Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Waminal Hoob 43

43….

Runtse idonsa yayi sosai yana kokarin daidaita numfashinsa
Komai xai faru yau baxai kasance da laylah ba sai yayi mugun koya mata hankali lokaci daya ya turata da sauri ya mike tsaye ya wani fisgi hannunta a xindir din,ya jefata waje wani



Kallo yayi mata da idonsa da suka gama
Canja kala ya bude mata su sosai yana
Fa?in.”bana bukata ke wace irin manyyace ki
Jika kayanki kiyi tasha
Kin manta lokacin da nake rokonki ki bani
Hakkina mema kike fada a lokacin??”ae lokacin haduwar mu
Baiyi ba kin manta??
Ko xan kwanta dake
Sai na roka kuma sau daya a wata,idan bana
Tsare kaina da yanxu
Na fada xina ,i hate you so much laylah na tsani dukkan Halinki
ya fada yana buga kofar,da wani irin shock take kallon
Kofar Lokaci daya hawaye suka wanke
Mata fuska jikinta babu inda baya rawa,
Ya za’ayi da maganin
Da ta gama dirkawa kanta ta kashe kudi
Sosai a tafiar nan,
Ga wani irin ciwon
Mara da takeji lokaci
Daya,buga kofar ta shigayi da karfi tana
Jin yarda ruwa ke xubar mata a kasa
Sabida niimar da ta saukar mata,bata ta?a
Sanin haka akeji ba sai yanxu,tana jin yarda yatsun kafarta ke wani irin rawa,ta dafe mararta gamida xubewa a wajen tana kwalawa Khaleel wani
Irin kira ,kenan Khaleel shima haka yakeji
Idan yana bukatarta,
Lokaci daya taji ta tsani kanta,tafi minti goma tana buga kofar,
Jikinta yayi wani irin saki dakyar ta lallaba
Ta koma dakinta wani
Irin ciwon mara ta kwanta dashi tana ta juye a gado ,kafin safe wani irin xaxxabi
Ya rufeta da ciwon mai tsanani,ganin tayi da gaske ciwo naso yafi
Karfinta ta lalubi wayarta dakyar ta dialling lambarsa,
Kusan Kira ukku tayi masa bai daga ba,
Wani irin kuka ta fashe dashi Ammah ta shiga kira ta dde tana ringing kafin ta daga,laylah ta fashe mata da kuka lokaci daya tana fada mata bata da lafiya,sosai
Hankalin Ammah ya tashi tana fa?in.”yanxu xata Turo mata Ramlah suje Asibiti ,da haka ta datse kiran har daki ta samu Aunty Ramlah da zancen,Aunty Ramlah ta kalli Ammah tana fa?in.”ina Khaleel din ya shiga sai lokacin Ammah ta tuna Khaleel,Bara na kirasa ya daukota kuje Asibiti,Ringing daya ya daga da respect yake
Fadawa Ammah ina kwana.”Ammah ta amsa tana tambayarsa meke damun Laylah baya gidane??”gabansa ya fadi lokaci daya ya daure ya fadawa Ammah baya gida,shi bai ma san bata da lafiya ba.”sakin baki Ammah tayi tana sauraren Khaleel kafin tace .”Kai wane irin shashane matarka na ciwo baka sani ba,”yarda Ammah ta rika yimasa fada a waya tamkar xata dakesa,rai a dagule yake fadin”kiyi hakuri Ammah bari naje na dubata,bawai kaje ka dubata ba yanxu ka daukota kaxo ga Ramlah ka dauketa kuje Asibiti,wai meyasa baku baiwa matanku muhimmanci ne.”Ransa a bace ya kashe wayar ,Aunty Ramlah ta tabe Baki tana fa?in.”kema Ammah da neman magana kike kin manta matar tasa itama shaidaniya ce,Ammah tayi murmushi take fa?in.”,komai rashin jin maganarta Allah ne yayi umurni ya sauke duk wani hakki nata da yake kan wuyansa,
“Me na maki xakije ki hadani da uwata!”Ya fada cikin daga murya ,ta girgixa kai hawaye na xubar mata take fa?in.”kayi hakuri dan Allah bana da lafia shiyasa na kira ka,kuma baka dagaba shiyasa na kira,ya wani hade rai yana fa?in.”meke damunki??cikin rawar murya take fa?in'”xaxxabi da ciwon kai,ki shirya muje Asibiti ya fada fuska babu walwala ta kallesa hawaye na cika idonta,tana mamakin canjawar Khaleel tana karawa,duk sabida macce yake yimata irin wannan wulakanci,kabarsa kawai.”ta fada tana janye fuskarta cikin tasa,ya wani daure fuska yana fa?in.”ba dole sai abunda kike
So shi za’ayi ba wannan umurni ne kina batamin lokaci idan kin shirya ki sameni a mota ,da haka Yabar mata dakin kallonsa tayi hawaye na cika idonta lokaci daya,kurawa fuskarta ido yayi ko kadan baya jin tausayinta,idan yace har yanxu babu soyayyar Laylah yaqoob
Acikin xuciyarsa yayi karya ,ya sota iya so
Ya bautawa soyayyarta tamkar xai mutu,sabida soyayyar ta ya kasa baiwa mahaifiyarsa farin cikin da takeso tuntuni na bata jikoki,shi kuma lokacin soyayyarta ya rufe masa ido baiji bai ganin kowa sai laylah yaqoob,baiyi tunanin ko a mafarki xai iya soyayyah da wata a duniya ba baya ga laylah yaqoob har akai
Ga maganar Aure,yasan ta wannan hanyar kawai zai iya hukuntata ko xata tuba ta dawo hankalinta.magani kawai aka rubuta mata suka dawo ,cikin rawar murya take fa?in.”ka saukeni gidan Ammah,baiyi musu ba ya juya kan motar,da sauri Nooriyah ta tarbota tana yimata ya jiki,
Hakama Aunty Ramlah,Nooriyah ta kalleta tana fa?in.”A hado maki break fast Aunty,laylah na girgixa Kai take Fa?in.”nagode noory da fada Ammah ke fa?in.”toh meye acikin da baxa kiyi break fast ba,jeki hado mata da haka noory ta juya ta nufi Kitchen Yana tsaye a kitchen a tsaye bata san meya shigo dauka ba,jin tayi ta kasa karasawa cikin kitchen din,ganinta yasa ya wani hade rai,ya dauki cup da spoon ya wanke ya nufi kofar fita,hanya ta basa tana wani dauke kai,shima ko kallonta baiyi ba Yabar cikin Kitchen din,lumshe ido tayi tana sauke numfashi,
Yau laylah na tare da noory ,nooryn ce keta hidima daita kasancewar yau babu event,sai gobe juma’a waleema ce da daurin Aure yau kowa yana gida,ana gama sallar magrib laylah ta kalli noory cikin sanyi murya take fa?in….”Ammah fah?”
Tana sama wajenta xaki??”laylah ta daga kai ,kije tana sama bazata sauko kasa ba sai bayan sallar ishaai,da haka laylah ta mike da Hijab dinta har kasa ta nufi kofa,
Bayan ta fice Aunty Ramlah dake zaune kan Bed tana waya da maigidanta bayan ta gama ta kalli noory tana fa?in.”me wannan matar ke fada maki??”ni Naga ta xama wani iri lokaci daya tayi wani irin sanyi,noory tayi murmushi tana fa?in.”tace zata ga Ammah,Ramlah waxeer ta tabe Baki tana fadin.”maybe duniace ke shirin juya mata baya tunda kika ganta da Hijab haka har kasa,su Inteesar ne da batool waxeer suka shigo dakin,Aunty Ramlah ta daka masu tsawa tana fa?in.”dakin arnaye ne da xaku shigowa mutane babu sallama,
Sanin halinta yasa Batool waxeer ta juya hakama Inteesar kusan tare suka shigo kowane sallama dauke a bakinsa,noory ta amsa tana sakin murmushi kafin ta ?ora da fa?in.”ina kuka fito yammatan Ammah,Batool tayi murmushi tana fa?in.”Yaya Hakeem ya kaimu yawo nida intee ita dai Aunty Ramlah batace komai ba,Inteesar ta dire Leda agaban noory tana fa?in.”ga naki tsarabar,da murmushi take fada masu ta gode,yanxu babu wacce tayi sallah cikin ku kuna can kuna xaga gari,Batool ta turo baki tana fa?in.”yanxu fa xamuyi shima a mota ya barmu ya shiga Masallaci,kiran Ammah ne ya shigo a wayar Aunty tana dagawa,ta fadawa Ammah gata nan zuwa da haka tabar masu dakin,Batool ta dawo gaban noory da sauri tana fa?in.”dama so nake Aunty Ramlah ta fita mu baki labari,dama kan maganar Yah Hakeem ne da intee,xare ido Inteesar tayi ta shige toilet da sauri,,noory tace kema kije kiyi sallah idan kin gama muyi magana……
Hawaye suka fara Rolling Akan face din laylah cikin shesshekar kuka take fa?in.”gaba daya ya canja Ammah,baya bari mu kwana daki daya dashi kullum yana raba dare yana hira da wata a waya,bayamin magana mai dadi abu kadan sai hantara da cin mutunci ko hakkina na Aure ina binsa yana yimin wulakanci,ta karasa maganar tana fashewa da wani irin kuka mai sosa rai,gamida saka kanta cikin cinyoyinta,kukanta ya karya xuciyar Ammah sosai ,yayin da Aunty Ramlah ko kadan bataji tausayin laylah ba,ta xuba ido kurum taji mai Ammah xata fada,Ammah ta kalli Aunty Ramlah tana fa?in.”ki kirasa yanxu a waya Ramlah komai yake ya aje yazo yanxu,kusan minti Ashirin sai ga Khaleel a dakin Ammah ganin Laylah yasa ya hade rai yaki Karasowa cikin dakin,wani kallo
Ammah ta shiga wurga masa babu musu ya shigo cikin room din gamida xaunawa,fuskarsa babu wani walwala,
“Tarbiyar da na baka kenan cin xalin macce da wulakanta ta…..”Ammah tayi maganar sounding so pissed up,shaye da toka yake fa?in.”meya kawo wannan maganar Ammah,ya karasa maganar da sanyi murya.ba haka za’ayi ba a fara yimasa bayani mana kafin a hau kansa da fada,nan
Aunty Ramlah ta juya kansa tana yimasa bayani ,kallon laylah kurum yake cike da mamaki,Ya kalli Ammah yana fa?in.”kawai kishine ke damunta dan xan kara Aure.”yayi maganar sounding so very serious cikin muryarsa ,da rarrafe laylah ta matso ta kama kafar Ammah ta wani irin rushe da kuka,kiyi hakuri dan Allah da duk irin abubuwan da nayi maki tun farkon Auren mu har kawowa yanxu
Sharrin shaidan ne,
Wlhi ban taba kaucewa hanya ba,ban taba bin wani boka ba dan na mallake Khaleel ,nasan duk hakan ne aranku,soyayyar da yake yimin ce yake son duk abunda nakeso,da wannan soyayyar da yake yimin nake duk abunda naga dama,dan Allah Ammah ki yafemin wallahi na Maki Alkawari xan maki duk Abunda kikeso xan biki sau da kafa,ki fada masa ya yafemin
Wlhi idan yayi min kishiya xuciyata tarwatsewa xatayi ,wlhi na daina shan duk wani magani hana daukar ciki,ina son ciki ina son Naga Dan Khaleel waxeer a jikina,ta fada tana wani irin fashewa da Ammah kuka mai cin rai,gaba daya ta gama karyawa Ammah xuciya,cikin sanyi murya Ammah ke fa?in.”bakiyi min komai ba laylah Allah ya yafe mana gabaki daya,kuma Ni baxan iya hanasa kara Aure ba,kiyi hakuri kiyi hakuri dan Allah.”Ammah ta fada cikin kwantar da murya,ta kalli Khaleel
Tana fa?in.”daga yau komai ya wuce,bana son karaji ka dauki matarka ku tafi Allah ya sauwake sai da safe,ya rigata fita daga room din,Ammah ta kara yimata nasiha tace ta tashi tabi mijinta,
da wani kallo Aunty
Ramlah tabita har ta fice daga room din
Aunty Ramlah na girgixa kafa ta saki wata shewa tana fa?in.”Ai wlhi Khaleel ya burgeni da naji xancen xai kara Aure ji nayi tamkar na tashi nayi rawa ko na goyasa wlhi,,,kishiyar shine dai-dai daita ae naxata tace baxata zauna da kishiya ba,
Ke baki ga yarda jikin
Shegiya yayi la’asar jin
Xancen kishiya Khaleel waxeer bai taba burgeni ba irin yau,ae xan kirasa naji yar wani gidace bana son bikin nan ya dauki
Lokaci saura asirin shegiyar daya ya tonu,
Wai har mu xata yiwa bariki tace bata ta?a zuwa wajen boka ba,
Abubuwan da Khaleel
Ya rika yi ae akwai ma
Wanda hankali xai dauka,da wanda hankali sam baxai dauka ba,saura wannan matsiyaciyar
Ya fada min tunda tabar gidan nan basuyi waya ba,
A fusace ya nufi dakinsa na barci da gudu ta cimmasa har tana hardewa,xai rufo kofar tasa hannu ta rike kofar,hawaye na xubar mata take fa?in.”kai baka yafiya ‘ne wai ??”sakar mata kofar yayi ya nufi toilet da sassarfa ,juyawa tayi ta nufi dakinta tana jin wani irin kuka naxo mata,washe gari aka daura Auren Rumaisa mijinta dan Kaduna ne Ammah a legos yake aeki,bayan an sauko jumu’a akayi kayatacciyar walima a gidan Baffa Waxeer,karfe shidda nayi akayi shirin kai Amarya a gidanta…kowa anata shiga mota dan raka
Amarya noory ta nufi get ,gida takeso ta wuce su Batool sun karbi motar hannunta,
Kuma Ammah ita xata kai amarya dakinta,
Takawa tayi daga Mention din Baffa xuwa na Ammah,babu wani nisa,jin tayi ana yimata horn Bata ko kalli motar Ba taci gaba da tafiya,haka ba’a fasa bintaba ,sai da ya cimmata ya tsayar da mota gamida sauqe glass,
“Ke baxaki je kai amarya ba,ya fada yana kallonta da murmushi akan kyakkyawar fuskarsa,
Ta girgiza kai tana fa?in.”sai zuwa jibi
Xanje mexai hana yanxu,ta girgixa kai
Tana fa?in.”baxani ba yau Yaa Hakeem wai meke damunka ne??
Ya girgixa kai yana fadin.”babu shiga na saukeki gidan Ammah,ta ware masa ido tana fa?in.”ae na kusa lokaci daya ya hade rai yana fadin.”saboda dai kina tsoron kar ya gammu,
Yana gama parking acikin compound din Ammah shima Aliyu ya fito daga gidan,da car key a hannunsa da alamar fita xaiyi, wannan karon babu shaddar daurin Aure jikinsa yayi wanka ya canja kaya zuwa kananun kaya,ta kalli Hakeem tana fa?in.”Nagode Angon inteey ya wani hade rai lokaci daya,yana fadin.”Yaushe muka fara irin wannan wasar dake,saurin rufe bakinta tayi tana basa hakuri,kasa shiga motar yayi zuciyarsa na mugun tafasa yayi tsaye yana
Kallon yarda ta bude baki tana Daria,ko kallo bai isheta ba ta nufi Entrance din shiga gidan,da wani irin kallo ya bita ,yana tuna haduwarsu ta jia,jin yayi Hakeem nayi masa horn yayi masa banxa ya shige motarsa,Dukansu barcin gajia sukayi ranar Assabar basuyi karin kumallo ba sai kusan 11
Suna cikin karin kumallo sai ga Areefa ta dawo jaye da bag nata,kowa idonsa na kanta itakuma idonta na kan Aliyu ranta yayi balain ?aci lafiarsa lau
Kenan yaki daga wayarta,ta karaso tamkar bata so haka ta gaisheda Ammah da Aunty Ramlah ta juya kan Aliyu tana fa?in.”baby dama lafiar ka kalau haka kawai kaki daga wayana.??”ta fada tana so su hada ido,
Ya kalleta ido cikin
Ido yana fa?in.”ina busy shiyasa Areefa
Kuma kin San na tsani
Naci gabanta na faduwa take kallon Aliyu waxeer yana kallon cikin idonta yake gasa mata magana,xatayi magana ya mike Yabar mata wurin
Yana jin wani iri yana jin kunya ace wai dan cikin jikin Areefa nasa ne,duk ya tuna hakan
Ransa na balain ?aci,
Lokaci yayi da xai fara
Bincike cikin Rayuwar
Areefa mansoor,har ya nufi sama komai ya tuna ya dawo,ya karbi
Bag dinta ya kirkiro
Murmushin dole yana fa?in.”muje ki huta,
Dan sanyi taji da wani
Irin shock Ammah da Aunty Ramlah suka bisa da kallo,yafi minti biyar a dakin sai gashi ya fito,lokaci daya Aunty Ramlah ta dawo gabansa cike da bacin rai take fadin meye haka???”yaushe wannan wasar naka zai kare dan Allah,
“Da mamaki yake fa?in.”me nayi Aunty??
Kana nufin xaka cigaba da renon dan shegen da bana ka ba.”ta fada da bacin rai cikin muryarta ,ya dage kafada yake fa?in.”bana da tabbaci
Akan hakan,dan Allah mubi komai a hankali
Daga haka ya nufi stairs Yana Jin xafi a xuciyarsa haka yana
Jin idonsu Aunty Ramlah akan sa dole ya daure ya cigaba da kula Areefa ko xai samu abunda yake nema,ta wannan hanyar kawai ce zai samu abunda yakeso,
Yasan Ammah xatata tajin babu dadi da kuma Sarkin kishi…

Baxan fasa Allah ya isaba ga duk wacce ta karanta hakkina bata biya ni ba,idan kina da zuciya ke ya’r halak ce ki daina karantawa daga yau…..

Littafin Waminal Hoob
Na kudi ne#500
Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma’u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan lambar#09060259200
Shaidar biya ta wannan lambar#08086207764

Team#NOORYALI FOREVER#??
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom Aydah??

Post a Comment for "Waminal Hoob 43"