Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Waminal Hoob 27

Aydah??: 27

Baki bude Khaleel waxeer ke kallon Aliyu.har ya kai karshen zancen ya kasa furta kalma ko daya,sau uku yana buda baki da niyar ya yiwa Aliyu magana ya kasa,jin labarin yake tamkar a firm din hausa.tambayar kansa yake Anya hakan na kasancewa in real life kuwa?”Aliyu yaushe na fara wasa da kai da xaka tsaya a gabana kana shiryamin karya.!”Khaleel waxeer yayi Maganar


sounding so serious acikin muryarsa,
Aliyu ya kamo hannunsa cikin tashin Hankali yake fadin”believe me gaskiya nake fada maka Auren mu da Nooriyah contract marriage ne da gaske nake Khaleel waxeer noory budurwar Farhaan Shagari ce.!”Ya fada yana sauke numfashi da yake riko tun daxu,
“Khaleel waxeer ya dafe kansa yama rasa tunanin da ya kamata yayi,ya dago Yana kallon Aliyu da shima baya cikin natsuwar sa yake fadin”Kana nufin ko cikin da aka tabbatar akwai sa jikinta shima karyane baka taba kusantar taba??”Khaleel waxeer ya fada yana tsaresa da idanunsa,Aliyu waxeer ya dafe kansa yana fadin bbu abunda ya taba shiga tsakanina da noory,
Khaleel waxeer ya kallesa cikin ido da ido yana fadin”the best solution sakinta xakayi ae kayi Alkawarin xaka saketa ka dauki Alkawarin haka,kawai ka saketa kabarwa Farhaan ya Aura Ammah kuma kabarni daita xanyi mata bayanin komai fushinta na dan lokaci ne,kasan bata da riko ko kadan haka xata yafe maka,sabida bata son Allah yayi fushi da kai Akan haka Right?””shi dai Aliyu kallon Khaleel waxeer kawai yake sam wannan shawarar da ya kawo batayi masa ba,Ya dakune fuska yana fadin wannan wace irin shawara ce yah Khaleel ,gaskiyya Bata karbu ba a wajena ka canja wata .sakin noory ba mai sauki bane a waje na,ko dan farin cikin Ammah.”Khaleel ya girgiza kai yana sakin blushing yake fadin.”sabida farin cikin ka dai,da sauri Aliyu ya kallesa yana fadin”kamar ya farin cikina.”Aliyu Are You fall in luv with her?”da sauri ya kalli Khaleel waxeer yana girgiza kai yake fadin.i’m not I’m not Yayaah.!”to ka saketa mana,kallon Khaleel waxeer yake zuciyarsa na bugawa,
Xaka xauna daita baka sonta ae baxai ma yuyu bane………..”idan wani abu ya sameta sai na karar da duka dangin Farhaan sai yayi da ya sani na a dunia, Khaleel waxeer yana girgiza kai yake fadin .”Shi da budurwarsa meye na iko akanta A fusace Aliyu ya nufi kofa,dan maganganun Khaleel waxeer na kara bata masa rae,xai xauna shi daya ya samu mafita ya kalli agogon dake manne a damtsen hannunsa ,
Yana duba lokaci kusan awa biyu kenan,da yin waya da Farhaan,xaiyi tunanin awa daya yasan ta yarda xai bullowa Farhaan Shagari…..Hannu yasa yana jan xip din rigarta,wayarsa ce ta fara ring ya kalli mai kiran da sauri Nafeesa Shagari ce,jin yayi gabansa yayi wani irin bugawa da sauri ya sauka kan bed din ya dauki wayar gamida shigewa toilet ya daga wayar batareda yayi magana ba,Farhaan kana ina yanxu??”Yarda Nafeesa ke maganar tana jan numfashi yasan bbu lfy gabansa na faduwa yake fadin”lfy kiyi min bayani dan Allah !”mami bata da lafia tana kwance a gadon Asibiti kaxo yanxu,jin yayi hankalinsa yayi mugun tashi .da sauri ya fito toilet Yana hada wani xufa ya kai kallonsa kan Nooriyah ,awa kusan biyu kenan da yayi mata Allura ,idan mami ta mutu bai nemi gafarar ta ba baxai taba yafewa kansa ba,mami tana kwance a gadon Asibiti yana kokarin aekata xina da maccen da yake yiwa wani irin so.!!”da wane irin fuska xai kalli Nooriyah idan ta farfa?o ,maganganun da daddy ya fada masa suka shiga dawo masa akai,Wasu irin hawaye Masu zafi suke mirginowa akan fuskarsa,shi kansa baxai yafewa kansa ba.Yarda ya rika hurting Besty dinsa da Nooriyah,Yaci Amanar best friend dinsa ta hanyar kwantawa da Budurwarsa,jin yyi gaba daya duniyar tana juye masa .bai taba sanin haka kalar tashin hankali yake ba sai yanxu,ya dauka xai iya binne duk wani xunnuban shi idan ya Auri Nooriyah ashe ba haka bane,bai isa yayiwa ?addara wayau ba,yau yaji ya kara son bestyn sa wani irin soyayyar sa mai girma yaji yana kara bin dukkan jikinsa,gaskiyyar noory ne ya kamata ko da sau daya ya baiwa Aliyu waxeer farin ciki tamkar yarda ya basa,,
Ya girgiza kai yana tuno kalaman Areefa mansoor,ita ta shirya duk wannan Abun bata wannan hanyar yaso bullowa Besty dinsa ba,bai shirya nunawa noory kalar sa ba,da kalar halinsa sai gashi Areefa mansoor ta cillasa a ramen da bai isa ya fito ba,ya tabbata ya rasa Nooriyah har abada baxata kara kallonsa da mutunci ba,yau da kansa yake kokarin Raping innocent girl irin Nooriyah,da ya aekata haka da baxai taba yafewa kansa ba .”A yau kin taimakeni Nafeesa Shagari ban san dame xan saka maki ba,
Typing ya shigayi a wayarsa.
_kayi hakuri kayi hakuri Dan Allah!”ban cancanci yafiyar ka ba yanxu ,ka yafemin dan Allah karka tambayeni dalili Besty na bar maka noory har abada bata cancanci xama dani a matsayin mijin Aure ba,kai ne dai-dai Rayuwarta daga yau daga yanxun nan,xan tayaka binne wannan sirrin nayi maka Alkawarin xan tayaka binne wannan sirrin Besty ka yafemin,idan naci Amanar ka agabanka ko a bayanka na aekata maka laifi mai girma wanda nasan baxaka yafemin ba,baxan kara zuwa inda kake ba sabida wannan laifin_”!
Karshe ya saka sunan sa,kafin ya basa Address yaxo yaje da noory tana a guest house dinsa,xaije Asibiti mami batada lafia,da haka ya kashe wayar ya saka kayansa ya dauki car key dinsa,ya tsaya yana yiwa Nooriyah kallon karshe,lokaci yayi da xaiyi nisa da Rayuwarsu haka xai tsaya da kafafunsa ya hana Areefa mansoor shiga cikin Rayuwarsu,Hawaye kawai ke gudu akan fuskarsa,ya shiga mota ya tayar yana fadawa maigadi Aliyu xaixo yanxu idan yaji horn dinsa ya bude masa,da haka yaja motar da gudu yana halbata kan titi.burinsa ya isa Asibiti yaga jikin Mami,Koda ya Isa Asibiti yayunsa na tsaye a emergency da kuma mahaifinsa da gudu ya karaso yana sauke numfashi yake fadin .”Ina mami?”Salma Shagari ta karaso gabansa dama itace mai zafi acikin su ta cakumi kwalar rigarsa,hawaye na xubar mata take fadin”daga yanxun nan idan numfashin mami ya daina aeki idan xuciyarta ta buga kaine Farhaan kaine Farhaan Shagari baxamu taba yafe maka ba.”ta fada tana girgiza sa da karfi tana wani irin kuka mai cin rai,Aunty Nafeesa taxo ta riketa tana fadin meye haka Salma.”ki dawo natsuwarki dan Allah.”Farhaan ya rike daddy dauke da nashi kalar tashin hankali yake fadin”daddy Ina mami,Alh.omar ya shiga nuna masa kofa,
Da gudu ya nufi kofar suka ci karo da wata nurse da ta fito daga dakin,malam kayi hakuri ba’a shiga Emergency wani kallo Farhaan keyi mata cikin ihu yake fadin”uwar tawa kike fadamin ban isa na ganta ba xan ga mai hanani shiga dakin nan,
“Bani hanya Malama ya fada yana daka mata tsawa,a tsorace nurse din taja da baya tana kallonsa fadawa yayi dakin yana sauke numfashi da dukkan karfinsa yake fadin mami.”!ya fada yana xubewa saman jikinta,
Dai-dai lokacin mami ta bude idonta tana kallon Farhaan,saurin kara rufe idon tayi jin suna yimata nauyi,
.”mami pls ki tashi mu tafi gida kiyi hakuri ki yafemin nayi maki Alkawari daga yau daga yanxun nan xanyi duk Abunda kikeso nayi maki Alkawarin xan auri xahra azeez cikin satin Nan inhar xaki yafemin ki daina fushi dani.”da gaske ka damu da lafiata ??”mami tayi maganar murya can kasa,da sauri ya dago kansa yana kare damke hannunsa cikin nata yake fadin.”na damu dake da lafiyar ki fiye da kowa da komai a dunia.”pls ki tashi mami ya fada hawaye suna xubar masa.lumshe ido mami tayi a hankali dai-dai lokacin Alh.omar ya shigo shida su Nafisa,ya kalli Farhaan wanda tun xuwansa baiyi magana dashi ba,Farhaan tashi ka fita.”Yana girgixawa daddy Kai Yake fadin”dan Allah Daddy karka ce na tafi kayi hakuri Dan Allah.”lokaci daya mami ta bude ido tana kallon daddy take fadin kabarsa dan Allah.”shiru Dukansu sukayi a dakin likita na shigowa dan duba mami,suka fita dukan su……….Bai san sau nawa ya karanta sakon Farhaan Shagari ba ya kasa fahimtar komai acikin sakon,sai Address din da ya Turo masa wanda yafi maida hankali akansa,wani irin horn yake dannawa a kofar gidan Farhaan Shagari , Addu’a kawai yake yayi ido biyu da Farhaan Shagari sae ya ha?a masa jini da majina duka a lokaci daya,ko rufe motar baiyi ba ya nufi cikin gidan yana kwalawa Farhaan Shagari kira,
Amma me har ya shiga cikin parlorn bbu alamar Farhaan a gidan,tsayawa yayi tsakiyyar parlorn zuciyarsa na bugawa,
Addu’a yake akan Allah kar ya baiwa Farhaan sa’ar noory shine abu na karshe da Farhaan zai aekata masa wanda yake jin baxai iya yafewa ba……. stairs ya nufa yana kwalawa noory kira,kofar da ya gani a bude anan ya fada,
Kallonta kawai yake.
Baya yaja yana jin kafafunsa nayi masa wani irin nauyi.Alllah yasa mafarki ne allah yasa ba gaskiyya bane,karasawa yayi har inda take ya shiga kiran sunanta cikin tashin hankali jin yake Muryarsa tamkar ba tasa ba,girgixata ya shigayi da dukkan karfinsa har lokacin bata motsi da karfi yake fadin”Farhaan mekayi mata meka yiwa yar mutane,Yana jin dukkan hop dinsa akan noory na karyewa,Yana da kishi kishin da baxai iya misiltawa ba,ko shi kansa kishinsa na basa tsoro kullum acikin sujadarsa yana rokon Allah ya rage masa kishi musamman akan iyalinsa,idan tunaninsa ta tabbata idan xarginsa ya kasance gaskiyyane ,xai hakura da Nooriyah hakura na har abada dan baxai iya daukar wannan abun ba zuciyarsa xata iya tarwatsewa duka.dama tun farko shisshigine ya kaisa,
Meyasa soyayya bata tashi wullasa ko’ina ba sai ta wullasa a inda bai kamata yaje ba.
Hawaye masu zafi yaji suna xubar masa kishi yaji yana cin zuciyarsa,wani xaxxabi yaji yana bin jinin jikinsa lokaci daya, hawaye suka cigaba da gudu akan fuskarsa yau shine da arhar hawaye har haka?? Kiran Khaleel waxeer ya shigo a wayarsa bai bi takan kiran ba,ya dauki noory da wayarta da ya gani yashe a wurin ya nufi kofa,har kusan 9 Khaleel waxeer na tare dashi a gidan sa suna parlor suna tattauna matsalar sun dauko doctor a sirrance,ya duba nooryn ya fada masu Allurar barci akayi mata mai karfi nan da wasu yan awanni xata tashi,bayan fitarsa Khaleel ya dubi Aliyu cike da wani irin tausayin kanin nasa yake fadin.”na xata xaka ce ya duba tane mu samu tabbatacin Farhaan bai kwanta daita ba,Aliyu ya girgiza kai yana fadin”Ta yaya zai duba min mata tayaya zai duba wurin da bai kamata ya duba ba,
Baxan iya daukar wannan ba,Abun tausayi abun daria haka kishin Aliyu na basa mamaki.kuma a hakan yake cika bakin baya son Nooriyah ji yarda ya zama cikin awa daya kacal.”idan haka ya faru da gaske kotu xata rabamu da Farhaan,dangantakar mu Abokantakarmu xata tarwatse kowa ma ya huta.”Khaleel waxeer yayi masa sallama yana fadin”suyi waya idan ta farfa?o,sai kusan goma na dare ta farfa?o ihu ta fasa lokaci daya tana fashewa da kuka tana kai hannunta kasanta cike da mugun tashin hankali,lokaci daya ta mike tsaye jikinta bbu inda baya rawa,dai-dai lokacin Aliyu ya turo kofar dakin da take tayi kansa tana fadin meya yayi min ka fadamin xuciyata xata bugawa,kuka take mai cin rae tana rike da Aliyu da shima yake jin wani iri hannunta ya rika ya zaunar daita gefen bed,natsuwarta yake bukata kafin ya fara yi mata tambayoyin da yake so yayi mata baxai iya jira har sai da safe ba,
“Baki ji canji ajikin ki ba,da sauri ta girgiza kai,
Lokaci daya Aliyu idonsa suka kai a xip din rigarta da yake a waje.saurin dauke kansa yayi yana jin bugun zuciyarsa har cikin fuskarsa,lokaci daya noory ta mike tsaye taja skirt din jikinta ya sauka kasa daka ita dai underwears taxo taja xip din rigar taji sa a bude,ko takan Aliyu waxeer bata biba ta nufi kofar fita tana fashewa da wani irin kuka kara ta mutu da taga wannan Ranar,Allah ya dau ranta yanxu nan ta huta.”duhu taji yana mamaye idanunta,baya ta tafi xata fadi Aliyu yayi saurin tarota yana girgixata yana kiran sunanta,sai dai ta riga da ta suma a hannunsa,kwantar daita yayi ya dauki bottle water ya kwance marfin ya xube mata su akan fuska.breath noory !”breath Dan Allah.” Ya fada da wata irin murya tari ta shigayi da karfi dagota yayi da sauri sauran ruwan da suka rage ya bata tasha,dan Allah ka ciremin wannan rigar ka dubani.”tayi maganar da wani kalar tashin hankali,
Kan bed ya kaita ya kwantar daita,ya shiga shafa kanta yana fadin”ta huta karta kara magana,kallonsa kawai take ta kasa yimasa magana,xuciyarta taji tana yimata ciwo.”idan yanxu a bata wuka ace ta kashe wani Farhaan shine mutum na farko da xata fara tun kara……Hawaye kawai ke xubar mata,a daren ranar Aliyu na tare daita da ta fara barci sae ta farko a firgice,sai Aliyu ya riketa haka suka kwana a wahalce,
Koda safe kasa hada ido da Aliyu tayi idonta har sun canja kala sabida kuka dakinta ta koma ta rufe kanta har kusan 12 na rana baiji motsinta ba ,shima bai ta kura mata ba ya cigaba da hidimomin sa haka Khaleel waxeer ya hanasa tun karar Farhaan Shagari,
Ya fada masa babu abunda yayiwa nooryn shi ya tabbatar da haka,acikin sakon da ya turo Aliyu yaga hakan,haka maganganun da Farhaan Shagari yayi duka sun daurewa Khaleel kai ya rasa wane xai kama aciki.”bangaren Farhaan kuwa kwana ?aya mami tayi a Asibiti aka bata sallama suka dawo gida dama jininta ne ya haye sabida damuwar farhaan din,bbu abunda daddy ya fada masa sai ya kiyaye dan shine matsalar Mami ,Haka yayi kokari ya gama da mami lafia ko zai ga haske acikin Rayuwarsa,xahra Axeez itada mahaifiyarta sunxo har gida sun duba mami,wanda mami taji dadin haka sosai,
Xahra sai rawar kafa take agaban Farhaan shi dai iyakarsa ya bita da kallo,
Kallonsa kawai take da wani irin tashin Hankali,tana girgixa kai tana fashewa da daria bakin ciki,Farhaan Ni xaka yaudara ??”tayi maganar tana cakumarsa,ya hankada ta yana fadin”Aliyu bai cancanci wannan sakayyar ba,ko kadan baki dace dashi ba Areefa mansoor ke bakar Ashaana ce wanda duk kika tunkara sai kin konesa,xan tsaya da kafafuna na tabbatar baki kara shiga cikin rayuwar Aliyu waxeer ba,Haka na sadaukar masa da soyayyar da nake yiwa Nooriyah ,ta hanyar hakan kadai xan saka masa da Alkhairin da yayi min A baya.”ke kina tunanin idan Aliyu yasan ke yar hannu ce ko giyar wake yasha xai kara kallon inda kike har ya kai ga Auren ki.”Baki san waye shi ba,karma kiyi kasadar shiga Rayuwarsa kina bude a haka,a daren na Auren ku xai kasheki sabida kishi Dan haka kiyi ta Kanki,adalci daya xan iya yimaki,
Na amince xan karbi duk Abunda kika haifa da hannu biyu,ban sani ba ko daga shi baxan kara samun wani a dunia ba.kema ki tuba ki komawa Allah.”Ya dauko rafar kudi har guda ukku ya damka mata yana fadin”ki fara taba wannan canji sabida lafiarki da babyn dake jikin ki,idan ya girma xan fadawa mami nasan xata ji tausayina ta yafemin,
Idan ya isa haihuwa bani da shakku akan mami,na riga da na fada mata kalar tawa ?addarar haifa mata jika shege,da haka ya shige motarsa ya bar Areefa mansoor da wani irin shock kwance akan fuskarta,marin kanta ta shigayi da karfi tana so ta tashi daga wannan mummunan mafarkin….

*Wawaye aci gaba da karanta book batareda an biya hakki ba,Ni kuma baxan fasa jan Allah ya isa ba,idan kin isa ki daina karanta min daga yanxun nan duk kika karanta kalma koda daya baki biya ba ban yafe maki ba*!”

Littafin waminal Hoob na kudi ne#500
Account Daitails
0004151137
Jaiz Bank
Asma’u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan lambar#
09060259200
Shaidar biya ta wannan lambar#08086207764

ASMY#??
WM#??
NooryAli#Forever??
[9/15, 6:11 PM] Asmy Mom A
ASMY??

Post a Comment for "Waminal Hoob 27"