Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Rainon Soja 14

*️RAINON SOJA️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*

 


Page 14
______________________
*Alhamdulillah mun dawo daga É—an gajeren hutun da muka tafi na kawo maku Cigaban wannan littafi Mai taken rainon soja…ina fatan Ubangiji Allah ya bani ikon kammalawa cikin aminci kaman yanda muka fara. Don Allah kar ki karanta ki fitar mun , haka duk wacce ta karanta bata biyani haƙƙina ba ban yafe ba…ga masu buÆ™atar payment regular group ₦500…Vip group ₦1000… Special payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 ko katin MTN ta Wannan number na sama Æ´an Niger katin Artel 500f.*
________________________

Don haka Ma’eesha ta isa munzalin da Mutum kamar ka koda na kirki ne bai kamata ya shiga jikin ta bare kuma kai . Khalil ya Æ™are maganan tare da shan kunu yana haÉ—e giran sama da Æ™asa tamau. Kallon sa Ali haidar yayi yana sakin wani shu’umin murmushi kana ya kauda kan sa can gyefe yana duban inda Ma’eesha take itama idanun ta akan su , don zuciyar ta ya bata da akwai wani abun ne shi yasa Khalil ya dirko daga saman bene hawa na É—aya . Ganin kuwa yanda fuskar sa tayi tamau yasa ta Fahimtar tabbas da akwai abun da Ya shiga tsakanin shi da Ƙanin nasa .

Ganin yanda Ali Haidar yayi masa banza yasa Khalil Æ™ara fusata nan ya cigaba da cewa“Miskilancin banza da wofi wurin iskanci kafi kowa shahara ”.

Dariya Aliyu yayi yana shafa sajen fuskar sa tare da cewa“ Khalil kenan! Wai duka wannan sababin saboda Kawai hugging É—in Ma’eesha da nayi daga faÉ—i Kasan da zata yi shine kake ta wannan maganganun….kaman ta waye Ni Ali Wacece kuma ma’eesha a tare dani? . Maganan lalata mata da kake yi ai wannan ya isa ya tabbatar maka da cewa Ni Lafiyayyen namiji ne. Sannan mene zanji a jikin wannan Yarinyar? Ka dube ta fa ka gani Æ™wailah da ita mene zanji a jikin ta ya Khalil.

Ni kake faÉ—a mawa magana? Khalil yayi magana yana takowa daf dashi don Zuciyar sa ya fara tafarfasa .

Juyawa Ali haidar yayi yana Æ™ara kallon É“angaren da Ma’eesha take kana ya Juyo yana zuba ma Khalil Lulun idanun sa . Cike da Miskilalliyar Muryar sa ya furta “ Kaci albarkacin ta bana so muna saÉ“ani a gaban ta…don Allah ya Khalil mu daina irin wannan Abun yanzu , Kar ka manta tun muna yara muke samun matsala akan ma’eesha a yanzu ne har ka nuna kasan darajar ta? . ÆŠaga kafaÉ—a yayi alamun bai dame shi ba . Yana juyawa tare da wuce Khalil da ya tsaya yana kallon sa .

Takawa yayi yana isa inda Ma’eesha take sai raba ido take don tsoron sa Ma’eesha keji Æ™warai da gaske .

Wuce ki bani wuri!

Ya furta fuskar sa babu alamar wasa ko sakewa. Sum-sum ta juya tana wucewa tare da bashi wuri . Ya Khalil ina kwana . Ta furta da Sauri tana raba shi ba tare da ta jira Jin amsar da zai bata ba . Cike da fara’a ya furta lafiya lau Ma’eesha maza ki yi break fast .

Takaici ne ya kama Aliyu , Humm Wai me Khalil yake nufi ne? Son Ma’eesha yake yi ko mene? Zuciyar sa ta fara masa wannan tambayoyin. Saurin Girgiza kai yayi yana cewa “ a’a Sam ba haka bane ba , don Khalil a wannan watan za’a sanya baikon sa da Rahama. To mene wannan tijaran nasa yake nufi kawai saboda nayi hugging É—in ta. Ya manta Meye ban sani ba na jikin Ma’eesha. Hattara tsarki Ni nake yi mata amma a yanzu yake faÉ—a mun munanan maganganu….ko yana tunanin ina jin wani abu dan gane da ita…Aikin banza sai na shayar dashi mamaki tare da shi za’a yi mana baiko dole na fidda É—aya a cikin biyu , Maryam ko Mimi. Hummmm….sauke numfashi yayi mai huci kana ya cigaba da maganar zuci da cewa “ Duka ba zaÉ“i na bane….Mami ke liÆ™a min su , a wannan karon i must accept it. Dole na zabi É—aya don na Æ™aryata tunanin Khalil akaina da Ma’eesha………….✍

 

Tom kunsan night update Babu yawa mu tara ana safe lafiya….muje yanda al’amarin zai kasance . Shin waye Mimi??? Sannan kuma Wacece Maryam? Wacce a cikin su Ali gadanga zai zaÉ“a ya kuke kallon wanga tafiyar……ku Cigaba da biyo alÆ™alamin mamanteddy✍ . Yau inshallah zamu bude Comment GRP don jin sharhin ku bisa ga wannan labari na rainon soja…….!

Post a Comment for "Rainon Soja 14"