Waminal Hoob 29
Asmy Mom Aydah??: 29
Sosae Ammah tayi farin ciki da zuwan su,ta kalli Aliyu tana fadin”yanxu nake xancen Nooriyah a raina,na xata ma jikin har yanxu.”Basu dade da xama ba sai gasu Khaleel waxeer shida Laylah,itama kwana biyu bata shigo wajen Ammah ba ulcer ta
sakota gaba.gaisheda Ammah sukayi dukan su,Ammah ta kalli laylah tana fadin”Ya jikin nata hop ta samu sauqi.”ciki-ciki laylah ke fadin taji sauki,
Sai da sukayi ishaai Ammah tace su tsaya suci abincin dare tare daita,ta kalli noory tana fadin”zata iya cin tuwon semo ko a girka mata wani??”girgixawa Ammah kai tayi dama can tuwon semo ba cimarta bace,Ammah ba sai anyi ba inada pizza gida idan naje ita xan ci da yougout ,,Kin tabbata zai kosar dake??”daga kai tayi cike da jin kunyar Ammah,typing Khaleel waxeer ya shigayi a wayarsa ya turawa Aliyu…”mekake jira buddy ka kashe boss Dan Allah ,wai meke damunka idan Ammah ta gano akwai matsala kasheka xata yi babu ruwana.”jin sako ya shigo a wayar Aliyu yayi saurin duba wayar,da sauri ya kalli Khaleel waxeer ya ware masa ido gamida bude hannuwa,kallonsu kawai laylah keyi.Nooryn ce ke serving kowa,da gangan laylah ta kwantar da bottle water a dai-dai wajen da nooryn take,noory ta daga kafa dan isa ga Aliyu waxeer taji ruwa ya jata,da wani irin sauri Aliyu ya tarota ta fado kansa gaba daya.Ammah na dafe kirji take fadin”meye haka meyasa bakya bin A hankali Nooriyah,Aliyu yabi ruwan dake kwance kan marbles da mamaki lokaci daya ya kalli laylah ta sha toka gamida dauke kai,da sauri Ammah ta kama hannun nooryn ta zaunar daita,ta kalli laylah tana fadin.”ta tashi tayi serving Aliyu Nooriyah ta xauna ta huta,bakin ciki tamkar xai kashe laylah waxeer a wajen………Haka suka karasa cin abinci tana kunci,sai kusan goma kowa yayi shirin tafia,suka yiwa Ammah sai da safe,A mota dukkan su shiru suka xauna,sai ga kiran Farhaan Shagari ya shigo a wayarsa ,kin dagawa yayi dan har yanxu bai sauko daga fushin da yayi da Farhaan Shagari ba,wani irin barci takeji yau duk taji bata jin ddin jikinta haka gabanta taji yana yawan faduwa,wanka kurum tayi tabi lafiar gado,shima a bangaren Aliyu wanka yayi ya duba sako a email dinsa,sai kusan 12 ya kwanta.shima bai dade ba yayi barci,harbin bindiga kawai sukeji kusan lokaci daya mami da daddy suka bude ido,cike da tashin hankali mami ke fadin”daddy bakaji karar bindiga ba,da sauri Alh.omar Shagari ya sauka kan bed yaje ya leka ta window,da sauri yaja da baya yana xare ido,mami ta dafe kirji tana fadin yan fashi kou daddy??”da sauri ta nufi kofa tana fashewa da kuka tashin hankali take fadin”Daddy Farhaan da Jamila, daddy ya jawota Yana fadin”.ki natsu Maryam,hawaye na xubar mata cikin tashin hankali take fadin”Jamila daddy.”da sauri daddy ya dauko wayarsa ,ya shiga kiran commissioner da yake abokin sane,
Kira wajen 3 yana yi masa bai daga ba,cikin tashin hankali mami ke fadin”bai dauka ba daddy.”ta fada tana rufe bakinta,
Da sauri mami ta saka Hijab ta bude kofar batareda ta jira mai daddy xai fada ba,shima akwai jallabiya a jikinsa ,yabi bayan mami da sauri dakin Jamila suka shiga bugawa a hankali,dama kuma Jamila bata dde da kwanciya ba.so barcin nata baiyi nauyi ba,ta bude kofa tana kallon mami da daddy gabanta na faduwa take fadin”mami meya faru??”Barayi jeki ki canja kayan jikin ki da sauri Jamila ta koma daki cikin minti biyu ta xura Hijab ajikinta babu inda baya rawa cikin jikinta,daddy ya kalleta yana fadin”maryam ki tsaya tareda Jamila bara naje na duba Farhaan,
Cikin tashin hankali mami ke girgixa kai take fadin”baxan iya ba daddy pls muje tare….Yarda mami yaga ta daga hankalinta ,
Yasa duka suka nufi bangaren Farhaan zuciyarsu na bugawa,
Su bahago na hango tahowar su dashi da sauran yaransa suka fito daga mabuyar da sukayi a bayan flower’s ,suka zagayesu da manyyan bindigogin su a hannu,
Kowane ya rufe rabin fuskarsa da bakin kyalle,cikin karfin hali mami ke fadin”dan Allah kuyi hakuri ko me kuke so zamu baku,Ina yaron gidan nan wajensa muka xo.”cikin rawar murya mami ke fadin”Bayana yayi tafia,lokaci daya bahago ya fisgo Jamila wacce ke bayan daddy,yasata cikin jikinsa yana fadin.”xaki fadi inda yake ko sai na yaga mutunci yarki a gabanta,lokaci daya hawaye suka wanke fuskar mami,cikin rawar murya take fadin.”dan Allah kuyi hakuri kar kuyi mata komai,haka suka saka su gaba har part din Farhaan,tsaye suka samu Farhaan acikin parlor Shima karar bindigar da yaji ya hanasa kwanciya,koda akayi harbin yana parlor ,baiyi zaton harbin ta cikin gidan su bane.”A fusace ya karaso gabansu ganin sun rike Jamila,daga hannu yayi xai kaiwa bahago duka ,bahago ya rike hannun nasa,Fashewa da kuka mami tayi ta xube a gabansu tana rokonsu da Allah kar su taba mata ya’yah,bahago ya mikawa Farhaan Shagari hannu yana fadin ya basu wayar hannunsa,wani kallo ya shigayi masu .mami ta daka masa tsawa tana fadin”kaba su mana,
Mika masu wayar yayi dama tana hannunsa,
Laptop Dinka??har dakin barcinsa suka tasa shi gaba ya dauko laptop acikin dakin barcin nasa ,suka rufe mami,daddy da Jamila.suka tasa Farhaan gaba har tsakiyyar parlorn suka ?ora masa bindiga da mugun shock Farhaan ke kallonsu,xai yi magana yaji bullet gefen kirjinsa,jin tashin bindiga yasa mami ta fashe da mugun kuka,tana dukan kofar da duka karfinta, sun kashesa daddy sun kashesa .”!”Addu’a kawai daddy yake a ransa gashi garin sauri ya baro wayar daki,suna ganin Farhaan din ya fadi sukayi takansu ,na daina jin motsin su
Farhaan mami ta shiga kwalawa kira da dukkan karfinta tana fadin yaxo ya bude kofar,sulalewa mami tayi a wajen a sume……..cike da wani irin tashin hankali Jamila tayi kanta,wani key ya shiga nema a dakin na Farhaan dakyar daddy ya samo sa, addu’a yake Allah yasa basu bar key jikin kofar ba,
Shi kansa daddy jikinsa bbu inda baya rawa,yana jin key din ya shiga ya sauke ajiyar xuciya,da gudu ya nufi parlor sai dai turus ya tsaya a wajen ganin Farhaan din kwance cikin jini. zuciyarsa yaji tana bugawa , jin yyi wani abu na tsaya masa a wuya………kusan karfe shidda na safe mutuwar Farhaan babu inda bata xaga ba,tun karfe hudu na Asuba commissioner yake gidan daddy shida yaransa,sosai ya ta baiwa daddy hakuri na rashin daukar wayarsa ,ya sata a caji barci ya daukesa,shima baya gari a ranar ya dawo.duk wani bincike sunyi basu samu komai akan mutuwar Farhaan Shagari ba,sai dai commissioner din ya tabbatar da turosu a kayi,ta yaya zasu karbi wayar hannun Farhaan da kuma laptop kadai,tambayoyi ake yiwa daddy sosai wasu ya bada amsa wasu yayi shiru,shi kansa daddy dauriya kawai yake ga mami kwance gadon Asibiti ,wacce har yau bata san inda kanta yake ba,Yarda Ammah taga ya shigo mata a gida da safe yayi mugun daga hankalinta,Ammah ta kalli Agogo kusan karfe 7,ya xube a gaban Ammah duk dauriyarsa ya kasa rike hawayensa,ammah ta shiga girgiza sa tana fadin”meya faru ina Nooriyah meya sameta ,yana girgiza kai yake fadin Ammah.”Besty Farhaan, cikin tashin hankali Ammah ke fadin meya samu Farhaan din” .Ammah ki cemin barci nake ki tashi ne dan Allah baxan iya daukar rashin sa ba,ki fada masa yanxu yaxo xan sakar masa noory ki bani biro da takarda Ammah.,,salati kawai Ammah keyi maganganun Aliyu din na taba ta,open ur eye’s Aliyu..”Ammah ta fada tana daka masa tsawa,ya kalli Ammah yana girgiza kai yake fadin.”xan hakura daita saboda farin cikin sa Ammah .rungume Ammah yayi yana fashewa da wani irin kuka mai fitowa tun daga karkashin xuciyarta,sai jikin Ammah yayi sanyi bata ta?a ganin Aliyunta haka ba bata ta?a ganin sa haka ba,
Shima Khaleel waxeer agigice ya shigowa Ammah ta kallesa tana fadin.”kayi min bayani Khaleel kar yasa zuciyata ta buga .
Ammah dama barayine suka kashe Farhaan Shagari.”kabbara Ammah tayi Aliyu ya nufi Khaleel ya rikesa yana fadin Yah leel pls ka fada mata bani ne sanadin mutuwarsa ba,ka fada masa dan Allah ya dawo xan saki noory ya Aureta baxan iya jure rashin sa ba,wai Aliyu ka haukace ne da kake maganar sakin matarka sabida abokinka.”Khaleel waxeer na girgiza kai yake fadin”kara ya fadawa Ammah gaskiyya kowa ma ya huta ,cikin minti goma Khaleel ya mata bayanin komai,kallon su kawai take, Khaleel ya rike hannayen Ammah yana fadin”dan Allah Ammah ki dauki abun nan da sauqi Ammah na girgiza kai tana masa wani irin kallo take fadin”wannan abun kake fadin na dauka da sauki ,mikewa tsaye Ammah tayi jin tayi dakin na juya mata saurin riketa Khaleel yayi ya zaunar daita gefen bed,jeka zo min da Nooriyah yarda Ammah yaga tayi yasa ya juya baiyi gardama ba Yabar Room din,tana moping parlor taji ana Danna door bell,Sama ta koma ta sako Hijab taxo ta bude kofar ganin Khaleel waxeer yasa xuciyarta tayi wani irin bugawa.ta gaishesa da ladabi,bai kalleta ba yake fadin”taxo Ammah na neman ta,
Talkami kawai ta xura a kafarta tabi bayan Khaleel wanda har ya nufi motarsa,tun a falon Ammah taji xuciyarta na tsinkewa, kasa ta xube tana gaisheda Ammah,Ammah ta amsa tana kallonta.
Karfin hali Ammah tayi na fadin”Abokin Aliyu ne ya rasu nasan bakiji labari ba,ga mijinki nan duk yabi ya daga mana hankali,
Dafe kirjinta tayi tana xare ido hawaye na taruwa a idonta take fadin.”Farhaan !”Farhaan ,sai kuma ta fara ihu,ganin su ukkun sun tsaya kallonta ta ?ora hannu akae tana fadin”dan Allah ku fadamin ta yarda xan gane kuce wasa kuke,
Wlhi Ammah xan fada Maki gaskiyya,komai da komai na Aurenta da Aliyu ta fadawa Ammah,har cikin da ake karya tana dashi duk bata da,baki bude Ammah ke kallonta ……..kenan da gaske ne??”ta nufi Aliyu da wani kalar tashin hankali tana fadin”kace wasa ne dan Allah ,na san yayi komai cikin fushine Amma ba halinsa bane,kai ka sani ba halin sa bane.”Ammah ta sauke ajiyar xuciya cike da jimami,ta kalli Khaleel waxeer tana fadin yaje da Aliyu su shirya dan samun jana’iza ,suma zasu shirya suxo gidan gaisuwar,ta kalli Aliyu cikin kakkausar murya tana fada masa ya dawo hankalinsa yanxu,kar kuma ace shine ya tura aka kashe Farhaan din tunda har sun samu sabani,kana jina Khaleel karka barsa ya daga daga inda kake,ka tabbata kana tare dashi.noory ta bisu da ido hawaye na xubar mata,wani irin zafi xuciyarta keyi mata da gaske Farhaan Ya rasu.”??wani xaxxabi taji yana cin karfinta,kusan karfe takwas da rabi tana kwance kan gadon Ammah,ta dunkule cikin duvet Ammah ta shigo dakin,da mug a hannunta,ta kalli Nooriyah wacce idanunta har sun canja sabida kuka.
Ammah ta xauna gefen bed tana fadin”ta tashi ta daure tasha tea,da sauri noory ta shiga girgiza kai hawaye na kara tarar mata ,take fadin”na koshi Ammah ,to mekika sha zaki ce wani kin koshi.”bana son musu tashi ki shanye kibani cup,Bata son yiwa Ammah musu ,ta karbi cup din ta kafa kai bata sauke ba sai da ta shanye duka tea dake cikinsa,da sauri ta koma xata kwanta Ammah ta dakatar daita,tana fadin ta bari ta huta sa’annan ta kwanta.har kusan 12 tana kwance a gadon Ammah,sai da akayi sallar axxahar suka shirya duka familyn waxeer suka nufi gidan gaisuwa,laylah sai kallon noory take dake famar sharar kwallah ta tabe Baki,
Tayi bakin cikin rasuwar Farhaan Shagari, kenan yanxu noory ta samu auren Aliyu waxeer a bagas,
Ammah na rike da hannun nooryn cikin mota take fadin”so kike mutane su fahimci wani abu a fara zargin ki kuma?”da sauri ta shiga goge hawayen idonta,ki natsu dan Allah Nooriyah kar mutane su fara zargin wani abu ki samu a matsala,da haka suka fita daga motar suka nufi cikin gidan,kai tsaye part din Mami suka nufa,yan uwanta kawai ne da yan uwan mijin sai Salma Shagari,mami har yanxu tana kwance a gadon asibiti,Ammah har magrib suna a gidan sai da akayi sallah suka tafi,kowa cike da al’ajabin rasuwar Farhaan din,
Dakin Ammah ta wuce kai tsaye,batareda ta tsaya parlor ba kukan da taji yana shirin taho mata yasa ta rufe bakin da gudu ta nufi toilet…..Ammah ce ta tsare Aliyu da plate a hannunta na white rice da stew ,da sauri ya shiga girgiza wa Ammah kai yana jin zuciyarsa nayi masa wani iri ,Ammah bana jin yunwa idan naci xanyi amai.”Ya fada babu wani walwala a fuskarsa,Ammah ta daure fuska tana fadin”ina wasa da kaine??”girgiza kai yayi buda baki yyi Ammah ta shiga basa,kusan rabi yaci ya fadawa Ammah idan ya cigaba daci xaiyi amae,kusan karfe goma ya shigo gidan Ammah ,kallonsa Ammah tayi tana fadin”baka kwanta ba.
Ya girgixa kai yana fadin”baxan iya kwana acan ba Ammah ,toh ka shiga ciki matar ka na nan ,itama xaxxabi take tun safe ,amma ta sha magani.gabansa ya fadi shi sai yanxu yama tuna da Nooriyah yana ta zama a parlor tareda Ammah har Kusan goma da rabi Ammah tace yaje ya duba matarsa,tura kofar dakin yayi can tsakiyyar bed ya sameta ta dunkule waje daya,rufe kofar yayi ya nufi kan bed .duvert din ya shiga ja,sukayi ido biyu dashi da sauri ta Runtse idonta xuciyarta na harbawa,
Murya can kasa yake fadin”Ya jikin ki??”kin ci abinci murya can ciki take fadin”ta samu sauqi kuma taci abinci da haka ta Runtse idonta ta matsu Yabar gaban ta
Shima kamar yasan abunda ke ranta bai takura taba yayi kwanciyar sa akan duguwar soofa din dake dakin,ya rage hasken fitila.dukan su cikin wannan daren babu wanda yayi barcin kirki,washe gari koda ta tashi bata gansa a dakin ba……har kusan 10 bata ga alamar shigowarsa ba,itama kanta dake ciwo tana ta kwanciya a daki.
Areefa tana ta kallon Siddiqa mansoor cike da takaici,wai na tambayeki mana Aunty Siddiqa Wai Farhaan kun hada jini dashi ne,xaki dauki mutuwarsa duk kisa Aranki,Ni dai wlhi bana jin dadin haka,bana son matsala ko kadan dan na girmi kowace irin matsala a rayuwar nan,idan kin shirya ki fito muje gidan gaisuwa ,sai mu wuce wajen malamin.”tayi maganar in I don’t care manner’s!”ita dai Siddiqa batace komai ba ta koma daki ta dauko Hijab dinta,ta dawo parlor tana kallon Areefa din daga sama har kasa take fadin”ba dai haka xaki gidan gaisuwa ba ,na rokeki ba danni ba ki saka Hijab,Areefa tayi wani irin juya ido nacin Aunty Siddiqa na damunta take fadin”mayafin da na saka fa.”gidan gaisuwa fa gidan gaisuwa Areefa.”tayi maganar da karaya a muryarta ,bakya tunanin a gidan mutuwa kema Allah ya dauki ranki..”tsaya anan dan Allah karki karasa ki daina yimin fatan mutuwa sabida saka Hijab,ki bani naki na saka dan kin san ko acikin kayana babu Hijab,sallah ma da dogayen riguna nake yinta.har suka isa gidan Gaisuwa Areefa na mitaa….
Take Note.!”
Team# bati Reader’s ban San ku ba ban san a wace dunia kuke ba,kuna karanta hakkin da ba naku ba batareda ko sisin ku ba,ba sai ku Rufe bakin ku ba sai kuka kasa yin haka sai xagi da cin mutunci,nida hakkina ku hanani magana,baku san ya nake squzzing duk wani free tym da nake dashi dan nayiwa wanda suka biyani dan faranta masu ba.sun san wahalar da ake sha shiyasa suka biyani hakkina tun kafin su karanta,idan na xalinci duk wacce take karanta min book batareda ta biya ba,tana kuma xagina a banxa Allah ya isar mata idan kuma kuka xalince Ni ya Rabbi ka saka min tun a duniya,
Haka wallahi tallahi duk wacce ta karanta koda kalma daya na book din nan,banda wanda na bayar a matsayin kyauta Allah ya isa ban yafe ba..
Littafin waminal Hoob na kudi ne #500
Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma’u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan layin..09060259200
Shaidar biya ta wannan layin#08086207764..
TEAM#WM
TEAM#NOORYALI FOREVER??
Post a Comment for "Waminal Hoob 29"