Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Waminal Hoob 11

PAID BOOK
Asmy b Aliyu..

Shuru dukansu suka xauna a motar yau Kiran da farhaan yyi masa Ya kai goma Amma yaki daga wayar,acikin unguwar g.r.a guest house dinsa yake wani Dan kyakkyawan gida horn ya shiga dannawa da sauri Mai gadi ya wangale get ya shiga ciki .mota daya ce acikin parking lot din,tana lullube da tamfal da alamar baa amfani da motar,parking yyi ya fito ya xagaya ya bude mata motar fitowa tayi daga motar


kamshinta duk ya cikasa ,Rufe motar yyi Yana fadin ki daina yimin yanga ba nine farhaan shagari ba.”da haka ya juya ya nufi Entrance din shiga gidan,da takunsa na kasaita.binsa tayi a baya yasa key ya bude kofar Mai dauke da glass door.
Tsaruwar falon kawai ya kusa ya gigita tunanin Nooriyah,komai na cikin parlorn kalar milk and gold ne.tsaye tayi tana karewa parlorn kallo,girgixa kansa Aliyu yyi Yana kallonta wannan Idan yafita daita xuwa wata kasa baisan Kuma ya xatayi ba sabida kauyanci.hawaye taji suna cika idonta lokaci daya ,tambayar kanta ta shigayi wannan wane irin Aure ne??”auren da bbu Danginta ko daya Anya batayi sakaci ba kuwa??”xubewa tayi acikin kujorun dake xagaye da parlorn hawaye masu xafin gaske na sauka akan fuskarta ,danna waya yake ya dago ya kalleta,sai yaga tana xubar hawaye mmki yakeyi yarda ko kadan kuka baya yi mata wuya,kukanta na Kusan karo na ukku kenan a parlorn baffa tayi ta sharar hawaye a motarsa ma yanxu Kuma haka.da wani irin sauti yake fadin ke kuka baya maki wuyane??”kifa kanta tayi ajikin kujerar tana Jin xuciyarta nayi mata xafi,,wayarsa ce ta fara ring ganin Mai kiransa Kuma a vedio call yasha mamaki ,wani irin blushing ya shiga saki kafin yyi picking call din…..Kura mata ido yyi tana sanye cikin vest da tree quater ajikinta,kananun kalabane akanta.kin gama Fushin Areefa Mansoor ??””yayi Maganar cike da wani irin aji A muryarsa,kayi laifi ka kasa nemana ko hakuri ka kasa bani.”sabida kasan baxan iya Rayuwa Babu Kai ba.”Ta fada cike da shagawaba tana turo masa kyawawan pink lips dinta,ya wara ido Yana fadin”xuwa yanxu yaci ace kinfi kowa sanin Halina Areefa Mansoor kin San baxan iya Rarrashin macce ba ,haka baxan iya Baki hakuri ba.”banga Laifin me nayi maki ba ,kawai kin dauki fushi Dani na xata ma munyi final break up dake.”yyi Maganar sounding so very serious a muryarsa,
Cikin Rawar Murya take fadin da gaske xaka iya Rayuwa Babu ni haidar,.”ya dage kafada yana fadin idan kaddarar muce a haka ya muka iya.”Kallonsa kurum ta tsaya tanayi maganganun sa suna yimata ciwo haka sun tabata,bata san meyasa Bata iya dogon Fushi da Aliyu waxeer ba,tana yimasa wani irin so da ko kanta batayi wa hakan,kaji ddi burinka ya cika da kae da Farhaan Shagari “.finally an daura Auren sai ka dawo hankalin ka yanxu,ban yarda ko daki daya ku kwana ba.”Idan aka cuceni kaida Allah ta fada tana dakune Fuska cike da kishi…….Maganar ta yabasa Daria sosai,saboda gaki uwata ke xaki fadamin Abunda xanyi kenan.”Ko farhaan da ya shirya Auren baya da ikon axamin dokoki akanta ,Dan nafi sa iko daita yanxu….”Anjima muyi waya bana da caji yanxu,cike da kishi ta kashe wayar,dagowa yyi suka hada ido daita ganin irin kallon da take masa,yace lafia??”dauke kanta tayi batare da tace masa komai ba,haka suka ta xama a falon Kusan awa daya,su Ammah ba karamin takurasa sukayi ba.
Baiga amfanin tahowa daita ba,mikewa yyi tsaye ya nufi kofa Yana fadin idan kin gama kukan ki taso mutafi Farhaan ya cuceni ya hadani da lalura,aranta tana Dana sanin wannan Auren wato itace lalurar?””Ganin inda suka shigo da motar tayi saurin kallonsa,Jin tayi jikinta yyi sanyi lokaci daya.waya ya fiddo ya Kira lambar kawu balele Wanda tamkar jiran Kiran Yake ya daga da sallama,gamu a kofar gidanka .”kunyi sa’a yanxu nake Shirin fita.
Da haka ya katse wayar Yana kallon Nooriyah da tayi wani irin shuru haka jikinta yyi sanyi lokaci daya,
Ya bude mata ido Yana fadin sai na fitar dake daga motar xaki fita kije kawunki na son ganinki .”minti goma kacal na Baki bana son jira,fita tayi daga motar batare da tace masa komai ba ,
Ta fara tafia cike da natsuwa Kura mata ido kurum yyi komai ya tuno yayi saurin dauke kansa gamida kwantar da kansa acikin kujerar motar dialling number Farhaan shagari yayi har ta katse bai daga ba,har xai aje wayar sai ga Kiran farhaan din ya shigo dauka yyi cike da masifa Farhaan ke fadin bakada kirki Besty.”Dan juya ido Aliyu yyi Yana fadin Rashin kirkin me nayi maka .”Kira nawa nayi maka a waya???”ina cikin mutane kasan bana son Kuma damuwa,Oh Really?”Farhaan yyi maganar cike da Jin haushinsa,wayana ya kusa hutawa acikin satin Nan xan Bata waya na huta idan ka isa ka canyeta ta wayar.”Aliyu waxeer ya fada cikin daga Murya kwantar da muryar sa Yyi Yana fadin”Baka san ya nake jibane Aliyu har yau Allah bai jarabceka bane da irin soyayyar da nake yiwa Nooriyah duk ranar da Allah ya jarabceka ,saika haukace…….”da sauri Aliyu waxeer ya katse sa yana fadin”Allah ya sauwakke aeni baxan iya wannan soyayyar ta wahala ba, kai da kaji xaka iya ae ga fili ga Mai doki.”Areefa na hankuri,Ita taji xata iya muyi waya anjima xan maidata gida……kabani mu gaisa Mana,baka gaisa dani ba .”I will tell her kana gaisheta kana Kuma missing nata bashi kenan ba.??”Idan dare baiyi ba xan hadaku vedio call.”Da haka Aliyu ya kashe wayar bai jira Mai farhaan din xai sake fada ba,ganin yayi Nooriyah na tahowa itada kawu,hannun kawu yabi da kallo Wanda ya rike Nooriyah dashi .shi Kuma wannan tsohon baya da hankali ne.”karamar yarinyya ce da xai wani rike mata hannu.”Yana xaune a motar har suka karaso ,ya sauke glass kawu ya washe Baki Yana gaisheda Aliyu,
Nooriyah sai sharar hawaye takeyi,wani sashe na xuciyarta tana Jin mugun haushinsa da tsanarsa ,girman Kai ya hanasa ya fito daga motar ya gaisheda kawunta,Kuma kawun ya gaishesa Yana amsa masa cike da wulakanci,kawu da kansa ya bude mata front side ta shiga ya rufe kofar.kawu na daga masu hannu har suka bar layin,Fuska a daure yake fadin katuwa dake har sai ya wani rike hannunki sai kace jaririya.”kin manta matsayinki Yanxu kinada igiyoyi ukku akanki.”baxan dauki wannan xunubin ba,ko Farhaan din dake saurayinki ban amince kiyi masa hirar soyayya ba,iyakacin ku gaisuwa idan mun Rabu sai kuje can ku tacin soyayyar ku,,Yarda Yake magana Yana tada jijiyoyin wuya Yana Bata mamaki ,sai dai batada lokacin sa a ynxu suna shiga waxeer mention ana Kiran sallar magrib ,waya yyi da Ammah ya fada mata sun dawo ,tabasa umurnin ya biyo daita ta cikin balcony mutane sun fara ragewa ,
Ajeta kawai yayi ya juya yayi tafiarsa batareda ya jira Ammah din tafito ba ,wanka Ammah ta saka tayi ta sauketa a room din da ta sauka tun farkon xuwanta gidan, Abinci aka jera mata Akan tray Amma ta kasa cin komai ko kadan Bata da wani appetite a bakinta,Ramlah waxeer ce ta turo kofar cikin shiga ta alfarma ta Dan Buda ido da mamaki tana kallon Nooriyah dake xaune kan rug dake tsakiyyar parlorn towel ne ajikinta sai Kuma Hijab da alamar tayi wanka Amma Bata shirya ba,Hajia Ramlah ta karaso da sauri tana fadin Ya haka daughter meyasa Baki shirya ba Baki ci Abinci ba Kusan awa daya kefa muke jira a tafi dake gidanki.”Jin haka gaban Nooriyah yayi wani irin bugawa tamkar wacce xaa Kai cikin kabari sai ga hawaye suka fara Rolling akan fuskarta,
Baki sake Hajia Ramlah ke kallonta.sai dai batayi mamakin ganin hawaye a idonta taba ,hakuri xakiyi Nooriyah haka ko wace macce takeji Idan xaa kaita gidan miji.”ko Abincin kinki taba komai still hawaye na xubar mata cikin muryar kuka take fadin na koshi Aunty,
Hajia Ramlah ta girgixa Kai tana fadin baxaayi haka ba ,na hada maki tea.daga Kai kurum tayi ,Hajia Ramlah ta shige kitchen da kanta ta hado mata tea a mug Mai kauri ta sata agaba dakyar Tasha rabi tace ta koshi,
Wata super sharatoon ta fiddo mata kalar brown da milk ajikinta doguwar riga ta saka ta fesa mata turarruka ta tayata ta saka mayafin kayan ,ta rike hannunta suka sauka parlorn Ammah,tana Jin ana sakin guda .aka xaunar daita tsakiyyar parlorn Ammah ,hajia Ramlah ta kalli Ammah tana fadin gata Ammah kiyi mata Addu’a da Nasiha,Ammah tayi murmushi tace ba yauba Ramlah kuje kawai Allah yay masu Albarka,da haka Ramlah waxeer taja hannunta da wata kawar Ammah suka fice daga parlorn duk da kasancewar gida dayane gidajen su Aliyu da Khalil waxeer Amma dukansu akwai Yar tafia daga part din Ammah,Hajia Ramlah tayi driving dinsu xuwa gidan Aliyu Wanda Yake kallon na Khalil waxeer,Koda suka shiga a babban parlon gidan,Aliyu waxeer na xaune da laptop a gabansa Yana operating dinta .xuwa lokacin yyi wanka ya shirya cikin Black cooton shirt Wanda ta kama jikinsa sosai har ana hango pecs dinsa,
Sai wandon jeans Wanda ya kasance fari Kal.”da ido Hajia Ramlah ta bisa ,dama kana gida??”yeah Aunty akwai aikin da nake satin Nan ma xan bar kasar,da mamaki take fadin toh Amma tare xaku tafi ko??”ta karaso tana xaunar da Nooriyah gefenta ,baice komai ba.batool ganin Yayanta a parlorn ta kalli Aysha waxeer tana fadin mu tafi kawai Aysha Yana Nan karya disgamu ga bansu Yasmin.”Juyawa sukayi sukabar parlorn ya rage daga shi Sai Hajia Ramlah,
Ta Mike tsaye tana fadin gaka A parlor ka Kara sa daita master bedroom ni xan koma ,
Allah yay maku Albarka ya Baku xaman lfy,gobe walima karfe 10 kar kaje ka Buda Baki kana sharar barci.”dakune fuska yyi Yana kallonta walima fa mata ke xuwa meye nawa aciki,ta wara ido tana fadin .”bakai xaka kaita bane karka bata Muna lokaci,ko mother’s day ka Hana ayi,ya shafa kansa Yana kallonta bai dai ce komai ba. Har mota ya rakata ya rufe koina ya dawo still tana xaune a parlorn taki cire lullubin saman kanta. Yana hararta yake fadin”.wani kika ajey da xai cire maki wannan uban mayafin.”bude fuskarta tayi tana kallonsa da kumburarrun idanunta,
Dauke kansa yyi baya son kallon cikin kwayar idanunta ko kadan,aikinsa ya cigaba da yi batare da ya kara kulata ba,har Kusan 11 Yana kan laptop har ta fara gyangadi ,Yana kallonta ,Kusan 12 ya rufe laptop dagowar da xaiyi tayi barci.Kashe fitullun parlorn yyi gamida nufar stairs ya wucewarsa master bedroom dinsa,har ya kwanta yaji Rashin kyautawarsa , akwai sanyi sosai a parlorn bedshoes dinsa ya saka ya sauko down stairs,
Ya dde tsaye Yana kallonta bubbuga kujerar ya shigayi da karfi Amma ko motsi batayi ba,Yana mamakin nauyin barcinta,Rasa yarda xai tasheta yyi.daukarta yyi cak ya nufi stairs daita har lokacin ko dogon motsi batayi ba,,Yana mamakin nauyin barcinta Yana karawa ,daki Mai kallon room dinsa Nan ya shiga daita Wanda shima off white ne komai na cikin room din ,Ahankali ya kwantar daita kan bed,
Ya cire mayafin dake shake a wuyanta,kurawa innocent face dinta ido yyi xuciyarsa na harbawa da wani irin yanayi,yaja duvert ya rufe Mata jikinta ya kunna Mata Ac bai kure Ac ba da sassarfa Yabar room din gamida ja Mata kofar……….A kunnenta aka kira Assallatu,farkawar da tayi ta jita akan bed cike da mamaki makunnin fitilar dake jikin gado ta kunna ,duk da dim ne tasan A daki ta kwana.
To ya akayi taxo Anan itada ke barci a parlor ko wannan mutunen Ya tasheta cikin dare ta dawo daki.”ta dde xaune kan bed kafin ta saukar da kafafunta kasa,ta kunna fitila Mai Haske ,haske ya gauraye dakin tamkar Hasken Rana.Aranta Addu’a kawai take tamkar baxaa mutu ba.ganin glass door daga bangaren Hagu yasa ta nufi kofar da sassarfa,duk A tunaninta ko kofar toilet ne,rasa yarda xata budesa tayi .xama tayi agefen bed ga fitsari tana Jin yarda take jinsa,
Ganin baxata iya rike fitsarin ba yasa ta nufi kofa da sauri ta fice daga room din ,dai-dai lokacin Aliyu waxeer ya fito daga nashi dakin,sanye cikin farar Jallabiyya sai kamshi ke tashi da alamar massallaci xai tafi,da mmki Yake kallonta.sai Kuma Ya nufi stairs da sauri ta cimmasa cikin rawar Murya take fadin fitsari xanyi Kuma bbu bandaki a dakin.”da mmki ya juyo Yana kallonta ,A bakina xakiyi fitsarin kenan??”Ya fada Yana wani daure fuska,kayi hakuri nata gwada bude kofar Bai bude ba,
Dakin ya shiga tabi bayansa,duba dakin ya shigayi yaga remonte din dake control door din kan doguwar soofa dake Room din ya dauko,ya danna saiga kofar ta bude Baki sake Nooriyah ke kallon kofar,ficewa yyi daga dakin yabarta tsaye,closer din kayanta ta gani dama Ammah ta fada Mata komai da komai nata na dakinta ,harta da sabbin towels an xuba Mata bbu Abunda bbu,ga jikkuna lefenta Nan suma an jera Mata,tana tunanin wannan kayan xasuyi shekara goma tana saka su basu kare ba.ta dde tsaye tana kallon kayan,kafin ta nufi kofar toilet Anan ma sai da ta Bata lokaci wajen kallon toilet din girman sa kurum xaa hade Rabin gidan kawu balele……wanka tayi gamida dauro Alwallah dama kaidarta ne tun tana gida Idan ta tashi sallar Asuba wanka xata farayi kafin ta dauro Alwallah,doguwar riga ta saka marar nauyi ta samu cikin hijab din da aka jera Mata Wanda sun Kai kala talatin ,ta dauki kala daya ta fito ta shimfida carpet ta tada sallah……….sai Kusan 7 ta gama Addu’oin ta ,ta gyara gado sauka kasa tayi tana gyara parlorn duk da bayada wani datti,
Tana gamawa ta koma daki ta cigaba da xama,karfe Tara Ammah ta Aiko masu da lafiyayyen break fast,tana jinsa a parlor Yana ci ta kasa fitowa,
Karar tafiarsa taji da alamar ya gama Kai tsaye ya turo kofar dakin da take,kallo Ya bita dashi .Murya can kasa tace masa ina kwana.”ba tareda Ya Amsa ba ,ya fada Mata xaije yyi wanka ta shirya xai sauketa gidan Ammah bayason jira,bai jira Amsarta ba ya juya ya nufi nasa dakin.kusan karfe goma suka fice daga gidan kowane cikin shiga ta alfarma,
Ba karamin dacewa sukayi da Juna ba,
Har parlorn Ammah sukayi sallama bbu kowa parlorn sai Khalil waxeer da laylah dake dinning Area suna break fast,
Da murmushi Khalil ke fadin Ango kasha kamshi .”da mayen Kallo laylah tabi Aliyu da kallo tana hadiyar yawun bakin ciki Kyan da taga yyi sai wani sheki yakeyi,tayi bakin cikin Da Areefa Mansoor ta rasa Aliyu waxeer.itakan har Aranta Bata son Nooriyah,har kasa Nooriyah ta durkusa tana gaida Khalil da laylah ,Khalil din ne kurum ya Amsa yayin da laylah ta wani dauke kai…….hannayen Aliyu taji Yana dagota da sauri ya kalli direct Cikin idanunta ,Yake fadin bana son irin wannan gaisuwar daga yau,a tsaye ma ya isa muje ku gaisa da Ammah yaja hannunta suna barin wajen ,Khalil yayi Daria Yana fadin Dan iska har Dani yayanka xaka saka tana gaisheni a tsaye.”Aliyu bai dai ce komai ba ya juyo Yana ma Khalil wani kallon da shi kadai ya San ma’anarsa ,laylah ta tabe Baki tana fadin .”Iyayi kawai Yaushe ya fara tarairayar macce haka??””sai kace ma matar tana da class Yana wani kankam ba akanta,Khalil ya wara ido Yana fadin”bbu wani can kedai kina taya kawarki kishi…”wani kallo tayi masa yayi saurin rufe bakinsa Yana sakin murmushi.karshe mikewa tsaye yyi Yabar Mata wurin,kallon takaici tabisa dashi….

Account Details
0004157137
Jaiz Bank
Asma’u Buhari Aliyu
Katin wayar MTN.ta wannan lambar#08086207764
Shaidar Biya ta wannan lambar#08086207764

Thank you.#
WH#??
HWA#??

Post a Comment for "Waminal Hoob 11"