Tayi Min kankanta 37
37*
“ke har yanzu baki girma da haye min cinya bane?”mummy ta faÉ—i tana shafa kan zahra.
Dariya tayi sannan ta Æ™ara gyara kwanciyar tata,tace cikin shagwaÉ“a”kai mummy,nawa nike gaba É—aya na,naga har yaya ma hawa yake wani lokacin”
“ay duk kun dena hawamin,ku kawomin jikokina su hau”mummy ta faÉ—i cikin nishaÉ—i.
Shuru zahra tayi,batace komai ba se murmushi.dan batun ya bata kunya.
Suna nan zaune a falon daddy ya shigo falon se Æ™amshin turare yake irin nasu na manya,yana ganin zahra yace cikim fara’a “yau ,zahran tawace agidan nan ah lalle mina da babbar baÆ™uwa”
Zahra wacce tun shigowarshi data shaƙi ƙamshin turarenshi zuciyarta ta fara tashi daurewa kawai takeyi,
Guri daddy ya samu ya zauna,sakkowa zahra tayi domin gaisheshi,amma ina aman daya yunƙuro mata be bata damar yin hakan ba.
Tuni ta gama É“ata gurin da aman,hankalin mummy da daddy ne yayi mugun tashi,mummy riÆ™e take da ita,daddy na jero mata tambaya”zahra me ya sameki dama baki da lafiya ne?”zahra ba baka se ido,ga wani sabon yunÆ™urin aman tanayi,
Kamata mummy tayi ta kaita ɗakinta,kai tsaye ruwan wanka ta haɗa mata,ta rakata har toilet ɗin ta rufo mata ƙofar.
Masu ayki mummy tasa suka gyara gurin,daddy kuma É—akinshi ya wuce yayo wanka,yasako jallabiya sannan yadawo É—akin mummyn.
Ay yana shigowa zahra taji ƙamshin turaren da gudu ta kuma komawa banɗakin,ta fara kyalaya amai,bin ta mummy tayi da sauri,ta riƙeta har ta gama,ta wanke mata baki da fuska,sannan ta kamota da nufin su fito.
Cogewa tayi a toilet É—in ta marairaice fuska tace “mummy ki barni anan turaren daddy ne bana son Æ™amshin shi,shine yake sani aman nan”
Wani farinciki ne ya ziyarci zuciyar mummy wanda rabonta da jinshi tun lokacin data samu cikin surayya,wanda har a fuskarta seda ya bayyana.
Sakinta tayi ta fito bakinta a washe,daddy dake zaune zaman jiran fitowarsu kallon rashin fahimta yake mata, yace”hajiya ina É—iyar tawa kika barota kikazo nan kina min dariya?”daddy yayi tambayar cikin É—aurin kai.
Dariya mummy tayi sannan tace”Alhaji to ay kai jikan naka kaine baya yi dakai,dan turarenka ne ke sawa yake wahalar maka da Æ´ar taka”
Janyota yayi jikinshi,yana murmushi yace cike da faraa”kina nufin zahra ta cikine da ita?”gyaÉ—a mishi kai tayi tana dariya.
Rungume mummy yayi cike da faraa,yana sumbatarta a goshi yace”tukuicin wannan albishir hajiya,zan sauya miki mota”
Sosai mummy ke godiya,daga haka sakin ta yayi yabar É—akin,fanka mummy ta kunna,ta buÉ—e windows,turaren yagama fita,sannan ta kashe fankar ta kullo windunan,ta koma toilet É—in ta kamota suka fito,ta kwantar da ita akan gado.
Abinci mummy tasa aka kawo mata taci,tasha ruwa,sannan mummy ta É—ibi jininta sannan ta bata Æ´at kwalba tayi fitsari aciki .
É—akin data ware a mazaunin asibitin tafi da gidanka ta nufa,taje ta gwada komai dan ta tabbatar da hasashenta,ayko sakamako na fitowa cikinne.
Sosai mummy ke godiya ga Allah daya ara mata tsawon rai na ganin wannan lokaci.
Hammad ko nacan cikin abokai anata chapter,jikinshi ne yaji be masa daɗi kewar matarshi duk ta dameshi,hakanne yasa yayi musu sallama gefin magriba,ya tuƙo motarshi zuwa gidan iyayen nasa.
Muje zuwa
Surbajo for life.
[1/7, 12:29 PM] Zahra Surbajo:
*TAYI MIN ƘANƘANTA*
*Zahra Surbajo*
*SHIMFIÆŠAR AURENA,na fara posting free page,wanda zanyi daga É—aya zuwa page 15 duka free,kiyi Æ™oÆ™arin biyan kuÉ—inki akan kari,kar ayi babu ke,ze nishaÉ—antar,faÉ—akar,wa’azantar,daku masu karatu,shikaÉ—ai ne irinsa beda na biyu, shi É—in na musamman ne 500 kacal*
*Zahra muhammed nasir 2084024749 UBA*
*07044600044 a turo shaidar biya tanan*
*masu tambayar ta littafi,ko sabo ko tsoho shima ki biya 500 din zan turo miki,masu cewa insasu a group shima ki biya 500 É—in zan saki*
Post a Comment for "Tayi Min kankanta 37"