Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Ni da Almajirina 9


NI DA ALMAJIRINA
(Our Incomplete Story)

Episode 9

A BIG THANKS TO MY SUPPORTIVE READERS

Yar baiwa tawa
Mrs Suleiman
Sofiyah Muhammad Abdullahi
Umu Afrah
Mum Khadijah
Maman Nabila
Ibar Hlamu
Fatima Musa
Ummu Shureim
Mrs Sadiq
Da sauran su HajjahKaka na gaisuwa 藍 kuma tana godiya ga masu COMMENTS AND SHARING 殺

Suna cikin magana kawai suka ji wani kara me firgitarwa, ba shiri aka fara darewa, kafin kace me an watse, ga gari yayi duhu sabida hadari, Atine taki fita wai dokiyoyin ta na gidan.

Babagana yace ummu Atine rayuwar ki ya fi dukiyar ki, don kibar nan kafin su karaso.

Kunen kare Atine tayi ta shige dakin da kayan lefe suke hade da akwatin sisin gwal, tana kokarin fito wa taji karan bindigogi cikin gidan, sumar tsaye tayi,

Suna shigowa ciki Babagana yayin yaren su na jeji, cike da mamaki suke kallon sa, kafin daya daga cikin su yace idan dagaske kana cikin sojojin jihadi miye ya kawo ka cikin gari kuma waye Amir dinka?

Babagana yace nazo salama ne da iyayena, yana fadin haka suka fara harbin sa harsai da suka farfarsa jikin sa da alburushi,sun san da cewa duk wani sojan jihadi ba abashi damar zuwa ganin iyaye ba, sun harbeshi ne sabida suna da tabbacin guduwa yayi

Atine dake tsaye kamar bishiya duk ta hada zufa, sukai awon gaba da ita, har da dukiyoyi,
Ruwan sama akeyi kamar da bakin kwarya amma gadan da zai kai ka Nijar cike yake da gawakin mutane, sun deba na diba sun kashe na kashewa, indai kai Namijine harbi ne,

Kai tsaye suka nufa Zauren Malam Garba idan suka fara sanarwa da cewa
“Ya ku almajirai wannan zaure ku fito Ya Amir yayi kira da ku zo ga sojojin jihadi, kunyi daurin kai a farko kunki bin mu amma wannan wata dama yake baku.

Malam Garba yayi hijar tun jiya zuwa wani qauye tare da manya Almajiran sa. Sauran Almajiran sa dake zauren cike da fargaba suke. Sun san ko basu fito ba za a iya kashe su, rabin cikin su suka fito, ko bata lokaci wajan kashe Almajiran ba suyi ba.. suka tafi da sauran Almajiran dake cikin zauren malam.

Fadar Ya Amir
Kabarori ke tashi gani nasarorin da suka samu acikin hour uku kacal, ba iya Nigeria ba duniya gabadaya yau ta san da zaman su…

Meeting na gaggawa Ya Amir ya kira sauran Amirs dake under him
Without any hesitation su ka hadu a cikin fadar Ya Amir

Bayan godiya da jijina Ya Amir yace zan yi tafiya na dan wani lokaci a dalilin Nasara da muka samu. Na samu babbar gayata dan haka zan daura amintace kuma hazaki kan kujeran mulki na, har na dawo inaso Kamar yadda kuke girmama ni ku girmama shi, duk da nasan da cewa duk kun girmesa, na rada Amir Auta, da ya cigaba da gudanar da kome har idawo na.

Kabara wajan ya dauka, cike da mamaki Baana yake ganin cewa shi aka rada.
Ya Amir ya dauko map da sauran takardu ya damka a hanun Baana, sannan yace aikin ka ya fara yau Auta, za a kawo ma yammata hudu dan sabon sarki sai ga sabon jini. Ya Amir yayi maganar yana me dariya sauran duk suka bishi suna dariya

Baana yayi saurin ce wa matata ta ishe ni Ya Amir, bana bukatar ko wacce mace.

Lalle Auta har yanzu kai yaro ne, matar ka daban yammatan hutawa daban asan ko wani sarki da kwakwara, kayi shaanin ka lokacin ka ne, kuma kafin na dawo inason naga jinin ka Auta.

Nagode Ya Amir ni bana bukatar ko wacce mace,jiki na da ruhi na duk na Falmata ce, Baana yayi maganar da dukan gaskiya…

Tunda ka fada haka yau dole ta taya ka farin ciki, kuma a yau nake son rabo ya shiga tsakanin ku da ita. Ya Amir yayi maganar a fusace..

Ya Amir ba yau ba kuma ba gobe ba, zan jira ta harsan da ta aminta dani Baana yayi maganar cikin girmama wa.

A hassale kuma a kausashe Ya Amir yace a yau nace kuma umurni na baka ba nema shawara ba. Yana fadin haka ya fice a fusace sauran duk suka bi bayan sa..

Ina kwance har yanzu nazarin shawarar HajjahKaka na keyi, kawai wasu mata biyu suka shigo dakin ba tare da ce dani kome ba sukai awon gaba dani, ba irin ashariya da HajjahKaka ba ta dura ba amma ko ajikin su.

Wani gadon sarauta suka ajiye sannan suka juya suka tafi, ba abin da zuciya keyi illa dukan uku uku, ina cikin raraba ido kawai naga mutum tsaye kaina da ga shi sai boxers, ban san lokacin dana kwalla ihu ba tsabar tsorata da nayi, ganin yana zuwa daf dani yasa na fara ja da baya ina kare masa kallo, ashe kaya ke boye sirrin jikin Baana? Sai kace wani wrestler (Roman Reings)

Don Allah Baana…..

 

Pharteema(DMK)
THANKS

Post a Comment for "Ni da Almajirina 9"