Skip to content Skip to sidebar Skip to footer

Ni da Almajirina 5

NI DA ALMAJIRINA
(Our Incomplete Story)

Episode 5

AFUWAN AFUWAN PLEASE KUYI TA HAKURI DA NI 
BUT SHIN KUNA SON UPDATE KULUM AMMA BA TSAWO KO
KUNA SON UPDATE SAU UKU A SATI WITH 5 READ MORE?


Tun kafin suyi nisa a hakan rami sai ga doyi ya gaureye ko ina, tuni kowa ya fara toshe hanci sa, wasu daga cikin har amai suka yi but hakan baisa sun dena hakan rami ba har yakai dasu gan wani bakin abu a nannadae,umurni head din su yayi dasu fito da abin. Hakanan suka fito da abin baki tass kamar a kona jakar, dan ba wanda zai ce mutum ne..

Head yace kuna da kare ne a gidan?

Fanne da kanta ya na duke ba abinda take yi sai karanto addu’oi ta dago tana kallon gawan Buba cike da mamaki ganin ya koma kare, karen ma a kone,ba iya ita ba gaba da ya wanda Buba ya mutu a gaban su were shocked..

Ina tambaya ki kiyi banza dani ko baki jin yare ne nai miki da hausa?head yayi mata tsawa

Fanne tace eh eh, muna da kare
But a zuciyar ta tana mamaki mu’ujiza na Ubangiji, Tabbas babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Tabbas Allah abin tsoro ne da girmamawa
Ji yadda Buba ya koma tun a duniya?

Cikin hanzari suka mayar da karen suka rufe kabarin, sannan suka tasa su gaba
Abin da suka ganin head ya isar wa Auta da information.. iya mamaki yayi dan yana da tabbacin cewa gawar cousin insa ne kwance ciki kabarin.

Jin Auta yayi shuru baice dashi komai ba, head yace Amir umurni ka muke jira?

Auta yace na umurce ku daku bar wannan gidan sannan karku sake zuwa, duk idan Buba ya shiga zai dawo, yana fadin haka Autan ya yanke kira
Yana girmama abin al’ajabi

Kamar yadda Auta ya umurce su, ko minti biyar basu yi ba, suka bar gidan..

Hamdallah Fanne ta dinga yi, ganin sun qufuta daga hannun azuluman nan. Fanne tace kun ga hikima irin ta Ubangiji? Acikin kankani lokaci har gawar Buba ya zama wani irin mumunar hallita?
Tabbas Annabi mu yayi gaskiya akan girman iyaye da kuma zubda jinin mumunai bayin Allah a doran kasa.
Addua sosai Fanne su kayi kafin ko wanne su ya shige dakin sa.

Labarin ya fara kai cikin garin Maiduguri, wasu na karyata wasu kuma suna gaskata farmaka yankuna biyu da akayi lokaci guda.

Hazakkakiyar yar jarida wato Journalist Binta(Namecy) ba tayi kasa a gwiwa ba wajan ziyarta yanku na biyu wajan tattaro bayanin ta tare da crew inta,saide tana tsaka da aikin Boss inta ya kira ta da taba duk wani abu da da ta keyi ta dawo, bai bata damar sauraran ta ba, ya yanke kiran.

Rai bace Binta ta sanar da crew inta suka bar aikin suka koma ma’aikata The Daily Record dake cikin garin Maiduguri, kai tsaye Binta ta shige office din ogan nata ta same sa yana waya. Saisai white Tom Ford shade dake idonta tayi tana kallon takardu dake samar teburin sa.

Yana gama wayar yace “Bint?

Cikin respect Binta tace naam Sir?

Daga yau sai yau bana son kara ganin wani report sannan ki goge duk wani report da kika dauka a yau dinan.ogan Yayi maganar in a authoritative manner.

Sir walh na ganin da idona jita jitai gaskiya ne, idan akace we’re the first to publish and broadcast live we might save thousands of people out there.

A hassale yace Binta do you want to get yourself into trouble? Umurni daga sama ne, when the time comes damu Yan jarida zamu fara bada gudumuwar mu, za muyi but for now No.

Please Sir listen to me, the people out there really need the media and the attention of the world.

Keep shut and leave my office now! Ogan yayi mata tsawa da ya sa ta girgiza, rai bace tabar office din.

Falmata

Falmata dai idanuwar ta, na samar white paper da kudin dake ijiye gaban ta, fashewa tayi da matsananci kuka mai kuna zuciya.

HajjahKaka tace Falmata addu’a zamu yi tayi har Allah ya kubutar damu, amma mutanen nan sam ba Allah a ransu, kin ga wannan mai tsiyayen duwaiwai Amir yake ko ma wa, duk cikin su ba mugu irin sa, ba gwama ma Ya Amir yana fara’a ba?

Ni HajjahKaka kashe kaina zanyi na huta da wannan trauma, har yanzu na kasa daina ganin gawar Batula a zuciya ta, sannan ace mutane dasu kashe best friend na, su zan aura? Gaskiya is better I commit suicide and have a rest of mind.

Sakin baki HajjahKaka tayi tana kallon ta, can tace lalle Falmata baki je islamiya ba? Kin ko san hukunci wanda ya kashe kansa kuwa?

Cikin kuka Falmata tace Allah gafur-rahim ne, HajjahKaka idan mutuwa nayi ba zan iya haukacewa akan traumatic experience coz it’s hunting me down.

Kije walkiri na nan na jiran ki, Ato harsai kin gwamace nan, idan ma zaki cire yahudanci dake zuciyar ki, ki cire ki kama Allah, shi daya ne tak zai cire ki cikin wannan bakin ciki da damuwa..HajjahKaka tayi maganar tana mai tausayin jikar ta..

Fadowa jikin HajjahKaka, Falmata tayi tana kuka mai tsuma zuciya, a haka har wahalaliyar barci yayi awon gaba da ita…

Ko minti goma ba tayi ba, wasu mata suka shigo dakin, ba tare da bata lokaci ba suka ajiye abinci mai yawa, da yaji naman kaji gaban HajjahKaka,

HajjahKaka tayi maganar cikin matsifa tace lafiya zaku shigo mana ba salama?

Mun zo biko ne matan sukai maganar kai tsaye.

Biko uwar ku dai kuka zo ba dai na jikata ba, maza ku kwashe tarkacen ku, ku bar nan.

Ciro bindiga daya daga cikin matan, tayi ta daura a samar goshin HajjahKaka tace, idan ba ki kame bakin ba sai na karar da alburushin nan a jikin ki,

Firit Falmata ta kama bindiga ta daura a samar goshin ta, tace please ni zaki harba ba ita ba, ki tausaya min Don Allah ki harbe ni na huta da wannan bakin ciki..

HajjahKaka tace Falmata kul na hane ki da wannan batun, kina kallon masu kama da kafuran farko ba imani ne dasu ba.

HajjahKaka ki sa baki ta harbe ni, gara na mutu da zama cikin su, Falmata tayi maganar cikin kuka mai cin rai..

Daya daga cikin matan tayi masu alama dasu fice daga dakin, mayar da bindiga wacce ke rike da bindiga tayi, kafin suka bar dakin, bin bayan su Falmata tayi tana mai rokon su da su harbe ta, har suka fita sararin jejin, daya daga cikin matan tace juyo a fusace ta wanke fuskar Falmata da tagwayen Mari nan take Falmata ta zube a kasa, saide bata kai da sauke hannun ba taji bullet ya shige kafarta, ba shiri ta zube a kasa,

Falmata da taji karan bindiga ta dauka ita aka harba, amma sai ta ganta tana numfashi, amma kuma ga jini na kwance inda take, a hankalin ta dago ta kalli Matar da ta mare ta kwance rike da kafarta da ya tarwatse sai jini yake bubulowa..

Amma mata sai awkin ba wanda yake tsaye hakuri take yi cikin yaren Kanuri, cike da mamaki Falmata take, dan tana gane yaren mayarwa ne ba ta iya ba, but the shocking jin

Masculine voice ya furta cewa akan Falmata zan iya kashe kowa Adijan, wa ya baki izni ki daura hannun ki a fuskar ta eh?

Jin mirya dake yawo cikin kunnen Falmata yasa ta dago da manya manya idanuwan ta, ta daura a samar fuskar….

KO WAYE FALMATA TA GANI 樂

 

Pharteema(DMK)
THANKS

Post a Comment for "Ni da Almajirina 5"