Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Ni da Almajirina 7


NI DA ALMAJIRINA
(Our Incomplete Story)

Episode 7

_MASU TSORON YIN COMMENTS KUYI ABIN KU I GOT YOUR BACK_ 

(NI DA ALMAJIRINA alkalamin zai koma hannun star din kamar yadda aka bani shawarar yin haka)

Saide karan ihun ba inda ya je sai cikin bakin Baana, bai bani damar motsi balle na samu damar kwatar kai na, he took control of me kamar wani beast.

Mutuwar tsaye nayi tsabar girman wannan lamarin, na tambaye kaina shin nine bakina cikin bakin ALMAJIRINA? Ko dai mafarki na keyi? Kai bana tunanin Mafarkina zai kawo min wannan lamarin balle kuma a zahiri, tun ina iya jin fitar numfashi har na daina..

A hankali na bude idanuwana dasu kayi min nauyi ina bin ko ina da kallo, abin mamaki sai ga ALMAJIRINA zaune ku sa dani? Sake runtse idanuwa na, nayi da tunanin cewa wani mafarki na sake shiga shiyasa na gansa, amma ko da na sake bude ido yana zaune a inda yake.

Fashewa nayi da kuka me kona zuciya, da kyar na iya bude bakina nace Baana yanzu da wannan zaka saka mana?
Ka tuna yadda mu ka rike da amana, da ci da sha sutura duk yana wiyan mu amma shine zaka yi min haka Baana?

Cikin sanyi murya Baana yace Hajjahna bana nufi ku da kome sai alkhair..

Will you shut up? Nayi magana da dan sauran karfina,ina kokarin mikewa daga kwance da nake amma sam na kasa tsabar yadda gabobina suka ririke.. Sakin kara nayi kafin na koma na kwanta.
Baana if what you said is true, Don Allah ka harbe ni yanzu kawai na mutu, nayi magana ina mai zubar da hawaye tunanin cewa NI DA ALMAJIRINA ne zaune haka kade ya isa zuciya ta, ta bugu tsabar bakin ciki.

Hajjahna ina son ki, ni me kaunar ki ce, tun farkon ganin ki na kamu da sonki, Hajjahna ki dena kiran mutuwa, dan bana tunanin zan iya rayuwa baki.

My jaw almost dropped out of shock, I just can’t believe what my ears, wai ALMAJIRINA ke futar kalmar so a gare ni?

“Zan mayar dake gun HajjahKaka amma Don Allah ki dena kiran ma kanki mutuwa.” Maganar da yayi ne ya dawo dani daga duniyar tunanin na, Baana ka Sani ko baka kashe ni ba, ni sai na kashe kaina.

A hassale Baana ya mike yace kina kashe kanki zan kashe kowa naki harta Musa Buzu, idan kina son mahaifin ki da kanin ki su rayu, to ki zama a raye, Baana yayi maganar ba alamar wasa, indai ina a raye kema sai kin kasance a raye, dan Baana ba zai rayu ba sai da Hajjahnsa.yana gama fadin haka ya cucumo ni kama wata yar jaririya ya fita da ni daga dakin be tsaya a ko ina ba sai bukkan da HajjahKaka take, tsawata min yayi da na shige ciki, ba shiri na dinga takawa kamar wata me koyan tafiyar har na isa inda HajjahKaka take zaune tare da Ya Amir.

Sakin salati HajjahKaka tayi hade da fashewa da kuka, ashe kina a raye, yanzu wannan munafikin bakin nan, kece min wai kina nan lafiya Falmata? Amma ya na ganki haka kamar wacce akayi wasan kura da ita..?

Da saurin karfin da ya rage min na karasa gun HajjahKaka ina me fashewa da kuka, HajjahKaka ki ta yani da addu’a ko Allah zai amsa rayuwa ta yanzu na huta?

Falmata ban gane ba? Ya naji kina warin maza? Warin gawasa nake ji a jikin ki? Karde ace sun keta miki hadin ki? HajjahKaka tayi maganar cikin tsoro..

Ya Amir yace wa ko zai mata haka? Mata da mijin ta? Ai HajjahKaka tun jiya tana rugume jikin mijin ta, yayi maganar yana wani shu’umin dariya kafin ya mike, yace sai mun dawo.

HajjahKaka tace Allah ya tsine maku ya dibe maku albarka, marasa imani, a haka zaku mutu a wulaqance, yanzu yarinya nan guda nawa take da zaku farma ke ta? Ai da kashe ta kuka yi da wannan abu?

Murmushi Ya Amir yayi kafin yace HajjahKaka, ba abinda bakin zai yi akan mu, na barku lafiya, Amarya sai mun dawo ko?

Shege da duwawu kamar na huran biki, baki kamar an banka ma jakar petir wuta, in shaa Allah, a wulaqance zaku mutu, Allah sai ya saka mana, har ya fice HajjahKaka bata dena dena dibe masu albarka ba.

Ni gabadaya hankalina baya gun su, abinda ALMAJIRINA ya fada yake ta dawomin, zai kashe mahaifina da kanina indai na kashe kaina?

Ke kiyi magana ko hankalina ya kwanta? Abin manya su kai maki kika koma haka ko miye? Tashi na kalle ki da kyau, HajjahKaka tayi maganar tana kokarin ta gani daga jikin ta.

Hawaye kawai ke zubowa uncontrollably… Na rasa ya zanyi da rayuwa ta, kiran suna na da HajjahKaka keyi yasa na mike, ta kare min kallo, can tace bakon watan ki ya zo ko? Da kai na amsa mata.

Falmata amma dudda haka kina wari maza, karde ace wani gardi ya more jikin ki? Tayi maganar tana kallon kayan dake jikina, dan uniform da ke jikina amma yanzu ready made gown ne, Jan rigar sama HajjahKaka tayi tana kallon cinyoyi na, kafin ta saki rigan tace Alhamdulillah babu abinda su kai maki

HajjahKaka Baana shine Ango… Na karasa maganar ina mai fashewa da kuka mai cin rai.

HajjahKaka tace wana Baana ne Ango? Kuma Ango wa?

Bakina na rawa nace wai ALMAJIRINA shine ya bada sadakina..

Sakin salati HajjahKaka tayi kafin tace yanzu Baana dama training da yake zuwa na yadda zasu duk tarwatsa rayuka da dukiyoyin al’uma ne? Kai mugu beji dadi ba, kuma mugu bai da kama, yanzu wa ze yarda cewa Baana ze iya kashe ko da bera bare kuma mutum.
Yanzu Falmata kina nufi a kirjin sa kike tun jiya?

Cikin takaici Falmata tace kirjin wa? Gara na mutu da wannan kazamin ya taba jikina, tunawa tayi da kiss jiya tayi saurin tofar da miyau.

HajjahKaka tace yanzu wannan murdeden katon ne ya aure ki? Yanzu bama wannan ba sai ya iya ce zai kwaciyar aure dake? To ai wanna sai de ya kashe ki dan…

Cikin kuka nace haba HajjahKaka ina gaya maki cewa Baana shine Amir amma ke maganar aure kike yi, bazan taba yarda na zama matar sa, saide ya kashe ni walh, ta Yaya ma za ace ALMAJIRINA shine mijina? Hankali ma baze dauka ba.

Tagumi HajjahKaka tayi ta kafe ta da ido, can tace to yanzu dai tudan Baana ya kwalafa rai akan ki sai da yasan yadda yayi aure ki, to wannan auren bai auru ba, yana ina? Yau ko ni ko shi yau, ki dena zubar da hawayen ki a banza, walh yayi kadan yace zai zama Ango, Baana yaushe ya zama mutum da har zai tunanin zama Ango chab ai saide ya harbe ni.

Ya Amir na barin dakin ya iske Baana tsaye yayi zurfi cikin tunani, Auta?

Kiran da Ya Amir yayi masa yasa ya dawo daga duniyar tunanin sa, ya amsa da naam Ya Amir?

Ka samu biyan bukata ko ka tsaya cutan kanka? Na gaya maka sharadar wannan aure, tunda Amir ya bace dole mu samo wani Amir daga sarkon ka, dan rashin Amir yayi min zafi Auta.

Ya Amir so nake na saye zuciyar ta, kafin na zama mallakin ta, ina son Falmata fiye da yadda nake son kaina..

Kana nufi kafi sonta a kaina Auta? Ya Amir yayi magana cike da mamaki maganar sa.

Aah Ya Amir, kai ka bani rayuwa ita kuma itace rayuwa ta, bazan iya rayuwa baku ba, zan iya sadaukar da kome akan ku.

Murmushi manya Ya Amir yayi kafin yace shiyasa nake son ka gaje ni Brainbox, amma ka Sani cewa Soyayya na saka rauni a zukatar maza, ban so soyayya ta sa ka koma ragon namiji Auta.

Sauke ajiyan zuciya Baana yayi kafin yace ragon namiji na office mu ko jarumai muna jeji.

Ya Amir yaji dadin wanna maganar ta Auta, shiyasa ya mayar da shi na hannun daman sa, yake daura shi gaba a wannan harkan.
Can Ya Amir yace yau za ai ruwan sama a Damasak ina so mu kwace garin, yadda zai jawo hankalin gwamnati akan mu dan su yarda da negation.. ?

Ya Amir negotiations tsakanin mu da gwamnati ba yanzu ba, sai mun karkato da hankali duniya akan mu kafin zamu fara zama da gwamnati..

To shikenan Auta, magana mutane da aka kama, zamu zabi masu karfin cikin su ayi training insu wajan hade makamai ko ya ka gani? Matan kuma sai su zame mana abin nishadi…

Aah Ya Amir ban da cin zarafin mata, dade ka ajiye su a madafa da kuma wajan dinki, da muna bukatar sabbabin kayan sawa, yanzu bara na kira Damasak command naji harsashen sa.

Ya Amir yace Auta kaje kaji da Amarya ka ni zan tsara komai, ka bata rubutu zaka samu kanta cikin sauki.

Ni nafi so ta so ni dan kanta ba tare da nayi mata wani abu ba Ya Amir. Zan ta bin ta har ta amince dani. Yayi maganar kamar yana da tabbacin hakan, yana gama fadin haka ya nufa hanyar bukkan dasu Falmata take..

Ina kwance rijib da luluba, HajjahKaka na kusa dani sai tofin addu’a take min, kawai sai muka ji..

 

Pharteema(DMK)
THANKS

Post a Comment for "Ni da Almajirina 7"