wordpress.com 


WATTPAD @khadeeja_candy 



*26*


Daf da zata tura kofar falon ta shiga, Saif ya buďe ta ta fito yana gyara hannun rigarsa, da sauri ta gaishe shi


“Yaya ina wuni”


“Lafiya kalau Safiyyah ina kika fito haka .?”


“Daga gidan wata kawata nake sai nace bari na biyo fita zakayi ne.?”


“Ae zan ďan leka gari ne kinsan yau sunday amman Huda tana ciki ai”


“Okey Allah ya tsare bari na shiga mu gaisa,”


Ra6awa tayi gefensa ta shiga falon tana faďin daman ai ba gurinka nazo ba.

  Kujera ta samu ta zauna,sai da taji tashin motarsa sannan ta kwalama Huda kira. 


“Anty Huda fito gani a falo”


Ta ďan daďe zauna kamin ta tashi, ta nufi hanyar falon, Tun kamin ta sauko kasa ta haskaka fuskarta da murmushi, bayan ta sauko ta zauna kusa da ita tana faďin


“Sannu da zuwa yan matan Hajiya”


“Yauwa ya gidan?”


“Lafiya, aiko yanzu Yayanki ya fita”


“Ae na gamu dashi ai har mun gaisa daman Allah Allah nake karna tarardashi”


“Hmmm ai yanzu bai fiye zama gida ba kullum busy yake”


“Ki kwantar da hankalinki mijinki ya kusa dawo wa gareki nan da wasu yan kwanaki”


Huda ta gyara zamanta ta dafata,


“Amman safiyyah ta wace hanya kike ganin zaki iya hana auren nan.?”


“Ta harya da muka shirya nida Sauranyinta idan ya amince”


“Saurayinta kuma waye kenan”


“Abokin ta ko kuma ma nace amininta wadda yakr shirin aurenta taki aurenshi ta za6i Saif”


“Me zakuyi kenan zai aure ta ne?”


“A a na aurenta zaiyi ba ai yanzu babu yadda za'ayi ya iya aurenta saboda an riga ansa rana yanzu haka daga gurinshi nake kuma idan har ya amince ana ďaura auren auren zai mutu”


Sam maganar bata yima Huda daďi ba dan ita so take a hana auren ba wai sai anyi a lalata ba, toh idan kuma hakan bai yiyu ba fa zamansu na aure zasuyi wadda ita kuma ba zata iya jurar ganin mijinta ta ko wace mace ba. 

   Cikin yanayin damuwa ta kalli Safiyyah,


“Amman kina ganin hakan zai yiyu kuwa karfa aje ayi auren daga karshe yaki rabuwa ni wata qawata ma faďa min take na shiga malamai nasa a lalata auren”


Safiyyah ta girgiza mata kai,


“Ban yarda da wannan ba ban baki shawarar shiga malamai ba dan ba hanya bace ni nan ni na tsara komai kuma ina son ki bar min komai a hannuna kawai abunda nake so dake ki daina nuna masa kishi da damuwa ki nuna masa kin yarda da kaddara” 


“Zanyi amman ina son kiyi min alkawarin ba za a samu matsala ba”


Tashi tayi tsaye ta rataya jakarta, tana faďin 


“Nayi miki bari naje gida kar Momi ta neme ni dan tun safe na baro gida Gurin Deen na daďe shiyasa kika ga ban zo nan da wuri ba”


“Ok zanyi duk yadda kika ce Allah ya bamu sa'ah”


Murmushi tayi, har ta juya sai kuma ta juyo tana wani abu da baki,


“Kafin na manta zaki bamu tsohon saurayinki aro dan shima zanu anfani dashi”


Dakan uku-uku gaban Huda yayi, wane tsohon saurayinta take magana ne, ya akayi tasan har yanzu suna tare, ina ma ta sanshi, cikin ranta take wannan tunanin nurmfashinta na wani abu irin na marasa gaskiya,


“Mi kike nufi ne ban fahimta ba”


Cikin karfi hali da taku tayi mata tambayar. Safiyyah ta bushe da dariya twyi kwallon cingan ďin dake bakinta,


“Kinfi ni sanin abunda nake nufi mana anty Habib nakr nufi tsohon saurayinki na da da yanzu abokin mijinki”


Zaunawa Huda tayi saman kujerar da raunanin idanu gumi na karyo mata. Nan Safiyyah ta kai hannu ta dafa kafaďarta,


“Ki kwantar da hankalinki na daďe da sanin kuna tare tun kamin ki auri Yaya ammanbban ta6a faďawa kowa ba yanzu ma dan kawai ta kama sai munyi amfanin dashi ne da bazaki sani ba”


Huda bata iya ce mata komai ba sai kawai ta bita da ido tana kallonta har ta fice. sannan ya jingina da kujerar tana mamakin yadda akayi tasan suna tare, toh ko dai itama yana tare da ita ďin ne, ko kuma wanine ya faďa mata amman kuma wayasan suna tare balle ya faďa mata, ? toh ya akayi tasan suna taren ne.? wannan tambayar ita ta tsaya mata a rai.


                           *****************

“Mummy wai...-”

 

Ganin hawayen dake idonta yasa Minal ta kasa karasa maganar ta nufeta da sauri tana tambaya 


“Lafiya Mummy kike kuka mi akayi maki ne.?”


Ďagowa mummy tayi da murmushi a fuskarta tace,


“Hawayen Farin ciki ne Minal bana bakinciki ba ashe zan ga wannan ranar da zan rika katin ďaurin aurenki a hannuna”


Rumgumeta Minal tayi,


“Ai kinsan Mummy komai lokacine dashi kuma yadda duk Allah ya tsara wani bai isa ya sauya shi ba”

“Haka ne Minal nayi farinciki na jidađi sosai ko ina zan aika wannan katin (iv) har gurin dangina”


A nan Minal ta gyara zamanta ta gaďiye yawun dake bakinta,


“Yauwa Mummy kinsan inda dangin mahaifina suke.? zaki iya kwatanta min su?”


Maganar sam batayi ma Mummy daďi ba, a fuskarta ma karara zaka iya karantar hakan,


“Miyasa Minal.? miyasa ke zaki neme su bayan su basu nemeki ba mi zakiyi musu.?”


Kwantowa tayi jikin Mummy, ganin yadda fuskarta ta nuna rashin jindađin maganar da tayi mata, sai ta canja manufar maganar ta


“Ni mi zan musu kawai dai zan yima masa cin mutunci ne jifa yadda na wulakanta ni”


Kanta Mummy ta shafa, tana sauke ajiyar zuciya,


“Basai kinyi mashi ba Allah yana kallo ai shine zai saka miki ki kyaleshi kinji.?”


“Okey my Mummy bazan sake ba”


“Allah yayi miki albarka yabkara miki lafiya”


“Amin mummy bari naje zamu duba gurin da zayi diner ne da irin kwaliyar da za'ayi masa”


“Ok sai kin dawo ki kula da kanki”


Murmushi tayi, ta tashi ta fice. Mummy kuma ta janyo wayarta ta shiga kiran masu fanti.



                      *☆ ☆ ☆ ☆ ☆ ☆*


Shi na mussaman Mummy take, dan ko zama yanzu bata samu, bayan tasa ana gyara mata yar'ta, sai ita kuma ta shiga gyaran gida, da kuma maida hankali gurin shiraruwan biki.

  Kullum mai dilka take zuwa tayi ma Minal, abunda da mai kyaun jiki cikin kwana biyu ta canja kala tayi kyau sosai batar jikinta ta wani taushi kamar kaďa, Yau ma kamar kullum tana zaune ana gyara mata jikin Safiyyah ta turo kofa ta shiga cike da natsuwa, kamar ba ita ba,

   Da sauri Minal ta tashi tsaye tana kallonta,


“Yau kuma da wace kike zo wane kalar cin mutunci kika zo dashi.?”


Minal ta tambayeta tana yatsinar hanci alamar masifa, dan yau koma da wace tazo ba raga mata zatayi ba, wacan karon ma dan bata da tabbacin son da Saif yake mata ne yasa ta kyaleta, amman yanzu kan sai ta mata tas tunda cin mutunci ba gado bane kowa ya iya,


A hankali ta dako kafarta har kusa da Minal, idonta cike da hawayen qarya ta soma magana,


“Banzo dan na 6ata miki rai ba Minal nazo ne danna nemi yafiyarki akan abunda nayi maki, ada ina ganin kamar ba daidai bane Yaya ya aure saboda abunda nake ganinki dashi a zahiri, sai Yaya ya zaunar dani ya karantar dani wacece ke ya kuma nuna min halinki, Minal na gane kuskure na kuma ina neman yafiyarki dan Allah ki yafe min”


Da sauri Minal takai hannu ta share mata hawaye,


“Daina kuka, ni daman ban rike ki da komai ba na yafe miki kuma naji dađi da kika gane haka”


Da kuka ta Qanqameta tana fađin na gode sosai Minal,

 Abunda da wayayyiyar mace nan da nan ta murje ido kamar ba ita ba sai jan Minal take da fira, tana yaba kyauta da fađin wai yayansu yayi dace,

Sai kusan magari ba tabar gidan bayan Minal ta cika mata bayan mota da alherai babu yadda ba tayi ba akan ita ba zata da komai amman minal ta rantse sai ta jedasu hakan yasa dole ta yarda tana mata godiya har ta bar gidan.



Babu inda Mummy batw raba Iv ba, sai faman zirga zirga take za ayima yar gwalo aure, kowa farinciki yake agidan banda Kairat da sai dai ta nuna a fuska amman a ranta jin take kamar an ďaure ta da sarqa.

    

Anko kusan kala shida akayi dan ko wane event sai da ka fitar masa da kalar kayan da za'a saka, Amarya kan aba'a magana dan tsaddandin kaya Mummy tasa aka ďinka mata banda waďanda ango ya kawo mata ga kuma na lefe,

   Tun daga Sokoto aka ďauko maiyi mata lalle da kitso. 

Ranar laraba akayi sa lalle, kuma ranar akayi anki amarya kamar yadda al'ada ta tana da, washe garin ranar akayi kamu. ranar jumma'ah akayi walima da daren ranar akayi arabiya night, A maimakon dina.

  Ranar assabar akayi ďaura aure bisa sadaki dubu hamsi ďaurin auren da yasamu halartar manyan yan'siyasa da masu hannu da shuni da kuma manyan yanbkasuwa har ma da yan kasashen waje abunda dai sai wadda ya gani, maroka kan an kwashi kuďi kamar ciyayi, Ango yayi kyau matuka kallo ďaya zaka masa kaga anihin zatinsa saboda yadda kayan suka kar6i jikinshi.


Sa maraicen ranar yan 6angaren amarya sukayi Fulani day, abun gwanin sha'awa kowa sai yabon bikin yake yan ďaukar hoto da bidiyo kullum sai sunyi aikinsu, sai kunga yadda Safiyyah ta saki jiki tana shigema amarya kamar ba ita ba,

   Babu irin mutane  da ba'a gayyato ba girin bikin har da mawaqan kudu Rahama sadau sune gaba gaba da Adam a zango cikin waďanda aka kayyato nan arewa, 

 Anyi 6arin kuďi kamar ba'a san zafin neman su ba, nikan nace ai kara da sukayi dan _idan da dama, dawo, adama asha da dama. ayi ta riya_ 😀



Da daren Ranar motocin ďaukar amarya suna iso, haka aka jerasu yadda kasan gwafna zaije kanfe, ko wace mota na tashi da wakar auren da Nura m inuwa yayi musu, kalolin motocin ďaya ko wace bak'a,

Nasiha sosai Alhaji Ibrahim Ahlam yayi mata, kasancewar daga gidansa za a wuce da ita gidan angonta, mummy kuma tun kamin tazo tayi mata tana, Kuka sosai Minal take na rabon da dayi da Mummy da kuma ganin yadda ita Mummy take kuka, sai kace waďanda suka rabu har abada,


   Daker aka sakata, Kairat sai hanquri take bata tana kukan itama wadda ya zame mata biyu, riqe take da hannun Kairat har aka isa gidan angon nata.

  Gida na gani na faďa tsabar haske sai kace da rana ne, ko ina na gudan fulawoyi ne.

 A hankali aka fito da amarya bayan an buďe mata motar, falo sai kace aljannar duniya, dan bazaka ta6a gane najeriya kake ba sai ka fito waje,

         Har cikin ďaki suka kai ta suka zaunar da ita saman gadon tunda Allah ya hallince ban ta6a ganin irinsa ba tsaya kwatanta muku yadda kyawon ďakin yake 6ata lokacine.

    Basu fi minti ashirin da zama ba, ango ya iso tare da abokansa sai tsiya suke masa, sai kace yanzu ne yayi auren fari, Kallo ďaya Kairat tayi masa ta ďauke kai shi kan ko inda take bai kallaba, ita dashi ango sukayi dan ita blue shadda tasa irin tashi.

   Bayan anyi abubuwan da al'ada ta tana da suyi musu sallama suka fice, har bakin kofar falo Saif ya rako abokaninshi yana musu godiya, su kuma sai sheďana suke masa.

    Da suka fice, ya umarce masu gaďi da su rufe masa gate, shi kuma ya rufe kofar falo, ya nufi hanyar ďaki,


Kanta a kasa ya tararda ita, cikin wani kyakkyawan mayafi da alama kuka take, baiyi mamakin kuka nata ba tunda yasan duk mace d bat ta6a aure ba sai ta samu kanta cikin wani kalar yanayi,

   Kusa ita ya zauna yasa hannu ya yaye mayafin dake jikinta yana murmushi,


“Kuka name kuka Minal tashi zakiyi muyi alwala muyi sallah nafila mu gude Allah ko”


Kai kawai ta ďaga masa alamar eh idonta na kasa ta kasa ďagosu ta kalleshi, ganin hakan yasa ya cire babbar rigarsa ya rika hannunta suka nufi banďaki,

   tare sukayi alwalar suka fito, ya shimfiďa musu abun sallah bayan ya mika mata katon hijab. Raka'a biyu sukayi, suka sallame sannan ya rika kanta yayi mta add'ah kamar yadda Annabi ya koyar damu, 

  Sannan ta tashi ta ďauko plate da kofi ya zuba mata kaza da madara wadda aka aje a gefe sai kace kantin sai dasu, ya shiga bata da kansa tana ci a hankali kamar wata karamar yarinya, madarar da zai bata ma sai da ya kwatar da ita saman jikinsa, sannan ya bata, bayan sun gama ya goge bakinsa ya goge mata nata, maida plate ďin azauninsa ya buďe akwatin kayanta ya fiddo mata kayan bachi ya mika mata,

   Hannu biyu tasa ta kar6a kamar yadda Mummy ta karantar da ita, duk rashin kunyar Minal yau sai ta samu kanta da kasa saka kayan gaban Saif wani irin nauyinshi take ji, dan haka ta nufi banďaki ta kulle kanta sannan ta saka kayan bachin, 


Koda ta fito shima ya saka nashi, akasale ta karaso ta aje kayan data cire saman kujera. Bata ankara ba taji ya ja mata hanci yana dariya,


“Wai yau Minal kunya ta kike ji ne.? nifa ban gane wannan noce noce kanba kodan na rabaki da Mummy yau?”


Ita dai har lokacin bata iya ce masa komai ba. Ganin hakan yasa ya nuna mata gado,


“Hau ki kwanta nasan kin gaji da yawa yanzu nima bachi nake ji”


Ba musu ta nufi gadon ta kwanta, nan shima ya kashe wutar ďakin yazo bayanta ya kwanta yaja bargo ya lullu6e ta, ya kuma lullu6e kansa.

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO


       NA


KHADEEJA CANDY 


Candynovels.wordpress.com 


WATTPAD @khadeeja_candy 



*27*


Bayan ya shafa addu'ar da yake, ya tashi daga saman sallayar ya nufi gadon, Bargon da ta rufa dashi ya fara janyewa, ya hura mata iska a hankali cikin kunne ya raɗa mata


“Tashi kiyi Sallah Bakwai ta kusa”


Cike da nauyin bachi ta buɗe idon ta kalli kyakkyawar fuskarshi daya kawata da murmushi, murmushin ta mayar masa sannan tayi unkurin tashi tana mika,


Bayan ta kare Sallah yazo gefenta ya zauna, ya zuba mata ido yana kallonta, sai da ta shafa addu ah sannan yace,

 

“Ga abinci can Mummy ta aiko tun ɗazu kuma tace zata sake aiko wani”


Juyowa tayi cike ta ladabi tace


 “Ina kwana”


“Lafiya kalau kin tashi lafiya”


Da murmushi ya amsa mata yaji daɗi sosai, abunda huda bata saba masa ba tun zuwanta gidan, wai ita a ganinta ka kwana gida ɗaya da mutun kuma da safe ka gaidashi, ita a gurinta bako akeyima haka.


“Lafiya kalau”


“Toh. yayi kyau sai ki tashi muje muci abinci dan Mummy tace baki jikirin yunwa tunda uwar safiya kike karyawa”


“Laaaahhh”


Ta ɗan zaro ido tana kallonshi, 


“Yaushe tace maka kodai kai kace da kanka.?”


Taɓe baki yayi ya ɗan juyarda fuska,


“Ta dai ce ke, sai idan mistake tayi ko bake take nufi ba, amman kuma idan ba ke bace mi yasa ta kawo wannan abincin da wuri haka tun gari baiyi haske ba”


Murmushi tayi mai sauti,


“Kawai malam kace min yunwa kake ji na tashi mije muci abinci ba wai ka ɗinga wani noke noke ba”


“A'a walllahi ai ni nakan kai sha biyu ma ban karya ba kuma jikina lafiya kalau ba kamar ke ba daman ace marasa kiba sunfi cin abinci”


Tashi yayi ya rika hannunta,


“Muje kiyi buroshi sai muci abincin”


Bathroom ya nufa rike da hannunta, Da kanshi yayi mata buroshi sannan yayi ma kanshi suka fito, a nan ya ɗauketa kamar wata yar baby ya nufi dinning room da ita, ita kuma ta shigar da kanta cikin kirjinsa sai faman dariya take tana faɗin ya sauke ta zata iya tafiya.


Sai da ya sauke ta saman kujerar sannan yace, 


“Ai nasan zaki iya tafiya kawai bana son ki wahala ne” 


Dariya tayi, shi kuma ya kashe mata ido ya shiga zuba mata abincin. 

    Da kanshi ya rik'a bata tana ci har sai da ya tabbatar da ta koshi sannan ya soma cin nasa, ido ta kura mishi kamar ba taɓa ganinshi ba, bai ankaro ba har sai da yq sarke da ruwan tea daya kuɓa, 


“Ke kus kici kanki wannan kallo har ina kika kokarin sa na ka sarke” 


Dariya tayi, ta tashi ta nufi kofar da ake bugawa, 

   Direban Dr. Salamatu ne rike da manyan kuloli da katon kwando gabansa, 

   Cike da girmamawa ya gaisheta, yace


“Wai gashi inji Hajiya tace a kawo muku kuma tace a gaida ku” 


Kofar ta kara buɗe masa, 


“Shiga dasu ciki amman kai ta aiko ɗazu.?” 


“A a” 


Ya faɗa bayan ya aje kalolin, sannan yasa hannu aljihu ya ciro wayarta ya mika mata, 


“Ga wayarki inji Kairat” 


Kai kawai ta ɗaga masa tana mamaki, ta mika hannu ta karɓa, shi kuma ya fice. 


Rufe kofar tayi, ta nufo Saif yana faɗin, 


“Toh Mr stomach ga wani abincin nn Mummy ta aiko” 


“Wace Mummy.?” 


“Mummy na mana” 


Ta bashi amsa daidai lokacin da ta zauna saman kujerar dake fuskartarshi, 


“Toh waya aiko da wannan? Ba mummy bace” 


“I don't think so dan kasan bazata aiko da abinci biyu lokaci ɗaya ba” 


“toh waya kawo.?” 


“Kai ya kamata na tambaya” 


“Wani ne ya kawo i thought ko direban Mummy ne” 


Minal ta ɗan yatsine hanci, 


“Or maybe aljani ne” 


Wata irin dariya yayi, 


“Daɗin abin dai tare muka ci ko! Ni har kinsa ma naji na koshi” 


Itama dariyar tayi, ta tashi da sauri ta nufi ɗaki ganin yadda ya nufota.






Guraren biyar da rabi motar Safiyyah  ta faka a gidan Minal, ta ɗan daɗe kamun ta fito cikin motar ta nufi babbar kofar falon, 

      Tana tura kofar falon kanshun turaren wuta ya daki Hancinta, 


   “Ina wuninku” 


Tace da mutanen data tarar zaune falon cikin far'ah, 

  Duk suka amsa mata da lafiya kalau suna mata ya gida, 


“Lafiya kalau ina Anty Minal?” 


“Tana ciki wuce” 


Ta fan gudu ta hau stars ɗin ta shiga ɗakin ta take zaton Minal ta ciki, katsancewar ɗakunann ba ɗaya bane, 


Cikin sa'ah kuwa ta tararda ita zaune ita da wasu friends nata suna fira, 

   Da far'ah Minal ta tarɓeta, tana nuna mata kujera, 

 

“Lallai Safiyyah sai yanzu tun ɗazu su Lubna suka zo har sun wuce” 


“Ayyah Anty wallahi naɗan je wani gurin ne shiyasa bamu zo tare dasu ba kiyi hakuri” 


“Babu komai tunda dai kinzo ai ya gidan” 


“Lafiya kalau ya Amarci” 


Minal ta ɗanyi kasa da fuskarta, tana faɗin


“Bari a kawo miki abinci  Jannat Please kice da Fillo ta zubo abinci” 


Wadda aka kira da Jannat ɗin ta tashi, tana gyara mayafinta da faɗin, 


“Okey bari daga nan ma na wuce kindai ji abunda na faɗa miki” 


Tashi sauran kawayen nata suma sukayi tsaye, wadda hakan yasa ita ma Minal ta tashi,


“Haba ku kuwa yanzu zakuje dan Allah ku bari sai isha i mana” 


“Au so kike angon yace mun matsa masa kenan a a ai ko yanzu munyi maki wuni ina laifi kar kisa idan munzo yace ba zamu shigo ba”


Ɗayar ta faɗa tana zaro ido, nan duk suka bushe da dariya suna mata addu'a Allah bada zama lafiya, 

  Ɗankwalinta ta ɗauko ta ɗaura tana wani abun da fuska kamar mai shirin yin kuka, 


“A'a dan Allah karki mana kuka bafa angon bane, ɗankwali kika gani ba hula ba”


Kai kawai ta rausaya tana murmushi ta rufe masu baya,


“Anty dan Allah ďan aro min wayarki”


Daf ta zata fice Safiyyah tayi mata maganar, juyowa tayi yana nuna mata gurin madubi,


“Gata can kan mirron bari na rakasu na dawo”


“Okey ba matsala”


Tana fita, Safiyyah tayi saurin nufar gurin da wayar take ta ďauka, tayi sa'ah bata da password, dawo wa tayi saman kujerar ta zauna ta shiga kiran wata numbar da wayarta, bugu ďaya aka ďauka,


“Yanzu zan fara ina son kayi komai cikin sauri”


Yata faďar hakan ya kashe wayar, tana kallon kofa,ta ďauki wayar Minal tana danne-danne jikinta sai rawa yake kamar mazari, wayarta take kallo tana rubuta abu a wayar Minal da alama sakone ko wani abun mai kamada haka,

   Har tayi ta gama Minal bata shigo ba, daďi yaji sosai ta mayarda wayar mazauninta tana busar da iskar bakinta da kaďa ido, ta ďan ďauki lokacin kamin ta taso ta fito ďaga cikin ďakin ta nufo falon,

 

  Bata isko mtanen data wuce ďazun ba sai wasu yan mata biyu, 

 

“Ina anty Minal.?”


Ta tambayi ďayar tana kallon kofar kicin,


“Tana ďayan falon a kirata ne?”


“A a indai tazo kice mata na wuce”


“Okey.zan faďa mata”


Bata tsaya komai ba ya bar falon cikin gaggawa, kan kace kwabo har tabar gidan.

 Minal kan sai da ta gama sallamar abokaninta sannan ta tuno da Safiyah da sauri dayo ďaki, ganin bata ganta ba yasa duk ta shiga damuwa, tunani kawai take tana ganin Safiya ganin zatayi tayi mata wulakanci.


Bayan sallah isha'i Saif ya shigo gidan, bai bari ta ganshi ba har sai da yayi wanka ya shirya cikin kayan baci sannan ya nufo ďakinta ďauke da ledodin dake hannunsa, tana zaune gaban madubi taji k'anshin turarensa ne ya daki hancin hakan ya tabbatar mata da ya shigo ďakin,

   juyowa tayi ta kalli k'ofa yana jingine sai kallonta yake yana murmushi, itama murmushin ta mayar masa ta taso ta nufi wadurof ta buďe ta fiddo wata doguwar riga ta yaďi kalar kore ta ďora saman gaďo, da hanzari ya karaso kusa da ita ya aje ledar hannunsa ya rumgume ta ta baya yana shakar kanshin dake tashi daga wuyanta,

  Lumshe ido tayi ita ta maida numfashin a hankali, wani kalar yanayi ta soma jinta ciki shi kuma yana kokarin wuce gona da iri sai cakuďata yake yana kokarin janye tawul ďin daga jikinta, 


“Saif zansa riga kasan kace idan ka dawo zaka kaini na ba Safiyyah hakuri”


Ta kokarin kwace kanta tace masa haka, a maimakon ya saketa sai kawai taga ya jara janta jikinsa ya rumgume idonsa a rufe ya raďa mata,


“Ke baki san wasa bane taya zan barki ki fita yanzu ni ba da gaske nake ba”


Cigaba yayi da abunda yake mata yana kokarin kwantar da ita saman gadon, cizo ta kaibmasa a hannu ta murďe masa kunne har sai da ya saki yar kara ya saketa ya kwanta rairai yana faďin


“Kai Minal kin cika matsala wai mi kike so ne.?”


Tashi tayi tana ďan turo baki


“Nace ka kaini gurin Safiyyah kaki kuma ni yunwa nake ji”


Daker ya sauko saman gadon ya zauna kasa yana faďe ledar


“Zo ga Pizza da madara”


Da sauri ta sauko tana gyara ďaurin tawul ďin nata ta zauna gabansa ya rika sa mata a baki tana ci, zuwa can, cin abincin ya canja salo tun tana kiya masa har ta hakura ta zuba masa ido.



Washe gari, bayan yayi wanka yazo ya tasheta ya ďauketa da kansa ya kai banďaki yayi mata wanka, sannan ya barota ta ďora dana tsarki tayi alwala ya fito da ita, Tufafi ma shine ya sa mata, har hijab sannan suka kabbatar sallah asuba, 

   Bayan sun kare bata ko tsaya addu'ah ba ta koma saman gadon ta cigaba da baci.

Bata farka ba sai goma har da yan mintuna, koshi badan ta gaji da bacin ba sai dan yunwa ce ta tasheta, zaune da ganshi jefen ta ya zuba mata ido yana murmushi, a nan ta turo baki tana masa kuka,

Hannu yasa yaja bakin nata yana kwaikwayar kukan nata, da buga kafafu irin yadda take tun tana yi da gaske har abun ya koma bata dariya ganin yadda ya marairaice kamar karamin yaro yana koyonta. dariyar da tayi yasa ya jata jikinsa ya rumgume yana faďin 


“Haba ko ke fa kin tashi kinga masoyinki kusa dake ba sai kiyi farinciki ba amman kina min kuka”


Ta ďan turo baki,


“Toh ba kai bane”


“Nine da nayi me faďa min mi nayi”


Ya tambaya yana mata wani kallo da murmushi, sai kawai ta rufe idonta ta 6oye kanta cikin kirjinshi. kiss yayi mata cikin gashin yace


“Tashi muje kiyi break fast tun ďazu ke nake jira fita nake son yi”


Ta ďago ta ďan hararesa, 


“Fita Kuma, kaje ina.?”


“Bafa nesa zanje ba kawai gurin Momi ne sai kuma gurin Aiki saboda meeting ďin da zanyi da wasu jafanis kuma Dad yace dole nine zanje shiyasa kawai zanje amman ina karewa zan dawo i promise you”


Kuka ta shiga k'irk'iro masa,


“A gaskiya nima toh sai na fita bazan daďe ba zan dawo”


Sauka yayi saman gadon, ya ďauke caf ya nufi hanyar falo yana faďin


“Rufa min asiri fitarki ba yanzu ba”


“Ni gaskiya sai naje sai na fita daman ina son fita”


Ta faďa dai-dai lokacin daya sauketa saman kujera ya shiga zuba mata abinci, yana murmushi, ita kuma sai wani turo baki take ala dole tana fushi, baibi ta kanta ba ya ďinga ďura mata abinci har sai da ya tabbatar da ta koshi sannan ya maidata ďaki, yana mata cakulkuli aiko ta hau dariya kamar ba ita. Nan ma wasan canja salo tayi sai da ta sallame shi sannan ya bar mata ďakin ita kuma ha hau baci.


   A gaggauce ya shirya saboda kiran wayar da ake matsa masa dashi, sai tsaki yake ja wai mutun yayi aure ďan hutun sati ďaya ma ba za'a barsa yayi ba, cikin black suit ya shirya bar gidan.


                              ****        ****       ****

 Momi na zaune ďakinta Safiyyah na kwance saman kafafunta wayarta tayi ringing, Safiyyah ce ta tashi taje gurin wayar ta ďauko mata ganin numbar Saif yasa ta danna picking ta mika mata,


Momi ta kar6a ta kara a kunne cikin sallama,


“Assalamu alaikum Saifullahi”


Daga ďayan 6angaren ya amsa mata,


“Na'am Momi an tashi lafiya.?”


“Lafiya kalau ya gidan naka.?”


“Lafiya kalau Momi nace bazan samu biyowa yanzu sai zuwa anjima saboda meeting ďin da Dad ya tura ni yanzu haka ma ina kan hanya”


“Toh ai da yanzu da anjima duk ďaya ne Allah ya kaimu”


“Amin Momi sai nazo”


“Toh...”


A nan ta kashe wayar, tana murmushi, Safiyyah ta kalleta


“Momi mi yace ne.?”


“Wai ba zai samu zuwa ba, sai anjima zaije miting yanzu”


Momi ta bata amsa tana dannar wayar, Zaunawa tayi kusa da ita kamar mai tunani tana kallon wayar Momi.

  Zumbur! ta tashi tsaye kamar an tsakareta har sai da Momi ta kalleta,


“Ke lafiya?”


“Lafiya kalau Momi indomie dake kan wuta na tuno”


Ta bata amsa da sauri ta fice. A maimakon ta nufi kicin ďin sai kawai ta nufi ďakinta, ta kulle kanta ta nufi gurin wayarta ta ďauka ta dannan ma Huda kira,

   Ringing tayi tayi tana katsewa bata ďauka ba hakan yasa taja tsaki ta ďauki gyalenta da makulin motar ta ta fice.

  A harabar gidan Saif ta faka motar ta ta fito a uzurce ta shiga cikin gidan, Ganin bata ga Huda falo ba yasa ta nufi ďakinta tana mata mahaukacin kira,


“Huda Huda Huda wai kina ina?”


Shigarta cikin ďakin yayi dai-dai da farkawar Huda daga bachi, 


“Ke ďan Allah tashi har ta wani baci kike kishiyarki na morewa”


 Ta faďa a lokacin data zauna kusa da ita, Huda ta ďan murja ido tana hamma tace


“Lafiya dai Safiyyah”


“Ba kan lafiya ba tashi zakiyi dan wannan shirin da nace miki zamuyi yanzu yavm kamata muyi ba basai ya dawo ďakinki ba”


“Mi kike nufi?”


“Saif ya fita aiki yanzu saboda miting ďin da Dad ya cilasta masa zuwa kuma daya fito gurin Momi ya nufa kinga komawarsa gida ba yanzu ba kenan”


Huda ta sauko da kafafun ta saman gadon,


“Nifa ban gane abunda kike nufi ba”


“Oh Huda Plan ďin da mukayi yau ya kamata mu aiwatar da shi kamin Yaya Saif ya dawo”


“Taya hakan zai faru ba kince sai yana ďakina ba?”


“No yanzu zamu aiwatar da shi ba sai yana ďakinki ba”


Bata tsaya komai ba ta ciro wayarta ta shiga neman numbar Deen,

 Tayi sa'a wayarsa na buďe kuma bata daďe tana ringing ba ya ďauka,


“N'am Deen Kana ina yanzu.?”


Banji mi yace mata ba kawai naji tace masa kalau ta shiga koro masa bayani, xuwa can kuma tayi shiru kamin ta sake cewa,


“Ok yanzu zanzo na ďauke ka da kaina zan shigar da kai gidan amman bana son a samu matsala fa”


Tana kaiwa nan ta tashi tsaye cikin sauri ta nufi kofar fita, Huda na mata magana ko saurarenta ba tayi sai faďin take ta bari har ta dawo,

 Kai tsaye gurin da Deen ya kwatanta mata yake ta nufa, Ta fita daga motar ta ta shiga tashi motar mai bakin gilas shi kuma ya shiga gidan baya ya kwanta kamar ba kowa. masu gadin gidan basu hanata shiga ba kancewar sunsan fuskarta, sai ma gaisuwar da sukayi mata cikin bangirma. sama sama ta amsa musu dan hankalinta baya gurin,

    Tana fakawa ta nufi cikin gidan ta bayan ta faďa masa karya fito.


 Tun daga bakin kofar ta soma kwallah salamar tana kiran Anty kina nan ciki, jin ba'a amsa mata ba yasa ta nufi ďakinta, Motsin ruwan da taji ne ya tabbatar mata da wanka take, juyowa tayi da sauri ta dawo gurin Motar ta buďe ma Deen tace ya fito, cikin sauri ya fito suka shiga cikin falon, sai tafiya suke kaďan kaďan kamar wasu 6arayi,

     Ďayan ďakin ta buďe masa ta shiga da sauri, ta maida kofar ta rufe, sannan ta nufi ďakin da Minal take. koda ta shiga ta tararda ita tana tsane jikinta da ďan guntun tawul, 


   Minal na ganinta ta saki fa'ah tana mata sannu da zuwa, Ita samasama tayi mata far'ah ta zauna tana wani numfashi suka soma gaisawa, Hakuri ta rika bata akan abunda ya faru ranar. ita kuma sai murmushin karfin hali take tana faďin,


“Babu komai wallahi Anty yanzua har zan wuce sai nace bari na biyo na sha ruwa”


“Aiko wallahi kin kyauta bari na kawo miki ruwan yau ni kaďai ce gidan”


“Allah sarki”


Ta faďa tana ďan soshe soshe. Minal ta zura doguwar rigarta ta nufi hanyar fita tana faďin,


“Bari na kawo miki ruwa”


“Toh Anty wallahi kishin ruwa ya matsa min”


Tana ganin Minal ta fice, Ta nufi gurin wayarta da sauri ta ďauka ta shiga mata danne danne, Jin motsin shigowarta yasa tayi saurin maida wayar mazauninta, ta koma ta zauna tana haki,

      Saman ďan karamin tebur Minal ta ďora mata drinks ďin da buskin tana faďin,


“Ga abinci can dinning idan zaki ci”


“Yauwa sannu Anty”


Kallo ďaya zaka mata ka gane babu natsuwa a tare da ita, ruwan ma kaďan tasha ta tashi tana faďin ta tafi, babu yadda Minal batayi ba akan ta tsaya har a ďan jima amman tak'i, a dole tasa Minal ta kyale ta tayi mata sallama ta fice.



                     ******         ***********     ********


Wunin Ranar Minal bata zauna falon ba sai dai tabi ta wuce idan zata shiga kicin. Sai bayan Sallah isha i ta fito sanye da wata haďadďiyar doguwar riga pick kala ta nufi kicin sai kanshi turare take.

    Ruwan Tea ta ďora saman gas ta fito ta dawo ďakinta, ta sake ďaukar wani turaren ta fesa, tana kokarin zama taji an ta6a mata baya, da sauri ta juyo cike da tsoro dan a zatonta aljani ne tunda bata san tabar kowa ďakin ba.


“Deen!”


Ta kiran sunan nasa da karfi tana dafe gaba, da murza ido wai ko gizo ne idonta ke mata.

Matsowa ya rikayi cikinta yana mata wasu kalamai kamar wadda yayi shaye-shaye,


“Kina da kyau Minal naso na kasance na Miji na farko da zai fara saninki Ya mace amman sai kika min butulci Minal baki cancanci zama matar kowa ba sai ni ina sonki sosai Minal”


Tana baya yana binta, yana binta cikin tsoro tace,


“Deen ya akayi ka shigo cikin nan Lafiya kake.? Deen meke damunka?”


“Babu abinda yake damuna Minal sai kaunar ki.....”


Hannu ya kai ya riko ta ya yana shafata, da son rabata da kayan jikinta, A nan ita kuma ta shiga kokuwar kwace kanta, tana faďin,


“Deen miye haka ka dawo hankalinka mana kai ne ma kuwa wai ya akayi ka shigo nan gidan ne?”


Bai saurareta ba sai kokarin rana ďin da yake da kayan jikin cikin karfin hali ta shiga kicin kicin ganin ta kwace kanta, suna haka taji kiran Saif a falo, 


“Baby na”


Dakan uku uku gabanta tayi mata, da sauri ya saketa ya yayi baya murmushi, ita kuma ta rufe baki tana zaro ido, 


“Ka gani ko abinda nake gudu yanzu ya zanyi ?”


Cikin Murya kuka tayi masa tambayar duk ta kiďime, jikinta sai rawa yake. Da murmushi yace mata,


“Kije ki tar6eshi mana karya shigo”

Da sauri ta ďaga masa kai ta juya ta fice, tana fita ta rufa mata baya taku biyar ďin dake tsakaninsa da ita yayi masa taku biyu ya fisgota da karfi ta faďo masa ta baya yana faďin,


“Toh ni ya zakiyi dani?”


Tsaye tayi kamar hoto daga ita har Saif, shi yana kallonta da Deen itama tana kallonsa idonta a zare kamar zasu fito.

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO


         NA


KHADEEJA CANDY 




*28*


Sam Saif ya kasa tantance abunda idonsa suke kallo, Deen ne a gidansa tare da Amaryarsa ko kuma gizo idonsa suke masa! 

   Cikin rashin kuzari ya tako ya nufo gurin da take tsaye, ganin Deen na ja da baya yasa yaja ya tsaya


“Da gaske ne kenan, na ɗauka gizo idona suke min dan ban taɓa tunanin ganinki da Deen a gida na ba” 


Yanayin yadda yayi maganar ya karantar da ita ɓacin ransa karara gashi kuma bayyane a fuskar sa, Juyowa kalli Deen idonta taf da hawaye ta sake kallon Saif sai wani motsa baki take ta kasa magana, bata kara katsewa ba sai da taji muryar Deen tana shigar mata kunne kamar ana tada bom, 


“Dan Allah Saif kayi min rai bada son raina nazo gidan nan ba sai da nace bazan shigo ba tace nazo ba komai amman wallahi babu abunda ya faru tsakanina da ita” 


Maganar yake muryarsa cike da rauni kamar da gaske, nan Minal ta sake kallonsa a karo na biyu hawaye na zuba a idonta, 


“Kaji tsoron Allah Deen” 


Ta juyo gurin Saif, 


“Wallahi Saif bansan....” 


Ganin irin kallon da yake mata yasa ta kasa k'arasa maganar sai kawai ta fashe da kuka, 

   Kofar fita ya nuna ma Deen, 


“Zaka iya tafiya Deen” 


Kamar walkiya ya fice daga falon, fuskarsa na nuna damuwa da tsoro, a baɗili kuma zuciyarsa ce cike da farin ciki, halin da yaga Minal da Saif sun shiga. 


Ɗakinsa ya wuce, zuciyarsa na wani irin bugawa da zugi,

  Saman gado ya faɗa yana maida numfashi ya rumtse ido yana haɗiyar yawu kamar mai haɗiyar maɗaci,

   Magagganun Safiyyah yake tunawa lokacin daya fito daga gurin Momi zai nufo gida ta biyo shi tana kiransa, da kamar ba zai tsaya ba sai kuma ya tsaya ya kalleta, 


“Ya akayi ne kike min wannan kiran?” 


Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta soma magana kasa-kasa, 


“Yaya ka sani bana son abunda zai cutar da kai kasan yadda nake cutuwa idan naga ranka ya ɓace, 

  Yaya bana jin daɗin abunda Huda take maka balle yanzu da kaje aka auro Minal yarinyar da anyi maya shaida da rashin tarbiya, Yaya nasan ba zaka fahimce abunda nake nufi ba saboda sonta ya rufe maka ido amman Yaya dole ne na faɗa maka gaskiya koda zaka ga bak'ina Yaya gani nake kamar Minal ba ɗan Allah ta Aure ka ba kamar tana da wani buri a kasa duba da irin sak'waninta na da kuma yadda take son Deen amman ta barshi ta zaɓi ta Aure ka, 

   Yaya bana son idonka su kallo maka abunda zuciyarka bazata iya jurewa ba Yaya.... -” 


Hannu ya ɗaga mata ya karaso kusa da ita, 


“Wai dan Allah Safiyyah miyasa baki jin kunyar kallon idona kina faɗa min mummunar kalma akan Minal, 

 Sai yaushe zaki kwantar da kanki damuwarki taki ce tawa tawa ce Safiyyah ke baki kula da bana damuwa da mamuwarki ba miyasa kike cusa kanki gurin ganin kinyi abunda zaki burge ni a kan Minal? Nasan wacece Minal Safiyyah ba sai kin faɗa min” 


Bai tsaya jiran abunda zata ce ba ya juya nufi gurin motarsa, 

   Har ya iso gida cike yake da jin haushin Safiyyah yana ganin tana masa shigar shagala. yanzu kuma sai yake ganin kamar gaskiya ta faɗa masa, 

   

“Saif... -” 


Da raunaniyar murya ta kira sunan nasa, ta tsaya daga bakin kofa tana kallonsa, 

   Buɗe ido yayi ya tashi zaune ya kalleta cike da son jin abunda zata faɗa. Ganin hakan yasa ta k'araso kusa dashi ta risina kamar mai rokon gafara. 


“Saif.... Zan iya faɗa maka wani abu ka yarda?” 


Bai ce mata Ae ko a'a ba hasalima bashi niyar yi mata magana har sai yaji karya da zata tsara masa dan yasan karya ce, tunda shi ganau ne ba jiyau ba, Ita bata tsaya jiran abunda zai ce ta cigaba, 

“Wallahi Saif na rantse maka da Allah bansan yadda akayi Deen ya shigo cikin gidan nan ba, Wallahi Saif bani na kirasa ba” 


Murmushin yak'e yayi, 


“Minal kenan, please karki soma faɗa min abunda kika san duk wadda kika faɗawa ba zai yarda ba balle ni dana gani da ido na, 

   Minal taya Deen zai shigo cikin gidan ya kai har cikin ɗakinki kare da karau har ku fito tare sannan kice baki san yadda akayi ya shigo cikin gidan ba?

   Taya ma Deen zai shigo cikin gidan nan ba tare da sanin ki ba gidan dake cike da masu gadi Haba Minal” 


“Yushe zuciyarka ta rufe tayi karfi haka daka kasa fahimta ta? Taya zan gayyato wani namiji cikin gidana ina amarya koda halina ne ballantana ba halina bane Saif kasan wacece” 


“Yes nasan wacece ke Minal” 

Ya tari numfashinta tare da tashi tsaye yana mata wani kazamin kallo, 


“Nasan abunda zaki iya aikatawa, nasan kin ɗauki kula wasu mazan ba komai ba, kin faɗa min da bakikin ke babu wadda ya isa yasa ki canja hakinki kin faɗa min ba zaki taɓa iya rabuwa da Deen ba ko kin manta?” 


Hannayensa biyu yasa ya tashe ta tsaye, ya dafa kafarɗarta. 


“Nasan abu ne mai wahala rabuwarki da Deen Minal, kowa ya san ki dashi ba abun mamaki bane idan ance an ganki dashi yana ɗaya daga cikin dalilin ya yasa na kyaleshi ya fita ba tare da nayi masa komai ba, 

  Idan anji Minal ni zayi ma dariya  ace min Allah ya kara saboda anta jamun kunne akan halinki amman naji na gani nacezan Aurenki i thought that idan na Aure ki zaki zubarda halinki marar kyau na tallafi rayuwarki muyi rayuwa mai kyau da Nagarta ashe nayi kuskure....”


Sakinta yayi ya nufi k'ofar fita, ita kuma har lokacin hawaye take, abunda da farar mace nan da nan fuskarta ta rine tayi wani ja, fatar idonta ta lumburo bakinta sai rawa yake kamar mai jin sanyi, tasan ta baro kyau tun ranar haihuwa tunda tayi ɓarin bakin cewa ba zata iya rabuwa da Deen ba, kuma ba wadda ya isa ya sata abunda bata tashi ba, 

  Tana haka Saif ya shigo ɗakin riƙe da wayarta ya mika mata, 


“Idan shigowar da Deen yayi ba tare da haɗin bakinki bane bakisan ya shigo ba toh wannan saƙon fa waya aika.?” 

  

A hankali ta ɗago ido ta kalli fuskarsa, idonsa sunyi wani irin ja, jijiyar kansa ta tashi kallo ɗaya zakayi nasa ka gane mugun ɓacin rai dake cikin ransa, 

A kasale ta mika hannu ta karɓa, sannan ta kai ɗayan hannunta ta share hawayen dake idonta tana duba sakon. 


_DEEN. Zanyi miss ɗinki sosai Minal kamin ranar da zamu haɗu_


_MINAL. Na sha faɗa maka Deen ka daina damun kanka aure na da Saif na ɗan lokaci ne kuma zama na dashi ba zai yanke tarayya ta da kai ba_


_DEEN. Bazan iya hak'urin rashin ki ba har na wani lokaci Minal kinsan yadda nake sonki_


_MINAL. Karka damu duk ranar da ya ɗan daga min kafa zan rik'a kiranka_


_DEEN. ok i love you sai na jiki_


_MINAL. i love you too_


                 SAKON YAU


_MINAL. Deen kazo yanzu idan kana free Saif ya fita amman kayi sauri kamin ya dawo_


_DEEN. ok gani nan zuwa kiyi min kwaliya mai kyau i can't wait to see you dear yau zan zama ango nima_


_MINAL, Ka daiyi sauri karya dawo kasan ba wani daɗewa zamuyi ba_


_DEEN. Yes gani kan hanya mi zan zo miki dashi?_


_MINAL, hot kiss_



Hawayen idonta ne suka rik'a sauka saman wayar, tun tana iya ganin alphabet har ta daina saboda cikar da idonta sukayi da kwallah, yanzu kan bata da hujjar kare kanta ada tana tunani idan da nusar dashi wata kila zai fahimta amman yanzu ba taya zai yarda ba ita ta tura wannan saƙon ba, bayan gashi a wayarta amman ita tasan idan za'a kashe ta a sake sa mata rai a kashe ta ba tasan tayi wannan chat ɗin da Deen ba, hasalima tun ana sauran kwana hudu bikinta bata sake saka shi a idon ta ba, balle a waya, 


“Ba ke kikayi ba.?”


Ya tambaya a tsawace fuskarsa kuma babu annuri. Yanzu kan tasan bata da wata mafita babu ta inda zata iya kare kanta, hausawa sukace gudun da ba tsira kwanciya ta fishi, Ganin haka yasa ta kalleshi fuska a raunane tace


“Nice Saif nina aikata”


Duk yadda ransa yake ɓace sai ɓacin ran yanzu yafi na ɗazin saboda ta amsa da kanta ita ta aikata, toh idan kuma bata amsa ba ya zatayi bata da wata mafita sai wannan babu ta inda zata iya kare kanta.


“Miyasa kika karyata farko ? bayan na gani da ido na”


Bata ce masa uffan ba, saboda nauyin da bakinta yayi mata sai ruwan hawaye take kamar kurma, sai kawai ta juya kamar kazar da kwai ya bashema ta ciki ta nufi kofar fita.


“Minal....-”


Cikin muryar maza yayi mata kiran muryar dake da wahalar fassara. 

Cak tayi tsaya bakin kofar, ta lumshe ido tana haɗiye wani kololo daya tsaya mata a wuya,


"Thank you so much Minal I really appreciate it”


Har lokacin bata ji tana iya furta masa wata kalmar ba. Buďe idon tayi ta tattara rigarta ta nufi ďakinta da gudu, 

 Saman gaďo ta faďa ta rushe da wani irin kuka mai tsuma zuciya, tana jan gashin kanta, sosai sosai tayi kukan nan da nan idonta ya rumburo, Zufa ce ta shiga karyo mata ta ko ina sai numfashinta ya rika fita sama-sama, da sauri ta tashi ta cire rigarta ta shiga bathroom ta tsakarwa kanta shawa.



               ****          ****       ****


Safa da marwa Saif ya rikayi cikin ďakin bayan fitar Minal, Tunanin yake miyasa Minal tayi masa haka miyasa ma ya aureta, bayan yasan halinta kuma ta riga ta faďa bazata ta6a canjawa ba, ? _amman miye na mamaki ai daman can haka halinta yake tunda bata ďauki mu'amala da wasu mazan wani abun ba auren da nayi mata nima dai nati ne kawai dan ganin na canja mata hali,_ 

Wata zuciyar ta soma tunasar dashi abunda ya manta, Amman fa Minal ba karamar yarinya bace a matsayin da take yanzu yaci ace tasan abunda ya dace da wadda bai dace ba, kai Minal tasan komai da gangane take tunda har tasan ta kula wasu mazan ta 6oye ma mijinta, shiyasa Huda take burge ni nasan tana yimin ba dai-dai ba amman bata yarda ta kula wasu mazan tana kokarin kare mutuncinta tana taya ni kishin kanta sosai,


“I hate you Minal.. i hate her so much.-”


A fili ya furta zuciyarsa cike da tsanar ta, Gaba ďaya ma jin yayi ya tsani gidan dan daga ďakinsa yana jiyo kukan da take a ďakinta, Wani dogon tsaki yaja ya fice daga ďakin,

  Da wani irin karfi ya buɗe Motarsa yaja ya rufe still da karfin kamar ita ce tayi masa ƙaifin, yadda ya ruƙa horn sai da ya bawa masu gadin tsoro, da gudu suka buɗe masa gate ya fice yana rike da sitarin da wani irin karfi.

 .  

Ya daɗe zaune cikin motar kansa jingine a sitari sai ajiyar zuciya yake saukewa, daga bisa ya fito ya nufi kofar falon hannayensa zube cikin aljihu yana tafiya guda guda, karaurawar dake gefen ƙofar ya danna ya jingina da ƙofar yana lumshe ido,

   Jin an buɗe ƙofar yasa ya ɗago ya kalleta, ita kuma ta sakar masa murmushi tana faɗin,


“Ango kenan shine ƙka tsaya a waje kamar baƙo”


Baice mata komai ba sai kallonta yake fuskarsa ba yabo ba fallasa, daga bisani ya jata zuwa jikinsa ya rumgumeta, yana sauke ajiyar zuciya,


“Ina sonki sosai Huda ina sonki”


Yana faɗar hakan tayi murmushi ta ƙara ƙanƙameshi a ranta tana faɗin _Ta faru kenan_ A fili kuma sai ta ƙara shigewa jikinsa,


“Nima ina sonka sosai Saif”


Sun daɗe a tsaye gurin kowa da abunda yake saƙama zuciyarsa, zuwa can ya saketa jin wayarsa na ruri ya ɗauko wayar daga cikin aljihusa yana duba mai kiran, Nasir ne abokinsa hakan yasa shi saurin dannan picking ya kara wayar a kunne,


“Hello Nasir kana ina ne?”


“Ina majalisa naga kayi min four miss calls lafiya dai?”


“Lafiya amman ba lau ba i need to see you”


“Ok kazo ina gida ai”


“Ok gani zuwa”


Yana kashewa, ya kalli Huda


“Je ki kwanta zan leƙa gari”


Wani maraurauce fuska tayi


“Ba zaka shigo ba?”


Kai kawai ya ɗaga mata dan baya jin iya yi mata magana sosai, tsaye tayi tana kallonsa zuciyarta cike da farin ciki, tana ganin ya shiga motarsa ta rufe ƙofar da sauri ta nufi ɗakinta da ziman kiran Safiyyah,


                                   ☆  ☆  ☆


Nasir yaja wani dogon numfashi, yana tattara girarsa yace,


“Kai yanzu Saif ka tabbatar da da kanta ta kira sa?”


“Haba Nasir ga abu ƙarara na gani tayi masa tex sannan kuma ta faɗa da bakinta itacw tace yazo”


“Sai naga kamar Minal ba zata iya yi maka haka ba dan Minal tasan miye aure and..-”


“And what..?”


Saif ya katseshi yana masa wani kallo,


“Ba yaro bane ni Nasir nasan mi nake yi duk abinda ta aikata da ganganta aikata shi, kawai rainin wayo ne yayi mata yawa take son nuna min kamar bata san miye duniya ba”


“Saif ba haka bane Ya kamata ka kwantar da hankalinka ka bincika komai yadda ya kamata Baka sani ba ko wani sherin ne”


“Ba wani sheri malam kai duk yadda zakayi ka kare Minal ka iya wazai mata wani sheri kawai malam ka faɗa min abun yi tunda kace karna sake ta”


“Saki ba yi bane Saif yaushe akayi auren nan ko sati anyi da zaka cw zaka saketa ? yanzu idan ka saketa zaka jefa zuciyarta data mahaifiyarta cikin wani halin, kuma ka koma abun labari”


“Ba damuwa ta bace dan ta shiga wani halin ai ita batayi tunanin halin da zan shiga ba kadan yadda nake ji yanzu”


Nasir ya dafashi,


“Nasan kana da zafin kishi Saif amman ka kwantar da hankalinka ka koma gida yanzu gobe da safe zanzo gidan”


Tashi yayi, tsaye yana jan tsaki,


“Nifa banga wani abun da zaka zo kayi min ba malam”


“No Saif ba haka bane, kasan aba son yanke hukunci cikin fushi kayi haƙuri har zuwa gobe please”


Rausayar da kai yayi ya nufi ƙofar fita Nasir na bayansa yana bashi maganganu.


     


                       ***          ***         ***


Daren ranar baci ƙwara yayi daga idon Minal, ko alamun bachi ba taji ba balle bachin, a zaune ta kwana tana kuka, har aka kira sallah asuba. bayan tayi sallah ta dawo parlour ta zauna idonta sutun sutun ko gani batayi sosai, juyi ta riƙa yi saman kujerar tana jin tsanar duniyar da take ciki.

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO


         NA


KHADEEJA CANDY 



*29*



Wasa-wasa yau kwanan Minal huɗu bata saka Saif a ido, duk tsawon lokaci ba tada abinci sai kuka iya karta ta sha ɗan ruwa tea ko shi kaɗan daman can Minal ba mace ce mai son cin abinci ba, duk wayar da suke da Mummy bata taɓa faɗa mata ba halin da take ciki ba, duk da Mummy tasha tambayar da koda wata matsalar ne saboda yanayin da take ji na muryar ta ba kamar yadda ta saba jinta ba, Minal bata taɓa nuna mata wani abun ba sai dai tace mata ba komai. 


    Juyi take tayi saman gado, hawaye nayi mata zuba, tunanin halin da take ciki take da kuma wadda zata shiga, miyasa Deen yayi mata haka? Miyasa Saif ya kasa fahimtarta? Tashi tayi zaune tana tunanin kodai wani aljanin ne yayi mata haka a iya saninta bata san tayi wannan chat ɗin da Deen ba, sannan tana mamakin yadda aka yi ya shigo gidan har yakai cikin ɗakinta ba tare da sanin ta ba? Ita tasan Deen ba zai mata haka ba kuma idan ma yayi mata toh wannan sak'on fa da bata san ta tura ba ya akayi hakan ya faru da ita. 


“Anty Minal...-”


Kiran da akayi mata ya katse mata tunani kuma ya tsorata ta, duk da muryar maiyi mata kiran tayi kama da ta Safiyyah amman bata gama tantancewa ba tunda yanzu ta gama tunanin aljanu kuma bata ji shigowar kowa ba sai kiran sunan nata,

    Tashi tayi tsaye tana kallon ƙk'ofa zuciyarta sai rawa take,


“Assalamu alaikum Anty”


Safiyyah ta kunno kai cikin ɗakin tare da sallama,

  Saida Minal ta sauke ajiyar zuciya sannan ta amsa mata tana ƙirƙiro murmushi


“Wa'alaikissalam Safiyyah”


Ta amsa tare da zaunawa a kusa da ita,


“Na'am Anty Lafiya kike kuka?”


Sai a lokacin ta tuno da hawayen dake fuskarta, da sauri tasa hannu ta shafe tana dariyar da bata kai zuci,


“Lafiya kalau kai ido na ne yake ciwo ya su Momi”


“Lafiya ƙalau suke tare muke da Yaya Nasir ƴyana Falo yana jiranki”


Jimmm ta ɗanyi, azuciyarta tana tunanin ko yana tare da Saif ne, bata son wani yasan halin da take ciki duk da tasan bata aikata ba, amman tasan tunda Saif ya kasa fahimtar ta babu wanda zai fahimce ta, dan haka bata son wani yaji,  sai ta sake sauke ajiyar xuciya sannan ta kalleta,


“Oke jeki ce masa gani nan zuwa”


“Ok”


Ta faɗa tare da juyawa tana murmushi. Da saƙe-saƙe ta fito ɗakin ta nufo falon har ta zauna bata san ta zauna ba saboda tunanin da take,


“Lafiya?”


Nasir ƴya buƙata, ta kalleshi tare ɗa faɗaɗa murmushinta,


“Lafiya ƙalau gata nan fitowa”


Kai ya ɗaga mata ya ciro wayarsa yana danne-danne. Sautin ƙarar takalminta yasa shi ɗaga kai a hankali yana kalleta,

   Yadda take tafiyar kamar wata marar lafiya ko kuma nace marar lakka, ta naɗe jikinta da sari ja irin na shuwa arab, yayi mata kyau sosai kamar wata balaraba, kasa ɗauke mata ido yayi har ta zauna.


“Ina wuni Nasir”


Ta gaisheshe kanta na kallon ƙasa,


“Lafiya ƙalau Minal”


Ya amsa mata still yana kallonta, sai a lokacin yaga ramar da tayi dan har kashin idonta ya fito kamar wata mai ciyon ƙaujamau, Tausayinta ne ya shiga fisgarta ganin yadda idonta ke kwance da ruwan hawaye, kodai wani abun Saif yake mata? Tambayar taya jefa fama kansa kenan yana kallonta,


“Anty kamar akwai abunda yake damun ki?”


Safiyyah ta tambaya fuskarta na nuna damuwa kamar gaske,


“Babu abunda ƴyake damu na”


Ta amsa mata ba tare data kalleta ba,


“Amman Anty naga kinyi rama sosai kuma fuskarki na nuna akwai  damuwa a tare dake”


“Babu komai Safiyyah Kinsan daman lafiya bata ishe ni ba”


“Haka ne Allah ya baki lafiya”


“Amin”


Nasir ya kalli Safiyyah,


“Tashi kije waje zamu yi magana”


Ta ɗanyi murmushi,


“Yaya Nasir kenan ba sƙon Yaya Saifu bane ai zaka iya faɗa ai”


Ya haɗe mata fuska,


“Bazan faɗa ba ke kika aiko ne ko kuma lokacin daya bani saƙon a gabanki ya bani? Kinfa san bana son iskanci ko?”


“Yaya miye abun faɗa daga magana, naga ni Ƴar'uwar Saif ce kuma..-”


Ya katse ta, a fusace


“Ke tashi ki fita nace kona ɓata miki rai shiyasa da zan fito kika ce zaki biyo kinsan bana son gardama ko?”


Ta fusata sosai, hakan yasa bata sake musa masa ba ta tashi, duk da taso taji abunda zai faɗa ɗin, amman kuma tasan halinshi zai iya yi mata tass a gaban Minal, 


“Na tafi anty”


Ta faɗa tana kallon Nasir, 


“Ba awaje zaki jirashi ba”


Minal ta tambaya ganin yadda take gyara gyalenta da rataya jika,

  

“A a daman ni gida zanje sai nace ya rage min hanya”


“Allah ya kiyaye”


“Amin”


Bata sake cewa Nasir komai ba ta fice,

   Bayan kamar minti biyar da fitar ta, Nasir ya kalli Minal yace,


“Mi Saif yake miki wanda har tasaki rama haka”


“Baya min komai babu wata matsala a tsakanin mu”


Ta amsa masa muryarta a raunane,

    Hakan ya ƙara karantarda shi halin da take ciki na damuwa,


“Bai kamata ki ɓoye min ba Minal Saif ya faɗa min komai, amman ni ban yarda da abunda ya faɗa min ba saboda nasan ba zaki aikata ba”


Sai a lokacin ta kalleshi, suka haɗa ido,


“Miyasa kace haka Nasir bayan ga gaskiya ƙarara na na aikata”


“Baki aikata ba Minal ba zaki aikata irin wannan abun da auren ki ba zan iya yarda kin kira Deen cikin gidanki ko kuma nace ya kawo miki ziyara amman ban yarda zaki aikata wani abun ba kamar yadda Saif yake zargi,

  Bai kamata ace kin bar abu a ranki ba idan wani abun Saif yake miki ki faɗa min Minal?”


“Baya min komai Nasir hasalima tun ranar da abun ya faru ban sake sashi a ido ba, be sake shigowa gidan nan ba kuma idan na kira baƴa ɗauka in na masa text baya reply”


Tagumi tayi tana goge hawayen da suka zubo mata wanda taso ta tsaidasu suka ƙi tsaiduwa,


Wani irin tausayinta ne ya fusgi zuciyarsa, sai yaji kamar a tsokar jikinsa hawayen suke zuba haka yaji kamar ya tashi ya koma kusa da ita ya share mata hawayen ya rumgumeta,

  A take tsanar Saif ya shiga zuciyarsa, miyasa yake gallaza mata har haka? dan me zai ɗauke mata ƙafa har na kwanaki huɗu, akan abunda zuciyarsa ta tabbatar masa da bata aikata ba, shi taya ma zai faɗa mata saƙon da Saif yace ya faɗa mata? Sai yanzu ya gano dalilin Saif na shirya tafiyar da yayi ba tare data sani ba, kuma har yake son tafiyar ba tare daya faɗa mata ba, ko ƴyanzu ma in ban da ya tirsasashi da ba zata sani ba, 

    Tunani yake yadda Saif yake amsa masa maganar duk da yayi masa ta Minal da kakkausar murya, wanda ke nuna har yanzu cikin ɓacin rai yake,


“Saif yanzu kana ganin kayi tafiyar nan da Minal.baifi ba a maimakon Huda?”


“Da huda nake ra'ayin tafiyar Nasir ban ma faɗa ma Minal ba kuma bazan faɗa mata ba sai dai taji na tafi”


“Saboda mi naga ai itama matarka ce kuma hakkinta ne idan zakayi tafiya ka faɗa mata, ka kuma tambayi ta idan tana buƙatar wani abun”


“Toh baxan yi mata hakan ba au nasan dai abinci da yake cikin gidan zai isheta har na wani lokacin, dan Allah ka daina yi min maganar Minal Nasir indai kana son mu zauna lafiya”


“Amman dai kasan Allah ne ya ɗora maka hakki haka ko”


Ya fita cikin motar yana faɗin,


“Na wakiltaka kaje ka faɗa mata kayi mata duk abunda ya dace”


Bai tsaya jiran abunda zaice ba, ya nufi bayan motar ys fiddo kayan da suka siyo ya nufi cikin gidan,

  Nasir na kokarin ribas Safiyyah ta fito daga falon Huda ta nufoshi tana tsayar dashi, 


“Ya akayi ne?”


Ya tambaya bayan ya tsaya ɗin,


“Dan Allah Yaya ka sauke ni gida”


“Ba gida zanje ba gurin Minal zani Saif ya ban sƙo na kai mata ne”


“Oke muje kawai”


Da sauri ta shiga motar. Cike da son ta bishi ɗin dan taji wane saƙon ne Saif ya bashi ya kai ma Minal.

   Gyara zaman da tayi ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi, 

   Ya kalleta a kasale muryarsa kuma na nuna rashin jindaɗi yace,


“Saif yace na faɗa miki tafiya ta kamashi zuwa Londom kuma gobe zai wuce duk abunda kike so ki faɗa min”


Da sauri ta kalleshi hawayen dake idonta suka ɓalle, suka cigaba da zuba, bakinta na rawa tace,


“Toh.”


Da sauri ta tashi ta nufi dan samun damar yin kukan da take haɗiyewa,

 Shima tashi yayi tsaye, yana kiranta, bata amsa masa ba saboda halin da take ciki bata son juyo balle ma har ta dawo.



Ƙasan carpet ta faɗi tana wani irin kuka abun tausayi, 

   Ƙasa tayi mata zafi gashi kuma yanzu ƙsaman nason kama mata da wuta, Saif zai tafi ya barta bai damu da duk halin da zata shiga ba, miyasa har yanzu Saif ya kasa fahimtarta ko yayi mata uzuri?

     Da sauri ta ɗauki wayarta da makulin matarta ta bar gidan. Tuƙi take tana kuka kanta babu ɗankwali jikinta ko mayafi babu daga ita sai doguwar riga ta isa gida,

   Sai tayi fakin wani tunin yazo mata, shin mi zata cewa Mummy wane hali mummy zata shiga idan ta faɗa mata? Shin mummy ma zata yarda da bata aikata ba?

  Ganin bata da amsoshi waɗannan tambayoyi yasa ta share hawayen dake idonta, ta buɗe motar ta fito ta nufi cikin gidan.

    

“Assalamu alaikum”


Ta shiga falon da ƴar far'ah kamar gaske, duk idonta a kumbure yake,

  Tsohuwa ce ta amsa mata cike da mamakin abunda ya kawo ta gidan yanzu gata kuma a yamutse,


“Wa'alaikissalam Minal kece haka?”


“Nice Tsohuwa ya gida?”


Ta faɗa tana kallon Kairat dake kwance saman doguwar kujera tana bachi,


“Gida lafiya kalau Kairat ce kawai ba lafiya”


“Miya same ta”


Da sauri ta karasa kusa da ita, ta rame sosai tayi baƙi kamar ba ita ba, 

  Tsohuwa ta taso daga inda take ta nufo Minal tana faɗin,


“Tun ranar da kika tare washe gari ta tashi da rashin lafiya kuma Hajiya tayi tayi ta kaita asibiti ya ki ankira likita ya duba ta taki yarda a dole aka sama ta ido ko abinci kirki bata ci”


Tausayinta ne ya kamata Minal, nan da nan kukan dake tare da ita yayi kokarin dawowa, a take ta manta da nata damuwar, tana kallon fuskar Kairat, mi yake damun yar'uwata haka? Wane irin ciwo ne wannan miyasa bata son taje asibiti? bayan nasan Kairat da tsoron ciwo!

  A hankali ta kai hannu ta taɓa jikinta, hawayen dake idonta suka zubar Kairat a fuska, Hakan yayi sanaɗiyar tashinta daga bachi,

   

Tana ganin Minal ta zabura ra tashi zaune, tana kiran sunan nata da kasallaliyar murya,


“Minal kice?”


“Nice Kairat mi ke damunki?”


“Aike ya kamata nayi ma wannan tambayar kinga yadda kika rame?”


Hannu takai ta taɓa wuyanta, sai kuma damuwarta ta dawo mata arai, tashi tayi ta nufi hanyar ɗakin Mummy,


“Minal Ina Saif...”


Tambayar ta tayi mata tasa ta juyo, ta kalleta,


“Yana gida gobe zaije London shine yace nazo gida”


“Kizo gida kamar ya?”


Kairat ta tambaya fuskarta ɗauke da mamaki. Duk yadda Minal tayi kokarin ɓoye damuwarta sai da ta bayyana a fuskarta saboda hawayen da suka shiga zubo mata, Duk da rashin kuzarin da Kairat take ji bai hana ta tashi ta rika hannu Minal suka nufi ɗakinta,


                         **           **           **


Da kanta ta zaunar da ita saman gadon tana kallon fusakarta,


“Minal faɗa min meke damunki?”


Idonta na hawaye tace,


“Kairat jindaɗi na ragaggene, mafarkina yankanke ne a duk lokacin dana hango haske sai naga karshensa duhu ne, bansan nayi ma duniya take juya min baya ba i know rayuwata yar kaɗan ce amman naso jindaɗina na kasance dogo sai gashi ban samu haka ban Duk ƙlokacin da farinciki na raɓe ne toh bakin cikin da zai shafe ni sai ya fishi yawa”



Kukan da take yasa Kairat kuka,


“Minal ki faɗa min abunda yake damunki mi Saif yayi maki?”


Bata ɓoye mata komai ba, cikin abunda ya faru komai sai da ta faɗa mata.

   Sosai jikin Kairat yayi sanyi, sai dai itama ɗin ta yarda da Minal ba zata iya aikatawa ba amman miyasa Deen ɗin yayi mata haka? Waya shirya mata wannan abun dole a kwai wani abu akasa, tausayin Minal ya kamata akoda yaushe cikin bakin ciki take Sai yaushe jindaɗin ta take mata fata zaizo mata, farincikinta a yanzu Saif ne kuma shima ya juya mata baya.

   Hannu tasa ta share mata hawayenta, itama tana kuka, tace,


“Kiyi hakuri Minal zanyi masa magana kinji?”


Kai Minal ta ɗaga mata duk da tasan ko tayi masa maganar ba yarda zaiyi ba,


“Please Kairat karki faɗama Mummy zata iya shiga wani hali kinji?”


“Bazan faɗa mata ba”


Suka rumgume juna suna kuka.

    Sun ɗauki lokaci a haka sannan ta taso ta fito daga ɗakin ta baro Minal.


  Gardem ta nufa ruke da wayrta tana danna ma Saif kira,

    Sai da tayi masa miss calls biyar ana shida ya ɗauka,


“Ya akayi.?”


Muryar Saif ta ratsa jiyoyin jikinta da kunnenta ta game ilahirin jikinta,

   Wani dogon numfashi taja sannan yace,


“Dan Allah dan Annabinsa ina son kaganinka na haɗa ka da girman Allah”


“Me xanyi miki.?”


“Kazo dai yanzu ina son ganinka dan Allah da ya halince ka”


Bai bata amsar zaizo ko bazai zoba sai kawai taji ya katse kiran, lumshe ido tayi ta sauke ajiyar zuciya, ta juyo jikin a mace ta dawo falo.


Toh yanzu ya zata ɓulloma ƙlamarin ba lallai bane ya gansu da maganar ta waya sai dai kuma tasan ba zai zoba tunda ya kashe mata waya, toh kodai ta kyaleshi, wata zuciyar tace baza iya jure ganin Minal haka ba, kuma tasan Mummy ma idan taji zata iya shiga wani halin.

  Tana cikin wannan tunanin mai gadinsu ya shigo yace Saif na sallama da ita a waje,

  Tashi tayi da sauri bayan tace masa yace tana zuwa ta shiga ɗaki ta ɗauko hijab ɗinta ta nufi kofar fita,

   Tsaye ta hangonshi jikin motar hannayensa zube cikin aljihu yana sanye da wata shadda blue colour ta karɓi jikinsa sosai ɗinki yayi masa kyau, fuskarsa babu annuri,

   Ita kuma fuskar tasa take kallo har ta karasa kusa dashi,


“Na gode da kazo Sannu da zuwa”

  

“Ba godiya nazo kiyi min ba ba kuma tarbarki nake so ba dalilin kiran nake son ji”


Ya faɗa kamar a fusace, ajiyar zuciya ta sauke murya a kasale tace,


“Dan Allah kazo mu shiga ɗakin baki sai muyi maganar”


Baice mata komai ba sai kawai ya nufi hanyar ɗakin bakin ita kuma ta rufa masa baya, tana kare masa kallo.



Bayan sun zauna, ta kalleshi tana murzar hannunta tace,


“Saif Minal ta faɗa min abunda ya faru, nasan zakayi wahalar fahimtar ta amman ....-”


Hannu ya ɗaga mata,


“Idai maganar Minal ce toh ki hutar da kanki babu ta yadda zaki juya min kwakwawa alhalin ga gaskiya ina gani da ido na kuma ta faɗa ta bakinta ta amsa laifinta”


“Saif ba haka bane nasan Kasan Minal amman ba zata iya aikata irin wannan a cikin gida ka ba...-”


Tashi yayi tsaye, yana mata wani kallo,


“Na auri minal ne saboda ina sonta kuma ina tunanin idan na aureta zan iya canja mata hali sai gashi na tararda tuwon da ta tuka a gidana yafi wadda take tukawa a gidansu,

   Sai a yanzu na yarda ta zancen mutane da suke cewa Minal bata da tarbiya bata dace dani ba”


Ta tashi tsaye itama,


“Haba Saif! Wannan wace irin magana ce haka nasan kana tare da ɓacin rai amman ya kamata ka tausayawa Minal kayi tunanin halin da zata shiga kodan rashin mahaifin nan ta take mafama dashi”


“Rashin mahaifi.?”


Yayi murmushi,


“Nina sa mata rashin mahaifin ne ? Minal bata da tarbiya Kairat bata da kirki bata min halacci ba sai yanzu nake nadamar auren ta da nayi”


Kairat ta fusata sosai, dan haka ta nuna masa tsaya,


“Karka sake zagin Minal karka sake ce mata bata da tarbiya kar bakinka ya sake faɗin wata mummanar kalma akan Minal idan hankalinka ne ya ɓace toh ya dawo jikinka Saif”


Matsowa yayi kusa da ita yana murmushin gefen fuska,


“Kina sonta da yawa Kairat shiyasa kika da ɗaukar mata da soyayyarki shiyasa kika rika kai kawo wajen ganin na aureta kika rika kareta bayan kinsan bata dace dani ba,

  Kika zaɓi ke ki mutu ita ta rayu, akaina kike wannan ciwon Kairat na sani”


Kai ta girgiza masa,


“Kayi kuskuren fahimtar Saif babu soyayyarka a cikin zuciyata ko kaɗan”


Kara matsowa yayi kusa da ita ta yadda tana iya juyo bugun zuciyarsa, yace


“Ki kalli kwayar ido na ki faɗa min baki sona ki karya ta kanki da kanki indai har da gaske babu sona a cikin zuciyarki!”


Kasa ɗago kai tayi ta kalleshi balle har ita iya furta abunda ya bukace ta dayi.

 Hakan yasa shi yin murmushi mai sauti,

 

“You see ba zaki iya ba, kin cutar dani Kairat da kika karkata zuciyata zuwa ga Minal bayan kinsan halinta kin kuma san bata dace dani ba, i hate you but i hate her more”


Yana kaiwa nan ya kaɓe mata rigarsa ya juya a fusace ya bar mata falon,

  Sai da taji tashin motarsa sannan ta share hawayen dake idonta ta nufi kofar cikin gida, tana buɗe kofar taga Minal tsaye a bakin kofar da hawaye shaɓa-shaɓa a fuskarta.





_ME ZAKU CE AKAN WANNAN.? ME KUKE TUNANIN ZAI FARU A GABA.?_


#VOTE

#Comments

#Oneheart

#KhadijaAbubakarAlkali

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO 


          NA 


KHADEEJA CANDY 


*_Ga barka da Sallah na baku, ni kuma ku aje min nama😋 zanzo na karɓa😊_*


*30*


“Miyasa baki faɗa min kina sonshi ba? Miyasa kika bari na aureshi bayan kinsan ke yake so?”


Sune tambayoyin da Minal ta riƙa yima Kairat tana hawaye,

   Itama hawayen take sai motsi take ta baki, kamar mai son yin magana ta kasa,

       Girgiza ta Minal ta shigayi da ƙarfi tana kuka.


“Ki bani amsa mana Kairat miyasa kika sadaukarda soyayyarki ga wace farin cikinta kaɗan ne?

  Miyasa kika bari na auri Saif bayan kinsan ba nice mace da yake so ba kinsan ban dace da rayuwarsa?

       Miyasa zaki cutar da kanki kuma nima ki cutar da akan abunda zaki iya juyashi ya zame miki farin ciki?”


Kuka Kairat take yi sosai kukan da bazata iya furta mata koda  ‘A’ ba balle ta amsa mata tambayoyinta.

     Ganin hakan yasa Minal ta saketa tayi baya-baya har ta jingina da bango, ta sulale ƙasa tana matsar gashin kanta,


“Allah na tuba idan wani abun na maka Ya Ubangijina na tuba ka yafe ni, Allah karka kama ni da laifin da bansan na aikata ba Allah karka ɗora min abunda bazan iya ɗauka ba”


A hankali taji an shafa tsakiyar gashin kanta zuwa bayan ta sannan aka duƙo dai-dai tsawonta an sa hannu a anshafi gefen fuskarta,

   Wani sanyi taji ya ratsata, ta lumshe ido tana ƙara saita fuskarta ga Mummy,


“Ko wane Bawa da irin jarrabawar da ake jarrabarsa da ita Minal, kowa da adadin Allah ya ɗibar masa na rayuwarsa da jidaɗinsa da farinciki da kuma mutuwarsa,

Ba'a taɓa dauwama a abu ɗaya Minal jindaɗi bai taɓa ɗaurewa ba,

    Dole ne ka mutu ka barshi ko kuma shi ya ƙare ya barka, kamar haka ne wahala bata ɗaurewa, dukan abunda yake fararre toh ƙararrene wannan abun, Ɗan Adam baya taɓa samun abunda yake so 100%, 

    Allah yana jarraba bayinsa badan baya sonsu ba sai dan ya gwada imaninsu da irin juriyarsu, wani yana can yana neman irin rayuwarki bai samu ba, yana neman farinciki koda ma wadda bai kai naki ba bai samu ba,

     Kiyi haƙuri Minal ki kasance kicin bayin da haƙuri yake zame musu riba, kiyi haƙuri dan Allah kar lokaci yazo wanda haƙurin zai zame miki dole kuma a lokacin baki da lada, kiyi haƙuri Ƴata kici jarrabawa ki yarda da ƙaddara baki san abunda mahaliccinki ya tanadar miki ba”


Kai ta girgiza ma Mummy alamar gamsuwa ta rumgumeta suna kuka,

Kairat ma tana tsaye a gun da take tana nata kukan, aka sara mai ba wani haƙuri.

  Sun daɗe a haka sannan Mummy ta rika ta suka tashi tsaye tare ta nufi hanyar ɗakin.

      Wanka mummy tasa tayi sannan ta kwanta taja bargo ta lulluɓe, zaune mummy tayi kusa da ita tana kallonta har bachi ya ɗauke ta,



                  ***       ***        ***


Bata farka sai bayan la'asar, tana tashi ta sake yin wanka tayi sallah, sannan ta nufo downstairs, Babu kowa falon sai tv dake ta aikinsa, windon falon ta nufa tayi tsaye tana kallon Parking space, wani yanayi take ji mai wuyar fassara, bata jin kuka a yanzu sai dai na zuci ta take, fuskarta tayi wani fari kamar marar jini, lumshe ido tayi ta sauke ajiyar zuciya.


“Minal...-”


Buɗe ido tayi ta juyo tana kallon Kairat ba tare da ta amsa ba,

  Karasowa tayi kusa da ita idonta cike da hawaye tace


“Kina jin haushi na ko?”


Ko dai bata ɗaga mata ba balle tayi mata magana sai kallon fuskarta take,


“Na sani Minal, amman ina son ko fahimce ni bana nufin ɓata miki rai ko kara miki bakin ciki Minal nafi son farin ciki kin fiye da nawa bazan iya auren abunda kike so ba, 

   Banyi hakan da wata manufa ba sai dan sama miki farinciki saboda yadda kike sonshi”


Har lokacin bata ce mata komai ba sai kawai ta ɗauke kai jin hawayen da suke son zuɓo mata,

   Ganin hakan yasa Kairat ta juya jiki ba kwari ta nufi hanyar upstairs


“Kina son shi Kairat”


Cak. Kairat ta tsaya ta juyo ta kalleta tana share hawayen ta tace,


“Idan nace miki bana son shi nayi karya Minal babu wata cikakkiyar mace da tasan kanta zats kalli Saif tace bata sonshi koda bai nuna mata ba balle ya nuna, 

  Saif yana da cikar kamalar mace bata isa ya kalleta yace yana sonta taki amsa masa ba duk yadda nake son wani Minal nafi sonki da dashi”


Hannu Minal tasa ta share hawayen da suka zubo mata tana murmushi, ta soma magana a hankali tana takowa kusa da Kairat,


“Nasan Har yanzu baki gama karantar waye Minal ba Kairat har yanzu baki waye ni ba,

 Nasan kina sona Kairat you don't have to tell me nasan kina son farin ciki na nasan zaki iya yin komai a kaina amman kinyi abu ɗaya daya ɓata min rai kuma nake ganin laifin ki akanshi kin san minene.?”


Ta dafa kafaɗar Kairat tana kallon fuskarta,

 

“Saboda me zaki sadaukar da soyayyarki ga wanda kika san soyayyarta zata zame mata bakin ciki da damuwa,

 Miyasa baki faɗa min Saif baya so na ba miyaaa zaki zugashi ya aure ni bayan kinsan ba nice zaɓin sa ba miyasa kika yi haka Sister?”


Hannunta Kairat ta rika,


“Saif yana sonki sister wallahi ni shaida ce da ace baya sonki da bazai aure ki ba kinsan waye Saif Minal babu wadda ya isa ya sashi abunda bai tashi ba,

 Kece mace ta farko da ya fara so kuma ya aure ki a yadda kike, Minal nice bana da tabbacin son da yake min saboda yana sona na dan halayen da yake tunanin na ɗara ki dasu, da ace zan canja hali da ba zai so ni ba amman ke kinga a yadda kike kuma yake sonki a haka ɓacin rai ne yasa shi yin kalaman da yayi miki ɗazun Minal ke kanki kinsan Saif yana sonki kuma kinsan duk namijin da yaga matarsa da wani dole yaji bakin ciki da ɓacin rai”


Shiru Minal tayi kamar mai nazari, tana haɗiye yawun dake bakinta,


“Amman Kairat yana sona ya kasa yayi min uzuri?”


“Ba zai miki uzuri ba saboda zuciyarsa a rufe take amman nasan gaskiya zata bayyana”


“Yes zata bayyana Kairat nasan da wannan dan karya bata taɓa ɗorewa ba but...-”


Sai kuma tayi shiru, ta share hawayen fuskarta, ta janye hannayenta daga rikon da Kairat tayi mata ta nufi ɗakinta.

   


Bayan Sallah insha i mummy ta shiga ɗakin, rike da kofin tea da biskit, dunkule ta hango Minal saman gado kamar marar lafiya, ganinta haka ya ɗaga mata hankali, tayi saurin karasawa kusa da ita ta yaye bargon tana faɗin,


“Minal baki da lafiya ne.?”


Tashi tayi zaune cike da karfin hali ta kirkiro murmushi,


“Lafiya ta Kalau Mummy sanyi ne kawai nake ji me kika kawo min?”


“Tea da biskit nasan tunda kika zo baki ci komai ba, are you sure lafiyar ki kalau?”


Mummy ta tambaya cike da damuwa a fuskarta,

Hannu tasa ta karɓi tea ta sha dan ta kara tabbatar ma da Mummy lafiyar ta kalau duk da ita kanta tasan bata da lafiyar,


“You see mummy i m fine”


Kanta mummy ta shafa, tana murmushi zuciyarta kuma cike da tsoro,


“I hope so tashi muje muci abinci nasa anyi miki shimkafa da miyar kifi abunda kike so”


“Bana jin cin abinci yanzu kuma kinga nasha tea sai dai ko zuwa anjima”


Mummy ba dan taso ba ta kyale ta, sai dan bata son tirsasa mata,


“Okey promise me anjima zaki ci”


“I promise mummy”


“Thank you”


Ta faɗa tana shafa kanta, sannan ta tashi ta fice,

   Sai goma na dare ta sake dawowa ɗakin ganin bata fito ba ta saka ta agaba suka ci abincin tare.

  Haka mummy ta rika yi mata a duk lokacin cin abinci sai ta zubo suci tare, ita kuma dan ta farantawa mummy ta kuma nuna mata bata damuwa sai taci duk da yake wani lokacin kaɗan take ci. Sam bata yarda mummy taga kukanta tun tana ɓoye kukan har kuka ya daina zuwa mata da kansa, sai dai ƴnauyin kirjin da take ji.


  Yau ma mummy ta ɗibo abinci kamar yadda ta saba, amman yau a falo ta zaune,  


“Kairat jeki ki kira min Minal”


Tace da ita tana kokarin karɓar ruwan da talatu ta ke mika mata,

 Sai da ta kalli abinci sannan ta tashi ta nufi hanyar ɗakin Minal,

   A bakin kofa ta tsaya ta sauke ajiyar zuciya sannan ta kai hannunta ta murɗa kofar ɗakin ta shiga.

Takardu taci karo dasu cikin ɗakin ki duk an watsar Minal kuma ta ba kofar baya ta rike kai da alama kuka take,

   Hannu Kairat takai ta ɗauki ɗaya ɗaga cikin takardar dake bayan Minal,


_Miyasa ka tafi ka barni? Miyasa bakayi hakuri an same ni ta halal ba? Miyasa baka yi tunanin ya rayuwa ta zata kasance ba? Me na maka Haka me na maka?_


Shine abunda Kairat ta gani a rubuce, koda ta gama karantarwa idonta cike yake da kwallah, a hankali ta zauna bayanta ta dafa ta,


“Kuka kike yi sister.?”


Bata ɓoye nata ba ta juyo tana ɗaga mata kai,


“Yes kuka nake yi kukan da bashi da magani, miyasa ya buga min tabon da ba zai gogu ba? da zanga Mahaifina a yanzu da nayi masa tambayoyi masu yawa”


Hannayenta biyu tasa ta riki fuskar Minal, idonta cike ta hawaye ta soma mata magana kamar mai rarrashi


“Ashe har yanzu baki koyi Hakuri ba Minal? Har yanzu baki fahimce miye duniya ba?”


“I try but you know what? Ke shegiya ce bada aure aka haife ki ba wannan kalmar ita tafi komai bakan ta min rai miyasa mutane basa fahimta ne shin ni nayi kaina ko kuma jindaɗina ne na kasance haka? Yanzu Huda ta kirani ta gaya min magana son ranta ta aibanta ni tayi tirr da rayuwa mena tarewa mutane ne ? Dame zanji!”


Kuka take sosai har muryarta na rawa, ganin hakan yasa Kairat ta rumgime ta suna kukan tare.

  Zuwa can ta janye jikinta tana share mata hawaye tace


“Karki bari Mummy taji wannan maganar hankalinta zai iya tashi”


Kai ta ɗaga mata tana kara goge hawayen,


“Taso muje tana falo tana jiranki zaku ci abinci”


Nan ma kanta ɗaga mata ta tashi ta shiga banɗaki ta wanke fuskarta sannan Kairat ta rika hannunta suka fice.



                     ***    ***    ***  


SAIF............


Tunda ya sauka London, baya cikin walwala duk wani jindaɗi da yake tunanin idan ya baro nageriya zai samu bai same shi ba, shida yazo da zimmar yin wata biyar sai gashi ko wata uku bai yi ba yaji ya kosa da garin,

 Wani gefen kuma gani yake ko dan Huda taki yarda ta biyo shi shiyasa abubuwan suka taru suka yi masa yawa, ga damuwar da yaxo da ita tayi masa tsaye a rai a maimakon ta ragu sai ma karuwa da take.

  Idan ya rufe idosa babu wanda yake ganin sai Minal, gashi sai mafarkai yake yi barka tai, duk wani sukuni dake tare dashi sai ya rasa shi, gani yake kamar zai iya cire Minal a ransa amman ya kasa yanzu da yake son ɗasa kiyayyarta a zuciyarsa, soyayyarta ce take karuwa, wani ɓangare na zuciyarsa kuma sai tausayinta yake ji, yes rayuwar Minal abun tausayi ce amman miyasa tayi min haka naso muyi rayuwa mai kyau ni da ita amman ta ruguza min tsari ta wargaza min lissafi.

  Wani dogon numfashi yaja ya lumshe ido, 

_nasan a duk inda kike kina bukata ta kusa dake, koda mun rabu zuciyoyin mu ba zasu iya rabuwa ba,_


“Why? Minal why?”


A fili ya furta ya tashi daga kwance da yake yana kallon sili kamar wani bakon ɗakin.



                 ***   ***   ***


A hankali ta sauke idonta daga kallon silin da take, ta mai da dubanta ga wata fulawa dake gefen kofar sitting room, tana sauke ajiyar zuciya,

   _Har yaushe ne lokacin da nake mafarki zaizo? Sai yaushe Saif zai gane gaskiya? Ina son ka gane gaskiya Saif ba dan na zauna da kai ba sai dan muyi rabuwar mutunci, daga lokacin da ka gane gaskiya Na rabu da kai kenan rabuwa ta har a bada_ 

  A zuciyar ta take wannan maganar, tana dafe da kanta,

wani kololo taji ya tsaya mata a zuciya ya tokare mata gaba, yayi nauyi sosai, ajiyar zuciya ta shiga saukewa, wai ko zata samu sawaba, 

ta tashi ta nufi windon dake facing ɗinta ta rike labulayen tana kallon Garden.

   Abu taji ya gangaro mata daga hanci kamar majina,

 da sauri ta nufi dinning, ta ɗauki tissue ta goge, sai gashi ya kara zubowa kamin ta hankara har ya zubar mata a hannun, ɗago hannun tayi ganin abu kamar jini tana dubawa, jinin da gaske ba kama bace, 


“Innalilahi wa'inna ilaihi raji'un”


A fili ta furta tana zaro ido, numfashinta ya shiga rawa a'lamar tsoro.




COMMENT ON EVERY LINE,  AND YOU SILENT READERS PLEASE VOTE 


#OneloveOneheart

#KhadijaAbubakarAlkali

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO


         NA


KHADEEJA CANDY 



*31*


Da sauri ra nufi ɗakinta, tana shiga ta maida kofar ta rufe tana maida numfashi, 

   Ta daɗe a gurin a zaune, kamin ta tashi jiki ba kwari ta shiga banɗaki, ta kunna fanfo tana kwanke fuskarta da hanci. Fashewa tayi da kuka lokacin da idonta suka kai kan madubin dake gabanta ta kalli fuskarta, sai ita kanta taba kanta tausayi,a gefe ɗaya kuma Mummy take tausaya ma bata san halin da zata shiga ba idan bata raye tasan yadda Mummy take son ta kuma suka Shak'u, Mummy bata da kowa a yanzu sai ita kamar yadda itama bata da kowa sai mummu, toh idan guda ya mutu ya bar guda ya guda zaice ta rayuwarsa zata kasance? 

    A hankali ta sulale kasa tana tana rera kuka a hankali, ta yadda babu wanda zaiji sai wanda ke kusa da ita, jinin ko sai zubo mata yake kamar ana k'ara turo shi. 

   Kuka tayi sosai har idonta ya lumbura, fatar idonta tayi ja, sai da taji an kira sallah, sannan ta tashi tayi alwala ta ɗauki wani karamin tawul ta rufe hancinta dashi saboda zubar da jinin yake mata, sannan  ta fito daga banɗakin kamar wanda aka cirewa lakka. 

    Tawul ɗin tasa ta ɗaure hancinta sannan ta canja tufafin dake jikinta ta saka hijab tayi ta soma sallar, bayan ta kare ta cire tawul ɗin ta kai shi toilet ta sake ɗauko wani tana daɗe hancin da shi kamar mai jin wari, 


“Minal...-”


Jin kiran Mummy yasa ta kara gyara zaman tawul ɗin a hancinta ta juyo tana kallon kofa, 

  Mummy ta shigo fuskarta shimfiɗe da murmushi, 


“Minal muje kici abinci nasa an... -” 


Shiru tayi bata k'arasa ba lokacin da hankalin ta ya kai kan hancin Minal, 

Cikin tashin hankali ta k'arasa kusa da ita, ta dafata tana tambayar ta muryar ta na rawa, 


“Minal...mi..ya sa...mu hancin... Cin ki? Ko ciwon ne ya tashi” 


Murmushi tayi kamar da gaske, babu abinda yake damunta, 


“A'a Mummy mura ne” 


Kokarin goge hancin ta tayi ta yadda Mummy ba zata gane ba, ta buɗe shi tana faɗin, 


“Kin gani, mura ne babu wani abun majina ce take min zuba” 


Tana faɗar hakan ta maida tawul ɗin kan hancinta, sanin idan bata mayar ba jinin zai iya mata zuba har Mummy ta gani, 

  Mummy bata sake ce mata komai ba sai kawai ta mata murmushi ta juya ta bar ɗakin zuciyarta na rawa da bugawa, 

   Sauri sauri take mai kamar gudu ta nufo falo da zimmar ɗaukar wayarta dake kan kujera, 


“Lafiya Mummy?” 


Kairat ta tambaya ganin yadda hankalin Mummy ya tashi, 


“Minal ce na gani tana rufe hanci ina jin ciwon ta ne ya tashi tace min mura ne amman nidai ban yarda ba” 


Cikin muryar kuka take bata amsar, tana neman wata number a wayarta, 

   Da gudu Kairat ta tashi ta nufi ɗakin Minal, durfane ta tarar da ita tana kuka kamar mai neman gafara, da sauri ta dafata idonta cikin da hawaye tace


“Sister are you crying?” 


“Yes Kairat bazan iya ɓoye miki ba, but please karki faɗa ma Mummy” 


“Oh my God” 


Da sauri ta tashi ganin yadda jinin take zuba a hancin Minal ta nufi kofar fita, 

  Minal. Sai kiranta take amman bata jita ba tsabagen hankalinta baya gurin. Karo suka tashi yi da Mummy, dan tana kokarin fita Mummy ta shigo, 

   Da gaggauwa Mummy ta nufo Minal, 


“Tashi muje asibiti na kiran Likitanki baya nan amman yace zai kira wata Dr. Zainab zata duba ki” 


Tashi tayi ba musu, Mummy ta rik'a ta suka fice, gidan baya ta zauna ita da Kairat Mummy na driving suka nufi asibitin. 



                      ***   ***   ***


Kaɗan-kaɗan yake cin abinci yana wasa da bakin kofin da aka zuba masa drink, 

   Momi na lure dashi, tun zaman shi gurin chokali huɗu kawai yakai bakinsa sai kamar wanda baya son abinci ko kuma aka sashi ci dole, Tasan matsalar iyaline take damunsa tunda Safiyyah ta faɗa masa abunda ya faru tsakanin sa da Minal, yanzu kuma yayi dawowar da ba'a zata ba kuma yaki sauka gidansa ya sauka a gurin ta, 


“Saif duk kai kasa kanka cikin wannan matsalar yanzu da ace yar'uwarka ka aura zaka shiga wannan halin ne? Yaro da kai kana jama kanka matsala haka siddau” 


Ajiyar zuciya ya sauke ya busar da iskar bakinsa, 


“Oh Mummy so nawa zan faɗa miki Safiyyah bata daga cikin tsarin matan da nake so wallahi bazan iya aurenta ba kuma ko na aureta ba daɗi za muji ba tunda ni bana so” 


“Su waɗannan da kake so ai sun nuna maka son duk cikin su babu na kwarai kowa gasa maka giɗa yake a hannu, da ita ka aura da duk haka bai faru ba tunda ita tana sonka” 


“Ko tana sona dole ne sai hak'uri tunda ba ayi ma namiji auren dole” 


Tashi yayi dan baya son ta kara sako masa wata maganar, ya ɗauki makulin motarsa yana faɗin


“Ga file can idan Dad yazo sai ki bashi ni zanje gida” 


Taɓe baki tayi, 


“Toh ka gaida gidan kuma ina son ka natsu ka sake tunani Saif.... ” 


   Bai ce mata komai ba ya juya ya fice ransa a jagule ita kuma ta bishi da kallon tausayin halin da ɗan nata ke ciki. 


                               ***


    11pm, dai-dai Minal ta farka, ta kwashe awa biyu tana bachi, dan suna isa Dr. Zainab ta karɓe aka wuce da ita ICU Unit 2 tayi mata alurrar bachi, ta saka mata drip.

       Kokarin tashi ta shiga yi sai taji an rik'a ta an tayar zaune, ɗago kai tayi suja haɗa ido ta Kairat fuskarta shakaf da hawaye, 

  Saurin ɗauke kai tayi, tana haɗiye yawu,


“Ki aje kukan ki har lokacin da yinsa zaiyi sai kiyi amman ba yanzu ba” 


Hannayenta Kairat ta kama tana kuka, 


“Minal mi yasa kika saka kanki a damuwa, Dr. Tace ciwon ki yayi tsauri sosai” 


Dr. Zainab ce ta shigo, rike da wasu files, ta shiga duba Minal da tafiyar numfashinta a computer tana rubutawa. 

    A nan Minal tayi ta kara matse hannunta cikin na Kairat idonta cike da hawaye tace, 


“Sis please promise me zaki kula da Mummy” 


“I don't have to kinsan zan kula da ita, amman ki bar wannan maganar” 


Hawaye ne suka shiga zuba a idon Minal, ganin hakan yasa Kairat ta kasa ɓoye kukan ta har sai da ta fasa shi, 


“Please stop crying Sis you are very strong woman i wll fight it you can fight this sick” 


“Bana tunanin haka Kairat wannan ba irin ciwon da kike tunani bane, blood cancer ne kuma kinsan ina da sikila. Kairat Mummy ce damuwa ta bansan irin halin da zata shiga ba. Zan mutu da bakin cikin abu biyu a rai na bakin cikin zan mutu na bar Mummy ita kaɗai kuma Saif yana min kallon maciyiyar amana” 


Ido Kairat ta tsura mata tana hawaye, Dr. Zainab ma kallonta take cike da tausayawa. 






KUN TUNA WACECE DR. ZAINAB?

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO


         NA


KHADEEJA CANDY

 


®

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA) 



*32*



Tsit ɗakin yayi, kamar ba kowa babu abunda kake ji sai sautin kukan Kairat, Minal ma kuka take amman ba mai sauti ba, Dr. Zainab ta dafa ta idonta cike da hawaye,


“You have to be strong, ciwon dake jikin ki ba shi ke tabbatar miki da mutuwa zaki yi ba, so nawa masu lafiya suke mutuwa su bar marar lafiya? Wannan ciwon naki dalilin tashin sa rashin shan magani da kike yi har na tsawon watanni kuma kika ɗauki damuwa kika saka a cikin ranki, 

 ki sassautawa zuciyarki ta yadda zai taimaka mana gurin daidai ta tafiyar numfashinki da kuma samun lafiyarki, sannan kuma ya taimaka kama baby dake cikin ki tayi rayuwa mai lafiya”


Da sauri Minal ta kalleta, cike da rashin fahimta, Kairat ma kallonta take dan tayi maganar ne kamar a dunk'ule,


“Dr ban fahimta ba me kike nufi ne?”


“Kar dai kice min baki san kina da ciki ba?”


Ta tambaya tana kama hannun minal tana saitawa da agogon dake manne a hannunta,


“Kina nufin Minal tana da ciki na haihuwa?”


Kairat ta tambaya, cike da son sani Dr Zainab tayi murmushi,


“kina da ciki na haihuwa na uzara da nasa miki ɗazu na'ura ce dake nuna duk abinda ƴake cikin jikin mutum ta nuna kina ɗauke da ciki na wata uku har da yan kwana ki”


Rufe baki Kairat tayi tana murmushi mai haɗe da hawaye, Minal kuma ta lumshe ido tana haɗiye yawu, 


“Nasan Saif zai fi kowa farinciki idan yaji saboda yadda ya daɗe yana neman haihuwa”


Buɗe ido Minal tayi ta kalleta, wacece ita? ya akayi tasan Saif? taya ma tasan ita matar Saif ce,

  

“Wacece ke?”


Kairat ta tambaya cike tana mata kallon rashin yarda,

  zaunawa Dr.Zainab tayi saman gadon ta Minal take ta kama hannunta tana murmushi


“Karki yi mamakin taya nasan Saif kike aure, ke da shi duk yan manyan mutane ne kinsan babu yadda za'ayi ayi auren ku yan kasa basu sani ba,

  babu jaridar da bata buga labarin auren ku ba anan najeriya, nasan Saif yana matukar son haihuwa ne saboda abokin aiki na ya taɓa duba shi shi da matarsa”


Minal ta share hawayen da suka zubo mata,


“I just can't believe ina da ciki bsn taɓa jin alamu ba”


“Ba lallai bane kiji alamu akwai cikin da sai ya girma yake sa mace ta canja wani kuma tun farko yake sawa wani kuma sai a tsakiya”


Lumshe ido Minal tayi tana maida numfashi, Dr. Zainab ta kalli Kairat


“A bata kayan marmari taci fruit kar a bata abu mai zafi da kuma mai nauyi idan tace zan dawo na bata magani”


Ta faɗa tana haɗa takardun dake hannunta, kai Kairat ta ɗaga mata


“Okey Doctor thank you”


Murmushi tayi


“It's my job”


Bayan ta fice, Kairat ta rumgume Minal tana dariya,


“I can't believe this dear Alhamdulillah naji daɗi sosai”


Murmushi Minal tayi wanda ba zan iya fassara yanayinsa ba na farinciki ne ko akasin haka ko kuma na har ƴyanzu bata yarda da tana da cikin ba!

  Shigowar da wata abokiyar Mummy tayi ko kuma nace mai take mata baya, yasa Kairat ta sake ta suka kalleta, ko wanne fuskarsa babu ɗauke da murmushi,


“Masha Allah Minal an samu sauki Allah ya kara lafiya haka muke son gani”


Ta faɗa yayin da yake kokarin karasowa kusa dasu, Kairat tayi dariya


“Ina Mummy ko tayi bachi ne?”


“Ai kinsan ba zata iya bachi bata Minal a ido ba taje gida ta ɗauko wasu abubuwan ne”


Kairat tayi murmushi mai sauti,


“Nasan Mummy idan taji zata fi kowa farin ciki nice zan faɗa mata”


Murmushi matar tayi duk da bata san me suke yima murmushin ba tace,


“Kamin na manta akwai wani da yazo yanzu yana son ganinki na faɗa masa ma bachi kike amman yace yana son ganin ki ko da kina bachin ne nayi nayi dashi yace shi sai ya ganki”


“Wanene?”


Minal ta tambaya,


“Ban san shi ba amman dai yace min Deen ne sunanshi”


Da sauri Kairat tace,


“Karki barshi ya shigo je kice bachi take”


“No Sis”


Minal ta tari numfashinta,


“Barshi ya shigo inason magana da shi”


“Minal why mutumen nan fa shiya yayi miki wannan abun ki ganshi kiji me?”


Minal bata ce mata komai ba ta kalli matar kawai tace,


“Je kice ya shigo”


Tashi tayi ta juya ta fice, Kairat ta tashi a fusace tana faɗin,


“I hate you Minal”


Minal ta amsa mata,


“I know”


Taja tsaki ta tashi rai a ɓachi ta fice. Bata fi minti biyar da fita ba Deen ya turo kofar ɗakin ya shigo, fuskarsa cike da damuwa suna haɗa ido da Minal.yayi saurin kauda nashi idon kamar mai jin kunya,


“Why are you here?”


Ta tambaya murya kasa-kasa. kamar ya fasa kuka ya karaso kusa ita yana faɗin,


“Naji ance ciwon ki ya tashi”


“So what is your concern”


Risinawa yayi yana kallonta,


“Deen i care for you... -”


“You care for me?”


Ta tari numfashinsa,


“Did you hear yourself? you are the reason why I'm here you are the reason why I'm like this, ka kashe ni da rai na Deen you betray me, 

Duniya tana kokarin karantar dani darussan da ban cancanci koyon su ba, everyone is trying to hurt me even the I trust, miyasa rayuwa ta zamo min haka? what I have done?”


 Ta karasa maganar cikin kuka. Hannu ya kai zai rika hannunta,


“you didn't done anything Deen”


Da sauri ta janye hannun,


“Don't touch me”


Ta faɗa kamar a tsawace, bai damu ba ya cigaba da faɗin maganar dake bakin shi,


“Sani akayi Deen, ba wai dan naso ba sai dan ina tunanin idan nayi hakan Saif zai sake ki sai ni kuma na aure ki i love you Minal”


Ta gyara zamanta,


“Miyasa baka faɗa min kana so na ba tun farko? da ka faɗa min da bazan zaɓi Saif na barka ba ban tsɓa maka kallon masoyi ba kallon amini nake maka kuma ɗan'uwa,

tell me waya saka ka manta da amintar dake tsakanin mu ? waya sa ka cutar dani bayan baka taɓa min haka ba? waya saka ka cuci kawarka aminiyarka wanda ta aminta da kai waya saka ka cutar da wanda farin cikin ta kaɗan ne?”


Kasa amsa mata yayi sai hawaye yake, yana kallonta cike da tausayawa, itama hawayen take tana kallonshi,

  Suna Haka Kairat ta turo kofa ta shigo, rike da plate ɗin fruits fuskarta babu annuri ta kalli Deen,


“Fita zata ci abinci”


Hannu yasa ya share hawayenshi murya na rawa yace,


“Please Kairat Let me talk to her”


Tsaki taja ta aje plate ɗin, ta shiga jan rigarsa kamar wani yaro,


“Tashi ka fita nace kace haka kake son ganinta kuma ka ganta ko ba haka kake son ganinta ba ƙwance”


Duk yadda yaso ya tsaya kairat kin tsayawa tayi sai turashi take waje, a bakin kofa ya tsaya yana kallon Minal yace,


“Minal kisa wannan a zucuyarki Deen yana sonki yana kaunarki kuma yayi nadamar abunda yayi and he always care for you”


Kau da kai tayi hawaye suka gangaro mata, Kairat kuma ta tura kofar ɗakin da karfi tana matsifa.




     WASHE GARI............

 Mummy da kanta take bata breakfast sai shafa kanta take, cike da jindaɗi jindaɗin da yake shine har cikin rayuwarta da kuma ilahirin jikinta, Mafarkin ta ya kusa ya zama gaskiya ita ma ta kusa samun jika,ta kusa ta ginama kanta rayuwa tayi ma kanta family kamar kowa. jin take kamar ta ɗauki minal ta haɗe cike da shauki take bata abinci har taci ta koshi, 

   Kairat ce ta shigo tare da Nasir, ko wanne fuskarsa ɗauke da murmushi, sai da ya gaisa da mummy sannan ya kalli Minal yana mata ya jiki, mummy ta amsa masa da taji sauki ta tashi ta fice ita da Kairat.

 

“Kairat ta gaya min albishir mun samu baby”


Da sauri tayi kasa da kanta,shi kuma sai kallonta yake yana murmushi, 


“Ni zan fara yima Saif wannan albishir ɗin nasan goro na babba ne”


Ita dai bata ce masa komai ba,sai dai ta kan samu kanta da faɗuwar gaba a duk lokacin da ta tuna Saif ko kuma aka anbaci sunanshi. Bai daɗe a ɗakin ba yayi mata sallama da fatar kara samun sauki ya fice.

   

   Yana fitowa harabar asibitin ya ɗanna ma Saif kira, bugu ɗaya ya ɗauka kamar mai jira,


“Hello Nasir”


“Naam Saif kana ina?”


“Ina gida lafiya?”


“Lafiya kalau wane gidan?”


“Gurin Momi mana”


“Gani nan zuwa zanyi maka albishir albishir ɗin da ban taɓa maka irinsa ba”


Bai tsaya ya sake cewa komai ba ya kashe wayar yana murmushi, gurin Motarsa ya nufa yana shiga yayi mata key.

  Kai tsaye gida ya nufa, koda ya shiga ya tararda su zaune parlour har Mummy suna fira, Bayan ya gaisa da Mummy ya nemi kujera ya zauna yana murmushi. Saif kan sai kallonshi yake yana jiran yaji albishir ɗin da yace masa, shi kuma yaki magana sai faman murmushi yake, ganin hakan yasa Saif yayi masa magana


“Kace zaka min albishir kuma naji shiru”


Duk kallon Nasir sukayi har Mummy Lubna tace 


“Lallai kuwa babban albishir ne dan ga farincikan ka nan ya kasa ɓoyuwa”


Dariya yayi yace,


“Sai an faɗa min abinda za a bani idan na faɗa”


Saif yaja tsaki, Momi kuma tace 


“Me kake so?”


“Motar ki”


Yadda yaba Momi amsar sai ya bata dariya,


“Za a baka faɗa mana”


Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan Saif yana murmushi yace,


“Ka kusa zama uba, Minal na ɗauke da ciki na wata uku”


Dimmm Saif yaji maganar kamar an sako masa ita daga sama,baki a buɗe yake kallon Nasir, kamin ya maida idonsa ga Momi dake faɗin,


“Masha Allahu”


A nan ya tabbatar da ba mafarki yake ba faduwa yayi yana yima Allah sujada,

 kowa farin cike har Lubna da kannen ta amman banda Safiyyah data dafe kirji ta zaro ido,


“Tana ina ne?”


Safiyyah ta tambaya, Nasir ya bata amsa,


“Tana asibiti jiya aka kwantar da ita”


“Wace asibitin?”


“Success special hospital”


“Waya faɗa maka taya akayi kasani?”


Tsaya yayi yana kallonta yadda take jero masa tambaboyi kamar yar jarida,

Hawun dake bakinta ta haɗe ta tattaro girarta tana kallonshi.

   

“Yaya Nasir Kana da tabbacin cikin dake jikinta na Yaya ne?”


Da sauri Saif ya kalleta, nan take ta canja ma kowa tunani murmushin da yake fuskokinsu sai ya ɓata farin ciki ya koma ciki.



DON'T FORGET TO VOTE AND COMMENT


#Onelove

#Oneheart

#KhadijaAbubakarAlkali

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO


         NA


KHADEEJA CANDY

 


®

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)



_Ina son nayi anfani da wannan damar wajen yin godiya ga yan'uwa abokai da kuma marubuta da makaranta da masoya waɗanda suka taya ni murnar cin wannan gasan da nayi i really appreciate it Allah bar zumunci_



*34*



Lubna na zaune falo taji kukan wayar Momi, sanin kanta ne Momi bata son ana ɗaukar mata waya idan ba wani uzurin ba, hakan yasa tayi kamar bata ji kiran ba tun da mai wayar bata nan, sai da taji an matsa da kiran sannan ta nufi mazaunin wayar ta ɗauka tana duba mai kiran, Number Safiyyah ta gani hakan yasa ta saurin ɗaukar wayar dan tasan ba lafiya ba ganin Miss calls Goma sha ɗaya,


“Hello Ant...-”


“Ba ita bace security ne ke magana mai wannan wayar tana kwance asibiti a yanzu haka”


“Wace Asibitin me ya same ta?”


Cike da tashin hankali take masa tambayar,


“Rahama hospital ta faɗo ne daga upstairs”


Da gudu ta nufi parlour baki gurin da Momi take ganawa ta yan shan miya,


“Momi Momi”


Yadda take mata kiran sai da gabanta ya faɗi,


“Lafiya Lubna wannan kira haka?”


“Momi ba lafiya ba Safiyyah na asibiti ta faɗo daga upstairs”


Ta faɗa tana kuka,


“Wane Upstairs kuma?”


“Ban sani ba Momi ni dai yanzu aka kira wayarki da nurmber ta ina ɗauka wani ya faɗa min haka”


“Subhanallahi wace asibitin ce?”



“Rahama”


Da sauri ta bar parlour ita da lubna ta nufi ɗakinta, gyale kawai ta ɗauka da jaka ta fito suka nufi parking space,

 

Koda suka isa asibitin likitoci na kanta suna yi mata aiki, guri Momi ta samu ta zauna tana kiran wayar Saif ta shaida masa abunda ya faru

    Cikin kankanen lokaci shima ya iso gurin hankalinshi a tashi taya tambayar yadda akayi ta faɗon, ɗaya ɗaga cikin securities ɗin da suka kawo ta gurin ne ya shiga musu bayani jiki na rawa,


“Muna dai ba zamu ce ga taka maimain abunda ya faru ba mun dai hi kuwar ta koda muka karasa sai muka ganta kasa a sume, sai dai mutanen gurin sunce faɗowa tayi wasu kuma suka ce turo ta akayi”


Kamin Saif ya kara musu wata tambayar likitoci suka fito daga ɗakin kowannane sanye da safa a hannu.


“Yauwa Doctors ya ake ciki?”


Daya daga cikin su ne ya amsa mata,


“Tana da rai sai dai ta samu karaya a hannu da kafa kuma fuskarta ma ta gogwalje (ta jijjimu) yanzu dai munƴyi mata alurar bachi”


“Innnalillahi wa'inna ilaihi raji'un”


Momi ta fashe da kuka ita da Lubna, Saif ya gyara tsayuwarsa yana faɗin,


“Toh yanzu Doctor miye abun yi?”


“Yanzu dai sai idan ta farka zamu karasa duba ta muga ko da wata matsalar, sannan kuma sai a shirya yi mata aiki”


Ya shafa kansa,


“Shike nan Doctor Mun gode”


“Your welcome”


Bayan Doctor ya wuce yazo yana lallaɓa Momi taje gida shi zai xauna a nan, amman sam taki gani cewar ta idan tayi hakan sai ace dan ba ita ta haifeta ba shiyasa tayi mata haka.


  Guraren Magariba, Gwoggo Laraba ta iso, sai kuka take jikinta na rawa, daker Momi ta samu ta lallaɓa ta tayi shiru ta natsu, kan kace kwabo ƴyan'uwa sun cika asibitin gurin duba Safiyyah.

   Bata farka ba sai kusan goman dare, daker ta iya buɗe idonta saboda nauyin da sukayi mata, sai taji jikinta kamar an ɗaure ta sa sarka, wani wahalallen nishi tayi shiya jayo hankalin mutane dake ɗakin kowa ya shiga mata sannu, Saif kuma ya fita neman Likita.

    Bai daɗe ba ya dawo tare da likitan, ya shiga dubata yayi mata allura, sannan yace mutane dake cikin ɗakin su rage ba a son marar lafiya ayi masa taro, ba musu suka fita aka bar Momi da Saif sai Gwaggo Laraba.


“Kwai inda yake miki ciwo?”


Murya kasa kasa ido kuma taf da hawaye tace


“Ko ina ciwo yake min miya same ni ne?”


Likintan ta kalli Saif,


“Zuwa anjima ka dake kira na sai na duba ta kamin mu shiga da ita ɗakin bincike yanzu ko an bata wani abun ba zata iya ci ba”


Kai Saif ya ɗaga masa, Momi ta matso kusa da ita tana kuka,


“Safiyyah miya kaiki Wannan restaurant ɗin?”


_Restaurant_ Ta faɗa cikin ranta wace restaurant kuma ita fa ta manta abunda ya faru, kenan ita ta jima kanta toh miye sila?

 A hankali tunanin ta ya fara bata abunda ya faru da ita nan tasa kuka, taba da tabbacin wanda ya turo ta ɗin amman tasan Deen ne.


“Sannu Safiyyah”


Muryar Saif ta katse mata tunani, kallo ɗaya tayi masa ya ɗauke kai,


“Wai ya akayi hakan ya faru dake ne?”


Gwaggo Laraba ta tamabaya tana kuka ganin hawayen da suka zubo ma Safiyyah,

 Saif ya dafa ta


“Gwaggo wannan ba shi bane tana bukatar hutu yanzu karki ɗaga mata hankali kiyi hakuri zata ji sauki insha Allahu”


Kai Gwaggo Laraba ta ɗaga tana kuka,


“Saboda...Saif..... ne...Gwaggo....”


Safiyyah ta faɗa murya na rawa, da sauri Saif da Momi suka kalleta Gwaggo Laraba ma kallonta take,


“Kamar ya saboda nine nina turo ki kika faɗo ne ko mi kike nufi?”


Saif ya tambaya a tsawace, Momi ta watsa masa harara,


“Toh ko rufe ta zakayi da duka ne da yake kai marar tausayi ne ko?”


“Momi ba wai rashin tausayi ba taya zata min karya”


“Ba karya nake maka ba Saif tunanin ka ne ya dame shiyasa na bar gida naje can dan na samu sassauci har hakan ya faru dani ban sani ba”


Ta faɗa a wahale hawaye na gaggaro mata, abun ka da wanda kake ki nan take yaji kamar ya kamo ta ya shake ta karasa mutuwa, Fuuuu ta fice daga ɗakin dan yasan yanzu da ya kara wata maganar Momi cikinsa zatayi da faɗa, Momi ta kai hannu ta shafa ta cike da tausayawa,


“Dan Allah ki rika sawa kanki sanyi Safiyyah ki bar damun kanki”


Sannan ta tashi ta fice Gwaggo laraba na watsa mata harara,

Bayan ta fice ta kalleta 


“Wato har yanzu baki cire son Saif cikin zuciyarki ba ko?”


“Gwaggo ya zanyi na cire abunda bani na wasa kai na ba wallahi ina son Saif Gwaggo”


“Amman ai su basu damu da son da kika masa ba, tun da da basu barshi ya auri bare har biyu ba, kuma ki duba ko yanzu yadda yake miki, koda ƴake ba laifin sa bane laifin uwarsa ne tunda ita ta goya masa baya yayi yadda yake so gashi nan kinje kin kare kanki a banza ko tausayin ki basa yi, inama ruwanta tunda ba yarta bace”


Kuka sosai Safiyyah take kuka da baya fita,


“Na gwammace mutuwa ta da rayuwa ta Gwaggo nafi son na mutu na huta”


“Ba zaki mutu ba zaki ji sauki in Allah ya yarda kuma walllahi ko ina yawo da zane sai kin auri Saif, ba dai dan sunga ba ki gata shiyasa suka miki haka ba, yarinya ta tashi a hannunku ta girma amman wai dan mugun sheri ku kyale yaron ku yayi yadda yake so da ita”


Tayi kwafa cike da ɓachin rai tana wanu karkaɗa kafa, 

   Guraren Sha ɗaya likitoci suka shigo tare da nurses suka chanja mata gadi suka wuce da ita wani ɗakin dan yi mata gyara.



WASHE GARI....................



2:47pm


Minal na zaune Kairat tana mata fira Dr. Zainab ta turo kofar ɗakin ta shigo fuskarta ɗauke da murmushi hannunta kuma rike da allura, 


“Minal ya karfin jikin naki?”


“Yayi sauki alhamdulillah”


Ta amsa mata tana murmushi, Kairat ta gaishe ta cike da girmamawa, bayan ta amsa tace


“Sai ki rika mana yar uwar taki zanyi mata alura”


Ba musu Kairat ta tashi ta rika Minal, abun ƙa da mai neman lafiya duk da bata son alurar sai ta tsaya kurun akayi mata,

  Bayan ta kare ta kalleta tana murmushi


“Kin san Alurar me nayi miki?”


Kai ra girgiza mata tana murja gurin,


“Alurar zubar da ciki ce”


Ras! Ras!! Ras!!! Gabanta ya yanke ya faɗi taja baya da sauri tana zaro ido, Kairat ma tashi tayi tsaye tana kallonta rike da baki,


“Mi...mina...miki.. Wane laifin abinda ke ciki na yayi miki?”


Mere baki tayi,


“Baki min komai ba kuma abunda yake cikin ki bai min laifi ba, 

   Biya akayi na zubar da wannan cikin naki”


“Waya biya ki? Waya saki wannan aikin?”


Kairat ta tambaya tana cin kalar rigarta, kallonta tayi


“Relax young lady”


“Wane irin Relax ke baki da hankali ne ? Zaki zubar da cikin yar'uwata kuma ki ce min relex sai kin faɗa min wanda yasa ki wannan aikin, ko nasa a kulle ki”


“Ba matsala ba bace dan kinsa an rufe ni saboda wanda yasani wannan aikin shine zai fiddo ni”


“Waya saki?”


Minal ta tambaya numfashinta na rawa,


“Saif mijin ki shiya sani”


Hankalin Minal bai kara tashi ba sai a lokacin, bata san lokacin data jingina da bangon ɗakin ba ta sulale kasa zaune tana hawaye,

  Mi tayi ma Saif da zai sa a zubar mata da ciki ? Mi yake nufi da ita ne?


“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”


Shine abunda Kairat take ta maimaitawa bayan ta saki rigar Doctor,

  Dr. Zainab ta kalli Kairat


“Kar kiga laifi na nima sani akayi kuma wanda ya sani yace min shine uban wannan yaron kuma yace Minal ma tasan da maganar i hope u understand”


Basu mata uffan ba kowannen su hawaye yake itama bata jira cewar su ba ta juya ta fice,

 Sai a lokacin Minal ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi ta makure kanta jikin jina kamar wata marainiya tana kiran sunan Mummy.

[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO


         NA


KHADEEJA CANDY

 


®

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)



*33*



Ganin yadda hankalin su duk ya karkata gurinta ya bata damar ci gaba tana kallon Momi, 


“Nasan Minal tana son Yaya sosai so zata iya yin komai dan taga da dawo masa, maybe ba ki cin sa bane bamu da tabbatacin haka” 


A fusace Nasir ya kalleta, 


“Wannan wace irin magana ce haka Safiyyah.... -” 


Momi ta tari numfashi sa


“Tana da gaskiya Nasir maganar ta abun dubawa ce” 


“Idan ma har haka kuke jima tsoro ai zamu iya jiran har ta haihuwa sai a yi gwajin jini a gani ko, in yaso sai muyi da rainon ciki” 


Hakan ma baiyi ma Safiyyah daɗi ba ta kalle Nasir cike da jin haushi, 


“Yaya Nasir taya zamu rik'a rainon cikin da bamu da tabbatacin namu ne ko ba namu ba, cikin shege.... -” 


Tasssss Saif ya wanke mata fuska da mari, jin ta anbace cikin da shege shi kanshi ba shi da tabbatacin nashi ne ko ba nashi bane amman zuciyar shi na bashi wani abun daban, kwakwalwalshi a yanzu rikece take daman ya daɗe da rasa natsuwar dake tare dashi, 


Tsawa Momi ta katsa masa, 


“Saif miye haka daga faɗan gaskiya maganar ta fa abun dubawa ce” 


Tashi yayi rashin a ɓace yana faɗin


“Momi i need to think” 


Ya fice, Nasir ma tashi yayi ya fice, cike da jindaɗin mari da Saif yayi ma Safiyyah, 

  

“Duk abunda za'a faɗa masa ba yarda zai yi ba saboda kamar ba banza suka barshi ba”  


Safiyyah ta faɗa tana shafa gurin da ya mare ta ɗin, Lubna ta girgiza kai, 


“A a anty ni gani nake kamar cikin na Yaya ne saboda... -” 


“Saboda me ke baki da hankali ne Lubna yarinyar nan shi fa da kansa ya kamata da wani taya zamu tabbatar cikinsa ba wannan sam ba cikin Saif bane” 


Safiyyah ta faɗa a fusace, ta tashi ta nufi ɗakinta


“Allah ya kyauta” 


Momi ta faɗa tana janye tagumin dake fuskarta, Lubna ta amsa da ‘Amin’ 


         

                  ***   ***   ***


Jingine da Mota Nasir ya tararda Saif ya kifa kai idonshi a rufe kamar marar lafiya,

   Dafashi Nasir yayi cike da tausayawa,


“Saif ka daina damun kanka da yawa you are too young for that bai kamata a'ce kana samun matsalan iyali a yanzu ba”


Juyowa yayi yana sauke ajiyar zuciya ya kalli Nasir


“Nasir na rasa meke faruwa da ni al a murran nan suna kokarin rikata ni”


“Saif kar maganar Safiyyah ta shiga kanka ni gaskiya ban yarda Minal ta aikata abunda kake zaton ta dashi ba wannan cikin naka ne Saif”


Fuskarsa ya shafa 


“Nasir da ace ba ni na gani da kai na da zan iya yarda kazafi akayi mata, kuma da ace ba Deen bane nan ma zan iya mata uzuri amman kasan yadda take son Deen”


Nasir ya tattara girarsa,


“Ka yarda kenan ba kicin ka ba ne? Baka kusan ceta ba ko?”


Wata bazawarar dariya yayi yana gyara tsayuwarsa yace


“Taya za a kaiwa namiji lafiyayye mace kyakkyawa kamar Minal ya kwana ɗaki ɗaya da ita gado ɗaya yace babu abunda ya shiga tsakanin su! A kasan ba zai yiyu ba, A washe garin daren da mukayi first night na kamata da Deen and you know what she's virgin”


Ya faɗa yana kallon shi, Nasir ya taɓa hannunshi 


“Good wannan kawai bai isa ya karantar da kai Minal bata aikata ba, karka manta Saif Deen fa gani nake kamar yana sonta zai iya yi mata haka ko dan ya ɓata tsakanin ku”


“Yes Saif ina wannan tunanin but abunda yake ban mamaki shine taya akayi ya kai har cikin ɗakinta bata sani ba kasan ba zai yiyu ba kuma ita da kanta ta amsa ƙlaifinta after that, chat ɗin da suka yi kasan babu mai ɗaukar mata waya ya haɗa mata wannan ko?”


Shiru Nasir yayi dan bashi da abun cewa a wannan gurin, lallai ko kotu akaje yasan Minal bata da mafitar wannan shima kanshi yana mamakin yadda hakan ya faru, sai dai shi bai yarda wani abun ya shiga tsakanin su ba, sai dai zai iya yarda ita ɗince tace yazo, toh kuma chat ɗin da sukayi kayi fa! Oh Allah,

  Ya dafe kanshi yana sauke ajiyar zuciya,


“Wai toh ya a kayi kaga chat ɗin da sukayi?”


“Safiyyah ce ta faɗa min”


“Safiyyah?”


Ya karɓa sunan da karfi fuskarsa kuma cike da mamaki, 


“Toh taya akayi Safiyyah tasan abunda yake cikin wayar?”


Kafaɗunsa  ya ɗaga


“I dont know kasan mata suna share ɗin phones ɗinsu, ni dai ba ma wannan ba i need to Minal ya aza ayi?”


“Tana success special hospital ICU unit 4 but amman maganar nan abun dubawa ce Saif i doubt yadda tasan chat ďin”


Saif bai sake ce masa komai ba dan shi hankalinshi bai bashi abunda ya ba Nasir ba, buɗe motarsa yayi ya shiga,


“Bari naje na ganta i can't wait to see her”


Kai kawai ya ɗaga mashi yana kallon motarshi har ya fice,




                ****************


Safiyyah tun da ta shiga ɗakin yake safa da marwa zufa na karyo mata, daga bisani ta figi gyalenta da makullin mota ta nufi parking space,


   Kai tsaye gidan Huda ta nufo, bako sallama ta shigo parlour, kallo ɗaya Huda tayi mata itama hankalinta ya tashi ganin damuwa karar a fuskarta dan tasan duk abunda ya samu Safiyyah ya same ta,


“Lafiya Safiyyah me ya faru?”


Hannayenta ta rika suka zauna,


“Ba lafiya ba Huda Minal na ciki na wata uku kuma kinsan na Saif ne!”


Ihu Huda tayi da ɗora hannu saman kai ta fashe da kuka


“Na shiga uku na lalace taya hakan ta faru ? Wayyo ni Allah na”


Safiyyah ta daga ta,


“Babu lokacin wannan Huda mafita ya kamata mu nema saboda Saif bai gama yarda cikinsa bane Momi ma haka kamata yayi mu samu mafitar zubar da cikin, kinga kamin a ankaro cikin ya riga ya zube”


Sai a lokacin hankalinta ya ɗan kwanta,


“Kin kawo shawara toh yanzu ya zamuyi ina Minal ɗin take?”


“Tana asibiti jiya a ka kwantar da ita”


“Toh yanzu miye abun yi?”


Huda ta tambaya,


“Tunani nake yi ko zamu je asibitin ne mu samu wani likita yayi mata allurar zubar da ciki sai mu biyashi”


“Kina ganin hakan zai yiyu ?”


“Zai yiyu mana kuɗi miye basa sawa sai idan mutun baya dasu”


“Wace asibitin take ne? Akwai wata aminiyata babbar likita ce nasan zata iya taimaka mana”


“Walkan kinga ta kwana gidan sauki kenan, a Success Special hospital aka kaita”


“Wallahi can kawar tawa ke aiki amman wannan abun yayi daɗi”


Huda ta faɗa tana dariya, wani ihun daɗi Safiyyah tayi har da buga kafa


“Wayyo daɗi”


Tuno Saif yasa ta rufe baki,


“Inji Yaya baya nan dai?”


“Baya nan ke kuwa a da bazan bari muyi maganar nan a parlour ba”


“Toh kinsan yanzu yadda za'ayi tashi zakiyi muje gidan su likinta mu yi mata magana muji yadda za ayi”


“Toh bari na kira ta naji ko tana gida”


Tashi Huda tayi ta nufi ɗaki.

  Bata jima ba ta fito sanye da Hijab tana faɗin 


“Tashi muje tace tana gida amman anjima kaɗan zata je aiki”


Tashi Safiyyah tayi cike da jinda ɗi ta suka fice,



***    ***


A hankali taji ana taɓa mata fuska ana shafa kanta zuwa wuyanta, numfashi ta sauke a hankali ta kara karkaro kanta ta dan taji daɗin yadda ake shafa ta ɗin duk da bata san waye ba,

Kanshin turaren da taji yasa tayi saurin buɗe ido, kan fuskar Saif ta saukar da su yana mata murmushi,


“Kamar Saif....”


Ta faɗa tana maida idon nata a lumshe, dan gani take gizo idonta yake mata saboda da famarkin shi da take,

 Jin an taɓa mata ciki yasa ta kara buɗe idon, dirr kuma ta sake sauke su akan fuskarsa, yanzu kan ba gizo idonta ke mata ba, Saif ne ganin hawayen dake kwance cikin idonsa, hannu tasa ta ture masa hannu sai ta rike mata hannun gam yana hawaye,


“Minal.....”


Sai kuma yayi shiru ya kasa magana, toh me zai ce mata? Cikinsa ne ko ba nashi ba bashi da tabbaci bai kuma kamata ya bata hakuri ba tunda ita tayi masa laifi kuma in har da gaske ne shi ba zai iya zama da ita ba.

   Yana wannan tunanin yaji tana kokarin kwatar hannunta, a nan ya sakar mata hannun ya kalleta kamar zaiyi magana sai ta rigashi,


“Please Saif i need to be alone”


Hannu yasa ya share hawayen da suka zubo masa ya juya cike da jin haushin tashin ta da yayi daga bachi tunda gashi ya rasa abunda zai ce mata, daman shi burinsa ya ganta kuma ya ganta bai san salon da ya kaishi taɓa mata fuska ba.


  Bayan ya fice ta sauke ajiyar zuciya,


“Alhamdulillahi”


Ta faɗa tana lumshe ido, ta samu sassaucin halin da take ciki, tasan Saif ya yarda da cikinsa ne a jikinta shiyasa ya kawo kansa gurin ganinta.



   A ɓangaren Safiyyah suna fita suka nufi gidan Dr. Zainab, karba tayi musu mai kyau ta kawo musu abin sha, bayan sun ɗan taɓa fira suka bayyana mata abunda ke tafe dasu, Sunsha mamaki lokacin da take gaya musu ita ce Doctor dake duba Minal, 


“Ni nake kula da ita sai dai abunda kuke so ba zai yiyu ba dan ba aiki na bane”


Safiyyah ta marairaice murya,


“Haba Dr dan Allah ki taimaka mana wallahi ko nawa kike so zan baki ki ma bani account number ɗinki zan turo miki so mun taɓo”


Sam Dr.Zainab ta ki yarda, hakan yasa Huda nuna mata ɓachin ranta a fili,


“Haba Zainab ace duk amincin dake tsakanin mu kin kasa yi min wannan aikin bafa ita mukace ki kashe ba kuma abunda xaki xubar fa ba a riga an busa masa rai ba”


“Abunda kike son na aikata abune mai matukar wahala Huda ba zan iya ba”


Sata gaba sukayi ita da Safiyyah suna mata magiya, ta roko da daɗin baki, ganin zasu ɓata mata lokacin zuwa aiki yasa tace


“Shi kenan zanyi Shawara”


Sunji daɗi sosai basu bar gidan ba sai da Safiyyah ta karɓi account number ɗinta,

   A mota firar kawai suke suna jin daɗi, sun san matsalar su ta warke, bayan Safiyyah ta sauke Huda sukayi Sallama ta nufi gurin da Deen yake, dan tun ɗazu ya matsa mata da kira wai yana son ganinta,


  Wani babban restaurant mai kyau da tsada naga ta nufa tana yin farking ta kira shi a waya,


“Gani na iso kana ina?”


“Ina ciki hawa na biyu na ganki ai karaso kawai”


Kashe wayar tayi ta rufe motar ta ta nufi gurin,

  Tsaye ta tararda shi bakin kofar hall ɗin fuska babu annuri yana kallonta,


“Ya akayi ne Deen sauri nake yi gida zanje ka dame ni da kira”


Shiru yayi kamar ba dashi take ba, ganin bashi da niyar magana yasa tayin dariya,


“Deen kenan idan wani abun kake so ka faɗa ni wuce zanyi yanzu fa ba kamar da bane da zaka rika yi min haka haka da hankali na riga na gama da naka kawai ka jira result” 


“Result ɗin me?”


Sai a lokacin yayi magana,


“Idan ta fito ka aureta mana bashi kake jira ba”


“Kin riga kin ɓata ni gurin Minal babu yadda za'ayi ko da Saif ya sake ta na iya aurenta sannan yanzu haka Minal na can asibiti kwance a dalilin abunda muka mata”


Iskan dake bakinta ta bursar


“Deen Deen kana bani mamaki wani lokacin fa kasan ba xaka iya jurar lokacin da komai xai daidai ta ba miyasa ka aikata”


“Ai ke kika sani na aikata koɓ”


Ya faɗa a fusace,


“Nasa ka ka aikata kai ko kunya baka ji ba ? Mace kamar ni xata sauya maka tunani ka aikata abunda baka yi niya ba? funny kar fa ka fito min da wani can ko kace wai tausayinta zai sa ka tona ma kanka asiri”


“Ko kuma ke na tona miki ba”


“Ka tona na ma kanka dai ai kasan ko kotu aƙaje kai ne tsamo tsamo a cikin laifin tunda kai ka shiga har ɗakinta kuma ka rika matar mutane kuma ka nuna ma mijinta kana tare da matarsa, so kayi hankali dan naga har yanzu baka gama sanin wacece Safiyyah ba fool!”


Wata harara ta watsa masa ta juya tayi tafiyarta, ya fisacta sossai yasan duk abinda ta faɗa kansa hakan yake dan ta riga ta ɗaure gashi kuma tasa yaci amanar minal ya ɓata kansa gurinta, har shi zata raina ma hankali haka?

   Rufa mata baya yayi da sauri, zuciyarsa cike da tsanarta. Cikin sa'ah kuwa ya cin mata a stairs tana sauka bata an karaba kawai taji an turo ta da wani irin karfi, gangarowa tayi tana wani irin ihu da ya ɗauki hankalin duk wanda ke cikin restaurant ɗin.



IMAGE WHAT HAPPEN NEXT.............

[9/14, 9:07 AM] Auntie Candy: BABBAN GORO


         NA


KHADEEJA CANDY

 


®

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)




*36*


Kasa Saif yayi da kanshi ya ƙlumshe ido yana sauke ajiyar zuciya,


“Ka yarda da ni Saif zan maka duk yadda kake so amman idan nima kayi min yadda nake so”


Buɗe ido yayi ys kalleta,


“Wa nene wanda kike son a sako miki.?”


“Mijin Mahaifiyata ne bayan rasuwar Mahaifin mu mahaifiyata ta aure shi ni kaɗai ce ta haifa da Babana sauran duk nashi ne tun da aka kamashi ita da sauran yan uwana sun kasa samu natsuwa ni kaina na kasa samun natsuwa saboda rashin natsuwar nata”


“Mi yayi aka kamashi?”


“Yan danfara suka danfare shi ya ranta musu kuɗi sai suka gudu shine su kuma suka kamshi”


“I hope gaskiya kika faɗa min!”


“Ko da yana da wani aibin toh ban sanshi ba, dan ni haka mahaifiyata ya faɗan min kenan”


“Fine Miye sunan shi?”


“Sunanshi Alhasan Muhammand Yola”


Wayarsa ya ciro daga aljihu ya dannan kira, bata daɗe tana ringing ba aka ɗauka,


“Ka bincika min wani da aka kama mai suna Alhasan Muhammad yola”


Yana faɗa ya kashe wayar, ya kalleta 


“Make sure gaskiya kika faɗa min akan Huda dan duk na gani karya kike sai na sa an wulakan ta ki”


“Gaskiya ce mana Saif how do think mace kamar ni can lie to someone like you!

 idan zaka yarda zan fara baka evidence yanzu”


Bata tsaya jiran abinda zai ce ba ta ɗauko wayarta, ta shiga danne-danne, daga bisani ta ɗago ta kalleshi


“Ka buɗe Bluetooth ɗin ka zan turo maka wani abun yanzu sannan ka bani number wayar ka zan turo maka wasu abubuwan ta whatsapp”


Bai mata musu ba ya mika mata wayar ta tura masa abubuwan, ta mika masa wayar tana faɗin,


“Ina son ka kunna wannan Audio ka ji a cikin Audio akwai wanda zaka ji yadda suka shirya komai tsakanin ta da Safiyya na abunda akayi ma Minal kuma nasa maka wata number mai sunan Faruk inason kasa number a wayan Huda jaga ya sunan zai fito sauran abubuwan sai ka cika alkwari nima zan cika maka”


Hannu yasa ya karɓa bai ce da ita komai ba kwakwalwarshi a tushe take, shi har yanzu bai yarda ba sai ya samu hujojin akan hakan, yana zuyawa ta kira shi


“Saif.... Kayi kuskuren auren Huda ka aureta ba tare daka bincika wacece ita ba baka bincika tarbiyarta ba Huda tana tare da abokin karatun ka ko kuma nace abokin ka tun bata aure ka ba sanadiyar sa ta sanka ka ganta kace kana sonta”


Bai juyo ba kuma har lokacin bai ce mata komai ba ya fice.

  Har ya isa parking space bai san ya isa ba saboda tunani.da yake magangun Dr.Zainab ne suke masa yawo kai ya daɗe tsaye gurin motarsa kamin ya buɗe ya shiga,  koda ya isa gida har wani ciwon kai yake ji a cikin motar ma ya daɗe zaune kana ya fito ya nufi cikin gidan.

Yana tura kofar falon Huda dake zaune sanan kujera ta taso da gudu ta tarbeshi tana faɗin,


“Oyoyo Habibi sannu da zuwa” 


Kallo ɗaya tayi masa ta ganshi abnormal, sai dai ba zata iya tantance halin da yake ciki ba, saboda yayi kamar marar lafiya kamar kuma mai damuwa.


“Dear lafiya na ganka haka?”


Ta tambaya cike da damuwa, Kallon fuskarta yake sai yanzu yake tuna wasu abubuwan nata, maida ta yayi gefe ya nufi upstairs hanyar ɗakinsa yana shiga ya maida kofa ya rufe ya zauna gefen gado ɗafe da kai, 

   daker ya samu ya shiga banɗaki ya watsa ruwa ya fito, ya saka jallabiya da gajeren wando, Sai a ƙlokacin natsuwa ta ɗan shige shi, yana shirin zama Huda ta shigo ɗauke ta turen drinks fuskarta ba far'ah, kusa dashi ta zauna ta zuba masa drinks ɗin tana masa magana,


“Dear ga Drinks ɗin ka kasha nasan rayuwar ka zatayi sanyi sai ka faɗa min abinda yake damunka”


Ko ɗago wa baiyi ya kalleta ba balle ya bata amsa, sosai hankali ta ya tashi rabon da taga ɓacin rai shi irin wannan har ta manta, toh mi yake damunshi ko wani abun akayi ne?


“Saif kayi min magana mana ko nayi maka wani laifin ne?”


Ta faɗa cikin muryar kuka, sai a lokacin ya kalleta ya ɗan murmusa kamar babu komai,


“Wani ne ya ɓata min rai a office amman karki damu ya wuce”


Drinks ɗin ta karɓa ya sha yana janta da fira dan ya kawar mata da zagin dake ranta,

  Ita kuma hankalinta ya kwanta ganin ya dawo dai-dai.



DARE.....................

  Tare sukayi hira a ɗakinta sai da ya tabbatar da bachi ya ɗauke ta sannan ya ɗauki wayarta ya saci kafa ya fice ɗaga cikin gidan ya nufi gurin motarsa ƴa buɗe ya shiga bayan ya rufe ya kunna Audio da Zainab ta tura masa,

   Ba karamin mamaki yayi ba jin abunda Audios ɗin ya kumsa jikinsa ya mutu sosai da abunda kunnuwansa suka ji masa, tabbas muryar Huda ce kuma duk maganganun da yaji akan sa ne sai kuma Minal wani gefen da saurayin nata, Duk wasu tambayoyin da yake son sani ya samu amsar su a Audios. jufa ce ta shiga karyo masa a nan take yaji kansa na tsarawa, wayarta ya ɗauka ya saka number da Zainab tasa masa, Ga mamakinsa sai ga number ta fito amman ɗauke da sunan _FAIRUZA_ a nan take ya danna ma number kira da wayarta, Bai kara katsewa ba sai da yaji muryar namiji muryar abokinsa ƴa ɗauka,


“Hello Sweetheart baki yi bachi ba?”


Bai amsa ba sai kawai ya kashe wayar, ya fito cikin motar a fusace ya nufi ɗakinta, yana isa mai number ya kara kira, wani mugun bugu Saif ya kai mata ta farka a firguce tana haki, wayar ta mika mata ba tare da yayi mata magana ba daman already yayi picking yasa hands-free,


Karɓa tayi amman bata kara wayar a kunne ba sai kallon Saif take jikinta na rawa,


“Hello Sweetheart naji kiran ya katse ne kp network ne?”


Jin muryar mutunen yasa ta kalli gaban wayar number da taga hankalinta yayi matsifar tashi, kamar wanda ya ruɗe sai tace 


“Wanene?”


Tana kallon Saif,


“Wanene kuma Faruk ne ba Huda bace?”


Shiru tayi batayi magana ba sai kallon Saif take abunda ka marar gaskiya nan da nan idonta ya faɗa wani zafi ya rufeta baki buɗe tana numfashi kamar marar lafiya, jin hakan yasa mai kiran ya kashe.

[9/14, 9:07 AM] Auntie Candy: BABBAN GORO


         NA


KHADEEJA CANDY

 


®

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)



*35*


Fita Kairat tayi da saurin ganin yadda Minal ke kiran sunan Mummy tana kuka,

  Ga mamakin ta sai ta tararda ita ma Mummy tana nata kuka wanda ya fi na Minal shiga rai, miya faru ko ita ma ɗin taji abunda Dr. Zainab ta aikata?. 

  Kasa mata magana Kairat tayi sai kawai ta dafa ta tana hawaye, A firgice Mummy ta juyo sai a lokacin ta tuna duniyar da take, ganin hawaye a fuskar Kairat yasa ta share nata hawayen tana tambayar ta


“Lafiya Kairat mi kike yi ma kuka?”


“Abunda kike yi ma kuka Mummy”


Ta faɗa hawayen na kara zubo mata, a zatonta Mummy tana kuka ne akan abunda Dr.Zainab tayi


“Wallahi Mummy duk cikin Minal ya zube sai nayi shari'ah da wannan likitar bazan yafe mata ba”


Mummy ta rika hannunta cike da fashin fahimtar inda ta dosa


“Mi kike nufi Kairat mi ya samu ciki Minal.?”


Ta share hawayen da ke idonta,


“Mummy Dr tayi mata allurar zubar da ciki”


Sakinta Mummy tayi ta jingina jikin gina ta lushe ido tana sauke ajiyar zuciya,

  Ta kasa gasgata abunda Kairat ta faɗa da kuma wanda Dr Zainab ta faɗa mata, miye gaskiya mi Dr take kokarin yi?


“Innalillahi wainna ilaihi raji'un”


Ta faɗa a fili still idonta na rufe hawaye suka zubo mata,


“Mummy ya kamata muyi wani abu ba wai mu tsaya tunani ba yanzu ba lokacin tunani ba ne”


Cewar Kairat cike da kaguwa,  Mummy tayi mata kallon natsuwa kallon ɗa da uwa irin nasu na manya,


“Kairat Dr Zainab ta faɗa min ciwon Minal yana matakin....karshe ne zan iya rasa ta ko wane lokaci ta faɗa min idan har inason rayuwar ta dole ne nasa hsnnu a fitar da ita waje ayi mata canjin jini and you know yadda canji jinin yake zata iya rasa ranta babu tabbacin rayuwarta”


Dora hannu Kairat tayi saman kai a maimakon tayi kuka sai tayi murmushi mai tare da hawaye murmushin da ake cewa yafi kuka bakin ciki, ta cire ɗankwalin dake kanta ta jefar kasa ta rufe baki tana hawaye,

  Mummy ma kuka take amman na zuci ko wannen su xuciyarsa ɗauke take da tausayin Minal, Sun daɗe a gurin babu wanda ya sake cewa wani abu sai faman sauke ajiyar zuciya Mummy ke yi, suna haka Dr Zainab ta iso gurin rike ta wasu files a hannunta, tsayawa tayi dai-dai Kairat ta dafa ta,


“Ki kwantar da hankalin ki ban zubar da cikin nata ba I'm just trying to help alurar bachi nayi mata yanzu haka tana can tana bachi”


Kairat ta kalleta kwakwalwarta a jagule bata ce mata komai ba, Ita bata ji ta ce mata ba ta cigaba,


“Na faɗi hakan ne dan kawai na ɓata Saif a idon Minal, a binciken da nayi na gano Minal tana fama da ciwo zuciya mai tsana ni kuma nasan akan Saif ne, a halin da ake yanzu Minal ta fi son abunda yake cikinta saman da Saif sanadiyar wannan abun da na faɗa zata sasauta ma zuciyarta sonshi ta kula da abunda yake cikinta

    Kairat mutuwa ba a hannuna take ba amman Minal zata iya rasa ranta a ko wane lokacin abun tausayi rai biyu za a rasa tun da ga ciki a jikinta”


Sai a lokacin Kairat tayi mata magana,


“Amman taya akayi kika san Minal.na son Saif har haka? Ban yarda dake ba Dr faɗa min wacece ke?”


Murmushi tayi ta gyara tsayuwarta,


“Nasan Abunda yake damun Minal saboda ni likita ce, nasan halin da Minal take ciki saboda ni aminiyar kishiyarta ce Huda nice kaɗai mace da zan iya wanke Minal a.yanzu ni nasan yadda aka kulla komai”


Ja da baya Kairat tayi cike da tsoro tana kallonta, Mummy ms kallonta take cike da rashin fahimta,

Ganin hakan yasa ta cigaba


“Kairat yanzu taimako ɗaya nake son kiyi ma yar'uwarki ina son ki ɗauki waya ki kira Saif ki faɗa masa nayi ma Minal allurar zubar da ciki”


“Saboda me?”


Kairat ta tambaya,


“Saboda yazo nan na faɗa masa gaskiya na wanke minal daga zargin da yake mata kinsan ganin Saif ba abu ne mai sauki ba sai idan shi yaso ganinka”


“Miye dalilinki na taimakon Minal? Bayan ke aminiyar Huda ce wata kila ma dake a ka haɗa kai akayi mata wannan shaerin?”


Mummy ta faɗa tana mata wani kallo mai cike da tsana,

Murmushi kawai tayi ta kalli Kairat,


“Ki kirashi yanzu nan”


Tana kaiwa nan ta juya ta bar gurin, Mummy ta matso kusa da ita,


“Karki kirashi Kairat baki sani ba ko wani sherin ne take son kulla mana”


Kai kawai ta ɗaga ma Mummy ta nufi Hanyar da zata sadata da ɗakin da Minal take kwance, ganin hakan yasa Mummy ta rufa mata baya suka shiga ɗakin tare.



*               *               *                *


Ya daɗe tsaye a bakin kofar sannan ya mika hannu ya buɗe ya shiga, shi kan inba dan faɗan da Momi tayi masa ba jiya babu abunda zaisa ya sake shiga ɗakin dannya bashi haushi shiyasa tun jiya da aka fito da ita daga aikin bai leko ba,


Tana kwance an ɗaga kafarta da akayi ma aikin  da wani farin abu hannunta kuma na saman cikinta idonta a buɗe fuskarta so indecent. Sai da ya karaso kusa da ita sannan ya ɗauke idonsa daga kallon tsanar da yake mata, daga jiya zuwa yau tsanar da yake mata ta karu sosai ko dan faɗan da Momi ta masa oho ko kuma dan kowa ganin laifinsa yake yana ganin wai kiyyayar da yake nuna mata yayi yawa ne, shi dai bai san dalili ba daman can Allah bai haɗa jininshi da ita ba tun tashin ta gidan su.

  Tun daga buɗe kofar ɗakin tasan shine ya shigo saboda kanshin turarensa jira take har sai yayi mata magana sannan ya juyo ta kalleshi, jin bashi da alamun yi mata magana yasa ta juyo da fuskarta ta kalleshi, hawaye ne suka cika mata ido yana sane da tana sonshi amman yayi mata wulakanci ya tsalake ta yayi mata biyu baya tausayin halin da take ciki shi sam bata gabanshi wannan wane irin mutun ne haka miyasa ma ta kamu da sonshi har haka.....?


Murmushin da yayi mata ne ta katse mata tunani, dan abunda bata taɓa zato bane daga gareshi, hakan yasa ta samu karfin motsawa har da sa ɗayan hannunta ta share hawayen da suka zubo mata,


“Sannu Sister”


Jimmm tayi bata amsa ba bakinta yayi mata nauyi sosai, daman tun da aka fito da ita daga aikin ba wata magana take ba daga ae sai a a,

Kujera yaja ta zauna yana fuskantar ta rasa yayi abunda zai ce mata


“Kin ci abinci.?”


Ya faɗa instead of yace mata ya jiki, daɗin tambayar da yayi mata da hana ta ɗaga masa ko da kai ne balle tace masa ‘Ae’ shi kan ba karamin juriya yake ba gurin sake mata fuska dan kawai yana son bin umarnin Momi ne,


Wayarsa ta tayi kara kamar mai jira ya fito da ita da sauri yana duba mai kiran, Number Kairat ce har yayi kamar ba zai ɗauka ba sai kuma ya dannan picking ya kara a kunne, saboda isa yaki yayi magana duk da faduwar da gabansa yayi saboda kukan da yaji Kairat ɗin nayi,


“What”


ya amsa da karfi tare da mikewa tsaye,


“Waya mata?”


Bansan me aka ce masa ba na dai ga ya kashe wayar ya juya da sauri ya bar ɗakin.

    Kai tsaye ya ya nufi asibitin yana isa ya nufi ɗakin da yasan Minal take, yana tura kofar ɗakin ya ganta kwance ya sharar bachinta hankalinta kwance zuciya kuma zaune, numfashinta na tafiya dai-dai, da sauri ya karasa kusa da ita ya shiga duba jikinta kamar wani likita ganin babu alamun wani abu a tattare da ita yasa shi ɗan ja baya ya dafe kai yana sauke ajiyar zuciya, zuwa can kuma ya matso yana kallon fuskarta, ya kai hannu ya shafa cikinta,


“You love her Saif you can't leave her can you?”


Dr. Zainab ta faɗa tana takowa kusa dashi a hankali, a fusace ya juyo yana mata wani wawan kallon


“Me kika mata.?”


“Me kake tunanin zanyi mata? Meye damuwar ka da abunda zanyi mata tun da baka damu da abunda ya shafe ta ba baka son abunda yake cikinta!”


Ta karasa maganar dai-dai lokacin da ta karaso kusa dashi, ta aje wasu files ya kalli Minal cike da tausayi sannan ya sake kallon shi,


“Saif yarinyar nan tana level ɗin da zata iya ransa ranta a yanzu a anjima a gobe, kuma idan ta mutu rai biyu za'a rasa rayuwarta da kuma abinda yake cikinta amman hakan bai dame ka ba baka damu da duk abinda zai same ta ba sai yanzu nake ganin laifin duk mace da take sonka dan baka cancanci a so ka ba baka san miye so ba baka san darajar so ba ba kuma san zafin so ba! 

 miyasa baka tsaya kayi tunani ba Sai kawai ka ɗauki karan tsana ka ɗorawa Minal ?”


Hannayensa yasa cikin aljihu yana murmushin gefen fuska,


“Kin cancanci a biya ki da wadan nan kalaman tell me nawa suka biya ki i can paid more you know Who I am right?”


“Ba biyana akayi ba Saif gaskiya ce zatayi halinta lokaci yayi da ya kamata kasan wayr Huda wacece Safiyyah kuma wacece Minal”


Tsaki yaja ya ya juya da nufin ficewa daga ɗakin,


“Minal bata aikats abunda kake zarginta dashi ba, Abinda idonka suka gani plan ne da kanwar ka Safiyyah ta haɗa tare da Deen da Huda aka haɗa komai!”


Cak ya tsaya dai-dai lokacin da ya kai bakin kofar ya juyo yana mata wani kallo irin karki raina min hankali fa,ganin hakanyasa ta cigaba


“Ina da sheida akan hakan Saif nasan kasan ni aminiyar Huda ce duk abinda tayi sai ta faɗa min ina da voice record ɗin duk abinda ya faru zan iya haɗa plan ka kama Huda da idonka kaga irin cin amanar da take maka tare da abokinka matarka  Huda ita kanwar ka Safiyyah sun same ni har gida suka ce na zubar da cikin Minal saboda idan ta haihu asirin su zai tono zasu bani ko nawa nake so ina sa security camera a gida na tana zan iya nuna maka komai idan kana so Saif Huda bata haihuwa ita kanta tasan da wannan amman tana shan magani hana haihuwa saboda tana jin tsoro kar Allah ya jarrabe ta ta samu ciki da wacan abokin naka kuma tasan duk ta haihu sai ta samu matsaƙa da wacan abokin naka ko kuma nace tsohon saurayinta, baka taɓa ksmata da kwayoyin hana haihuwa ba? ita da kanta ta bugo min waya ta faɗa min”


Shi kan yama kasa gane duniyar da yake shin mafarki ne ko gaske ? maganganun yaji kamar saukar wahayi, idan har da gaske ne miyasa zata tona asirin aminiyarta?

  kamar tasan abunda yake ranshi sai kawai ta tako ta karaso kusa dashi


“Nasan zakayi mamakin dalilin fallasa sirrin Aminiya ko? toh akwai dalili duk waɗannan abubuwan dana faɗa maka ba zan tabbatar maka da su ba har sai ka biya min wata bukata tawa”


Kallonta yayi fuskarshi ɗauke da mamaki zuciyarsa kuma cike tambayoyi, bai tanka mata ba ita ma ɗin bata jira ya tanka mata ba tace


“Wani tsoho nake son kasa a sako daga gidan yari ni kuma zanyi maka duk abinda kake so”


Har lokacin bai iya mata magana ba but still yana kallonta maganganun ta sai dawo mishi suke.




KUN SAN WANENE TSOHON.?

[9/16, 6:47 AM] Auntie Candy: BABBAN GORO


         NA


KHADEEJA CANDY

 


®

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)



_Filin wasan giwa ba na biri bane idan kaga kashi a turmi bana wadan kare bane kuma wanda ya raina tsayuwar wata sai ya hau ya gyara, ra'ayi riga👌🏿_

    



*37*


“Wanene wannan Huda..!?”


Ya tambaya cikin tsawa, fuskarsa na nuna ɓacin ransa karara dan har jijiyar wuyansa ta tashi, 

  Ba jikinta ba har hanjin cikinta zan iya cewa rawa suke, abunka da marar gaskiya sai kawai ta fashe da kuka, Fusata sosai ya karayi cikin ɓacin rai ya zaburo mata da gaggausar murya 


“Ba magana nake miki ba ki ban amsa mana karamar yarinya ce ke da zaki tsaya kina min kuka!”


Hantar cikinta ce ta kara kaɗawa yayi mata tsawar da bai taɓa mata irinta ba, da sauri ta share hawayen idonta ta kalleshi da ido kamar zasu fito


“Ban sani ba Saif ban sanshi ba”


Yayi mata wani kallon rainin wayyo


“Baki sanshi ba na samu number shi a wayarki?”


Kukan ne ya sake dawo mata amman wannan karon marar sauti, saukowa tayi saman gadon ta zube kasa kamar mai neman gafara sai murzar hannayenta take tunani take yadda zata kare kanta amman bata da mafita, buɗe baki take sonyi tayi masa magana ta kasa, toh mi zata ce masa hakuri zata fara bashi ko kuma kare kanta zata yi duk tabi ta ɗimauce lokaci ɗaya sai zufa ke karyo mata.


“Tashi kije gida Huda karki yar da ki kwana a gidan nan”


Kamar saukar wahayi taji maganar, abunda bata taɓa zato ba ko da a mafarki ba, ne hakan yake nufi? sakinta yayi kenan ko me?



“Gi....gi...gida ..fa..ka..ce Saif..”


Ta faɗa muryarta ta rawa, shi kuma ya bata amsa a tsawa ce 


“Gida nace ki tafi kinsan mi nake nufi ai karki yarda na dawo tarar dake a ɗakin nan”


Yana faɗa ya juya a fuce ya fice, lallai da sauran rina a kafa, dan ba wai ya hakura bane da sauran magana, ita kanta tasan asirinta ya tonu, bata da hanyar kare kanta fatan ta ɗaya kar ya rabu da ita.



               *       *       *


A fusace ya isa asibitin da Safiyyah take, bai damu da dare ba dan goma ta gota shaɗaya ake batu, da wani irin karfi ya tura kofar ɗakin, sai da ganin Momi da Gwaggo ya katse masa hanzari,


“Saif Lafiya dai?”


 Momi tayi masa tambayar cikin mamakin ganin shi yanzu da kuma jallabiya, tasan Saif baya son fita da jallabiya a ko ina idan ba gida ba. 

Duk yadda yasa ya ɓoye damuwarsa a fuska kasawa yayi saboda ɓacin ran nashi yayi muni da yawa sai dai bai faɗa mata komai,


“Ba komai Momi gurin Safiyyah nazo”


Ya faɗa kamar baya son magana, sautin muryarsa da kuma yanayin fuskarsa ya karantar da Momi halin da ɗan ta yake ciki, lallai ba lafiya ba  ganin mai ido da sanda,

   Gashi kuma yazo da dare abunda bai taɓa ba tun da aƙka kawo Safiyyah, 


“Momi ƙku ɗan bamu guri zamuyi magana”


Maganar ta bata mamaki wace irin magana ce da ba zai iya faɗi a gabanta ba? Gwaggo ce ta katse mata hanzari ta hanyar buɗe kofar fita tana faɗin,


“Bari mu fice tun da ba a son muji”


Ganin ta fice yasa Momi ita ta fice zuciyarta cike da rashin yarda.

  Suna fita Safiyyah ta kalleshi fuskarta ba yabo ba fallasa, tasan waye Saif tun kamin tasan kanta ta kuma san irin tsanar da yake mata babu abinda zaisa ya taso cikin dare yazo duba ta daga ganin ma fuskarsa ka san ba lafiya ba, ga kuma guguwar harar da yake watsa mata,

  Kofin dake hannunta na tea ta aje ganin yadda ya nufo ta kamar mai shirin ɗaukar ranta yau kan ita dashi sai Allah, gawa ta rike mai mata wanka duk da bata san meke tafe da shi ba amman tasan ba alheri bane,


“Mi Minal tayi miki kike cutar da ita? Mi yasa kike son kashe min ɗana jinina? yaushe zaki karantar da kanki ba zan taɓa son ki ba? wace irin mahaukaciya ce ke?”


A lokaci ɗaya yayi mata waɗannan tambayoyin yana ɗaga murya, hantar cikinta ta kaɗa cikinta ya ɗuri ruwa, yawun dake bakinta ya tsinke asirin ta zai tonu, fuskarsa take kallo idanunta a razane tana neman mafita,

  Kura mai wayo abunku da yar bariki a nan take taso saye shi da murya kamar tayi kuka


“Subhanallahi wannan wace irin magana ce haka Yaya? me kake nufi ne? Kar dai a shafa min bakin fantin da aka shafa ma Minal a juyar da wannan lamarin a gare ni”


“Kinsan me nake nufi Safiyyah, kuma wallahi duk wani abu ya samu ɗa na ki kaddara ke ya sama”


Hawayen dake makalle a  idonta suka zubo, jin yadda ya katsa mata tsawa


“Na san baka so na yaya maybe yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa aka min wannan sherin amman yaya ba zan aikata maka haka ba me zai sa na aikata maka haka waya yake kokarin haɗa ni da kai ne?”


Kuka take yi ta marairaice murya kamar gaske, bai saurara mata ba dan yanzu baya ganinta da kima balle yaga tausayinta, shi dai so yake ya kara tabbatar da gaskiyar abunda yaji da kuma wanda Dr Zainab ta faɗa masa, ita kuma taki bashi damar hakan dan ta marairaice ita sam ba ita bace haɗa su ake son ayi,

     Akwai kamshi gaskiya a labarin da Zainab ta bashi tun da gashi ya kama Huda Safiyyah ce kawai ta rage masa so yake ta amsa da bakinta ta aikata ɗin ko kuma ta nuna masa alamun hakan dan yasan wannan kukan na munafurci ne wai ita yar duniya shi take son rai na ma hankali.

Jin yayi shiru yasa ta fara tunanin ko hakarta ta cin ma ruwa ne? Lallai ya fara yarda da ita tun da har ya tsaya sauraren kukan ta, ta kalleshi idonta rau-rau da hawaye,


“Wai Yaya waya faɗa maka wannan maganar ne?”


“Ubanki ne ya faɗa min”


Bata an karaba yayi mata ɓarin makauniya ya wanke mata fuska da mari biyu masu kyau, har sai da taga wasu yan taurari nan take bakinta ya haɗe da jini da miyau, bai damu da ciwon dake kafarta ta ya ɗebeta kamar kayan wanki ya jefar ya hau shurinta kamar an aiko shi,

   Razanannar karar da ta saki yasa Momi suka shigo da gudu, Yadda yake aika mata shurin sai da yaba Momi tsoro, duk yadda taso ta jashi baya kasawa tayi shi kuma yaki ma kallonta sai shurin Safiyyah yake,


  Tassss-Tasss Momi ta watsa masa mari, bai ji zafin marin ba duk da marin ne yasa ya ɗan natsu ya kalleta,


“Ba kada Hankali baka da imani Saifullah mi yarinyar nan tayi maka haka? koma wani abun tayi maka aika duba halin da take ciki”


Cikin kuka Momi tayi masa wannan kalamin, dai-dai lokacin Nurses suka shigo tare da Gwaggo dan ita ce ya fita ta kirasu ganin Safiyyah ta suma,

. Kukan Momi yasa jin ba daɗi shiyasa shi bai ma jidaɗin da ya tararda ita a asibitin ba daman yasan hakan sai ya faru ko da bayan idonta balle a gabanta, 


“Momi yarinyar nan ita ta kulla komai duk abinda ya faru da Minal ita ce ta kullah kuma a yanzu haka so take ta zubar da cikin Minal”


Yana kai aya Momi ta sake watsa masa wani mari, ta kalleshi rai a ɓace Cikin muryar kuka tace


“Ba kada hankali Saifullahi daga wani can yaje ya zugo ka sai ka ɗauka dan kawai ka raina yarinyar nan, nasan baka sonta amman ba zaka ɗauki karan tsana ka ɗora mata ba akan me yarinyar nan bata da Uwa ba uba amman kabi ka takura mata me ta tare maka ne? ba zan yarda kana ci mata zarafi ba kabar ganin kai ka ɗai na haifa namiji kana yi mata yadda kake so ina kyale ka, ba zan sake bari ka ci amarta ba ba zaka sake cutar ta ba”


“Momi ina da hujja akan hakan .....”


Ta katse shi,


“Rufe min baki fool wani ya isa ya kawo maka wata hujja ne bada idonka ka kama Minal ba yanzu ka dawo kace wai Safiyyah ce, ɓace min da gani fita kabar ɗakin nan”


Bai iya musu da Momi ba tun tasowarsa, hakan kuma bata taɓa bashi umarni yaki bi ba, yasan wacece uwa dan haka baya son ɓacin ranta, ganin hawayen dake zuba a idonta yasa shi saurin ficewa daga ɗakin,

   A harabar asibitin ya fito yana sauke ajiyar zuciya, ya ɗan samu sarari tun da ya bugi Safiyyah har ya sumar da ita duk da ba hakan kawai yaso ba, Huda ce kawai ba zai taɓa sama hannu ba dan yasan maganinta daya tabbatar da zarginsa zai yanka mata ticket.



_KUYI HAK'URI DASHI ZAMA NE BANA SAMU AMMAN IN SHA ALLAH ANJIMA ZAKU JINI LOVE YOU ALL_

[9/17, 10:22 AM] Auntie Candy: BABBAN GORO


         NA


KHADEEJA CANDY

 


®

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)



*38*


Ya daɗe a harabar asibitin kamin ya nufo gida, 

Ko da ya shigo sha-ɗaya saura kwata, ganin kofar Parlour a buɗe ya tabbatar masa da Huda bata gidan, 

   Kai tsaye ɗakin sa ya wuce, ringing ɗin wayarsa ne ya amsa masa sallamar da bai yi dan karar wayar ce ta tarbe shi, kamin ya karasa ya ɗauka kiran ya yanke, ɗaukar wayar yayi yana dubawa kusan twenty something miss calls ya tarar, Abban Huda ne da Umma ta sai kuma Nasir da wasu two numbers da bai sani ba, tsaki yaja ta wurgar da wayar yasan duk maganar Huda ce zasu masa shi, kuma a yanzu bata gabansa wani haushin ta ma yake ji, yana kokarin cire jallabiyar dake jikinsa aka kara kiran a nan ya ɗauki wayar yasa ta silent, ya ɗaura tawul ya shiga bathroom ya sakar ma jikinsa ruwa.


   Ya daɗe a banɗakin daga bisani ya fito rayuwarsa a jagule ya rasa inda zai sa kansa yaji sanyi, Shi tun da yayi aure baya iya cewa ga ɗauraren lokacin da ya kasance cikin farin ciki, duk da auren so sukayi da Huda amman kullun cikin samun matsala suke, idan wannsan ta kare wannan ta taso, ya kara da Minal ita kuma aka zo aka mata wannan sherin, shin sai yaushe zai san jindaɗin rayuwar aure ?

      Gashin kansa ya shafa a dai-dai lokacin da ya zauna gefen gado,

   

  “Mi yasa irin waɗannan abubuwan suke faruwa da ni ne? Komai na duniya Allah ya ban amman banda wannan oh god!”


A fili ya faɗa yana matsar gashin kansa, zuwa can ya tashi ya saka kayan bachi ya kwanta saman gadon a rairan yana kallon sili,

   Tunanin Huda yake gani yake kamar ba gaske ba ne baza ta iya yi masa haka ba, a nan take zuciyarsa ta soma karanto masa wasu abubuwan da take ɓoye masa da kuma waɗanda ya gani yake kuma zarginta,


“Innalillahi wainna illaihi raji'un”


Wannan shi ake kira da ana zaton wuta a makera sai aka same ta a masaka,

 Miyasa bai yi ma Minal uzuri  ba? Miyasa bai saurareta ba? Miyasa bai yi bincike akan hakan ba?, Sai a lokacin ya soma tunanin irin kuka da Minal ta rika yi da kuma yanayin fuskarta, 


“Miyasa kika amsa kin aikata Minal? Bayan baki aika ta ba? Miyasa?”


_Saboda ba zaka yarda ba,_

 Wata zuciyar ta bashi amsa,

Da a'ce tun farko kayi mata uzuri ka saurareta ka kuma yi bincike da duk hakan bai faru ba, da yanzu ka gano gaskiya an wuce gurin, yau gashi har tana asibiti da cikin ka cikin da ka daɗe kana nema cikin da family ka suke so cikin da za'a haifa naka magaji ka samu ɗa ka zama mutun kamar kowa amman aka saka maka shakku a akansa ka kasa bashi kulawar da ta dace,


“Noooooooo!”


Da wani irin karfi ya faɗa ya kai ma katifar gadon wani mugun bugu, wanda na tabbatar da mutum ne sai ya suma,

   Fillo yaja ya rumgume yana kuka,


“Oh Minal oh Minal”


Kwakwalwarsa ta cushe tunaninsa ya bushe, wani kara tsana ya ɗorawa kansa da kansa a yanzu, shi kansa yasan bai kyautawa Minal ba sai a yanzu yake ganin laifin kansa. Tashi yayi zaune jin yayi babu wanda yake son gani idan ba Minal ba, A gogon ɗakin ya kallah, 

  Karfe ɗaya da minti talatin da bakwai ns dare haka a gogon ya nuna, bai damu ba ya tashi ya canja kayan dake jikinsa daga na bachi zuwa kananan kaya, ya ɗauki makullin motarsa ya fice.



                ***     ***     ***


Ko shakku babu kai tsaye ya nufo asibitin, duk da yana tsamanin tayi bachi, amman shi dai ko fuskarta ya kalla ya samu sauki dan jin yake yau idan bai sata Minal a ido ba ba zai iya bachi ba. 

   Abunda bai yi zato ba ya hanga kamin ya karasa bakin kofar Emargency, Deen ne a jingine da kofar ya rumtse ido fuskarsa a takure,

    Toh mi yazo yi asibitin? Kar dai ace gurin Minal ya zo?

   Ita ce tambayar da Saif ya rika yima kansa har ya isa kusa dashi Fuskarsa a murtuke kamar bakin kumurci,


“Mi kazo yi asibitin nan ɗan iska matar mutunci”


Ba shakka wannan muryar Saif ce hakan yasa shi buɗe ido ya kalleshi, kamar bakin hadarin gabas haka yaga fuskar Saif babu annuri yana mashi wani kallo irin zan iya ɗaukar ranka,


“Kaji haushi Deen ɗan cin amana mayaudari ɗan shaye-shaye”

   

Irin wulakantaccen kallon nan yake mashi yana faɗa mashi waɗannan kalaman,


“Na cancanci ko wane irin Suna Saif sai dai ba kai ya kamata ka kira ni da shi ba Minal ce kuma ta ki ta kirani taki ta saurare ni”


“Akan me zata saurare ka banza kawai wulakantance wanda bai san hallacin ba, ai daman baka cancanci tayi abota da kai ba mace da yar uwarta mace musulunci ƴa yarda tayi abota da ita ba irin ku ba”


A nan take idonshi suka cika da hawaye, daman tuni kukan zuci yake a gurin


“Nayi mata butulci Saif na raba ta da farincikin ta nayi sanadiyar tashin ciwon ta, nayi hakan ne da zaton idan na aikata zaka rabu da ita ni kuma na aure ta sai gashi hakan bai samu ba, Safiyyah ta yaudare ni Saif Ita ta zugani na aikata komai ta nuna min idan nayi hakan zan samu yadda nake so, idan mutun nason abu duk hanyar da zai bi ya samu abin zai bi sai idan ba dama ta hakan ne ta ci riba a kaina har ta sani na amanar aminiyata”


Saif ya taɓe baki cike da tsanar Deen


“Bazan taɓa yafe maka ba Deen, ba zan taɓa yafe maka ba”


“Bana son ka yafe min ba yafiyar ka nake so ba wanda nake son ta yafe min ta ki ta kalleni balle ta yafe min ɗin,

 Saif ina son kayi min wani abu ɗaya ka rike Minal da amana ka kula da ita dan Minal tana son haka tana son a ko yaushe taji ta jikin wani, Minaƙ bata taɓa ba bada kanta ga wani namiji ba Trust me Saif kai ne farin cikinta”


Yana kaiwa nan bai jira abunda Saif zai ce ba ya share hawayen idonsa ya kama gabansa,

  Da kallon tsana Saif ya bishi yana nazarin maganganunshi har ɓace masa da gani, lallai akwai alamar nadama a fuskarsa da kuma hawayen da yaga ni a idansa ga kuma kalamanshi, sai dai har yanzu wata irin tsanar sa yake ji marar musaltuwa, zuciyarsa ta nuna masa Deen babban makiyinsa ne da idan zai samu dama zai iya kashe shi, nikan nace har da dai zafin kishi.

  

                                   ***

Ya daɗe a tsaye yana sauke ajiyar zuciya kamin ya kai hannu ya tura kofar ɗakin,

   Mummy da Kairat suka juyo suna kallon shi, 

  Ras! Ras! Gabanshi ya faɗi dan bai yi zaton suna cikin ɗakin ba, Dakewa yayi kamar ba komai ya gaida Mummy yana kallon Minal fuskarsa ba walwalah, 

   A maimakon ta amsa mashi sai kawai ta tareshi da waɗansu maganganun


“Saif. Minal tana da bukatar Hutu a yanzu bata son damuwa da duk abunda zai ɗaga mata hankali, 

da zaka hakura ka tafi da zaifi kwanciyar hankali tun da kaga bachi ma take”


Dimmm! Yaji ransa ba daɗi duk da ba'a cikin faɗa tayi masa maganar ba, amman yasan me take nufi basa da bukatar shi a kusa dasu,

   Ya ɗan karasa shigowa yana faɗin


“Ko da ba zaki barni naga matata ba, nasan ba zaki iya hana ni duba babyn daƙke cikinta ba”


Kairat ce ta yari numfashinshi tana mishi kallon uku saura kwata,


“Minal ba matar ka bace Saif zata dai haifa maka ɗan ka ta baka”


Maganar ta soke shi, sai dai bai ce mata komai ba dan yasan shi ɗin mai laifi ne, dan idan ba haka ba, Kairat bata isa ta tsaya tana faɗa masa waɗannan kalaman ba,

         Ganin sun fice yasa shi karasa kusa da ita yana kallon fuskarta kamar a lokacin ne ya soma saka ta a ido,

  Hannu ya kai ya shafa cikinta, yanzu fa ajiyar sa ce a ciki wani irin kalar daɗi ya ziyarci zuciyarsa, sai a  yanzu yake jin tausayinta yake kuma kara tabbatar da lallai ita ce matar da ta dace dashi tun da gashi an shiga tsakanin su amman sun kasa rabuwa har gaskiya ta baiyyana, gashi kuma just one night Allah ya bashi abunda yake nema, 

   Wani dogon numfashi yaja ya sauke hawayen dake makale a idonsa suka zuba saman hancin Minal, hannu ya kai ya shafa fuskarta yana murmushi yaja hancinta tunawa da yadda suke wasa lokacin da kazar na da gashi, yasa babban yatsan sa yana shafa gashin girar ta.


      Shigowar Dr.Zainab yasa shi saurin share hawayensa ya juwo ya kalleta,

   Wani murmushi tayi masa ta karaso kusa dashi tana duba Minal,


“Ina fatar Alkawari na yana nan, ɗazun matar ka ta kirani tana faɗa min ka kore ta”


Basar da maganar yayi kamar bashi dake ba,


“Mi ke damun minal yanzu?”


“Strains ne kawai sai kuma karin jinin da za'ayi mata”


“Karin jini kuma?”


Ya tambaya da fuskar mamaki,


“Yes matar ka na bukatar jini sosai kasan ciwon da yake tare da ita dole a rika mata karin jini kullum,

     Dan ciwon nasu tsotse jini yake yi a ko yaushe zaka ganzu a tauye”


Wani irin tausayinta ne ya fige shi sai a lokacin yayi mata kallon tsafta, lallai tana da bukatar jini duk da shi ba likita bane amman yaga hakan a tattare da ita,


“Idan jini na zai yi zanso a ɗiba a saka mata”


Ta ɗago ta kalleshi dai-dai lokacin da ta gama bincika Minal ɗin ta ɗauki files ɗinta


“Muje Office”


Tana faɗar hakan ta fice daga ɗakin, 

  Shi kan ya daɗe a ɗakin yana kallon Minal yana shafa fuskarta wata sabuwar rayuwa yake ji a game da ita ya samu kansa cikin wani yanayi da shi kaɗai yasan ya ake ji ya kuma san ma'anarsa, sai da yaji ya ɗan damu sukuni sannan ya nufi office ɗin Dr.Zainab.

   

Kujerar dake fuskantar ta ta nuna mashi alamar ya zauna,

Ta cigaba da gyara waɗansu takardu dake gabanta, bayan ta kare ta kalleshi,


“Nayi magana da Dr Sa'adatu akan jinin da za'ayi mata kari and...-”


YA tari numfashin ta,


“Idan zai yiyu ina son a ɗibi jini na a saka mata”


“Idan muka samu hakan zamu fi jindaɗi, Sai mu auna jinin naka muga idan yazo ɗaya da nata sai a ɗiba, amman duk da hakan zamu nema wani jinin dan bana tunanin jinin ka zai ishe ta”


“Dr wannan wane irin ciwo ne haka?”


“Blood cancer ne i thing ka sani?”


“Na sani amman miyasa yake shan jini haka ne? Na kasa fahimtar wane irin ciwo ne wannan?”


Dr. Zainab ta gyara zamanta ta soma masa bayani a natse


“1 Leukaemia shine medical name na blood cancer ɗin Blood cancers affect the production and function of your blood cells. Most of these cancers start in your bone marrow where blood is produced. Stem cells in your bone marrow mature and develop into three types of blood cells: red blood cells, white blood cells, or platelets. In most blood cancers, the normal blood cell development process is interrupted by uncontrolled growth of an abnormal type of blood cell. 

    These abnormal blood cells, or cancerous cells, prevent your blood from performing many of its functions, like fighting off infections or preventing serious bleeding.

 1. Fatigue

2. Shortness of breath

3. Fever and 

4. Bruising or bleeding

5. Joint or bone pain

6. Sleeping problems

     Wadannan common signs ɗinsa kenan


  They're always on blood transfusion saboda yawancinsu are anaemic coz cancer cells din suna zuqe jini fiye da zato sai su hana normal cells na jikin mutum samun jinin daya kamata”


Ajiyar zuciya ya sauke ya dafe kanshi ya lumshe ido, ya ɗan daɗe a haka kamin ya ɗago ya dake kallonta 


“Yanzu babu yadda za'ayi Minal ta rabu da ciwon nan gaba ɗaya?”


Yawun dake bakinta ta haɗiye tana kallon shi,


“Idan har za'ayi treating dinsa akan bi matakai ne guda uku


Chemotherapy-surgery-radiotherapy


 Chemotherapy shine farko use of anticancer drugs knn


Radiotherapy kuma ionizating radiation ne ake using a kashe cancer cells din gabadaya kuma shine last stage and yafi tsada,

      Sai dai kuma Surgery is not a common option  but wani lokaci ana amfani dashi don a yi repairing bone damage”


Ajiyar zuciya ya sake saukewa a karo na biyu still yana kallon ta 


“Dr I'm talking about yadda zata rabu dashi kwata-kwata ta zama normal kamar kowa”


“Shi fa cancer before ayi  treating ɗinsa dole sai anyi considering abubuwa kamar haka:

- Ko kinada ciki

-Whether you've had another cancer in d past

-The cancer cell location


Kuma shima stages ne, in ya zama cronic to sai Allah‬ dan gaskiya basu cika surviving ba shi yasa zaka ga they're always depressed,

First stage is marked by an enlarge presence of lymph nodes

 Second stage is marked bythe enlarged presence of spleen as well as liver

 Sai third stage is marked by d development of anemia,

 Na karshe 4stage din shine by a drastic full in d rate of blood platelets

D 3$4 are more risky

   D 1 responded better more dan sauran”


“What do you mean?”


Ya tambaya hankalinsa a tashe, sai da ta nisa sannan tace


“Zaka iya rasa Minal a ko wane lokaci saboda ta kai matakin da ba baza a iya treating ɗin ta ba”


Dif ya ɗauke wuta na ɗan lokaci,sai da ya sauke ajiya zuciya sannan numfashinsa ya dawo normal,


“I hope kasan ba ciwon cancer bane kawai yake damun Minal, tana da sickler”


Da sauri ya tashi tsaye,


“Ya isa Dr muje kawai a ɗibi jinin nawa”


Ba musu ta tashi suka fice tare.



         *                  *                     *


Bayan sun auna sun ga jinin nashi zai yi mata suka ɗibi gora uku, sun rubuta masa magani suka kuma faɗa masa abubuwan da zai ci waɗanda zasu kara masa jini, 

    Shi dai har akayi aka gama tunanin Minal ake hankalinsa yana gurinta ana gamawa ya nufo ICU,

   Bachi take har yanzu hankalinta a kwance, ya daɗe yana kallon fuskarka daga bisa ni ya kwanta gefenta saman gadon cike da tausayinta, yasa hannunsa ya ɗan tallabo ta ya rumgume ta tsa-tsam,


“I will always stay Minal I never wanna lose you, ke ce farin ciki na,

  A yanzu ke ce kaɗai fata na ba zan iya rayuwa ba ke ba I love more than I did before ko da kin guje kin ki ni Minal nothing's changed no one could take your place and I'm sorry that it's this way but I will be with you I'm here with you I will stay”


Kamar a mafarki take jin kalaman, sai dai digar hawayensa a kan fuskarta ya tabbatar mata da ba mafarki bane, cikin hanzari ta buɗe idonta sai kawai ta jita jikin mutum kam-kam ya rumgume ta, tasan Saif saboda kanshin turarensa da taji kuma tasan duk duniya shi kaɗai ne yake iya yi mata irin wannan rumgumar mai kara mata son shi, 

    Amman hakan bai hanata unkurin son raba jikinta da nashi ba tana ihu,


“Shiiiiiiiiiiiiii stop shouting”


Ya faɗa yana shafa gashin kanta yana kara rumgumeta ya yadda ko motsin kirki ba zata iya ba,


“Saif ne mijinki ne Minal i miss you so muchi please karki raba ni da jikin ki”


Bata saurara ba ta cigaba da kaceniyar ganin ta kwaci kanta amman ina karfin namiji da mace ba ɗaya ba gashi daman ba wani karfi ne da ita sosai ba, yi tayi har ta gaji amman ta kasa kwatar kanta shi kuma yaki ya sake sai ma kara matse ta yake da kirginsa ta a dole ta hakura,


“I hate you more than you think I don't wanna see your face, bana son ka Saif ka cutar da ni na tsane ka sosai-Sosai”


“I know.....”


Ya faɗa yana kara chusa hancinsa cikin gashin kanta.



_Ku yi hakuri da ni I'm just a lazy Writer 😇 Kar kuyi fushi Ku cigaba da kasancewa da ni tafiyan yanzu aka fara,  keep vote and comment ina jin daɗin su sosai😍_


#Oneheartonelove

#KhadijaAbubakarAlkali

[9/21, 8:08 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO


         NA


KHADEEJA CANDY

 


®

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)



*39*


Shigowar masu mopping ne yasa shi farkawa, A hankali ya raba jikinsa da nata ya sauka saman gadon ba tare da ta farka ba, A masallacin dake asibitin yayi sallah, ba shi ya dawo ɗakin ba dai bakwai da rabi. 

   Zaune ya tarar da Minal tana shan tea, Mummy na gefen ta zaune Kairat kuma na tsaye tana matsa mata kafafunta, ganin shi yasa Kairat haɗe fuska kamar taga mala'ikan mutuwa, Minal kuma kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kai. Mummy ce kawai ta ɗan sakar masa Fuska, 


“Saif....”


Yaji daɗi sosai hakan yasa shi risinawa har kasa ya gaishe ta


“Na'am Mummy an tashi lafiya?”


“Lafiya Kalau Mun gode sosai Dr ta faɗa mana Ka bada jini”


“Mummy miye abun godiya, Minal nayi ma fa ba wata ba”


Wani wawan kallo Kairat ta watsa masa,


“Ai dole ayi naka godiya tun da kasan Minal ba dolen ka bace yanzu .....”


Ya tari numfashinta


“Dole na ce Kairat idan banyi mata ba wa zanyi ma? Ni Allah ya ɗorawa hakkin yi mata komai matata ce idan ba ki san da wannan ba ki sani yanzu”


Zata sake cewa wani abun Mummy ta ɗaga mata hannu, hakan yasa ta jifa da kafar Minal ta fice a fusace,

  

“Kayi hakuri Saif kasan halin yara”


“Ba komai Mummy ni ya kamata na baku hakuri akan abunda nayi dan Allah ku yafe min”


Kamar mummy zata dake ce masa wani abun sai kuma ta tashi tsaye tana murmushi ta fice, a hankali ya ɗago ya kai dubansa gurin Minal dake kallonsa ya tashi yaje kuda da ita ya zauna har lokacin kallon shi take kamar mai jin tsoro ko kuma wanda bata yarda dashi ba, hakan yasa shi jin ba ɗaɗi hannu ya kai zai riko hannunta, da saurin ta janye hannun ta har tea dake a ɗayan hannunta ya zube, bai damu ba ya sake kai hannu ya riko hannun nata yana murzawa a hankali


“You hate me Minal right?”


Sai kuma ya ba kansa amsa


“Yes you hate me Minal a know”


Ita dai kallonshi kawai take bata ce masa uffan ba idonta na kwance da wani farin ruwa mai kamar hawaye kuma ba hawaye ba,


“Dan Allah Minal ki yafe min wallahi na gane kuskure na kuma yafiyar ki nake nema Minal na cutar da ke  na sani Minal na-”


Shigowar Nasir yasa shi katse maganar yasa hannu yana share hawayen da suka zubo masa, 


“am sorry” 


Ya juya zai fita, Saif yayi saurin dakatar da shi


“No Nasir shigo kawai” 


Juyowa yayi yana murmushi


“Naji daɗin ganin ku haka Saif ina fatar ka gane kuskuren ka” 


Shiru yayi kamar ba zaiyi magana ba, sai kallon Minal yake dake kallon Nasir tana motsa baki, 


“Saif Dad yana son ganin ka”


Nan shiru yayi ya kai hannu yana shafa kan Minal, yasan matsalan ba zata wuce akan Huda ba ko kuma dukan da yayi ms Safiyyah shi kuma a yanzu ko ɗaya baya shakka dan yasan yana da gaskiya,


“Nasir kaje gani nan zuwa”


Ya faɗa ba tare daya kalleshi ba, Nasir bai tsaya jiran komai ba ya juya ya fice. Kallon kallo suke shi da Minal kowane da abunda yake karanta a idon ɗan'uwansa, Wani kalar yanayin yake ji kanta a ciki yanayin da ita kaɗai tasan me yake nufi, kasa ɗauke ido yayi daga kallon kwayar idon nata da yake tausayinta yake ji da kaunarta da begensa na kara kamashi, ganin hawaye sun zubo mata yasa shi saurin matsawa da faffaɗan kirjinsa ya rumgume ta yana sauke ajiyar zuciya, lumshe ido tayi hawayen suka cigaba da zubo mata tana kokarin raba jikinta da nashi kara kankanme ta yayi,


“Ba zaki iya raba jikina da naki ba Minal baki da wannan karfin a yanzu karki wahalar da kanki”


       ***                   ***                    ***


Wata irin tsawa Daddy ya katsa masa ganin yayi shiru bai bashi amsa ba,


“Ko ba da kai nake magana ba? Kayi shiru mi yasa ka rai na mutane ne me ka ɗauki kanka”


Saif dake zaune kasan carpet ya ɗago kai ya kalli Daddy


“Wallahi Dad ba zan iya zama da Huda a yanzu ba halinta ya kai wani fannin da bazan iya zama da ita ba”


“Mi tayi maka? Haka kawai zaka ce ka gaji da ita dan ka rai ma hankalin mutane wai ko kana kokarin haukacewa ne haka fa jiya akace ƙaje ka duki Safiyyah”


Momi ta taɓe baki


“Ai ni har tunani nake ya fara shaye-shaye dan ni ban san shi da wannan halin ba”


Nasir ya kalleshi


“Saif idan kasan da wata matsala kawai ka faɗa zai fi ka fitar da kanka daga zargi”


“Akwai wani abun Nasir amman ba zan faɗa ba sai gani ga Huda da iyayenta”


Tsaki Daddy yaja ya tashi tsaye rai a ɓace


“Kaje ka samu Baba karami kuje can gidan su a sasanta ka tabbata kamin gobe ta dawo gidan ka”


Yana kaiwa nan ya kakkaɓe rigarsa ya fice daga parlour,

 Momi ma tashi tayi tana nuna Saif da hannu,


“Ka kali Kanka Saif tsakanin jiya da yau kawai ka canja kama idan kayi nan kayi nan Kana zaman zamanka kaje ka jawo ma kanka matsala gashi akan yarinyar nan kana kokarin haukacewa”


Yasan da Minal take koda bata fito fili ta faɗa ba hakan yasa ya tari numfashinta yana kokarin mikewa tsaye,


“Momi wallahi Auren Minal alheri ne a gare ni Minal mace ce ta gari tana so na da gaskiya Momi sai a yanzu na gane Huda cuta ta take son da Huda take min Momi so ne wanda ba zai hana ta aikata komai ba Momi aure na da Minal rahama ne yaushe akayi auren amman har Allah ya a zurta mu da samun baby”


Kai Momi ta girgiza


“Lallai basu barka banza ba Saifullahi tun da har ka yarda cikin dake jikin Minal naka ne”


“Wallahi nawa ne Momi kuma zan tabbatar miki da hakan vary soon....”


Tsaki taja ta tashi ta fice tana sakar masa maganganu, Nasir ta kalleshi,


“Saif ya akayi aka gane gaskiya?”


Bai ɓoye ma Nasir komai ba ya faɗa masa daman can basa yar ɓoyon sirri tsakanin su, Nasir bai yi mamaki daman can yana zargin Safiyyah da kulla wannan abun kuma gashi zarginsa ya zama gaskiya, Huda kuma daman an daɗe ana labarta masa halin da take ita da abokin na Saif sai dai bai yarda ba tun da bai gani da idonsa ba,


“Alhamdulillah Saif naji daɗin wannan abun naji daɗin da asirin nan ya tonu yanzu ko ba komai yanzu me lokacin da Minal ta fi bukatar kulawarka”


“Haka ne ni kai na na ji daɗin hakan Sai dai ni bazan iya ci gaba da zama da Huda ba Nasir wallahi ta riga ta fita rai na”


“Ba ta dace da kai ba Saif kaddara ce tasa ka Aure ta, sai ba zan baka shawarar rabuwa da ita ba ka kara yin bincike” 


“Babu wani bincike da zan kara yi Nasir, yanzu dai muje mu samu Baba karami


              ***          ***          ***


Suna fita gidan suka nufi gidan Baba Karami (Kannen Daddy), ko da suka isa har Daddy ya buga masa waya ya faɗa masa komai su kaɗai yake jira, dan haka daga isarsu suka kama hanyar gidan su Huda, 


  Baban Huda yayi musu kyakkyawar tarba sanin daga inda suka fito da kuma mutuncin su, yasa aka kawo masu kayan share-share, babu abunda suka taɓa daga drinks ɗin suka maida hankali ga abunda ya kawo su,


“Amhh Alhaji Mun zo ne akan maganar Huda anzo ne dan a sasanta kasan shi zanan aure dole ne ayi ta samun haka ko a manya balle yara”


Baba karami ne yayi maganar cikin muryar manya  mai nuna da gaske yake,Baban Huda ya ɗan nisa


“Haka ne amman kuma ya kamata asan abunda ake a yanzu, Saif fa ba yaro bane ya kamata ace yasan me yake yi a yanxu bai kamata ace ko da yaushe  ana samun matsala akan abu ɗaya ba mu hankalinmu ba kwance ba suma na su ba kwance ba”



“Haka ne Abbah amman ita Huda ta faɗa maka wani abu ne?”


Wannan karon Saif ne yayi maganar,


“Bata faɗa mana komai ba daga ni har Mamar ta, ta dai ce mana kai ne kace tazo gida sai kuka take duk tabi ta tashi hankalin ta”


“Ai ba zata faɗa ba tun da tasan abunda ta aikata”


Duk kallon rashin fahimta sukayi masa, ban da Nasir da ya ɗan noce kai dan yasan halin da ake ciki,


“Mi tayi maka wani abun ta aikata ne?”


Abban Huda ya tambaya,


“Abbah zanso ka kira Huda a yanzu ita da Mama dan ayi komai a gaban su”


Saif ya faɗa yana kallon fuskarsa, Wayarsa ya ciro ya danna kira ana ɗauka yace 


“Kizo tare Huddallah”


Yana faɗar hakan ya kashe wayar, fuskarsa ba walwalah.

  Ba su daɗe ba suka suka shigo parlour Mama ta zauna saman kujera Huda kuma ta zauna kasa idonta a kumbure kanta a kasa kamar ta gwarai,

    Saif ya kalleta cike da tsana ya soma magana


“Huda Abbah ya faɗa min baki faɗa musu abunda ya faru ba shin zaki iya faɗi a yanzu?”


'Dagowa tayi da sauri ta kalli Saif ta kalli Abbanta da Nasir sai kuma ta sunkuyar da kai idonta cike da hawaye,

 Ganin hakan yasa Saif baiyi wata-wata ba ya fiddo wayarsa ya kaunna musu rekodin ɗin ya kure murya yadda kowa zai ji, bayan sun gama ji ya faɗa musu wasu abubuwan da yagani da kuma yake zargi, kowa ya cika da tsananin mamaki a naɓ take tsanar ta ta shiga zuciyar mahaifinta mamanta kan daman ta daɗe tana zargin ko bata rabu da saurayin nan nata ba ganin yadda take yawan faɗin shi da kuma yadda take son shi sosai. Makurewa tayi gefen kujera kamar wanda ruwa yaci tana hawaye dan ko kukan bata iyawa,


“Da gaske ne Abunda ake zargin ki dashi Huddallah?”


Kamar daga sama taji tambayar da mahaifin nata yayi mata, ɗago kai tayi cike da nauyin ido ta kalli Saif sai kuma ta sake mai da kanta kasa,


“A'a Abbah sheri ne akayi min ni ban aikata ba”


Kai Saif ya girgiza yana mamakin karfi hali irin nata,


“Huda kiji tsoron Allah ki faɗi gaskiya kinsan dai ba zan miki karya ba ko”


“Saif tace bata aikata ba idaɓ ka gaji da zama da ita ne kawai ka sauwaka mata ba sai kayi mata kazafi ba”


Maman Huda ta faɗa da kakkausar murya, da sauri Huda ta kalleta


“A a Mama dan Allah karki min haka bq zan iya rayuwa ba Saif ba”


“Zaki soma daga yanzu Huda dole ne ki koyi hakan, bazan sake zama dake ba Huda ba kazafi nake miki ba ina son ki rantse da qur'ane baki aikata ba”


“Bazan rantse ba Saif ba zan rantse ba”


Kai tsaye ta bashi amsa, Abbanta ya kalleta,


“Toh kin aikata kenan?”


“Abbah ban aikata ba taya za'ayi ina matar aure na zauna da wani namijin? Bazan rantse ba kuma ni nasan ban aikata”


“Karya nake miki kenan? Idan har da gaske baki aikata ba ai sai ki rantse shi kenan kin wanke kowa daga zargi”


“Ba zan rantse ba Saif ba zan karɓi abunda nasan ban aikata ba”


Da wani irin karfi take bashi amsar hawaye na mata zuba,

  Abbanta ya tashi tsaye,


“Ka sauwake mata Saif ba sai ka wulakanta ta ba”


Saif ya ɗan murmusa


“Karka ta da hankalin ka Abbah bana da niyar barin gidan nan har sai na sake ta dan ba zan iya zama da maziniya ciya ba makaryaci”


“Ni ba maziya ciya bace ma makarya ciya bace karka sake kirana da waɗannan sunayen”


“Idan har ke ba makaryaciya ba ce ki kawo wayarki na kira Faruk yanzu”


“Bazan kawo ba, Nasan nayi zama da Faruk amman a baya ba yanzu ba duk wanda yayi min wannan sherin bazan taɓa yafe masa ba” 


Kalmar _Nayi zama da faruk a da_ ita tasa duk suka kalleta har Baba karami, Saif yaji daɗi ganin gaskiya na ta soma fitowa,


“Ko ki faɗa ko karki faɗa ba zan iya ci gaba da zama dake ba Huda, Dan haka na sake ki saki ɗaya!”


Faɗuwa tayi kasa gurfane kamar mai neman gafara tana kallon shi, Daga Abbah har Mama baki suka saki Baba karami kuma ya rika faɗin 


“Subhanallahi”


Nasir kuma ya rike Saif ganin zai ci gaba,


“Na sake ki saki biyu......”


“Saif........”


Da wani irin karfi ta kira sunanshi, tana haki da girgiza mai kai


“Na aikata Saif wallahi na aikata dan Allah karka sakin da zama zai haramta a garemu Saif na amsa laifina dan Allah ka yafe min....”


Tana kaiwa nan Abbah ya watsa mata mari, hakan yasa ta kai wa kasa sume.

  Saif kan ko a jikinsa dan tashi ma yayi ya fice daga farlon, Baba karamin ne da Nasir suka nufi gurinta.


     Bai damu da ya koma ciki ba tsaye yayi a waje har aka fito da ita aka shiga mota da ita aka ɗauki hanyar asibiti, su kuma suka shiga tasu suka nufi gida.

[9/23, 1:04 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO


         NA


KHADEEJA CANDY

 


®

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)



*40*


Suna isa gida Part ɗin Daddy suka fara shiga, suka tarar da ya fita, a nan suka nufo part ɗin Momi, a  parlour suka tararda ita zaune tare da bakinta suna tattaunawa, shigowar su yasa ta sallami bakin tana kallon fuskokin su,

   Baba karami ne ya fara labarta mata abunda ya faru kamin Nasir ya ɗora da nasa, Saif ya kunna mata Audio recording ɗin taji komai, ba lamarin Huda ne ya bata mamaki ba na Safiyyah ne ya kiɗima ta sosai ganin a gidan ta tashi kusan ma itace ta raine ta amman ace ita ce ta shirya wannan mugun kulli gashi yarinyar a fuska kamar saliha,

 sai a lokacin Momi ta soma tunano wasu abubuwan da taga Safiyyah nayi da kuma irin son da take yi ma Saif, sun taɓa wannan maganar ita da Lubna har Lubna takr cewa tana zarginta da shirya ma Minal wannan sheri amman Momi tace a a ganin kamar ba zata iya aikata mugun abu irin wannan ba,

       Baba Karami ya nisa ya kalleta a natse


“Yanzu ni abinda nake gani shi ne kije asibitin gurin Huda ki duba lafiyar ta”


“Babu inda Momi zata je akan me? Wallahi Baba kaji na rantse ko toh wallahi ko sama da kasa zasu haɗe bazan mai da Huda a matsayin matata ba balle har naje duba ta dan haka Momi ma ba zata je duba ta ba dan xuwa duba ta zai sa tayi tunani ko za a yafe mata ne”


Saif ya faɗa kamar da faɗa, Momi ta kalleshi


“Ba kai ke da ikon yanke hukunci ba Saif sai Mahaifinka yazo duk yadda yace haka za'ayi”


“Ba zan ki yi muku biyayyah ba Momi, amman wallahi ba zan sake zama da Huda a matsayin mata ba”


Nasir ya kalli Momi 


“Momi ni abunda nake gani shine a barta har tayi nadamar abunda ta aikata, mu mai da hankali gurin Minal yarinyar nan lafiya ma bata ishe ta ga kuma baby dake cikin ta, idan muka bata kula har ta haihu a nan ne zamu tabbatar da baby na Saif ne ko kuma ba nashi ba”


Shiru Momi tayi alamar nazari ita kanta tana ji a jikin cikin da yake jikin Minal na ɗanta ne, sai dai tabbaci ne ba tada shi ta daɗe tana son taga ɗan Saif gudan jininta,


“Haka ne amman Sai mahaifin ku ya dawo duk yadda yace haka za'ayi”


  Da wannan sukayi mata Sallama kowa ya kama gabansa.

  A asibiti Saif ya tare, bai dawo gida ba sai dare a gidansa ya fara isa sai da yayi wanka ya canja tufafi sannan ya fito ya nufo Gidan gurin Momi, Kannensa kawai ya tarar a part ɗin dan momi tana part ɗin Daddy.

   Bayan ya ɗan zauna ya nufi dinning ya zuba ma kansa abinci, yana cikin ci wayarsa tayi ringing ɗauka yayi ya duba ganin number Daddy yasa shi saurin yin picking,


“Ina nan gida, toh gani nan zuwa”


Shine kawai abunda ya faɗa ya sauke wayar, ya tashi daga cin abincin da yake ya zari kyale ya goge bakinsa ya nufi part ɗin Daddy,

   Da sallama ya shiga Momi ta amsa masa bayan ya zauna ya gaida Momi da Dad momi ce kawai ta amsa Daddy kan harara kawai yake watsa masa,


“Ashe baka da hankali Saif, na yi tunani kasan mutun ci ashe ba ka san shi ba suma sunyi tunanin hakan shiyasa suka ɗauki yar su suka aura maka

  A tunani na kasan meye aure ashe kai wawa ne kana girma kana cin kasa kana son zubar ma da kanka mutunci kana son ɓata tarbiyar da na shekara ina gina ka akai buɗewar ido yasa ka manta kowa a gaban ka ka aikata abunda Allah baya so, har yaushe zaka zama cikakken namiji mai daraja ka rasa inda zaka sakar musu ya sai a gaban idon su bayan ka gama aiban ta musu ita,

 Daman kasan baka isa aure ba kaje ka nema! ba kai ne na frko da na fara aurar ba babu wanda ya taɓa zuwa min da wata matsala sai kai ka tsiri auren mata biyu da kuruciyar ka, yanzu kuma kana son ka maida kanka mai auri saki ko.?”


Sai a lokacin ya ɗan dago kai ya kalli Daddy,


“Wallahi Dad ba haka bane ita da kanta ta amsa ta aikata kuma ina da sheda akan haka Dad.....”


Dad ya katse shi a tsawace


“Shedar banza da wofi, na fahimci ka fara shaye-shaye kuma har yana kokarin taɓa maka kwakwalwa ya mai da kai mahaukaci har yar uwarka kana kokarin yi mata sheri”


Momi ta dafa shi,


“Ba haka bane Alhaji wani gurin yana fa da gaskiya ni kai na nayi.....”


“Kin yi me? So kike ki goya masa baya ko ai nasan komai yake yi da haɗin bakin ki ake yinsa daman ku mata karamar kwakwalwa ce da ku duk yadda yara suka ce zasuyi sai ku biye su toh ni ba zan ɗauka ba!”


Saif ya sauke ajiyar zuciya cike da ladabi yace,


“Dad kayi hakuri idan ranka ya ɓace amman wallahi abunda nake faɗa maka akan Huda gaskiya ne haka ma na Safiyyah”


“Bai dame ni ba bazan matsa maka ka mai da huda ba ba kuma zan saka zama da ita dole ba amman ina shedai maka ba zaka sake yin wani auren ba...”


Saif zaiyi magana Dad ya ɗaga masa hannu,


“Bana son wata magana tashi ka bar min parlour na”


Ba musu ya tashi ya fice Momi ta bishi da kallon tausayi har ya fice,

 Daddy kuma ya bishi da kallon haushi dan shi gani yake kamar yana yin haka ne dan ya samu damar sakin mace tunda yayi ma Minal Huda ce ta biyu, so yake ya mai da kansa mai auri saki.


***


Kallo ɗaya Daddy yayi ma Momi ya gane ranta ya ɓace ganin yadda ta ɓata fuska kamar tayi kuka, yasan yadda Momi take son Saif dan shi ne ɗanta na fari kuma ɗa ɗaya tilo namiji a cikin ɗiyan da ta haifa saɓanin shi da yake da wasu yayan da uwar gidansa, sai dai kuma duk a cikin matansa babu mace da yake so irin Momi hakan yasa baya kaunar ganin ɓacin ranta, 

   Kokarin sakin fuskarsa yayi yana kallonta,


“Kin ɓata rai tun da nayi ma ɗanki faɗa ko? Kin fi son a bashi gaskiya ko da baya da ita uhm?”


“Ba haka bane Alhaji naso ka bashi dama ya faɗa maka yadda abun yake idan bai faɗi abunɗa yake ransa ba ya za'ayi kasan gaskiyarsa, yarinyar nan fa mutane da yawa sun ɗora zarginsu akanta nima kai na daɗe ina zarginta amman kai daga zuwan ka haushi da faɗa akan wata can bare kaki ka saurari ɗan ka”


Ajiyar zuciya ya sauke yana kallonta,


“Bana son goya masa baya ne kar gaba yaje ya aikata abunda yafi wannan, kuma kinsan hausawa na cewa kaso naka duniya ta kishi ka ki naka duniya ta so shi, kin ga haka kwana kin baya yayi da Minal yanzu kuma ya sake da Huda”


“Abunda Yayi ma Minal Abban Lubna sheri ne akayi mata yanzu kuma ya gano gaskiya, Huda kuma da gaske ne ta aikata ba sheri akayi mata ba”


“Wa yayi mata sherin?”


“Safiyyah ce, shine dalilin da yasa yaje ya dake ta ranar a asibiti”


“A'a ki daina zancen Safiyyah ya za'ayi safiyyah tayi ma ɗan'uwanta wannan abun”


“Naji amman kasan ai baza ayi mata sheri ba ko? Kuma ni bana son kayi fushi da shi akan wata can da bata ma san kana yi ba”


Murmushi ya ɗanyi ya kau da kansa, hakan yasa ta kwanto jikinsa tana faɗin,


“Ina son kayi min izini gobe zanje duba Minal asibiti”


Yaji daɗin tambayar da tayi masa, Yana ɗaya daga cikin abunda yake kara masa sonta, duk inda zata je sai ta nemi izininsa duk da kasancewar ta yar boko kuma yar siyasa amman bata taɓa yarda ta fita ba tare da izininsa ba, Hannu yasa ya rumgumo ta cike da jindaɗi


“Nayi miki, ba ta da lafiya ne?”


“Eh kasan Tana fama da ciwon nan na blood cancer kuma ga cikin da ke jikinta”


“Toh Allah bata lafiya ya sauke ta lafiya”


“Amin haba ko kai fa amman ka wani taso min ɗazu da matsifa duk kasa na tsorata”


Dariya yayi irin tasu ta manya yana kara janta jikinsa.



        ***             ***            ***


Saif na fitowa part ɗin Daddy ƴyaji duk ya tsani gidan, babu abinda Saif ya tsana irin faɗa, faɗan da Daddy yayi masa yasa rance ya ɓace sosai, yasan kuma babu gurin da zai samu sassauci idan ba ganin Minal yayi ba dan a yanzu ita kaɗai ce farin cikin sa, komawa yayi part ɗin Momi ya ɗauki makullin motarsa ya bar gidan.


                  ***              **          ***  


“Sister ina zoben ki.?”


Kairat ta tambaya lokacin da idonta suka kai kan yatsun Minal,


“Saif ne ya cire shi”


“Saboda mi?”


“Wai yana so”


“Kuma kika kyale shi ya ɗauka”


“A a ban ma sani ba hannu na kawai ya rika ya zare”


“Kin ban mamaki Minal kinyi saurin ba da kai ace duk wulakancin da Saif yayi miki kina kulashi har ki bashi damar rika hannun ki yay....”


“Kairat.....”


Mummy ta tari numfashinta tana zuba ma Minal abinci a plate, ta cigaba


“Da zaki lura da zaki gane Saif yayi nadama Kuma yana son Minal sosai a yanzu”


Kai ta girgiza,


“Oh Mummy abunda nake kokarin lurar da ku ba shi kuke son ganewa ba, yana son ta zai wulakanta ta yaki saurarenta”


Mummy ta zauna kusa da Minal tana kallon Kairat


“Dole ne duk namijin da ya kama matarsa da wani yayi abunda Saif yayi koma abinda yafi wanda Saif yayi,

 Zuciya a ɓace take a lokacin ido a rufe kunnuwa kuma a dwaɗe ba zai iya sauraren ta balle har yayi mata uzuri amman kin ga a yanzu da gaskiya ta bayyana yanzu ne zaiyi ma kansa bitar karatun da ya manta,

  Minal tana bukatar kulawar Saif a halin da ake ciki yanzu ko dan abinda yake cikin ta.....-”


Shigowar Saif yasa Mummy katse maganar da take ta kalleshi, Hannayensa zube cikin aljihu fuskarsa ba yabo ba Fallasa ya gaishe ta,

 Da mamaki ta amsa masa ganin dawowarsa yanzu bayan bai daɗe da tafiya ba, abinci dake Hannunta ta aje ta tashi ita da Kairat suka fice,

  Murmushi ya sakar Minal ganin yadda ta sako masa ido tana kallonsa, da sauri ta rufe idon nata kamar mai bachi, karasawa yayi kusa da ita yaja mata hanci 


“Tashi ki ci abinci ba wani bachi”


Buɗe ido tayi sai kuma ta ɗan haɗe fuska, yana taɓa mata hannu ta fisge, bai damu ba ya zauna a kusa da ita ya ɗauki abinci yayi one spoon zai kai mata a baki ta kawar da fuska


“Zan iya ci da kai na ka aje”


“Oh Kairat tace miki wani abu kenan ko?”

  

A nan ya aje abinci ya tashi da zimmar fita, tayi saurin riko hannunsa,


“Ba ta ce min komai ba kawai dai bana son ka bani ne”


Dawowa yayi ya zauna,


“Duk abinda nake miki Minal ina yi ne ɗan baby na da yake jikin ki, da kin haife min shi ba zaki saki ganina ba”


Yana faɗar hakan ya tada ita zauna ya soma bata abincin.

   Sai da ya tabbatar da ta koshi sannan ya aje plate ɗin ya gyara mata jikinta ya kuma gyara mata kwanciyarta, ya hau gefen gadon ya kwanta, ya jata zuwa kirjinsa yasa mata hannu ciki riga, zabura tayi ta tashi zaune tana kallon shi


“What.?”


Ya tambaya kamar bai san abinda yayi ba,


“Dr yace na dai na kwana da wani a ɗaki ɗaya”


Ta faɗa murya kasa-kasa, murmusawa yayi


“Common Minal karki mai da ni wani kalar mutun mana, ko ba likita bane ni ai nasan aikin su, ko ki kwanta ko na ɗauke ki muje gida mu kwana”


Karantar da gaske yake a idonsa yasa ta koma ta kwanta ta bashi baya, Hannu ya sake sa mata A inda yasa ɗazu, ganin tana unkurin sake tashi yasa ya rumgumeta still hannun nashi yana cikin riganta,


“For the sake of our baby......”


Ya raɗa mata a kunne yana lumshe ido, buge masa baki tayi da kanta tana murkususun kwace kanta


“Sake ni naje wani ɗakin na kwanta bachi nake ji”


“No kwanta a nan ba zan miki komai ba i promise”

  

Ya faɗa yana zare hannunsa daga cikin rigan nata, a nan ta gyara kwanciyar ta, shi kuma ya sauke ajiyar zuciya ya shafa kansa yana haɗiyar yawu.


    

     ***                   ***                  ***


MORNING @9:21AM.............

       

     Da kansa ya haɗa mata kari, ya rika bata a baki tana ci har ta konshi sannan ya washe komai ya mai da gefe, ita kuma ta kwanta tana kallon windo, a nan ya shiga matsa mata kafafu a hankali, ganin tana jindaɗin matsar yasa shi fara wuce guri yana shafar cinyoyinta, 


“Please Saif stop..”


Ta faɗa tana janye kafafunta, ɗauke hannunsa yayi yasa yatsunsa cikin gashin kansa yana matsar gashin ya lumshe ido.

  Ringing ɗin wayarsa yasa shi buɗe ido, yasa a hannu aljihu ya ɗauko wayar yana dubawa, number Momi ce


“Hello”


Ban ji me aka ce masa ba na dai ji yace


“Ok”


Ya kashe wayar ya fita.

   Bai daɗe ba ya dawo ɗakin tare da su Momi da kannensa,

  Tashi Minal tayi zaune tana kallonsu, murmushin da ta gani a fuskar Momi yasa ta kalli Saif, shima murmushin ta ga yana yi mata. Momi ta nufo ta ta kama hannayenta


“My child.....”


Sai idonta suka cika da hawaye, rumgume ta Momi tayi tana shafa bayanta,


“Kiyi hakuri yata ki yafe mana rashin sani ne yasa muka wulakanta ki ashe ke alheri ce a gare mu”


Kuka Minal tasa ma Momi kuka mai ban tausayi da tsuma zuciya, Momi tayi ta bata hakuri har su Kairat da Mummy suka shigo, Kairat taji daɗin ganin Momi sosai hakan ya tabbatar mata da lallai Saif yayi nadama tun da gashi har mahaifiyarsa ta zo ganin matarsa, Fira Momi da Mummy suke hirar yaushe gamo, sun ɗan daɗe suna tattaunawa sannan Momi tayi musu sallama.


         ***               ***              ***


Kai da kawo Abban Huda ya rika yi a gurin Saif ganin yadda ita Huda ɗin duk tabi ta haukace akansa, amman Saif ya ce sam shi kan ba dashi ba gaɗa a hurumi, shi kan ta riga ta fita ransa, ganin hakan yasa shi zuwa gurin Daddy ya tuntuɓe shi da maganar Daddy bai ki tasa ba sai dai kuma shi ɗin mutun ne da baya tursasa yayansa yin abunda basu tashi ba yasan a halin yanzu Saif ya riga ya yafe ta, hakuri kawai Daddy ya bashi yace su cigaba da addu'ah.



    Sannu-sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba aje ba, kuma bayan wuya sai daɗi hankalin Minal a yanzu kwance yake babu abinda ƴke damunta, kula take samu ta ko'ina bata da matsala a yanzu in ban da rashin lafiyar da take fama da ita dan ciwon yaki ci yaki canyewa kullum sai karuwa yake kamar ba abunda ake yima magani ba, hakan yasa likitoci suka bada damar ya rika fita da ita suna ɗan zaga gari sai dai ba tafiya mai nisa ba ko da a cikin asibitin ne zasu iya yinta, ganin cikinta ya fito kuma yana ɗan yi mata nauyi.


  Yau ma kamar kullum yana zaune saman gadon tayi matashin kai da cinyarsa yana karanta mata magazine yana saka mata gauta a baki.


“Saif...” 


Ta kirashi a hankali, bata damu da ya amsa mata ba ta cigaba


“Huda ta kira ni ɗazu”


Rufe magazine ɗin yayi ya kalleta,


“Mi tace miki?”


“Kawai ta gaishe ni kuma ta tambayi kana nan nace mata a a lokacin ka ɗan fita ne”


“Da wace wayar ta kira ki?”


“Waya ta mana”


Hannu ya kai ya ɗauki wayar dake kan filo


“Daga yau ba ke ba waya sai kin haihu”


“Haba dai karka min haka mana wallahi ita ta kira ni”


“Naji ai, na dai ce ba zaki sake rika waya ba that's all”


“Amman Saif da ka saurare ta baka sani ba ko wani abun zata ce maka ta faɗa min wai tana kiran ka baka ɗagawa”


Leɓenta ya rika ya ɗan matsa kaɗan,


“Da ba ke bace kika min wannan maganar da sai na buge miki baki”


Turo baki ta ɗanyi, wai ita ala dole tayi fushi, yadda tayi ɗin sai ya bashi dariya har ya aika mata da kyautar kiss yana shafa ta. 

Shigowar Dr. Zainab bai sa ya dai na abunda yake ba, tun da ba yau ta soma ganin yana taɓa ta ba kuma a ganinsa ba haramun yayi ba sai dai ace yayi rashin kunya,

   

“Sannun ku da hutawa”


Ta faɗa tana murmushi, tashi Minal tayi zaune


“Yauwa Dr sannu da zuwa”


“Yauwa Minal ya lafiyar jikin?”


“Alhamdulillah”


  “Ina ganin ni daga yau za muyi canji aiki da abokin aiki na wato likitan da yake kula da ke ya dawo kuma shine zai cigaba da kula da ke har lokacin da zaki samu sauki”


Ta kalli Saif da bai san ma abunda take faɗa ba dan  hankalin baya gurin, wasa yake da yatsun Minal yana goga mata fuskarsa yana raɗa mata wasu maganganu a kunne wanda ita kaɗai tasan manufar su kuma take jin mi yake faɗa, 


“Saif ...”


Dr. Zainab ta kirashi ta yadda zai iya bata aron hankalinsa


“Yes”


Ya amsa mata ba tare da ya kalleta ta ba, sai dai ya ɗan ɗago kai alamar yana sauraren ta,


“Na gode sosai da ka cika min alkawari na a yanzu haka mahaifiyata tana cikin farin ciki nima kuma ina cikin sa dan farin cikin ta shine nawa”


“Your welcome”


Ya faɗa yana ɗan cizon kumatun Minal. Murmushi tayi 


“Minal Allah ya kara lafiya ya kuma saukar da ke lafiya”


“Amin na gode sosai”


Juyawa tayi ta fice daga ɗakin tana murmushi, indai sabo ne ta saba da ganin irin  wannan soyayyar a gurin Saif tun da Huda ma yana mata kuma ganinta bai sa ya daina abunda yake.


    ***                ***              ***


“Saif Mi kayi mata hala?”


Kiss ya rika mata yana faɗa mata,


“Wani ne nasa aka sako mata ko mijin mamanta ko me oho wani dai Alhasan Muhammad Yola”


Ras! Ras! Sunan ya kayar mata da gaba duk da bata san mai sunan ba, amman ba zata manta da Mummy ta faɗa mata fullname ɗin mahaifinta ba shima Alhasan Muhammad Yola, sai dai ba lallai bane ya zamo shi ɗin bane, 


“Mi ya faru? Ko kin sanshi ne?”


Ya tambaya ganin computer ta nuna faɗuwar gaban nata,


“A'a ban sanshi ba”


“Miyasa gaban ki ya faɗi?”


“Babu komai”


Baya son ya matsa mata da tambaya, gashi kuma yaga yanayin ta ya canja kwantar da ita yayi yana buga bayan ta alamar tayi bachi.

   Amman ina bachin yaki yazo mata sai ma ta dasawa kanta sabon tunani, ganin hakan yasa ya tashi ya sauko da ita saman gadon


“Muje mu ga gari”


Da sauri ta gyara tsayuwarta daman abunda take nema kenan, shi kuma ya rika hannunta ya ɗauki wasu abubuwan da likita yace ya rika, rika mata idan zasu fita.


                ***    ***     ***


        Yawo ya rika yi da ita har sai da tace masa ta gaji sannan ya biya wani shago ya saya mata kayan ciye-ciye, a maimaikon ya dawo da ita asibitin sai kawai taga ya nufi wani gida da ita,


“Mi za muyi a nan?”


Ta tambaya tana kallon fuskarsa shi kuma ya bata amsa yana kokarin kashe motar


“Karatu”


“Wane irin karatu kuma?”


Bai ce mata komai ba ya buɗe motar ya zagaya gefenta ya buɗe mata 


“Fito muje ciki ba zamu daɗe ba”


“Mi zamu yi a ciki?”


“Idan muka je zaki gani ai”


Kamar tayi masa musu sai kuma ta fito suka nufi kofar shiga cikin gidan.

     Saman kujera ta zauna tana karewa parlour kallo shi kuma yayi murmushi ya zauna kusa da ita yana jan hancinta, tana kallon shi ya ɗaga mata gira ya kai hannu ya taɓa cikinta,


“Saif ka daina mana”


Ta faɗa kamar zatayi kuka,


“Baby na ne ai”


Unkurin tashi tayi yayi saurin rumgumeta yana dariya, ya shiga matsa mata jiki yana murzawa cikin wani irin salo wanda ita kaɗai tasan fassarar sa,

 kallon tuhuma tayi masa, shi kuma ya ɗaga mata kafaɗu yasa mata hannu cikin riga, zatayi magana ya haɗa bakinsa da nata..........



    ***               ***                ***


A ɓangare Safiyyah ma bata da wata matsala, dan Momi bata nuna mata komai ba gashi kuma tana samun kula gurin Gwaggo, kafar ta ma zan iya cewa ta warke tafiyar ta ce kawai ke da saura ta dawo dai-dai,

   abu ɗaya ne yake damun ta wanda kullum shi ne yake ci mata tuwo a kwarya, son Saif son da ba zai taɓa gogewa a zuciyarta ba, son da bai taɓa bari taga laifin Saif ba, son da kan rufe mata ido ta aikata komai,

   Ajiyar zuciya ta sauke ta lumshe ido, Gwaggo dake rike da carbi ta kalleta


“Ki dai na damun kanki Safiyyah, ki bari kawai ki kara jin sauki hankali ya kwanta zamu samo kan Saifu sai mun ba kowa mamaki”


Bata ce komai ba ta kai hannu ta ɗauki plate ɗin indomie dake gabanta ta fara ci.


  

                            ***     ***   ***

Wasa-wasa yanzu cikin Minal yana cikin wata na bakwai, duk wanda ya ganshi sai a ɗauka yayi wata tara saboda girman da yayi, 

  Sai dai kuma wata matsalar ɗaya, ciwon ta a yanzu yafi na da, dan zubar jinin sosai take yinsa abun har ya fara ba likitocin tsoro kusan kullum sai an sa mata jini, gashi a yanzu har hannu take sawa ta cika shi da jinin dake mata zuba a hanci,

     Yau ma Saif na shigowa ya ga ta cika hannun da jini har da sare, tasa ya ɗauko ya tara mata ta zuba jinin ya shiga gyara mata jikints jinin na kara mata zuba,

Ita kanta taji tsoron yadda taga zubar jinin yau daman ta daɗe da sadakarwa tasan ba zata tashi ba, ganin tsoron dake fuskarta yasa Saif ya rumgume idonsa taf da hawaye,


“Za ki ji sauki Minal okey karki da ta hankalin ki”


“Dan Allah Saif ka Auri Kairat marry her and make her happy ta yadda zaku kula min da abunda zan haifa,”


Ya ɗago fuskarta


“Haba Minal taya zan aure ta ina auren ki ? Ba zan sake yin wani auren ba dake zan zauna har a bada”


“Ba zamu yi irin wannan zaman ba Saif mafarkin mu ba zai taɓa tabbatuwa ba,

   And Saif ka faɗawa Kairat ta kula min da Mummy da Baby na”


Hawayen dake idonsa suka zubo sai kawai ya samu kansa da wani irin kuka kamar mace, hannu tasa ta shafi fuskarsa


“Saif I love you I love you so much, If there ever comes a day when we can’t be together, keep me in your heart, I’ll stay there forever”


Ganin tana kokarin zauta shi yasa ya sake ta yana share hawaye,


“Bari na kira Dr”


Rike shi tayi


“Karka je Saif ina jin daɗin rumgumar nan da kayi min ina jin wani sanyi yana ratsa ni, Saif ka cigaba da nema min gafarar ubangijina ko da bayan mutuwa ta kuma kace Mummy ta yafe min, idan ka ga Mahaifina ka tambaye shi mi nayi masa ya gudu ya bar mu ni da Mummy na? Kace masa wace riba ya ci?. Saif ka nunawa ɗana kabari na ka karanta masa kyakkyawan tarihina ka ɓoye masa mummuna ka sashi a jikin ka ka nuna masa so kaji? Kar ka masa irin abunda mahaifina yayi min, 

Saif ka faɗawa Deen na yafe masa kuma ina sonsa yana nan a matsayinsa na aminina Saif ka rika tunawa dani kaji ka rika yi min addu'ah”


Ture ta yayi da karfi


“Ya isa Minal ya isa”


Ya juya ya fita yana hawaye ya kira Dr. Hankalin Dr ya tashi sosa ganin yanayin ciwon nata a yau, cikin sauri ya rubuta mata wani magani wanda zai tsayar da zubar jinin,

    jiki na rawa Kairat ta siyo maganin, dan Mummy da Saif hankalin su a tashe yake komai basa iya wa,

  ana kawo maganin likitan ya bata ta sha, yasa wata nurse ta gyara mata jikinta Saif kuma ya hau saman gadon ya rumgume ta yana shafa kanta.

   ba ayi minti goma sha biyar da shan maganin ba jinin ya ɗaina mata zuba, sai dai kuma suka nemi numfashinta suka rasa ga idonta yana motsi amman ba numfashi, a nan hankalin likitocin ya kara tashi da sauri suka canja mata gado suka nufi wani ɗakin da ita suka sa mata abun neman numfashi suka saita numfashin da computer suna dannar kirginta, amman ina mai kira yayi kira manzo mutuwa mai gaggawa idan lokaci yayi ba tsaya wa,

 a nan suka ga ta kangare ido tana motsi da baki kaɗan-kaɗan.


                     ***      ***      ***

      Su Mummy na tsaye cirko-cirko suka ga likitan ya fito, kallo ɗaya yayi ma Mummy tausayinta ya kama shi, yasan yadda Mummy take son Minal dan shine likitan da take kula da Minal tun tana karama yasan yadda hankalin Mummy yake tashi duk lokacin da ciwon ta ya tashi, 

   yanzu taya zai iya faɗa mata mutuwar ta!  Su kuma sai kallon shi suke sun kasa tambayarsa ya ake ciki.

   Suna haka wani likitan ya fito daga ɗakin yana faɗin


“Dr. Sulaiman Abunda yake cikin ta yana da rai.........”


Dummmm gaban Mummy ya faɗi idonta cike da hawaye ta kalli Dr


“Ta mutu kenan?”


“Kiyi hakuri mutuwa tana kan kowa kuma idan lokaci yayi ba a tsaya wa”


Wata irin kara Mummy ta saki tana ja da baya, Kairat tabi gini ta sulale kasa zaune, Saif kuma ya nufi ɗakin da sauri yana faɗin 


“No no no no nooooo!”



BABBAN GORO 41


Faɗuwa Mummy tayi zaune tana wani irin numfashin tana kallon tiles, da sauri likita ya nufe shi da Kairat, Kairat ta dafa ta,


“Mummy Mummy”


A nan ta ɗago ta kalli Kairat idonta a raunene kamar mai jin tsoro, ta jata jiki na rawa ta rumgume


“Minal my child.....”


Fashewa Kairat tayi da kuka hakan yasa Mummy tayi saurin sakin ta, ta matsa can ta dafe kai ta rumse ido,

   Ta ɗan daɗe kamin ta buɗe idon ta kalli kofar ɗakin da Minal take ciki, a nan ta tashi tsaye ta nufin tafiya sai kafafun ta suka kasa ɗaukarta ta faɗi, da sauri likitan ya rika ta yana kiran wasu nurses,

  Unkurin ta sake yi a karo na biyu da nufin sake tashi a nan ma faɗuwan tayi dan jikinta yayi ma kafafunta nauyi basa iya ɗaukar ta,

  A nan ta soma jin wani kalar abu na daban, zuciyarta tayi mata nauyi kanta ya sara sai ta rika jin kamar mafarki take kalmar Dr ta rika dawo mata _Duk mai rai mamaci ne_ sai a lokacin idonta ya cika da hawaye alamun rashin ya fara fisgarta, kamin ka ce kwabo sai gata tana kuka mai haɗe da dariya,


“You know what? Minal she's always asking me Mummy idan bana nan ya zaki ji! Minal ina ma zaki zo yanzu kiji yadda nake ji....”


Kairat ta matso kusa da ita ta kama hannunta tana kuka mai tsuma zuciya,


“Mummy kiyi hakuri haka Allah yaso”


Fashewa Mummy tayi da kuka


“Mutuwa baki kyauta min ba, Minal ita kaɗai ce farin ciki na ita ce family na ita kaɗai na mallaka a duniyar nan miyasa zaki ɗauke ta ki bar ni bayan ni nafi dacewa dake haba mutuwa haba mutuwa....”


Rufe mata baki Kairat tayi tana girgiza mata kai,

   A nan ta mai dubanta gurin Kairat


“Kin ga Minal ta tafi ta bar ni ko!......"


Shiru tayi tana kallon tafin hannunta, zuwa can ta sake kallon Kairat tace


“But never mind i will take good care of her clothed and her room so that I can be with her again I will always....... ”


Sai kuma tayi shiru tana kallon yatsun hannunta hawaye masu zafi na mata zuba,


“She's will come back to me very soon”


Ta faďa tana fisgar gyalenta tana kuka.

   Yanayin kalamanta da kuma abunda take ya tabbatar ma da likitan tana kokarin barin hankalinta ne, A nan yasa wasu Nurse suka ɗauke ta aka ɗora ta saman kujera suka nufi wani ɗakin da ita sai surutai take...


          ***       ***    ***  


Kamar mahaukaci Saif ya shiga ɗakin, ya nufe ta da sauri ya shiga girgiza ta


“Minal Minal Minal Minal wake up!”


Da wani irin karfi yake girgiza fuskarta, zafafan hawayen dake masa zuba na ɗiga a saman  kumatun ta, ganin bata motsa ba ya hannunshi ya matse mata baki 


“Talk to me Minal Saif ɗin ki ne please Minal please”


Ya faɗa yana taɓa lips ɗinta da wani irin karfi. A nan wata nurse ta nufo shi ta ɗafa tana janshi baya


“Kayi hakuri ta riga ta rasu iya.......”


Bata karasa maganar ba ya kai mata wani mugun haushi nan take bakin nata ya fashe da jini, ba shiri ta fasa ihu tayi waje da gudu.

   Hannu yasa ya tallafo kan Minal ya rumgume ta tsam-tsam a kirginsa kamar mai rai yana kuka


“Please Minal karki Min haka kin san bamu taɓa irin wannan wasan da ke ba, Minal wake up please ko dan babyn mu kin san Mummy tana son ki how can go and leave her! Im still here”


Dukowa yayi dai-dai ita ya haɗa fuskarta da tasa hancinsa yana gugar nata yadda ya sata mata lokacin da take raye,


“I love you Minal...”


A hankali ya faɗa idonshi a lumshe yana goga mata hancinsa hawaye na mishi zuba, yasan da tana da rai da yanzu ta shafa kanshi ko ta mayar masa da amsa.

    Hakan yasa ya sake ta yayi baya yana kallon fuskarta kamar wanda yaga wani abun tsoro ya fashe da wani irin kuka yasa yatsunsa cikin gashin kansa yana matsar gashin da kokarin buga kansa a ginin ɗakin.


  Daga likitocin har nurses ɗin babu wanda yayi unkurin yi masa ko da magana balle ma taɓa sa sai kallonsa suke.

   Shi kuma kuka yake ba kakkautawa kamar karamin yaro, can kuma ya tashi tsaye da sauri kamar wanda akayi ma shocked ya bar ɗakin da gudu,

   Duk gun da yabi kallon sa ake har ya isa parking space, bana jin yasan lokacin da ya buɗe motar ya shiga har yayi mata key, sai da ya tsinci kansa a saman ti-ti sannan ya fara tunanin ina zai je?


_Gida gurin Momi_ Wata zuciyar ta bashi amsa a nan ya kara gudun motarsa kamar mai wasan tsere ya danne sitari da hannu ɗaya babu ruwansa da wanda ke kan ti-ti sai dai idan kai kaso rayuwar ka ka kauce ba dai shi ya kauce maka ba.

    Yadda masu gadin gidan suka ganshi yasa suka tak'a masa bingigoginsu, ganin yadda ya nufo gate ɗin da gudu abunda suka san bai saba yi ba, abu ɗaya ya gana du buɗe masa wuta sanin Motar Saif ce basu sani ba ko shi ɗin ne sai dai suyin shirin ko ta kwana,

   Wata mahaukaciyar horn ya danna musu  amman ba su buɗe gate ɗin ba ganin yadda suka yi ciro-ciro suna kallonsa yasa ya buɗe Motar ya fito ya nufi cikin gidan yana kuka kamar mai sauti kamar mace.


       Yanayin yadda ya turo kofar falon yaba Mummy tsoro, bata kara katsewa ba sai da ta ganshi yana kuka, tun kamin ya karaso kusa da ita ta nufe shi tana tambayar ba'asi,


“Subhanallahi lafiya? Miya same ka haka?”


Hannayensa ya shiga nuna mata yana wani irin kuka mai karfi


“Momi Min....”


Muryarsa ce ta sarke ya kasa karasawa saboda kukan da ya taushe masa zuciya. Cike da tsoro Momi ta dafa shi tana faɗin


“Mi ya same ta mi ya samu Minal ɗin?”


“Momi ta .....ta..t....”


Kin fitowa maganar tayi, ya faɗi kasan tile yana maida numfashi ya fashi da wani irin kuka mai karkarwa da kara ya kai ma tile ɗin wani mugun naushi.


“Innalillahi wa inna Ilaihirraji'un”


Shine abunda Momi take ta maimaitawa tana jimama mi ita a zaton ta ko ba'ace abunda yake cikinta ya samu matsala ba ita ba sai.

   Da sauri Lubna ta fito daga ɗakinta ta nufo gurin da suke, bata tambayi miya faru ba dan yanayin da taga ɗan'uwanta tasan mutuwa ce kawai zata iya sashi shiga cikin irin wannan halin,

  Nan itama na ta idon suka ciko da kwallah a hankali ta risina ta dafa ɗan'uwan nata tana masa kallon tausayi. 

A firgice ya ɗago suna haɗa ido ya rumgume yana kuka ɗa faɗin


“Lubna Minal Minal Minal”


Kukan suke daga ita har shi har Momi babu mai ba wani hakuri.


             ***            ***            ***

Zaune take guri ɗaya tana rusa kuka kuka ne wanda ake cewa shi ke zuwa da kansa shi yake yin kansa, kukan take ji yana zo mata ta ko'ina zuciyarta ta faɗa tayi kasa jijiyar kanta ta taso idanunta sun kumburo majina sai tsiyaya take mata,


“Kuka ba shi da muhimmaci a gare ta yanzu addu'ah take so”


A hankali ta ɗago ta kalli Doctor sai kuma ta kara rushewa da kuka.

   Ajiyar zuciya ya sauke ya mika mata wata farar takarda mai rubutu,


“Baby da yake cikinta yana da rai shi muke son muyi  tiya ta mu ciro dan haka muna bukatar sa hannun ki tun da Dr. Salamatu hankalinta baya jikinta, Saif kuma ya bar asibitin”


Kamar bata ji abunda yace ba ta cigaba da rera kukan tana wani wahalallen numfashi


“Urgent ne Kairat, sign to save yours sister child....”


Hakan da yace mata sai yasa kuka nata ya tsagaita kalmar shi ta tuna mata da maganar Minal lokacin da take exercise a falo garin kallon Tv ta tashi faɗuwa sai a kayi sa'ah Kairat ta kawo tayi saurin tare ta tana faɗin


“Glad i save you”


Sai ita kuma tayi Murmushi ta kalli Kairat tace


“You will always save me and my family Kairat put this in your heart...........”


Hannu ta kai ta dafe zucuyarta hawaye na zubo mata a hankali,


“Kairat ke muke jira”


Kiran da yayi mata yasa ta ɗago jajayen idanunta ta kalli paper, still hawaye na mata zuba ta mika hannu ta karɓi pen ɗin da nufin signing.


Hello my people naga addu'o in ku naji daɗi kuma na gode sosai  mamana taji sauki thanks all for your prayers I really appreciate it Allah bar zumunci, Keep your eyes open i always update Insha Allah just keep vote and comment on every line thanks for the love heart you all


HAFSAT AHMAD wannan Shafin na ki ne kedai bless you dear



BABBAN GORO 42


Assalamu Alaikum readers of  ™BG i want to use this opportunity to say something hope za ku ba ni aron hankalin ku! I know we are writing to entertaining, but we have to touch the reality, ina son duk mai karanta littafan KHADEEJA CANDY ya rik'a sawa a ransa kamar gaske ne yake faruwa saboda ina tafiyar da littafai na ne akan abunda hankali zai ɗauka.

  Na samu messages ɗin readers wasu like karki kashe mana Minal please. wasu like idan kika kashe ta kin ɓata Novel ɗin ki. wasu like ni ban taɓa ganin inda aka kashe star a Novel ba. Wasu idan kika kashe ta me kika yi kenan. wasu like bai kamata Minal ta mutu ba. wasu like Please ki ce dogon suma tayi and list goes on and on and on and on and on......

Haba dears! Yanzu dan Minal tana star a Novel sai a ce ba za mutu ba? Ke yanzu dan ana sonki a gidan ku sai ace ba zaki mutu ba? Ki rika sawa a ran ki kamar ke ce ko kuma wata ce hakan yake faruwa da ita, wasu na cewa wai Minal bata ji daɗin rayuwa ba ya kamata ace taji daɗin rayuwa kamin ta mutu ina son ku koma baya ku karanta gurin da kuka manta, Minal tayi rayuwa mai kyau kuma ta jindaɗi  Mummy ta nuna mata gata sosai har hakan yasa ta fara shaye-shaye babu wanda ya isa ya tsaya ya faɗa mata wata magana ta kyale shi remember? daga lokacin da ta fahimci bata da uba ta soma fuskantar bakin ciki a rayuwarta, masu cewa ya kamata ace ta gana da mahaifinta ba duka abunda mutun ke so yake samu ba, Nasan wata mata da iyayenta suka yi auren kasa da kasa babanta ɗan Najeriya mamanta yar Ghana sai suka rabu tana karama lokacin da ta girma ta mallaki hankalin kanta sai ta nemi ganin mahaifiyarta haka ta haɗa kuɗi motar ana sauran kwana uku ta tafi aka kira aka faɗa mata mamanta ta rasu kuma bata taɓa ganin mahaifiyar ta da ido ba, image idan Novel ne sai a ce bai yi kyau ba right? karku manta Mahaifin Minal shi ya wulakanta ta da kan shi, akwai masu cewa taya za ace  Minal ta mutu ta bar Mummy bayan ita kaɗai ta mallaka a duniya da ace reality ne da nace mu ku haka Allah yake ikonsa idan yaga dama akwai wanda har ya gama rayuwar sa ba zai taɓa ganin jininsa ba akwai wata friend ɗita maybe wasu daga cikin kun sun santa ana ce mata Hannatu Ismail tana daf da kare karatun ta Allah ya karɓi abarsa kuma ita kaɗai iyayenta suka haifa sun ɗora mata buruka da yawa babu irin jindaɗi da bata yi a gidan su amman mutuwa ta kutsa ta ɗauke ta toh haka rayuwa take muna cikin sha'anin mu take ɗauke mu. ya kamata mu rik'a kula da irin wannan, na fahimci wasu suna karanta Novels ne kawai da nishaɗi kalilan ne ke karanta su fahimci sakon da abun ke son isarwa ko kuma darasin dake ciki.

Idan a reality ne kuna ganin mai ciwo irin na Minal zata rayu? No way duk da nasan rayuwa a hannun Allah take karku manta the Doctor said mai blood cancer leukemia in dai yayi Cronin they can't survive kun tuna? sannan ku koda yaushe ace dogon suma a Novels always in reality hakan yana yawan faruwa? No nasan ita ce ansar! To haka zaku rika sawa a zuciyarku idan kuna karantawa after that akwai Kairat, Huda, Safiya, Saif duk suna raye only Minal is gone and she has to, bari na tsaya a nan kar wasu suce na cika surutu i says a lot, anyway thank you for your time i really appreciate your efforts ina fatar za ku fahimci bayanin nawa zaku kuma tuna abunda kuka manta. I heart you all stay bless all the best one heart one love 😍 happy reading👌🏿


42


Kairat nayin Sign ya juya da sauri ya shiga ɗakin da take, tare da taimakon nurses da wasu likitoci aka shiga da ita ɗakin tiyata,  a kofar ɗakin tiyatar Kairat ta tsaya tana safa da marwa hawaye na mata zuwa tana jiran a fito da ita kashe kunne tayi taa sauraro jin take kamar ace mata Minal ɗin tana raye.

   Sun ɗauki awo uku a ɗakin suna yi mata tiyata, cikin nasara aka yi mata aikin suka fito baby girl sai dai bata da lafiya sosai dan duk a takure take numfashinta ma sai a hankali. suna fitowa da ita Kairat ta nufo su da sauri da nufin karɓar yarinyar jiki har karkarwa yake kamin ta mika hannu Doctor ya rike ta a nan ta kalleshi ta kalli baby, 


“Sorry Kairat ba zaki iya taɓa ta yanzu ba bata da isassar lafiyar da za'ayi mata haka a yanzu zamu sata cikin kwalba ne zuwa wani lokaci saboda yar bakwai nin ce”


Ya faɗa yana kallon Baby dake hannun wata nurse, karasa tayi kusa da baby ta tsaya tana kallonta sannan ta risina ta manna mata kiss a goshi. a nan Dr ya ɗaga ma nurse ɗin kai ta wuce da ita, haka Kairat ta bita da kallo har ta ɓace mata da gani. kafaɗunta Dr ya dafa ya juyo da ita ta yadda zata fuskance shi ya soma mata magana a hankali


“Kairat dole ne ki zama mai hakuri you are the only person da Dr.Salamatu zata gani ta jidaɗi sai kuma baby da Minal ta bari,

  Dr Salamatu da daɗe da sanin Minal ba zatayi rayuwa mai tsawo ba tana yawan bincika ta akan ciwon ta ni kuma ban taɓa ɓoye mata komai ba duk mai rai dole ne ya yarda da mutuwa ko da kuwa kafiri ne balle musulmi sai dai hanyar da zata zo maka ɗin zata girgiza ka,


Kairat kece zaki cire ma Dr Salamatu kewar Minal dan ke kike zama da ita bai kamata ace ke kika kuka ita tana yi ba mamaci baya son haka addu'ah ku take da bukata idan ke kika kuka waye zai lallaɓa ta ya nuna mata hanyar yin hakurin? you have to be strong nasan ke da Minal tare kuka tashi dan tun lokacin dana fara kula da Minal tare na ke ganin ku tun kuna kanana nasan zaki ji zafi sosai but dole ne ke ki ɓoye naki kukan ki haɗiye damuwarki for the sake of Mummy”


Hannu tasa ta share hawayenta tana kallonsa cike da fahimta, ganin hakan yasa shi cigaba


“Nasan yanzu ta farka dan alluran da nayi mata na awa biyu ne please stay with her wipe her tears”


Kai ta ɗaga masa tana sauke ajiyar zuciya, shi kuma ya sake ta ya nufi hanyar waje. Sai da tayi ta sauke ajiyar zuciya ya fi goma tana share hawaye ya fi a kirga sannan ta nufi hanyar da zata sada ta da ɗakin da Mummy take ciki.


Zaune ta tarar da ita tana murza wata munduwa dake hannunta hawaye na mata zuba, har Kairat ta zauna kusa da ita bata ɗago ta kalleta ba, a nan Kairat ta kai hannu ta ɗago Fuskarta, Mummy kamar mai jira sai ta fashe da kuka tana faɗin


“Lokacin da nayi birthday Minal ta bani wannan abun hannun tace min tana son na sashi a hannuna na rika tunawathat do you  remember?”


“Yes i remember Mummy ta baki shine dan ki rika tunawa da ita kiyi mata addu'ah ba kiyi mata kuka ba please Mummy karki ce min baki shirya ma zuwan wannan ranar ba ke da kanki kike faɗa min wata rana Minal zata tafi ta barki har a gabanta kin faɗa ita ma ta sha faɗa miki haka,

   ta kan ce miki ko da bata nan ni ina nan kuma nima nace miki haka Mummy ba Minal kawai kika haifa ba har da ni why you behaving like this ko da yaushe sai kice baki da kowa sai ita mi yasa kike min haka? mi yasa kike yi ma Minal kuka a lokacin da take da Bukatar addu'ar ki bata sha faɗa miki ba karki mata kuka idan ta rasu ko bata faɗa miki ba kuma bata tafi ba Mummy sai da ta bar miki copy ta”


Cike da natsuwa Mummy ta kalleta sai ta jata jikinta ta rumgume still tana hawaye


“Kuka shine yake yin kansa Kairat ba sai ana kirasa ba but I will try”


Kamkame ta Kairat tayi tana nata kukan a hankali yadda Mummy ba zata ji ba. 



Silent readers run da ba Ku votes ban ya ban ya... 😹


Dear, Readers still a'ce dogon suma tayi? waiting for your comments



BABBAN GORO 43




“Kuka kike yi ko Kairat?”


Mummy ta tambaya jin hawayen Kairat na mata zuba a bata, 

   Batayi magana ba sai kawai ta kara kankanme Mummy tana cigaba da kukan, a hankali Mummy ta ɗagota ta rika fuskarta ta hannayenta tana murmushin karfin hali


“Ki daina kuka kinji ki daina mata kuka lets go home”


Ta faɗa tana kokarin saukowa saman gadon cikin da karyayyar zuciya.


     ***


Ganin yadda Saif yake kuka yasa Momi ta haɗiye nata kukan tasa hannayenta biyu ta tado da shi zaune ta rika fuskarsa ta yadd zai fuskance ta


“Kayi hakuri haka Allah ya kaddara maka haka yaso ya kasance a gareka kuka ba naka bane Saifullahi, ka zamo na miji ka yarda da kaddara mamaci baya son kuka musaman ita da ba a ko kai ta makwancintaba addu'ah ce kololuwar soyayyar da zaka nuna mata ka daina mata kuka”


Bai dai na kukan ba sai dai ya sassauta muryarsa ta yadda ita kaɗai zata iya jinsa sai Lubna dake kusa da ita,

  Wayarsa ce dake aljihu ta shi ga ringing alamar kira, bai kula wayar ba ya haɗe yawun dake bakinsa ya unkura da nufin tashi Momi tayi saurin rike shi ta zaunar ta kalli Lubna 


“Dauko min ruwan sanyi”


Tashi tayi tana share hawaye ta nufi firijin, ta ɗauko mata tare da kofi ta kawo. 

     Buɗewa Momi tayi ta zuba masa ruwan a kofi ta kai masa a baki. da wani irin karfi yake shan ruwa kamar wanda yayi wata bai sha ruwa ba, yana gama sha ya sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya ya ɗosa kansa kan cinyar Momi ya lunshe ido.

    Hannu tasa tana shafa kanshi a hankali a zahiri tana tausayin ɗan ta ganin duk yadda ya birkice lokaci ɗaya ya koma kamar karamin yaro.


     Taɓa kofar da aka yi yasa Momi ta ɗago ta kalli Nasir da ya kunno kai cikin falon kamar marar lakka jikinsa babu kuzari, yana karasowa kusa da ita ya kai hannu ya ɗafa Saif, da sauri ya buɗe ido jajayen idanunsa ya ɗago yana kallonsa,


“I'm sorry friend” 


Shine abunda Nasir ya faɗa yana matsa kafaɗar Saif hawaye na masa zuba,


“Da gaske ne ta rasu kenan!”


Saif ya tambaya idonsa taf da hawaye, kai Nasir ya ɗaga masa yana matsar kuka dake son fito masa.

  Hannu Saif ya kai ya shafa gashin kansa ya girgiza kai yana kallon zoben  Minal dake hannunshi,  bazai manta lokacin da ya karɓe zoben a hannunta ba, tana masa matsifa da faɗar 


“I hate you Saif  karka cire nin zobe”


Yana dariya yace


“No Minal komai zakiyi sai na ɗauki wannan zoben yayi min kyau Minal i love you”


“Saif no please ni na siya abuna karka cire min ina son abuna Saif bana sonka”


“Really! Bana damuwa da rashin son da kike min ni ina sonki Minal sosai kuma yanzu ne zan nuna miki son”


Ya faɗa yana kara fisge zoben daga hannunta, ganin yadda ta haɗe tai yasa ya rika fuskarta zaiyi mata kiss ta buge masa baki da karfi,bai damu ba ya ya rike fuskar nata da karfi yayi mata kiss ɗin sai kawai ta fashe da kuka, ya rumgume ta tsamtsam kirjinsa yana shafa kanta da bayanta alamat rarrashi, sannan ta kai hannu tana taɓa zoben nata dake hannunsa.


          A-hankali ya rika murza zoben yana tuna abunda ya faru hawaye na masa zuba yana sauke ajiyar zuciya.

     Ganin hakan yasa Nasir ya rumgumoshi yana buga kafaɗarsa, a nan Saif ya fashe da sabon kuka bakinsa na rawa,

   Kiran wayoyi ne keta shigowa ba kakkautawa daga wayar Saif har ta Momi da Nasir duk cikinsu babu wanda ke da damar ɗaga wayar balle har yayi magana,


                  ***    ***   ***


Cike da Mutane  Mummy ta tararda gidan, da alama sun samu labarin abunda ya faru, bata kula kowa ba ta shiga falonta idonta cike da hawaye. Kairat kan kasa shiga tayi a gurin ta durkushe tana kuka kamar ranta zai fita,


                        ☆ ☆ ☆

                          ☆ ☆

                            ☆


Ko da karfe biyu tayi anyi mata sutura kamar yadda addinin musulunci ya tana da an tsaftace ta an saka ta cikin makara.

   Bayan masu yi mata wanka sun fito Mummy ta tashi ta nufi kofar ɗakin tana tafiya kamar ta faɗi, da sauri Hajiya Suwaiba ta rike ta tana faɗin


“A a karki shiga Salamatu karkije ki faɗi kar kije kina kuka kan gawarta kuma kinga ba a son haka”


Hannu mummy tasa ta ɓanɓare hannunta tana haɗiyar yawu,


“Zan iya Suwaiba ba zan faɗi ba, babu abunda zanyi insha Allahu dan Allah karki hani gani Minal” 


   Sakinta tayi ba dan taso ba sai dan ganin hawayen dake kwance a idonta.

   Cikin rashin kuzari Mummy ta karasa kofar ɗakin ta tura kofar bayan ta sauke ajiyar zuciya ta shiga, a bakin kofa ta tsaya tana kallon gawar Minal, Kwance take cikin karaga an naɗeta da farin likkafani, Minal da bata son takura yau gata guri ɗaya ba motsi, yarinyar dake saka tufafi a mai tsada  gata a cikin likkafani.

   Kau da ido Mummy tayi tana girgiza kai, can kuma ta juyo ta kalleta 


“Minal......”


Ta kirata a hankali idonta cike da hawaye, sannan ta karaso kusa ita ta risina ta girgizata, gani take kamar bata mutu ba, ji take kamar ta tashi tayi mata magana. Hannu tasa ta shafi fuskarta zuwa kanta


“Yau na kira ki Minal baki amsa min ba, na girgiza ki baki motsa ba, kaico mutuwa! yau Minal kece a nan kwance kece a cikin wannan shigar,yau zaki kwana ba a gidan duniya ba yau zaki kwana gurin da ba gado ba katifa ba shimfiɗa yau zaki kaɗaita ke  kaɗai, shikenan bazan sake ganin ki ba ba zaki gani ba,

Wayyo Allah manzon mutuwa mai gaggauwa mutuwa mai yankan kauna lallai yau ta bakunci gidan mu yau kin tafi kin barni Minal, daman kin daɗe kina faɗamin wannan ranar kin daɗe kina jiran wannan ranar,

      Ya Allah ga yata nan Allah ka zama shaida na yafe mata duk abunda tayi min Allah ka yafe mata kurakuranta Allah ka yalwanta makwancinta Allah ka faɗaɗa mata kabarinta Alllah ka karɓi bakoncinta”


Daga nan ta faɗi zaune ta ɗora hannu saman kai tana kuka mai karfi,


“Wayyo ni Allah Wayyo Ni Salamatu farinciki na ta tafi ta barni Wayyo ni Allah na”


Da gudu matan suka shigo suka fita da ita suna bata hakuri aiko kamar suna kara mata kukan sai zo mata yake, har tasa mutane da yawa suma suka rika kukan.


     Daf da za a fita da gawarta ayi mata sallah Saif ya shiga ɗakin, Nasir kuma ya tsaya daga bakin kofa.

Yana shiga ya isa gurin da take yasa hannu ya karfi ya buɗe mata fuska, ido ya kura mata yana mata wani kallo, jin yake kamar ya kira ta ta amsa ko kuma tayi masa magana amman ina ta riga ta zama gawa! 


“Na yafe miki Minal na yafe miki duk abunda ke tsanin mu kuma zan cigaba da nema miki gafara kamar yadda kika bukata Allah ya jikanki ya yafe miki laifukan ki i love you so much Minal I love more than I did before I love you,

  Naso na rayu da ke naso na nuna miki so kin tafi lokacin da nake da bukatar ki kince kina sona taya zan gane bayan kin tafi kin barni miyasa kika barni Minal? tell why!”


Da karfi ya furta yana shishikar kuka, hakan yasa Nasir shigowa ɗakin da sauri ya rikashi ta nufin fita dashi amman ya ki suka rika ja'in ja, sai faɗin yake


“Let me talk to her I want to tell her something”


“Something like what Saif ta riga ta rasu muje waje”


“No babu inda zanje sai ta amsa min tambaya na”


Da karfi Nasir ya kira sunansa ya fisgi hannunsa wanda hakan yasa ya dawo cikin hankalinsa,

   fashewa yayi da kuka yana faɗin 


“Please Nasir kace min bata mutu ba Innalillahi wa inna ilaihirraji'un”


Rumgumesa Nasir yayi sai duk suka fashi da kukan tare.


   

         **************


Bayan anyi sallah la'asar ne, akayi mata nata sallah, manyan yan kasuwa ne da yan siyasa suka hallarci Sallah jana'izar Minal cikin su har da Alhaji Bashir Bature da Ibrahin Ahlam.

    Bayan an kare aka ɗauke zuwa gidanta na gaskiya. har aka kaita aka dawo Kairat bata san anyi ba dan zaune kawai take amman hankalinta baya jikinta kallo ɗaya zaka mata ka gane hakan. 

     Haka aka rika zuwa ana yi ma Mummy gaisuwa da waɗanda ta sani da waɗanda bata sani ba tun daga kan talakawa har masu kuɗi abunka da mutun mai jama'ah.


         ***      ***      ***


“Assalamu Alaikum Assalamu Alaikum”


Haka ta shigo falon tana sallama da kare masa kallo kamar wata bakuwa, sai da takai tsakiyar falon sannan taji an amsa mata, juyowa tayi tana kallon kofar kicin, Lubna ce tsaye fuskarta ba yabo ba fallasa 


tace,


“Ko an sallamo ku ne?”


“Eh an sallame mu tun safe kinsan yau friday anfi sallama friday da kuma monday gidan Gwaggo Muka wuce shine yanzu ta kawo ni ita kuma ta wuce gidan mutuwa, ance rasuwa akayi a gidan ko?”


“Eh Minal ta rasu”


Lubna ta faɗa tana kokarin fashewa da kuka. Ras ras ras gaban Safiyyah ya faɗi kamar yanzu ne ake sanar mata da sokon mutuwar, kasa tayi da ido kamar mai tunani, zuwa can kuma ta ɗauke kai ta kalleta


“Ina Saif.?”


“Yana can gidan tare da Momi”


Ta bata amsar tana share hawaye,


“Allah ya jikanta yayi mata rahama”


Ta faɗa kamar bata damu ba, ta nufi hanyar ɗakinta, maida kofar ɗakin tayi ta rufe bayan ta shiga sannan ta tsaya tana karema ɗakin kallo, tana wani irin murmushi na jindaɗi, daga bisa da ware hannayenta ta faɗa saman gadon tana lumshe ido,


“Mutuwar ki tayi ma Safiyyah rana AlhamdullahI Allah wani nauyin ya ragu”


Abunda ta furta kenan, taja filo ta rumgume zuciyarta ciki da nishaɗi.



WHAT NEXT? 


ina Deen?


Wane nauyi aka rage ma Safiyyah?


Ya rayuwar Mummy da Kairat zata kasance ce?


Wane irin hali Saif zai samu kansa?


Ina labarin Huda?



Plenty plenty love guys😍 ku cigaba da hakuri da ni I'm still a lazy Writer, kamar ku lazy readers da basu vote 😢 please vote and comment on every line.



BABBAN GORO 44




Har a kayi sadakan bakwai Mummy bata runtsa ba ko sau ɗaya, yadda take ganin rana haka take ganin dare gaba ɗaya bachi yayi kaura daga idonta tunanin Minal ya hanata sukuni duk ta bi ta canja ta koma wata kalar mace.

       Kairat kan abun ya zame mata biyu kewar minal ga kuma damuwar da Mummy take ciki, sai abun ya taru yayi mata tsaye musamman na Mummy da ita take gani yanzu, dan tasan Minal ta tafi inda ba zata taɓa dawowa ba. 


   Ajiyar zuciya ta sauke ta tashi daga kwancen da take ta sauko saman gadon ta nufo downstairs, a hankali take takawa har ta sauko. a kujerar dake sitting room ta hango mummy zaune ta kafe idonta da wani diary dake hannunta, karasawa Kairat tayi kusa da ita ta zauna, sai a lokacin ta lura da Album ne ba diary ba.

    hannu tasa ta karba ta buɗe cike da son sani me ke ciki. hoton farko data fara gani shine na Minal tana rumgume da Mummy tana dariya! da sauri ta rufe album ɗin tana haɗiyar yawu, Mummy ta kalleta tana murmushi mai wuyar fassara


“Kin san abunda yafi damu na?”


Kai Kairat ta girgiza idonta cike da hawaye


“Minal bata taɓa ganin Familyna ba she's always like Mummy yaushe zaki kaini na gansu, yaushe zasu zo su ganni.... na kan faɗa mata ke kaɗai ce family na Minal ke zaki sake ginani kiyi min family na zama kamar kowa yanzu kuma ta tafiyar ta.....”


Dago kai Kairat tayi ta kalleta, hawayen da ta gani a idonta sun sata farinciki, don rabon da taga hawayen Mummy tun bayan an kawar da Minal, ko bata faɗa ba tasan kukan zuci ne take wanda yafi na fili haɗari.

   kara matsowa tayi kusa da ita tasa hannu tana share mata hawaye


“Kar mutuwar Minal tasa ki karaya Mummy I believe kema zaki yi naki family kinsan Minal ta bar miki baya kuma nima ina nan, Mummy kar tunanin baya ya hana ki tunani gaba”


Kallonta Mummy tayi still tana hawaye


“Ba zan bari ya zame min ciwo ba saboda sune suka guje na suka wulakanta ni mahaifina na cikina ya kasa ya fahimce yayi min uzuri akan abunda ba da son raina aka aikata shi ba basu cancanci zama dake ba Minal sunce ba zasu karɓe ki ba...”


Jinginawa Kairat tayi da jikinta tana faɗin


“Na sani ko ba daɗe ko ba jima sai sun dawo nemanki sai sun zo gareki Mummy kuma sai sunyi nadamar abunda sukayi miki”


Rumgume ta Mummy tayi tana girgixa kai


“I don't need them”


“Yes Mummy we don't need them”


       Sun daɗe a haka kamin Kairat ta ɗago ta kalleta


“Mummy me kike so ki ci?”


“Komai bana bukatar komai....”


Bata fuska tayi ta tashi ta nufi upstairs tana kuka, da sauri Mummy ta kalleta mi kuma yasa ta kuka yanzu mi akayi mata? tashi tayi ta bita tana tambayar ba'asi,

   Har ɗaki Mummy ta bita, tana kokarin kwanta saman gado ta rikota


“Lafiya Kairat mi a'kayi?”


Batayi magana ba sai cigaba tayi da kuka, hankalin Mummy duk yabi ta tashi nan take ita ta fashe da kuka, ganin hakan yasa Kairat ta tsagaita nata kuka ta shiga share hawaye, mummy ta rika fuskarta


“Mi akayi Kairat? faɗa min”


Cikin muryar kuka tace


“Haba Mummy yaushe rabon da ki ci abinci kullum haka kike wuni inma kin ci to ruwan tea ne.

   Ya kike son naji da rayuwata Mummy? so kike kema na rasa ki wallahi idan na rasa ki mutuwa zanyi mummy ki taimaka min kar nima na faɗa wani hali...”


Hawayen dake idonta ta share tana kallon fuskar Kairat, daman can Kairat tafi damuwa da ita sama da Minal duk wani motsi da take akan idon Kairat yake kuma duk abunda tasan Mummy bata sonshi takan yi kokarin bari gudun ɓacin ranta, saɓanin Minal.

   hannayenta Mummy ta kama


“Shi kenan na daina daga yau, faɗa min ke kike so na ci?”


“Shinkafa da miya”


Ta faɗa sanin shine abinci da tafi so. rumgume ta Mummy tayi


“Okey je ki dafa min zanci kinji ki ɗaina kuka i love you”


Ta kara kankameta ta lumshe ido


“I love you too Mummy”


          ***     ***    ***


Momi na kokarin zuba abinci ta kalli Suraiya,


“Jeki kira min yayanku yazo muci abinci”


Lubna ta taɓe baki


“Momi dama kin kyale shi kinsan ko yazo ba cin abincin zai yi ba”


“Idan na kyale shi abun sai yafi haka muni”


“Ni wallahi Yaya har tausayi yake bani duk yabi ya rame ya koma kamar wani kurma daga eh sai a a kamar mai rashin lafiya”


Faɗar Lubna. Safiyyah da tun ɗazu kanta ke done taa ɗannar waya ta ɗago ta kalli momy 


“Gaskiya ya kamata a ɗaukar mishi mataki Momi abun nan fa kamar yana son taɓa kwakwalwarshi mutun kullum sai rama yake duk yabi ya canja kamanni”


Lubna ta karɓa mata,


“Gaskiya kan Momi ni har tsoro nake ji kar muje mu rasa shi dan inya zama kansa wani ciwon fa”


Tagumi Momi tayi tana sauke ajiyar zuciya,


“Nima abun yana damu na amman ya na iya baya jin magana babu lallabar da bamuyi masa ba ni da Nasir akan yayi hakuri amman yaki hakura”


“Addu'ah ya kamata ki cigaba da masa da kuma sadaka”


Lubna ta kalli Safiyyah


“Gaskiya kan wasu fa har malamai suke shiga ana yi musu rubutu dan abun ya sassauta musu dan Yayar wata friend ɗita haka tayi da mijinta ya rasu sai da kayi ta mata rubutu sannan ta samu sauki”


Momi tace 


“Toh wai ko shi za a gwada ne? muga ko Allah zaisa a dace”


Safiyyah ta aje wayar dake hannunta


“Ni kaina tuni naso yi miki wannan maganar amman kuma nayi shiru gudun kar kice nayi miki katsa landan amman gaskiya ya kamata a tashi tsaye dan abin nan baɗan ya taɓa shi ba”


Momi tayi shiru alamar nazari,


“Kiyi ma Gwaggo magana ko tasan wani dan kinga ita tasan sokoto sosai kuma tana yawan zuwa”


Kamin Momi tayi wata maganar suka shi sallamar sa, duk suka amsa masa banda safiyyah ta tayi masa kallo ɗaya ta ɗauke kai,

   kamar marar lafiya yake tafiya har ya zauna Momi kallonshi take.


   Plate ta ɗauka ta zuba masa abinci ta tura masa gabansa, kauda fuska yayi ya ɗauki ɗrinks yasha ya tashi, 


“Ba zaka ci abincin ba?”


Momi ta tambaya tana kallon sa


“Na koshi Momi”


“Ka koshi me kaci?”


Cike da takura yace


“Momi bana iya cin abu mai nauyi don't force please”


Bata ce masa komai ba ta sauke ajiyar zuciya, shi kuma  ya ɗauke kai ya fice sululu kamar marar lakka.

    Momi ma kasa cin abincin tayi ta aje spoon ďin ta dafe, tashi Safiyyah tayi ta nufi hanyar  Garden dan tasan can ya nufa.

     

    “I Love you so much Minal nasan bazan taɓa samun mata irinki ba, naso muyi rayuwa mai kyau da jindaɗi amman hakan bai samu ba i hurt you Minal i hurt you much.... No can replace your place I love more than I did before....”


Zantukan da ta tarar yana yi kenan yana murza zoben hannunsa hawaye na masa zuba,

    Wani irin juyi kanta yyi zuciyarta ta buga da karfi hawaye suka shiga mata zuba


Har yaushe zai daina tunanin wata yayi nata sai yaushe zan san da ita dake kusa dashi? Miyasa zuciyarsa ta kamu da son mugun namiji irinsa? Cikin zuciyarta take yima kanta wannan tambayar sai kuma ta juya da sauri ta nufi ɗakinta.


                     ***   ***   *** 


    Tuki take a hankali tana tunani har ta isa bakin gate ɗin gidansu. Ita kanta tasan abunda take kokarin yi ba mai yuyi ba ne sai dai zata gwada ne dan ko Allah zaisa a dace. Ta daɗe cikin motar kamin ta buɗe ta fito ta nufi harabar gidan, ko ina ta bi an aiki gaishe ta suke suna mata kallon tausayin ganin yadda duk tayi rama kuma ta koma suku-suku.


“Haba Kairat dubi yadda duk kika bi kika rame kika lalace haba Kairat ki rika sassauta ma rayuwarki mana shi fa wanda ya mutu ya riga ya tafi ba dawowa Kairat ko ke kika haifi Minal iya ka kenan”


Hajiya Suwaiba ce take mata faɗan bayan ta shiga parlour suna gaisawa. Kairat dai bata ce komai ba sai hawaye take, 


“Kiyi hakuri Kairat kinji ki barma Allah komai kinga nima bana jindaɗin gani ki haka”


  “Toh Hajiya zan yi insha Allah bari naje naga Abbah na koma kar Mummy ta tashi bachi ba ta ganni ba”


Kairat ta faɗa tana kokarin mikewa tsaye. Zainab dake zaune gefen Hajiya Suwaiba tana dannar waya ta taɓe baki tana kallon Kairat


“Mummy dai Mummy dai Yayi yar gidan Mummy ai yanzu kan dole ki zama yarta tunda Minal ta mutu yanzu ta san dake, ke kuma Mama sai ki yafe mata ita tunda ita ta haife ta”


Kallonta Kawai Kairat tayi ta ɗauke kai, Hajiya Suwaiba dai bata ce da ita komai ba tabi Kairat da kallo har ta shige part ɗin Abbah.


   

Zaune ta tararda shi sanye da glass yana duba wasu takardu dake gabansa,

  A hankali ya ɗago ya amsa mata sallamarta ya maida idonsa gurin takardun


“Ina wuni Abbah”


Tace dashi bayan ta zauna,


“Lafiya kalau ya maman naki?”


“tana lafiya”


Takardun dake gabansa ya maida gefe ya kalleta a natse yace


“Kairat kiyi hakuri da halin da kike ciki duk abinda kika ga ya samu bawa toh daga ubangijinsa yake, ki barma Allah komai kinji? Nasan kin shaku da Minal amman idan kikayi hakuri sai komai ya wuce ki rage damuwa”


Ajiyar zuciya ta sauke,


“insha Allahu Abbah zanyi hakuri, ni ba ma abunda yake damu na kamar Mummy damuwarta tafi damuna a yanzu dalilin hakan yasa nazo gurinka neman alfarma”


“Alfarma kamar ta me?”


Abbah ya tambaya, a nan ta gyara zamanta tayi kasa da idonta tana koro masa bayani,


“Abbah kasan Mummy bata taɓa yin aure ba iya tsawon rayuwar ta wanda hakan ya saka bata da zuri'ah bata da wanda take kallo taji sanyi idan ba Minal ba kuma gashi yanzu Minal ta tafi ta barta da ace tana da wasu yayan bayan minal nasan abun zaiyi mata sauki tunda tana da gimshike a rayuwarta”


“Kairat ban gane inda kika dosa ba me kike nufi ne?”


Sai da tayi hijadin haɗe yawun bakinta sannan ta cigaba


“Abbah Mummy mace ce da ko wane namiji irinka zai sota sai kuma so ta kasance matarsa Abbah dan Allah ka taimaka min ka Auri Mummy na zamo mai uwa da uba guri ɗaya kuma damuwata data mummy ta ragu....”


“What...?!”


Abbah ya tambaya a tsawace yana cire cire glass ɗin idonshi, ita kuma taja baya da sauri ta tashi tsaye tana hakki.



                   ***    *** 

SAFIYYAH..........





VOTE  AND COMMENT AS LONG AS YOU CAN




BABBAN GORO 45



Sululu ta fito ɗakin, fuskarta ba yabo ba fallasa, tana tafe tana murza yatsun hannunta har ta shiga parlour, idonta a kasa ta risina 


“Hajiya zan tafi kar Mummy ta tashi bata gan ni ba”


“Me kika je yi gurin Abbah ko Mummy ce ta aike ki?”


Kamin Hajiya tayi magana Zainab ta aika mata tambayar tana mata kallon kul. Daga duken da take ta amsa mata


“Abunda Ya take zuwa yi gurin Mahaifinta”


Zainab ta tsire baki


“Au rashin kunya zaki yi min daga tambaya Allah Mama idan baki tasar ma yarinyar nan ba irin tarbiyar Minal zata koya tunda uwar rikon su ɗaya, kinga ysrinya na kokarin min rashin kunya”


Ta karasa faɗa yana kallon Hajiya Suwaiba, ɗagowa Kairat tayi ta kalli Zainab cike da ɓacin rai


“Minal.dai bata duniyar Mummy kuma ba abokiyar wasar ki bace”


“Au iskanci zaki min tunda na taɓo uwarki ko?”


Hajiya Suwaiba ta kalleta


“Wai miyasa kike haka ne, Salamatu warin ki ce? ko da kika buɗe ido kin ganta a cikin gidan nan amman baki da marainiya sai ita!”


A tsawace take mata maganar tana hararar ta, tsire baki tayi 


“Ni wallahi bana son ta kwata-kwata tun tashi na ni rayuwarta bata min sam”


Hajiya ta watsa mata harara


“Tunda baki sonta ai sai ki kashe ta marar kunya kawai”


Ta maida dubanta ga Kairat


“Tashi kije kinji Allah yayi miki albarka ki gaida Suwaiba”


ta amsa da ‘Amin’ tana kokarin tashi.

    


      Bayan ficewarta Hajiya ta kalli Zainab tace


“Bana son abunda kike Zainab bana son halin nan naki sam miye baiwar Allah na. tayi miki ne wai ni wallahi yanzu har tausayi take bani ta koma ita kaɗai kin ɗauki karan tsana kin ɗora maka ba gaira ba dalili tunda banga abunda ta tare miki ba”


Bata fuska tayi 


“Ni wallahi bana sonta bata kwanta min a rai ta cika son kanta da yawa”


“Daga yau karki sake faɗar wata magana marar daɗi a kanta gaban Kairat tunda kinsan ba daɗi take ji ba”


“Ina kan zata jidaɗi an taɓa uwarta, duk tabi ta maida kanta wata kala akan Minal na tabbatar da itace ta mutu babu wanda zai damu”


Hajiya dai bata ce mata komai ba taja tsaki.



     Jiki ba karfi Kairat ta isa gida, tun daga parking ɗinta ma zaka gane haka dan can nesa da lot tayi shi. ta daɗe cikin motar kamin ta fito ta nufi kofar parlour. tana shigowa Mummy ta tashi tsaye tana kallonta fuskarta na nuna alamun damuwa,ganin hakan yasa Kairat ta ɓoye nata damuwar ta kirkiri murmushi


“Mummy har kin tashi”


Kai ta ɗaga mata


“Ina kikaje Kairat ? na tambayi su Talatu sunce basu san inda kikaje ba ina kika je?”


Rabon ido Kairat ta shigayi tana tunanin abunda zata ce mata, ba zata ce mata gida taje ba tunda tasan tambayar ta zatayi me taje yi? wata da barar ce ta faɗo mata, ta haɗeye yawun bakinta.


“Naje Asibiti ne gurin ganin Baby”


Mummy ta ɗan lumshe ido ta tasa leɓenta


“Yayi kyau amman idan zaki fita ki rika faɗa min kinji? bana son kina fita bada sanina ba kuma zan rika cin abinci kinji zan rage damuwa kinji?”


Ta faɗa tana taɓa fuskarta idonta cike da hawaye. jinginawa Kairat tayi da jikinta tana murmushi tasan abunda Mummy take gudu gani take kamar tafiya zatayi ta barta ta fahimce Mummy bata son tayi nisa da ita a yanzu dan ko a cikin gidan tafi son tana kusa da ita kullum.


“Mummy ki kwantar da hankalin ki babu inda zanje, ina nan tare dake a ko da yaushe”


Rumgume ta Mummy tayi tana sauke ajiyar zuciya. can Kairat ta ɗago


“Mummy baki taɓa tambayar baby ba ko dai kin manta ne?”


“Ban manta ba bana son naje ganin ta ne ta tuna min da Minal”


“Aa Mummy ai Minal ce ta dawo kinsan sunan da ya saka mata?”


“Wa?”


“Saif mana ai kullum yana zuwa dubata”


Shiru ta ɗan yi


“Wane sunan yasa ka mata?”


“Minal yasa mata kinga still minal na raye”


Mummy ta sauke ajiyar zuciya, taja hannun Kairat suka zauna saman kujera tana murmushi ta kalli Kairat tace


“Zaki iya tuna lokacin da Minal take cewa idan kuka haihu ku saka ma yayanku Minal da Kairat?”


idon Kairat ya kawo rowa, tayi murmushi mai tuna bakin ciki.


“Na tuna Mummy Har nake ce mata za a sake yin Kairat da Minal a tare”


Mummy ta ɗaga mata kai tana mayarda kukan dake son fito mata


“Ina son gobe naje naga baby”


“Okey Mummy zan kaiki insha Allah muje kici abinci”


Ta faɗa tana share hawayen da suka zubo mata.


                 ***     ***    ***


“Wai Momi yaushe za ayi bikin Lil Minal? kin fa san dole a yanka mata rago kuma Doctor yace nan da kwana goma ko sati zai sallame ta”


A hankali Saif ya ɗago ya kalleta. ita kuma tayi kamar bata san dashi cikin parlour ba tana dannar wayarta, Momi haɗa masa tea tayi murmushi tace 


“Ai dole ne wannan Allah dai ya kara mata lafiya”


“Amin Amman Momi nan za a kawo mana ita ko? dan gaskiya ba zamu yarda tayi nisa da mu ba kodan rage ma Ya Saif kewa”


Lubna ce tayi maganar tana wasa da biron dake hannunta,


“Eh kan gaskiya nima haka nake tunani sai dai kuma suma kamar ba zasu yarda ba”


Safiyyah ta kalleta


“Sai sun yarda Momi ai mun fiso karfi dan mu ɓangaren uba ne, ni wallahi ina son baby tausayi take bani gata kyakkyawa”


“Ai naga kin ɗora ta dp tayi kyau.amman Momi madara za a bata ko?”


Lubna ta tambaya,


“Ko kuma a samo mai bata nono xaifi gaskiya”


“Taf aiko abune mao wahala”


“Ba wahala tunda ga kuɗi”


Safiyyah tace


“Momi kar ma ki wahalar da kanki ni kaina zan iya shayar da ita”


“Kai kina budurwa?”


“Eh toh miye a ciki da aje a samo wanda ba asan halinta ba fa wallahi ni zan iya indai momi ta amince”


“A a ba ayi haka ba tsohuwa dai za a samo sai musa a bincika mana halinta”


shiru tayi ta cigaba da chat ɗinta.Saif dai bace komai sai shan tea yake yana nazari, yana karewa ya dire kofin ya tashi ya fice.


           ***        ***      ***


Koda Mummy ta tashi, Kairat ta gama haɗa komai na kari. bathroom ta shiga ta fito sannan ta nufo downstairs.

     A hankali take sauko tana kallon Kairat dake jeran abincin a dinning


“Morning my child”


Juyowa Kairat tayi ta kalli Mummy, ta jidaɗin yadda ta kira ta da sauri ta nufeta ta rumgume


“Morning Mummy hope kinyi bachi mai kyau jiya?”


Murmushi Mummy tayi


“Nayi me kike shirya mana ne?”


“Abunda kika fiso”


Ta faɗa tana jan hannunta suka nufi dinning ɗin,

  kujera ta ja ma mummy bayan ta zauna ta shiga zuba mata abincin. ci mummy ta rikayi ba dan tana so ba sai dan ganin yadda Kairat ɗin ta saka mata abincin a gaba ta zuba mata ido.

   Sai da Kairat ta tabbatar Mummy ta koshi sannan ta zuba ma kanta ta shiga ci sama-sama dan itama ba son abincin take ba, sai da ta kusa koshi ta ɗago kai ta kalli Mummy


“Mummy kije ki shirya kar rana tayi dan nafu son muje lokacin da Dr. Humaira take duty koda wani abun da wani bayanin da zata mana”


Shiru tayi, tayi kamar ba taji abinda Kairat tace ba. ganin gakan yasa Kairat ta kira ta


“Mummy”


Kallonta tayi da ɗan damuwa a fuskarta


“Kairat Me zai hana mu bari har wani lokacin tun yanzu kinga ai rana tayi”


Fork ɗin take hannunta ta aje ta kama hannun Mummy tana magana a hankali


“Mummy ki daina damuwa komai mai wuce ne kamar ba ayi ba, nasan abinda kike tunani ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru insha Allah”


Kai kawai Mummy ta ɗaga mata ta tashi ta nufi ɗakinta


“Mummy ki fa shirya dan ni na shirya tufafi kawai zan saka”


Daf da zata shige ɗakin Kairat tayi mata maganar, bata ce mata komai ba ta shige abinta.


      Sai shaɗaya har da wani abu sannan Mummy ta shirya, basu bar gidan ba sai kusan shabiyu da rabi. Suna isa suka wuce gurin Doctor Isma'il (Dr dake duba Minal) da far'ah ya tare su yana na'am na'am da Mummy da kanshi yaja mata kujera ta zauna ta bude fijin ya ɗauko mata lemo ya zuba mata yana janta da yar fira, sam ya manta da Kairat take tsaye tana ɗan watsa masa harara, ta Mummy kawai yake yana mata maganganu game da rayuwar duniya, Mummy dai in banda Murmushi da girgiza kai babu abinda take.


“Mummy tashi muje kar Dr Humaira ta fita ba mu ganta ba”


Ta faɗa da ɗan jin haushi ganin firar tasa ba mai karewa bace, Mummy ta juyo ta kalleta zatayi magana ya riga ta


“Kije kawai Kairat sai na kaita ta duba ta”


Tsaye ta ɗanyi kamar ta masa tirjiya sai kuma ta juya ta fice cike da jin haushi.

   tana tafe tana kalle-kalle ta ɗan tunani cikin ranta har ta shiga gurin, daf da zaka karasa gurin Baby ta hango Nasir yana ɗaukar Baby hoto da sauri ta juyo da nufin fita dan bata son ya ganta,sai kawai taji tayi kwara da mutum.

   Dagowa tayi da sauri ta kalli Saif dake shirin yi mata magana ganin ita ce yasa yayi shiru yana kallonta,


“Karaso mana Kairat kina kokarin gudu kamar kinga Mayu!”


Nasir ya faɗa still yana ɗaukar hoton, gabanta ne ya ɗan faɗi _Ashe ya ganni_ ta faɗa a ranta sannan ta juyo kamar munafuka ta isa gurin Baby,


“Sannu Kairat ya gida ya karin hakuri?”


“Lafiya kalau Hakuri mun gode Allah”


Ta amsa kamar mai jin kunya, 


“Kaga Dr Humaira?”


Ta tambaya tana ɗan leki Babyn. sai a lokacin ya kalleta


“Dr tace nan da yan kwanaki zata sallame ta dan haka mu samu mai shayar da ita dan ruwan nono zaifi inganta jikinta saman da komai”


Kai ta da ɗaga


“Wannan ba matsala bane zan iya shayar da ita”


Nasir yayi mata wani kallo,


“Zaki iya Kairat budurwa face ke?”


“Toh miye a ciki ba yata bace sai miye dan ina budurwa?”


Saif ya nufo su yana faɗin


“Safiyyah ma tace zata iya i think...”


“You think what?!”


Ta faɗa kamar a tsawace tana kallon Saif daya karaso gurin kamar a kasale,


“Babu wanda zai shayar da ita sai ni ni zan shayar da yata okey”


Saif dai bace mata komai ba ya kalli Nasir, Nasir ya kalleshi, tana ganin hakan ya juya fuuu ta bar ɗakin.


    Bata daɗe ba sai gata ta shigo ɗakin tare da Mummy da Dr isma'il.da Dr Humaira,  cikin ladabi Nasir da Saif suka gaida Mummy sannan suka gaisa da Dr isma'il, daker Mummy ta iya ɗaga idonta ta kai dubanta ga Baby, wani irin faɗuwa gabanta yayi ta daɗe tana kallon baby kamin ta kauda idonta da suka cika da hawaye. Kairat ta kalli Dr Humaira


“Dr nice wanda zan shayar da baby i....”


Nasir ya tari numfashinta


“Dr budurwa ce”


Dr tayi murmushi


“Budurwa ce bazara ce tsohuwa ce wannan duk ba matsala bane ni zan rubuta mata magnin da zata sha ruwan nononta ya kawo da kuma abubuwan da za ci”


Mummy ta girgiza kai 


“A a Kairat ba zan barki kiyi hakan ba ke budurwace”


“Yes ni budurwa ce Mummy amman ba budurci na zan zubar ba ba mutunci na zan yaga ba shayarda ita ne kawai zanyi na kuma kula da ita kamar yadda Minal ta bukata”


Ajiyar zuciya Saif ya sauke ya ce


“Wannan ba matsala bane Safiyyah ma tace zata iya babu wani damuwa game da wannan”


“Wace irinnSafiyyah wai?”


Kairat ta nufo shi da masifa


“Idan har Safiyyah zata shayar da ita toh babu wanda ya dace ya shayar da ita sai ni dan babu abinda ta haɗa da Safiyyah Safiyyah ba zata shayar da yata ba i won't allow it”


“Safiyyah yar uwata ce Kairat wannan babyn kuma yata ce dan haka Safiyyah na da alaka da ita”


Ido ta tsura masa kamar mai karantar abu a fuskarsa sannan ta juyo gurin Mummy


“Mummy karki juya min baya karki bar wani ya shayar da ita sai ni please mummy”


“No Kairat ba zanyi miki haka ba”


Mummy ta faɗa tana jan hannunta. a nan Kairat ta fashe da kuka ta durkushe a gurin.

  Dr. Isma'il ya kalli Mummy yace


“Gaskiya duk kika hana Kairat shayar da yarinyar nan baki mata adalci ba a ganina babu wanda ta dace ta shayar da ita irin Kairat ko dan ke ki rika ganinta kusa da ke kuma itama Kairat ɗin ta samu sassauci”


Saif zaiyi magana Nasir ya rike hannunsa ya rigashi


“Babu komai in dai ta ɓangaren mu ne mun amince Kairat ta shayar da ita”


Baki Sake Saif ya kalli Nasir da mugun mamaki, sai dai ba damar ya musa ma amininsa a gaban wasu sai kawai ya fisge hannunsa daga rikon da Nasir ya masa ya fice daga ɗakin.

    Sai a lokacin Kairat ta tashi tana share hawayenta tana kallon Mummy dake hawayen. Nasir yayi fuskar zolaya yana kallonta


“Shi kenan daga magana sai ki faɗi kina kuka kamar wata yarinya, har da zuwa ki kira Mummy dan ta shigar miki ko?”


Harara ta ɗan watsa masa


“Toh ai bata shigar min ba”


Mummy tayi murmushi tana share hawayenta. sun ɗan daɗe a ɗakin kamin daga bisani Kairat tabi Dr Humaira office ɗinta ta rubuta mata maganin da zaisa ruwan nononta yayi saurin kawowa ta kuma faɗa mata abubuwan da zata rika ci wanda zai karawa ruwan nonon inganci.


      Saif na zaune parlour ya haɗe rai sosai sai kwafa yake, Momi dai kallonsa kawai take tana mamakin abunda yasa shi yin hakan. Nasir na turo kofar parlour yayi cikinsa da matsifa daman shi yake jira.


“Saboda me zaka min haka Nasir ko an faɗa maka ni bana son kaina ne ko bana sonta ai saboda ina son kusance na da ita yasa nake son a kawo ta a nan gidan a shayar da ita”


Dafa shi Nasir yayi


“Weather you like it or not Kairat ce tafi dacewa ta shayar da yarinyar nan kodan Mummy”


Ya buge masa hannu


“Na nesa da kai ka sani ba kasan na kusa da kai ba, toh ka koma ka faɗa musu ka canja shawara a nan gidan za a shayar da ita”


A nan Momi ta tambaya


“Wai meke faruwa ne?”


Nasir ne yayi mata bayanin komai, Safiyyah dake taɓe ta fito tana murmushi


“Oh Ya Saif daman saboda wannan ne kake ta fushi na na ɗauka ma wani abun ne daban wannan ba matsala bane Yaya da ni da Kairat duk ɗaya muke yadda kaƙe ganin nan gidan ka ne can ma gidan ka ne zaka iya zuwa ka wuni can zaka iya ɗauko yarka kazo nan da ita tun da dai shayar da ita ne kawai Kairat zatayi”


Ka rasasa zancen daidai lokacin da ta karaso kusa dashi, a nan Momi tasa baki


“Haka ne kuma kaga idan aka yayeta ko kuma ta ɗanyi wayo zaka iya maiɗota nan a ciki gaba da bata madara”


Safiyyah tace


“Idan ma hakan baiyi maka ba Yay zaka iya rokon Mummy akan ta bar Kairat ta dawo nan gidan dan Baby kawai nasan Mummy zata yarda dan bata cika matsala ba”


Ajiyar zuciya ya sauke ya zauna saman kujera yana nazarin maganganun. A hankali Safiyyah ta kai dubanta gurin Nsir da ya kafe ta da ido yana mata wani wawan kallo, suna haɗa ido tayi saurin kawar da nata idon ta nufi ɗakinta.


  Tana shiga ɗakinta ta maida kofar ta kulle tana safa da marwa, can ta nufi wyarta ta ɗauka ta nanna kira bugu biyu aka ɗauka cikin sauri tace


“Hello Shafa kina ina?............”




             ***         ***         ***


Saif kwana yayi yana nazarin maganar Safiyyah, daga karshe dai ya yanke shawarar zuwa ya samu mummy da maganar Kairat ɗin ta dawo gidan su da zama ɗin dan shi dai baya son yayi nisa da LIL MINAL kamar yadda yake kiranta.




    Safiyyah ce zaune a parlour su Shafa tana labarta mata halin da take ciki, Shafa ta kalleta 


“Amman Safiyyah miyasa kika bashi shawarar ya bar ta acan a shayar da ita beside miyasa ma kike son shayar da ita?”


glass cup ɗin dake hannunta ta ajeye 


“Saboda shi da Momi su yarda da gaske nayi nadama kuma na cire Saif zuciyata su yarda ina son abunda Minal ta haifa, abunda yas nake son shayar da ita saboda a yanzu babu abunda Momi da Saif suke.so kamar wannan yarinyar idan ina shayar da ita dole zai rika kula da ni zai rika tausayina kuma zai ga girma na yace ya shayar da yarsa ta hakan zan samu kansa har sona ya shiga zuciyarsa”


Kai Shafa ta ɗaga alamar gamsuwa sannan tace


“Toh yanzu ya kike so muyi da maganar Kairat?”


“So nake kije gidan iyayenta da suka haife ta ki faɗa musu tana nan ta shirya shan magani dan ta ba yar Minal nono nasan ba zasu yarda ba tunda budurwa ce ba ta taɓa aure daga haka nasan yar zata dawo daga gareni ni bazani ba tunda sunsan fuskata”


Kalkalewa Shafa tayi da dariya tana bugun kafaɗar Safiyyah 


“Shegiya kawata baki da kyau”


Safiyyah ta kalleta


“Hmmm ai kowa yaci tuwo dani miya yasha”


      

           ***         ***         ***


Yadda suka tsara haka kuwa sukayi Shafa ita ta shirya da kanta ta shiga motar ta ta ɗauki hanyar gidan Ibrahim Ahlam.

   Bata sha wahala gurin shiga ba dan masu gadin kallo ɗaya sukayi mata ganin ba yar kananan mutane bace suka buɗe mata gate, a natse tayi parking ta fito ta nufi cikin gidan,

   Cikin sa'ah ta tarar da Hajiya Suwaiba zaune parlour ta ita kaɗai, guri ta samu ta zauna bayan anyi mata iso, sannan ya gaishe ta cike da ladabi, da far'ah Hajiya ta amsa tana faɗin


“Ban gane ki ba”


“Eh ba zaki gane ni ba saboda baki san ni ba amman nazo miki da maganar ne mi muhimmaci”


Hajiya ta gyara zama


“Wace magana nace haka?”


“Nasan baki san Kairat tana shan maganin kowowar ruwan nono ba dan ta shayar da yar da Minal ta bari, idan kuma har kin sani kika kyale ta to gaskiya kinyi kuskure dan Kairat budurwa ce ba matar aure ba hakan zaisa duk namijin da zai aureta ya rika mata wani kallo, gaskiya ku canja shawara ku samu wata ku biyata tayi muku wannan aikin ba Kairat ba”


Tana kai aya Hajiya ta kalleta ta mugun mamaki tace 


“Wallahi bata faɗa min ba ban ma san me ake ciki ba taya zan yarda Kairat tayi haka”


Shafa ta tashi tsaye tana faɗin


“Zaki iya kiranta ki tambaye ta dan nasan ba zata ɓoye miki ba sai an jima”


Bata jira abunda Hajiya zata ce ba ta juya da sauri ta fice daga parlour. Hajiya da kallo ta bita tana mamakin maganar. kasa natsuwa tayi sai nazarin maganar take wata zuciyar nace mata karya ne can dai ta tashi ta nufi part ɗin Abbah.

   Cikin sa'ah ta tarar ya tashi daga bachin da yake yana zaune rike da carbi da aƙlama lazimi yake. Sai da ta jira ya shafa sannan tace 


“Har ka tashi a she”


“Eh tun ɗazu”


Ya faɗa yana kallonta dan yasan bakinta da magana, tashi tayi


“Bari na kawo maka abinci”


“A a zauna tukuna naga bakin ki da magana ya akeyi.?”


Ajiyar zuciya ta sauke ta shiga kura masa bayani. Kai Abbah ya gingina yana murmushi


“Kairat tana da tunani da hangen nesa yarinya ce mai kaifi basira, tun a bukatar da ta farko na gane hakan”


Hajiya ta kalleshi


“Haba Alhaji budurwa fa ce ba zaura ba ina zan yarda da hakan sam ba zan barta ta aikata wanna kwaɓa ba”


Abbah yayi yar dariya


“Haka zaki gani zaki ga kamar tana shirme amman daga baya zaki gane tana da tunani dan nima haka nayi lokacin da tazo min da zancen Auren Salamatu...!”


Abbah bai ko kai aya ba Hajiya ta daki kirji ta tashi tsaye tana zaro ido,


“Na shiga uku ni suwaiba Kairat ce tace maka ka auri Salamatu? anya Kairat cikin hankalinta take kuwa inna illahi”


Abbah yayi mata wani kallo


“Miye na ɗaga murya haka daga magana Salamatu ce fa sai kace wata bakuwar ki”


“Toh in salamatu ce fa ai daman nasan daga kai Har Kairat ɗin ba banza ta barku ba tun da kurciya ba ayi abu ba yanzu za ayi oh wato ta kwace min miji ta lalata min rayuwar ya ko? tunda ita bata da makoma Toh Wallahi ba zan yarda ba”


Haka ta rika matsifa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, Abbah dai in banda kallonta babu abinda yake har ta gama bururutan ta, ta fice.


         ***         ***        ***

Mummy na cikin bachi ta rika jin hayani ni tun tana ɗaukar mafarki ne har ta farka taga da gaske hayaniya ce ake ko kuma nace faɗa, jin kamar muryar Hajiya Suwaiba yasa tayi saurin saukowa downstairs. Tana kawowa Hajiya ta nuna da yatsa tana hantarar fuska


“Ke kuma munafuka macuciya daga yau sai yau babu ke babu yata bari mijina azzaluma dan kinga baki da makoma ko shiyasa kike son ɓata tawa rayuwar ko wato ki malleke min miji yata kuma ki lalata mata rayuwa to kinyi ƙkaɗan, ni ban taɓa tunani zaki aikata abunda kika aikata ba wallahi”


Ta juyo kan Kairat dake kuka


“Ke kuma kinji na faɗa miki ki haɗa duk abinda kika san naki ne ki bar gidan nan ina xaune na aka zo aka faɗa min komai dan haka ki bar nan gidan tun wuri”


“Haba Hajiya Mummy fa uwata taya zatayi abunda zai lalata min rayuwa ? ba itace tasa ni ba nice nasa kai na”


Kairat ta faɗa cikin kuka,


Hajiya ta hantareta ta hannu


“Aikan ba uwarki bace tun da tayi nufin ɓata miki rayuwa babu ke babu ita daga yau nice uwarƙki nina haife ki”


“Ita kuma ita ta raine ni Hajiya tun ina karama a hannunta na tashi”


Hajiya ta saki baki


“Laaaaa ashe da gaskiyar Zainab au haka ta koya miki ki bata muhimmaci sama da ni dana haife ki?”


  Dr.Salamatu da tun ɗazu kallonsu take ta karaso kusa da Hajiya tana faɗin


“Wai me yake faruwa ne ni ban gane kan wannan maganar da kuke ba?”


Hajiya ta watsa mata harara,


“Kin fi kowa sani tun da ke kike shirya komai ni nayi mamakin abunda kike kokarin wallahi wai har ki yarda Kairat tasha maganin nono bayan kinsan budurwa ce koda yake banga laifin ki ba tunda ba Minal bace ai ita tattalinta kike da yake ita ce yar ki Ke kuma na faɗa miki ki haɗa kayanki ki dawo gida in har ba so kike duniya ta juya miki baya ba”


Tana kaiwa nan ya juya a fusace ta fice. Mummy ta kalli Kairat 


“Kin gani ko ɗaya daga cikin illar da nake gudu kenan kinga tun ba a kai ko ina ba mun fara ko?”


“Ba haka bane Mummy kishi ne ya rufe mata ido kuma nasan zata sauko”


Kairat ta faɗa tana share hawayenta Mummy tace


“Kishi kamar ya?”


“Saboda naje na Samu Abbah da maganar ya aure ki shine take ganin kamar ƙkece kika tura ni”


Tassssssss! Mummy ta watsa mata mari idonta jawur tace


“Fita ki bar min gida”


Dafe kunci Kairat tayi kamin ta juya da gudu ta nufi Garden. 

Tsugunawa tayi gurin tayi ta kuka, sai da tayi mai isar ta sannan ta tashi ta shiga cikin gidan ta ɗauki key ɗin motar ta ta fice daga gidan.


              ***       ***       ***


Ko da Saif ya shigo ya tararda Mummy zaune a parlour jugummm kamar marar lafiya ta tsura ma tv ido duk da hankalinta ba a nan yake ba,

   Sai da yayi sallama kusan uku sannan ta ɗago ta kalleshi ta amsa mushi ciki-ciki, bayan sun gaisa ya koro mata bayani akan kudurinsa.

      Mummy ta kallesa A hankalce ta soma magana,


“Saif ba zan yarda Kairat ta koma gidan ku da zama ba, Kairat ba Muharrar ka bace komai zai iya faruwa idan har hakan kake so zaka iya auren Kairat dan ta zama mallakinka kaga ita da yarka duk suna karkashin ikon ka da kulawarka, 

   A halin yanzu Kairat ta canja shawara ba zata shayar da Yarka ba ɗan haka sai ka nemo mai shayar da ita”


Mummy na kaiwa nan ta tashi ta shige ɗakinta, Saif ya bita da kallon na rashin fahimta da kuma mamakin maganarta.

  Kamar haɗin baki wayarsa tayi kara yana duba yaga number Kairat kamar kar yayi picking sai kuma ya ɗauka 


“Saif kazo ka same ni ina Happy Island”


Tana faɗar hakan ta kashe wayar. 


      Yana tuki yana tunanin lokacin da Minal take faɗa masa tafison zuwa Happy Island idan tana cikin ɓacin rai saboda guri ne da babu ruwa kowa da kowa ga iska yana kaɗawa babu wanda zai dame ka kayi kukan ka har ƙa gaji babu takura.


    Yana yin parking ya hango ta tsaye jikin icce rumgume da hannayenta, ya ɗan daɗe yana kallonta sannan ya karasa kusa da ita, bata jira ya mata magana ba ya ta juyo ta kalleshi idon ta cike da hawaye tace,


“Ka faɗa ma Safiyyah ta fita hanya ta, ni ba irin Minal bace ta kama gabanta kar kuma ta sake taka kafa taje gidan mu dan nasan ita kaɗai ce zatayi wannan kule-kulen tun da Hajiya tace zuwa akayi aka faɗa mata Wallahi idan bata fita hanya ta ba zata san wacece ni!”


“Kaiyrat .....”


Bata amsa mishi ba ba ta kuma tsaya saurarensa ba ta nufi gurin motar ta.

    Kamar walkiya, Saif ya iso gida cikin fushi ya tura kofar parlour ya shiga. duk suna zaune parlour har Momi kai tsaye ya nufo Safiyyah yana faɗin


“Me kika je yi gidan su Kairat?”


Zabura tayi dan a tsawace ya tambayeta gashi ya nufo ta kamar xai dake ta,

Cikin rawar Murya tace


“Wace Kairat kuma miye haɗina da Kairat da zanje gidan su?”


D sauri Momi ta tashi ta shiga tsakanin su ganin yadda yanayin Saif ya canja tan tambayar abunda ya faru, daker ya ita faɗa mata abunda Kairat ta faɗa masa. a nan Safiyyah tasa kuka tana rantsuwa


“Wallahi wallahi ban je gidan su Kairat ba mi zai sa naje nayi haka wallahi ban taɓa zuwa gidan ba idan har na taɓa taka kafata zuwa gidan su Kairat kada Allah yayi min rahama”


Tana kaiwa nan ta nufi ɗaki tana kuka. Momi ta kalleshi 


“Saif batayi ba tun da kaji tayi wannan rantsuwar akwai dai ko wanene amman ba ita bace Safiyyah ta canja yanzu”


Zaunawa Saif yayi saman kujeara yana sauke ajiyar zuciya.


              ***     ***     *** 


Tun da uwar Safiya Talatu take safa da marwa daga bakin gate zuwa ɗakin Mummy saboda wani tsoho da ya takura sai yaga Mummy,  wannan karon tana shigowa Mummy ta katsa mata tsawa


“Wai Talatu akwai wasa tsakanin mu ne na faɗa miki bana bukatar ganin kowa a yanzu kije ki faɗa mishi bana da damar ganinsa ko wanene”


Talatu jiki na rawa tace


“Wallahi Hajiya shine ya matsa har da kukansa kuma yace yana tafe da magane mai muhimmaci Hajiya da kin saurare shi ko kaɗan ne dantijo ne”


Mummy ta daɗe kamin ta bata amsa


“Je kice ya shigo parlour”


Da sauri ta tashi ta fice, mummy kuma ta tashi ta shiga bathroom tayi wanka tana fito bata ko shafa mai ba ta saka tufafinta dan bata jin zata iya shafa man, ta ɗauki katon hijab tasa ta nufo downstairs dan tun tana bathroom Talatu ta faɗa mata mutumen ya shigo,


  “Ina yake?”


Mummy ta tambaya tana kallon talatu dan ita bata ga kowa a parlour ba, Nuna mata shi talatu tayi 


“Gaya a can”


Nuna shi da Talatu tayi yasa ya taso ya nufo mummy idonsa cike da hawaye, da rawar murya ya kira sunanta


“Sala...ma..tu...”


Yana kiran sunan nata ta watsa masa mari ta sake watsa masa mari, bai yi unkurin hana ta ba har ta wanke masa fuska da mari takwas masu kyau. sannan ta nuna masa kofar fita da yatsa dan bata iya masa magana.




WAI INA DEEN NE?


INA LABARIN HUDA?


ME ZAKU CE AKAN WANNAN DOGON PAGE? 


ME KUKA HANGO ZAI FARU A GABA?


PLEASE VOTE VOTE VOTE AND COMMENT ON EVERY LINE.



46


Wannan Shafin Sadaukarwa Ce Gare Ki FEENAH BABY




Hawaye ne suka gangaro daga idon dattijon, ya kalli Mummy da fuskar tausayi ya ce


“Kiyi min ko wane irin hukunci Salamatu na cancanci ko wane irin hulakanci daga gare ki amman ina son ki saurare ni ki kuma....”


Bai karasa ba Mummy ta ɗaga masa hannu har lokacin batayi magana ba ta nuna masa kofa, a maimakon ya juya ya fita sai kawai ya faɗi zaune yana kuka


“Dan Allah ki saurare ni nasan ni mai laifi ne amman kiyi ma girman Allah ki saurare ni”


Sai a lokacin Mummy tayi masa magana da jan ido,


“Sauraren tsawar bakin hadari yafi min saurarenka ganin mutuwa ta yafi min ganin ka, ka fice daga gidan nan tun kamin na kashe ka!”


Kallo ɗaya zaka yi fuskata ka tabbatar da furucin dake fita daga bakinta har cikin zuciyarta yake, shi kuma ya wani marairaice ya koma abun tausayi sai kuka yake yana kokarin rika kafarta


“Ki kashe ni Salamatu matukar kashe ni zai sa ki sassauta min wallahi a shirye nake na mika miki rayuwa ta Salamatu dan Allah ki saurare ni”


“Wallahi ko zan  kashe ka ka sake rai na sake kashe ka ka sake rai na sake kashe ka bazan sassauta maka ba dan haka ka fice min daga gida”


Kuka yake sosai kuka mai ban tausayi, 


“Dan Allah ki saurare ni Salamatu ko dan yar mu....!”


“Y'a ....”


Mummy ta ɗan ja baya tana mishi wani kallo da ba zan iya fassara shi ba, shi dai ba kallon mamaki ba, kuma ba kallon tsoro ba, ba kuma kallon tausayi ba.


“Kai baka ji kunyar furta wannan kalamin daga bakin ka ba? ashe kasan kana da Y'a lallai rashin kunyar ka da yawa yake” 


Mummy ta kalli Talatu tun ɗazu take tsaye tana kallon ikon Allah


“Ki ra min Sani da Mu'azu”


Cikin sauri ta juya ta fita, bata daɗe ba tadawo tare da su ko wanne sai kallon Dattijon yake da alama ta  labarta musu gulmar. Mummy ta nuna musu shi


“Kun ga fuskarsa kun ga kamaninsa?”


Duk suka ce Eh har talatu, Sani ne ya duka yana kallonsa dan kara tabbatar da kamanin nasa.


“Ku fitar min da shi kuma karku sake bari ya shigo min gida duk kuka barshi ya shigo min gida a bakin aikin ku!”


Kallonta sukayi suka sake kallonta jin furucinta sannan suka shiga kokarin mikar dashi tsaye. 


“Idan ke ba zaki saurare ni ba toh ki sadani da Y'a ta, dan Allah ki nuna min ita”


Ya faɗa cikin kuka yana kara zubewa. Hannu Mummy ta ɗaga musu alamar su rabu da shi ta nufi upstairs tana faɗin


“Biyo ni na nuna maka Y'ar ka”


Cike da kwarin guiwa ya tashi ya rufe mata baya har suka shiga ɗakin Minal. Mummy sai da ta kai tsakiyar ɗakin sannan ta juyo ta kalleshi ta nuna masa pictures ɗinta


“Ka ganta nan, gaka tufafin nan, kaga takalminta nan, ga gadonta can da kayan kwaliyarta”


Duk abunda ta nuna masa kallo yake dan shi sam bai gane inda ta dosa ba, can ya ɗaga kai yana kallon hotunan nata,

Wani gurin tana tare da Mummy wani gurin da Kairat wani da Yan makarantar su wani kuma da Deen sai wanda sukayi da abokanta na kasar waje da kuma wanda tayi tare da Mummy da Kairat. Tabbas yarsa ce dan babu abunda ta rage a kamaninsa wani kallo ya bi ɗakin da shi wanda zan iya cewa na farin ciki ne da kuma jindaɗi.


“Ina take.?” 


Ya tambaya yana kallon Mummy idonsa na zubar da hawaye.

Mummy kamar mai jira a take ta bashi amsa,


“Ta tafi inda zaka je zanje mu tsayu da ni da kai da ita a gaban mahalincin mu ayi mana hisabi na jidaɗin da ba kayi ido biyu da ita ba na jidaɗin da bata raye bata ga wulakantaccen uban ta ba!”


Nan take kalarsa ta canja hawayen da ke masa zuba suka tsaya, ya saka hannunsa ya dafe gefen zuciyarsa ya faɗi zaune yana kallon tile ɗin ɗakin  kamar wanda bai san inda yake ba.

Mummy ta kwala ma Sani kira, yana shigowa ta nuna masa shi.


“Ku fitar min da shi karku sake bari ya shigo min gida”


“Toh Hajiya”


Da sauri ya duka ya shiga kokarin tayar da Dattijon tsaye, daker ya tashi tsaye har lokacin yana dafe da zuciyarsa ya rika tafiya a hankali sani na ruke dashi har suka sauka downstairs.

       faɗuwa Mummy tayi zaune ta kai hannunta gurin takalmin Minal taja ɗaya ta rumgume ta fashe da wani irin kuka muryarta har rawa take.


                         ***             ***             ***


A hankali Kairat take driving, har ta isa gidansu, bayan tayi parking taja gyalenta ta share hawayen da suka zubo mata sannan ta fito ta nufi cikin gidan. Babu kowa farlon hakan yasa ta nufi ɗakin Hajiya. tun kamin ta karasa take jin shesshekar kukan Hajiya, ta daɗe bakin kofar sannan ta kai hannu ta tura kofar a hankali.

     Unkurin ɓoye kukanta Hajiya tayi ta maida fuskarta gefe tana share hawaye. Kairat ta karasa kusa da ita ta risina ta ɗora hannayenta saman guiwoyin Hajiya


“Ga ni Hajiya gani na dawo”


Bayan ya gama share hawayen nata ta juyo ta kalli Kairat


“Ai kara da kika dawo ba zaki sake zama can gidan ba”


A hankali Kairat ta soma magana


“Hajiya yanzu idan na mutu ya zaki ji?”


Wani kallo tayi mata


“Wace irin magana ce wannan?”


“Hajiya ki auna ki gani yanzu idan na mutu ya zaki ji. naga ke baki shaku da ni kamar yadda Mummy ta shaku da ni ba a hannunta na tashi tun ina karama ita tayi ta ɗawainiya da ni har na kawo a inda nake yanzu rana tsaka sai kika ce zaki raba mu bayan mun shaku da juna kuma ni kaɗaice farincikin ta a yanzu shin idan kece ya zaki ji?”


Shiru Hajiya ta ɗanyi kamin ta kalli Kairat


“Toh saboda me zata sa kije gurin Abban ku kice ya aure ta wane irin halacci ne ba muyi mata ba!”


Tashi Kairat tayi tsaye, ta zauna kusa da ita ta yadda zata fuskance ta.


“Hajiya na tabbatar zuciya ce a kirjin ki Hajiya ba ko taɓa tausayin Mummy ba? ba ki taɓa mata fata na ta sake samun wasu yayan ba? Mummy bata taɓa yi ma Abbah kallon so ba kullum a uba take ganin shi bata taɓa sha'awar auren mijinki ba tun zaman ta gidan nan bata taɓa cin amanar wani ba baki taɓa jin ance an ganta da wani ba,

  Duk da hakan zuciyarki bata yi sha'awar ta kasance abokiyar zaman ki ba? Wallahil azim Hajiya Mummy ba ita ta tura ni tasa nayi ma Abbah magana ba nice naga dacewar hakan kuma nayi masa bata sam da wannan maganar ba sai yau sanadin haka yasa tayi min wannan marin”


Ta nuna ma hajiya gefen fuskarta gurin da yatsun Mummy suka kwanta mata a kunci. ido Hajiya ta tsura mata tana kallonta kamar mai karantar abu a fuskarta. zuwa can ta ɗauke kai ta sauke ajiyar zuciya. Kairat ta rika hannunta


“Na sani Hajiya Mummy ba zata taɓa yarda ta auru Abbah ba. saboda halaccin ta ki kwantar da hankalinki aure ba zai taɓa shiga tsakanin Mummy da Abbah ba”


Hajiya dao bata ce mata komai ba, hawayen dake makkale a idonta suka zubo mata a nan ta dantse bakinta. Sun daɗe a haka ganin bata da niyar magana yasa Kairat ta tashi. har ta kai bakin kofa sai kuma ta juyo ta ta kalleta daga gun da take da duka kasa ta haɗe hannayenta kamar mai neman gafara tana hawaye tace


“Na haɗa ki da girman Allah Hajiya karki hana ni shayar da Lil Minal, Hajiya ko da Minal na raye ni mai iya shayar  da Y'arta ce balle bata raye, Kullum Minal tana faɗa har a gaban ki cewar idan ta haihu ni zan raini yarta dan Allah Hajiya karki hana ni yin wannan shi ne farin ciki ne”


Har lokacin Hajiya bace mata komai ba sai hawaye take. Kairat ma bata sake cewa wani abun ba ta tashi jiki ba gwari ta fice.


          

                       ***                  ***                   ***


Nasir ya sauke ajiyar zuciya tare da shafa kansa,


“Toh kai yanzu ya kake ganin za'ayi?”


“Ya za'ayi ban da a kyale ta in yaso sai Safiyyah ta shayar da ita”


“No”


Nasir ya girgiza kai


“Ni kaina ban yarda Safiyyah ta shayar da ita ba Kairat ce ta cancanta ta shayar da ita kuma na tabbata da ta samu damar yin wasiya da sai ta faɗi haka”


Shiru Saif yayi yayi ma bakins wani abu alamar damuwa


“marry her and make her happy shi ne abunda Minal ta faɗa min lokacin da zata rasu tace min ka auri Kairat dan ku kula min da abunda zan bari that's mean na bar Kairat ta kula da yarta but the problem is ita ta ki aminta”


Nasir ya tari numfashinsa


“Wannan ba hujja bace kamata ƴyayi ka lallaɓa ta baka san dalilinta ba tun da kaga abun ya kai har gurin iyayenta”


Saif ya kalleshi 


“Lallaɓa ta? karamar yarinya ce da zan lallaɓa ta”


“Ba a haka Saif yarinyar yar ka ce bai kamata ka nuna halin ko in kula ba beside ni wallahi Kairat ɗin nan har tausayi take bani yarinya ce mai hakuri da hangen nesa ta raba hankalinta gida biyu ni ina ganin ma ta wannan hanyar zaka iya cika burin ka ka kuma cika wasiyar Minal”


Kai  Saif ya gyaɗa


“I'm not ready yet”


Nasir zaiyi magana wayar Saif tayi kara, ganin number Abbah yasa shi saurin ɗauka,


“Hello. okey gani nan zuwa”


Shine kawai abunda ya faɗa ya kashe wayar ya kalli Nasir


“Daddy na nema na”


“Ok muje kaji kiran nasa sai muje gidan su Kairat ɗin”


Tashi sukayi tare suka shi ya nufi part ɗin Daddy Nasir kuma ya nufi parlour Mummy.


   Da sallama ya shiga. bayan ya samu guri ya zauna ya kalli Daddy yace 


“Gani Dad”


Sai da ya gama duba jaridar dake gabansa sannan ya ɗago ya kalli Saif.


“Akan maganar Huda ne ko ɗazu sai da Mahaifinta yazo gidan nan, ya faɗa min ko abinci bata iya ci a yanzu ta koma wata kalar mace su kansu yanzu abun ya dame su”


“Toh ya za'ayi da Kaddara tayi hakuri kawai haka Allah yaso”


“Ba haka naso ji daga bakin ka ba Saifullahi ya kamata ace a yanzu ka duba mata nasan iya nadama yanzu tayi ta kuma kaga ko dan yawon da mahaifinta yake a gidan nan ya kamata ka mutun ta shi”


Bakinsa ya cika ma iska


“Dad ni fa ban gane ma maganar ka ba wannan zirga-zirgar da mahaifinta yake yi ban ga amfaninsa ba kai ma sai naga kamar kana manta babu aure tsakani na da Huda”


“Akwai aure tsakanin ku mana ba saki biyu ka yi mata ba?”


“Biyu nayi mata a yanzu can farko na yi mata ɗaya kaga babu aure kenan ya cika uku”


“Subhanallahi”


Daddy ya faɗa yana ɗan nazari


“Dad ita kanta tasan da haka sai idan sune bata faɗa ma ba amman Momy ma tasan da wannan”


Nisawa Daddy yayi 


“Bari zanyi magana da Abban nata amman ka tabbata da gaske ne dai ko?”


“Wallahi Daddy da gaske ne ka tambayi Momy tasan komai”


Kai Daddy ya ɗaga masa yana tunano abubuwan da suka faru.


                    ***               ****             *****


Kairat na shigowa parlour Talatu ta tashi tsaye da sauri tana faɗin 


“Yauwa kara da Allah ya kawo ki”


Kairat ta kalleta


“Lafiya ina Mummy?”


“Tana can kuma ina jin kuka take. wani ne yazo mai kama da Minal wallahi fuskarsu ɗaya ina jin Babanta ne ko kuma ɗan'uwan Babanta shi ta shiga ɗakin Minal tun ɗazu har yanzu ta ko fitowa tun ina jin sautin kukan har na daina”


Da gudu Kairat ta nufi upstairs. Kwance ta tararda Mummy duk ta watse komai na ɗakin fuskarta a kumbure idonta kuma suyi jawur alamar taci kuka har ta gaji.  Sai da Kairat ta karema ɗakin kallon sannan tayi cikin Mummy da masifa


“Haba Mummy kefa ba yarinya ce yar da kaddara nai da marar kyau yana cikin imani. Allah baya ɗorawa rayuwa abunda ba xata iya ɗauka ba. duk abunda Ubangiji yayi dai-dai ne Mumny ki yarda da wannan Allah bai raba ki da Familyn ki ba sai da ya baki wasu, bai karɓe miki farinciki ba sai da ya baki wani yanzu kuma ya karɓe miki Minal kin san abunda yayi miki tana di ? dukan tsanani yana tate da sauki Mummy yaushe zaki san da haka?”


A maimakon Mummy tayi magana sai kawai ta fashe da wani sabon kuka, nan itama Kairat tasa nata kuka


“Kuka kike yi Mummy, Hajiya ma kuka na baro tana yi. ya kuke son nayi da raina ne?. Wayyo Allah na ina ma ni ce na mutu ba Minal ba da baki shiga halin da kike ciki ba yanzu da ran Hajiya bai ɓace ba har ya kai ta gayin saɓani da ke, da Saif bai rasa matarsa da lil Minal bata rasa mai shayar da ita ba Alhamdulillah Allah ni kan na gode maka”


Ta faɗa ta karfi sannan ta juya tana kuka ta bar ɗakin.  Tashi Mummy tayi zaune ta share hawayenta sai kuma tayi shiru kamar mai tunani zuwa can ta tashi ta nufi ɗakinta.


          

                        ***       ***       ***

Tare suka shigo parlour ko wanne sanye da farar shadda, bayan sun gaisa da talatu Nasir ya zauna Saif kan tsaye yayi kamar bako.


“Ina mutan gidan?”


Nasir ya tambaya yana kallon upstairs, Talatu ta tashi tana faɗin


“Tana ciki bari na mata magana Kairat kan tana Garden”


Kai Nasir ya ɗaga mata Saif kuma ya juya ya nufi hanyar Garɗen ɗin.

   Sautin kukan ta ne ya sadashi da gurin da take, zaune ya hango ta ta kufa kai da guiwa tana kuka, ya daɗe yana kallonta haka kawai sai ya samu kansa da rashin jindaɗin kukan nata. karasawa yayi kusa da ita rumgume da hannayensa.

           Kanshin turaren da taji ne yasa tayi saurin juyowa ta kalleshi, sai kuma ta maida fuskarta ta shiga share hawayenta


“Me kike yi ma kuka.?”


Ya tambaya yana kara gyara tsayuwarsa


“Ba komai ba kuka nake ba”


“Ba komai kamar ya ko wani abun akayi miki ne?”


“Nace maka ba komai”


Ta faɗa kamar mai shirin sake yin kukan. Tashi tayi tsaye ta saka takalmin ta ta nufi hanyar parlour abunta ta barshi tsaye. kafaɗunsa ya ɗaga ya rufa mata baya. Da ruwan kuka ta shiga parlour ganin Nasir yasa ta sha jinin jikinta ta ɗan natsu


“Ina wuni”


Tace dashi tana kokarin ɓoye kuka nata, bai amsa mata ba ya kalli Saif dake bayanta ya sake kallonta ya kalleshi, Saif ya ɗaga kafaɗunsa alamar bashi da ruwa a kukanta, a sannan Nasir ya amsa gaisuwarta


“Lafiya kalau ya gida?”


“Lafiya kalau”


Ta zauna saman kujera tana kallon center carpet, Nan shi ma Saif ya samu guri ya zauna yana kallonta


“Saif ya faɗa min Mummy tace masa wai kin fasa shayar da Lil Minal haka ne?”


Shiru ta ɗanyi, ita dai bata san tayi wannan maganar da Mummy ba maybe Mummy tace haka ne dan ta hana ta shayar da ita, sai da ta ɗanyi gyaran murya sannan tace


“A da ba amman yanzu ni zan shayar da ita”


“Ba zaki shayar da ita ba Kairat Saif na faɗa maka ka nemo mai shayar ita Kairat ba zata shayar da ita ba ba matar aure bace ba bazawara bace ba kuma tsohuwa bace ba zan yarda ta shayar da ita ba!”


Mummy ta faɗa tana saukowa downstairs, Nasir ya kalleta dai-dai lokacin da ta karasa saukowa


“Wannan ba matsala bane Mummy Kairat ba zata fara shayar da Lil Minal ba sai Saif ya aureta. shi kansa yayi tunani akan hakan shiyasa ya yanke wannan shawarar”


Daga Saif har Kairat tashi sukayi tsaye suna kallonsa, Kairat ta saki baki tana kallon ikon Allah, Nasir ya ɗan taɓe baki


“Kunyar kake ji ne? ba shine abunda ya kawo mu ba ba kai da kanka ka faɗi hakan ba?”


Mummy dai sai kallon Saif take shi kuma ya sakar ma Nasir ido yana masa kallon da shi kaɗai ya san amsar sa.Nasir ma daga zaunen da yake ya tsare Saif da ido yana masa kallon jiran amsa.


ME KUKE TUNANIN SAIF ZAI CE?


SHIN KAIRAT ZATA YARDA?


YA SAFIYYAH ZATA JI INA TAJI WANNAN MAGANAR WANE MATAKI KUKE GANIN ZATA DAUKA?


MIYASA DATTIJON NAN YAKE SON MUMMY TA SAURARE SHI?


ME KUKE TSAMMANI GABA? 


KEEP VOTING AND COMMENTING,  I WILL UPDATE IN TIME. LOVE YOU GUYS 😍


                                    ***


DEENAH da SALEENA dake zuwa muku tsofin novels ɗi na ne nake ɗaukowa ɗaga blog ina kaiwa wattpad saboda na samu wani da ya shiga bog ɗina ya  sace min littafin na LAMARIN DUNIYA ya canja masa suna shiyasa nake ɗauke shi daga blog ina kaiwa wattapad sai nake musu sharen ba wai na fara rubuta sabbi bane.



47



Sun daɗe suna kallon juna shi da Nasir kamin ya ɗauke kai ya kalli Mummy sai kuma ya saci kallon Kairat da ido sannan ya zauna yana sauke ajiyar zuciya.


“Samu guri ki zauna mummy”


Ya faɗa ba tare da ya sake kallonta ba, Kairat tayi musu kallon rashim fashimta


“Ta zauna kamar ya? ni ban gane nufin wannan abun da kuke kokarin yin ba ni dai na riga na aminta zan shayar da ita dan haka duk wata magana ku ajeta gefe”


Saif ya kalletaƙkamar a fusa ce


“Ki bamu guri Kairat ba dake zanyi magana ba wannan tsakanin ni da mummy ne”


Zatayi magana Mummy ta tari numfashinta


“Jeki ɗakin ki Kairat”


“Mummy...”


Sai kuma tayi shiru, tsaye tayi kamar ba zata ba sai dai kuma ba zata iya yin musu da Mummy ba, ba dan taso ba ta juya ta nufi hanyar ɗakinta. Bayan Mummy ta zauna Saif ya kalleta a natse ya soma magana


“Mummy kina da gaskiya na hana Kairat ta shayar da Lil Minal. ni kaina sai da nayi tunani na gano hakan dan haka nima ban bada goyon bayan ta shayar da ita ba.


   Sai dai kuma Mummy ba zan iya ba wata wanda ba Kairat ba ta shayar da Lil Minal saboda ban san halinta ba ban san ya addininta yake ba, kuma kinga ba wai zata shayar da ita kawai bane zata raine ta ne ta nuna mata tarbiya har na ɗan wani lokacin.

   Babu matar da na yarda da ita irin Kairat a yanzu, kuma ba zai yiyu ta shayar da ita tana budurwa ɓa dole sai tayi aure.


in kuwa haka ne toh ni nafi kowa cancantar na aureta tun da yata zata shayar sannan kuma ina son na rika ganin su karkashin kulawata kuma ta haka ne kawai zan iya cika wasiyar Minal hakan kuma ba zai taɓa samuwa ba sai da haɗin kanki da kuma amincewar Kairat ”


Tun da ya ɗauko magana Mummy tayi natsu tana saurarensa, shiru tayi kamar mai tunani, ta ɗan daɗe kamin ta ɗago kai ta kalleshi


“Kayi tunani mai kyau Saif zan kuma goya maka baya ɗari bisa ɗari in har da zuciya ɗaya zaka yi. sai dai kuma ba zan cillas ta yin abunda bata so ba ba kuma zan hana ta abunda take so ba ina fatar ka fahimta”


Kai ya ɗaga mata 


“Bana nufi hakan Mummy, ko kaɗan babu hakan cikin rai na kawai ina son kiyi shawara ne ke da ita ki kuma nuna mata abunda ya dace”


Yana kawai nan ya tashi tare da zuba hannayensa cikin Aljihu


“Na barki Lafiya Mummy sai naji daga gare ki”


Nasir da tun ɗazu mamaki ya kashe shi ya tashi shima yayi mata sallama ya fice.


    A Mota Nasir yayi ta yima Saif magana yaki ya amsa masa sai tukinsa yake har suka isa gida sai da yayi parking sannan ya kallesa 


“Dan mi zakayi min haka Nasir? wannan ba shine karo na farko da kake min irin wannan katsa ƙandan ɗin ba ban san miyasa kake min haka ba!”


Tuntsurewa yayi da dariya


“Ba gashi ka faɗin abunda yake ran ka da kanka ba ni ai soso maka gurin da yake kaikayi ne kawai nayi. Kuma Saif in bakayi auren nan yanzu ba yaushe kake tunanin zakayi shi? kai fa ba yaro bane kasan abunda ya dace”


Saif dai bai sake ce masa komai ba ya buɗe Motar ya fice.

ganin haka yasa shima ya buɗe motar ya fita. a tare suka shiga parlour Nasir na ta jan Saif da maganar shi kuma ya masa shiru kamar ba dashi yake ba.

  Guri ya samu ya zauna yana kallon Momy dake kallonsu ya gaishe


“Momy an wuni lafiya?”


“Lafiya kalau ina kuka fito haka? tun ɗazu na aika a kira min kai akace ƙa fita”


Ta karasa faɗa tana kallon Saif,


“Eh mun ɗan fita ne”


Ya bata amsa yana kallon Dinning dan yasan ba zai wuce maganar abinci ba, dan yanzu ta mauda shi kamar karamin yaro ganin baya son abinci.


“Gidan Dr. Salamatu muka fito Momy”


Kamar wanda aka matsi bakinsa haka maganar ta fito a baki Nasir yana ɗan Murmushi


“Me kuka je yi ko maganar Lil Minal ne?”


Nasir ya nuna shi


“Zai miki bayani ni yunwa nake ji”


Da kallo Saif ya bisa har ya zauna saman kujerar dininning yana mamakin yadda take aron bakinsa yana ci masa albasa,


“Lafiya dai ko?”


Momy ta tambaya ganin yayi shiru baice komai ba sai hararar Nasir yake. Sai a lokacin ya kalli Momy yana mata wani murmushi daya kara fitar da ramarsa, zaiyi magana Sallamar Safiyyah da Lubna suka katse su.

Haɗa baki sukayi da Momy gurin amsa musu sallamar Lubna ta zauna kusa da shi yayinda da Safiyyah ta zauna kasa tana kallon tv.


“Ina jinka”


Momy ta faɗa tana mai hankalinta gurinsa


Sai da ya nisa sannan ya fara kora mata bayani,


“Momy akan maganar shayar da Lil Minal ne, toh shine Mummy tace ba zata bari ta shayar da ita ba tunda ba ta da aure. kuma nima ina goyon bayan hakan tunda gaba sai iya zame mata matsala”


“Oh yanxu ta fasa shayar da ita kenan?”


Momy ta tambaya,


“Eh toh ba wai ta fasa bane ita tana son ta shayar da ita matsalan ba daga gare ta bane, Toh shine Nasir ya bani shawarar na aureta kawai ta yadda zata iya shayar da ita tana matata kuma karkashin iko na tun ni daman ba son nake Lil Minal tayi nisa da ni ba.”


Annuri ne ya cika fuskar Momy ta jidaɗin maganar sa sosai, daman abunda yake da munta a yanzu kenan dan gani take idan yana da mata wannan damuwar da yake ciki zata ragu.


“Kayi tunani mai kyau Saif hakan na nuna ka fara yarda da kaddara kenan. kuma kayi sara kan gaɓa, jiya fa muke magana da Abbah ka yake cewa ya kamata ka samu matarm aure ta yadda zaka rage wannan damuwar”


Murmushi Saif yayi


“Momy ai yarda da kaddara waji bi ne ga duk musulmi, kawai dai sabo ne da kawa zuci irin na ɗan'adam”


Lubna ta rika hannunsa tana murmushin jindaɗi,


“Wow Yayana ya kusa zama ango Allah ya tabbatar da alkhairi amman Yaya zakayi mata mai mutunci wallahi ana yabon Kairat da tarbiya nima yarinyar tana burgeni. amman Yaya ta yarda?”


“Yardar nata dai nake nema duk da nasan abun zai zame mata wani iri”


“Gaskiya kan sai taji daban sai kayi hakuri da ita”


“Ko kuma ita tayi hakuri da ni ba”


Ya mayar ma Momy da amsa yana ɗan taɓe baki. tashi Safiyyah tayi tana kokarin ɓoye kukan ta, ta nufi ɗakinta. Duk suka bita da kallo har ta shige.

    Maida kofar ɗakin tayi ta rufe wani irin kuka mai karfi ya zo mata, bata son ta fasa shi su jita duk da tasan sai sun zargeta ganin bata sa bakinta ba, gashi kuma ta taso ta baro musu ɗakin.

   Makullin Mota ta ɗauka tare da waya ta shiga bathroom ta wanke fuskarta sannan ta nufo downstairs.


       Ko da ta sauko Momy da Nasir kawai ta tarar sai kuma Saif dan Kairat bata gurin Momy kawai ta kalla


“Momy zan ɗan fita naje gidan Gwaggo”


“Toh ki gaishe ta Allah ya tsare”


Bata amsa mata ba kai kawai ta ɗauke ta nufi hanyar da zata fitar da ita daga Parlour. Nasir ne ya bita da Ido har ta fice, sannan ya kalli Saif dake aikin dannar waya ya ce


“Ina jin maganar auren nan da kayi ne yasa taji ba daɗi”


Kafaɗunsa ya ɗaga ya taɓe baki, alamar bai damu ba ya cigaba da abunda yake. Momy ta sauke ajiyar zuciya


“Wallahi yarinyar nan tana son ka Saif ni wallahi har tausayi take bani da zaka bi shawara ta da ka aure ta”


Sai a lokacin ya aje wayar dake hannunsa ya kalleta


“Momy da zan iya auren Safiyyah da tuni na aure ta yun da ba bakuwar fuska ta bace a nan gidan fa ta tashi”


“Toh ai ko ɗan haka yaci ace kayi mata wannan halaccin, ina fa maka tsoron kar kaima kaje ka samu mai yi maka haka gaba kayi aure na ɗaya ka barta ka kara wani ka barta yanxu ka zo da maganar wani ai mutane ma sai su zargi abu cewa za'ayi dan ita ba yata bace yasa kake mata haka gashi taki ta tsayar da Miji”


Nasir ya ce


“Kar hakan ya dame ki Momy nan gaba kaɗan xata fito da mijin aure dan kanta”


“Ni abun har mamaki yake bani wallahi wai mace da aka sani da kunya ita zata fito kiri-kiri ta nuna tana son ka ni bana son irin wannan rayuwar”


Saif ya faɗa yana taɓe baki Nasir ya karɓa masa


“Aiko yanzu mata yawancin su duk haka suke sai ɗaiɗai ku su suke kai tallar kansu da kansu gurin maza musamman in suka ga wanda yayi musu”


Momy ta ɗan ɓata Fuska


“Toh. miye haramun ne? ai Annabi yace duk abunda kake so ka ce kana son shi, sannan a zamaninsa ma an samu mace da taje tace tana son Annabi (S.A.W) balle yanzu da zamani ya canja”


“Momy ai ana barin halal dan Kunya, irin wannan can daban irin wannan daban wannan baya jawo komai sai rage ma mutun kalama da mutunci a idon namiji”


Saif na kaiwa nan ya tashi ya nufi dinning area.


         Kacar  Safiyyah taga ta isa gidan Gwaggo, aiko tana shiga faɗi falonta ta fashe da kuka dan fashe kurjin da yake mata ciwo. da gudu Gwaggo ta fito daga kicin tana tambayar 


“Lafiya? wani ne ya mutu?”


“Da mutuwa ce Gwaggo da yafi min sauki”


“Miya faru haka ne Safiyyah?”


“Gwaggo Saif aure zaiyi”


Ta faɗa cikin kuka har muryarta na rawa, 


“Oh shine kike wannan kukan ? yau kika saba ganin Saifu yayi aure ne? tashi ki share hawayen ki da yarda Allah kece amaryar”


Cigaba tayi da rairai kukan tana faɗin 


“Gwaggo ba zaki gane ba”


“Na gane mana Safiyyah babu abunda Saifu da Mahaifiyarsa keso sai ki mutu. ai tasan ta yadda zata iya sashi ya aure ki amman taki kuma tsan yana sonki da yanzu kece baki sonsa cillas ta miki aurensa zatayi. matar nan ko dan tashin da kikayi a hannuta yaci ace tayi miki wannan karancin. amman batayi ba dan tsabar mugunta”


Cikin kuka Safiyyah ta kalleta,


“Wallahi Momy bata so na Gwaggo bata tausayi na rayuwar yayanta kawai ta sawa gaba ko dan taga bana da uwa ba uba shiyasa take min haka”


“Na sani Safiyyah ai matar ɗan uwa ba ɗan uwa bace shiyasa nake son ki daina kuka lokacin kuka ya wuce kamata yayi mu tashi tsaye muyi abunda xai fitar da mu”


“Toh Gwaggo me zamu yi? bana ganin akwai wata mafita”


“Akwai mafita. nasa abinci ka min wani malamai kwararin kuma an samu mo min ta hanyar su zamu bi har bukatar mu ta biya”


tashi Safiyyah tayi tana share hawaye, 


“Gwaggo yaushe zamu je?”


“Ba sai mun je ba su da kansu zasu zo nan gidan zan zuba kuɗi a ɗauko min su daga duk inda suke suyi min aiki”


Rumgume ta Safiyyah tayi tana kuka.


                 Kairat ta tashi zaune tana kallon Mummy idonta cike da hawaye


“No Mummy ba zan iya ba”


“Zaki iya Kairat Saif yana da mutunci yana ɗa karamci bana jin zaki samu matsala a zaman ku dashi”


“Ba shi nake nufi ba Mummy ba zan iya auren Mijin Minal ba, ba zan iya auren wanda bana so ba”


“Ta wannan hanyar ce kawai zaki iya share min hawaye na ta wannan hanyar ce zaki wanke ni daga zargi, ta wannan hanyar ce kawai zaki iya shayar da yar ki cikin kanciyar dan duk namijin da kika aura ba zai yarda ba taɓa yarda ki shayar da yar wani ba ba kuma zan barki ki shayar da ita kina budurwa ba”


“Mummy....”


Mummy ta tari numfashinta


“Kairat ina son kiyi tunani ki kuma yi shawara amman mummy ki ba zata cutar da ke ba”

            

Kai Kairat ta ɗaga mata tana lasar bakinta idonta kuma cike da hawaye, Mummy ta shafa kanta ta tashi ta fice.


    Wayarsa ce take ta ringing alamar kira, shi kuma yayi kamar bai jita ba sai tunane tunane yake, sai da aka masa kusan kira biyar sannan ya tado kai ya kalli wayar dake kan mirrow. ɗauka yaƴi bayan ya danna picking ya kara a kunne, shiru yayi bai yi magana ba hakan yasa mai kiran yin magana


“Hello Saif....”


Muryar Huda ce cikin kuka ta kira sunan nasa. Dafe kai yayi ya ɗan yatsina fuska


“Ya a'akayi?”


Ya tambaya kamar baya son magana, ta ɗan daɗe kamin ta sake cewa wani abu


“Na kira ne naji muryar ka na kuma roki gafarar ka a zaman da mukayi, nasan munyi samun taɓani kuma naci amanar ka dan Allah Saif ka yafe min har abada ba zan taɓa samun miji mai hakuri da juriya irin ka ba Kayi min halacci ta ko ina kayi min adalci Saif baka taɓa cin amana ta ba baka taɓa tauye min hakkina ba ina rokon Allah ya haɗa ka da mata ta gari wanda ba zata ha'ince ka ba Allah ya raya maka abinda Minal ta bari. karka manta da soyayyar Huda a zuciyarka ina Huda na son ka sosai Saif karka manta da wannan.....”


Da sauri ya kalli wayar jin kiran ya katse. wani dogon numfashi yaja ya lumshe ido, maganganunta suka tsaya masa a rai. damuwarsa ta karu yana cikin wacan tunani yanzu kuma ga wani dafe kansa yayi jin yana masa wani sara. babu abunda ya faɗo masa a rai sai Happy Island tashi yayi ya ɗauki keys ɗinsa cikin yan mintuna ya bar gidan.


                             ***      ***      ***


“Allah sarki Sweet Friend wai ke da niyarki sai zama zaki yi sai ranar da yazo yace yana sonki? ai an daina wannan yayin yanzu idan kawai kika ga wanda yayi miki zuwa kawai zakiyi a asirce shi shikenan sai yadda kika yi dashi”


Shafa ta faɗa tana wani rausayar da kai, 


“Toh ai ni ba zuwa gurin bane kar sa ka kauce hanya ka kwasar ma kanka zunubi”


“Ah lallai sabuwar shiga ce kwace hanyar na yaushe ai tunda kika ce baki yarda da kaddarar son da Allah ya ɗora miki ba na son Saif kika ki hakura kin daɗe da kwance hanyar.

   Zunubi kuma na nawa? ba ke kika shiga kika fita ba har sai da kika kulla zargi tsakanin mata da miji zama ya gagare su kika ɓata amintar aminai ai kin daɗe da tara wannan zunubin sai dai kawai indan munyi wannan sai mu taru mu tubar ma Allah”


Shiru Safiyyah tayi bata ce komai ba kamar mai tunani,

hakan yasa Shafa taɓe baki


“Ba zai fa taɓa sonki ba tun da kika nuna kina sonsa, bama kece gabansa ba ai maxa sun gware a wannan fannin arkinki ɗaya wannan ba ɗan duniya bane da sai dai yace yayi amfani da wannan damar ya nemi lalata ki”


Ajiyar zuciya Safiyyah ta sauke


“Toh yanzu ni dai yaushe zamu je?”


“Ni idan zaki yarda yau ɗin nan zamu je ba sai gobe ba akwai wani boka a kauyen abujar nan yana aiki sosai kamar hankan wuka sannan ko wane irin aiki yana yi sai dai fa kuɗi”


“Toh ko zamu je can ne kamin Gwaggo ta gwada nata? kuɗi ba matsala bane matukar akwai biyan bukata”


“Ni kuma nace miki matukar akwai kuɗi to akwai biyan bukata, idan kin shirya kawai ki tashi muje”


Tashi tayi tna faɗin 


“Bari na ɗan watsa ruwa.”


                              ***         ***        ***


        Magana take da kanta tana safa da marwa can ta samu guri ta zauna ta dafe kai tana dauke ajiyar zuciya, 


“Innalillahi wa inna ilaihirraji”


Shine abunda ta furta tana lumshe ido, bata buɗe ba duk da tafiyar da take ji a bayata har sai ta taji anyi mata magana


“If you need someone to talk to I'm here”


Juyowa tayi da saurin jin kamar muryar Saif, shi ko ne ba kama ba ya rumgume hannayensa yana kallonta


“Me kazo yi a nan?”


Kallon gurin ya shigayi kamar bakonsa 


“Na kan zo nan wani lokacin dan samun natsuwar zuci. tun lokacin da Minal ta faɗa min nan ne gurin zuwanta sai na samu kai na da sha'awar na kasance a gurin ko da yaushe,

    Kamar yadda kema nasan hakan ne ya kawo ki dan naga yadda kika shigo hankalin ki ba kwance ba”


Yawun dake bakinta ta haɗe ta kalli itace dake gurin, shi kuma idonsa na kanta Yana karantar damuwarta


“You can trust me Kairat”


Ta Kalle shi 


“Why should I?”


“Cos I'm the only one you can trust”


Dauke kai tayi hakan yasa ya zagoyo gefenta ya zauna yana kallon tsuntsayen dake gurin ya soma magana a hankali


“Kaiyrat babu ta yadda zaki iya shayar da lil Minal sai kina da aure miyasa ba zaki yarda kiyi auren ba idan har da gaske kike kina son Minal kina kuma son abunda ta bari, taya kike tunanin tarbiyantar da Yar Minal ba tare da ta girma a hannun ki ba? ko kin manta wasiyar Minal ne Kairat?”


“A a ban manta ba, naji ba zan iya shayar da ita ba sai ina da aure amman kuma ba zan iya auren Mijin Minal ba, i can't”


“Ba Mijin wata zaki aura ba mijin ki zaki aura uban yayanki”


Ya faɗa yana kallonta ita, ma shi take kallo. hakan yasa ya kara fuskantar ta


“Kairat bana son ki ra a ranki zamuyi wannan auren ne dan so da kauna kisa a ranki zamuyi wannan auren ne dan sadaukarwa. 

   Zakiyi hakan dan Mummy da lil Minal kinsan me? a lokacin da Minal zata rasu ta faɗa min na aure ki na saki cikin farinciki, even on her bed dying ta kula da farin cikin ki misa ke ba zaki iya kula farin cikin yarta ba? ya kike tunanin lil minal ta girma ta buɗe ido taga mahaifiyarta ba raye ba?”


Kai ta girgiza idonta cike da hawaye


“Ba zan iya auren ka ba, ba zan nuna ma lil Minal bani na haife ta ba”


“Taya zaki nuna mata hakan bayan baki auri mahaifinta ba.? banyi wani dogon zama da Minal ba Kairat abunda kike tunani ba shi bane nasan zakiyi rika ga yadda na saba rayuwata da minal ke kuma nayi rayuwa dake no ba haka bane kanun Minal ina da wata matar kin tuna kuma na zauna da ita mukayi tamu rayuwar daban ki sa a ranku saurayi zaki aura wanda bai taɓa aure ba ke zaki koya masa rayuwar aure ki karantar dashi naki karantun a makarantar ki”


Kallonshi take tana mamakin yadda waɗannan kalaman ke fita bakinsa kamar bashi ne yake maganar ba sai kuma ta girgiza kai


“Still ba zan iya ba Saif ya duniya zata kalleni...? i just can't.”


Murmushi yayi mai sauti murmushin da ya kara fitar da kyau da kuma kamalarsa,


“Duniya zata rik'a ɗaga ki ne, mutanen cikin ta kuma su rika kallonki karkace kiyi ta tafiya haka har baki ankara ba lokaci ya k'ure miki baki yi abunda zai amfane ki ba. Nasan yadda kike ji Kairat I feel the same way”


Hannu ta kai ta ɗauki handbag ɗinta ta rata ya


“I need to go home”


tashi shima yayi tsaye,


“Yes go home Kaiyrat kije kiyi tunani mai kyau kiyi abunda zai fidda ki karki manta da baya Kaiyrat karki cutar da kanki karki cutar kar kuma ki bujirewa Minal”


Cikin kwayar idonsa take karantar abunda yake fita bakinsa, kallon kallo suka rika yima junan su kowanne ta tasa sakar a zuciya. ita ce ta fara yin jihaɗin ɗauke nata idon daga nashi ta haɗeye yawun karamin bakinta ta, taka a hankali tana tafiya kamar mai tausayin kasa.


    Da ido ya bi ta yana mata kallon da shi kansa bai san na minene ba? sha'awa, tausayi, so, ko kuma kauna! wani kalar yanayi nake jin kansa ciki yanayin da bai taɓa jin kansa ciki ba wani kalar yanayi ne mai wuyar fassara.

   A hankali ya kai hannu ya shafa kyakyawan gashin kansa ya tada kai yana kallon itace dake gurin yana lumshe manyan idonsa a hankali.

Mamakin kansa yake yadda yake rokonta ta aure shi bayan bai taɓa yi ma wata mace hakan ba. wani gurin kuma gani yake yana da gaskiya saboda wasiyar Minal da kuma lil Minal.


                        ****           ***      *****


BAYAN KWANA BIYU....


      Safiyyah ce kwance ɗakinta fuskarta ɗauke da murmushi sai juyi take ta kafa tana jindaɗi. yau ne zata fara gwada maganin da malamin ta ya bata kuma ta yarda zaiyi mata aiki. tana jin fakawar Motar Saif ta tashi ta sauri ta leka windo ganin shi ɗin ne ya kara mata jindaɗi, 

   Da sauri ta dawo ta buɗe jakar ta ta ɗauko wani kwalli ta buɗe maciyin ta kira sunan Saif sau uku ta tofa sannan ya shafa. daman haka yace mata duk zata shafa ta kira sunansa dan da sunan akayi aikin.

      

Tana gama shafawa ta mayar a jaka ta nufi madubi ta dauki hoda ta shafa ta gyara jan bakinta ta buɗe wata durowa ta ɗauko wani turare daga ganinsa kasan na magani ta shafa, sannan ta juyo jiki na rwa ta nufo parlour.

   Ta koyi sa'ah tana saukowa yana danno kai cikin parlour, yana sanye da shada sky blue tayi masa kyau sosai kansa ɗauke da bakar hula.

wani fari tayi masa da ido ta sakar masa mirmushi 


“Ya Saif sannu da zuwa”


A maimakon ya amsa sai kawai ya wanke mata fuska da mari.




Kuyi Hakuri da wannan Anjima Wani Zai Zo Amman Ban Muku Alkawarin Mai Yawa Ba.😀 

just keep voting and commenting on every single line. Stay bless Candy Love you from the bottom of her heart.😍


MY QUESTIONS.


TUN FARKON FARA KARANTA LITTAFIN NAN ZUWA YANZU ME YAFI BURGE KU? 


INA YAFI BAKU HAUSHI?


INA YAFI BAKU TAUSAYI?



48


Ja tayi baya da sauri ta dafe junco dan ba karamin mari yayi mata ba, 


“Lafiya mi tayi maka haka?” 


Momy ta tambaya tana tashi tsaye, sai a lokacin ya lura da Momy, juyar da fuska yayi ya ɗan haɗe rai. A nan ya shiga neman dalilin marin nata da yayi ya rasa, shi kan shi bai san dalilin marin nata dayayi ba shi dai kawai ya samu kansa da jin haushin murmushin da tayi masa da magana. 


“Momy parking tayi ba dai-dai ba gurin da nake aje mota na take ta aje” 


Ya faɗa yana kokarin kare kansa, tunawa da yau gurin da yake parking yaga motar ta fake, 


“Haba dan Allah dan Annabi sai kuma kayi mata wannan mari haka? Sai kace karamar yarinya, ai sai kaje kace ta ɗauke motar ko.? Ba ma ita ra fita da Mota ba Lubna ce” 


Shafa kansa yayi yana ɗan yatsinar fuska ya zauna saman kujera, kallonta yayi kamar yace tayi hakuri sai kuma yaji ba zai iya ba, ya kalli Momy data ranta ya ɓace ya ce 


“Na ɗauka ita ce sorry Momy” 


Banza Momy tayi dashi tana kallon Safiyyah da ta rufe ido tana hawaye, juyawa tayi kamar kazar da kwai ya fashe ma ta nufi ɗakin. 


“Ni Wallahi halin naka ya fara isa ta bana son abunda kake yima yarinyar nan ko kaɗan” 


Momy ta faɗa tana jan tsaki cike da ɓacin rai. Kallonta ya sake yi


“Momy kiyi hakuri” 


“Wane irin nayi hakuri fusabilillahi abun da kake mata kyautawa ne? Ko kuma dan tana zama nan gidan sai ya baka damar yi mata duk wulakancin da kaga dama” 


“Momy mistake ne fa” 


“Wane irin mistake daga shigowar ka ka fece yarinya da mari kace mistake haka ake mistake to Wallahi daga yau sai yau ko Kallon banza karka sake mata balle ka ɗaga hannu ka dake ta” 


Momy na kawai nan, ta tashi a fusace ta shige ɗakinta. Gashin kansa ya shafa ya ɗaga kansa 


“Oh my goodness Momy ba zaki saurari abunda nazo dashi ba akan na mari Safiyyah, ya salam!” 


Ya faɗa yana girgiza kai. 


***          ****        *** 


“Assalamu Alaikum” 


Yayi sallamar yana kokarin kunno kai cikin parlor, cikin taku irin nasu na manya. Dr Salamatu ce ta amsa masa Kairat kuma ta karasa gurinsa a guje ta rumgume shi


“Sannu da zuwa Abbah” 


Ta faɗa cikin wani irin jindaɗi tana dariya, shina dariyar yayi yana faɗin 


“Yauwa yar Salamatu ya gidan naku?” 


“Gida lafiya kalau” 


Ta masa yayin da take ɗago kanta daga jikinsa, hannunta ya rika suka nufi three sitter suka zauna. 


“Ina wuni Salamatu” 


Abbah ya gaishe ta ganin yadda ita ɗin ta kasa masa magana sai wani abu take kamar ba ta jidaɗin ganin shi ba. Daker ta asa tana ɗan murmushi. Kairat ta tashi cike da zumuɗi 


“Abbah bari na kawo maka Abinci yanzu muka gama ni da Mummy” 


“Toh yar Mummy ba sai kin kawo min ba ruwa ma ya isa” 


Kicin ɗin ta nufa tana faɗin, 


“Toh Abbah” 


Bata daɗe ba ta fito ɗauke da ture mai drinks da cup, a gaban sa ta dire ta ɗauki lemu ta zuba masa ta mika masa


“Gashi Abbah kasha lemon gidan mu” 


Karɓa yayi yana murmushi ya kurba kaɗan ya aje sannan yayi ma Mummy kallon natsuwa. 


“Gurin ki nazo ke da yarki” 


“Allah yasa ba laifi muka yi ba” 


Mummy ta faɗa tana ɗan murmushi, Abbah ya gyara zaman sa


“Jiya ne iyalan Alhaji. Bashir bature suka zo gidana akan maganar Kairat sun ce min daga nan aka turo su kuma yace da amincewar ku, haka ne?” 


Kairat tayi saurin yin kasa da kanta cikin kunya ta mataa gurin Mummy, Mummy kuma tasa dariya tana shafa kanta 


“Eh haka ne daga nan na tura su can” 


Abbah yayi dariya


“Ance Saifullahi ne mijin margayiya” 


“Eh. Haka ne sun daidaita dashi da ita ne sai nace idan har da gaske yake yaje can ya same ka ashe ya je” 


“Eh sunje Jiya, ni kuma nace ba zan ce komai ba sai naji ta bakin ku, amman naji daɗi wannan abun sosai Allah ya tabbatar mana da alheri” 


Mummy ta amsa da


“Amin” 


Abbah yayi dariya yana kallon Kairat 


“Toh ke kina son shi dai ko?” 


A gudu ta tashi ta shige ɗaki tana rufe ido. Abbah ya kalli Mummy da ta bita da kallo ya ce


“Sai a samu su rana kenan?” 


“Eah a sa musu amman kayi shawara da Hajiya tukuna” 


“Nayi mata magana ai tace nazo nan na same ki ai kece uwarta” 


Shiru Mummy tayi tana nazari, ke hakan yake nufi kenan? Babu ruwanta da lamarin auren ko muma me? Maybe bata ji daɗin haɗin auren da aka yi ba. Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta kalli Abbah 


“A sa musu kuma inda hali kar asa da tsawo saboda Babyn ta kasan an kusa sallamo ta daga asibiti kuma kasan ita ce zata shayar da ita” 


“Masha Allah amman kunyi tunani mai kyau gaskiya dan ba kowa bane zai iya yima ma rokon gaskiya ba, Bari na saka muku wata ɗaya yayi?”


“Wata ɗaya bai yi nisa ba?” 


“Toh bari aka muku sati biyu” 


“Toh ina madallah da hakan Allah yasa albarka” 


“Amin” 


Shiru ne ya biyo baya kowa hankalinsa ya koma kan tv, zuwa can Abbah ya kalleta


“Toh ni kan zan wuce inda wata matsalar zaki iya sanar min, duk da akawai wata maganar da nale son yi dake amman ina ganin sai an gama wannan hidimar ta Kairat” 


Mummy ma tashi tayi ganin ya tashi tace


“Na gode sosai ka gaida Hajiya” 


Ta basar da wacan maganar, murmushi kawai yayi dan yasan da gangan tayi hakan, ya nufi kofa ita kuma tayi masa rakiya har gurin Mota. 


   Kuka Kairat ta samu kanta dayi lokacin da ta shiga ɗakinta kuka marar dalili dan itama kanta bata san dalilin kukan nata ba, ita dai kawai taji kuka yazo mata ba kakkautawa. 

     Kusa da ita Mummy ta zauna lokacin dats shigo cikin ɗakin ta kalleta cikin damuwa


“Kairat bana nufin cilasta ki, bana burin kiyi auren da baki so ban roke ki ki auri Saif sai dan ansan akwai ɗigon son shi cikin zuciyarki, na haɗa ki da girman Allah karki auri Saif matukar kina tunanin aurensa zai zame miki matsala ko kuma tursasawa daga gare ni” 


Dagowa tayi ta ɗora kanta saman cinyar Mummy, 


“Wallahi Mummy ni kaina ban san dalilin wannan kukan nawa ba, kawai dai ina jin wani abun ne daban, babu cilastawar ki ko ɗaya a wannan auren ni naji zan iya kuma nasa kai na karki taba zargin kanki” 


“Amman Kairat bana jindaɗin wannan kukan da kike yi yana kuna min zuciya” 


“Ba zan sake ba Mummy insha Allah” 


Ta faɗa tana share hawayen ta, Mummy ta shafa kanta. 


“Allah yayi miki albarka ya biya ki” 


“Amin” 


                               ☆ ☆  ☆     ☆ ☆ ☆       ☆ ☆ ☆


Cikin satin Abbah yasa yanka musu sadaki ya kuma duk wani abun da yace uba yayi ma yarsa, cikin satin kuma akayi komai cikin har da kawo tufafin da Kairat zata saka, Saif yasha mayar nu gidan yana tambayarta ko da wani abun datake bukata tace masa a a. duk wani abu da yan mata suke yi ita kinyin tayi ciki har da kin raba katin aurenta, walima ma dan Mummy ce ta shirya ta shiyasa kawai zata halarta. babu yadda Mummy bata yi da ita ba akan ta ɗan yi wani event ko da ɗaya ne amman taki. 

   Safiyyah kan tattarawa tayi ta koma gidan Gwaggonta wai ba zata iya zama a gidan Momy ba dan ba zata iya jure yadda Saif yake disgata ba, gashi yanzu abu ɗaya da biyu zai sako maganar Kairat ko lil Minal.

   Duk wani abu da ya dace ya tayi ma yarta sai da Mummy tayi ma Kairat shi, tun daga gyaran jiki zuwa tufafi har kan abunda za a saka mata a ɗakin. hakan sai yasa Kairat ta zama yar gata dan Hajiya ma irin nata gatan take nuna mata, Abbah ma duk abunda aka siyo sai ya nuna mata ya kuma tambaye ta abunda take so, amman hakan bai taɓa sa taji daɗi ko da sau ɗaya ba. 

   Ana saura kwana biyu a ɗaura aure Hajiya Suwaiba ta zo gidan, Mummy taji tsoron ganin ta dan bata san da wace tazo ba, tunawa da zuwanta na karshe a gidan, Murmushi dake fuskarta yaba Mummy karfin gwuiwar yi mata magana


“Sannu da zuwa Hajiya Allah dai yasa ba laifi muk yi ba”


Hajiya ta zauna tana murmushi tana kokarin zaunawa,


“Ya gida ya hidima”

   

“Alhamdulillahi ya naku?”


Mummy ta faɗa tana kallon Fusakarta. 


“Masha Allahu na fito gidan Ramatu ne nace bari na biyo tun da ku baku zuwa ga shirye shirye yayi nisa”


Dariya Mummy tayi suka cigaba da fira sai dai kowa bai sake jikin kasancewar Mummy tunanin da wace tazo, ita kuma tana jin nauyin Mummy akan abunda tayi masa.


        

           RANAR ASSABAR.........

Rana ce da da dandanzon mutane suka shedi ɗaurin auren KAIRAT IBRAHIM AHLAM da SAIFULLAH BASHIR BATURE, anyi taro kosai tun daga kan yan'siyasa yan kasuwa sarakauna malamai da kuma daidai kun jama'ah, Daga  garuruwa daban daban, bayan ɗaurun Auren mutane suka ɗugun zuma zuwa gurin liyafar cin abinci. 

        Bayan gama liyafar Saif ya nufo gida tare da wasu abokaninsa, Kallo ɗaya zakayi masa ka ganr shine angon duba da yanayin shigarsa da kuma yadda fuskarsa ke annuri kanshi turare kan ba a magana, kallo ɗaya Safiyyah tayi masa ta ɗauke kai ta cigaba da kallon tv tana wasa da makulin hannunta, 


“Sannu Ango Allah ya bada zama lafiya”


Shafa ta faɗa tana murmushi, Safiyyah ce ta amsa da amin kamar ba komai, sannan ta kalli Lubna take da zuba da Nasir tana faɗin


“Ke suda muje ni dai akwai gun da naƙe son zuwa”


“Ina zaku?”


Nasir ya tambaya yana kallon Lubna dake tsaye kusa dashi ta rike masa hula


“Yauwa Ya Nasir muje ma ka kai mu gidan Ya Saif zamu je ɗakin Lil minal zamu gyara”


“Ita lil Minal ɗin har an mata ɗaki?”


Tayi wani fari da ido,


“Taf tun yaushe yau ɗin ma wasu kayan zamu kara sakawa”


“Toh masu abu su keci da rana kuna shagalin ku”


Duk suka sa dariya har Safiyyah, a nan Luban ta tirsasa shi tasa shi gaba a dole ya kai sai da yayi driving ɗin su har gidan a mota in banda tsokanar Lubna babu abunda yake har ta saka masa kuka.

Dukan su sun yaba kyau gidan da kuma yadda aka gyara ɗakunan musamman ɗakin Lil Minal sasancewarsa ɗakin yara yana da ɗaukar hankali idan an gyara shi.  A tare suka shiga jera sauran kayan ganin aikin nasu ba mai karewa bane yasa Nasir yayi tafiyarsa yace idan sun maga su buga masa zai zo ya ɗauke su. Ai ko Safiyyah ta jidaɗi sosai yana fita itama ta fita daga ɗakin ta nufi gurin da aka dasa itace dan kwaliya, hannu ta kai ta kalli wani ɗan karamin ice ta duka a gurin tana gina, wani abu naga ta ɗauko ta saka cikin karamin ramen ta rufe waige waige take har taƴi ta gama tana Allah Allah kar wani ya ganta, Tashi tayi tana karkaɗe jikinta ta lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya can kuma ta buɗe ta nufi cikin gidan.

       wani kallo Shafa tayi mata mai alamar tambaya ita kuma ta ɗaga mata kai, sai ko wannenasu ya ɗauke kai suka cigaba da shirya ɗakin.


      Nasiha Sosai Mummy tayi ma Kairat bayan Abbah da Hajiya sunyi mata nasu, Kuka sosai Kairat ta rikayi kamar ranta zai fita kwaliyar da akayi mata duk ta bace Mummy ma ba karamin kuka tayi ba, saboda tunawa da auren Minal da kuma ganin za a barta ita kaɗai. daker aka ɓanɓare hannun Kairat a jikin Mummy, Motar ma daker aka saka ta, sai wani abu take kamar mai aljannu. ko kuma nace wanda za a cire ma rai, har wani numfashi take saboda kuka. 

            Har a ka isa da ita gidan angonta kuka a motar ma ba karamin yaki akayi ba wajen fitowa da ita a shiga cikin gidan ba, a ɗakin aka wuce da ita kowa sai yaba kyau gidan yake da kuma kayan da ka zuba ma Kairat, masu ɗaukar hoto nayi an video camera ma nasu aikin suke. ita kan bata kula komai ba kuka take har abokanin ango suka shigo dashi. zolayarsa suka rikayi shi dai in banda murmushi babu abunda yake shima kana gani zaka san bai kai zuci ba, Nasir ne kawai ya ware kansa daban yana musu nasiha irin ta zaman aure da kuma hakuri, har sauran abokanin suka rika janshi wai sai kace shi ɗin aure ne dashi. sai da suka canye lokacin su har suka shiga na amarya da ango sannan suka bar gidan bayan anyi abubuwan da al'ada ta tana da. 


    Gyara zamansa yayi ya kalleta yana sauke ajitar zuciya, shi kansa ba wani farinciki yake ji ba, jinsa yake daban yana tuna rayuwar aurensa ta baya, motsin abun warwaronta ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi, ya sake kallonta a karo na biyu


“Godiya ta tabbata ga Allah wanda cikin ikonsa da amincewarsa da rahamar sa ya nuna mana wannan rana, wanda yau gani ga ki a masayin miji da mata, wannan lamarin na Allah ne shi kaɗai yasan abunda ya tsara mana da kuma wanda zai tsara mana nan gaba”


Ita dai har lokacin kanta na kasa cikin mayafi.


“Sai ki tashi muyi ma Allah godiya”


ta shi tayi ta nufi kofar bathroom ɗin tana wata tafiya kamar ta faɗi, bayan ta ɗauko alwala ta fito shima ya shiga yayi ya fito.

   A tare suka gabatar da Sallah raka a biyu suka yi addu'ah, sannan ya juyo ya kalleta


“Ga abinci nan nasan baki ci komai ba, ni zanje ɗakina na kwanta”


Bata ce masa komai ba shima ɗin bai jira tace masa ba ya tashi ya nufi ɗakinsa. aiko tana jin rufewar kofar ɗakinsa wani sabon kuka yazo mata ta tashi ta koma saman godon ta kwanta tana rera kuka a hankali. da haka bachi yayi gaba da ita


               WASHE GARI.......

Sai tara da rabi Saif ya fito daga ɗakinsa, yana sanye da jallabiya baka tayi masa kyau sosai kamar ba wanda ya tashi daga bachi ba, ganinta tsaye gurin dinning yasa ya karasa gurin yana ɗan murmishi kamin yace wani abu tayi saurin dukawa ta gaidashi cike da ladabi


“Lafiya kalau kin tashi lafiya”


Cikin jindaɗi ya amsa mata. ita kuma ta amsa masa cike da jin kunya, 


“Ga abincin ka nan”


Ta faɗa tana kokarin barin gurin. 


“Kinci naki ne?”


“Aa a ɗaki zan ci”


Oka kawai ta faɗa yaja kujera ya xauna, bayan ya kare ya koma ɗakinsa ya shiga bathroom yayi wanka yana fitowa ya shirya cikin wata shadda Lemon green yasa hula baka ya nufo ɗakin Kaoeat sai kanshin turare yake.

   zaune ya tarar da ita gefen gado sanye da babban hijab wanda ya suturce mata dukan jikinta, da alama ita wankan ta fito kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai


“Ni zan ɗan shiga gari idan kina bukatar wani abun sai ki kirani ko kiyi ma mai gadi magana”


Kai ta ɗaga masa ba tare da kalleshi ba, shi kuma ya juya ya fice daman daga bakin kofa ya tsaya.

    Wunin ranar mutane ne suka rika zuwa gidan tun daga ɓangaren Momy har zuwa yan'uwanta da abokanin arziki, masu zolayarta suna yi masu mata nasiha nayi mata. sai kusan insha kowa ya watse aka barta ita kaɗai aiko taji kamar ta fasa ihu ko kuma ta bisu amman ina ba dama yanzu rayuwa ta sauya.

       Bayan tayi wanka ta shirya cikin atamfa black and white ta saka bakin hijab ta nufo dinning dan jera kulolin abincin da aka kawo, Tana cikin aikin raji an buga kofa a hankali, sau biyu zuwa uku. yi tayi kamar ba taji ba har sai da aka sake yi sannan tace 


“Wanene?”


Shiru ba a amsa mata ba hakan yasa ta nufi kofar ta buɗe, ga mamakinta sai bata ga kowa ba babu ma mutun balle alamunsa. mai da kofar tayi ta rufe ta juyo zata kunno kai cikin parlour,

   Buga kofar da akayi yasa ta sake juyowa babu kwankwanto ta buɗe kofar da bismillah.

    Minal ce tsaye bakin kofar sanye da bakar riga gashin kanta har godon bayanta tana kallon Kairat da wasu irin kalar idanu manya manya, fuskarta ba yabo ba fallasa. Ba shiri Kairat ta buɗe baki, ta zaro ido tana kallonta numfashinta na kokarin ɗaukewa jikinta kuma ya shiga rawa kamar mazari. 


GUESS WHAT?😱  Please keep voting and commenting on every line 😘bohot bohot shukuriya 🙌 love you all guys 😍




49


Ji tayi kamar ana zooming ɗinta saboda tsoro. Daker ta iya rufe idonta ta furta




"Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un" 


Ta daɗe a haka kamin ta buɗe idon ta sake kallon bakin kofar, neman ta tayi ta rasa, tayi ko sama ko kasa, da sauri ta maida kofar ta rufe tana haki


Saman kujera ta dawo ta zauna dafe da zuciya, 


Toh ko dai gizo idonta yake mata ne?


Shine abunda ta tambayi kanta tana lumshe, toh idan ba gizo ba kan minene tun dai Minal ba dawowa zatayi ba, wannan tsoro ne da kuma rashin sabo da zama ke kaɗai. 

Tana haka taji an sake turo kofar a karo na biyu an shigo parlour, kulle idonta tayi gam, har sai da taji sallamar Saif sannan ta buɗe idon tana amsa masa


"Wa'alaikumussalam" 


"Sannu da zuwa" 


"Yauwa sannu dai ke kaɗai ce a gidan" 


Ya faɗa yayin da yake kokarin karasawa kusa da ita, ita dai har lokacin kanta na kasa tana doubting abunda ta gani, 


"Bari naje nayi wanka sai muci abinci ko?" 


As usual bai tsaya jiran abunda zata ce masa ba ya nufi ɗakinsa ita ɗin bata ce masa komai ba dan abunda take tunani ya isheta. Har yayi wankan ya fito a gurin da ya bar ta ya tararda ita kuma har lokacin kanta a kasa, tsayawa yayi yana kallonta kamar maj karantar abu a fuskarta, 


"Kaiyrat" 


Ya furta a hankali, zabura tayi ta tashi tsaye kamar wanda ta razana, 


"Na'am" 


Sai kuma tayi kasa da kanta, 


"Ga abincin ka can ni na ci nawa" 


Bata tsaya jiran abunda zaice ba ta nufi ɗakinta. Shi dai da kallo ya bita har ta shige sannan ya ɗaga kafadunsa ya taɓe baki ya nufi gurin dinning ɗin. 


Cike da zullumi da fargaba Kairat tayi bachin ta na biyu a gidan, har garin Allah ya waye tunanin yadda taga Minal take har yanzu ta kasa yarda ita ɗince zigo ne idona suke mani shine abunda take ta maimaitawa tana kawar da tsoron dake ranta, bayan tayi Sallah asuba ne bachi mai daɗi ya ɗauke ta bata farka ba sai kusan goma na safe, 


"Alhamdulillahil lazi'ahyana ba'adama a matana wa'ilail-nushur A'uxubillahi minasheidanin'rajin" 


Bayan tayi addu'a tashi daga bachin ta mike tana mika ta nufi banɗaki, bakinta kawai ta wanke sai fuska ta fito ta ɗauki hijab ɗinta ta saka sannan ta nufo downstairs. 

Zaune ta samu Saif a dining room yana cin abinci, karasawa tayi ta risina har kasa ta gaishe shi dan abunda Mummy ta faɗa mata kenan cikin jindaɗi ya amsa yana mata


"An tashi lafiya" 


"Lafiya kalau" 


"Ga abinci nan ki ci ban tsaya jiran ki dan nasan ba zaki ci dani ba" 


Ya faɗa yana kokarin tashi tsaye, tana daga duken tace 


"Yaushe zamu kawo Lil Minal?" 


Tsayawa yayi yana kallonta, 


"Wai da cewa nayi sai nan da sati biyu ko uku kinga kamin lokacin kin ɗan saba abubuwa ba zasu miki yawa ba" 


Jin tayi kamar ta zaburo masa tayi cikinsa da masifa, amman Mummy ta hana ta dan ta faɗa mata wannan ba ɗabi a bace ta matar kirki, bata ce masa 'Eh' ko 'A'a' sai kawai ta tashi ta nufi ɗakinta.

Binta yayi da ido har ta shige sannan shima ƴa tsaya yana tunani miye yanke wannan hukuncin bayan saboda Lil Minal ɗin ta aure shi? Dan da kula da ita, amman shi kan gani yake kamar abun zai zame mata wani irin idan aka kawo mata ita yanzu ganin shekaran jiya nan aka kawota a gidan. Amman kuma miye ruwansa tunda ita take son haka ɗin!

Dakinta ya nufa yana shiga ya same ta dukunkune can gafen gado kamar marar lafiya, ganin shigowarta yasa ta tashi zaune tana jiran abunda zai ce mata.


"Kaiyrat"


Ya kira sunanta kamar ba lakka a jikinsa, shi dai baya jindaɗin yadda take kin sake jikin nan dashi ko kuma nace da gidan. Ta ɗan kalleshi kaɗan yayin da take kokarin amsawa


"Na'am"


Karasawa yayi kusa da ita, cikin yanayi mai kamar ya na damuwa


"Yaushe kike son na kawo miki ita?"


Shiru ta ɗanyi kamar mao nazari can kuma ta ɗan kalleshi


"Gobe?"


Ta faɗa kamar mai neman amsa,


"Allah ya kai mu"


Ya juna ya fice. Wunin ranar wuni Kairat tayi shiru shiru gashi yau gidan ba kamar jiya ba ba mutane sosai, ga kuma abunda yayi mata tsaye a rai tunanin yadda zatayi rayuwa a gidan da kuma yadda zaman ta zai kasance da Saif.

Kaɗan kaɗan take ɗan taɓa fira da kawarta, tana cin kankanar dake gabansu. 


"Sai ɗa kinyi hakuri Kairat ita rayuwar Aure yar hakuri ce musamman irin wannan auren naki, ki kawar da komai da yake ranki ki fuskanci Ubangijinki kisa ni bauta kike ba wai zakiyi rayuwar jindaɗi bane, yadda kake son rayuwa ba zata kasance maka a haka ba baka taɓa samun komai 100%"


Kai kawai Kairat ke ɗaga mata tana sauraren nasihohin da take mata kasancewarta matar aure.

Ana sallah la'asar tayi ma Kairat sallama, wai mai gida yace kar ta daɗe, Dariya kawai Kairat tayi tana girgiza kai ita kuma ta rika zolayarta tana mata maganganu irin nasu na matan aure. Har gurin Mota Kairat ta raka ta bayan ta fice ta tsaya tana kare ma harabar gidan kallo.


Biyar saura kwata, Saif ya shigo gidan ya daɗe a mota sannan ya shigo cikin parlour,


"Ummu Minal fito ga Lil Minal ɗin ki"


Shine abunda ya faɗa yana kallon kofar ɗakinta yayin da ya kai tsakiyar parlour. Lekowa ta fayi kamar wata karamar yarinya wai ta gani indan da gaske yake, aiko da gudu ta karasa saukowa ganin Baby a hannunsa, 

A maimakon ya mika mata baby sai kawai yaja baya da sauri yana mata kallon zolaya


"Wa zaki fara tarba ni ko ita?"


Kallonsa tayi da kyau shi kuma ya sakar mata manyan idon shi, kun kuyar da kai tayi tana murza yatsun hannunta,


"C'mon answer me mana idan kina son na baki ita"


Ya faɗa yana kallon fuskarta. Sake ɗagowa tayi ta kalle shi sai ta sake sanda kai, wani wasan yana yi mata ne dan ta sake jikinta, amman ina bata da niyar hakan. A dole ya mika mata yar dan yadda taga ta dake ɗin nan tsaye guri ɗaya yasan ba cewa zatayi ba


"BISMILAHI RAHAMANIN RAHIM"


Shine abunda ta furta sannan ta karɓi lil Minal ɗin, rumgume ta tayi a kirjinta. Daman can Kairat mace ce mai son ɗiya ballan tana wannan da take da dalilai na sonta. 


"Na gode"


Ta faɗa tana kallonsa idonta cike da hawaye, murmushi yayi mata yace


"Dr tace idan zaki bata nono ki bata nonokin na dama kuma ki wanke shi kamin ki bata sannan tace karki bata nono yanzu sai nan da awa bakwai ko kuma ma ki bari har sai gobe tace duk ba matsala bane Momy tace gobe zata zo tare da wanda zata rika lura miki da ita"


Kasa tayi da kanta alamar kunya, taɓe baki ya ɗanyi shi kan bai ga abun kunya a maganarsa ba tun da ba wata ɓaran ɓaramar yayi ba, a nan ya barta ya shige ɗakinsa.

Sallah ce kawai take sa Kairat ta aje Lil Minal amman duk abunda zatayi tana rumgume da ita.

Bayan Sallar i'sha tayi shirin bachinta ta saka hijab kamar yadda ta saba ta hau saman gadon ta kara jan lil Minal kusa da ita tana mai jindaɗi sai kallonta take tana murmushi da alama ma idon ta biyu duk da idon nata a rufe suke amman sai motsi take da baki tana motsa baki.

Kamar wanda aka ce ɗago ki kalli windo, tana kallo ta ga Minal da siffar da ta ganta a farko kuma nan ɗin ma ita take kallo, wata razanannar kara da saki ta sauko saman gadon ba shiri ta fisgi lil Minal ta bar ɗakin tana ihu.


Keep voting dears 




50


Da sauri Saif ya ɗago kai daga daga gurin da yake zaune ya kalli upstairs, 


“Lafiya.?”


Ya tambaya yana kokarin aje magazin ɗin hannunsa ya tashi ya nufi upstairs ɗin yana cigaba da tambayar ta, bata faɗa masa gaskiya ba sai ta canja maganar,


“Wata na gani gurin windo”


Kunna kai yayi cikin ɗakin yana dube dube. ganin bai fahimci abunda take nufi ba


“Ba fa a ɗakin ba ta waje a windo na ganta”


Windo ya nufa ya shiga dubawa, shikan bai ga komai ba sai kawai yaja windon ya rufe, ya juyo yana faɗin


“Ina jin ita cen dake waje ne kika ango iska ne ke kaɗasu kinga garin akwai hadari, kuma kin bar windin buɗe amman ai kinga babu yadda za'ayi wai ya iya haurowa ta wannan windon tun da ba kasa yake ba” 


Ita dai tana tsaye a bakin kofa rumgume da Lil Minal, 


“Ba komai kiyi addu'ah ki kwanta”


Kai ta ɗaga masa ba dan ta yarda ba komai ɗin ba, har ya fice a bakin kofar take tsaye sai wani abu take da fuska kamar mai shirin yin kuka, can taji ba zata iya jure wa ba, ta juyo ta sauko downstairs.

   Ba kowa parlour sai tv dake ta aikinsa, haka ta zauna sai kalle kalle take kana ganinta kasan babu natsuwa a tare da ita, sai a jiyar zuciya take saukewa, tana haka Saif ya fito sanye da jallabiya dark blue, 


“Gate na dawo mikike so a siyo miki?”


Ya faɗa daidai lokacin da ya karaso kusa da ita


“Bana bukatar komai”


Ta faɗa kamar bata son magana. Sai da ya kai bakin kofa sannan ta ce


“Please karka daɗe”


Juyowa yayi yana murmushi,


“Tunda kina jin tsoro ko.?”


Kasa kasa ta kalleshi ta ɗauke kai. Shi kuma ya fice yana cigaba da murmushin.

     Aiko kamar kar ya fita wani irin tsoro ya kara rufeta, ta rumgume Lil Minal a kirjinta gam ta rumtse ido, jin Lil Minal ɗin na motsi yasa ta buɗe idonta ta ajeye ta saman kujera tasan rumgunar ce wata kila bata so, tashi tayi da nufin kashe tv saboda karar da tayi yawa, sai kawai taga an kashe tv ba tare da ta karasa gurin ba, aiko ba shiri tayi baya baya tana haki.


“Ashe ki baki da amana Kairat? saboda zaki aurar min miji? kin yaudare ni cin cuce ni Kairat kuma ba zan taɓa barinki cikin kwanciyar hankali ba matuƙar kina cikin gidan nan”


A gefenta taji maganar tana juyowa ta ganta cikin bakar siffar da ta saba ganinta, wata mahaukaciyar kara ta saki ta faɗi kasa tana ja da baya sai uhun take ba kakkautawa, aiko sai bin ta take tana son kamota Kairat na ganin ta kusa karasowa kusa da ita ta kara sakin wata irin kara. jin an taɓa ta ta baya yasa ta rika numfashin a jure kamar zai ɗauke


“Nine Kairat ni ne”


Ina! tayi nisa bata jin me yake faɗi sai kaiwai ta cigaba da ihun jikinta na rawa, juyowa yayi ta ganta yasa bakinshi cikin nata ya rike kanta gam, sunyi minti goma a haka sannan hankalinta ya dawo ganin hakan yasa ya sake mata kai ya cire bakinshi daga nata ya rika kafaɗunta yana girgizata,


“Kairat”


Bata iya amsawa saboda numfashinta har yanzu rawa yake,


“Close ur eyes”


Da sauri ta rufe idon kamar mai jiran umarni


“Relax, relax ur body”


Ba musu tayi yadda ya umarce ta


“And stop breathing as long as U can”


Dif numfashin nata ya ɗauke ta daƙiƙin tsayar da shi da tayi


“Now breath”


Ya faɗa yana kallon fuskarta. A hankali ta sauke ajiyar zuciya sannan ta cigaba da numfashinta,


“Open ur eyes”


Tana kallonsa ya ce


“I m here its me okey”


Fashewa tayi da kuka, ya rumgume ta yana mata magana a kunne kamar mai raɗa


“Shiiiiiiii ya isa faɗa min miya faru?”


“Minal na gani Saif”


Bata ɓoye masa ba, ta faɗa masa dan a yadda ra ganta yanzu ya wuce misali gashi har da magana tayi mata. Lil Minal ya nuna


“Wannan ?”


“A'a Minal dai margayiya”


Kai ya girgiza,


“Oh no no no Kairat baki ganta ba tsoro dai kike ji kuma kinsa tunaninta cikin ranki”


Dagowa tayi daga jikinsa daman ba rumgumar take so ba dan kawai tana jin tsoro ne,


“Wallahi na ganta Saif da ido na, ba wai ina tunaninta bane kuma tayi min magana”


“No Kairat kin taɓa ganin wanda ya mutu ya dawo?  babu kuma mai rai baya ganin mamace ba ita bace tsoro ne kawai kike ji”


Shiru tayi tana hawaye, daman tasan ba zai yarda ba babu ma wanda zata faɗa ma ya yarda da ita amman ita tasan abunda take gani. 

  Unkurin tashi tayi, daker ta mike tsaye kafafunta basa iya ɗaukarta. A nan shima ya tashi ya lakamo hannunshi ya rika kunkurunta 


“Let me help you”


Bata masa musu ba dan tasan ba zata iya kai kanta ɗaki ba, da ɗayan hannunsa ya ɗauki Lil Minal ya nufi upstairs. har cikin ɗakinta ya kaita bayan ya zaunar da ita ya kwantar da Lil Minal, sannan ita ya kwantar da ita ya cire mata hijab ya goge mata fuska.


“Ki daina kuka, kiyi addu'ah”


Blanket ya lulluɓa mata sannan ya kashe wutar ɗakin ya fice. Yana fita, taji ita ba zata iya kwana ɗakin ba duk wani rashin karfi da take ji sai taji ya cire mata, da wani irin kuzari ta walkato saman gadon ta sauko ɗaukar lil Minal ne kawai ya zame mata dole aiko tana ɗaukarta ta fice daga ɗakin a guje. ɗakinsa ta nufa ta daɗe tsaye bakin kofar sai tunane tunane take, kamar ta koma kuma taji ba zata iya ba.Sam ta manta da ba mayafi jikinta haka ta faɗa ɗakin tare da sallama. 

  yana zaune saman gado laptop na saman kafafunsa yana dannawa ya ɗago ya kalleta


“Again?”


Kai ta girgiza tana karasa shigowa ɗakin, 


“A a nan dai zamu kwana ni tsoro nake ji”


Wara ido yayi ya kalli gadonsa sannan ya kalleta yana ɗaga kafaɗunsa


“Zo ki kwanta”


Gefen gadon ta nufa ta zauna kasa rumgume da lil Minal tana faɗin


“Nan ya isa”


Kitson kanta ya tsaya kallo yana mamakin yadda ta zauna aka tsara mata dashi ta kuma wanda ta tsara mata shi, kanana ne kuma an tsara shi cikin waninsa da sarkaki dan wani kan wani akayi shi gashi kuma ya sauko mata har baya gwanin sha'awa. bai ankaro ba yaga ta sulale kasa kwance, Laptop ɗin ya kashe ya aje saman dorowa ya sauka ya zagaya gefenta ya ɗuka ya ɗauki Lil Minal


“Idan ke zaki iya jurar tsayin wannan gurin ita ba zata iya ba, kuma ki tashi ki hau kan gado ko ki koma ɗakin ki idan baki yarda dani ba miya kawo ki ɗakina”


Tashi tayi zaune ta ɓata fuska kamar ta fasa kuka ta kalli gadon. bayan ya kwantar da Lil Minal ya kalleta


“Rufe ɗaki na zanyi”


Tasan me yake nufi ta fita ta bashi ɗakinsa, ita kan har ga Allah ba zata iya kwana ɗakinta ita kaɗai ba dan jin take kamar kara ganinta zatayi, ganin babu sarki sai Allah yasa dole ta hau saman gadon ta takure kanta can karshen gadon ta kundule cikin nayafin rufa kamar wanda aka cilasta.

   Taɓe baki yayi yaje ya rufe kofarsa ya kashe wutar ɗakin, yazo ya kwanta ya lulluɓe shi da Lil Minal. 


    WASHE GARI..... 

Bayan yayi sallah asuba ya tashe ta tana faɗin 


“Tashi kiyi sallah”


Cikin gigin bachin ta tashi, har zatayi mika sai ta tuna ba ɗakinta take ba da sauri ta murza ido ta ɗauki lil minal ta nufi kofar fita. Shi dai kallonta kawai yake har ta fice.


         Bayan ta kare Sallah, ta sake komawa bachi. bata farka ba sai takwas har da kusan rabin, bathroom ta shiga tayi wanka, bayan ta shirya ta sake komawa banɗakin ta wanke nononta kamar yadda Dr tace bayan ta fito tazo ta ɗauke ta ta ɗaga hijab ɗinta da nufin bata nonon sai kuma ta kasa, ta daɗe a haka sai tunane tunane take, ba karamin jihaɗi tayi ba wajen ɗaurewa ta saka mata nonon a baki, kamar mai nema ta kama da karfi tana sha, runtse ido Kairat ta rikayi kamar mai jin zafi tana dantsar baki tsigar jikinta sai tashi take. Jin motsin shigowar mutum yasa ta buɗe idonta tana ganin Saif tayi saurin sakin hijab ɗin tana faɗin


“Sai ka shigo min ɗaki ba Sallama”


“Eh ya ranki?”


Ya faɗa kamar mai jiranta shi daman tun jiya yaga taken taken ta sam bata yarda dashi gani take kamar wani abu zaiyi nata da ya ɗan motsa sai ta tashi zaune tana kallonsa hakan kuma ba karamin kona masa rai yayi ba. Fitar da ita tayi ta aje saman gadon tana ɓata fuska


“Daukarta ki bata nonon”


Banza tayi masa. ganin yadda ya nufo ta yasa ta ɗauke ta dan bata san nufinsa ba, ta mayar cikin hijab ta cigaba da bata nonon,

  Ta ɗai san ba xai doke ta amman kuma zai iya cewa sai ya ba lil minal ɗin nono da kansa. kwafa yayi ya zauna gefen gadon kusa da ita ya tsare ta. ita kuma ba damar tayi masa magana tasan jiraye yake da ita. Jin Sallamar Mummy yasa shi tashi ya nufi parlour yana amsawa,


“Sannu da zuwa Mummy kece da safen nan haka?”


Ya faɗa fuskarsa shimfiɗe da murmushi yana karasa saukowa downstairs, tana kokarin zaunawa ta ce


“Nice break fast na kawo muku ta kuma mai yima baby wanka ina ya ta”


“Tana ciki”


‘Kairat...’


Ya kwala mata kira, sai gata ta fito ɗauke ta lil Minal ɗin, tana ganin Mummy ta sauko da gudu tana murmushi,


“Yi a hankali mana”


Ya faɗa yana kallon Lil Minal, ita dai bata kula shi kula shi ba har ta karasa gurin mummy ta aje Lil Minal ta rumgume Mummy, sai kuma ta fashe da kuka


“Mummy i miss you”


“I Miss you too daughter ya gidan?”


“Mummy gidan ba daɗi ni ba zan iya zama ba”


Mummy ta rika fuskarta, 


“Zaki saba Kairat komai da sannu sannu ake dainawa”


“A a Mummy tsoro ake bani”


“Tsoro..?”


Mummy ta faɗa tana kallon Saif. Murmushi yayi Yace 


“Mummy tsoro ne take ji, ta cika tsoro wai Minal take gani ina ganin tasa tunanin ta da yawa ne”


Mummy ta rika hannunta suka zauna fuskarta ɗauke ta damuwa,


“Minal kuma mafarki dai kike yi ko?”


“Mummy ba mafarki bane ganinta nake yi har da magana tayi min jiya”


“What .? no Kairat ya za ayi ki ga wanda ta rasu ba zai yiyu ba”


“Mummy idan ina ɗakina take zuwa”


“Toh da Saif ba ganta ba idonki ne Kairat”


“Mummy ba ido na bane ina ganinta a zahiri ai ba ɗaki ɗaya muke kwana da Saif ba”


“Saboda me?”


Shiru tayi ta ɓata fuska,


“Baki san ba kyau raba gado da miji ba ko wani abun ya faru ne”


Kai ta girgiza alamar a a, mummy tace


“Toh akan me zaki rika kwana ke kaɗai? wannan ai ba ɗabi'ah bace dole ki rika gane gane”


Talatu tace 


“Hajiya karfa kiyi latti kinsan kince tara da rabi zaku shiga meeting”


Mummy ta kalli Kairat


“tashi ki ɗauko abu Talatu zatayi ma Lil Minal wanka, ita zata xauna a nan tana kula da ita kamin ki iya yi mata wanka”


Saif ya ɗauki lil minal ya kalli Talatu, 


“Muje na nuna miki ɗakinta”


Ba musu ta tashi suka nufi ɗakin. Bayan sun shige Mummy ta kalli Kairat tace


“Kar na sake jin kun rab gado da mijinki sai kace ba wayayi ya ba idan kika saba masa da hakan ke ce zakiyi nadama nan gaba, baki san babu kyau ba? muharraminki ne fa Kairat ɗan Allah karki sake haka kinji?”


Kai ta ɗaga tana kuka mai kamar na shagwaɓa kuma bana shagwaɓa ba.


“Ki rika addu'ah kinji? I will do something about it”


“Toh Mummy amman ba zaki daɗe ba zaki dawo ko?”


“Eh ba zan daɗe ba”


“Promise”


“I promise”


Rumgume Mummy tayi tana wani narkewa jikin mummy kamar zata shige. Saif ya fito daga ɗakin, karaso kusa da su yana kallon Kairat ya taɓe baki. 


“Tashi ki jera abincin ku a dinning”


Mummy ta faɗa tana shafa kanta, tashi tayi ta nufi dinning ɗin tana share hawaye. Mummy ta kalli Saif 

“Kairat amana ce a gare ka Saif farincikinta shine nawa ka kula da ita sosai kuma kayi hakuri da ita da sannu komai zai zama daidai”


Kai ya ɗaga mata ya tashi tsaye ganin itama ta tashi ɗin. da sauri Kairat ta karaso gurin ta rika hannun Mummy kamar wata karamar yarinya


“Mummy tafiya zaki yi?”


“Eh sai na dawo kinji ki rika addu'ah”


Wani irin ɓata fuska Kairat tayi taji kamar ta bita Saif dai sai kallonta yake har Mummy ta fice, sannan yayi dariya yaja kumatunta.


“Sagarta ko miyasa baki bita ba?”


Rufe fuska ta ɗanyi tana share hawaye. Hannunta ya rika


“Muje mu ci abinci”


Da kansa ya haɗa mata tea ya tura mata gabanta, sannan ya haɗa nashi.



KARFE UKU DA MINTI GOMA SHA DAYA..........


Safiyyah ta digo gidan, da Sallama ta shigo parlour fuskarta ɗauke da murmushi. haɗa baki sukayi da Talatu gurin amsa mata. kallo ɗaya Kairat tayi mata ta ɗauke kai kamar bata san inda ta fito ba.


“Amary bakya laifi”


Ta faɗa tana kokarin xunawa, Kairat dai bata ce da ita uffan ta sai kallon tv take, Talatu kuma na rumgume da lil Minal. Taɓe baki Safiyyah tayi tana kallon Falon


“Yaya na nan”


“Baya nan”


“Ina yaje?”


“Nima bai faɗa min ba”


A tsatsaye Kairat take amsa mata tambayarta still bata kalleta ba. Talatu na ganin hakan ta tashi ta nufi ɗakin da Saif yace mata shine nata.

  Safiyyah ta tsire baki


“Wai ya kike min magana kamar baki san wacece ni ba?”


Sai a lokacin ta kalleta


“Na san wacece ke mana, sheɗaniya kuma makira”


Tashi Safiyyah tayi tsaye 


“Wannan wace irin magana ce haka kardai ace kema shaye shayen kike.”


“Asibiti nake sha, miya kawo ki gida na?”


Kyalkyalewa tayi da dariya


“Gidan ki ko gidan yayana daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zaki tun tafiya batayi nisa ba har kin fara kiran shi gidan ki?”


“Akwarai gidana ne saboda ni aka auro aka kawo”


“Karki manta kamin ke am kawo wasu, kuma hakan yana tabbatar miki da ana canja mata ba a canja yar'uwa ba”


“Waɗan can, an canja su ne ta wani dalili, ni ko zama daram dam kujerar karfe fita ki bar min gida makira annamimiya”


Wani irin zaburowa Safiyyah tayi kamar zata mari kairat


“Ni ce makira?”


“Eh sunan ki ne ko kin canja wani?”


Tsaye tayi suna kallon kallo akuya kallon kura, ita Kairat, jin parking ɗin motar Saif yasa ta jindaɗi tana jin motsin taɓa kofar palo ta fashe da kuka. cuke da damuwa ya karaso kusa dasu yana tambayar ba'asi


“Lafiya miya faru?”


“Mari na tayi tana faɗa min maganganun banza”


Kairat najin haka batayi wata wata ba ta watsa mata marin sannan ta nuna ta da yatsa


“Ita giwa tafiyar ta bata ɗaya data saura ni makircina a fili nake yinsa kuma babu yadda za'ayi”


Zaburowa Safiyyah tayi zata rama Saif ya rike ta,


“Wai miye haka ne”


Safiyyah kuma dai sai kunce kuncen ta rama marinta take, can Saif ya warguna ta, ya tura ta 


“Tafi gida Safiyyah wuce”


Tsaye tayi tana yima Kairat wani mugun kallon sannan ta juya ta fice cike da jin zafin marin da Kairat tayi mata. bayan ta fice Saif ya kalli Kairat rai a ɓace


“Miye haka dan Allah daga zuwanta sai faɗa?”


“Toh waya ce tazo dole ne sai tazo”


“Dole ne tazo mana tunda ɗan'uwanta kike aure kuma ko bata zo dan ki ba xata zo dan lil Minal”


“Bama bukatar ta ni da lil Minal karta sake zo mana gida, bata da wata alaka da mu”


“Ni tana da alaka da ni Yar uwata ce ke kuma matata ce ko wacce matsayin ta daban, tana da yanci ta shigo gidana kamar yadda kike da yancin zama, beside Safiyyah ma ba wata mafaɗaciya ba ce i know her sai dai idan ke kika taɓa ta”


Hawayen dake makkale a idonta ne suka zubo, ta kalleshi 


“You take her side”


Kai ya girgiza mata,


“This is not the right time to take anyone side, Kairat bai kamata a ce kin fara wannan halin yanzu ba, duka duka yaushe kika zo gidan nan?”


Bata ce masa komai ba ta juya ta nufi upstairs. Zaunawa yayi saman kujera yana shafa kansa, baya nufin ɓata mata rai sai dai kuma ba zai bata damar ta raina masa yan'uwa ba duk da shi ma ɗin ba son xuwan Safiyyah yake ba, amman ba zai nuna mata ba dan karta raina masa yan'uwa dan da haka ne wasu matan ke samun kofar rai na yan'uwan miji. 


     Da dare tana Zaune parlour tana buga Candy Bom a waya. Saif ya fito daga ɗakinsa rike da waya a hannu ya nufo gurin da take zauna ya ya fisge wayar, tana kallonsa yace


“Coffee please”


Tashi tayi ta shiga cikin ta haɗa masa ta kawo masa kallonta yayi a hankali sannan ya mika hannu ya karɓa yana faɗin


“Mummy ta kira ni yanzu tace kin kirata kina kuka kuma baki yi magana ba kin kashe, miyasa kika kirata?”


Zaunawa tayi tana shafa gefen fuskarta


“Ba komai”


Ta faɗa ta murya kamar ta shagwaɓa. gyara zamansa yayi yana kallonta


“Ita gaskiya dole a faɗe ta Kairat, Bana nufin ɓata miki rai kuma ita dole ne na bata rashin gaskiyarta”


Bata ce masa komai ba ta aje remote ɗin hannunta ta ɗauki lil minal ta kalleshi


“Sai da Safe”


Ta tashi ta nufi upstairs. da ido ya bita har ta haye a maimakon yaga tayi ɗakinta sai kawai yaga ta shiga ɗakinsa, Murmushi yayi ya cigaba da kallon yana kurɓa tea a hankali.


      Ba'ayi minti goma da shigarta ɗakin ba yaji ta fasa ihu ya kalli upstairs ɗin


“Oh my goodness”


Ya faɗa yana kokarin aje tea cup ɗin ya tashi ya nufi ɗakin.

    Wannan karon ya tabbatar da gaske Kairat tana ganin wani abu dan yadda ya tarar ana janta tana jan kanta ta rike gado gam sai uhun take, da sauri ya rikata shima tana janta da dukan karfinsa, janta taji ana kara yi sai dai baya ganin mai jan nata ita. komawa a'kayi gurin Hijab ɗinta ana janta da karfi kamar za a fisge mata fuska, cikin sauri ya cire hijab ɗin ya ɗauke ta kamar jaririya ya mai da gefe ya rumgume ta. 


   Hijabin aka fisga ya faɗa ta windon baya, Sai sa kallon ikon Allah yake wai yau a ɗakinsa. ita ko sai kamkamesa take tana faɗin 


“Saif fitar da ni daga ɗakin nan”


“Okey okey”


Ya faɗa yana kara rumgume matarsa. saukowa yayi da ita downstairs, har lokacin suna rumgume da juna, a palo suka tararda Talatu sai rabon ido take tana ganinsu tace


“Lafiya nake jin ihunta?”


Kai ya ɗaga mata


“Lafiya kalau Baba jeki ɗakin ki”


Ba musu ta shige ɗakinta ba dan ta yarda ba komai ɗin ba, wayarsa ya dake kan kujera ya ɗauka ya shiga dialing wata number. bugu biyu aka ɗauka,


“Shigo ina neman ka”


Haka kawai ya faɗa ya kashe wayar. ya cigaba da shafa ta, ita kuma sai rera kuka take a hankali.

  bayi mintu biyu ba aka buga kofar parlour Saif yace


“Yes shigo”


Yana shigowa ya kalle shi yace 


“Ka zaga kai da mutanen ka gurin ita cen nan ku duba min gurin komai kuka gani ku faɗa min”


“Yes Sir”


Ya juya da sauri ya fice. saman kujera Saif ya zauna still yana rumgume da ita sai tunani yake, daker ya samu ta sake shi ta zauna saman kujera amman bata yarda tayi nisa dashi ba dan kunkurunta na gugar nasa sam ta manta da wani abu wai kunya da kuma gudunsa ta take.

   Bayan kamar mintu na arba'in suka sake jin an buga kofar,


“Yes come in”


Saif ya faɗa, a nan mutunen ya turo kofar ya shigo bayan ya karaso ya aje hijab ɗin Kairat da wani kololon abu kamar fatar damisa. wani irin tuma Kairat tayi kamin Saif ya ankaro har ta haye saman jikinsa ta rumgume shi gam.


“Ga abunda muka gani babu kowa a gurin mun dai samu rame sai muka tona shine muka ga wannan”


Mutunen ya faɗa yana kallon Kairat kamar zaiyi dariya kuma bai yi ba, 


“Okey jeka dashi can gurin ka idan an tashi zan neme ka”


Tashi yayi ya fice. sannan Kairat ta ɗago ta sauka saman jikinsa. kirjinta ya kalla yana murmushi, sai tasa hannu ta kare gabanta ta ɗan noce kai. taɓe baki yayi a ransa yana 


Ba yanzu kika gama rumguma ta ba


Tashi yayi. tana ganin hakan ita ta tashi. Daren kin yarda tayi su kwana ɗaki a dole palo suka kwana, kuma guri ɗaya jikinta na gugar nasa, da taji ɗan motsi ta shige masa. Shi kuma ya samu abunda yake so an ba kura fiɗa. lil Minal kuma ta kwana hannun talatu.


                           ***        ***    ***

     A tare sukayi sallah asuba, suka koma bachi amman wanna karon a ware sukayi bachi dan taga safiya ce sai ta ware kanta can gefe tana bachinta.

   Ringing ɗin wayarsa ne ya katse masa bachi, ganin number Momy yasa shi saurin ɗauka cikin muryar bachi.


“Hello Momy”


Ban ji me akace masa ba na dai ga ya tashi amman gadon yana faɗin


“Okey gani nan zuwa”


Banɗaki ya shiga bayan ya aje wayar ya watsa ruwa ya fito a gagauce ya shirya, ya fisa turare. har ya kai bakin kofa sai kuma ya dawo ya duka a hankali yayi ma Kairat kiss a goshi ya fice.


      

Cikin yan mintuna ya isa gidan bayan yayi parking ya shiga cikin parlour. Ihunta ne ya amsa masa sallamar da yayi ya kalli Momy da hankalita ke tashe yace


“Wai me ya same ta?”


“Wallahi ba mu sani ba, ni dai ina ɗaki naji ihunta shi kenan fa abun har yanzu kuma bata magana sai kuka da ihun nan da take”


Momy ta faɗa kamar zatayi kuka, Hannayesa ya zuba cikin aljihu yana sauke ajiyar zuciya


“Da yaushe abun ya same ta?”


“Jiya da dare misalin shaɗaya na dare”


Tsaki yaja ya nufi ɗakinta yana girgiza kai.




WHO MISS ME? 😢 PLEASE VOTING AND COMMENTING ON EVERY SINGLE LINE 



51



Can karshen gefen gado ya hango ta, ta wani kwalo ido jikinta sai rawa yake idon nata yayi wani zurfi kamar wanda ta shekara bata ci abinci ba. Karasawa yayi kusa da ita ya risina, suna haɗa ido ta fashe da kuka


“Safiyyah”


Bata amsa kiran da yayi mata ba babu ma alamun zata iya magana, dan ko kukan da take idon ne kawai yake hawaye, nan take tausayinta ya rufe sh, ajiyar zuciya ya sauke ya kalli Momy


“Yanzu miye abun yi?”


Cike da damuwa Momy tace


“Ina ganin asibiti zamu kai ta muji ko minene”


Kallonta ya sake yi kamin ya taso shi da Momy, A parlour suka dawo ko wannne fuskarsa ɗauke da damuwa, Saif ya ciro wayarsa dake cikin aljihu ya kara a kunne,


“Ya a'akayi?”


“Kana ina?”


“Ina waje”


“Waje?”


“Eh tare da Lubna ba”


Katse wayar yayi, ba ayi minti biyu ba Nasir ya shigo falon tare da Lubna kusa da Saif ya zauna yana gaisawa da Momy, sannan ya tashi ya leka ɗakin Safiyyah,Bai daɗe ba ya fito ya sake zaunawa a inda ya zauna ɗazun yana faɗin


“Anya ba shaye shaye take ba?”


Momy tace


“Nasir Safiyyah bata shaye shaye ban taɓa gani ba.Kin kira Gwaggon taku?”


Ta karasa tana kallon Lubna


“Eh na kira ta tace ga tana nan zuwa”


Nasir ya girgiza Kai


“Idan aka je asibiti ai maji amman ni nasan babu yadda za ayi haka ya kamata ba tare da dalili ba”


“Bance maka babu dalili ba amman ni nasan Safiyyah bata shaye2”


Cewar Momy. Sako naji alamun ya shigo a wayar Saif yana duba ba ya tashi


“Momy bari naje naga wani, idan kunje asibitin duk yadda akayi sai ki kirani a waya”


Kai kawai ta ɗaga masa ya taso shi da nasir suna tattauna maganar.


     Two Hours Later

Ya nufo gida bayan yayi fakin ya nufi kofar falon, tsayawa yayi yana dannan bell ɗin gidan kamar wani bako, buɗe kofar da tayi yasa ya ɗago kai daga duniyar tunanin da yake ya kalleta. sanye take da katon hijab idonta ya ɗanyi jan, fuskarta kuma ta kumburo alamar tayi kuka. ido ya sakar mata kamun ya kai hannu ta rika fuskarta 


“Me kuma ya same ki na kuka? mi ya faru?”


Janye fuskarta tayi ta juyo ya shigo cikin falon,


“Ba komai”


Ta faɗa tana kokarin zama,


“Kinyi breakfast?”


Ya tambaya yayi da ya zauna kuaa da ita shiru tayi ba amsa hakan tasa ya kai hannu ya rika hannunta ya shiga murza yatsun ta


“Na ɗauka ba a baki tsoro sai cikin dare?”


Dayan hannunta tasa ta share hawayenta


“Ba ita na gani ba, wani mafarki nayi marar kyau kuma da na tashi kai na gani tsaye gefen gado kana min murmushi ina unkurin tashi.sai naga kafafunka ba na mutane ba”


Wani dogon numfashi ya sauke ya busar da iskar bakinsa sannan ya soma magana alhankali kamar mai magana da yarinya,


“Kairat yaushe rabon ki da addu'ah?”


Shiru tayi ba amsa,


“Kin dai na ko?”


Ya bukata, ciki ciki ta amsa masa


“Ina yi”


“No Kairat idan kina addu'ah babu abunda zai same ki, Kairat naga kina da karatun ki Suratul Bakara ɗin nan zaki iya karanta ta kuma duk gidan da aka karanta ta sai sheɗan ya kwana arba'in bai leka gidan ba toh ina ga sauran abubuwa masu cutarwa?.

      Idan ma ba zaki iya ba akwai kula uzai irin kulhuwallahu ahad, kul a'uzu birabbi falaq da birabbin nas, ko wanne uku da safe da maraice ce ga kuma a'uzu bikalimatillahi, Bismillahi lazi ta ma uku da safe uku da yamma ko kuma hasbunallahu ɗari huɗu da hansin safe da yamma kinga hasbunallah ɗin nn ba dai abu mai cutarwa ba sannan zaki rika ganin haske cikin lamarin ki kuma duk abunda ya shige miki duhu sai Allah ya bayyana miki shi in kuma damuwace sai Allah ya yaye miki idan kuma ba zaki iya ba ki rika yin bakwai da safe bakwai da maraice ki rike ayatul kursiyu da Amana rasullu wallahi babu abunda zai same ki matukar kina karanta su daidai sannan ki riki istigifari ta salati suma haske ne so sai”


Kai ta ɗaga masa cike da gamsuwa, ɗayan hannunta ya riko


“Ina fatar ba zaki sake cemin Kinga wani abun tsoron ba?”


Kallonsa tayi ya sakar mata murmushin sa mai kyau da tsada,


“Kuma ina fatar za a rage samin hijab ɗin nan dan Allah cikin gida”


Kallonsa ta sake yi ta ɗauke kai ta tashi ta nufi ɗakinta, shi kuma ya jingina da kujera yana lumshe ido, can ya tashi da sauri kamar wanda ya tuna da wani abu ya nufi ɗakinta.

   Tana kokarin ɗaura tawul ya shigo ɗakin da ala wanka zata shiga, da sauri ta ɓoye bayan labule kasancewar ɗan karamin tawul ne jikita kuma bai ɗauru kirjinta sosai ba, 


“Lafiya?”


Ta tambaya still tana ɓoye bayan labulen, shiru yayi kamar ba xai ce komai ba wata zuciyar sai ce masa take yaje ya buɗe labulen wata kuma na hana shi,


“Momy tace ki fara girki yau”


Ya faɗa bayan yayi gyaran murya,


“Toh naji”


Ta faɗa irin ta kosa ɗin nan ya fita.Murmushi kawai yayi ya juya ya fice, sai da taji rufewar kofar palon sannan ya leko ganin da gaske ya fita yasa ta fito ta faɗa toilet ɗin a guje kamar wanda aka ce ma dawowa zaiyi.


                         ***           ***            ***

Kairat na zaune palo taji an danna bell, kofar kawai ta kalla ta ɗauke kai, dan wuyar tashi take ji kuma bata da tabbacin mai danna bell ɗin maybe ma tsoro ne ake son bata, sai da aka danna bell ɗin yafi a kirga aka koma buga kofar sannan ta tashi ta nufi kofar. tana buɗewa ta buga ihu


“Oyoyo Kawalli romon jaɓa”


Ture ta matar tayi tana dariya


“Ni dai karki ji min kina fama da amarci”


Hannunta Kairat ya janyo suka shigo cikin parlour tana faɗin


“Ni dai bana son lalata wane irin amarci kuma?”


“Ga shi nan sai wani haske kike na sani ko har kin samu”


Dariya Kairat tayi sosai


“Oh Maman Namra baki raɓo da abun dariya kin fara halin ki ko?”


“Ba wani hali sai gaskiya wanene zai aje ki a gida har na tsawon wannan lokacin ace ba komai”


“A a ni dai ba komai ni dai ya gida ya yara?”


“Lafiya kalau yara suna ƙkaduna ban zo da ko ɗaya ba”


“Aiko dai baki kyauta ba da kinzo mana ko da Namra”


“Yayan naku ne ya hana kinsan halin shi wai dan kar naje na zauna”


“Oh Yaya manya har yanzu ba a daina halin nan ba”


“Haf za a daina abunda aka saba ne? ai kara miyi lokacin mu karya wuce ku ba gashi kuna naku ba”


Kai Kairat ta girgixa


“Oh Wannan matar ba zaki daina wannan halin ba bari naje n ɗora girki tun da kinzo”


Ta ɗan wara ido


“Ba dai girkin rana ba ko?”


“Shi fa yau ma zan fara”


“Kuma kikayi latti haka? ko maigidan naki ba a gida yake cin abinci ba?”


Dariya kawai tayi ta nufi kicin ɗin.

     Bayan ta kare girkin ta zubo musu taliya suka xauna palo suna ci, sai fira suke firar yaushe gamo!

    Bayan sun gama cin abinci taje ta saka hijab ɗinta ta ɗauko lil minal tana bata nono kwalo ido matar tayi


“Aiki idan zaki bata nono rufewa kike?”


“Eh bana son ana gani”


“Toh miye abun ɓoyo naga dai ni yar uwarki ce mace shi kuma mijin ki ne”


“Shima ai ina rufewa idan ma yana gida Hijab naƙe sawa”


“Akan me a a gaskiya ki daina wannan ai shi kike cutarwa”


“Haƙa ɗazu yake ce min wai na dai na saka masa hijab cikin gida”


“Aiko ke ko dai ba ki kyauta ba baki san wasu mazan basa son haka ba? karki saba ma mijinki da abunda bai saba ba ki daina nisantar mijinki kinga body contact yana matukar muhimmaci, da kuma saka tufafin da zai kama jikin ki ka fitar da halintar da Allah yayi miki ga mijin ki ki daina ɓoye masa jikin ki

  sannan bari na baki wani sirrin idan zaki ba mijin ki abu ki rika basa a baki ko kuma kiyi masa da hannu sannan ki karanta masa bismillah kafa tara ki tofa ga abunda zaki bashi ko da ruwa ne hakan ma wata mallaka ce ta sosai duk abunda kika san mijin ki na so kiyi kokarin ganin kin aikata masa shi idan kika san lokacin da mijin ki zai dawo toh kiyi saurin yin wanka ki shirya ko da zaizo ya tararda ke kamar amarya abincin da kika san mijin ki naso kuma kiyi kokarin ganin kin tanadar masa shi shi koda yaushe kinga wannan nono da kike ba yarsa wallahi na tabbata ba karamin daɗi yake ji ba, shima kuma kansa yana bukatar kulawa ki rika kula dashi tun da naga kina da mai kula miki da Minal ɗin, ki rike yan'uwansa kamar naki ki rike mahaifiyarsa kamar taki ko ko abu yayi miki kar kiyi saurin nuna masa fushin ki kar ki zamo mace da ko yaushe zata ta kai karar mijinta gida kar kuma ki zamo cikin matan dake faɗar sirrin mijinsu. kinga shagwaɓa tana sa namiji ya so ki fiye da tunanin ki idan zaki masa magana ki rika masa cikin lafazi mai daɗi kuma mai kamar shagwaɓa ki rika shige masa a jiki idan har yana gida karki yarda ki zauna ba a kusa dashi ba ko kuma saman jikinsa idan kuma dare ne ki kwanta a kusa dashi sosai ta yadda idan ya kwana shi kaɗai ko kuma da wata zai rika tunawa dake, ki koya ma kanki cin fruit da madara suna da muhimmaci sosai a jiki mace ki kuma kasance cikin kanshi koda yaushe, ki rika masa kunya hakan nada kyau ko da kin shekara ɗari da mijinki hakan nasa kauna kuma mijinki zai miki kallon cikakkiyar mace sai dai kuma ba irin wannan kunyar take mai cutarwa ba sannan idan yana miki faɗa karki tamka sa har sai ya sauka sai ki zauna ki fahimtar dashi idan kuma a waje ne aka ɓata masa rai sai ki kwantar masa da hankali kuma ki zama mai yawan kyauta ga kowa hakan zaisa ki zamo tauraru ga yan uwan mijinki da kuma makota kuma ki zama mai yawan fari da ido a gaban mijinki”


Zugum Kairat tayi tana kallonta har ta kai aya sannan ta ja numfashi


“Ki ce littafi zan ɗauko kina faɗa min ina rubutawa”


Dariya tayi tace 


“Zaki iya haddace wa ai, amman dai kinga wannan sirrin idan kika rika shi zaki mallaki mijin ki babu boka babu malam idan ma gaba ya karo miki kishiya ita bata saba da wannan ba sai yaga dabam sai ki ga kullum dai kece dai wannan abun ne yasa matan waje ki karɓe masa mazaje ko kuma idan aka miki kishiya sai ace ta kwace miji wata kuma ba magani wallahi wannan abun kawai ya ishe ta”


Dariya Kairat tayi


“Lallai Ummu Namra kice da wannan kika mallake mana Abban Namra”


“Sarai baki ba baya son nayi nisa dashi ba? gobe gobe fa zan koma bai yarda na kara ko kwana ɗaya ba”


Ta faɗa tana wara ido. Sun ɗan daɗe suna fira sannan ta tashi tayi shirin tafiyaƙalheri Sosai Kairat ta haɗa mata ta kuma rakanta har gurin mota.


     


    DARE.........


Tana zaune ɗakinta tana ba Lil Minal Nono Saif ya shigo, rasa tayi inda zata saka kanta kamar ta tashi ta ɗauko mayafi ta rufe jikinta sai dai kuma ba dama tun da har ya zauna kusa da ita yana kallon Lil Minal. Ita kuma duk ta tsargu gani take ita yake kallo aiko nan da nan tayi saurin rufe rigarta daman lil minal ɗin tayi bachi.


“Idan an gama da ita ayi dani Please” 


Ya faɗa ba tare da ya kalleta ba, Kallonsa tayi kaɗan 


“Tea” 


Yana faɗa ya tashi ta nufi kofar fita. Kwantar da lil minal tayi sannan ta tashi ta nufi kicin. Cikin kankanen lokaci ta haɗa masa ta nufi ɗakin nasa ba karamin jihadi tayi ba na shiga ba tare da lullube a jikinta ba. Cikin ciki tayi sallama ya amsa mata tana kallon laptop ɗin gabansa. Tana kokarin aje kofin ya mika mata hannu alamar ta bashi ba muau ta mika masa sai ya haɗa da hannun nata ya karɓa ita kuma ya zaunar da ita saman gadon kusa dashi ya sauko da kafafunsa yana sauke ajiyar zuciya. 

    Kaɗan ya kurɓa tea ya aje ya kalleta


“Thank you” 


“Always” 


Ta faɗa tana unkurin tashi. Tashi shima yayi yana murmushi, 


    “Bari naje gida na dawo Momy tana son gani na Safiyyah ce ba lafiya me kike so na kawo miki”


“Ba komai”


Ta faɗa kamar bata son magana, shi dai da kallon ya bita har ta fice sam baya jindaɗin yadda take kin sakewa dashi bai san abunda yasa ba sai yaga kamar zaman gidan baya mata daɗi.


                          ***         ***         ***

     A palo ya tararda Momy kamar yadda ta saba sai dai wannan karon har da Gwgaggo da Shafa da kuma wata yarinya da bata wuce sa'ar Shafar ba, Nasir na gefe yayi zugun yana kallon yarinyar.

    Saif sai da ya gama kallon takardun hannunsa sannan ya kalli Momy yace


“Toh Momy ko mu fitar da ita waje? tunda su nan sunce babu abunda yake damunta”


“Wannan lamarin bana asibiti bane Saif al amarun jinnu ne”


Gwaggo ta faɗa


“Kamar ya?”


Nasir ya taɓe baki Ya nuna yarinyar dake.zaune gurin yace


“Wai wannan yarinyar ko aljanunta suka ce wai aljanu ne.daga gidan ka suka fito shine suka yo nan sai suka tarar ita ce kawai ba tayi addu'ah ba shine suka shige mata”


Wani kallo Saif yayi ma yarinyar. sai kuma ya kalli Momy ya kalli Nasir. 


“Ni fa ban gane kan wannan maganar ba”


Momy tace


“Wai ajiyar su ce a gidan mafita shine akwai a barsu su ɗauki ajiyar tasu sai su kyale Safiyyah, idan kuma ba haka ba wai har Matar ka sai sun taɓa kuma sunce kar a kuskur a banye ajiyar su zasu ɗauki abun su da kansu”


“Rubbish”


Saif ya faɗa yana murmushin gefen fuska dan shi bai yarda da wannan labari ba. tashi yayi 


“Momy bari naje da safe zamuyi magana yanzu kan kaina yana ɗan ciwo”


“Wannan fa ba maganar wasa bace Saifullahi”


Nasir dai in banda taɓe baki babu abunda yayi, Saif bai saurare su yasa kai ya fice. Momy kuma ba tayi unkurin hana shi ba dan ita kanta bata yarda da wannan lamarin ba.



     Yayi kaɗan ko? Don't mind na muku alkawarin wani tomorrow morning just keep voting and commenting 




52 



Ko da shigo Kairat har tayi shirin bachin ta tana kwance saman gadonsa Iil Minal na gefenta, a zatonsa tayi bachin da gaske sai ya kai hannu ya shafa fuskarta yayi mata kiss yayi ma lil minal.


“I love you all”


Ya faɗa sannan ya xaga ɗayan side ɗin ya hau saman gadon yana picking call ɗin da alayi masa. Sai da Nasir ya kai Aya sannan yayi dariya yace


“Ni ma ai nasan kuɗin su kawai take son taci yaushe rashin lafiyar ta kamata a barmu mu gama na asibitin mana idan ba mu dace da tukuna a kawa mana wata maganar aljannu,

   Amman wannan ni sam ban yarda da ita ba kuma kaji wani iskanci a rasa inda za a ce sai gida na”


Sun ɗan daɗe suna wayar sannan ya kashe ya rage wutar ɗakin ya kwanta. washe gari suna cikin breakfast ɗaya daga cikin yaran gidan suka ya shigo bayan ya gaida su ya kalli Saif yace


“Wai wani ne a waje yana son ganin Madam ni kuma ban yarda dashi ba shiyasa ban barshi ya shigo ba”


“Wanene?”


Kairat ta tambaya,


“Wai ko shine Abokin Minal”


“Jeka ce ya shigo”


Da sauri Kairat ta faɗa Saif ya girgiza masa kai


“Karka barshi ya shigo”


Sai bayan ya fita ta kalli Saif kamar zatayi kuka


“Miyasa ka hana shi ya shigo dan Allah ka barsa wata kila yana da abun cewa”


Baice mata komai ba ya tashi ya nufi hanyar Stairs, da sauri ta sha gabansa


“Dan Allah Saif ka barsa ya shigo ina son nayi masa wasu tambayoyi”


Kafaɗunta ya dafa


“Me zaki ce masa me zai zo nema gare ki? gurin Mummy ya kamata yaje”


“Please idan baka son ya shigo maka gida ka barni naje na gansa”


“Fine”


Ya faɗa ba dan yaso ba ita kanta tasan ba da son ransa ya amsa mata ba. har ta juya sai kuma ya riko ta ya rungumeta a kirjinsa


“I can't I'm sorry”


Lumshe ido tayi, sam bata ji daɗin hakan ba sai dai kuma babu yadda zatayi tunda wanda yake da iko da ita ya hana ta.


    MUMMMY..........

A gajiye ta dawo daga aiki, wanka ne kawai ya zame mata dole daman hakan take duk ta dawo aiki ruwa kawai take kurɓawa ta wanka sannan ta ci abinci. bayan ta gama cin abincin ta buɗe laptop ɗinta tana nazarin wasu abubuwan. Sallamar Tsohuwa ce ta sata ta ɗago kai


“Wa'alaikissalam”


“Hajiya sannu da hutawa kin yi baki a parlour”


“Baki?”


“Eh Hajiya Suwaiba ce da wasu mutane”


Aje Aikin Mummy tayi ta cire gilas ɗin idonta ta tashi ta nufi parlour.

      Tsayawa tayi tsakiyar parlour ta kasa rasawa kisa dasu ta kuma kasa komawa, Dukansu kuka suke ban da Mummy da idonta take a kafe yake.


“Na daɗe da manta ina da ku a duniya bana tunanin kuna da bukata ta kamar yadda nima bana bukatar ku miya kawo ku nan ?” 


Tashi hajiya suwaiba tayi ta karasa kusa da ita ta dafa ta,


“Kiyi hakuri ki zauna Salamatu za kuyi magana a natse”


“Bana bukatar magana da kowa miye haɗin ki dasu?”


“Sune suka bukaci ganin ki”


Juyawa Mummy tayi da nufin barin palo sai kuma ta samu kanta da kasawa hawaye suka cika idonta.

   

“Salama tu”


Wata tsohuwa ce ta kira sunan nata idonta na zub da hawaye, juyowa Mummy tayi itama tana hawaye ta kalleta rabon da taji muryarta a kunnen har ta manta wasu hawayen ne suka kara kawo mata ziyara, sai kuma ta fashe da kuka da bata san dalilin yinsa ba.


   “Ki saurari iyayenki ki kuma yi musu uzuri sai yanzu suka fahimci baki da laifi ta dalilin Alhasan”


Wani tsoho mai tsaga a fuska ya faɗa yana hawaye,


“Ko da ina da laifi Baba abunda kuka yi min bai dace kuyi min ba, ko da da gaske na aikata kamata yayi ku rumgume ku yarda da kaddara ku tausaya min amman sai kace baka san haka ba. Ka raba ni da mamana tun ban kai lokacin rabuwa da ita ba, kace ka bar maka gidan ka na manta ka kar na sake waiwayar ka akan abunda ba zai taɓa tabbatuwa ba baka damu da duk halin da zan shiga ba. shim haka ya dace iyaye su yima yayan su idan kaddara ta faɗa musu?”


Kuka take sosai tana faɗin maganar. shima kukan yake abun tausayi


“Nayi hakan ne dan gujema zagi da ɓatancin suna a idon duniya sai gashi kuma ban tsira ba, tun lokacin da na kore ki ban sake dogon farinciki ba sai Allah ya ɗora min sonki yasa min tunanin ki da kuma tunanin irin rayuwar da zakiyi. duk kuma lokacin da naso neman ki sai abunda kika aikata ya tsaya min a rai shi ya hana ni ganin farin ki ya hana ni na neme ki saboda a tunani na da gangan kika aikata sai a sanda Alhasan yazo neman ki mu ka tabbatar da gaskiya”


Gurfawa yayi kasa yana kuka kuka wanda yake na gaske ya haɗe hannayensa


“Salamatu ki gafarta min”


Da sauri itama da duka sai kuma ta tashi ta rumgume Mamanta itama kukan take sosai kaminnta ɗago kai ta kalleta tace


“Ki yafe mana Salamatu”


“Na yafe muku Mama mai rai ajizine kuma kowa baya wuce kaddarar sa har gobe ku iyaye na ne no matter what happen”


Sun daɗe suna kukan har hajiya suwaiba babuɓmai iya ba wani hakuri, har sai da sukayi kukan suka gaji sannan Mummy ta koma kukan farinciki, sai dare Hajiya Suwaiba ta bar gidan. 

  Washe gari Mummy da kanta ta haɗa musu abun kari cikin zumuɗi da jindaɗi. sai dai ku ɗin sun kasa sake jikin da ita kunyarta suke ji musamman Baba sun kan su sunsan abunda sukayi mata basu kyauta ba. itakan sai ta nuna musu kamar komai bai faru ba cikin jindaɗi ta kawo musu breakfast ta bisu da kallo zuciyarya cike da farinciki.


Allah mai Hikima lokacin da ya karɓe min ku sai ya bani Minal yanzu kuma ya karɓe abunsa sai ya dawo min da ku


A ranta take wannan maganar tana kallon yadda suke cin abinci. ba karamin daɗi mummy taji ba ganin Mahaifanta kusa da ita.


                       ****       *****       *****


A hankali Kairat ta kai hannu ta buɗe kofar ɗakin 



lil Minal sai a lokacin ta samu damar tsayawa tana kare masa kallo. ɗakine da aka kawata shi da kayan masu kyau ɓangaren tufafinta daban ɓangaren da gadonta yake dabam abun gwanin sha'awa. 



Murmushi tayi ta karasa kusa da kayan nata ta buɗe ta ɗauko wata riga mai kamada ta sanyi da hula da talkami ta fito, a palo ta tsaya tana nuna ma Talatu kayan da za a saka mata, karɓa tayi ta tashi tare da Ita ta nufin ɗakinta dan Saif ya hana ayi mata wanka ko ina sai ɗakinta. itama ɗakinta ta nufa taje tayi wanka ta shirya cikin jar a tamfa mai ratsin baki. tana fitowa ta nufi kicin girki tayi na musamman dan Mummy ta faɗa mata tana nan zuwa kuma zata zo mata da wani abun mamaki. 

    Bayan ta kare ta dawo parlour ta zauna akai akai ta kalli kofa duk ta kosa Mummy tazo sai da ɗauki wayarta kamar ta kira sai kuma ta fasa tana haka har lil Minal ta tashi daga bachi aka kawo mata ita karɓa tayi tana shirin bata nono, taji an taɓa kofa,


“Oh my god”


Da sauri ta tashi tare da ita ta nufi kofar da zumuɗi ta buɗe, da mamakinta sai taga ba Mummy ba, 


“Wanene ka.....”


Kasa karasa tayi lokacin da ya ɗago kai ya kalleta, kamannin Minal ta gani shimfiɗe a fuskarsa. 


“Shigo”


Ta ce dashi cike da ladabi, ba musu ya shigo cikon palo ya xauna a gurin da ta nuna masa, sannan ya soma magana kamar zaiyi kuka


“Wata alfarma nake nema a gare ki”


“Faɗi ko ta micece zanyi maka matukar bata fi karfi na ba amman ka fara faɗa min wanene kai?”


“Zaki san wanene ni a cikin alfarmar da zakiyi min”


“Wace alfarma ce wannan”


“Na bi duk hanyar da zan bi wajen ganin Salamatu ta saurare amman taki a yanzu ma bana da hurumin bi koda kofar gidan ta ne an faɗa min ta hanyar ki ne kawai zata iya saurare har kuma ta yafe min, so nake ki shiga dani gurin da take ki kuma roke ta data saurare ni ko da ba zata yafe min ba”


Shiru tayi tana kallon yadda yake hawaye jikinta duk yayi sanyi, suna haka wayarta tayi kara alamar kira a sanyaye ta ɗauki kiran 


“Hello Mummy”


“Na'am Dear ba zan samu damar zuwa ba amman na kira Saif zak kawo ki yanzu a nan zaku ci abincin rana har Abbahn ki yana nan tare da Suwaiba”


“Okey Mummy”


Ta amsa kamar ba taji daɗi ba, ta kashe wayar. tashi tayi ta nufi ɗakinta, bata fito ba sai da taji shigowar Saif sannan ta aje Lil Minal ta, taso ta nufo downstairs,


“Wow Beauty na”


Ya faɗa yana kallonta fuskarsa ɗauke da murmushi,


“Sannu da zuwa”


Sai da ya aika mata kiss sannan ya rumgume ta yana faɗin


“Yauwa Wannan kwaliyar fa?”


Gurin wuyanta ya ɗora kansa yana goga mata dogon hancinsa, ita kuma sai kokarin zame jikinta take


“Akwai mutane a falon fa”


Bai kula ta ba sai da ya gama abunda yake son mata wannan ya juyo yana kare ma falon kallo, sai a lokacin ya lura da abunda take magana a kai, juyowa yayi ya kalleta da ɗan ɓacin rai


“Amman kuma shine baki saka hijab ba?”


“Kai kace min na daina sawa a gida”


“A ina nufin idan mi kaɗai ne a gidan ba jeki ki saka hijab ɗin ki”


Murmushi tayi mai sauti har da fitar da halshe tana masa kallon zolaya, ta juya ta nufi upstairs, shima da kallon ya bita dan bai taɓa ganin hakan a fuskarta ba tun da tazo gidan.

     Tana shiga ɗakin ya shigo juyowa tayi ta kalleshi


“Mummy tace ka kai mu gida a can zamu ci abincin rana shine tace mu wuce da wannan mutunen”


Ta faɗa dan tasan sai ya tambaye da wanene kuma bata san karyar da zata nasa ya yarda suje dashi ba,


“Really?”


Ya tambaya kamar bai yarda ba, taɓe baki ta ɗanyi


“Na taɓa maka karya ne?”


“Na sani ko yanzu zaki fara”


Yaja hancinsa juyawa tayi.sanin nufinta yasa shi kisgota ta faɗo saman kirginsa suka faɗa saman gado. sunfi minti talatin a kan gadon yana aika mata da sakwannin ita kuma tana son kwace kanta amman ta kasa har ta gaji ta hakura. sai da yaji wayarsa na ringing sannan ya sake ta ta tashi tana duba wayar number Mummy ce baiyi picking ba dan yasan yana picking zata ce masa ya kawo Kairat. Bathroomƴa nufa, bai daɗe ba fito ya ɗauki keys ɗinsa,


“Saka hijab ɗin ki muje”


Da sauri ta nufi gurin da hijaban nata suke ta ɗauki wanda yayi kala da atamfar ta saka sannan ta ɗauki lil Minal ta kalleshi alamar ta shirya,

  Matsowa yayi kusa da ita ta yadda tana iya jin bugun zuciyarsa tana mata wani kallo


“Idan muka dawo anjima zan baki wani muhimmin sako”


“Wane irin Sako ne haka?”


Ta tambaya kamar bata san abunda yake nufi ba duk da tasan manufarsa. murmushi kawai yayi yaja hannunta suka fito.


Sai da zasu shiga mota Saif yake ma Alhasan kallon tsaf nan take gabansa ya rika faɗuwa yanayinsa ya canja. Bai ce da ita komai ba tun da suka shiga motar ita bata ce masa ba har suka gidan kowa da abunda yake tunani. ta ɗan daɗe cikin motar sannan ta fito Talatu ce karshen fita tasa hannu ta karɓi lil Minal ta wuce. A hankali take takawa gabanta na faɗuwa har suka isa cikin palon, 

   “Miye haɗin ki da wannan Kairat ina kika haɗu da shi?”


Mummy ta tambaya tana nuna sa da yatsa, bata bata amsa ba sai da suka kai tsakoyar parlour sannan ta kalli Mummy tace


“Dan Allah Mummy ki saurare shi na tabbata yayi nadama kuma akwai abunda yake son ce miki”


Tassssss Abbah ya wanke mata fuska da mari cike da ɓacin rai. Da sauri Saif ya jata ya maida gefensa ya ɗago yana Abbah wani kallo kamar zai rama mata.



LIL MINAL 



53


Fashewa tayi da kuka Saif ya rumgume ta. Palon yayi tsit baka jin komai sai sautin kukan Kairat, Saif kan duk ya ɓata rai sam bai jidaɗin Marin da akayi mata ba gashi daman ran nasa a ɓace yake. jin kukan yayi yawa yasa Mummy ta nufe ta ta dafa ta


“Kairat”


Nan Saif ya sake ta ta rumgume Mummy ta cigaba da kukan, Mummy ta kalli Abbah


“Da baka mare ta ba”


“Na mare ta akan me zata shigo dashi cikin gidan nan har tace ki saurare shi ina kuka haɗu da shi?”


Ya karasa da faɗa yana kallon Saif, Kamin yayi magana Kairat ta ɗago ta kalle Mummy


“Shine ya kawo kansa akan yana so na masa iso gurin Mummy, saboda kin ki saurare shi, Mummy duk mai rai ajizi ne, matukar akwai rai a jikin ɗan adam toh kullum shi mai aikata laifi ne ubangijin mu ma muna masa ya yafe mana kina ganin da Minal na da rai kinyi mata adalci kenan ki wulakanta mata mahaifi?”


Wani wawan kallo Abbah ya watsa mata


“Sai yanzu na tabbatar da baki da hankali da tunani Kairat kin manta duk abunda yayi mata shi ya raba da duk wani jindaɗi na duniya yanzu har yana da damar da zaice a saurare shi ko an saurare shi yana da abun faɗi ne?”


“Ya zamo sila ne kawai dan haka Allah ya kaddaro mata ko dashi ko ba dashi sai hakan ya same ta miyasa ba zakuyi imani da hakan ba?”


Ta juyo gurin Mummy,


“Kalle shi mummy kalli yanayin shigarsa ke kanki kinsan ba cikin jindaɗi yake ba wannan kawai ya ishe shi ishara”


Hawaye ne suka cika mata ido ta sauke ajiyar zuciya, ta lumshe ido. ta daɗe a haka sannan ta zauna. Kairat ma zaman tayi tana kallon Mummy ganin hakan yasa Abbah ya tashi a fusace ya fice. sai a lokacin Hajiya Suwaiba ta samu damar magana,


“Kiyi hakuri Salama'tu ko bai komai kinyi masa nisa yanzu”


Kallonta Mummy tayi ta Kamar tayi magana sai kuma tayi shiru. Karasowa yayi kusa da Ita ya risina kasa idonsa na hawaye ya ce


“Kiyi hakuri Salamatu ki dubi girman Allah ki yafe min nasan na cutar da ke na kuma yi kuskure, tun daga lokacin da na gudu na barki ban sake ganin Alheri a rayuwa ta ba, lokacin da abun ya faru sai na bar yola na koma katsina da zama gurin yayan mahaifina a nan ne na haɗu da wata yar mai kuɗi muka kulla soyayyah gaf da zamuyi aure mahaifinta ya nema min aiki a Sky Bank sannu sannu har aka bani manager na Bankin sai dai tun da nayi aure duk wani jindaɗi na rayuwar aure da ake samu ni ban samu ba kullum da kalar cin mutumcin da take min saboda ganin karkashin mahaifinta na samu aiki gashi kuma Allah ya jarraɓe ni da wani abu na rashin samun haihuwa dan tun da na aure ta sai dai tayi ɓari amman ba dai cikin ya tsaya ba, muna haka na kulla soyayyah da wata yarinya wanke ke aiki karkashina

    Sai muka rika kazantaciyar rayuwar ni da ita ta haka ta yaudare ni tasa na na shiga na fita na ba wani kawunta aron kuɗi kusan miliyan talatin daga lokacin da ta fahimci tafiya ta fara nisa sai ta bar zuwa aikin shi kuma babu shi babu labarinsa. matar da nake aure kuma ta addabe akan sai na sake ta ita ba zata iya zama dani ba, ba dan naso ba na sake ta sai naje na auri wata bazawara mai manyan Yaya duk da hakan ban samu haihuwar ba muna haka banki suka bukaci kuɗinsu ni kuma bana da su tun ina sa musu rana har suka gaji suka sauke ni daga mukamin bayan an same ni da wasu kananan laifuka da suka kama ni dasu daga karshe dai sai suka sayarda duk wani abun da na mallaka suka kuma kai ni kotu daga haka aka saka ni gidan yari, shekaruna shida a can ina cikin ta bakwai kwatsam sai gashi anzo kai tsaye aka ce an sallame ni, bayan sallama ta daga gidan yari na samu labarin mijin yata ne yasa aka sallame ni kuma ya biya kuɗin. a lokacin ne na samu kai na cikin wata rayuwa mai cike da nadama da dana sani tun daga lokacin na saka kafata gurin neman ki amman ban samu hakan ba har naje Yola gurin iyayenki na tabbatar musu da gaskiyar halin da na saki daga haka nazo abunja duk da hakan sai da nasha wahala gurin neman ki duk da yake ba a ɓoye kike ba, bani abun bakin ciki sai na tararda wanda nazo dan ta bata duniyar, bana iya misalta miki halin da na samu kai cikin ba ban san abunda zan ce ma halaccina ba ko da ke kin yafe min ita fa nasan ta tafi da son tasan waye uban ta na cutar da ku na cuci kaina......”


Shine yake kuka mai sauti Mummy kuma hawaye take wasu na bin wasu, Kairat ma kukan take Saif ma idonsa cike da hawaye. Kairat ta tashi ta karɓo Lil Minal a hannun Talatu taje ta mika masa tana faɗin


“Wannan shine abunda Minal ta bar mana. kamin ta rasu kance min ina ma zata ga mahaifinta da zata tambaye shi miyasa ya gudu ya barta baiyi tunani halin da zata shiga ba wace riba ya ci? ita kan tana son tayi masa wannan tambayar”


Rumgume Lil Minal yayi yana wani irin kuka. Saif ya tashi da sauri ya bar parlour, nan mummy ita ma ta fashe da kuka Kairat daman shi takeyi babu wanda baiyi kuka ba cikin parlour mutuwar ta ta dawo musu sabuwa.

       Saif na bita ya nufi gurin motar sa ya kifa kansa ya lumshe ido kansa sai sarawa yake. bai ɗago ba har sai da yaji kukan wayarsa yayi yawa number Lubna ya gani yana ɗagawa tace


“Momy na neman ka”


Kashe wayar yayi ya sauke ajiyar zuciya ya buɗe motar ya shiga daman can baya son komawa parlour cikin hanzari ya bar gidan.

    Har ya isa gidan ransa a ɓace yake babu abunda yake tunani sai Minal. ya daɗe cikin motar bayan yayi parking sannan ya fito ya nufi hanyar da zata sada shi da parlour gidan. Tsaye yayi yana kallon Safiyyah da ke kwance gurin tana kuka, kanta ba ɗankwali. tana ganinsa ta tashi zaune still tana hawayen abun tausayi. A sanyaye ya karasa kusa da ita ya risina yasa hannunshi a fuskarta yana share mata hawayen. ganin kukan nata yaki tsayawa yasa yaja zuwa kirjinsa ya rungume ta! sai shima ya samu kansa da kukan bai san dalili ba.


   “Yaya...”


Lubna ta kira sunan nasa tana tsaye bakin kofar fuskarta ɗauke da mamaki. Haka yayi kamar bai jita ba duk da ya ganta, ya kara kankame Safiyyah ya lumshe ido.



TOFA! ANA WATA SAI GA WATA ? YAYA KENAN?


SHIN KUNA GANIN ABBAN MINAL YA CANCANCI YAFIYA KUWA?


KEEP VOTING DEARS😍

54




Ya daɗe a haka sannan ya buɗe ya ɗago yana share hawaye,. Har lokacin Lubna na tsaye tana kallonsu tada ita yayi tsaye ya rik'a hannunta suka nufi cikin parlour, saman kujera ya zaunar da ita sannan shima ya zauna yana kallonta yana murmushi. Lubna ma zaunawa tayi a kujerar dake fuskantar tasu ta kura musu ido kamar tv. 


“Ta ci abinci?” 


Ya tambaya yana kallon Lubna, Kai ta girgiza masa, yana ganin haka ya tashi da kansa ya nufi dinning ya zubo abincin a plate, ya dawo kusa da ita ya zauna ya rik'a bata a hankali tana ci, 


“Lafiya?” 


Ya tambayi Lubna ba tare daya kalleta ba ganin yaddata sakar masu ido ko kyaftawa bata yi, tashi tayi tana faɗin 


“Bari na kira maka Momy” 


“Ban saki ba” 


Ya tari numfashinta, a nan ta koma ta zauna still bata daina kallon nasu ba. Sai da ya tabbatar da ta koshi, ya bata ruwa ta sha. Sannan ya tashi ya nufi ɗakinta Momy. 


     Goma saura kwata Saif ya shigo gida, kana ganin yanayinsa kasan baya cikin  walwalah, kai tsaye ɗakinsa yana tunani, sam bai lurada Kairat dake falo ba har sai da tayi masa magana


“Sannu da zuwa” 


Da sauri ya juyo, sai a lokacin ya lura da ita, a maimakon ya amsa sai kawai ya zagayo ya zauna kusa da ita yana murmushi ya kai hannu ya taɓa sakar wuyan ta 


“Wannan kwaliyar fa”


“Uhm” 


Kawai tace ta ɗauke kai ta tashi, da kallon Saif ya bita har ta shige ɗakinta sannan ya sauke ajiyar zuciya ya tashi ya shiga ɗakinsa, wanka yayi ya shirya ya sauya kayan jikinsa zuwa jallabiya fara da gajeren wando ya fesa body spray, ya hau saman gado ya kwanta yana shafa cikinsa. Babu wanda yake tunani a yanzu sai Minal maganar ta da akayi ɗazun ya dawo masa da tunanin ta a ɗayan ɓangaren kuma ga maganar da Momy tayi masa wai shine silar shigar Safiyyah wannan halin. 

   Kairat ce ta faɗo masa a rai cikin hanzari ya tashi ya nufi ɗakinta, tana kwance taji an turo kofar ɗakin, Lil Minal na gabanta ta zuba mata ido sai kallon ta take. zuciyarta ta nasalta mata Saif ne ya shigo ga kuma kanshim turarensa da fara kai ma hancinta ziyara tun kamin gayar ya iso, har ya mai da kofar ya rufe bata motsa a daga inda take ba tana jin ya kusa karasowa kusa da ita ta lumshe ido kamar mai bachi. Leka ta ya fara yi yana idonta a rufe, sai ya zauna gefen gadon yana kare mata kallo kamin ya kai hannu ya mirgino ta ta juyo gefensa ya rungume ta tsamtsam a kirjinsa


“I'm so sorry Momy ce ta kira ni shiyasa ban dawo ba, kuma hankalina ya ɗauku ban je na ɗauko ku ba” 


Har yayi surutansa ya gama bata motsa ba balle ma tayi masa magana, ganin bata da niyar maganar yasa ya tashe ta zaune ya ɗora bakinsa daidai kunneta ya soma mata magana kamar mai raɗa


“Haba yar gidan Mummy kiyi hakuri mana nasan nayi laifi amman a yafe min dan Allah” 


Sai a lokacin ta buɗe idon ta, ta kalleshi 


“Amman kuma shine baka dawo ba sai yanzu” 


Fuskarta ya rik'a yana rufe ido da buɗewa yace


“Kin san Safiyyah ba lafiya shine na.........” 


Sai kuma yayi shiru kamar wanda ya tuna abu, basar da maganar tayi sai ta kalli cikin kwayar idonsa


“Ka ci abinci?” 


“A'a tun abincin Safe” 


“Miyasa.?” 


Bai bata amsa ba, ita ma kuma bata kara tambaya ba sai kawai ta sauka saman gadon ta rika hannunsa for the first time 


“Muje kaci abinci” 


Tashi yayi tsaye, a maimakon yayi tafiya sai kawai taji ya rungume ta, ta baya yana sauke wani dogon numfashi. Sai gashi ita ma ta samu kanta da sauke numfashin mamancin nashi ta lumshe ido, kamkamkan ya rungume ta shima idon nashi a lumshe, sun daɗe a haka, sai kanshim jikinsa take shaka rahamar jikinsa ta baibayeta a nan ta soma jin sanyin dake fita daga jikinsa kamar raɓa, ɗagowa tayi tasa hannunta ta ɓanɓare rikon da yayi mata ba tare da ta juyo ba tace


“Bari na haɗa maka tea jikinka da sanyi” 


Bai ce mata uffan ba ita bata jira yace mata ba ta fice daga ɗakin, Bata daɗe ba ta dawo hannunta rike da plate ɗin fruits ɗayan hannun kuma rike da Cup ɗin tea. Wani ɗan karamin tebur ta jayo ya ɗora cup da plate ɗin sama sannan ta kalleshi. 


“Ka fara shan tea sai kaci fruits ɗin zaka fi jindaɗi idan baka ci abu mai nauyi ba” 


Murmushi yayi mata as respon ya ɗauki tea ya fara sha, kallonsa take a sake tana karantar wasu abubuwan game da shi. Daga shigowarsa zuwa yanzu ta fahimci yana cikin damuwa, sai kuma ta samu kanta da jin ba daɗi ganin halin da yake ciki, yanayin yadda yake shan tea sai ya saka ga ganin kamar baya jindaɗi sa, ba kuma daɗin sa ne baya jin ba tun da tasan mijinta ma'aboci shan tea ne da kuma coffee akwai dai abunda ya ɓata masa rai. Bayan ya shanye tea ɗin ta karɓi kofin tana faɗin 


“Faɗa min yau da ina da ina kaje bayan gidan Momy?” 


“Ban je ko ina ba a gidan kawai na wuni, Na manta ban tambaye ko yadda Mummy tayi da Mutumen ta ba” 


“Zan faɗa maka gobe yanzu faɗa min abunda yake damun ka” 


“Ni..?” 


Ya ɗan zaro ido sai kuma yayi murmushi ya cigaba da cin Apple ɗin dake gaban sa, nan tasa hannu ta ɗauke plate ɗin fuskarta babu alamun wasa tace


“Faɗa min abunda yake damun ka Saif Please” 


“Ya kamata sunana ya canja launi a bakin ki fa yanzu” 


Ya faɗa yana son basar da wacan tambayar. Murmushi mai sauti


“Toh wane suna kake so?” 


“Ke ce zaki sa min da kanki” 


“Fine Abbah lil Minal” 


Dariya yayi 


“Sunan yayi tsawo kuma bai min ba” 


“Toh faɗa min sunan da kake so mana” 


“Ba xan faɗa ba kece dai zaki zaɓa min” 


“Hubby” 


Kai ya girgiza, 


“honey” 


“Nop” 


Shiru tayi tana nazari dan duk sunan da ta kawo masa cewa yake a a, can ta kalleshi 


“K'albee yayi maka?” 


Kai ya ɗaga mata cike da jindaɗi ya janyo ta zuwa jikinsa ya rungume, 


“Zan ji daɗi idan kika kira ni haka” 


Murmushi tayi


“Haka zan rika kiran ka har sai kace na daina” 


“Aiko ba rana” 


Ya faɗa da dariya, yana ɗan shafa bayanta shiru ne ya biyo baya shi dai yana abunda yake ita kuma tana saurare sa kamar ɗalibar da ake yima darasi, ta natsu sosai tana saurarensa, har sai da taga yayi nisa sannan ta kira sunan sa a hankali


“K'albee......”


Kamar ba zai amsa ba zuwa can kuma ya amsa mata a wahale can cikin makon shin shi 


“Umhm” 


“Faɗa min mi yake damun ka?”  


Bai yi magana ba sai kawai dai cigaba yake da abunda yake mata, ganin hakan yasa ta janye jikinta ta matsa gefe tana gyara rigarta tana ganin ya matso sai ta kara matsawa,


“Dan Allah karki min haka Kairat yana ɗaya daga cikin abunda yake sani damuwa ki daina hana min abunda Allah ya halitta min wallahi wahala nake”


Cikin walallaliyar murya yayi maganar idonsa a rine.

Ita kanta da san da hakan dan tana lura da irin halin da yake shiga idan suka kwana tare, tsayawa tayi kamar mai tunani tana haka taji ya rika ta bata unkurin hana shi ba, ya ci gaba da abunda yake mata ita kuma tayi shiru tana sauraren karatun nasa, ganin ya wuce gona da iri yasa ta rik'a kokarin kwace kanta a nan ya nuna mata karfi ba ɗaya ba, kiransa ta rika yi amman ina yayi kisa baya jin kira. Rawa jikinta yake ta ko ina kan kace kabo sai gata tana kuka da hawayen ta. 

      Daren ranar daga ita har shi basu yi bachi mai tsawo ba balle ita da sam bachin bai mata daɗi ba. Washe gari shi ya taimaka mata tayi wanka tare da alwala ya shinfiɗa carpet tayi Sallah, tana sallamewa ko addu'a bata tsaya yi ba ta kwanta a gurin sai bachi. 


  Bayan ya gama haɗa breakfast ya shigo ɗakin tsaye yayi kanta tana kallonta fuskarta ciki da annuri sai murmushi yake, can kuma risina ya kai hannu ya shafa fuskarta. Juya tayi ta ci gaba da bachin, murmushi yayi bai yi unkurin tashin ta ba ya juya gurin Lil Minal yasa hannu ya ɗauke ta ya fice. 

     Sai sha ɗaya har da kwata ta farka koshi ba dan ta gaji da bachin ba sai dan yunwa da ta tashe ta. Ba dan dole ba da ba zata fita daga ɗakin ba, sai dai kuma babu yadda ta iya tun da ba kiransa zatayi ba, daker ta tashi tsaye ta nufi kofar ɗakin tana wata tafiya. Yau kan sai taji sauka stairs yayi mata wahala kamar ba kowace ta saba ba, 

     Saman kujera ta gansa zaune rike da lil Minal yana ɗaukar ta hoto, har kasa ta duka ta gaishe shi cike da kunya


“Ina kwana” 


Bai amsa ba sai kawai yasa ɗayan hannunsa ya rika.ta suka tashi tsaye tare, 


"Sai yanzu kika tashi"


Ya faɗa kamar mai raɗa kai kawai ta daga masa tana kokarin zame jikinta, lil Minal ya aje yasa hannyensa ya zagaye kugumta yana murmushi


"Dan Allah ka sake ni yunwa nake ji"


Bai yarda ya sake ta ba ɗin sai ya ɗauke ta cak ya nufi gurin cin abincin da ita. sai da ya tabbatar da ta koshi sannan ya zuba ya ci kaɗan ya sake ɗauko ta a dawo da ita saman kujera ya rumgume ta yana sauke ajiyar zuciya.

  

“I'm not baby dan Allah ka kyale ni”


“of course you are”


Duk yadda taso ya sake ta kiyawa yayi har sai da tayi kamar zata masa kuka sannan ya sake ta ta tashi da sauri ta nufi ɗakinta.

    Wanka ne kawai ya zame mata dole tana yinsa ta ɗauko lil Minal ta bata nono sai da ta tabbatar ta koshi sannan ya kwatar da ita gabanta ita ma ta kwanta sai bachi.


    Da dare takeaway yayi masu dan wuni tayi tana bachi shi kuma yana ganin tayi bachin ya sa kafa ya fita bai dawo ba sai bayan Sallah isha i,

  Bayan ya shiga ɗakinsa yayi wanka ya dauko abinci ya nufo ɗakinta a bakin kofa ya tsaya ya sauke ajiyar xuciya sannan ya shiga da sallama,

   Duk yadda yaso ya ɓoye damuwarsa dai ta gano dan idonsa take karantar halin da yake ciki ita kaɗai ta ci abincin sho bai ciba sai saka da yayi gaba yana kallo kamar tv,

    Bayan ta kare cin abincin ya janye abubuwan dake gabanta ya matso kusa da ita ya rumgume ta, a nan ta kara fahimtar halin da yake ciki. 

    

Haka suka kwashe kwana biyu ita da shi, ita ta kasa ta tambayeshi damuwarsa shi kuma ya kasa faɗa mata, sai dai kuma duk tsawon kwana biyu nan bai barta ta huta ba, kullum da salon da yake zo mata.

   Yau ma bayan sun gama breakfast ya tashi kamar jiya ya nufi ɗakinsa, har yayi abunda zaiyi ya fito tana zaune a inda ya barta ganin yanayin shigarsa ya tabbatar mata da fita zaiyi. sai da ya kawo bakinsa daidai kumatunta zai mata kiss tayi saurin jayewa ya sake dawowa ɗayan gefen ta sake kauda fuskarta,


“Lafiya?”


Ya tambaya yana fuskantar ta, kallonsa tayi


“Bai kamata ace kana ɓoye min damuwar ka ba a tunani na yanzu ni da kai mun zama ɗaya”


shiru yayi sai kuma yaja kujera ya xauna ya kama hannunta,


“Matsalar Safiyyah ce take damu na saboda Momy da Gwaggo sun ce nine silar shigarta wannan halin hakan yasa yanzu Daddy shi ma ya kasa fahimta na”


Tasan me yake nufi tun da ta daɗe da sanin babu wanda Safiyyah take kauna irin Mijinta. sai dai kuma me su suke nufi har ya kai suna ganin laifinsa? ko aurenta suke so yayi? dan ta samu wannan amsar yasa tayi masa wata maganar.


“Toh ka aure mata sai ka wanke kanka”


Rumgume yayi yana dariya


“Funny girl ina ni ina Safiyyah bana mata kallon matar da zan iya aure ba zan iya zaman aure da Safiyyah ba sai dai kuma nima kai na tana bani tausayi sosai”


Wani sanyi taji ya tsara zuciyarta kara lafewa tayi jikinsa,


“To yanzu ya zakayi?”


“Oho gani ga Allah ni dai fata na kawai ta samu lafiya”


“Toh miyasa ba zaku sata under medication ba?”


“Gwaggo ce bata yarda ba wai kara firgita mata kwakwalwa za'ayi sai dai a nema mata na hausa”


“Ka barta ta nema mata na hausan wata kila a dace”


Sun daɗe a haka manne da junna sannan ya sake ta ya fice.


    

                                  ***    ***     ****

        


Abu kamar wasa sai ga Safiyyah ta kwashe wata biyar da wannan lalurar tun ana ganin kamar sauki sauki yanzu abun ya fara wuce gona da iri, kuma duk da hakan Gwaggo taki yarda a kaita wajen maganin turawan ma sai an saci idonta ake bata,

   Sannu sannu ake sabo yanzu kan Kairat ta san kan gidanta da kuma mijinta, ga kula da lil Minal da take sosai da sosai itama yanzu tayi kyau tayi wayo dan yanzu tana cikin wata na bakwai, in ka ganta kamar ka sace ka gudu. 



    Tana cikin kicin tana aiki taji an danna bell lil minal kuma ta kwala ihu saboda tsoro, da gudu ta fito tazo ta ɗauke ta,


“Ya akayi mi ya faru?”


Shiru tayi ta kalli kofar falo jin an sake danna bell ɗin, ɗauke da ita taje ta buɗe kofar, Da sauri ta rumgume Mummy ta welcomin ɗin ta.

  

“Ashe ma kinji sauki ce min akayi ɓaki da lafiya”


Mummy ta faɗa tana kunno kai cikin parlour,


“Naji sauki Mummy waya faɗa miki?”


“A shanun talla naji ina mai gidan naki?”


“Ya fita tun ɗazu Mummy ina Abbah na”


“Abbah ki? ai kinsan inda yake”


Murmushi tayi


“Haba Mummy ya kamata ace kun wuce wannan gurin tuni tun yaushe ake abu ɗaya dan Allah! haba Mummy ki amince masa mana Mummy yanzu ko dan karamcin da Abbah yayi miki ba zaki yarda ki aure shi ba”


“Yayi min ne saboda Allah dan Allah ki rufe min baki ko ruwa baki kawo min ba zaka ɗauko min wani shirme”


“Haba Mummy Abbah fa ko ke ko bake ba ya riga ya shirya aure a yanzu da aje a ɗauko mana wanda bamu sam halinta ba fa ao kara ke kuma kinga Hajiya ma da kanta ta roke ki miyasa kike son watsa musu kasa a ido ne? wallahi mummy sam bana jindaɗi in kina cewa Dr. Isma'il zaki aura ko dai dan yafi Abbah kuruciya ne?”


Mummy ta zaro ido


“Kairat zaki tashi ki kawo min ruwa ko sai na bar miki gidan ki?” 


Tashi tayi tana dariya ta mika mata lil minal ta shiga kicin ta ɗauko mata  drinks da yan kayan ciye ciye ta dire mata.

   Sunyi kusan awa biyu suna fira, Mummy na batun tashi Saif ya shigo, yaji daɗin ganinta sosai dan rabonta da gidan har ya manta duk rashin lafiyar da Kairat take yi bata leko gidan ba har taji sauki,  Cikin mutumci da girmamawa suka gaisa Mummy take tambayarsa ya mai jiki


“Jiki da sauki”


“Ta warke kuwa?”


“Aa har yanzu tana nan abunda dai sai dai hamdala”


“Allah ya sauwake amman da kun gwaɗa gurin Deen ko Allah zai sa a dace”


Kairat ta mere baki


“Wallahi Mummy nayi ta masa magana yaki yarda shi har yanzu yaki ya manta abunda ya faru”


Mummy ta kalleshi,


“Saif ba a son musulmi da riko, ka amanta abunda ya faru kuma ai ba wani abun zaka je nema ba sai lafiyar yar'uwarka kuma ba kyauta zai maka ba”


Kasa kasa ya watsa ma Kairat harara,


“Shi kenan Mummy zan gwada insha Allah”


“Toh Allah ya sa a dace ni kan bari na tashi kar baki da zanyi suzo ba su tararda ni ba”


Sallama tayi ma Saif, Kairat kuma ta rakata har gurin mota tana mata maganar Abbah ta, Mummy dai bata ce masa uffan ba taja motar ta ta rufe. 



YAU MA SAI NACE VOTING AND COMMENTING? 



55


Sai da taga ɓacewar Motar Mummy sannan ta juyo, tana shigowa Saif ya cafkota ya wani walkato ta ta juya ta juyo ta faɗo korjinsa, hannunta ya ɗan matse fuskarsa na kan kafaɗarta yayi mata magana kamar mai raɗa


“Wa yace ki daɗe?”


“Ba kowa ba” 


Ta faɗa da dariya tana son kwace hannunta dan taji zafin rikon da yayi mata, shi kuma yaki sakinta sai kanshin turaren wuyanta yake shaka, suna haka Lil Minal ta rarrafo tazo ta kama kafan babanta hakan yasa ya saki Gimbiyar ya ɗauki yarsa yana murmushi, dariya tayi ta rika zallo Kairat kuma ta nufi kicin tana ɗan turo masa baki. 


            Bayan sun gama cin abincin dare Kairat take kara masa maganar Safiyyah, ta damu da ita a yanzu tsaɓanin baya da ba ruwanta da ciwonta ko dan yanzu taga abun yana damun Momy da Saif ne oho! Ita kanta Safiyyah yanzu ta zama abar tausayi bata magana kuma komai bata iyawa sai idan gwaggo ce tayi mata ko kuma yar aikin da ka ɗaukar mata, wani. Lokacin kuma bata komai saikin kuka, ga magani anyi nema har an gaji har yanzu shiru. Kansa ya shafa ya ɗan gunɗe baki


“You know how much I hate him” 


War tayi da ido


“Oh my dear, kar wannan ya dame ka ai ba cewa nayi ka so shi ba lafiyar Safiyyah zaka nema ba wani abun ba ko dan Gwaggo da Momy and Kalbi babu abunda zai iya mana yanzu abunda yayi maka a baya zafin son ta yasa yayi maka haka tun da yana tunani zaka iya sakinta shi ya aure, 


  Kuma abunda ya faru a baya ai ya zame maka darasi yanzu wani ba zai kawo maka wani abun ka rufe idonka ka cutar da kanka ba” 


Iskar bakinsa ya busar


“Fine amman shine zai zo ya same ni a nan” 


Dariya tayi


“Haba dai wanda keso ba shi ke biya kuma wallahi kasan Deen ba xai kawo kansa gidan nan dan matsalar Safiyyah ba, karka manta yanzo ka hana n ganshi kuma ni yanzu ko number sa bana da” 


“Me kike Nufi ke nan mune zamuje?” 


“Idan mun je ai ba yada kai bane, kuma ka samu Momy ku tattauna” 


Tashi yayi ya rika hannunta, 


“Mu rufe babi wasu muyi na mu babin zo muje mu kwanta” 


    Tashi tayi tana wani irin yauki da jiki ta ɗora kan ta saman kafaɗarsa, hannunsa sarke da nata suka nufi upstairs. 


          

Washe gari bayan ya tashi daga aiki ya biya gurin Momy,  sai da yayi kamar yana yi sannan Momy ta sake dashi, dan fushi take dashi wai yau kusan kwana nawa bai leko gidan ba, shi dai hak'uri kawai yake bata yana dariya yasan ba dan komai bane sai dan Safiyyah zata ce ya daina kula da ita ne, 


“Ya mai jikin?” 


Ya tambaya yana kallon yadda zata amsa masa,


“Jiki yana nan yadda yake  jiya Gwaggon ku tazo ta ɗauke ta wai zata kai ta wani gurin a gwada a gani” 


“Wai ita bata gajiya da na hausar nn ne, ni da har nace ko mu kai ta gurin wani mai kula da masu irin ciwon mu gani” 


“Toh ni ai lamarin ne yanzu na rasa gane ma kansa kullum abu ɗaya” 


“Jarrabawa ce idan Allah ya kawo ma bawa sai hak'uri” 


“Sai ka bari idan sun dawo sai muje gurin da kace ɗin Ya Kairat da lafiyar jiki?” 


“Taji sauki sosai yanzu ai” 


“Allah ya kara sauki amman nace Ba zata yaye Lil Minal ba? Kar tazo tasha ciki abu ya zama biyu gata tayi jikinta” 


“Toh wai Momy Lil Minal bata saba da shan komai ba banda nono kuma kinga cikin ai wata huɗu ne yanzu kin ga akwai sauran lokaci” 


“Aifa sai ka yi, wato har yanzu baku fara bata komai ba ko! Ko yar madarar nan ta yara ai kwai saba mata da ita” 


“Za a bata”


Ya faɗa yana ɗan sosa kai, Momy ta taɓe baki


“ku dai kuka sani, idan ba a sharar masallaci ba ayi ta kasuwa” 


Shi dai dariya kawai yake. Sai kusan la'asar ya bar gidan, Yana ɗaukar hanyar gidansa gabansa ya soma faɗuwa, sai jikinsa yayi masa ba daɗi cikin wani yanayi ya isa gidan, bayan yayi parking ma sai da ya ɗan daɗe cikin motar sannan ya fito ya nufo cikin gidan, 


Da sallama ya shigo jin ba'a amsa masa ba yasa ya zauna saman kujera yana


“Mom Lil Minal I'm back” 


Shiru nan ya tashi ya leka kicin bai ganta ba, kai tsaye ɗakinta ya nufa yana tura kofar ɗakin da faɗin


“Madam ko bachi kike ne?” 


Nan ma ba kowa a ɗakin sai Lil Minal dake bachi tana sauke ajiyar zuciya, da ala kuka tayi har ta gaji bachin ya ɗauke ta, bathroom ya buɗe nan ma bata ciki a nan ne hankalin sa ya fara tashi 


_Toh ina ta shiga.?_


Ita ce tambayar da yayi ma kansa, a nan ya juya ya shiga ɗakinsa nan ma bata nan cikin sauri ya dawo parlour yana tunanin gurin da zata shiga ya dai san bata fita bata faɗa masa ba to ina ta shiga?, gurin mai gadi ya nufa yana tambayarsa, nan shima yace shi dai bai ga fitar ta ba, dawowa yayi cikin parlour ya danna mata kira sai kawai yaga wayar saman kujera tana ringing, ɗaukar wayar yayi yana dubawa  can kuma ya aje ya nufi hanyar da zata sada shi da Garden, 


Kwance ya hango ta kasa dafe da ciki, cikin sauri ya k'arasa yana kiran sunan ta, durkusawa yayi yana girgiza ta ganin bata motsa ba yasa ya ɗago ta ta ɗora ta saman kafafunsa, 


“Lafiya mi ya same ki?” 


Cikin firgice ya tambaya, hawaye ne yake mata zuba bata iya magana sai cikin da ta sa hannu ta dafe, hannu yasa gurin cikin yana dubawa 


“Miya faru ciwo yake miki ne?” 


Kai kawai ta iya ɗaga masa sai hawaye take, da sauri ya ɗauko ta ya nufo parlour da ita, saman jikinsa ya rungume ta, ita kan kallonsa kawai take tana hawaye, ganin abun banayi bane yasa ya ɗauke ta ya nufi asibiti da ita, yana isa aka wuce da ita Emergency taimakon gaggawa aka shiga bata, a waje Saif ya tsaya hankalinsa a tashe ya ciro wayarsa ya danna ma Mummy kira ya sanar da ita, bayan ya kashe ya kira Momy ita ya faɗa mata, yana kokarin zama Lil Minal ta faɗo masa a rai, cikin sauri ya ciro wayarsa ya saki kiran Momy, bugu ɗaya ta ɗauka 


“Hello Momy na manta na baro Lil Minal gida a tura Lubna ta kula da ita yanzu Please” 


“Okey gamu nan zuwa” 


Bayan ya kashe wayar ya dafe kansa yana tunanin abunda ya samu matarsa haka, ba ayi minti goma ba sai ga Mummy ta iso gurin hankalinta a tashe, 


“Ina take Saif?” 


Shine abunda Mummy take tambaya cikin tashin hankali, gaishe ya fara yi ta amsa masa sama sama, tana kara tambayar sa ina take, 


“Tana ciki Basu fito ba har yanzu” 


“Toh wai miya same ta ne? ” 


Bakin abunda ya sani ya faɗa mata dan shi kansa bai da takai maimen abunda ya same ta, zaunawa tayi a ɗayan kujerar tana kallon kofar ɗakin Kairat da take ciki. Bayan kamar minti arba'in likintan ya fito ɗaga ɗakin tare da wasu nurses guda biyu mata, da sauri Saif ya tashi da Mummy suna tambaya likitan ba'asi, 


“Gaskiya ba mu gano ko minene ba a yanzu amman dai ko minene a cikin cikinta yake yanzu za muyi mata hoto ne sai mu bincika cikin nata” 


Ya faɗa bayan ya sauke ajiyar zuciya, 


“Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un” 


Shine abunda Mummy ta faɗa ta faɗi zaune saman kujera, Saif kuma yasa hannu sa aljihu yana kallon Momy da ta iso a yanzu, 


“Lafiya miya same ta ne?” 


Babu wanda ya iya amsa mata daga Saif har Mummy, likitan ya kalli Saif yana faɗin 


“Ina son muje office kayi mana bayanin abunda tace tun daga safe zuwa yanzu” 


Kai kawai ya ɗaga masa ya bisa  baya jiki ba gwari, wani file ya karɓa hannun nurse ɗin bayan sun zauna Saif ya soma masa bayani 


“Tea kawai muka breakfast da shi da safe da bread sai egg shima bana jin tace dan tun da ta samu cikin nan bata son kwai sosai sai, ni dai daga nan na fita ban sani ba ko a kara cin wani abun bayan fita na” 


Bayan ya gama rubutawa ya mika masa file ɗin, 


“Zaka sa mana hannu a nan” 


Bayan yasa hannun ya kalli likitan yace


“Dan Allah kayi duk abunda ya dace Please” 


“Insha Allah zamu yi duk abunda ya dace” 


Juyawa yayi jiki ba gwari ya fice daga office ɗin. 

    

Haka likitoci suka wuni akan ta suna bincikar ta, amman basu gano mike damunta ba dan ko hoton da kayi mata basu ga komai ba, abu ɗaya suka sani shine ko minene a cikin cikinta yake. 

   Sai dare Mummy ta kira Hajiya Suwaiba ta faɗa mata, ba ɗauka lokaci ba suma suka iso tare da kannen Kairat da kuma Nafisa yayar Kairat, 

Abunda likitan ya faɗa musu shi Mummy ta faɗa ma Hajiya Suwaiba, babu wanda hankalinsa bai tashi ba ganin irin halin da take ciki kuma gashi likitocin sunce basu gano abunda yake damunta ta, 


Duk yadda Mummy taso Saif yaje gida kiyawa yayi a dole suka kyale shi ya kwana asibitin tare da ita, lokaci lokaci ta kan buɗe idonta ta kalleshi sai kuma ta rufe kamar mai bachi duk maganar fa yayi mata ba zata buɗe idon ba, balle ta motsa ko tayi masa magana, a yanayinta ma kamar bata san inda take ba, 


Har gari ya waye Saif ba rumtsa ba, a masallacin asibitin yayi sallah asuba, sannan ya sake dawowa ɗakin, kujera yaja ya zauna ya haɗa hannunshi da nata ya rik'e idonta taf da hawaye, ji yake kamar rasa ta zai yi, 


“Allah ya baki lafiya i Love you so much” 


Ya faɗa yana lunshe ido yana sauke ajiyar zuciya yana haka Mummy ta shigo, bayan sun gaisa ta tambayi shi jikin, yace mata da sauki hawayen da taga a idonsa yasa ta ɓoye nata hawayen, tana kokarin yi masa magana likita ya shigo ɗakin, 


Bayan ya duba ta ya kalli Saif yace


“Za mu canja mata ɗaki kuma ba bukatar wani ya shiga ɗakin idan ba likita bane sai dai zaku iya ganinta ta windo ina fatar zaku bamu haɗin kai” 


Ajiyar zuciya Saif ya sauke, 


“Doctor ko dai mu fitar da ita waje?” 


“Eh to ba zan hana ku fitar da ita waje ba amman da kun bar ta muyi mata irin na mu mi gani tunda kaga abun daga jiya zuwa yau ne wannan ɗakin da za'a kai ta za'a kula da ita sosai ka kwantar da hankalinka zata samu sauki insha Allah matsalar kawai mu gano abunda yake cikin ne” 


Cikin zafin rai yace


“Dr ya za'ayi na kwantar da hankali na bayan kun kasa ku gano abunda yake damunta, tun jiya yarinya ba ta san inda take ba amman kun kasa yin komai” 


Likitan ya dafa shi


“Muna kokarin ganin mun gano haka sai dai kuma ina son kasan lafiyar ta da ciwonta a hannun Allah yake ba a hannun mu ba, kuma kun fa ya kum sai Allah addu'a kawai ya dace kayi” 


Buge masa hannu yayi ya tashi a fusace ya fice daga ɗakin, tsaban zafin rai ko Hajiya Suwaiba bai tsaya gaidawa ba ya nufi harabar asibitin, tsaye yayi gurin motarsa yana shafa kansa zuciyarsa na bugawa da karfi, oho me zai yi shi kanshi yasan addu'a ce kawai mafita tunda baya iya bata lafiya sai abunda Allah yayi, 


“Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un” 


Shine abunda yake ta maimaitawa yana son haɗe kukansa, buɗe motar yayi ya zauna ya haɗa kansa da sitarin ya rufe ido, 

  Jikin Ringing ɗin wayarsa yayi yawa yasa ya ɗago ya ciro wayarsa daga aljihu daf da zata katse ya danna picking 


“Hello Momy” 


Yanayin muryarsa ya tabbatar mata yana cikin damuwa, 


“Na'am ya mai jikin?” 


“Alhamdulillahi” 


“Idan ka fito kazo gida” 


“Toh Momy” 


Ya daɗe kamin ta kashe wayar, key yayi ma motarsa ya soma tafiya a hankali, lokaci lokaci yake shafa gashin kasa zuwa wuyansa ya sauke ajiyar zuciya, gida ya nufa kamar yadda Momy tace masa, bayan yayi parking ya daɗe cikin motar sannan ya fito ya nufi cikin gidan. 

   Kallo ɗaya Momy tayi masa ranta ya kara ɓace sam bata son taga ɗanta cikin damuwa dan tafi kowa shiga damuwar, 


“Momy ina kwana” 


Ya faɗa yana kokarin zama, sai da ta zauna sannan ta amsa basa


“Lafiya kalau dan Allah karka sa kanka a damuwa da yawa zata samu sauki” 


Kai kawai ya daga mata yace


“Ina lil Minal?” 


“Tana can ɗakin Lubna muje dinning kaci abinci” 


“Momy bana jin zan iya cin wani abu” 


Bata matsa masa ba ta tashi ta nufi ɗakin Lubna bata daɗe ba ta fito ta nufi dinning. Ba a jima ba Lubna ta fito ɗakinta ɗauke da lil Minal ta nufo shi, lil Minal na ganin Abban ta ta fara zillo 


“Pah pah pah” 


Haka take faɗa tana kokarin mika kanta ya dauke ta, hannu ya mika ya karɓe ta cike da tausayinta ya rungume ta ya lumshe, wani irin tausayinta ne ya lulluɓeshi, 


“Karɓi ga tea ka sha” 


Maganar Momy ce tasa ya buɗe ido sai ya sauke su kan kofin tea, daga bisani yasa hannu ya karɓa, kaɗan ya kurɓa ya ajeye, Momy ta zauna kusa dashi cikin damuwa ta kalleshi


“Ita fa rayuwar duniya komai ɗan'hakuri ne jarabawa kala kala akan yi ma bawa da sannu sai kaga komai ya wuce, ni banga abun ɗaga hankali a wannan ciwon nata ba insha Allah zata ji sauki” 


Iskar bakinsa ya busar


“Momy baki san yadda nake ji Kairat bane, na rasa Huda na rayu na rasa Minal na rayu Kairat kan dana rasa ta nima za'a rasa ni, Momy tun jiya yarinyar nan bata san inda kanta yake ba gashi su kuma sun kasa gano mi yake damunta” 


“Kayi ta addu'a Allah zai bata lafiya” 


“Ina fatar hakan amman Momy har fa ciki ne jikinta ina tsoron lamarin nan” 


“Ka bar komai a hannun Allah shi zai maka magani zata samu sauki insha Allah” 


“Allah yasa” 


“Amin”


“Ba zaka ci abinci ba ka daure ka ci ko kaɗan ne” 


“Ba zan iya i ba Momy bana jin yunwa” 


“Da dai ka daure” 


“Ba zan iya ba Momy” 


Duk yadda Momy taso ya ci abincin ki yayi dan sam baya jin yunwa baya ma sha'awar wani cin wani abu, 

   A wunin ranar haka ya wuni in banda ruwa babu abunda ya kai bakinsa, a ɓangaren lil minal ma haka ne dan bata sha komi aka bata sai ruwa sabo da nono gashi ba a koya mata shan komai ba, bai koma asibitin ba sai dare ba kuma komai yasa haka ba sai dan baya son ganin halin da matarsa take ciki. A hankali yake tafiya lil Minal na lafe a kirjinsa tayi lamo kamar wanda tasan abunda yake faruwa. 

   A bakin kofar ɗakinta ya tararda Doctor tare da wasu, fuskarta ba yabo ba fallasa ya mika ma doctor hannu suka gaisa, 


“Idan ka shiga wannan shi ne shiga na karshe da zaka kuyi dan anjima kaɗan zamu fara aikin mu idan kuma mun fara kuda ganinta sai a window” 


Likitan ne yake faɗin hakan yana kallon Saif fuska da fuska, kai kawai ya iya ɗaga masa ya sauke ajiyar zuciya ya tura kofar ɗakin ya shiga jiki a sanyaye, Mummy ya gani zauna saman kujera ta saka Kairat a gaba tana kallonta sai hawaye take wasu na bin wasu, Hajiya Suwaiba da Abbah na daga gefe suma ita suke kallon ko wannensu fuskarsa ɗauke da damuwa dan Hajiya Suwaiba kaɗan ya rage hawaye bai zubo mata ba, cikin kararriyar murya ya gaishe su, Abbah kawai ya iya amsawa dan Mummy bata ma shigo ba, Hajiya Suwaiba kan tana buɗe baki tasan kuka ne zai fito,

   Karasawa yayi kusa da ita ya zagayo ɗayan ɓangaren, bai kula kowa ba ya mika hannu ya riko hannunta ya ɗago shi yayi masa kiss, sannan ya sake kai hannunsa ya shafa fuskarta, Mummy kan sai surutai take mata kamar wanda ke son zautowa, 

“Dan Allah ki tashi Kairat kinji Mummy ba zata iya rayuwa ba ke ba, komai kike so zan miki ke kaɗai kika rage min” 


Da kuka ta karasa maganar ta jingina kanta saman gadon, Abbah ɗauke fuskarsa yayi Hajiya Suwaiba kuma ta gumɗe baki kar kuka ya fito mata, Hannu Saif ya kai ya sake rike hannun nata gam tana dantsar baki, lil Minal kan sai bachinta take dan tun yana tsaye bakin kofa bachi yayi gaba da ita daman jikin nata kamar a mace yake, jin ta matsa hannunsa yasa ta kalleta da sauri sai ko yaga idonta a buɗe tana kallonsa, bana jin yasan lokacin daya risina a gurin yana kiran sunan ta, hakan ne ya hankaltarda su Mummy da Abbah suma suka kalleta, kallo Mummy tayi tare da kiran sunan ta murya kasa kasa kamar wanda aka taushe ma sheɗa, 


“Mu.. mmy...”


“Na'am Kairat na'am na'am” 


Da sauri Mummy take amsawa har bata iya tsayawa ta sauke numfashi, ɗauke kai tayi ta kalli Abbah da Hajiya Suwaiba sai kuma ta rufe ido kamar mai bachi, ta ɗauki kusan minti talatin a haka bata sake yin koda motsifa balle ta sake buɗe idon, ga dai numfashi tana yi amman ba magana ba alamunta, duk sukayi tsit kamar ba kowa ɗakin. Bayan kamar minti biyar likitoci suka shigo ɗakin tare da Nurses, ɗayan likitan ne ya nemi su Abbah da su fita, Hajiya Suwaiba ce ta fara fita Abbah ne na biyu sai Saif, Mummy kan daker ta fita daga ɗakin.  


A cikin Mota Saif ya rik'a rusa kuka kamar wani mace, har kukan nashi ya tashi lil minal daga bachi ta soma masa kuka, rarrashinta yayi daker ya samu ta koma bachin, 


                         ***              ***               ***

Washe gari, bayan ya dawo daga sallah asuba, ya hau gado ya kwanta kasancewar jiya baiyi bachi ba kwana yayi nafisa yana nema ma matarsa lafiya gurin Allah, bachin nasa bai yi nisa ba ya soma jin kukan Lil Minal, kamin yayi wani yinkuri yaji kukan bakin kofar ɗakinsa, 


“Wanene?” 


Ya tamabaya jin ana buga kofar


“Nice” 


Lubna ta amsa tana jijjiga lil minal, tashi yayi ya buɗe kofar ya karɓe ta


“Mi kika mata” 


“Ban mata komai ba Momy ce tasa ayi mata ɗure madara tun shekaran jiya ba komai a cikin ta” 


Kai kawai ya ɗaga mata ya maida kofar ya rufe ya shiga jijjiga ta saman kafaɗarsa, 


“Mah mah mah” 


Kawai take kira har bachi yayi gaba da ita, saman gadon sa ya kwantar da ita ya lulluɓeta da bargo, ya ɗauki jacket ɗinsa yasa, yana kokarin fita wayarsa tayi ringing, ya daɗe yana kallon screen ɗin ganin bakuwar number, sai da tayi ringing har ta tsare aka kara bugowa sannan ya ɗauka, 


“Gani nan a waje ina son ganinka akwai magana mai muhimmanci da zan faɗa maka” 


“Wanene” 


“Idan ka zo zaka gani” 


Dih dih dih..... Kiran ya katse, ya daɗe yana tunani sannan ya saka wayar aljihu ya fice. 

     A harabar gate ɗin ya fito yana tunani har ya isa gakin gate ɗin, daker securities suk barshi ya fita wai saboda tsaron lafiyarsa duk da haka sai da wasu sojoji uku suka raka shi cikin farin kaya, ganin ba kowa a waje yasa ya ciro wayarsa ya kira number ana ɗauka yace


“Ina kake gani a waje” 


“Ina nesa da gidan ku kasan ba'a bari mutun ya karaso ba tare da izinin ku ba” 


Kashe wayar yayi ya fara tafiya suna binsa a baya, ganin tafiyar ba mai karewa bace yasa ɗayan sojan ya shiga gaba dan basu yarda da wanda inda zaije ba, ɗayan ma babu yadda baiso ya ki tafiyar ba wai ya kira mutum ne yace ya karaso amman Saif yaki dole suka kyalesa, a sannu suka fara hango mota fake gefen tt da bakin glass, sai da Saif ya kusa karasowa kusa da motar sannan ya fito daga motar sanye da farin yadi ya dora rigar sanyi a sama, Saif na ganinsa ya ya kalli securityn yace 


“Za ku iya komawa nasan shi” 


“No Sir just keep walking zamu tsaya a nan amman ba zamu koma ba” 


Cigaba yayi da tafiya har ya isa gurin, 


“Ya akayi” 


Shine abunda Saif ya faɗa yana yi masa wani kallo, sai da ya rungume hannayensa sannan ya kalli Saif yace


“Baka bukatar waɗannan mutanen i won't hurt you” 


“Ba shi na tambaye ka mike tafe da kai” 


“Kan rashin lafiya Kairat ne”


Kallon tsaf Saif yayi masa, 


“Kamar ya me ka sani akan rashin lafiyarta” 


“Safiyyah ce musabbabin rashin lafiyarta, adalilin asirin da tayi mata, shin kasan dalilin warke war da Safiyyah tayi ne ya jefa Kairat cikin halin da take ciki yanzu” 


Cikin rashin fahimta Saif ya kalleshi


“Ban gane ba ya akayi kasan da hakan?” 


“ba zan faɗa maka ba yanzu amman ina son kaje ka samu Safiyyah da Shafa kayi musu wannan tambayar sune zasu faɗa maka hanyar samun lafiyar matarka” 


“Safiyyah bata da lafiya bana jin zata iya yi min wata magana a yanzu” 


“Ta samu lafiya idan kaje gida ka bincika” 


Yana kaiwa nan ya buɗe motarsa har zai shiga sai kuma ya ɗago ya kalli Saif


“Sai dai kuma Kairat na samun lafiya zaka rasa Safiyyah” 


“Deen.....” 


Saif ya kira shi


“Idan na tararda labarin ba haka bane fa” 


“Ka kashe ni” 


Kai tsaye Deen ya bashi amsar, Saif ya sake cewa


“Miye dalilin ka na faɗa min wannan maganar?” 


“Saboda Minal.....”


Cikin wata irin kalar murya ya karasa maganar ya shiga motarsa ya bar wajen, sai da Saif ya daina hangosa sannan ya juyo cike da Tunani ya nufo gida. 



MI KUKE TSAMMANI GABA?


FEW PAGES REMAINING INSHA ALLAH 😊


Keep voting and commenting one heart ♥



56


Part ɗin Momy ya nufo, zuciyarsa cike da sake-sake  saman kujera ya zauna yana shafa kansa, wani tunanin yazo masa, wayarsa ya duba ya shiga nema number Safiyyah, ya daɗe yana nazari kamin ya danna calling, 

Dauke wayar yayi daga kunnensa bayan sun sanar masa da number tana kashe, Number Lubna ya kira ita kan ta shiga sai dai tayi ta ringing har ta kashe ba'a ɗauka ba, sai a kira na biyu ta ɗauka ta muryar bachi


“Hello Yaya” 


“Sauko gani nan parlour” 


Yana faɗar hakan ya kashe wayar, yana mai cigaba da nazari, ta ɗaukar kamar minti biyar zuwa takwas sannan ta fito sanye da kayan bachi ta ɗora top sama, kusa dashi ta zauna tana hamma


“Yaya gani” 


Kallonta yayi a natse


“Ya za'ayi naga Safiyyah yanzu? Kin san inda Gwaggo ta kai ta gurin magani?” 


“A'a amman yanzu ai tana gidan Gwaggo kaje can zaka ganta” 


“Sun dawo ne?” 


“Eh sun dawo tun jiya ko shekaran jiya oh jiya, oh na dai mata amman taji sauki fa” 


Gyara zamansa yayi cike da mamaki yace


“Taji sauki” 


“Eh baka sani ba, maybe dan hankalin ka ba kwance ba yasa Momy bata faɗa maka ba amman taji sauki gaskiya” 


Shiru yayi yana tunani, 


“impossible” 


Da karfi ya furta har Lubna ta kalleshi 


“Lafiya yaya?” 


Kallonta yayi


“Da gaske taji sauki kin ganta da idonki?” 


Tashi yayi yana faɗin


“Lafiya kalau i need to see her” 


A gaggauta ya fice daga parlour, da kallon mamaki Lubna ta bishi har ya fice sannan ta tashi ta nufi ɗakinta, part ɗin sa ya koma ya ɗauki keys ɗin motarsa ya nufi parking space, yana shiga motarsa ya ɗauki hanyar da zata sada shi da gidan Gwaggon sa, a bakin gate ɗin gidan ya fara tsayawa yqna tunanin idan ya shiga me zai ce mata! Ka fara shiga ka fara gasgata zancen Luban tukuna, a nan ya danna horn, mai gadin ya buɗe masa, har kusa da kofar yayi parking, ya fito ya nufi kofar parlour, bell ɗin gidan ya tsaya bakin kofar yana kallon Windows ɗin parlour, 

Sai da ya danna yafi a kirga sannan aka buɗe masa kofar, wata matashiyar yarinya ce sanye da uniform, 


“Ina kwana Yaya” 


Bai tsaya amsa gaisuwar nata ba ya kunno kai cikin parlour yana faɗin 


“Ina Gwaggo?” 


“Tana ɗakinta bari na kira ta” 


Ta faɗa bayan ta maida kofar ta rufe ta nufi ɗaya daga cikin ɗakunan tana karanta, kamin ta karasa Saif ya kirata 


“No Farida zo ba sai kin kira ta ba” 


Da wowa tayi tazo daidai shi ta tsaya, 


“Gani Yaya” 


Dukowa yayi tq yadda ita kaɗai zata iya jin mi yake faɗa yace


“Ina Safiyyah?” 


“Tana ɗakin su Husna” 


“Taji Sauki?” 


“Eh taji sauki haukan ya cire”


Shiru yayi kamar mai nazari, sannan ya sake kallonta yace


“Samo min biro da Paper” 


Da sauri ta juya nufi wani gurin da ina jin an tana deshi ne don aje bags dan  bags ɗin suna da yawa, wata ja naga ta ɗauko ta nufo inda yake ta zauna ta bude ta fiddo littafi ta ɓalli paper ta ciro biro ya mika masa, 


“Thanks” 


Ya faɗa yana kokarin karɓa, a nan ya shiga rubutu a paper ya dunkule ya mika mata tare da bironta, 


“Ga wannan ki ba Safiyyah idan ta tashi bachi kinji?” 


“Toh tafiya zakayi?” 


“Eh kice ma. Gwaggo ina gaida ta” 


Yana kaiwa nan ya juya ya nufi kofar fita. Ya daɗe zaune cikin mota bayan ya isa gida, sai da lil Minal ta faɗo masa a rai sannan ya fita daga motar ya nufi Part ɗin sa, yadda ko yake tsammani haka ta tashi daga bachin sai kuka take tana kiran 


“Mah mah mah” 


Tana bursar da yawu, murmushin karfin hali yayi ya mika hannu ya ɗauke ta


“Yeee kin tashi yar mama” 


Kara fashewa tayi da kuka, ya shiga jijjiga ta ya fito ya nufo part ɗin Momy, dinning ya nufa gurin da ya hango su Momy suna breakfast, Momy ta mika mata hannu


“Zo ki sha tea” 


Juyar da fuskarta tayi ta kara fashewa da kuka, Saif ya ɗanyi Murmushi yaja kujera ya zauna yana faɗin


“Momy ina kwana” 


Momy ta amsa cike da jindaɗin ganin yau ran nasa a sake ba kamar baya ba duk da idan ka kalleshi zaka gane yana cikin damuwa, 


“Momy ai bata manta ɗorin da kika sa akayi mata ba” 


Murmushi tayi, ta shiga haɗa ma Saif tea, 


“Momy anjima Safiyyah zata zo ko da bana nan dan Allah a kira ni” 


“Miya faru?” 


Momy ta tambaya daidai lokacin da ta aje masa tea gabansa, 


“Wai Safiyyah tana da hannu cikin rashin lafiyar Kairat shine nake son na tabbatar” 


“Inji wa kuma wannnan wace irin magana ce haka” 


“Nima haka tazo min sai dai ban tabbatar ba yanzu ne  ake son na tabbatar” 


Momy ta dafe kai


“Wannan abun har yaushe zai kare tsakanin ka da Safiyyah ne? Yarinyar nan daga samun lafiyar ta sai kuma ka ɓullon da wannan abun” 


Bai ce komai ba ya kurɓa tea ya tashi yana faɗin 


“Zanje Asibiti sai na dawo” 


Momy bata ce masa komai ba har ya fice. Ba shi ya dawo gidan ba sai azahar duk da bai samu ganin Kairat ba dan basu barsu ya shiga ba ya window ya tsaya yana kallonta sannan ya dawo gida har lokacin lil minal na lake dake wanka ma daker ya samu ta sauka yayi, yana fitowa ta rarrafa ya ɗauke ta, ɗauke da ita ya saka tufafinsa mai ma bata barshi ya shafa ba turare kawai ya fesa ya fito ya nufo Part ɗin Momy, Mai aikin Momy ce ta karɓe ta da karfi wai za'ayi mata wanka, Saif ko yabi ya ɓata fuska dan baya son jin kukan lil minal ɗinsa, yana kokarin zama Lubna ya fito ɗaga ɗayan parlour tana leken ɗakin Momy har ta karaso kusa dashi ta zauna tana haki, shi dai kallonta yake har ta fara magana


“Yaya Safiyyah ta kira tace ba zata samu damar zuwa ba wai Gwaggo ta hana ta sai ta kara samun karfin jiki, amman Momy tace kar a faɗa maka” 


Fuskar tunani yayi da mamaki, sai kuma ya shi da sauri Lubna ta rika hannunta


“Yaya karka ce nina faɗa maka Momy tace bata son tashin hankali, zata iya yi min faɗa” 


“Ba zan bari taji ba” 


“Toh ina zaka?” 


“Gurin ta sai na tabbatar da abunda nake zargi ki kula min da Lil Minal please” 


Bai tsaya jiran mi zata sake cewa ba ya fice.




57


Kai tsaye ya shigo cikin gidan, kana kallon fuskarsa kasan wani abun ne ke tafe dashi, Sama sama ya gaisa da Gwaggonsa yana tambayar ina Safiyyah


“Lafiya?” 


Gwaggo ta tambaya ganin yanayinsa 


“Lafiya kalau nazo gaishe ta ne naji ance taji sauki” 


“Eh taji Sauki bari a kira maka ita” 


Tashi tayi ta nufi ɗakinta ba ɗan ta bamsu ba komai ɗin ba, dan tasan Safiyyah bata da matsayin da Saif zaizo gaishe ta ɗan taji sauki duk da tana ganin yana tausayin halin da take ciki, amman kuma miyasa tun lokacin bai zo ba sai yau! 

  Da wannan sake-saken ta tura kofar ɗakin Safiyyah ta shiga. Kofar ɗakin ya tsura ma ido har sai da yaga fitowar Gwaggo, 


“Gata nan zuwa” 


Kai kawai ya ɗaga mata ta shige ɗakinta, ya sake maida idonsa kan kofar ɗakin da yake saton Safiyyah na cikin dan ɗakin Gwaggo ta shiga, ta ɗan jima kamin ta fito har ya fara tunanin koya tashi ya shiga ɗakin ne, sai gata ta fito sanye da Abaya fara da farin gyale ta lulluɓe kanta, a hankali take tafiya har ta k'arasa kusa dashi, ko wannen su yana kallon ɗan'uwansa, ita tana masa kallon data saba masa sai dai yau ya ɗan babbanta dana kullum, shi kuma yana mata kallon ta iya zai fara! Shi fa har yanzu bai gama yarda ita ce da hannu a ciwon Kairat ba, tunawa da abunda tayi ma Minal yasa shi kawar da wacan tunanin nasa, ya ɗauke kai daga kallonta yana muna mata kujera


“Zauna mana kinyi min tsaye a ka” 


Sai a lokacin ta samu damar yi masa magana, sai dai jikinta yana bata kamar wani abu zai faru, yadda gabanta yake faɗuwa ita kanta tasan ba lafiya ba duk da wata zuciyar nace mata na ganin Saif ne sai dai bata gama gasgata hakan ba, 


“Ya jikin naki?” 


Muryasa ta daki dodon kunnenta, kamar ta ɗago kai ta kalleshi sai kuma taji ba zata iya ba, kanta a kasa ta amsa mishi


“Naji sauki sosai” 


Shiru ne y biyo baya, kamin ya cuta maganar data razana ta


“Kin warke Kairat ta kwanta, wani yace min warke warki ya haddasa ciwon Kairat” 


A razane take kallonsa, ta kasa buɗe baki tace masa komai sai tunanin take wanda ya faɗa masa wannan maganar take. Shafa, no Shafa ba zata sona asirinta ba to wanene? Ita kaɗai fa tasan sirrinta, ina Saif yaji wannan maganar? 


“Ba ki ce komai ba” 


Ya faɗa yana mai tsare ta da ido, zufa ce ta karyo mata ta gangaro tare da hawaye. Daga ita har shi kallon Kofa sukayi ganin shigowar Momy, Saif bai jidaɗin ganinta ba sam dan yasan ba zata barsa yayi abunda ya kawo shi ba, aiko ya canka a daidai dan tana karasowa kusa shi ta katsa masa tsawa


“Tashi ka wuce gida” 


“Momy..” 


“Rufe min baki ba zai yiyu ba Saif ba kai kaɗai muka haifa ba amman kullum kai ne da matsala cikin gida, karka manta mahaifinka yana da wasu yayan maza idan har ganin kake ni kaɗai na haifa namiji” 


Yanayin ta ya nuna ranta a ɓace yake kuma yasan ya baza ta saurara masa ba, mafita ɗaya ce yabi abunda tace, tashi yayi ba ɗan yaso ba sai dan bashi da mafita sai wannan ya nufi kofa, har zai fice ya tsinkayo muryarta tana magana dashi


“Gaskiya ne Saif, lafiyar dana samu ya haddasa ciwon Kairat” 


“Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un” 


Momy ta faɗa tana zauna, wannan furucin na Momy ya haddasa Gwaggo fitowa ɗaga ɗakinta daman can a tsawale take tana son tasan wainar da suke toyawa a falon, 


“Lafiya, miya faru?” 


Momy bata bata amsa ba sai ta kalli Safiyyah tana faɗin


“Me kike nufi asiri kika mata?” 


Kallon Momy tayi ta kalli Saif ta sake kallon Momy sai ta soke kai, hawaye na mata zuba


“Ba sabon asiri ba ne” 


Sai kuma tayi shiru, dawowa Saif yayi ya zauna Gwaggo ma ta zauna sai duk suka kafa mata ido, ta daɗe sosai kamin ta fara magana


Wannan ya faru da gaske


“Lokacin da nake haukan son ka ne Saif, bayan rasuwar Minal a maimakon ka kalle kace kana so na sai ka tsallake ka kace yar'uwarta kake so, 

   A lokacin ne ya shiga damuwa da neman mafita, sai kawata Shafa ta kaini inda wani malami ya fara yi min aiki akan zaka so ni, ya bani wani kwalli yace ya na shafa, ranar da na shafa kwallin ranar ce kayi min marin da baka taɓa yi min ba ba kuma tare da nayi maka wani abun ba, daga ranar sai na watsar da lamarinsa na sake zuwa gurin wani shima akayi a banza shiru ba, kuma sake zuwa gurin wani shima haka, a haka muka ziyarce malamin ukun huɗu sai a na biyar muka dace shima kuma cewa yayi dai idan baka tare da Kairat sannan ne zaka iya aure na, kai nasa aka fara yima sai dai duk inda na buga sai ace kai asirin ba zai kama ka ba, ita nayi mata aka ce ba zai kamata ba idan har ina son na samu nasara toh sai na ɗauki aljana” 


A nan tayi shiru tana hawaye, kowannen jikinsa yayi sanyi da jin tomin taɓun labarinta, sai da ta share hawayenta sannan ta cigaba


“Gani bana da mafita sai wannan yasa na zuba kuɗi akayi yanka aka bada duk wani abun da aljanar ke bukata na ɗauketa, sai aka samin ita cikin kwalba, da ita nake magana a duk lokacin dana tashi, farkon abunda ta farayi shine haddasa tsoron Minal a don Kairat, ita ce tace min naje na samu kayan da Minal tafi sawa cikin tufafin ta na kaima Malamin sai nace ba zan iya samun rigar ta sai tace na kawo hoton ta, 

nan ma nan ma nace bana dashi sai Shafa tace min na shiga media zan samu tunda ta taɓayin instagram tana kuma Facebook sannan jarida da dama sun buga hoton ta lokacin da ta rasu da lokacin auren ta da kuma lokacin da taso kashe kanta,

      hakan nayi na samu hotonta na kai malamin ya haɗa wasu siddabaru ya bani yace naje cikin gidan da zata zauna nayi gina na saka kwalbar a kasa sai wannan layar a sama na rufe, 

a lokacin ne na samu sa'a dan za'a je gyara ɗakin Lil Minal ne, 

a hakan mukaje tare da Lubna da shafa, Shafa ce ta ɗauke mata hankali har nayi abunda zanyi na gama bata gano ba, 

Tun daga lokacin ne duk abunda aljanar tayi ma Kairat sai na sani, takan faɗa min tana son haddasa fitina tsakanin ku amman ta kasa saboda tana son shiga cikin jikin Kairat ne gashi ita kuma tana addu'a duk lokacin data raɓe ta sai taji kamar zata kama da wuta, 

Kuma kullum cikin rufe jiki take, tayi-tayi har ta gaji bata samu sa'ah ba sai wata rana da Kairat ta cire ɗankwalinta ta wuni bata saka ɗankwalinta a kai ba, 

  A ranar ne ta samu sa'ah ta shiga jikinta, ta rika. Haddasa mata tsoron Minal tana ganin kmar ita dan kawai ta gagara zama a gidan ta fita. Wata rana ina zaune parlour sai naga aljanar cikin bakin kaya jikinta naci da wuta tace min bata daina Addu'a ba duk ta qona ta, kuma yanzu an tono layar dana binnen, 

kamin na yi wata maganar sai kawai yaji tayi ciki na, sai wani irin zafi ya rufe ni bansan lokacin da nayi ihu ba, daga lokacin ban sake sanin inda nake. Ba sai lokacin da na farka na gannin gaban malamin, 

Ban san hauka nayi ba sai da Gwaggo ta faɗa min, a gaban gwaggo nace zan rabu da aljanar sai malamin ya tuna min da alkawarin dana ɗauka ba rabuwa da ita har a bada idan har ina son rabuwa da ita toh sai na fasa kwalbar idan kuma har na fasa kwalbar na karya alkawari zata iya cutar dani, 

        A nan ya faɗa min a halin yanzu ma data fita jikina tana jikin Kairat kuma ta samu sa'ar shiga jikinta ta ta dalilin kiran sunanta da tayi ta amsa kuma data ganta sai ta ihu bata ambaci Allah ba, 

Ya faɗa min cikin biyu ɗaya ko dai ni ko Kairat” 


Tana Kai aya ta fashe da wani irin kuka, Gwaggo ta sun kuyarda kai, Momy da Saif suka kalli Juna. 



Please do voting and commenting for sake of God 😊


Love you all guys 



58



Kuka ta rika rusawa, jikinta har rawa yake, dukan su sai da idanunsu suka cika da kwallah, banda Saif da ya tafi wata duniyar ta tunani. Momy ta share hawayen idanunta ta kalli Safiyyah 


"Ni na rai ne ki tun kina karama har kika girma ni nayi miki tarbiya na baki duk wata kulawa da kike bukata, amman ban nuna miki wannan hanyar ba baki tashi kika ga ina binta ba, miya kaiki aikata wannan mummunan aiki Safiyyah?" 


Dagowa tayi ta kalleta


"Momy kin yi gaskiya baki nuna min irin wannan hanyar ba ban kuma ga kina binta ba, amman kece kika sani shiga wannan halin kika rufe ido kika kyale ɗanki yayi yadda yake so bayan kinsan ina sonsa kuma shi ne ya fara nuna min son tun farko, 

. Nasan da ace nice bana sonsa da sai kin bi duk hanyar da kike ganin zata ɓulle ki aura masa ni amman da yake nice nake so sai kika rufe ido kika manta da halin da zan shiga" 


Saukowa Momy tayi daga saman kujera zuwa kasa carpet, ta kama hannayen Safiyyah tana hawaye


"Ban taɓa jin banbanta ki da ɗan dana haifa ba, naso cillas ta Saif ya soki sai ya juya min baya Mahaifinsa kuma ta goya masa baya, kullum cikin ganin laifin sa nake, tun da kika kamu da wannan ciwon ban sake ganin farin Saif ba daga ni har mahaifinsa, 

kuma saboda ke ne Safiyyah da ace ina da halin da zaki aure dana sa ya aure ki, ki daina zargina Safiyyah" 


Lumshe ido tayi, tana wasu irin zafafan hawaye, 


"Babu laifin Momy a ciki, ba kuma laifi na ko na wani wannan laifin kaddara ne, shin zaki iyaja da ita?" 


Ba tare daya motsaa inda yake ba yayi mata wannan furucin, buɗe ido tayi ta kalleshi kamin tayi wata magana ya sauko saman kujera ya duka kasata yadda zata iya fuskantar shi, 


"Ashe ke jahila ce Safiyyah, tunda kike ganin Momy zata iya yi miki abunda Allah baiyi miki ba, bayan nan kika tsallake kika je gurin wani boka yayi miki abunda Allah baiyi miki ba jin jahilci kaddara, kin kuma jahilci Allah, dan shine yadda ya so ga wanda ya so ga kuma wanda ya so tun lokacin da kika yi kulle kulle wa Minal bai isa ya nuna miki duk abunda ya samu mutun daga Allah bane, yanzu kuma sai kisa na aure ki dole jahila kawai" 


A fusace yake mata maganar, har sai da taja baya tana sauke dogon numfashi, sannan ya kalli Momy yace


"Tashi muje Momy karki sake zubar da hawayen ki akan wannan" 


Bai jira cewarta ba ko kuma tashin ta ba ya nufi kofar fita, Momy ta rik'a fuskar Safiyyah 


"Miyasa kika faɗi wannan maganar Safiyyah? Miyasa baki rufa ma kanki asiri ba?" 


"Saboda a yanzu na banbance tsakanin tsakuwa da hatsi, na kuma gane shayi ruwa ne, na gaji Momy lokacin kuka ya kare kunci da bakin cikin soyayya ya kare na shafe shafin Saif a zuciyata, 

Na yarda da babu mai maka sai Allah Momy babu yadda banyi ba amman Saif yaki ya kula ni ma balle ya so ni, Momy na aikata abubuwa da yawa sanadin soyayyar Saif kuma gashi ban kai ga cin nasara ba, nayi sanadin shigar Minal cikin halin bak'in ciki, Soyayyar, kiyayyah, da kuma kishi abubuwa ne da suke rufa idon bawa, baya ji baya gani har sai ya aikata abunda zai aikata sannan ya gane kuskuren da yayi, 

Na ɓata tsakanin ta da Saif, na ɓata tsakanin ta da Deen, kuma ta mutu ba tare da na nemi gafarar ta ba, na yaudari kai na da abubuwa da dama da zuciyata ta rika raya min kamar wani zai iya bani ba Allah ba, na cuci kaina na yi hasarar lokaci na ɓata tsakanin na da ubangiji na na kuma ɓata tsakani na da ku" 


Kuka take sosai, Momy ma rungume ta tayi tana kukan, Gwaggo ma kukan take har da sarkewa. 



*** *** ***

Kansa saman sitari yana sauke ajiyar zuciya, jin yake ya tsani Safiyyah sosai fiye da da, duk da wani ɓangare na zuciyarsa yana tuna masa da irin son da take masa, sai dai kuma abubuwan da ta bayyana masa yasa ya kara tsanarta tunawa da Minal ga kuma halin da Kairat take ciki yanzu. Ya dade cikin motar sannan ya fito jikinsa kamar a mace ya nufi cikin gidan, saman kujera ya zauna ya dafa kansa yana murzawa, 

Sai da yayi awa uku da dawowa gidan sannan Momy da dawo fuskarta a kumbure alamar kuka tayi sosai, Lubna ce hankalinta ya tashi ganin Mahaifiyarta haka, gashi Saif ɗin ma tun da ya dawo baiyi ma kowa magana ba, kuma kana ganinsa kasan yana cikin damuwa ta damu sosai, saɓanin Saif da tasan me ke faruwa, da kallo ya bi Momy har ta zauna sannan ya sauke ajiyar zuciya ya girgiza kai yana cika ma bakinsa iska


"Ni Momy ban ga anfanin wannan damuwar da kike sa kanki ba, wannan yarinyar bata da tunani kuma wallahi duk abunda ya samu mata ta sai na raina mata hankali" 


"Kai ma ka yarda tana iya yi mata abunda Allah bai yi mata ba kenan" 


Kan Momy a kasa take masa maganar, Lubna na zaune kusa da ita cikin da rashin fahimta idan ta kalli Momy ta kalli Saif. Kai ya girgiza 


"Aa Momy ni ban yarda da wannan ba, kawai dai ita ce sanadi tun har ta faɗa da kanta" 


"Kamar yadda ka zamo mata sanadin shiga halin da ta shiga ko?" 


"Oh Momy ki daina shigar mata, kina son shafi laifinta ba, bata gurbi abunda ta shuka ba sai nan gaba" 


Tashi yayi yasa hannayensa aljihu, ya nufi kofa 


"Karka fasa kwalɓar nan Saif karka sake jefata cikin wani hali" 


Tsayawa yayi cak, ba tare da ya juyo ba yace


"Ban jefa ta ba Momy ba kuma zan jefa ta ba, ita dai ta jefa kanta" 


"Tun lokacin dana fara haɗuwa da Minal Kairat ce ka fara labarta min, sai kuma gashi kazo min da maganar Minal har ka aure hankalin ka bai kwanta ba har sai da ka auri Kairat, yanzu kuma ta kamu da rashin lafiya duk kabi ka fita hayyacinka har kana kokarin ɓatawa da yar'uwarka, 

Nasan Kairat tayi maka hallacin tun da ta shayar da lil Minal kuma yanzu tana ɗauke da wani cikin naka, amman ina son kasan wani abu guda ɗaya, Ana chanja mata ba'a chanja yar'uwa ba shin yanzu idan ka rasa Kairat yaya zaka ji?" 


Juyowa yayi da sauri ya kalleta, kamar zai yi magana sai kuma yayi shiru ya haɗiye maganar, tare da numfashin sa, sai a lokacin ta ɗago ta kalleshi 


"Haka zaka misalata yadda Safiyyah take ji a ranta baka da tausayi Saif ka canja kwatakwata kamar ba kai ba kana son kanka da yawa babu ruwanka da damuwar kowa sai taka zuciyarka ta mace! Tirr da irin son da kake yima Kairat tirr da son da xai rufe maka ido ka kasa ganin kowa sai ita kaji tsoron ranar da sonta zai wahalar da kai hakkin Safiyyah ya dawo kanka!" 


Tunda ta soma maganar ya dinga jinta gan gan gan kamar ana sara masa gatari aka, sam bai zaci wannan maganar daga Mahaifiyarsa ba, tun tashin ta Momy bata taɓa faɗa masa wata magana makamanciyar wannan ba, amman a yau ta faɗa masa saboda Safiyyah, tsabbas ranta a ɓace yake yake dan har cikin makoshinta furucin ke fitowa, 

Wani dogon Numfashi Lubna ta sauke zuciyarta na bugawa da karfi ta kalli Momy ta kalli Saif, Shima kallonta yayi ya kalli Momy sai ya ɗauke kai ya fice. 

Wata tafiya ce yake mai kamar sauri-sauri kuma ba sauri ba, kallo ɗaya zaka yi ma fuskarsa ka fahimci tafiyar ɓacin rai ce yake, yadda ya bar gida sai da hankalin securities ɗin ya tashi, haka ya hau tt yana wani irin gudu kamar dansa kawai aka shinfiɗa titin, kamar wani ifiritu haka ya isa gidansa cikin kankanen lokaci. Har ya zauna maganar Momy ce take masa yawo a kai, tashi yayi ya nufi firjin ya bude ya ɗauki robar ruwa ya ɗaga kansa ya kafa kai, da wani irin karfi yake shan su, sai da ya kusa shaye wa sannan ya sauke kansa yana maida numfashi da karfi, ya jefar da kwalbar, saman kujera ya dawo ya ya zauna ya lumshe ido,har na kusan na mintuna talatin, can kuma ya buɗe ido da sauri kamar wanda ya tuna da wani abu ya tashi ya fito harabar gidan, ma'aikatan gidan ya fara kwalama kira, jiki na rawa suka iso cikin girmamawa, ɗaya daga cikin su ya kalla ya nuna masa gefen da itacen gidan suke


"Can nake son kuje kuyi ta binciko min wata kwalba, tana nan cikin kasa ku duba da kyau karku ce min baku ganta ba" 


Da "Toh" suka amsa suka nufi gurin shi kuma ya juya ya dawo falon ya zauna, yatsun hannunsa cikin gashin kansa yana matsa gashin. 

Bayan kamar minti arba'in, aka kwankwaso kofar parlour, ya ɗan daɗe kamin ya bada izinin shiga 


"Yes" 


Turo kofar akayi aka shigo, hannunsa rike da kwalbar mai cike da hayaki, ya mika masa


"Ga abunda muka gani" 


A hankali ya buɗe ido ya sauke su kan kwalbar, da ido yayi masa nuni daya aje ta saman tebur ɗin dake kusa dashi, yana ajewa ya juya ya fice.

Kwalbar ya tsura ma ido, yana taɓa hancinsa kamar mai tunani, zuwa can ya tashi daga gimciren da yake still yana kallon kwalbar, sai da yayi bismillah sannan ya kai hannu ya rik'a kwalbar ya ɗaga sama yana kare mata kallo, wani abu ne a ciki mai kamar hayaki kamar toka da wani abu kasanta ja kamar ruwa jini,

Bismillah ya sake yi ya cira kwalbar iya karfinsa ya buga kasa, a nan take kwalbar ta watse.



59



Farin hayak'i ne ya turnike gurin daga bi sani hayakin yayi sama ya fita ta windo, Saif kan kallon hayakin yake ba ko kyata ido har sai da ya daina ganinsa, sannan ya kauda kai yana jan numfashi, ya daɗe yana nazarin maganar Safiyyah da kuma ta Momy sai dai maganar Momy ce take ɓata masa rai duk lokacin daya tuna, 

abunda ya aikata a yanzu gani yake ya aikata daidai ko ba komai ita ta jama kanta kuma itace silar rashin samun kwanciyar hankalin aurensa ga kuma laifinsa da Momy take gani duk a dalilinta, 

koma miye ta aikata can taje ta karata tun ba shi ya aike ta ba. tsiya ke tada tsohon bashi inji Hausawa, a nan ne ya soma tunanin taya akayi Deen ya san da wannan shirin na Safiyyah? Ita tambayar da ta rika zo masa a rai kenan tana masa yawo a kwakwalwah, 

wayarsa ce kawai mafita, haka wani ɓangare na zuciyarsa ya amsa masa, a hannunsa ya rik'a juya wayar bayan ya fiddo ta daga aljihu sa, kamin ya soma shafa screen ɗin yana kallon hoton lil Minal, sai da wayar da fara ringing sannan ya maida hankali akan wayar, sai dai bai kaita kunnensa ba sai har sai da mai kiran yayi daf da katsewa, 


"Ta ya akayi kasan da wannan labarin?" 


"Ta amsa laifinta kenan? Ka tabbatar da gake nake ko?" 


Aka amsa masa daga ɗayan ɓangaren, bai damu da ba da amsar tambayar da aka masa ba sai ya a kara jaddada tasa tambayar


"Taya akayi kasan da wannan plan ɗin?" 


Shima ya ɗan daɗe kamin ya amsa 


"Wata rana ne na fito daga kauyen mu, sai na haɗu da motar Safiyyah ita kuma tana kunna kai cikin kauyen, ganin kamar motar dana sani yasa na juya ya rika bin motar a baya har muka raba hanya,

Ta nan ne na hango fuskar Safiyyah kasancewar glass ɗin motor a sauke yake, a haka nayi ta binsu har naga gurin da sukayi Parking, a bakin kofar gidan wani babban boka dake garin namu, 


Nayi mamakin yadda akayi Safiyyah tasan da wannan bokon, tunawa da abunda tayi min ta kuma yi ma Minal sai ya kawar da wacan tunanin nawa, 

Bayan naga gidan da suka sauka sai nayi tafiya sai washe gari na dawo gurin bokan na zuba masa kuɗi mai yawa, a nan dake sai ya bayyana min abunda ke tafe da ita da kuma abunda ya aikata mata, ban gasgata hakan ba har sai da naji labarin Kairat ba lafiya,

Dana je gurin Mummy dan sanar mata sai na tarar hankalinta a tashe yake bata ma saurare na balle ta fahimci me nake nufi, nasan kai kaɗai ne mafita wanda zan faɗa ko da ba zaka yarda da ni ba, 

Sai dai nasan wata rana zaka gasgata ni ka kuma yarda ada abunda na faɗa" 


Lumshe ido Saif yayi, lokacin da Deen ya kai aya a bayanin sa, sannan ya sauke ajiyar zuciya ya tasa leɓensa ya ce 


"Thank you" 


Deen bai kara ce masa komai ba ya kashe wayar,bayan kamar minti biyar wani kiran ya kara shigowa, ba tare daya duba mai kiran ba ya dannan picking yasa hands free, 


"Kana ina Saif?" 


Muryar Nasir ce hakan ya tabbatar masa da shine ya kira ko da ba number sa bace, ya ɗn bata lokaci kamin ya amsa


"Ina gida" 


Wayar ya tsurawa ido bayan katse kiran, har lokacin zuciyarsa cike take da ɓacin rai. 


Sai da Nasir ya kare masa kallo sannan ya zauna kusa dashi yana faɗin


"Lubna tace min kayi faɗa da Momy miya faru?" 


Ba tare daya kalleshi ba ya amsa


"Bata faɗa maka dalilin faɗan ba bata ce maka mi nayi ba?" 


"Bata ce min ba, ta dai kira ta faɗa min" 


Sai a lokacin Saif ya kalleshi ya soma labarta masa abunda ya faru, dan abokin dariya ba'a ɓoye masa kuka, shiru Nasir yayi yana nazarin lamarin, bai ga. Laifin Saif ba ko kaɗan itama Momy ya san zafin rai ne ya haddasa tayi haka, kallon Saif yayi ya sake kallonsa damuwa ce kwanace a fuskarsa wanda ke nuna ta zuciya tafi wannan yawa, koba komai yasan yadda Saif ke gudun zuciyar Momy baya son ganin ɓacin ranta sam, kuma hakan kan iya haifar da ɓacin ran Abbah, Hannunsa kan kafaɗar Saif ya ce 


"Ka kwantar da hankali i will talk to her" 


"Ba zata saurare ka ba, idonta a rufe yake a yanzu ta kasa fahimta ta saboda Safiyyah, bata dubi halin da nake ciki da kuma wanda zan shiga" 


"That's Why nace zan yi magana da ita Just have a faith zamu samu mafita" 


Kai ya girgiza masa, shi kuma ya tashi sai shima ya tashi suka fito tare, shi ya ɗauki hanyar gidan Momy shi kuma ya nufi asibiti, 


Yana yin parking Lubna ta fito ta tarbershi, sai da suka kawo kofar shiga parlour ta fara masa magana kamar mai raɗa, 


"Momy ba zara saurare ka ba Ya Nasir, ko ta saurare ka ba zata fahimci abunda kake so ta fahimta ba, nima ɗazu akan hakan sai da ta tashi mari na" 


Ya ɗan zaro ido yana kallonta da yar dariya 


"Kece kema dakin samu rabon ki, amman ni nasan zata saurare ni" 


"Wallahi wahalar da kanka kawai zakayi kila ma kai ma ta kwaɗa maka marin" 


Wannan karon dariyar gaske yayi 


"Tana ina ne?" 


"Tana nan parlour ta haɗe rai sosai" 


Har lokacin magana take masa a raɗa wai kar Momy taji, kumatunta kawai yaja ya kunna kai cikin parlour, bayan kamar mintuna bakwai ita ta rufa masa baya. 


Har kasa ya risina ya gaisheta kamar yadda ya saba, sannan ya zauna a kujerar dake facing ɗin na ta, cike da fargaba ya soma magana dan shi ma kansa ya tsorata ta ganin yanayinta


"Momy, bai kamata a ce kina fushi da Saif ba, bashi da laifi cikin wannan lamarin kuma ki daina ganin laifin Kairat ita ma bata da laifi Momy Saif shine kaɗan ɗa namiji da kika haifa, baya da farinciki sai naki ya kamata a ce ke ce kika fi kowa fahimtar sa"


Yawun bakinta ta haɗe ba tare da ta kalleshi ta ce 


"Kasan wani abu Nasir?, Safiyyah tana sa gaskiya naso kai ma da yawa, da ace Saif ne yake son ta da duk yadda zanyi sai naga nayi wajen ganin ya aure ta, ko ka nasan ba karamin shiga da fita zakayi ba wajen ganin abokinka ya samu abunda yake so, 

Safiyyah Marainiya ce Nasir a hannu na ta tashi ya kamata ace na sama mata duk wani farinciki da take bukata, ban taɓa saka ta abu tayi min musu ba, duk abunda tasan yana faranta min itace kan gaba wajen aikata shi, sam sam sam ban kyautawa Safiyyah ba" 


"Amman Momy yanzu.... -" 


Hannu ta ɗaga masa, 


"Ka aje kalaman ka Nasir, nasan kana kokarin kare abokin ka ne" 


Bata tsaya jiran komai ba ta tashi ta nufi ɗakin ta, a sannan ya maido kallonsa ga Lubna ta ɗaga masa kafaɗu


"Ai na faɗa maka ba zata saurare ka ba" 


Sumkuyar da kansa yayi kasa yana jinjina al'amarin. 


Abu kamar wasa sai gashi Momy ta kusan kwashe kwana biyu babu ruwanta da Saif da duk abunda ya shafe shi, babu yadda bai yi amman taki ta kula shi, saboda har yanzu bata daina ganin laifinta ta, a duk lokacin da ta tuna Saif take ɗorawa laifin, gashi tana son zuwa sake duba Safiyyah amman ta kasa, saboda tunanin abunda zata ce mata. A ɓangaren Saif kan jin yake kamar ace masa rai ya huta, dan abun yayi masa yawa, ga matarsa a kwance, har yanzu ba wani sabon labari ga matsalan Momy shi, Mummy ma ta shirya komai da zata ayi aka kaita waje don duba lafiyar ta amicewar Saif kawai ake jira shi kuma ya kasa aiwatar da komai saboda Momy taki tasa baki cikin lamarin, cikin yan kwana biyu nan duk yabi ya rame abinci kirki baya ci iya kacinsa yan ruwan tea ko juice, ita kanta Momy tana tausayin halin da ɗan nata yake ciki ta dai ki nuna masa ne saboda har yanzu bata daina ganin laifinsa ba, dan iya kuskure tasan yayi, amman kuma ya za'ayi abun duk da ya girma ya riga ya gama girma, kuma tun ran gini tun ran zane. 

Babu ani gwari a tare dashi haka ya shiga ɗakinta, sai da ya zauna kusa da ita kasan carpet sannan ya kalleta 


"Momy an wuni lafiya" 


"Lafiya kalau ya jikin matar taka?" 


"Da sauki, Luban tace kina nema na" 


"Eh akan maganar matar ka ne, shawarar da zan baka ka bar matarka a nan, da nan da can duka ɗaya ne tunda Allah dai shine yake bada lafiya kawai kasa Allah a gaba kayi ta mata addu'a" 


Dagowa yayi ya kalleta akaro na biyu, dan bayi zaton jin wannan maganar daga bakinta ba, 


"Ina nan ina yi Momy kuma Insha Allah haka zanyi" 

"Allah ya bata lafiya" 


"Amin" 


Ganin ta kishingiɗa yasa shi tashi ya fito daga ɗakin zuciyarsa cike da tambayoyi, kao tsaye ɗakin Lubna ya shiga, bayan ya baro ɗakin Momy, tana zaune tasa plate ɗin abinci gabanta sai aikawa take tana dannar waya, 


"Ke"


Ta juyo da sauri ta kalleshi, 


"Yaya shigo mana ka tsaya can ko wani abu kake so ne?"


Shigowa yayi, yayi mata tsaye a ka, 


"Mi akace da Momy yau"


Dariya tayi, 


"Daman nasan sai ka tambaye ni shiyasa ya shigo ɗaki ai, kaga ta canja yau ko?" 


Kai ya ɗaga mata, 


"Wallahi Daddy ne ya rufe ta da ruwan masifa, yace shi sam na zai ɗauki wannan a gidan nan ba, akan me zata rika maka haka, yace idan har bata tausayin halin da kake ciki ai ta tausaya ma lil Minal, 

Yace kuma Safiyyah ita ta jefa kanta cikin mugun hali, ba kuma ba a cilasla maka yin abunda baka tashi ba, yace kuma Safiyyah itace shi take yar'uwarsa ba Momy dan haka babu ruwanta da abunda ya shafe ta, 

Daga karshe yace duk abunda ya same ka ita ce kuma ba zai kyale ba, yace duk kabi ka rame ka fita hayyacin ka da wani zaka ji!"


Shiru ya ɗanyi kamin ya ce 


"Ke taya akayi kika ji?" 


"Nice ma kai ma Daddy gulmar ai" 


"Wai daman Daddy bai sani ba?" 


"Eah mana, wacan karon ma ai ɗan yaga Safiyyah ta haukace ne shiyasa kaga yayi maka wannan faɗan kuma Momy ce take faɗa masa wai ai duk kaine da laifi" 


"Thank you" 


Haka kawai ya faɗa ya juya, yana murmushi ya fice. 


*** *** ***

Kamar ko yaushe, yau ma ya daɗe yana addu'a bayan ya kare sallah Nafila ta karfe uku da yake yi kullum, ya faɗawa Allah bukatar sa ya kai kukan sa a inda za a share masa, sannan ya tashi jiki ba gwari ya nufi kujerar dake gefen gadon ya zauna, tsare ta yayi da ido, yana tunano yar karamar rayuwar da sukayi a tare, sannan ya kai hannu ya shafa fuskarta da ta bushe, daga bisani ya tura hannubsa cikin nata ya rike yana murza yatsunta a hankali, ajiyar zuciya ya sauke ya jinginar da kansa jikin gadon, jin ta motsa hannunta bai sashi ya ɗago ba dan ba sabon abu bane a yan kwana ki nan takan motsa hannun, amman ba magana ko kuma wani motsin, 


"Sa... I.. F" 


Cikin wahalalliyar murya ta kira sunan nasa, aiko ba shi ya ɗago da sauri ganin idonta a buɗe yasa shi gwalo nashi idon ya saki baki yana kallon ikon Allah, ita kan sai kallonsa take da dishi dishin da take ganin, da ba dan kashin turarenta ba da kuma. Sanyi hannunsa ba da ba zata iya gane shi ba, daga kwance ta dake ya rungume ta, kamin ya ɗauke cak ya rik'a waliliya da itar tsakar ɗakin, zuwa can kuma ya ajeta ya faɗi yayi ma Allah Sujadar godiya, sannan ya ɗago ya sake rungume, 

Ita kan sai kallonsa take tun tana gani dishi dishi har ta fara gani daidai, tayi kokarin ta tunano abunda ya faru amman ta kasa, iya abunda ta sani shine ta daɗe tana bachi, zaunawa yayi saman gadon rumgume da ita kamar wata karamar baby ya rik'a fuskarta


"Kairat kina iya gani yanzu kina iya jina? Akwai inda yake miki ciwo? Meke damun ki yanzu?" 


Hawaye ne ya gangaro daga idonsa, hawayen da ba zan iya tantance na minene farinciki ko akasin haka!. Hannu tasa ta shafe masa hawayen tana kallon idonsa, wanda da ita dashi ban san na waye yafi zurfi ba, 


"Saif kuka kake yi? Mi ya faru da ni?" 


"Zan faɗa miki komai daga baya kawai ki faɗa min mike miki ciwo a yanzu?" 


"Babu" 


"Kin tabbata?" 


Kai ta gyaɗa masa, ya tashi, ita dai kallonsa kawai take har ya fice, be daɗe ba ya shigo tare da wasu likitoci guda biyu, Mummy ce ta uku, tayi mamakin ganin yadda ake mamakin tashinta sai abun ya koma mata kamar mafarki, 


_Miya faru da ni?_ shi ne abunda take ta tunano wa take kuma tambayar kanta amman ba amsa, bayan fitar likitocin Mummy ta rumgume tana kuka, tana yima Allah hamdala, 


"Mummy miya faru dani" 


"Komai ma ya faru dear na gode Allah da ya dawo min dake daidai" 


Tana kallon Saif ya sakar mata murmushi, sannan ya zauna saman gadon yama mai lumshe ido da buɗewa, Mummy ta tashi cikin zumuɗi


"Bari na haɗo miki tea ki sha ko kina son wani abun" 


"Tea ma is okey" 


Cikin sauri ta fita, sai ita kuma ta kalli Saif da fuskar damuwa 


"Miyasa aka kawo ni asibiti? Mi ya faru dani ne wai?"


Murmushi yayi, 


"Ni kai na bansan abinda ya faru dake ba, ni dai na dawo ne sai na tararda ke kwace a kasa kin dafe ciki baki iya magana, a nan ne sai na kawo ki asibiti daga lokacin sai hankakinki ya bar jikin ki" 


Shigowar Mummy ce tasa duk suka kalli kofa, Kairat sai nazarin maganar take dan har yanzu bata gano musabbabin abun ba, Mummy da kanta ta rika bata tea cikin wani irin jindaɗi, Kairat ta lura da hakan, sai tasa hannunta ta rika hannun Mummy, Mummy kuma ta jimke hannun jinjinjin, 


"Da ace na rasa ki Kairat da bansan yadda rayuwata zata kare ba" 


"Mummy ba zaki rasa ni ba, ki daina tunanin hakan"


Ta shafi kanta zuwa gefen fuskarta, idonta cike da hawaye ta ce


"Ina fatar haka" 


Ta ɗauki lokaci a ɗakin, sannan ta ɗauki cup ɗin tea ta fita, Saif kamar ita yake jira ya dawo kusa da matarsa, ya rungume ta. 

A jikinsa ta karasa bachin, duk da ba wani bachi sukayi ba. Hasken asuba na fara fitowa su Hajiya Suwaiba suka iso tare da Abbah, daman tun cikin dare Mummy tayi musu waya ta sanar musu, ganin su ne yasa Saif mika ma Mummy cup ɗin tea dake hanmunsa, ya ɗan matsa ba bada space tsakani su, sai Mummy ta cigaba da bata tea shi kuma yana gaisawa da su, Abbah ya kalli Mummy yana murmushi 


"Hankali ya kwanta ko Ummu Kairat?" 


Murmushin itama tayi, ta shafi kan Kairat, Hajiya Suwaiba sam bata jindaɗin maganar ba sai dai bata nuna masa ba, dan a yadda ta fahimta a yanzu yana son Mummy fiye da tunanin ta, ganin yadda duk damuwar ta ta zame masa tasa, a halin da Kairat take cikin ta fahimci Mummy yafi tausaya ma sama da ƴarsa Kairat. Hajiya ta murmusa irin murmushin da bai kai zuci ba tace


"Yanzu kuma ai kuka da tunani ya kare ko?" 


Mummy dai murmushi kawai tayi ta tashi ta nuna ma Abbah kujera, ita kuma ta tsaya daidai Hajiya Suwaiba still tana murmushin, 


"Ga kujera a zauna" 


Murmushin yayi mata ya zauna yana yi ma Kairat ya jiki, 


"Jiki da sauki Abbah" 


Ta amsa tana kallon Hajiya Suwaiba dake kallon Mummy ita kuma tana kallonta. Basu jata da fira sosai ba, suna gurin aka kawo mata breakfast daga gurin Momy kamar yadda aka saba, tara saura Saif ya bar ɗakin ganin basa da niyar fita ya nufo gida da zimmar ya sanar da Momy ya kuma yi wanka ya canja tufafi, a part ɗinsa yayi parking ya fito daga motar da zimmar ya shiga yayi wanka amman sai ya kasa zimuɗin sanar Momy yake, haka ya nufo part ɗinta zuciyarsa cikeda farinciki a fuskarsa ma zaka iya gane hakan, dan tun daga nisa Momy ta gane yau ɗan nata yana cikin farinciki, 


"Momy ya na ganki da shiri haka? Kar dai ace kinji?" 


Ya faɗa lokacin daya karaso kusa da ita hakoransa a buɗe, Momy ta ɗanyi fuskar mamaki


"Naji me? Da wani labarin ne?" 


"Yes Momy ba Kairat ta tashi ba" 


Ya faɗa yana wani abu kamar yanzu ya soma jin tashin nata a zuciyarsa, jin yayi ba zai iya ɓoye murnar sa ba har sai da ya rumgume Momy, Momy tayi dariya tare da godiya ga Allah


"Alhamdulillahi amman naji daɗin wannan abun, cuta ba mutuwa ba" 


"Wallahi Momy tun jiyada dare fa, kar ki so ganin yadda nake jindaɗi" 


"Ai na gani kan, gashi nan ya kasa ɓoyuwa a fuskarka, aiko yanzu shirin nan da nayi ina son naje duba ta ne idan na fito gurin Safiyyah" 


"Da banyi sauri ba da kin tararda ni a can ashe" 


"Lallai kan, bari naje so nake na dawo da gurin akwai bakin da za'ayi daga Europe" 


"Okey Momy nima wanka kawai zanyi na koma" 


Murmushi Momy tayi, aka buɗe mata motar ta shiga Saif ya maida ya rufe yana mata Allah ya tsare. 


Kamar yadda ta faɗa, a harabar gidan su Gwaggo driver yayi parking wani ya fito daga ɗayar motar da sauri ya buɗe mata cikin girmamawa, sauran suka shiga fito da kayanyakin da dace musu a nan zasu kawo, kayan kwalama ne waɗanda tasan Safiyyah tana so, kamar ko yaushe yau ma da sallama ta shiga parlour fuskarta ɗaukeda murmushi duk da Faɗuwar gaba ne a zuciya wanda ita kanta bata sam dalilin sa ba, 

Sallamarta da kuma sautin takun tafiyarta kana da kanshim turaren ta shine ya tabbatar mata Safiyyah Momy ce ta shigo, 


"Momy..." 


Ta kira sunan nata dan ta tabbatar, kasancewar ita kaɗai ce ke parlour, sai da Momy bata amsa ba har sai da ta zauna kusa da ita, 


"Na'am Y'ata" 


Hannu ta kai tana shafa jikin Momy har ta kai ga fuskarta, 


"Momy kece?" 


Shiru Momy tayi tana kallonta jikinta a sanyaye, dan ta kasa gasgata abunda idanunta suke gane mata, 


"Momy ke ce amsa min magana" 


Ta faɗa muryar tana gaf da kuka, Momy ta rika hannunta


"Ba ki gan ni bane safiya" 


"Bana iya ganin ki Momy idanuwana a yanzu rufe suke bana iya bambance baki da fari ko kuma haske da duhu, na kan kane kowa neta hanyar murya ko kuma kanshim turare ne kawai amman ba da ido ba" 


Hawaye na mata zuba take magana, Momy bata san lokacin da hawayen idanunta suka fara fita ba, ta sauko daga saman kujerar bakinta na rawa ta ce


"Safiyyah baki gani kike nufi? Yaushe makanta ta same ki?" 


"Momy bana gani, a yanzu haka ban gani komai sai duhu" 


"Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un, yaushe wannan abun ya same ki?" 


"An kwana biyu yanzu, Momy rayuwa ta kenan haka Allah ya kaddara min nawa al'amarin" 


Duk kan su cikin kuka suke maganar, musamman Safiyyah, 


"Momy ni da kaina na jefa kai cikin ramen daba zan iya fita ba, ni ka kona kaina da raina ni na salwantar da rayuwarta dan kawai biyan bukatar duniya kuma gashi ban samun biyan bukata ba, 

Momy abunda nayi neya dawo min, nayi nadamar abun da nayi, sanadin hakan nayi hauka yanzu kuma makanta na rasa masoya na guda biyu akan biyan bukatar da har gobe ba zata biya ba, 

Momy da ace na karɓi shawarar ki tun farko da ban faɗa wannan halin ba" 


Lumshe ido Momy tayi hawaye na mata zuba, 


"Kaddara ta riga fata Safiyyah haka Allah ya kaddaro miki rayuwar ki, haka aka so ya kasance a gareki" 


Gwaggo ce take maganar tana tsaye kofar kicin tana hawaye, Momy ta ɗago ta kalleta sannan ta share hawayen idonta, 


"Miyasa ba a faɗa min tun lokacin da abun ya same ta?" 


"Saboda babu abunda zaki iya yi mata, da kin damu da ita har haka ai da bata shiga halin da take ciki ba yanzu" 


Cikin kuka Safiyyah ta ce 


"Gwaggo, Momy bata laifin a nan nice da kai na siyar da kai na inda kuɗin fansar kaina ba zai taɓa samu ba, ba zata iya goge abunda yake rubuce tun kamin a haife ni ba, bata iya tayi min abunda Allah baiyi min ba, 

Hakika ko wane mumini yaba zama mumini har sai da jarrabawa, ni kuma an jarrabe ni sai dai ban ci tawa jarrabawar ba, 

Ina ma gaba na zai koma baya baya kuma ta dawo gaba da na gyara komai na rayuwata" 


"Miyasa kika aikata Safiyyah?" 


"Sheɗan ne Momy, ya rika doka min gangan ina rawa, ta kuma rufe min ido na rik'a hangen kamar nasara ce, ashe bakin ciki da dana sani ne suke kwankwaso min kofa, ni kuma na amsa musu ba tare da sani ba" 


Kuka sosai Momy tayi ita da Safiyyah babu mai iya ba wani hak'uri, jinjina al'amari take tana tausayin yadda mai ido farat ɗaya zai zama makaho, hannayen Momy ta kama ta rike gam


"Idan har kaddara ta tsaya a nan toh na gode Allah saboda nice na ɗebo ruwan dafa kai na da kai na, a yanzu na zama wata irin kalar mace hakika na cuci kai na da kuma cutar da wasu, bai haifar min da komai ba sai nadama da hasara, ki yafe min Momy" 


"Baki yi min komai ba Safiyyah koma kin yi min na yafe miki Allah ya warkar miki da wannan lalurar, zanyi duk yadda zanyi wajen ganin kin samu lafiya insha Allah" 


Cikin kuka Momy tayi maganar, sai da ta samu kujan nata ya ɗan tsagaita sannan ta share hawayen ta tashi jiki ba karfi ta fice. 

Bata je asibitin ba kamar yadda tayi niya, snanin bakin ciki da ɓacin rai har ta iso gida kuka take, daker ta iya labarta ma Lubna halin da Safiyyah take ciki, itakan bata yi mamaki ba, dan tun lokacin da abun ya same ta ta samu labari, ita tama yi tsammanin sama da haka ne zai faru da ita tunda ita ta jawa kanta, 


"Momy akan me zaki rika damuwa da halin da takr ciki ita fa ta jawa kanta, sannan ke ba wannan tarbiyar kika mata ba, ba ke kika nuna mata wannan hanyar ba, ita ce ta sauya rayuwar ta ɗauki wanda take ganin kamar itace mafita" 


"Akwai tausayi Lubna matukar zuciyar musulunci ce jikin ki kika ga Safiyyah sai kin tausaya mata, budurwa da makanta, yarinyar da babu abunda ta nema ta rasa, sanadin so ta kai kanta ta baro kuma ba tare da bukatar ta ta biya ba" 


Ajiyar zuciya Lubna ta sauke, ta ɗanyi kamar mai nazari, Momy ta share hawayem idonta ta nisa tana faɗin 


"Allah ka tsare mu daga muguwar kaddara, da mugun ji da mugun gani da tsaka mai wuyar sani da aikin inda na sani"


Kanta ta kwantar jikin Momy ta amsa ta


"Amin" 


*** *** ***


Kwananta biyu suka sallameta bayan sun tabbatar babu abunda yake damun ta, daker Mummy ta yarda aka maida da gidan mijin dan son tayi ta koma gida har sai yadda hali yayi tukuna, sai gashi Saif yakin yarda a dole ita ta hak'ura, 

Tunda suka dawo ba wani aiki take yi sosai ba, ga kula da take samu ta ko ina, duk bayan kwana biyu sai tazo duba ta, a ɓangaren Abbah ma haka yake dan a koda yaushe cikin waya suke, 

Bata da matsala ko ɗaya a yanzu, babu kuma abunda take zumuɗi kamar auren Abbah da Mummy, duk da a ɓoye za ayi shi,

amman hakan bai hana Kairat yin wasu abubuwan ba, haka ta rika kai kawo har aka ɗaura auren, aiko ranar farinciki gurin Kairat ba'a magana, gurin Hajiya Suwaiba kan bakinciki ne ya cika ta a nan ne Kairat ta kara tabbatar da Lallai kishi kumallon mata ne tana mamaki yadda Hajiya da ta girmi Mummy amman take kishinta,

haka tayi ta tausar ta da kalama da kuma nuna mata Mummy ba mace bace mai matsala, Abbah yaso Mummy ta tare a ɗayan gidansa ko kuma gidan da Hajiya Suwaiba take ciki amman taki ita dai tafi son gidan da take, tunda aka ɗaura aure sau ɗaya Saif ya yarda Kairat taje gidan Mummy, wai a yanzu shi ba zai yarda tana masa yawo da ciki ba ga kuma lil Minal take fama da quiya tunda aka yayeta a yanzu bata yarda da kowa daga Mah sai Pah, 


Wasa wasa lamarin Safiyyah sai karuwa yake tun ana ganin kamar za a warke haran fara fidda rai, dan babu asibitin da kai ta ba ta ido tun daga nan Nijeriya har waje amman abun sai karuwa yake dan a yanzu har kaikayi suke mata, 

Tana tafe yar jarorar da Momy ta samo mata tana janta har suka kawo gurin da akace bakon dake sallama da ita yana tsaye, 


"Gashi nan" 


Yar jarorar ta faɗa sannan ta sake ta ta juya ta basu guri, shirun da taji yayi yawa ne yasa ta mika hannu zata taɓa mutumen


"Ba mutun a gurin ne?" 


"Hmmm gani ba ganki amman baki iya gani ba, duniya kenan budurwa wawa, ai ni naso kin fi haka shiga matsala, Kyakkyawan dake amman ba ido, 

kin cancanci shiga ko wace irin matsala ta rayuwa, zaki iya tuno lokacin da kika ɓata tsakani na da Minal kika kira ni wawa saboda na biye miki mun aikata abunda kika yaudare ni a kai kuma kika yaudari kan ki, shin wace irin riba kika ci a yanzu?" 


Tunda ya soma maganar ta fahimci wanene, wani kalar bakinciki ne ya mamaye mata zuciya lokaci ɗaya hawaye suka rika bin fuskarta wasu na korar wasu, 


"Deen... -" 


"Yes anything for me again?" 


Bata ce komai ba har na tsawon wani lokacin, zuwa can ya kalleta up and down yace 


"Nazo ne kawai na ganki kuma na fi kowa farinciki shiga halin da kike ciki ina miki fatan alheri" 


Bai jira abunda zata ce ba ya buɗe motarsa ya shiga, ita ma ɗin bata ce komai ba har yaja motarsa ya bar gurin, sannan tasa hannu ta share hawayen idonta ta juyo da yar sandarta ta dafe dafehar ta shiga parlour, yar jarora na ganin ta, ta tashi ta rika ta, ta zaunar, 

Ajiyar zuciya ta sauke ta tsura ma carpet ɗin ido kamar wance ke ganin carpet ɗin, wasu siraran hawaye suka zubo mata, ta fi karfi minti talatin a haka sai hawayen take, yarinyar na ganin hakan ta tashi ta faɗa ma Gwaggo, sai gata ta sauko cikin sauri ta zauna kusa da ita


"Me kuma ya faru?" 


Sai da share hawayen sannan tace


"Mako mata nake tunani Gwaggo, na cuci mutane da suka yarda dani na zama mai fuska biyu har wanda bai san da zama na ba na cutar da shi" 


"Har yaushe zaki daina wannan tunanin Safiyyah yaushe zaki bar zuciyar ki ta huta?" 


"Sai ranar da na koma ga Mahalicci na, makoma ta nake tunani Gwaggo, idan amanar wasu ta tashi kama ni ya zata zo min, wata rana zata zo Gwaggo ke kanki zaki gaji dani ki gujeni, 

ba zan auru ba Gwaggo dan babu wanda zai auri makauniya, duka kawayena sun bar ni saboda suna ganin yanzu bana iya komai, hakika hausawa sunyi gaskiya da sukace duniya ta ishi kowa ri da wando wanda bai zo ba ta shirya masa balle mu da muke cikin ta" 


Gwaggo ta share hawayen idonta tana faɗin 


"Babu wannan ranar Safiyyah, bazan taɓa gudun ki ba Allah dai ya baki lafiya" 


"Amin amman wannan idon ka ba zan taɓa warke ba" 


"Kada ki yanke kauna daga Rahama Allah" 


"Kai ni ɗaki na zan kwanta" 


Gwaggo da kanta ta rika ta suka nufi ɗaki ko wane zuciyarsa babu daɗi. 


**** **** ****

As usual da ledoji ya shigo parlor, ganin bata parlour kuma bai ji motsinta kicin ba ya tabbatar masa da tana ɗaki, a parlour ya aje ledojin ya nufi ɗakinta, ya tura kofar ɗakin yana faɗin 


"I'm back" 


A wahale ta ɗago ta kalleshi tace


"Sannu da zuwa" 


"Yauwa Baby na, ina ɗayar Babyn?" 


"Ta raka Lubna da kawayenta rabon anko" 


"Kin san ban cika son yawan fitar nan da take ba ko, bana son ta saba da yawon nan" 


Ita dai bata ce komai ba nata ya ishata, sai a lokacin ya lura da halin da take ciki, 


"Meke damun ki?" 


"Marata ke ciwo" 


Ta faɗa tana dantsar baki, karasowa yayi ya rik'a ta daker tayi zaune, a nan yaga jini, zaro ido yayi


"Subhanallahi" 


Hannayensa yasa ya ɗauke ya nufi bedroom da ita, ya cire mata kayan jikinta ya gyara mata jikin sannan ya ɗauko doguwar riga yasa mata da hijab, ya ɗauke ta ta nufi mota da ita. 




60


Safa da marwa ya rik'a yi a bakin kofar, yana haka Mummy ta iso


"Tana ciki?" 


Shine abunda ta fara tambaya daga isowa, a natse ya gaishe ta bayan ta amsa yace 


"Eh tana ciki" 


"Haihuwar ne?" 


"Ina jin shine ban dai tabbatar ba" 


Kujera ta samu ta zauna, hankalin ta ba a kwance ba, sai Addu'a take, Saif ma ita yake a inda yakr tsaye, 

Bayan kamar awa biyu da wani abu wata nurse ta fito daga ɗakin da sauri, 


"Kuje ku kawo kayan jariri matar ka ta kusa sauka" 


Tana faɗar hakan ta nufi wata hanyar da sauri, shi kan tsaye yayi kamar wanda bai ji abunda tace ba, Mummy ta kalleshi 


"Kun sayi kayan jariran?" 


Ya ɗaga mata kai


"Eh suna can gida" 


"Okey ba ni keys ɗin zan ɗauko" 


Mika mata yayi dan shi kan baya jin zai iya barin gurin har sai yaji ance matarsa ta haihu. Mummy na karɓar keys ɗin ta ɗauki jakarta ta fice da sauri, ba tayi minti biyar da fita ba sai ga Momy ta iso tare da Nasir, ganin Momy ne yasa shi zama a kujerar dake gurin yana karfafa ma kansa guiwa, a gurin suma suka zauna ko wanne zuciyarsa cike da zullumi, suna haka har Mummy ta dawo, kusan set set biyar tazo dasu na kayan jarirai da duk wani abun da tasan za'a bukata, isowarta yayi dai dai ta fitowar nurse ɗin tace a bata kayan jarirai, Mummy na cikin gaisawa da Momy ta juyo, ta mika mata kayan, gurin karɓa ne ta kalli Saif tana murmushi tace


"Matarka ta sauka ta haifa maka kyakkyawan kuma lafiyayyen jariri" 


"Alhamdulillah" 


Shine abunda ya furta ta rungume Nasir yana dariya, Mummy da Momy ma ko wanne fuskarsa ɗauki take da farinciki, suna yi ma Allah godiya, 

Bayan sun gama gyara jaririn suka fito dashi daga ɗakin, Momy da Nasir suka rika rigangan gurin karɓa, 


"Masha Allah" 


Nasir ya faɗa yana rumgumar jaririn a hannunsa, Momy ce ta biyu gurin karɓa bayan Nasir, sannan Mummy, Saif ne na karshe, ya rungume ɗansa kamar wanda za'a kwace ma wani irin daɗi yake ji a ransa kamar yanzu ne aka fara masa haihuwa, 

Kula ta musamman Kairat ta rika samu daga gurin Momy da Mummy, da kuma Hajiya Suwaiba, kwanan ta biyu a asibitin suka salameta bayan sun tabbatar da lafiyar ta da kuma ta jaririnta, 


Gidan Mummy aka dawo da ita, duk da Hajiya Suwaiba taso a barta ta koma gidan su amman Mummy ta ki yarda, babu irin kukan da lil Minal bata yi ba ganin Momie ta ta wani ɗan, hakan yasa kullum Saif yake zuwa ya ɗauke ta sai dare zai dawo da ita wani lokacin kuma a can take kwana tare da shi. 

Bayan kwana uku da da dawowar ta aka kawo kayan barka, da kayan kauri, babu abunda ba a saka ba tun daga kayan jarirai har na mai jegon, tun ana kirga kayan har aka gaji, dan kowa akwatunansa daban na mai jego daban na Jariri daban abun gwanin ban sha'awa, sai labarin ake. Ranar suna yaro ya ci sunan kakansa, MUHAMMAD BASHIR aka masa lakani da Aniq. An ci an sha, babu abunda ba a raba ba, 

Bayan sunan da sati biyar aka bikin Nasir da Lubna, daker Saif ya yarda Kairat taje bikin duk da tayi arba'in sai dai Mummy bata barta ta koma ba tasa ana mata shiri n musamman. anyi biki abunda ake kira biki, an zubar da kuɗi kamar ba gobe, Saif ya nuna ba jinta a gurin biki ta ko ina, yadda yake ɓarin kuɗi sai ka ɗauka bai san zafin neman su ba, ranar Asabar aka ɗaura, bayan anyi dina amarya ta tare dare da aka ɗaura auren. 


Sai da Mummy ta gama shirya Kairat sannan ta barta ta koma gidan mijinta, bayan an samo mai taya ta reno. Fasalin rayuwar Saif ta canja daga marar mata zuwa mai mata har da yaya biyu, an yanzu kan shi kansa yasan ya girma, ita kan ta Kairat ta canja a yanzu dan kallo ɗaya zaka mata ka gane matar aure ce, saboda yadda ta buɗe ta zama babbar mace, daman hausawa sunce haihuwa na buɗe mace. Rayuwar suke yi ta jindaɗi da kwanciyar hankali, rayuwar da ita ko shi ba su taɓa mafarkin shiga ba. 

A ɓangaren Mummy ma haka abun yake bata da wata matsala ko damuwa a yanzu, hankalin ta a kwance, Abbah yana kula da ita sosai musamman cikin nan da take ɗauke da shi ita kanta tana farinciki, sai dai wani gefen tana jin kunya wai zata yi haihuwar tsufa, hakan yasa ba kowa ne yasan tana da cikin ba Kairat ma ita kanta bata san tana da cikin ba, Allah ya taimake ta mace ce mai babban jiki hakan yasa ba a gane cikin dake jikinta, idan ba wanda ke kusa da ita kullum ba. 


Komai ka shuka shi zaka gurba, in ji hausawa, kuma ramen mugunta gina shi ɗan kaɗan ba kato ba, dan wata rana kai ne zaka faɗa, rayuwa ta zamo mata ta tsanani da wahala, saboda rashin ido komai sai dai ayi mata, tun tana mafarkin buɗewar idonta har ta daina tun tana dafe dafe har ta saba, abun da yafi damunta shine na rashin auren da bata yi ba, ta tsaya bata lokacin ta akan wanda ya zama silar makantarta kuma bukatar ta bata biya ba, ganin zaman baya mata a gidan Gwaggo yasa ta tattara ta dawo gurin Momy, dan tasan duk kular da Gwaggo zata bata ba zata kai ta Momy ba, daman tayi tayi ta dawo ita ce taki ganin yanzu babu sarki sai Allah yasa ta dawo gidan, hankalinta yakan tashi duk lokacin da Saif yazo gidan ko ya kawo iyalinsa, babu irin kuɗin da Momy bata kasa ba wajen ganin ta samo lafiyarta amman ya ci tura. 


Da gudu ta sauko downstairs kamar wata karamar yarinya, rike da waya a hannunta, ta zauna kusa da shi, 


"Yanzu Humaira ta kira ni... -" 


(Humaira matar da Deen ya aura kenan) 


Kamin ta karasa ya walkato ta ta dawo saman jikinsa ta kama karamin bakinta


"Tace me?" 


"Ta haihu ta samu Ya mace" 


"Masha Allah Allah ya raya, yaushe?" 


"Wai yau kwana uku ranar Litinin za'ayi suna" 


"Toh Allah ya raya sai ki samu abunda zaki bata" 


"Ai dole zanje gobe nayi mata barka" 


"Yeah, cox jibi zanje wani business trip kuma kila dake zanje" 


"What?" 


Ta tashi zaune, 


"Wasa dai kake ko?" 


"Aa nima ɗazu Daddy yake sanar min, kuma yace yana da muhimmanci dole naje indai har an tabbatar da abun" 


"Gaskiya ni ba zani ba" 


Ta faɗa tana kukan shagwaɓa, 


"Saboda me?" 


"Yaushe muka dawo, ni gaskiya ba zan kara fita waje ba sai na yaye Aniq" 


Dariya yayi dariyar da sai da ta fitar da Beauty point ɗinsa


"Amman yarinyar nan kin raina mutane, oh ke abarki kije kina yawo a gari kina matsu ko baki son shayarwa kar ace kin haihu" 


"Eh mana ai yana takura min kuma ni gaskiya, ina son naga bikin Anty Fareeda yau fa sauran sati biyu" 


"Whatever, ni dai ba zan je ni kaɗai ba tun da kinsan ba wata matar ni dani ba" 


Kuka tasa masa ya rungume ta yana murmushi, kamin ya ɗaga ta daga jikinta yana mata kiss


"Bari ma naje gurin Daddy na kara tabbatar wa" 


"Allah yasa an fasa" 


"Ba Amin ba" 


Ya faɗa yana smirking. 


Da Sallama ya shigo parlour, Momy da Nasir suka amsa masa, 


"Ango ango ango kasha mai" 


Ya faɗa yana zaunawa saman kujera 


"Kai wane irin ango watan mu nawa da yin aure bana son shashancin fa" 


Dariya yayi


"Au gaban uwata zaka kira ni shasha?" 


"Uwata dai kai kana da uwa ne" 


"Aa sama na faɗo" 


Dariya sukayi har Momy, 


"Auto naga uwata ce sai ka nemo wata uwar kuma" 


"Sarakuwar ka dai" 


"Aa ni ba wani sarakuta uwata ce kawai kaga tafiyata" 


Bai bari Saif ya kara cewa wani abun ba yayi ma Momy sallama ya wuce, suka bishi da kallo suna murmushi. 


"Ya gidan ya kowa da kowa?" 


"Lafiya kalau, tana gaishe ki" 


"Ina amsawa Abbah ka yayi maka maganar tafiyar ko?" 


"Eh daga gurin shi na fito yanzu yace min Saturday zan wuce ya za a shirya min komai" 


Kamin Momy tayi magana Lil Minal ta fito da gudu ta rumgume masa wuya, 


"Oyoyo Bah Babyn Mah" 


Hararar ta yayi yana satar kallon Momy, Momy kan ɗauke kai tayi ta mai da hankalinta gurin Tv, 


"Bah ina Momie Aniq" 


"Ke ba Momie ki ce ba" 


"A a tunda ta haifi Aniq ni ba Momie na bace" 


Momy ta juyo ta kalleta tana dariya


"Ai na manta tace na zama Momy ta wai tunda taga bana da yara, wai Aniq ta bar masa wacan yayi ta kaya" 


"Har da Ni kin bar masa?" 


Saif ya tambaya, she's nodded her head 


"A a wallahi ai kai ba kai ka haife shi ba" 


Duk dariya sukayi, banda ita data yatsine fuska


"Ina kika shafo wannan?" 


Yana taɓa ink ɗin take Hannunta


"Ɗakin Anty Safiyyah" 


"Toh je kice ina gaishe ta" 


"Toh" 


Da gudu ta sauka ta nufi ɗakin, Momy ta kalleshi 


"Amman kan ba zaka faɗa mata tafiya zaka yi ba, dan zatayi kuka kuma kaga ba hutu suka. Samu ba balle kaje da ita" 


"Aa ba zata sani ba ma, ai kinga tafi son zama nan" 


"Eh tace fa ku ba iyayenta bane" 


Dariya yayi yana amsa kiran da aka masa a waya. 


**** **** ****

Kamar yadda Daddy yace masa Ranar Saturday ya bar kasar zuwa Paris, duk yadda Kairat taso ya barta bai yarda ba a dole ta hakure suka tafi tare, tafiyarsu da wata daya Mummy ta haifi kyakkyawar yarta, aka rada mata suna AMINA sai dai Meena suka kiranta, babu yadda Kairat bata yi ba dan tazo bikin amman Saif ya tsaya kai da fata yaki yarda wai shi ba zata barshi can shi kaɗai ba, sa'arta ɗaya ya kusa kammala abunda yazo yi, bayan suna da sati biyu suka dawo, a gidan Mummy Kairat ta sauka, ta kama jaririyar ta rungume sai zumudi take kamar zata haɗe ta, kamar su ɗaya da Kairat sai dai fari na Mummy ne, Mummy kunya take ji sosai wai tayi haihuwar tsufa ita tana haihuwa Kairat. Na haihuwa, a boye take bata nono ko kuma ta saka hijab,sai dai a can kasan zuciyarta farinciki fal aciki dan gani take kamar Minal ce ta yi dawo. 


BAYAN WADANSU SHEKARU


Tsiren gudu suke, kowa so yake ya wuce ɗan'uwansa, daga karshe dai Aniq yayi nasara, aiko da gudu yayi gurin Safiyyah yana faɗin 


"Anty. Ni nayi na ɗaya" 


"Sai wa kuma yayi na biyu?" 


Safiyyah ta tambaya tana tataba kansa, 


"Ni nayi ta biyu" 


Lil Minal ta faɗa tana smirking, 


Dariya tayi, 


"Good ina Amir ta nawa yayi?" 


"Amir yayi na karshe" 


Sweets ɗin dake hannunta ta ɗauko ta tana mika musu, duk suka rungume ta suna dariya da yi mata godiya, kansu ta rika shafawa tana hawaye. 


Kairat dake tsaye a windo tayi murmushi tana rungume hannayenta, bata sarar ba taji an jama kumatu, tana juyowa ya ɗaga mata gira ya kashe mata ido, mur tasha 


"Zaka fara ko bafa gida muke ba" 


"Gida muke kan Da nan da can ai duk ɗaya ne" 


Ya faɗa yana kara motsowa kusa da ita, 


"Dan Allah ka daina kar fa Momy ta fito ta gan mu" 


"Toh idan ta gani fa Haramun nayi? Bari ma ki gani" 

Dukawa yayi ya ɗauke ta Cak, ita kuma ta shiga cuku cukun ganin ta bar jikinsa har suka faɗa saman kujera still bai sake ta ba, 

Yana kokarin kai hannu ya cire mata ɗankwali yaji alamar motsin fitowar Momy, ba shiri ya sake ta ta nufi kofar fita da sauri, ita kuma ta tashi zaune tana gyara jikinta da murmushi a fuskarta. 


ALHAMDULILLAH!!! 


Godiya ta tabbata ga Allah madaukaki sarki mai kowa mai komai, wanda ya bani ikon kammala wannan littafin, oh Allah i hope for your mercy don't leave me for myself correct all my affairs for me, 


Komai yayi farko zaiyi karshe, na gode sosai da irin bibiyar da kuke ma wannan littafin, ina son so na tsakani da Allah, 


Mom shuraim 

Naffsy

Sadiya sale

Yar fulani 

Da feenah 

Suby jukus

Zainab ta House of novel 2

Da duk yan Khadeeja Candy novels da taskar khadeeja Candy,da duk grp ɗin da nake ciki duka ina godiya, 


My wattpad readers 

Ina godiya sosai da irin kaunar ku, ba zan iya lissafo sunan ku ba, ina son ku fisabilillahi

Kairat

Gaudiya

Onmyyasmin

Da ghosts readers duka thank you 


Facebook readers 

Ina godiya sosai da sosai Allah bar zumunci,


My writers

Miemiebee 

Phartiemaerk

Safiyyah Mrs j moon

Kamala Minna

Thank you all


Nagarta Writers Association 

Nagartacciyar kungiya mai Nagartaccen suna daga Nagartattun shugabanin da Nagartaccen aiki Kungiyata abun alfarina, Allah kara haɗa kan mu Amin


Sadaukarwar taki ce

Anty Maijidda musa maman biyu ina sonki fisabilillah

.

Tukuici ne

Ga duk wanda ya jure karanta wannan littafin daga farko har karshe i love you


daga karshe ni Khadija Abubakar Alkali nace muku saduwar alheri, ina rokon gafarar duk wanda na taɓa ɓatawa rai cikin kuskure ko ganganci ko rashin sani, ku yafe min nice taku Khadeeja Candy 2 +2 


Stay bless all the best one heart one love 😍 


Khadijacandy44@gmail.com

In case 


Post a Comment for "Babban Goro Complete Hausa Novel"