Tayi Min kankanta 38
38*
A harabar gidan ya adana motarshi sannan ya shiga falon,da sallamarsa,bakowa aciki hakanne yasa ya É—auka suna É—akin mummy,
Da saurinsa ya ƙarasa falon mummyn,zaune take kan kujera,Zahra tayi matashin kai da cinyarta,suna kallon news,wanda ita zahran sam bata fahimtar komai hankalinta na kan yayan nata.jinshi shuru da tayi se duk kishi ya taso mata.
Sallamarshi ce tasata saurin miƙewa tana duban hanyar daya shigo,da saurinta ta nufeshi,dan ta mance da mummy dake gurin.
Shima itan kawai yakeson gani,dan yinin da yayi babu ita duk ya takura,hannayenshi ya buÉ—e mata ta shige,ya maida hannun ya rungumeta,wata ajiyar zuciya suka saki atare,cikin shagwaÉ“a tana É—an dukan Æ™irjinshi tace”yaya shine ka tafi kabarni ko?”
ÆŠago haÉ“arta yayi ya tsura mata sexy eyes É—inshi É—an nazarinta yayi na Æ´an daÆ™iÆ™u,sannan yace yana shafa lips É—inta”baby me ya sameki bayan bana nan?ina can jikina ke bani kamar kina cikin damuwa kuma gashi nazo naganki ba yadda na tafi na barki ba,oya tell me”ya Æ™arasa maganar yana Æ™ara matseta a Æ™irjinshi.
Ƙara narke mishi tayi,cikin kukan shagwaÉ“a,tace”ba daddy bane yasako wani turare in naji Æ™amshin se amai yay ta zuwa min,wuni nayi inata amai”ta Æ™arasa maganar kwalla na biyo mata fuska.
A gigice yace “what!!!shi daddyn meyasa yasako abinda bakya so,yabarmin ke kinata amai,da mummy ce ze sako ne?”ya Æ™arasa maganar yana shafa gadon bayanta.
“ina fa ze sako rasa kunya,”mummy dake zaune kamar gunki ta bashi amsa.
Da sauri yakai dubansa gunta shi se yanzu ya ganta tun bayan shigowarshi,akunyace ya saki zahra ya ƙarasa gaban mummyn ya durƙusa yana sosa ƙeya.
Itama zahran bayanshi taje ta rakuɓe tana leƙo mummyn.
MiÆ™ewa mummyn tayi,tana murmushi tace”to daddy de besan matarka nada cikin da beson Æ™amshin turarensa shine yasa ya sako,ay masa afuwa”
Da sauri suka dibi junansu sannan suka kai dubansu gun mummyn,bakin Hammad har harÉ—ewa yake yace”mummy nufinki zahra nada ciki ko me kikeson kice?”
“kwarai tana da ciki,É—azu na dibata na tabbatar da hakan,se akula iyayen rawar kai,kuma ku tashi ku bar mana gida,dan Alhaji yasamu sukunin saka turaren dayakeso batare da anga bekensa ba”ta Æ™arasa maganar cikin sigar zolaya.
Wata irin runguma hammad yayiwa zahra hawaye na biyo idonsa,ya kasa cewa komai,se hawayen da yakeyi.hamdala kawai yakewa Allah,daya nuna masa wannan lokacin da baze taɓa mancewa ba.
Rarrashinshi zahra take da kyar yayi shuru ya É—ago idonsa yana kallonta,dariya yake ya kamo fuskarta yace “tnks you baby,tnks you,kim bani farinciki da yawa arayuwata wanda baki baze iya gode miki ba”
Kai kallonshi yayi gun mummy dake tsaye tana kallonsu cikin so da Æ™aunar ganinsu atare,yace”mummu ladan albishir da kikamin , zan siyo miki G-wagon 2020 ladan albishir”ya faÉ—i yana murmushi.
“Allah yay muku albarka ku tashi ku tafi gida kar dare yayi,zan ayko muku da breakfast”
Miƙewa sukayi,zahra ko wacce tunda akace tana da ciki wata mahaukaciyar kunyar mummy ta kamata,se ɓoyewa take a bayan hammad.
Mummy wucewa tayi ta ƙyalesu,ay tana gama ficewa Hammad ya manna bakinshi kan na zahra yashiga kissing da saurinsa kamar zaa kwace masa ita.
Seda taga yaÆ™i sakinta ne tasa mishi É—an kukan shagwaÉ“a,da sauri ya saketa yana faÉ—in”am sorry baby,muje gida ingaisa da babyna”yana kaiwa nan yaja hannunta suka fice bayan ta É—auko mayafinta.
Ko a mota hannun Hmmad nakan cikin zahra yana shafawa sosai ƙaunar zahra da cikin jikinta ke ƙara ratsa zuciyarshi.
Muje zuwa
Surbajo for life.
[1/9, 8:19 AM] Zahra Surbajo:
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
*Zahra Surbajo*
*sabon littafina shimfiɗar Aurena na kuɗi ne 500 kacal ki turo ki samu damar karantashi yana ƙunshe da sirrika masu tarin yawa,wanda se kin biya zaki ci ribar hakan,karki bari a sato miki ki karanta,500 ɗinki ta biya miki buƙata*
*zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*Aturo shaidar biyan tanan,banda katin waya ta acct kawai 07044600044*
Post a Comment for "Tayi Min kankanta 38"