Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Ni da Almajirina 6


NI DA ALMAJIRINA
(Our Incomplete Story)

Episode 6

Jin mirya dake yawo cikin kunnen Falmata, yasa ta dago da manya manya idanuwan ta, ta daura a samar fuskar, kallon mutum dake tsaye ta tsaya yi cike da mamaki, ganin cikaken namiji mai kiran jarumai, cikin white slung long pants and turtle neck sweater, ga kasuban dake kewaye a fuskar sa, kallon tsaf tayi masa but zuciyar ta, ta ki yarda da abin da idanuwan ta ke nuna mata.
“A hankalin Falmata tace ALMAJIRINA?

Bata san kalmar ya fito ba, sai ji tayi yace naam Hajjahna?

Gaba daya nima tsayuwa tayi ya gagara, kawai ta sulale kasa tana mayar da numfashi kamar taga dodo, da kyar ta hadiye wani abin mai zafi da daci a makogaron ta, kafin ta sake kallon sa, tana mamakin yadda ya canza kamar bashi ba… Can kuma ta tuno da wani abu ta mike a hassale ta nufi idan yake tsaye tace Baana?baice da ita komai ba, sai ma kallon ta da yake kamar ya hadiye ta.

Baana what the hell is going on here? Why are you here? Falmata tayi maganar kamar a kausashe.

Baana was driven by her, so bai ma san abin da ta ke cewa ba sai da yaji tace,
Ina magana shine kayi tsaye kikam kana kallo na,ido cikin ido?

Abin mamaki taga yana zuwa daf da ita, ganin haka ta fara ja da baya, ganin ta kusa faduwa yayi saurin riko ta gam to his body, kokowa ta fara yi na kwacen kanta..

Cikin sanyi murya Baana yace you’re having a fever Hajjahna, yayi maganar yatsan sa biyu na samar wiyan ta..

Cikin karfin hali ta samu damar kwatar kanta daga rikon da yayi mata, yanzu da kazamin jikin ka, ka tabani Baana? How dare you huh?

Matar da aka harba ta tsaya tana kallon ikon Allah ganin yadda Amir ya koma soko a gaban wanan yar figigiyar yarinya…

Wai ina magana ka zube ni da kallo ni sa’ar ka ce? Falmata tayi maganar cikin matsifa.

Ba tare da yace komai ba ya dauke ta in a bridal style, sai ka dauka jaririya ne ya dauka tsabar girma sa, tafiya ya keyi tana fizge fizge har ya isa wani Hut da wasu gardawa ke gadi, suna ganin, su ka basa hanya ya shige ciki, samar gado ya ajiye ta, tayi saurin mikewa ta wanke fuskar sa da mari har sau biyu, ganin ko gizau be yi ba, yasa Falmata questioning kanta
“Wai ko de ba ALMAJIRINTA bane wanna? Ko de an canza sa ne?

Ganin har yanzu ya kafe ta da mayun idonsa, ta tabbatar da cewa shine, dan ko a gida haka yake kallon ta, sai tayi masa tsawa yake cire idonsa.

Kiyi wanka sai ki ci abinci, zazzabin zai sauka, Baana yayi maganar a sanyayye yana kallon yadda ta rame tayi duhu kamar ba ita ba.

Wai kaine ko dai an canza ka ne? Dan ya canza gabadaya, kamar ba ALMAJIRINTA ba? Abin daure mata kai ya keyi, ko dai mafarki ta keyi? Tana cikin wannan tunanin Ya Amir ya shigo da fara’arsa yace Ga Amarya ga Ango, yau ranar Annuri ne..

Cike da mamaki Falmata take kallon Ya Amir kafin ta mayar da duban ta zuwa ga Baana, tana kokarin awna maganar da Ya Amir yayi? “Amarya Ango?”

Cikin fara’a Ya Amir yace Auta kayi abinda ya dace yanzu, kafin yammaci zamu tafi can, ka saki jiki ka angwace idan kuma ba kayi ba to ka san sauran bayani..

Cike da girmamawa Baana yace Ya Amir, indai sai nayi haka zan zama Amir me iko gara na Zauna a matsayi na, Ya Amir kawai a sake su, su tafi…

Murmushi manya Ya Amir yayi kafin, ya jawo hannun sa suka fita daga dakin..

Falmata dai gabadaya ta kasa fahimtar abinda su ka ce, ta na fahimta yaren bawai ba tayi ba, amma abin da suka fadi ne yasa kasa fahimtar komai, tana cikin wannan tunanin Ta, kawai ta gansa tsaye daf da ita, kokarin maganar ta keyi amma gabadaya bakin ta, yayi mata nauyi, idanuwan sa kade abin tsoratarwa ne, jin yadda ya fizgo ta, ta fado jikin sa, yasa ta kara tsorata da lamarin, bata tunanin ALMAJIRINTA ne wannan, ganin a rufo masu kofa dakin ya gwaraye da duhu ya sa Falmata sakin ihu sai de ba idan ihu ya je sai….

Pharteema(DMK)
THANKS

Post a Comment for "Ni da Almajirina 6"